Matar Damisa Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: MATAR DAMISA 1.txt
Chapter 35 of 69
cikin sanÉ—a tayo kan Janaid tana faÉ—in "yawwa ga dama ta zomun bari na samu na sanya masa zoben nan kafin ya ankara da shi"
yatsar hannunsa ta kamo a hankali ta sanya masa itama tayi gaggawar saka nata, tana sauƙe ajiyar zuciya "shikenam hankali ya kwanta mun rabu da masifar farko sauran na biyu shine zan rasa rayuwa ta," ta ƙara sa maganar tana zubda hawaye........
*MASHA ALLAH TO BE CONTINUE NEXT*
*INA MASOYAN AYUSH KUZO KU TAYA AYUSHERT DA ADDU'A NEXT PAGE KO TAYI RAI KO TA MUTU OHO, YAWAN COMMENTS ƊINKU SHI ZAI CETO RAYUWAR AYUSH, ƘARANCIN COMMENT ƊINKU KUMA SHI ZAI SHEƘE AYUSH HAR LAHIRA YACIIIN...*
*ASMEETAH NOVELâœï¸âœï¸âœï¸*
typing📲
🅠*MATAR* *DAMUSAA*ðŸ…
(the wife of a tiger)
*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*
( *ASMEETAH NOVEL* âœï¸)
*WhatsApp me 09065443871*
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________
https://www.facebook.com/103637491942644/
💫💫 *{{N W A}}* 💫💫
Ø¨ÙØ³Ù’ــــــــــــــــــــــم٠اللّه٠الرَّØÙ’مَن٠الرَّØÙيْم
*BOOK ONE*
ðŸ…¿ï¸ ------->69 & 70 <-------
____________________________
Ɗaga hannu tayi sama tana roƙon Allah "ya Allah ka temake ni, ka bani nasara akan ceton Junaid daga kogon hallaka..."
har ta gama Junaid bai motsa ba, ta tashi ta nufi gaban mirror, gabanta ne ya yi wani irin bugawa da ƙarfin gaske ta tsaya cak ta zazzaro manya-manyan idanuwan ta waje ganin anyi rubutu a jikin mirror da jini, "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un.." abunda ta furta kenam, jikin ta na kakkarwa ta soma karanta rubutun da akayi da jini a jikin madubi...
{{ "kun munafurce ni Æingel ke da mahaifiyar ki, kun toshe mun kafar da zan sanya ku a idanuwa na balle nasan abubuwan da suke faruwa daga É“angarenku, hakan yasa na É—auki mummunan mataki akan shi wanda kike so ki rasa rayuwar ki akansa, kafin ki mutu ya rigaki mutuwa Æingel, daki rasa rayuwarki gwara shi ya rasa tasa rayuwar, kiyi hakuri na kashe Junaid har lahira, babu ta yanda zan ganki shiyasa nayi miki wannan rubutun BISSALAM" }}
tsabar firgita da tsoro Ayush har faɗuwa tayi ƙasi ƙafafunta bazasu iya ɗaukar ta ba, jiki na rawa tayi kan Junaid wanda yake kwance kan gado ƙafafunsa rabi suna ƙasi, jijjigar sa ta farayi tana ƙiran sunansa cikin yanayin kuka "wayyo dan Allah Junaid ka tashi, na shiga ukuna na lalace Junaidd! Junaidd!! Junaid ka tashi mana...." ta fashe da matsanancin kuka tana bubbugar ƙirjinsa, ta tashi da gudu ta nufi toilet ta fito hannun ta ɗauke da ruwa ta soma kwara masa amma Junaid ko motsi babu ido a rufe, tsabar kiɗimewa daga ita sai towel a jikinta haka ta jawo Junaid kanta suka faɗo ƙasin gado tare tana rungume dashi, ihu take na fitar hankali tana ƙara ƙanƙame shi a jikinta,
idonta sunyi jawur hatta fuskar ta shima ya yi jawur abinka da farar mace,
kanta ne ya soma juyawa ta soma kwashewa da dariya daga dariya ta koma kuka haka ta rinƙa haɗawa dariya da kuka, still tana ƙanƙame da Junaid!
Inta kwashe da dariya lokaci guda kuma sai dariyar ta juye ihu ta soma ihu kamar ranta zai fitaa,
Da haka har ta fara shiɗewa, ta soma magana ciki -ciki "Yaya Junaid bazaka mutu ka barni ba, bazan rayu ba..." lokaci guda kuma ta yi wani irin ƙaara na gaske har sai da madubin ɗakin ya dagargaje tsabar ƙarfin ƙarar ihun data yi, shine last ihun ta itama wuyan ta ya karye ta kwantar da kanta saman ƙirjin Junaid, numfashi ya tsaya cakk,
ihun nan har sai da ya daki dodon kunnen maigadi tsabar ƙarfin ƙaarar,
shi maigadin da yake can bakin gate mai shegen nisa.
Jin wannan ihun mai razanarwa yasa mai gadi tsorita jikinsa ne ya hau ɓari yana faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, shikenam kwanan mu ya ƙare yau kam Junaidu ya koma Damusa ya kashe ƴar mutane, nasan yanzu kaina zai dawo bari na hau kan hanya na bar gidan nan tin kafin ya fito gare ni.
Da gudu Baba mai gadi ya buÉ—e gate ya fice a gidan...
(Shin mutuwa tayi ne ko suma Allahu A'alamu..).
******
Besty ce take kwance saman gadon Laila sai danna phone take tana watsa chiwgun a baki sai kara take tayi da su tana taunasu cikin salo, can saiga Laila ta fito daga toilet da É—aurin
towel a ƙirjinta tana faɗin "my Besty yakamata kizo ki watsa ruwan musulunci a jikin ki koh, gashi time to pray sai ƙiraye-ƙirayen sallar la'asar ake.
Besty kuwa idon ta nakan wayar hannun ta tace " kiyi sallar ki mana idan na tashi zanyi ai." Laila ce ta taho gaban Besty tana faɗin "ke ki tashi nace kije kiyi wanka bazan zauna dake haka duk jikin ki ƙazanta" ta ƙarasa maganar tana fizge wayar hannun ta,
tashi tayi Besty tana ɗura ashar tace "kutumar bura uba, nice baza ki iya zama dani ba a haka? saboda nazo gidan ku ne yasa kike mun wulaƙanci son ranki, shikenam zan bar gidan ku yanzu ai nima muna da gidan, kuma ke bazaki nuna mun musulunci ba," ta ƙarasa maganar tare da tashi ta fizgi wayar ta, ta jawo kayan ta zata saka suka ji bugan ƙofar ɗaki, a tsorace Laila tace "waye ne"
jin muryar Yayanta yana faɗin "Auta ki buɗe ƙofar mana" gaban ta ne yayi wani irin bugawa ta kalli Bestin ta murya ciki-ciki take cewa "ina kinga har Yayana ya dawo daga hospital shiyasa nake ta binki ki samu kiyi wankan kar yazo ya ganki a haka, gashi yanzu, ai saiki samu ki shige cikin toilet ɗin.."
wani irin harara Besty ta wurga wa Laila ta ja tsuka sannan ta shige toilet, itama Laila binta da kallo tayi kafin tayi ƙwafa ta nufi yanda wardrobe ɗinta yake ta ciro wata doguwar riga na material da gyalen ta mai ɗigon black and white ta ɗora su akan gado wannan ta fitar su ne wanda Besty zata saka..
itama ta ciro riga da skit blue da hular sa tayi saurin sanyasu, taji Yayanta yana faÉ—in "ke shanyar da kika yi fa ya bushe, wai mekike yi haka ne?"
"Yaya kayana dai nake sakawa nayi wanka ne..."
shuru yayi bai ce komai ba, sai da ta gama shirya wa tsab tukun tazo ta buɗe ƙofar da murmushi akan fuskar ta tace "your welcome my dearest bros" ɗan hararar ta yayi ta gefen ido yana faɗin "ni kike wa jan aji ko?"
taɓe baki tayi sannan tace "sorry my Bros...."
bakin gado ya samu ya zauna bakin sa cike da tambayoyi sai kalle-kalle yake ta yi a ɗakin kamar baƙonsa...
"waÉ—annan kayan waye..."
ya yi tambayar yana kallon Laila..
cikin ƙinƙina tace "Yaya! Aunty Maimoon ce tazo tinda rana, har bacci ya ɗauke mu yanzu tana wanka ne..."
Gabansa ne ya yanke jin an ambaci Maimoon, jinjina kai ya yi sannan yace "okay.."
tashi yayi zai fita Laila tace "Yaya meyasa ka tashi kuma?"
Murmushi ya yi sannan yace "bakomai inaso zanje nima nayi wanka yanzu dawowa ta, kinsan idan na dawo inhar banzo duba lafiyar ki ba hankalina baya kwanciya.."
Murmusawa tayi tace "proud of you my Bros, nagode da irin kulawar da kake nuna mun.."
Ficewa ya yi daga cikin É—akin
ita kuwa Laila murmushi tayi tasan saboda Maimoon yabar É—akin....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.