Basan Raina Bace Complete Hausa Novel
Reading file: Basan Raina Bace Complete Hausa Novel.txt
Chapter 2 of 17
__"to Malam *BASAM* naji masoyanka sunata fadin kayi kuka awajan taron domun yadda suka gani a mujallah. Komenene dalilin kukan naka?,'
___" amm alokacin nikaina bansan sanda kukan yazomunba domun taron jama'ar Dana gani wadanda sukazo daga kasa kasa gwamnoni da sarakai hardama sugabannin kasashe gakuma kyaututtuka danaketa karba daga wurare dadama so kukan murnane kawai nayi.'
Daria sukasa dukka,'
___"to Malam, *BASAM* Naji anacewa daganan kaitsaye filin jirgin kasa zaka wuce zuwa wacce kasa nadai namanta kozaka iya fadama masoyanka wacce kasa zakatafi.,'?
Murmushi yayi tareda dago idanunshi farare yace,'. __ " amm gaskia ne zanje Istanbul ahalin yanzu saura minty talatin jirginmu yatashi wani aikine da'aka turamu zamuyi nida abokan harkata wato Yan group dinmu uhm,'
___"to mungode Malam,' *BASAM* duka duka anan mukakawo karshen shirinnan saidai kamunnan zamu bude akwatin wayarmu domun karanta sakonnin masoyan *BASAM*
Nan yabude akwatin wayarsu sakonni kala kala aka karanta iya wanda za'a iya yayinda akabar sauran
___"to jama'a amadadin Gidan TV ni bala yunusa shu'aibu nakecemuku sai Allah yasake hadamu awani zangon nagaba,' ko bakonmu yanada Wanda yakeso yagaisar?',
___"well ina gaisuwa ga family dina Musamman kakata. Nasan tana jina tana ganina I'm gonna miss u Ummu sai mom dina ina gaidata tareda sweet sister Na kausar love Saikuma Beb dina itama danasan tanajina kuma tana ganina I so much love u Bby,'. Saikuma dukkan fan's dina love u oll,'
___"to masu sauraranmu laifin Dadi karewa amadadin yidan tvnmu daya sadamu daku ni bala yunusa shu'aibu tareda bakonmu *BASAM B SALEES WANDA AKAFI KIRANSHI DA BB,' mukecewa muwuni lafiya bissalam,'
Ummu tace,'. ___"wayyo sungama allah to yakiyaye maka hanya megidana nakaina,'
Kausar tace,'. ____"nima wlh tunyanzu nasoma missing dinshi tunkamun yabar kasarma,'
Daria Momy takeyi musu tace,'. ____"kukam zanga sanda zaku saba ace kullum indai babu *BASAM* agidannan kundinga missing kenan gashi shiba mazauniba daga wannan kasar zuwa wancan kasar,'
Ummu tace,'. ___"uhm munsani shakuwace kawai tasamu muje kewarshi,'
Wayar Momy tayi kara aikuwa kausar takwace wayar tayi magana da yaya *BASAM* sannan tamukama Ummu sukayi magana sai Momy akarshe sallama yayi musu tareda ajjiye wayar tashi.'
Kaitsaye motarshi tashiga harabar airport din yafito dawata katuwar jaka arataye abayanshi yanufi Yan clup dinshi dukgasunan a zazzaune nanfa akashiga gaisawa tareda dan taba hira kowa yanajida kanshi cewar shi gwanine wajan iya tseren doki,". Wayar*BASAM* ce tashiga ruri ahankali yamike tareda .atsawa gefe,'
___"hello hot milk yaya akayine yakike kuma kinadai lafiya ko?,
Cikin muryar damuwa tace,'. ___"heart beat ina lafiya sai missing dinka danasomayi tunyanzu naga hirarku tayi Dadi I love u my heart beat ina alfahari da iyawarka,'
___"come on Bby girl relax just smile bawani dadewa zamuyiba just 2 week's zamu dawo kinji banaso kina damun kanki I'm always with u kinji ko?,'
__"to naji heart beat dina,'
___"olrigt hot milk love u bye take care,' uhm muah kisses 😘
Kiss ya manna mata awaya kana yadawo tareda zama nanfa akabukaci dasu taso sunsoma shiga jirgi kasancewar sukadaine acikin jirgin yam club dinsu baki daya minty goma da shigarsu jirginnan yayi sama ✈ yasoma keta hazo,'
*love u oll*
🏓🏓🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓🏓
🏓🏓
🏓
*BASAN*🏓
*RAINA BACE*
*by______________*
*_badiat Ibrahim_*
*_______________11to15✍🏻*
Su Meenal ne suka fito daga aji antafi break Na Rabin awa azaune take itakadai tana tunanin Anas dinta kawartace takaraso gareta tazauna akusa da'ita
___"Kawata kiyi hakuri wannan wani kaddarace sannan wannan abunda yafaru rubutaccen al, amarine daga allah koda tsautsayi bai fadama Fatima ba hakan zaifaru dake Kawata akwai daci tareda ciwo wanda kakeso yake sanka yarabu dakai alokacinda kafi kowa bukatarshi lokacinda kafi tsananin bukatar taimakonshi amma yazamuyi haka allah yaso kuma kinsan ance Matar mutum kabarinshi allah baiyi zakuyi aure da samarinki biyu dasuka fasa auranki haka Allah yaso.'
Wasu siraran hawayene masu dumin gaske suka gangaro akumatunta tadago tanadan murmushi,'. ____"nagode hajjo da dukkan kulawarki agareni wlh komai yawuce inadai kokarin rarrashin zuchiyatane kawai domun kinsan taciremun soyayyar Anas araina kozan samu kwanciyar hankali Hajjo tasaka hannunta tana sharema Meenal hawayanta
Khadija wacce take bakin ajinsu tayi murmushi dan ganin yayarta tayi murmushi kanta tasauke kasa kawai,'
Misalin karfe shiddan yamma su Meenal suka tashi makaranta kaitsaye suka wuce gida suna shiga ana kiran magrib kaitsaye suka zari butoci suka daura alwala suka gabatarda Allah,'
Mama tashigo da sallama tace,'. ___"khadija jeki Dibo muku abincinku kuci kamun akira sallar isha,'
___"to mama khadija taje kichin tadebo musu jalob din shinkafa da taliya ta mankyada sunaci yayinda kowa yashiga tunane tunanen rayuwa kowa da abunda yake sakawa Meenal dai tadan cakkakala abinci tamike tareda kuskure bakinta tashinfida sallaya tasoma gabatarda sallar esha,"
Mama tace___"yayadai karatun naku ankara muku akai kuwa Meenal,?'
Kamun Meenal tayi magana yaro yayi sallama akofar dakinsu,'
___"dama Anas ne ya aikoni inkawoma Meenal wannan takaddar,'
Meenal takauda kanta gefe khadija ce tasaka hannu ta amsa tamikama Meenal bata dubaba takawai jefa acikin jakar makarantarta,' mama tadingajansu da hira tareda basu labaran abun daria har saida lokacin baccinsu yayi suka nufi dakin kwanansu,'
Meenal tana zaune atsakiyar gadanta bacci yaki zuwa mata Sam tanata tunani kanwarsu Fatima marigayiya idanu tadaga ta kalli bango hotonsune su ukune acikin hoton yayinda Fatima tadafa kafadar Meenal Suna daria,'. Meenal tatuno randa abun yafaru da Fatima,'
Da yamma ne lis mama ta aiki Fatima kai kudin adashi kasancewar layinda mama ta aiketa sabuwar anguwace akwai gine gine dadama daba'a kammalasuba anan tahaduda Yan iskan suka jata sukaimata fyade kusansu uku ahaka su Meenal sukaga Yar uwarsu jina jina dakyarma suka ganta asume kuma,'
Kukane yaci karfin Meenal tace,'. ___"Allah yasaka miki kanwata allah yasa kinhuta Allah yajikanki da Rahama,' Meenal tajuya takoma tareda kwanciya akan gadanta tareda runtse idanunta dakyar bacci yayi awon gaba da'ita taso karanta sakon Anas amma ina takasa koda bude takaddar sannan tayima kanta alkawarim bazata budeba domun ahalin yanzu tanata kokarin tursasama zuchiyartane domun tamanta da Anas,'
Dasafe Meenal tanata shirin zuwa islamiyya domun tanada jarabawa yau karfe bakwai nasafe a gaggauce tayi Karin kumallo sannan taima mama sallama tawuce dasaurinta dan batasan tayi latti,'
Tana tsaye abakin titi tarasa abun hawa duk kekenda tatawo acike take dam da Yan makaranta Meenal duktabi tadamu kanta gashi lokaci yanata tafiya,'
Suna tafe abota tana bayan motar direba yana tukata aikuwa tahango Meenal atsaye abakin titi tanata tare Keke,'
__"abakar kadawo baya daidai gaban waccan Yar makarantar,'
.___"angama ranki yadade yadda kikeso haka zamuyi,'
Meenal dataga motarnan tanufota saita sake dan matsawa gefe daidai karasowar motar gabanta Momy tazuge glass din motar cikin fara'a tace
___"'yata ina zakijene dahalama makaranta zakitafi ko?
Cikin murmushi tareda girmamawa Meenal tace,'. ___"wlh mama nadade anan wajan inata tare Keke amma shiru kowacce acike gashi inada jarabawa a islamiyya,'
Murmushi taima Meenal tace,'. ___"'yata inkin yadda da Allah kin yadda dani kishigo Mota mukaiki makaranta karkiji tsoro domun nibame cutarwa bace inkuma bakyaso shikenam ammadai bazanji dadiba,'
Meenal tadanyi murmushi ta kalli wannan hajia tace,'. ___"to mama zanshigane sabida kince innaki bazakiji dadiba nikuma banaso inzama silar rashinjin dadin wani dan haka Na yadda dake nakuma gode,'
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.