Matar Damisa Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: MATAR DAMISA 1.txt
Chapter 56 of 69
tagumi yayi sannan yace "nima haka nake tunani, bansan ya zanyi ba Laylah, tunani na ya gushe, bazan iya sama wa kaina mafita ba, tabbas nasan idan wannan maganar ta fito ba abunda zai hana na tafi prison, mahaifinta bazai ƙyaleni ba duk da shi ɗin abokin mahaifin mu ne, ina tsoro wallahi.."
Laylah ce tace "toh amma Yaya kana ganin Maimoon zata rufa maka asiri ne?.."
ta ƙarasa maganar tana kallon cikin ƙwayar idanunsa,
ƙararar zallar tsorone a cikin eyes ɗinsa yace "nima ban saniba.."
Tace "Yaya ga mafita É—aya.."
da sauri ya kalle ta yana faÉ—in "ina jinki Autar.."
tace "mezai hana mu riƙe ta a cikin gidan nan har ta warke, idan ta warke ta iya tafiya sai mu tura ta gida, kafin nan su kuma iyayen natan sun ankara da an sace ta, duk neman da zasu bazasu ganta ba, mu kuma mun ɓoyeta a cikin gidan nan, zamu karɓi wayarta mu kashe, sannan zamanta a cikin ɗakinka babu tsaro zamu gyara ɗakin ajiyar marigayi Abban mu dake can bayan ɗakunan gidan, tinda kaga ba'a san da ɗakin nan ba,
zamu cigaba da kula da ita, tinda ni yanzu bana zuwa school kula da ita ya rataya mun a wuya kai kuma sai ka cigaba da zuwa gurin aikin ka hankalinka a ƙwance ba mai zarginka akan kai ka ɗauke Maimoon, nima kuwa zan cigaba da zuwa gidansu saboda nuna baƙin cikina akan ɓatar Maimoon, itama idan ta warke insha Allahu bazata tona maka asiri ba ai bazata daina sonka ba..."
Doctor Hasheem sake baki yayi yana kallon Laylah,
a ransa yana jinjina mata da irin wannan basiran da Allah ya bata,
"Yarinya ƙarama ta iya samo mafita haka.." yana maganar zuci.
har saida ta kammala jawaban ta tukun ta kalleshi tace "toh ya kaga Yaya hakan yayi?.."
da sauri ya jijjiga kai yana faÉ—in "of course my yonger sister, kin kawo shawara mai kyau, hakan ma za'ayi, sai na cigaba da mata magani a nam ba,
toh amma Haydar fah? kinga yana gidan kar wata rana ya gano mu, duk da nasan bazai toni asirin mu ba amma nafison daga ke kar wanda yasan da wannan maganar.."
Laylah tace "to ba daman yanaso ya tafi katsina gurin Kakan mu ba ka hanashi! yanzu kuma saika barshi ya tafi tinda sun kammala exam.."
yace "gud.." yana farin ciki sai yanzu hankalinsa ya dawo jikinsa..
Laylah ta kuma cewa "wato Yaya harda zagina ɗazu saboda na ƙwanƙwasa maka ɗaki ko? kana so ka ɓoye mun aika-aikan da kayi, toh yanzun inda ban saniba ya zakayi da ita?..."
shuru Doctor yayi yana murmushi yace "ke dai bar maganar nan, mu fara zuwa É—akin can mu gyara shi sosai, mu kai katifa É—akin kinsa babu komai a É—akin sai gayyar datti da takardu..."
tace "toh shikenam amma kafin mu fara kaje kayi wanka ka canza wannan jallabiyar takan mai jini, kar kayi baƙo kuma a shige su..."
gaba ɗayan su suka ƙwashe da dariya,
ya tashi ya nufi ɗakinsa yana faɗin "bari naje kar addu'arki ta karɓu azo ayi baƙi..."
*******
Æangaren su Junaid...
Bayan ya shugo da zuƙeƙiyar motarsa direct waran ma'ajiyin motoci ya nufa yayi parking ana kusa da motar Mommy, sauƙowa yayi yana jan ƙafa ya nufi motar Mommy wacce tin isowar ta bata fito ba sai kanta data kifar akan sitiyari, buɗe murfin motar yayi ya shugo...
yana motsi da bakinsa daƙer ya iya cewa "Mom please forgive me, nayi kuskure babba dana sanya ki kuka, dan Allah Mom kiyi haƙuri insha Allah bazan ƙara aikata makamancin abunda nayi miki ba, bansan ya zanyi ba ina matuƙar ƙaunar Yushert...."
É—agowa Mommy tayi da murmushi a fuskarta ta kai hannu tana shafar gefen fuskar Junaid tace "da gaske my son! kana son Ayush amma baka son maganar Aure?.."
ta ƙarasa maganar tana kallonsa cike da zolaya,
yamutsa fuska yayi sannan yace "nifa bance bazan Aure ta ba.."
dariya Mommy tayi sannan tace "shikenam my son, nayi haƙuri nima kayi haƙuri da marin dana maka..."
turo baki ya yi yana faɗin "nifa banji zafin marin ba, ganin hawayen ki yafi komai ƙona mun rai kuma naji raɗaɗi sosai a cikin zuciyata..."
"it's okay My son, nima ba'a son raina na mareka ba, sannan ba wai akanka nake zubar da hawaye ba, sai dan rashin ganin Ayush kuma ba'a san yanda take ba,
ina zaune cikin ƙunci da takaici ina nazarin taya akai Ayush ta ɓata a cikin ɗaki ina sallah, sai gaka kai kuma kayo kaina kana mun wasu surutai, hakan yasa na zuciyo na huce takaici na a kanka,
Junaid! ba wai kai kaÉ—ai ka ke cikin matsala ba, nima kaina ina cikin damuwa..."
hura iskar bakinsa yayi sannan yace "toh mom aina zan samu Yushert?..."
ta juyo tana kallonsa tace "za'a sameta ka ƙwantar da hankalinka ɗan albarka na, ɗan fari kyakykyawa naaa..." tana masa wasa duk dan hankalinsa ya kwanta, shi kuwa ba alamar annuri a fuskarsa sai ma kawar da kansa gefe da ya yi..
yace "Mom ina dai kin haƙura ko?.."
ajiyar zuciya Mommy tayi sannan tace "Junaid na haƙura mana, a rayuwata bana ƙaunar na mareka saboda daraja uku da kake dashi a gurina,
na farko siffarka irin na mahaifinka ne kamar ku É—aya sak, idan na mareka gani nake kamar na mari mijinaa,
na biyu kai mai sunan mahaifi nane kuma abun alfahari na JUNAIDD, kamar yanda bazan so na ƙuntata wa mahaifina ba haka bazan so na ƙuntata maka ba albarkacin suna,
na uku kuma fuskarka yana da matuƙar daraja, bazan so na rinƙa marin fuskar ba saboda kai ɗaya nake da akwai, baka da Yaya baka da ƙanne shiyasa nake jii dakai my son, hakan yasa na sanya wa asibiti na suna JUNAIDU, GENERAL HOSPITAL ABUJA.
bana son abunda zai ɓata maka rai my Auta..."
murmusawa Junaid ya yi jin abunda mom ɗinsa take gaya, ta sashi a gaba tana ta masa surutai kamar wani yaro ƙarami...
yace "Mom fito mu tafi to.."
tace "ni ba yanda zanje ni daga cikin motar nan har saika mun dariya.."
kallon ta yayi shi har ga Allah bashi da niyar yin dariya a wannan lokacin, amma saida mommy ta nace masa akan saiya yi dariya,
ba tare da ya kalleta ba yayi murmushi har sai da waɗannan twince dimple ɗinsa suka lotsa, ba ƙaramin kyau yayi ba, mommy tace "wow gaskiya Ayush tayi dacen samun kyakykyawan namiji anan, thank god..."
yana jinta bai ce ƙala ba shi kaɗai yasan irin ƙololuwar baƙin cikin da yake cikin zuciyarsa na rashin Yushert ɗinsa,
haka suka fito daga cikin motar suka nufi compound,
mommy key tasa a ƙofar falo sannan ta buɗe suka shiga ciki....
duk da sun san babu kowa a cikin falon amma sai da sukayi sallama,
Ayush jin sallamar Mommy yasa ta buÉ—e eyes da sauri, ta É—ago tana faÉ—in "Mommy! Mommy!! ina Yaya Junaid É—ina..."
ta taso ta nufi gurin da suke a tsaye suna kallon ta cike da mamaki a fuskarsu,
Mommy kam bata gaskata cewa Ayush bace, kafin Ayush ta iso gurin da suke Mommy tayi waje da gudu tana faÉ—in "mun shiga uku aljanaaa...."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.