Trending Hausa Novels

Matar Damisa Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: MATAR DAMISA 1.txt

Chapter 33 of 69

da gudu Ayush tayi cikin babban falo tana baza idanuwa taga inane ɗakinta, domin akwai ɗakuna sosai ata cikin falo sai wanda ka zaɓa, ganin har yanzu Junaid bai shugo ba yasa ta faɗin "i can't wait gaskiya" ɗakuna ta fara buɗe wa tana lelleƙawa duk wanda ta buɗe sai ta ga wayam iya kujeru ne kawai, wasu ɗakunan baƙi ne, ba ɗakin da bata shiga ba amma bata ga ɗakin ta ba, tsayawa tayi tana tunanin "to ina ne ɗakina? kodai ba'a cikin falon nan yake ba", tana cikin wannan tunanin taji shugowar Junaid yana faɗin "ku shugo da kayan" wasu matasa biyu ne daya kira don su shugo da kayan da suka siyo cikin ɗakin Ayush,
Ayush zuba eyes tayi taga ina zasu kai kayan don tana da tabbacin yanda zasu kai kayan nan ne É—akinta,
ƙwatanta musu ɗakin Junaid ya yi!
kamar yanda ya gaya musu haka suka hau upstairs suna taka matakala kamar zasuyi ɗakin Junaid sai suka karya ƙwana ta ɓangaren hagun nan ne ɗakin Ayush kusan a jere dana Oga Junaid, sai dai shi nasa kana haurowa upstairs zakayi right hand ɗakin Ayush kuma ɓangaren hagun, Ayush ce itama tayi gaba zata bi bayan su bata ankara ba taji an riƙo hannun ta yayi wani irin juyi da ita kafin ya jawota jikinsa, suna fuskantar juna gashin kanta ne ya hautsino gaba duk ya rufe mata fuska, tsayawa yayi yana kallonta daga bisani ya kai hannunsa kan sumar kanta yana ture mata gashin, kyakykyawar fuskarta ne ya bayyana idonta a lumshe ga zara-zaran gashin ido suma sun kwanta sai sheƙi suke, hannunsa ya kai gefen fuskar ta yana shafa face ɗinta mai shegen laushi ga tafin hannunsa shima ba ƙaramin laushi ne dashi ba sai abun ya bada citta,
a hankali yake kai wa fuskar sa saitin nata tana jin yanda numfashin su yake hargutsuwa amma ta kasa buɗe eyes ɗinta, yana shirin kaiwa maroon lips ɗinsa kan ɗan ƙaramin bakinta yaji an katse masa hanzarin sa waɗanda suka shigar da kayan ne suka fito suna faɗin "Ogah mun kai, mun kammala shirya komai..."
Ok kawai yace tare da faÉ—in "send me your bank account"
washe baki sukayi suna godiya suka tura mishi, fita suka yi da murna domin sun san ba kuɗi kaɗan zai tura musu ba, kafin su fita daga harabar gidan kuwa har suka ji alert da sauri suka duba zaro ido suka yi baki ya gagara rufuwa baki a haɗe wajen cewa "five thousand and hundrend naira?? wow oga Allah ya ƙarawa rayuwa albarka wallahi, mutumin ya iya kyauta mai tsoka," haka suka bar gidan suna yabonsa....

GASKIYA BA CHAJI A WAYATA BARI NA BARKU HAKA SABODA DA 4% NAKE USING YANZU HAKA, KU BIYONI BASHI
NEXT PAGE MORE TYPING ZANYI DANA WANNAN PAGE....
*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*.

📲 typing ✍️

🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of tinger)

*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️✍️)

*WHATSAPP ME 09065443871*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK ONE*
🅿️ -------> 67 & 68 <-------

📲✍️✍️✍️ "fushi kike da ni?.."
Kawar da kai gefe tayi tana motsa lips kamar zata yi magana, fuskar nan ba annuri sai ƙaramin baki data turo, hannu yakai ya jawo leɓɓerin bakin ta, sakin ƙara tayi ta rufe bakin da hannunta acikin ranta kuwa tana faɗin "wannan Yaya Junaid ya cika mugunta wallahi, sai dai Allah zai saka mun"
Cikin rashin fahimta yace "zagina kike yi..." yaga bakinta na motsi, a ruÉ—e ta É—ago da dara-daran idanuwan ta tana girgiza masa kai "wallahi ba abunda nace, bakina ke mun ciwo" zaro ido waje yayi yana faÉ—in "your sweetest mouth ke ciwo..." shi kansa bai san ya faÉ—i haka ba, dasauri ya kawar da kansa gefe!
itama jin maganar tayi kamar daga sama, ta É—ago da sexy eyes É—inta tana kallonsa...
juyawa tayi ta nufi upstair yanda ɗakin ta yake, da sauri² take taka matakalan benin sai da taje can sama tsantsin benin ya zamar da ƙafar ta, ganin tayi sama yasa ta saki ƙara, daga sama tayo ƙasi sai timm a hannun Junaid ya yi saurin cabko ta kamar wata jaririya haka yake riƙe da ita, har ta saddaƙar ƙasa zata faɗo batayi tunanin Junaid zai iya riƙota ba domin da ɗan nisa a tsakanin su, buɗe eyes ɗinta tayi tana jujjuya su har gumi ya wanke mata fuska, zuciyar ta ne yake dukan uku-uku!
Sai daya ƙareta da kallo sannan ya saki murmushi ya fara taka stairs cikin nutsuwa yana ɗauke da ita, da haka har suka shiga new room ɗinta mai ɗauke da ƙayatattun funitures komai na ɗakin ɗan dai dai, ga flowers yanda aka shishshirya su,
wardrobe, mirror, drowers and others (gaskiya bazan iya lissafo muku tsarin É—akin ba sai dai ya tsaru kam).

launin colour ɗakinta kuwa purple ne, zuwa yayi ya kwantar da ita saman gadon ta, ya rufe ta da mayafi, ya miƙe zai tafi saida ya jawo mata ƙofar ya rufe sannan yayi nashi room,
Ayush tana kwance ta turo baki sannan tace "ji É—an iyawa shin yanzun dare ne har da rufana da mayafi, kodan ma baccin nake ji."
ta lumshe ido kamar mai yin bacci sai dai ba bacci ba kawai tana tariyo lokacin da ya taro ta zata faÉ—i daga saman beni, murmushi tayi ta rufe fuskar ta da hannayenta tace "i love you Yaya Junaid....

ta ɓangaren Junaid kuwa toilet ya shiga ya watsa ruwa a jikinsa sannan ya fito ɗaure da towel jikinsa ɗauke da danshin ruwa, ya goge jikinsa tsab ya mulka cream ɗinsa mai shegen daɗi ya feffeshe jikinsa da turare bayan nan ya nufi wardrobe ya zaro ƙananun kaya na shan iska 3quater da singlet masu launin milk, drower jikin mirrow ya buɗe zai duba hair cream abunda ya ci karo dashi ne yasa shi tsayar da hannun guri ɗaya ya zubawa littafin ido, daga bisani yakai hannu ya ɗauka abun mamaki har da takobi tsaya wa yayi yana jujjuya abubuwan, secret room ya nufa yana zuwa ya murɗa key ya shige ɗakin, waran ajiya ya samu ya ajiye ƙatoton littafin da kuma takobin ya yi ficewar sa....

******

Knocking akeyi a hankali ana furta suna "Lailah! Laila!! wai mekike ne haka kizo ki buɗe mun ƙofar dillah!!!,
Cikin gaga'ar bacci tace "wai kam waye ne?"
ta ƙarisa maganar tana lumshe ido, "bansani ba ƙaniya kizo ki buɗe.."
Murmushi Lailah tayi tana kwance a kasalance ta tashi, key ta murɗa sannan ta buɗe da smile akan fuskarta tace "Oyoyo my sweet ƙawass daman nayi kewarki.."
Shugowa tayi ciki tana murguÉ—a baki tace "ba wani nan inda kinyi missing É—ina ai da kin nemeni"
rungumar ta Lailah tayi sannan tace "sorry my besty kinsa Bros baya barina naje ko'ina bayan school" wani irin kallon sama da ƙasa Besty tayi wa Lailah tana faɗin "Ok kenam inban nemeki ba babu shan minti...???"
zaro ido Lailah tayi tace "why not my Besty! kinsan ba yau bane idan zamuje school muke wuce wa hotel ko? sannan gidan nan iya ni kaÉ—ai ce mace, sai Bros yana hospital da kuma Bros haydar shima yaje school zana exam, daga mu sai mu..."
kwashe wa sukayi da dariya suka tafa hannayensu suna faÉ—in "Shagaliiii.."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.