Trending Hausa Novels

Matar Damisa Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: MATAR DAMISA 1.txt

Chapter 23 of 69

Ƙarar gudun doki taji daga nesa ana nufan gurin da take tsaye, idonta akan yanda zataga ɓillowar mai tafo wa!

Wani mutumi ne fari tas dogo ne sosai ga ƙiran jiki kamar basamude duk jikinsa a murmurɗe gashi da ƙirar ƙarfi,
Ba riga a jikinsa sai wasu tarukucan sarƙoƙi a wuyansa da kuma dantsen sa duk sarƙoƙi yanda ya ɗaɗɗaure su a ƙatoton dantsen sa!
Suman gashin sa kuwa har gadon bayan sa ga laushi, sai wandon buzaye dake jikinsa,
Yana gudu da doki wanda shima yasha kwalliya, ta ƙasan sa kuma wani ƙaton damusa ne shima yake ta tiƙar gudu shima har da sarƙar sa a wuya...

Sai da yazo daf da Ayush sannan ya tsaya tare da sauƙowa akan dokin,
Tsayawa yayi a gaban Ayush yana kallon ta da murmushi a saman fuskar sa.
Yace
"Ɓingel na gaisheki gimbiya mai sarauta a hannu" sai da ya sunkuyar da kansa ƙasi alamar girmamawa sannan ya miƙa mata takobi mai shegen masifar kyau ga sheƙin da yake yana wal-wal, hannu tasa ta karɓa idonta akan mutumin mayar da tokobin tayi cikin gidansa
Tana faÉ—in "godiya nake...."

Shima damusan durƙusawa yayi ya gaishe da Ayush sannan ya miƙe,
Sake baki Ayush tayi tana kallon ikon Allah, a cikin ranta tace "ni kuwa a duniya nake?"

Kamar wanda yaji abunda tace sai ji tayi ya katseta da cewa
"Haƙiƙa keɗin gimbiya ce, kuma a duniya kike nan ɗin bayan masarauta ta ce! ba mai zuwa nan sai ni da kuma shalele na ya nuna damusar sa da hannu...."

Ayush baki na motsi kaɗan-² tace "waye ne kai?"
Murmushi yayi yana kallon ta yace "ɓingel, ni mahaifinki ne wanda kika daɗe kina son gani amma hakan baiyu ba sai yanzu gani ga ki ɓingel"

Zaro ido waje tayi cike da mamaki take kallonsa bata san lokacin da wani irin farin ciki ya ziyarce ta ba tana faÉ—in "yau ni ce a gaban mahaifina" lokaci guda kuwa ta fashe da kuka....

Tallafo kanta yayi yana faɗin "gimbiya bata kuka amma kin mayar da kuka abun sana'ar ki, hakan yana ƙona mun rai ɓingel,
Inaso ki zama jaruma, idan ana riƙe da takobi kuka ƙaiƙashewa yake!!!
Goge mata hawayen da ya zubo mata yayi da hannayensa masu laushin gaske...

(ikon Allah! A tunani na zanga wani dattijon tsohon boka sai kuma naga akasin haka,
Kyakykyawan mutum mai siffar jaruman bahindiye,
A tunani na zanga ƙazamin boka amma sai naga fashion man, a ƙalla shekarun sa bazasu wuce 45 ba, Ayushh kuma tana da 20years a duniya....)

"Ɓingel nasan kin tsaneni a cikin zuciyarki, sakamakon labarin da mahaifiyarki ta baki akaina, wanda hakan ba gaskiya bane,
Mahaifiyarki bata san komai a kaina ba, ni ba mungu bane, ni ba azzalumi bane, ni kaina nasan dalilin daya sa nake wahalar da Junaid wanda sirri ne a gareni, zaki san wannan sirrin amma ba yanzu ba akwai lokaci!
Ɓingel ki daina ɗaukar kanki cewa ke bakida ƴanci,
Ke Æ´a ce kamar kowa ni mahaifinki ne, kuma ta hanyar Aure aka sameki, amma sai dai mahaifiyar ki bata san da hakan ba,
Ni na sanar miki ne domin ki sakawa ranki nutsuwa, ki kwantar da hankalin ki a matsayinki na Æ´er masarauta gimbiya *MAYUSHERT* asalin sunanki kenam!!!
Sannan mahaifiyarki tana nan da ranta bata mutu ba, akwai lokacin da zakii ganta ba yanzu ba...
Kece AYANAR JUNAID hakan yasa damusa na baya iya motsi idan kina tare da Junaid domin duk wani motsin sa yana a tattare da Junaid,
Rashin motsawarsa kuma illa ne hakan yasa banaso kina kusantar shi saboda damusa yana cutuwa motsinsa kuma zaisa Junaid cutuwa,
Makaryar wannan tsafin kuma yana tattare da ke, hakan bazai yuba saboda zaki iya cutuwa, kuma zan iya rasa duk wani ƙarfin ikona...."

Ajiyar zuciya yajaa yana kallon ɓingel ɗinsa wacce itama kallon mahaifin natan take..

Leɓenta ne yake motsi da ƙer ta iya cewa "meye abun dake jikina na makaryin tsafin?.."

Dariya yayi short har sai da dimple ɗinsa ya lotsa yace "bazan sanar miki ba ɓingel, saboda nasan idan soyayya tayi nisa zaki iya cutar da ni,
Amma inaso ki sani cewa bazaku taɓa yin Aure ba a tsakaninku ke da Junaid,
Har sai an karya wannan tsafin jikinsa, idan kuma ba haka ba
*DAMUSA* *BAZAI* *AURI* *GIMBIYA* *MAYUSHERT* *BA*...

Kafin ta furta wani abu ya kuma katseta da cewa "ga wannan duk wani ƙundin tarihi na yana ciki, kada ki bari wani ya gani"
Wani ƙatoton littafi ne ya miƙa mata a bayan littafin an zana masarauta.....
Ya kuma cewa "duk wanda ya ɗauki littafin nan bazai taɓa buɗe shi ba, sai wanda yake da alaƙa da masarautar kamar ke...
Na barki lafiya Ɓingel.."

Juyawa yayi yahau saman dokin sa,
Ayush kuwa tana riƙe da takobi da kuma littafin da aka bata
Baki na rawa tace "shin menene sunanka?"

Murmushi yayi sannan yace " *SARKI* *RAAMAD*..

Ya kamata ki rage tsoro domin ke jinin Jarumi ne....
Sannan ni ba Boka bane sai dai na kasance ni matsafi ne, kuma ni musulmi ne! kada kuyi mun mummunan fassara..."

Yana kaiwa nan yayi tafiyarsa.
Ita kuwa Hasken daya kawota shine ya kuma É—aukar ta....
Sai tsintar kanta tayi a cikin toilet ga ruwan shower yanata zuba..
Jikinta ta duba taga jallabiyan Junaid aka maido mata dashi, ga kuma hannunta riƙe da littafin tarihin mahaifinta da kuma takobin da ya bata...

Bata ankara ba taji ance "Yushert wai mekike a toilet haka since."
Muryar Junaid ta jiyo yana magana..
Wanda tin É—azu shigowar sa room É—in bai ganta ba sai zubar ruwa yake ji,
A tunaninsa wanka take sake yi, bai yi tunanin babu kowa a ciki ba...

Rasa yanda zatayi da abubuwan da suke hannunta ta yi, da sauri ta buÉ—e drower cikin toilet ta a jiye su a ciki sannan ta rufe..
Ta kashe ruwan dake zuba sannan ta fito,
Zuba mata eyes yayi yace "daman ba wanka kike yi ba tin É—azun? to me kikayi kenan?"

kiɗimewa tayi ta soma ƙinƙina tana faɗin "daman daman da daman nayi ne"
Kallon ta yake cike da mamaki yace "kinyi mai?"
Gaba É—aya ta rasa mai zata ce, sai kawai zuba masa ido tayi...

Tashi yayi daga zaunen ya nufi toilet ya buÉ—e ya gama dube-dubensa
Yakai idonsa kan drower yasa hannu zai buɗe da gudu Ayush tayo kansa tana faɗin "na wanke toilet ne kar ka ɓata shi," ta kuma riƙe hannunsa wanda yakai zai buɗe gurin ma'ajiyin ta.

"Mtsw kuma shine ina tambayarki kika yi shuru?.."
Sunkuyar da kanta tayi ƙasa ta kasa ɗagowa,
Jan hannunta yayi suka fita daga cikin toilet,
Kai tsaye haurawa saman bed É—insa yayi
Ya kwanta tare da janyo mayafi ya rufe jikinsa
Tsayawa tayi Ayush, yace "ke bazaki kwanta bane?"

Murya ciki-ciki tace "ni bazan iya kwanciya a tareda kai ba"
"For what?"
Ya tambaya a takaice.
"Saboda bazan iya juran yanayin da zan shiga ba!"
"Ban ganeba? What do you means?"
Yayi tambayar yana kallon fuskar ta.
Sunkuyar da kai tayi ta kasa cewa komai...

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.