Matar Damisa Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: MATAR DAMISA 1.txt
Chapter 62 of 69
gaban Ayush ne ya faÉ—i rass, zuciyarta kuwa ya soma bugun 3+3, tsananin tsoron matar ne ya kamata gaba É—aya tasha ruwan jikinta, a ranta kuwa cewa take "subhanallahi ina tunanin wannan ce Rumana, domin itace naji ta ce isowar cikin dare zatayi kuma bayan haka itace mai yaren french baturiya, tab amma wannan banga wani kyau ba sai farin fata kamar wata zabiyan ga sumar kanta fari A'uzubillah wannan kam...."
ba tareda ta ƙarasa maganar zucin ba taga ana murza zara-zaran yatsu suna bada sautin ƙara a saitin ƙwayar idonta, firgitt tayi tana kallon Rumana wacce ta tsaya a gabanta ta kama kunkumi ta kuma kafa mata blue ɗin eyes ɗinta tace "what are you looking for?.."
shuru tayi Ayush bata ce mata komai ba,
ta ƙara tambayarta "who are you?.."
nan ma Ayush shuru tayi bata ce komai ba,
ran Rumana ne ya yi matuƙar ɓaci ta daka mata wani irin gigitaccen tsawa har saida Ayush ta firgita sosai, batada wata mafita kawai ta fashe da kuka...
Junaid yana tsaye a gefe ganin Rumana zata takura mata yace "please Girl leave her alone.."
Rumana ce ta juyo tana kallonsa da blue eyes É—inta tace "ok tell me who is her?.."
Junaid shima É—aure fuska yayi yana kallonta sannan yace "she is my sister.."
Rumana ganin yanda Junaid ya É—aure fuska ba annuri yasa ta shiga taitayinta, sunkuyar da kai tayi tace "okay.."
suna cikin wannan halin saiga Mommy ta fito tana murtsuka ido alamar daga bacci ta tashi jin hayaniya ne yasa ta fito tana faÉ—in "wai meyake faruwa ne a wannan daren..."
bata ƙarisa maganar ba suka yi ido huɗu da Rumana, sake baki tayi tana kallonta da farko har ta tsorita sai daga baya kuma ta ɗanyi murmushi tana kallon Junaid tace "ko dai ɗaya daga cikin ƴanmatan ka ne tazo? amma wannan itace Rumana ko? domin naji kace baturiya ce."
duk wannan maganganun da mommy tayi Rumana ba abunda taji aciki sai dai taji an ambaci sunanta wato Rumana,
kwata-kwata bata fahimtar hausa,
Mommy ƙareta take da kallo gata kuwa tana sanye da kayan sojoji a jikinta irin na ƙasar Australia...
Junaid ne ya yi gyaran murya sannan yace "Mom ga nan Rumana ta samu ƙarasowa sai a duba mata ɗakinda zata zauna.."
Mommy tace "ai duk ɗakunan a gyare suke, har na wanda sauran idan sun zo zasu zauna, yanzu dai ita wannan ga can ɗakinta ta nuna ɗakin da yake ƙasan benin da zai kai ka ɗakin Junaid,
ta ƙarasa maganar tareda jan akwatin ta zata nufi ɗakin dashi,
Rumana tana zaune akan sopa ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya tace "babu ɗaki ne a sama?.."
Mommy dai kallon Junaid tayi domin bata san mai ta ce ba domin da yaren french tayi maganar,
Junaid ne ya bata amsa da cewa "babu.."
hannu yayi wa mommy akan takai mata jakar É—akin da aka tanadar mata,
wuce wa mommy tayi tana jinjina kai, domin akwai magana a bakin mommy tarin-tarin..
Ayush tana tsaye da kofin tea a hannunta ta kasa motsawa sai kallon Junaid take cike da takaici ji take kamar ta rufe shi da duka,
gani tayi Rumana ta katse ta da cewa "am really hungry.." ta ware mata miƙaƙƙun hannunta alamar tana buƙatar kofin shayin..
Ayush miƙa mata kofin tayi kanta a sunkuye domin ba ƙaunar haɗa ido take da ita ba,
tana miƙa mata ta wuce zata haura saman stairs,
Rumana ta dakatar da ita tareda faÉ—in "come here.." tayi mata alama tazo da hannunta, a tunaninta Ayush bata jin yaren natan,
tana zuwa Rumana ta miƙa mata cup ɗinta tace "bazan iya shan wannan abun ba, ya yi kauri da yawa sannan sugar yayi yawa, go and find me coffee..."
Junaid ne ya buÉ—i baki zai maimaita wa Ayush abunda Rumana ta faÉ—a da hausa,
cikin zafin rai Ayush ta É—aga masa hannu da sauri tace "ba sai ka fassara mun ba..."
tana kaiwa haka ta nufi kitchen,
abunda Rumana ta kasa ganewa kenam amma tasan akwai wani abu a tsakaninsu, just tayi shuru ne kawai amma tasan ba ƙanwarsa bace domin a saninta da shi bashida bros or sis...
Junaid bin bayan Ayush yayi da kallo cike da mamaki "taya Ayush tasan abunda Rumana ta faÉ—a?..."
yana cikin wannan tunanin sai ga mommy ta fito tana faÉ—in "Junaid ka kaita É—akin ni zan wuce bedroom É—ina saboda ina jin bacci sosai, ya kamata kuma ku samu ku kwanta kafin sallar asuba, kunga gobe kunada hidima ba baccin rana..."
Mommy tana kaiwa haka ta wuce É—akinta,
shima Junaid magana yayi wa Rumana suka nufin É—akinta, yana kaita ya juya zai fito ta tsayar dashi tace "ina zaka je Beb?.."
yace "Girl i what to sleep.."
tace "ok before seat here and wait for me.." ta kama kafaÉ—arsa ta zaunar dashi a bakin gado..
a gabansa ta gama cire kakin sojan natan ta sanya sleeping dress sannan tazo yanda yake zaune ta hau saman cinyarsa ta zauna tana fuskantarsa tace "Beb you known i really miss you.." tareda da manna masa kiss a saman goshinsa tana shafar lallausar suman kansa,
Shi dai Junaid sai faman kakkauce wa yake saboda sun sani baya taɓa biye musu, kuma tinda yake da su bai taɓa yadda ya haɗa baki dasu ba, sai dai su gama iskancinsu na shashshafa shi amma bayan hug baya barin a kauce hanya saboda wasu dalilansa na farko su ba musulmai bane sannan shi ba irin mazan nan masu ƙwaɗayin mata ba ne,
mace ta farko daya taɓa sumbatar ta a rayuwarsa itace Ayush, kuma itace kawai yake biye mata suyi romance,
Rumana tana cikin kissing ɗinsa a wuya tana wasa da sumar kansa saiga Ayush ta turo ƙofa ta shugo hannunta riƙe da cup na coffee,
ganin halin da suke ciki ne yasa ta tsaya cak tana kallonsu nan da nan hannunta ya fara rawa, idonta har ya cicciko da ƙwalla tana kallon Junaid wanda shima ita yake kallo, gaba ɗaya ya rasa yanda zaiyi domin shima kansa baiji daɗin hakan ba, bai so ace Ayush ta zo ta sameshi a haka ba,
ita kuma Rumana ganin Ayush a tsaye ta kasa motsawa tace "you will not keep it?..."
Ayush jikinta a sanyaye ta ajiye cup ɗin tana jan ƙafa daƙer zata fice a ɗakin idonta kuwa na kan Junaid, shi ɗinma kallonta yake sun kasa ɗage idanuwansu daga na juna,
Ayush kuka ne yake shirin kuɓuce mata tayi saurin barin ɗakin,
hankalin Junaid ba ƙaramin tashi yayi ba,
É—aga Rumana yayi daga kansa ya kwantar da ita yana faÉ—in "ki kwanta ki huta.." kafin tayi magana kuwa har ya bar É—akin..
Ayush tangal-tangal take zata faɗi tsabar hajijiyan da yake ɗibarta da haka take haura upstairs a hankali gudun kar ta faɗo ƙasi, wani irin hajijiya ne ya fizgeta tayi baya zata faɗo daga saman beni,
ji tayi ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa, ƙamshin turarensa ne yake bugan hancinta anan ta ƙara tabbatar da Junaid ne,
lumshe idonta tayi wani irin ciwon kai ne yake damunta, gaba ɗaya ta kasa motsawa duk jikinta ya mutu babu sauran ƙarfi a tattare da ita..
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.