Matar Damisa Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: MATAR DAMISA 1.txt
Chapter 41 of 69
Ayush tana kwance jin abunda suke tattaunawa akai yasa ta zaro ido waje,
kamar wanda aka zabureta ta tashi zane tana faÉ—in "Mommy! Yayana Junaid bai mutu ba daman? dan Allah inason ganin Yaya Junaid, ku taimaka mun dan Allah.."
ta fashe da kuka tana magiya akan akai ta gun Junaid,
Mommy ce ta riƙe hannunta tana faɗin "Ayushert kiyi hakuri ganin Junaid a halin yanzu zai iya jefa ki cikin damuwa"
Ayush ce ta katse Mommy da cewa "Dan Allah ku taimaka mun, hankali na bazai kwanta ba indai banga Yaya Junaid ba...."
Doctor Hasheem yana zaune ƙololuwar baƙin ciki ne ya ziyarci zuciyarsa yana faɗin " Allahumma ajurni bi musifatu ƙalu innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Allah ubangiji yasa ba wata ƙulalliyar alaƙa ce a tsakanin Ayush da Junaid domin inhar hakan ta faru shikenam walwala zata ƙaurace mun, nashiga uku Ayush kar kimun haka please.." duk waɗannan maganganun a ransa ya yi su yana fuskantar Ayush wacce ta rikice wai ita sai an kaita gurin Yaya Junaid..
Ganin hawaye sharɓe-sharɓe akan fuskar Ayush yasa shi cewa "kinga Ayush tashi na kaiki gurin Junaid kinji, banson ganin kukan ki, kar kiyi mun asarar hawayenki" Mommy juyowa tayi tana kallonsa domin tasan mai yake nufi,
Ayush da sauri ta sauƙa daga saman gadon, ita ta farayin gaba sai Doctor ya biyo bayanta yana faɗin "tafiya a hankali mana, kar ki sanya ni cikin matsala"
suna tafiya a tare har suka isa ƙofar room ɗin, hannu Doctor yasa ya ture, cikin rashin sa'a suka same shi yanata sharar baccinsa, da gudu Ayush ta nufi gurinsa tana kiran sunan sa "Yaya Junaid! Yaya Junaid!! na gode Allah da yasa baka mutu ba, domin na tabbata dana rasaka a rayuwata gwara ni na mutu....."
gaban Doctor Hasheem ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske, kafin kace me har gumi ya wanke masa fuska...
ita kuwa Ayush tana zaune a bakin gado ta rirriƙe hannunsa ɗayan hannun kuma tana shafa sajen fuskarsa mai shegen kyau da sheƙi,
Doctor Hasheem gani yayi bazai iya juran ganin wannan takwaicin ba, shawara É—aya ya yanke cewa gwara shima ya sanar mata yana mutuwan sonta, domin yasan indai bai tara da wuri ba tabbas yana gaf da rasa Ayush duk da yasan Junaid ba Aure zaiyi ba...
gaban Ayush yaje ya tsaya sannan ya furta sunanta a hankali "Ayushhh.."
É—agowa tayi da rinanan eyes É—inta tana kallonsa bata ce komai ba tana sauraron mai zaice mata ne,
ganin ya ƙura mata ido kuma bashida abun cewa yasa ta kawar da fuskar ta gefe tana kallon kyakykyawan fuskar Junaid still hannunta na kan saman fuskarsa,
Hannu Doctor yasa ya riƙo hannun Ayush wanda yake kan fuskar Junaid sannan ya zamar da ɗayan hannun da take riƙe da hannunsa, ya miƙar da ita tsaye, yana mata wani irin kallo, ido cikin ido suke kallon juna ita dai Ayush abun mamaki ya bata a cikin ranta tace "wannan bawan Allah kuwa lafiyansa ƙalau? a gaban Yaya Junaid zai mun haka duk da yana bacci.."
haɗiyar yawu Ayush tayi sannan tace "Doctor ina jinka, kana riƙe da hannaye na sannan ka tasar dani daga zaune, shin wani irin kallo kake mun ne haka..."
Doctor Hasheem yana kallon cikin idanuwan ta yace "becouse i love you, I love you Ayushert, ke rayuwata ce sannan kuma mafarki na, ki cika mun burina na Auren ki dan Allah my Ayushert..."
Ajiyar zuciya Ayush tayi sannan tace "bai kamata ace munyi maganar soyayya a nan ba, saboda majinyaci ne a gaban mu..
"No Ayushert idan kika amince da soyayyata ni kin gama mun komai, inaso Junaid ya zame mun shaida duk da nasan baya cikin hayyacinsa, please my Ayush..."
yana murza mata lallausar hannayenta yana ƙara matsowa daff da ita,
a tunaninsa zata dakatar da shi sai kuma yaga akasin haka, farin ciki ne ya fara wanzuwa a zuciyarsa, hakan ya bashi daman rugumarta jikinsa yana faÉ—in "sorry my Ayush, keÉ—in farin ciki nane"
Itama kwantar da kanta tayi akan kafaÉ—arsa tana zubda hawaye ta kasa cewa komai,
ita dai hankalin ta yana kan Junaid, Doctor ne ya É—ago ta suna fuskantar juna, bakinsa yake shirin kaiwa nata saitin bakin, ganin lokaci guda Junaid ya buÉ—e idonsa, da sauri Ayush ta kawar da fuskarta ta nufi gurinsa tana faÉ—in Yaya Junaid ka tashi ne Alhamdulillah, ta zauna daf dashi tana shafar suman kansa...
shi kuwa Junaid yayi shuru baya iya cewa komai, sai binta da ido yake yi, ita kuwa hawayen farin ciki take zubar wa tana wasa da sajen fuskarsa da hannunta,
Doctor Hasheem kuwa zuba mata ido yayi, shi dai takaicinsa Ayush tafi nuna damuwa akan Junaid sosai ma..
ganin ransa yana shirin ɓaci yasa yayi saurin fice wa daga cikin room ɗin...
( ta wani ɓangare Ayush ta magance matsala Junaid a rashin sani, domin tinda Ayush ta taɓa shi, shikenam jaririn Aljani ya bar jikin Junaid sai dai an toshe masa bakin magana, bazai iya aikata komai ba...))
suna cikin wannan halin Ayush taga bai kulata ba, ta ɗago da kanta tana kallonsa tace "Yaya Junaid kayi shuru kayi mun magana mana ko zanji sanyi a raina, insha Allahu zaka samu sauƙi.."
tana kaiwa ƙarshen maganar ta saiga Mommy ta shugo da sauri tana faɗin "Ayush na karɓi takardar sallama, Junaid maganin gida yake buƙata bana hospital ba.."
cikin rashin fahimta Ayush take kallon Mommy tace "meya samu Yaya Junaid É—in har sai an nemi maganin gida..?"
Mommy ce tayo kan Junaid tana faÉ—in "kukan luÉ—a yake yi amma yanzu kuma naga baya cewa komai,"
ta dudduba shi naga jijiyoyin kwakwalwarsa basa motsi, kallonsa tayi cike da mamaki tace "Junaid meyake damunka ne haka?"
shi kuwa still idanuwansa suna kan Ayush ko ƙibta idon baya yi,
wasu likitoci ne suka shugo da keken guragu na asibity yanda zasu É—ora Junaid akai,
Ayush ganin yanda aka É—auki Junaid aka É—ora shi akan keken yasa ta faÉ—in "wai meyake faruwa ne da Yayana Junaid, Mommy inadai ba gurguncewa yayi ba, dan Allah Mommy ki sanar mun mana..!
Mommy ce ta zauna ta sanar da Ayush abunda ya faru har zuwa wannan lokacin...
Ayush ba abunda take sai kuka, idon nan ya yi jawur tsabar kuka har kayinta ya soma ciwo....
Da haka aka fitar da Junaid har harabar asibitin suna tura shi, sannan suka saka shi a cikin mota, Ayush ce ta zagayo ta ɗayan ɓangaren ta shugo,
Junaid ta kwantar a saman cinyarta, Mommy kuma ta zauna a gaban motar,
Doctor Hasheem ne ya shugo cikin motar yana draving É—insu yana kallon Ayush ta cikin madubin motar....
isar su gidan sukayi horn da ƙarfi,
Mommy tana faɗin "bansani ba ko Baba mai gadi ya dawo.." kafin ta rufe baki sukaji an buɗe gate, direct miƙar hanyar da zai sada su da harabar gidan suka nufa,
bayan Baba mai gadi ya rufe gate yana gudu ya biyo motarsu Doctor, cikin ƙanƙanin lokaci ya iso gare su yana faɗin "Hajiya ashe Junaidu ne ba lafiya..?"
tsayawa Mommy tayi tana kallonsa tace "Baba ina kaje? ka barmun gate a buÉ—e, sannan meya samu yarana?.."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.