Trending Hausa Novels

Matar Damisa Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: MATAR DAMISA 1.txt

Chapter 47 of 69

---------------------> Isar su cikin hospital kenam, likitoci da nurses suka nufi yanda Malam yake É—auke da Ayush, kwantar da ita akayi akan gadon nan na turawa kai tsaye emergency room aka kaita,
Mommy Office É—inta ta nufa ta zauna akan kujera ta kifar da kanta saman table tana rera kuka mai cin rai...

*******

Daƙiƙa 5 tana cika Ayush ta finci zoben Dish da ƙarfin gaske cikin zafin nama,
Junaid yana zaune acan sahara shi da Damusar sa suna jiran cikar wahadi, yana lissafin lokaci har sai da yazo kan na biyar kuma na ƙarshe yaga wani haske mai ƙulƙule ya taho kamar walƙiya ya shige jikinsa hasken yabi ta hannunsa ya ratsa jikin Damusar dake hannunsa yana kan Damusa Sujjur,
wani irin baƙin hayaƙi ne yake fita daga jikinsu, har saida wannan hayaƙin ya gama fice wa sannan aka ɓatar dasu, ruhinan ko wannen su ya koma kan gangan jikinsa...

******

Sarki Raamud ne ya tashi yana shirin barin wajen da gawar Damusa yake, har ya bar falon fadar,
Kamar wanda aka zaburi Damusa da ƙarfin gaske ya miƙe tsaye yana karkaɗa gashin jikinsa,
a tsorace Bara'at dake gurin ta ƙwalla ƙiran sarki "Shugabaaa...."

Jin wannan ƙiran yasa ya taho da gudu a tunaninsa MUNAFURR ne ya dawo, ganin Damusa a miƙe ya tashi yasa sarki ya nufi gurinsa da gudu yana faɗin "Sujjurr! Sujjur ka tashi nagode Allah, zunzurutun farin ciki ne kwance saman fuskarsa, yana shafar bayan Damusar,

Ji yayi ya shiga cikin wani irin yanayi da sauri yaja da baya yana faɗin "zoben dish, Ɓingel ta cire.." ya kalli Bara'at yana murmushi, ya kuma cewa "ita ta taimake su, ita ta ceci rayuwarsu, amma kuma ita tana cikin mawuyanci hali..."
kafin ya rufe baki wani baƙin hayaƙi ne shima yake fita daga jikinsa, raɗaɗin da yake ji kamar ƙunar wuta,
ya ƙanƙame jikinsa da hannayensa biyu yana fitar da numfashi sama-sama, ga jijiyoyin jikinsa sunyi burtsi-burtsi shi kaɗai ne yasan irin ƙunar da yake ji a jikinsa,
wannan hayaƙin duk tsafin da yake jikinsa ne yake ta fita..
har shima Damusan yanzu babu wani tsafi a jikinsa,
Sarki Raamud yana cikin wannan halin har hayaƙin nan ya fita gaba ɗaya, yana maida numfashi ya ɗago yana kallon Bara'at wacce ta zuba masa ido tana kallon abun mamaki, ya soma girgiza kai yace "yanzu babu wani abun tsafi da ya ragu a jikina, normal nake yanzu...""
Damusa ne yayi wani irin girgiza sai da wannan macijin da aka wurga masa ya faɗo ƙasi a mace, ...

******

Junaid yana ƙwance saman gado yasa hannu ya yaye mayafin da aka rufeshi da shi, ya tashi cikin hanzari hannun sa yana kan fuskarta sakamakon hasken da yayi masa yawa, daƙer ya buɗe kyawawan eyes ɗinsa fari sol, haske fatarsa ya ƙara fitowa, a hankali yake lumshe ido kamar mai jin bacci ya sauƙar da ƙafafuwansa ƙasan gado, yana miƙa tare da Hamdala ya tashi yana duban kansa,
abunda ya faru dashi ne yake dawo masa kwakwalwa abun yayi matuƙar bashi mamaki, ganin lokaci guda waraka tazo masa,
a hankali yake motsa sweet lips É—insa yana faÉ—in "Deams, mafarki nayi, taya hakan zata faru?..."

yanzu baya jin komai a jikinsa ga wani irin kyau daya ƙara, komai nashi ya canza, hatta sumar kansa yayi tsayi yazo masa kafaɗarsa ga yanda yayi baƙi sai sheƙi yake yi gwanin burgewa,
sajen nan ya kwanta asaman fuskar sa har zuwa gemunsa ya ƙara tsayi ga laushin bala'i baƙi ƙirin sai sheƙi shima yake,
ga ƙaramin baki kamar wanda aka ɗosana! maroon lips ɗinsa ya ƙara fito wa kamar wanda aka shafa maroon stick,
yayi fari sol ya fito asalin kalar iyayensa Bahindiyawa,
he look like his father and d same like sarki Raamud.....
Junaid an dawo masa da cikakkiyar lafiyarsa da kuma ƙirar ƙarfi, ya zama zankaɗeɗe dashi kamar wanda aka ƙara masa tsayi da kuma ƙirar ƙarfi....

*MASHA ALLAH*

*A SAMU A FARA PAYMENT FAH SABODA AN KUSAN GAMA BOOK 1 FREE*

*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*

typing📲

🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)

*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)

*WhatsApp me 09065443871*

*Laifin DaÉ—i qarewa*

*FREE BOOK ZAI ƘARE NE A ƘARSHEN BOOK ONE*

*BOOK TWO DAZAN SHIGA SOON PAID NE,*
*YANA TAFE DA SABON SALO, DA KUMA CAKWALKWALIN CAKWAKIYA, KADA KU BARI A BAKU LABARI DOMIN GANI DA IDO 👀 YAFI JII👉👂*

*MATAR DAMUSAA BOOK 2 PAY ONLY 150👌👇👇👇*

*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*9065443871, OPAY BANK.*

*OR*

*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*2267236949, ZENITH BANK*

*SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER*
👇👇👇
*09065443871*

https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK ONE*
🅿️ ------->83 & 84 <-------

Ayush tana ƙwance rai a hannun Allah, dole sai anyi mata aiki a cikin cibiyarta sakamakon fincikar zoben da tayi da ƙarfin gaske hakan ya jawo mata tsinkewar jijiyar cibiya, wanda Allah ne kaɗai zai iya tasar kafaɗunta, likitoci ne zagaye a kanta kowa da kalar maganin da yake mata,
wasu sunyi mata operation suna mata aiki a ciki, wasu kuma suna ƙoƙarin ɗaura mata ledar jini saboda ba ƙaramin jini ta zubar ba,
kwana sukayi akan Ayush suna aikin ceton rai...

da sassafe misalin ƙarfe 6 Malam ya shugo Office ɗin Mommy yana ƙiran ta cikin damuwa tareda faɗin "mun bar Gawar Junaid ya kwana ko waiwaya shi ba'ayi ba, yanzu haka ina tunanin ya sanƙare tin jiya da rana.."

Mommy ce ta É—ago hankali a tashe tace "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, hankali na baya jikina wallahi na manta.."
Shima Malam cewa yayi "wallahi kuwa nima ina gida Junaid ya faÉ—o mun a rai, bansa a raina ya mutu ba,
amma na ƙira malaman da zasu masa wanka wata ƙila mu tarar dasu a gidan.."
da sauri suka shige motar suka fice daga cikin hospital,
A ƙofar gidan suka samu mutane har an taru ga malaman da suke jira suma, har da Doctor Hasheem shima ya samu labarin mutuwar Junaid a gurin Malam, Baba maigadi ne ya buɗe musu ƙofa yana shaftar kuka domin mutuwar Junaid ba ƙaramin girgiza mutane yayi ba,
su Mommy suna shiga cikin gidan saiga jiniyar motar sojoji har guda 10 suma labari ya riske su,

iya waÉ—anda zasu je É—akin Junaid sune daga Malam Lawan sai Doctor Hasheem sai kuma wasu malamai su 2 da kuma wasu sojoji suma su biyu haka suka haura upstairs suka nufi É—akin Junaid, ita kuwa Mommy a falo ta zauna tana sake rera sabon kuka..

shigarsu ɗaki suka tarar da Junaid ƙwance ya kalli sama tareda jan mayafi ya rufe kansa kamar dai yanda aka barshi, sai dai shi a yanzu bacci yake,

Bayan tashin shi ya shiga toilet ya yi wanka ya canza kaya yayi sallah sannan ya sauƙa down stairs ya nufi kitchen cikin sa'a kuwa ya samu abun taɓawa, yaci abinci yayi nakk ya kora da ruwan sanyi, ya kwanta akan sofa har bacci ya ɗauke shi, a falon ya kwana sai da asuba ne ya tashi ya koma room ɗinsa ya ɗauro alwala sannan ya tsayar da sallar asuba, daga nan ne ya haura bed ɗinsa ya lulluɓe kansa da mayafi sakamakon sanyin da akeyi..

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.