Matar Damisa Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: MATAR DAMISA 1.txt
Chapter 7 of 69
Knocking ta fara yi taji shuru ko motsi bataji ba ta sake buga 'kofar still ba motsi
Almost 30minute tayi a tsaye tana sa'ke sa'ke a raanta
Daga baya ta yanke shawarar shiga kawai, cikin rashin sa'a tana shiga tayi tuntu6e da mutum a gabanta,
Juyowa tayi ta kalli gurin ganin Mommy a kwance yasa taji fad'uwar gaba,
"Innalillahi was inna'ilaihi raju'un Aunty meya sameki" jijjigata ta somayi taga babu alamar motsi
Juyawar da zatayi taga mutane uku aguri d'aya 2 bodyguard da mai gadi ja da baya tayi cikin firgici da tsoro tana waiwaya gabanta taga still 2 bodyguard kwance ba motsi
Daman bodyguard 4 ne a gidan sai mai gadi
Bakinta ne ya soma kakkarwa ko magana ta kasayi
Ga wani irin guminda yake yarfo mata
Cikin fargaba da tsoro take bin d'akin da kallo
Karaff idonta ya sau'ka akan Junaid dake manne saman bango rai a hannun Allah, 'Kara ta sau tare da toshe bakinta kuka ne yaci ranta yau taga abunda tinda aka haifeta bata ta6a gani ba.
Da gudun gaske ta nufi gurin da Junaid yake, jinin da yake d'idd'iga daga jikinsa duk ya 6ata tiles d'in d'akin,
'Dagowa da kanta tayi ta 'kura wa fuskarsa ido lokaci guda kuwa ta zaro Manya-manyan idanuwanta waje bakinta ne yake motsi kamar maiyin magana, jikinta kuwa rawar sanyi ta soma, cikin firgici ta jaa baya da sauri sai da ta fad'i 'kasi still idonta akan Junaid
Da kyarr ta iya bud'e bakinta cikin kuka ta fara fad'in
"Wayyo Allah nah Umma nah, Kaine ka kashe mun Ummana bazan yafe maka ba, ka sanya ni cikin maraici! Saika tozarta a rayuwa, sai kayi mutuwar wulakanci kamar yanda ka kashe mun mahaifiyata"
Gaba d'aya Ayush idonta ya rufe bata ganin halin da Junaid yake ciki, kamar zautacciya haka take maganganu cikin fitar hayyaci,
Saida ta gama surutanta ta mi'ke da gudu ta fice daga cikin d'akin...
Shi kuwa Junaid duk abubuwan da yake faruwa bai saniba , baya cikin hayyacinsa,
A halin yanzu taimako yake bu'kata
Kuma Ayush ce kawai zata iya wannan taimakon, in har ba itaba ba Wanda zai iya ceton Junaid daga hannun azzaluman Aljanun nan da kuma mahaifinta.
Barin Ayush cikin d'akin falo ta nufa ta kwanta 'kasan carpet tana rera kukanta mai cin rai, a halin yanzu ba mutumin da Ayush ta tsana kamar mutumin da ya kashe mata mahaifiya,
Kuma saita d'au fansar mahaifiyarta akan sa,
Wato JUNAID.........
TO BE CONTINUE INSHA ALLAH.
*ASMEETAH* *CE* âœï¸âœï¸âœï¸
*FREE* *BOOK*
🅠*MATAR* *DAMUSA* ðŸ…
(the wife of tiger)
*MALLAKIN*
*ASMEETAH* âœï¸âœï¸
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________
https://www.facebook.com/103637491942644/
💫💫 *{{N W A}}* 💫💫
Ø¨ÙØ³Ù’ــــــــــــــــــــــم٠اللّه٠الرَّØÙ’مَن٠الرَّØÙيْم
*BOOK* *ONE*
*PAGE* âž¡ï¸21 to 22
Ayush! Ayush!! Ayush!!! Cikin sassanyar murya ake kiran sunan nan, ita kuwa Ayush tana kwance akan carpet kuka yaci ranta taji ana kiran sunanta kamar daga sama, dakatar da kukan tayi tana sauraron kiran da ake mata, sautin zazza'kar murya ne yake dukan kunnenta a hankali take d'ago da kanta wani irin hajijiya ne yake d'iban ta a haka ta tashi zaune!
Da dara-daran idanuwanta wad'anda sukayi jawur ta d'agosu ta kalli yanda sautin sunanta yake fitowa, cikin firgici taja da baya ta zaro manya-manyan idanuwanta waje tsoro ne ya kuma bayyana akan fuskarta, baki na kakkarwa ta ambaci "Umaa" abunda ya fito daga bakinta kenam tana kallon gurin da wata zankad'edd'iyar mata take tsaye, tana sanye da fararen kaya daga sama har 'kasa ta rufe doguwar suman kanta da farin mayafi, da murmushi a kan fuskarta...
Ayush ce ta sake motsa baki tana fad'in "Umaanah" tana kuka kuma tana had'awa da dariya tayi farin cikin ganin mahaifiyar ta a wannan Daren misalin karfe 2:00
Itama Uman da murmushi a fuskarta cikin sanyayyar murya tace "Yarinyata nazo gareki ne domin na tunasar da ke abunda kika manta a baya, ki kasance mai taimakon al'umma idan kika fuskanci suna cikin wani irin hali, kada ki dubi girman laifin da mutum yayi miki idan ya bu'kaci taimakon ki kawai ki taimake shi kema wata rana idan kika shiga wani hali Allah zai taimake ki, kada ki tsani bawa! kada ki cutar da bawa!! kada ki bari ata sanadiyarki a cutar da bawan Allah, Ayush d'iyata! 'Dan uwanki yana bu'katar taimakon ki kije ki taimake shi kada ki damu Allah yana tare da mai hakuri, kije ki, ki je ki taimake shi........!
Tana kaiwa karshen maganar ta 6ace 6attt.
A firgice Ayush ta tashi zaune tana fad'in "Umaa! Umaana!! Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, mafarki Ayush tayi kwanciyar da tayi tana kuka ashe bacci 6arawo yayi awun gaba da ita, zuwan da mahaifiyar ta tayi acikin mafarki ta zo mata.
Ta waiwaya ko Ina bata ga kowa ba ga hawayen da ya bushe mata akan fuskar "tabbas mafarki nayi, Uma tazo mun" a lokacin ta fara tariyo maganganun mahaifiyar tatan lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka, Junaid ne ya fad'o mata a rai "Uma mutumin da ya rabaki da rayuwarki shi kike so na taimaka?" Kuka ne ya kwato mata sai wani tunani yazo mata a cikin zuciyarta take fad'in "Mahaifiyar shi ta taimake ni, ba don ita ba bansan Ina zan nufa ba, shin itama tana raye ne ko ta mutu? Tabbas suna bu'katar taimako a wannan halin" ta mi'ke tsaye cikin sauri lokaci guda kuma ta tsaya cakk
Alamar ta tsaya tunanin wani abu "amma meyasa naga shi wannan mutumin a manne da jikin gini ba tare da an d'aure shi ba, kuma jikinsa a faffashe kamar ma ya mutu"... 'Kirjinta ne yayi wani irin bugawa ta zabura da gudu ta nufi hanyar d'akin takawa d'aya biyu taji kamar an ri'ke 'kafarta ta doku a 'kasi danma carpet ne mai gashi da tunin taji ciwo,
Tana shirin d'agowa kunnuwanta suka jiyo mata kukan mujiya 🦉🦉 mai firgitarwa a tsorace ta kalli saman cilling yanda ta jiyo kukan kenam, wutar nepa gidan ne ya d'age sai duhun daya biyo baya ko hannunta bata iya gani wani irin tsoro ne yabi jikinta, kamar daga sama tajiyo wata 'katuwar murya ana cewa "AYUSHHHH KADA KI KUSKURA KI TAKA 'DAKIN NAN, WANDA YA KASHE MIKI MAHAIFIYA ZAKI TAIMAKA? TO LALLAI KEMA ZAI KASHE KI KAMAR YANDA YA KASHE MIKI MAHAIFIYA, KIYI TUNANI SHI BA MASOYINKI BANE MAKIYINKI NE, YANA NEMAN AHALINKU NE DOMIN YA GAMA DA RAYUWAR KU GABA DAYA HAHAHAHA, HAHAHA, HAHAHAHA haka ta ringa jiyowa dariya marar dad'in ji,
Jikinta ne ya hau 6ari murya na kakkarwa tace "waye Kai?"
"NIIII MAI BAKI KARIYA NE, still ya 'kara tintsirewa da razananniyar dariyar shi mai ban tsoro....
Lokaci guda kuwa haske ya bayyana ta daina jin kukan mujiyan.
"Innalillahi wa inna'ilaihi raju'unnn wannan wani irin bala'i ne a cikin gidan nan, Aljanu da mutane duk suna rayuwa a gidan nan" zuciyarta ne ta soma magana kamar haka "Ayush kar ki manta wannan Addu'ar da malamin nan ya koya muku ke da mahaifiyarki" anan ta tuno da Baba tsoho wanda yayi hijira zuwa dajin da suka zauna yayi tsawon shekara biyar atare da su, Babban malami ne na gaske shi ya koya musu karatun al'qur'ani mai girma tare da addu'oi ya koya musu alwala da yanda ake sallah su wankan janaba da haila ba abunda bai koya musu ba ta 6angaren addini, Ayush lokacin bata wuce 15yrs ba ita kuma mahaifiyarta tana 'kara koyan karatun ne domin wad'annan karatuttukan mahaifin Junaid ya koyar mata su tin suna GHANA.
Damuwar dai Ayush ta samu ta koya duk da itama tana koya mata wasu abubuwan!!
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.