Matar Damisa Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: MATAR DAMISA 1.txt
Chapter 37 of 69
tsabar tsoro da firgita sai da Bara'at ta faɗi zaune daga kneeldown ta dafe ƙirjin ta tana faɗin "shugaba ka kashe Junaid? Innalillahi wa inna ilaihi raju'un!" ta fashe da kuka "meyasa ka ɗauki wannan tsatstsauran hukunci? shikenam nima kuwa zaka rasani yanzu domin rayuwata batada wani amfani tinda har na gaza ceton Junaid."
Da gudu ta tashi ta miƙi hanyar fita daga cikin falon masarautar kai tsaye ɗakinta ta nufa tana shiga ta danna key, zuwa tayi ta ɗauko poisen zata sha,
wani irin bugu akayi wa ɗaki ya buɗu, cafko hannun ta yayi sannan ya yi wurgi da ƙwalbar gubar ya zabga mata mari ya hankaɗata saman gado yana faɗin " ban taɓa sanin baki da hankali ba sai yau, idan kika kashe kanki kin mutu kafura..."
katse shi tayi da cewa "wanda yayi kisan kai kuma fa?? ya kamata kaji tsoron Allah Abul Mayush, ka sani fa wata rana zaka mutu, bawai kai kaÉ—ai za'a bari a doron duniya ba,
Ka kashe Junaid ita kuma fa Ayush shin zata rayu ne? bakayi tunanin haka ba, ka yanke hukunci saboda ita to ka sani ko da ran Junaid ko ba ran Junaid Ayush zata mutu ne,
an zo wajen da bazata iya rayuwa ba tare da Junaid ba....."
ta tinshire da dariya tana tafa hannayen ta biyu ta kuma cewa "shin baka san Junaid da Ayush jininsu É—aya ba ne?
to ka É“arar yanda ka kashe Junaid haka Æingel É—inka ma mutuwa zata yi, bazata rayu ba......"
Ja da baya Sarki Raamud ya soma yi tabbas maganganun Bara'at sun juyar masa da kwakwalwarsa, zuciyarsa ne ta fara harbawa da ƙarfin gaske,
lokaci guda kuwa ya yi regret akan abunda ya aikata, "haƙiƙa Ayush itace mahaɗin Junaid, kuma jininsu ɗaya yanaso ya warware wannan al'amarin amma ya kasa..." haka ya tsaya cak yana maganar zuci, jikinsa ya sake baya jin daɗin jikinsa sosai, ga wani irin zazzaɓi da ya rufe shi..
lokaci guda kuwa ya zabura da sauri ya fice daga cikin room ɗin Bara'at wacce itama tsayawa tayi tana kallonsa cike da tsana da kuma mamaki ga hawayen da suke gangaro mata, kamar tasan abunda yake ransa ta furta cewa "yanzu haka nasan zai tafi ƙasar nigeria ne domin yaje ya dubo su Ayush...."
itama da gudu ta nufi waje, ta samu Sarkin har ya hau kan wani dokinsa mai ƙarfin gaske da kuma gudu, domin zai iya zuwa nigeria da wannan dokin ba tareda ya hau jirgi ba, domin yasan ta ko ina nemansa ake..
har ya fara tafi ta ƙwalla masa ƙira da ƙarfi tana faɗin " *kasa a ranka cewa kana barin cikin masarautar nan shikenam ka barshi har abada, kuma ba kai ba mulki! ƙa'idojin dokar kenam, na tunatar dakai...*
Sarki da jin hakan ya tsayar da dokinsa, gabansa na yankewa, idanuwansa
kuwa har sunyi jawur, fuskarsa ya nuna alamar damuwa ajiyar zuciya yaja sannan ya kanne idanuwansa sosai, yana so yayi kuka amma ba hali domin zubda hawayensa shima wani makaryin asiri ne a jikinsa...
Ba yanda ya iya haka ya juyo da dokinsa saboda mulkinsa shine babban abun tasirinsa kuma shine tushen sa na iyaye da kakanu...
Haka ya sauƙo yana tangaɗi hajijiya ne yake shirin ɗaukarsa, zuciyarsa tana bugawa da ƙarfin bala'i, tabbas shima yasan idan babu Ayush shikenam tashi tazo ƙarshe,
saida yazo daf da Bara'at ya tsaya yana kallonta cike da tausayawa kansa, bazai iya control hawayensa ba haka ya durƙusa da gwiwowinsa sannan ya fashe da wani irin matsanancin kuka kansa a sunkuye....
zaro ido Bara'at tayi tace "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, nashiga uku *SHUGABA* tinda uwata ta haifeni ban taɓa ganin damuwa a fuskar ka ba balle hawaye uwa uba har da rera kuka, abun babba ne, shikenam ka korar da ALJANUNKA sunga hawaye a idonka...."
Aljanun da suke cikin masarautar sa kuwa haka suka rinƙa ɓacewa,
duk wani abun tsafi sai ɓacewa suke,
duk abubuwan tsoro dake cikin dajin maƙarƙashe duk sun ɓace daman shi ya ƙirƙire su da yarjejeniyar bazasu ga hawaye a idonsa ba har abada...
gashi kuwa yanzu komai ya rushe masa ata sanadiyar Ayushert!
Haka masarautar nan ta dawo babu komai na tsafi a ciki, daga shi sai matarsa Bara'at sai kuma DAMUSAR JUNAID wanda shi kuma makaryin tsafinsa yana jikin zoben cibiyar Ayush,
Shima Sarki Raamud akwai sauran tsafi a jikinsa wanda shima makaryinsa yana a tattare da wannan zoben cibiyar Ayush,
suna tsaye a harabar masarautar sai ga wasu tsuntsaye suna shirin shugowa, da gudu Sarki ya miƙi hanyar babban gate wanda ya buɗe yaje ya rufe ya danna ƙwaɗo
haka tsuntsayen suka juya ba halin shugowa domin akwai hayaƙin da suna shugowa zasu ƙone...
ita kuwa Bara'at jikinta ne yayi sanyi domin za'a iya kawo musu hari a koda yaushe idan aka fiskanci babu masu kula da masarautar nan, tana cikin wannan tunanin taji ya riƙo hannunta suka shiga cikin falon masarautar, gaban Damusa yaje ya durƙusa yana shafarsa
murya na kakkarwa yake magana da Damusar "kai kaÉ—ai ne ka rage mun a halin yanzu daga kai sai matata, itama Allah yasa kar ta gujeni, ga shi na rasa É—iyata tilo, nasan Æingel mutuwa zata yi! banaso na rasa masarautar nan saboda amanar mahaifina ne.."
Hmmm! ajiyar zuciya yayi sannan yakai idonsa kan Bara'at wacce take tsaye kanta a sunkuye, ya taso yazo gabanta ya riƙe hannayenta yana faɗin "idan bakya son zama dani akwai sauran tsafi a jikina zan mayar dake nigeria a yanzu, sai dai amma gurin zama zai gagare ki..."
Bara'at tana kuka tace "ba yanda zanje ina tare da kai, gurin wacce zanje a nigeria nasan ta mutu, ina zanje to? sai dai mu mutu tare...." ta ƙarasa maganar tana kuka ta rungumi Sarki,
shima hawayen yake zubar wa yana mamakin ta yanda al'amarin nan ya afko masa lokaci guda,
Abubuwa sun taɓarɓare masa, lokaci ɗaya ya zamo kalar tausayi,
kamar ba shi bane *SARKI RAAMUD, SARKIN MATSAFAN DUNIYA*....
(( *Yaaa Salam!*
*ku duba abunda ya faru da Mahaifin Ayush lokaci É—aya,*
*ba'a jayayya da ikon Allah, duk abunda Allah ya tsara ba makawa sai ya faru kafin ƙiftawar ido,*
*Allah shine mai komai a hannu kuma shine mai mulki shine mai yin abunda yaso, duk tsafin mutum, duk izzar mutum, duk ƙarfin ikon mutum, duk zalincin mutum a lokaci ɗaya Allah zai gama da shi,*
*ya Allah kasa mufi Æ™arfin zuciyar mu ðŸ™ðŸ™* ))
******
Doctor Hasheem ne ya fito falo yana zaune akan sofa idonsa akan plasman,
Muryar Laila ya jiyo tana faÉ—in "Bros kai kaÉ—ai ne a falon?.."
Juyawa yayi zai mayar mata da amsa kwatsam eyes ball ɗinsa suka sauƙa akan Maimoon wacce tasha doguwar riga da gyalensa iri ɗaya tasha makeup ba ƙaramin kyau tayi ba,
ta ƙaraso gaban Dr Hasheem ta durƙusa gwiwowinta ƙasi sannan ta kamo hannayensa tana zubda ƙwalla tace "Yaya Hasheem! bansan laifin mai nayi maka ba, kasan ina matuƙar ƙaunarka, bazan iya juran rashin ganinka ba, bazan iya juran rashin jin muryarka ba, amma meyasa ka daina zuwa gidan mu? ka daina ƙirana a waya ko da saƙo ne,
why my Doctor! why!! why!!!...."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.