Farar Taska Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Farar Taska Part 1 Complete Hausa Novel.docx
Chapter 9 of 14
TWO WRITERS EMPIRE âœï¸âœï¸
Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su É—ebe muku kewa,
FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH
ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA
Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira É—ari shidda shidda, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya.
[8/3, 6:33 AM] J💕: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt?mode=ac_t
*FARAR TASKA*
Fertymerh Zarah
9
Murmushi Shamwilu yayi yana addu'a a ransa Allah yasa karshen auren yau, tana haihuwa idan ta gama idda ya aure ta koda karshen zaman sa da yasira zai zo karshe, akan soyayyar Ummy babu abinda ba zai iya ba. Yaran Suna zaune tana tsaye tana yiwa meelah faɗa akan abinda tayi wa mahaifinta, yaran suna maida mata magana akan rashin kyautawar mahaifin nasu babu zato taji ya haɗa kanta da nashi, tayi tangal tangal zata faɗi tayi saurin riƙe ƙofar ɗakin, nan take wani duhu ya mamaye idanuwanta, yaran suka tashi a tsorace suka nufe ta cike da tashin hankali, ransa in yayi dubu ya baci, yace "ashe amanata kike ci a waje, maza kike zuwa kina roƙon su kuɗi kike cemin aikatau kike zuwa, yau asirin ki ya gama tonuwa kuma wannan mashayin giyar da kike zagi a waje kin gama zama dashi domin zaki bar min gida a wannan daren ki tattara komai naki ki fice min a yanzu" tsananin tsoro da razana suka bayyana a ƙwayar idanuwanta duk da jirin da take ji bai hana ta durƙusawa da sauri ta riƙo ƙafafun sa ba, "kayi min rai mai gida, albarkacin ƴaƴan nan ka barni na cigaba da zama dasu ko da babu aure a tsakanin mu" yace "kin ji na rantse wallahi sai kin bar gidannan dake da shegun yaran ki, Sai a yau na tabbatar da cewa lallai ba ƴaƴana bane shiyasa kaf babu mai kama dani, a yau Shamwilu ya sanar dani komai a game dake har shi kansa da kike neman sa, ashe baki da mutunci haka shashasha har neman abokina kike, wlhy ki tattara a yanzu ki bar gidan nan kije can gidan kwartayen ki su baki gurin zama, tsautsayi ya saka shi sa ƙafa ya ture ta sai a cikin ta, nan take ta saki ƙafarsa ɗaya ba shiri cikin wata razananniyar ƙarar dana firgita yaran har shi kan shi ma, nan take ta zube gurin a sume, yaran suka soma taba ta suna kiran sunan ta amma ko motsi, jikin sa ya ɗauki karkarwa yaje yana tabata babu alamar numfashi a tare da ita, yace "Kai maza maza kuje maƙota ku sanar Ummy ta zame ta faɗi bata numfashi, wallahi muddin wani acikin ku ya faɗa ni na dake ta zan tsine masa albarka kuma ba zai zauna dani gidan nan ba" Deejah ta tashi da gudu taje ta kira Saratu yana ganin haka ya fice da sauri ya bar gidan yana addu'a Allah yasa ba mutuwa Ummy tayi ba, hankalinsa sosai ya tashi kuma ya shiga damuwa sai gaban sa dake faman faɗuwa. Saratu kuwa tana zuwa halin da ta sami Ummy aciki ya ɗaga hankalinta ta sami ruwa ta zuba mata a fuska da kyar Ummy taja numfashi cikin wahala sai a lokacin hankalin Saratu ya kai da jinin dake fita jikin Ummy, ta dubi yaran tace "ku jira a waje, ku yiwa mahaifiyar ku addu'a haihuwa zata yi" Sai suka ji daɗi sosai suka fice da farin ciki, Saratu ta dubi Ummy cikin tausayawa tace "me ya same ki Ummy? ta rumtse idanunta da kyar kafin tace" Saratu Ina ji mutuwa zan yi irin wannan azaba da nake ji a cikina, kinsan lokacin haihuwa na bai yi ba". Tace "Nima shine nake mamaki, mun ji ƙarar ki yanzu ni da Wadata sai kuma ga Deejah tace mu zo kin zame kin faɗi, na tabbata ba gaskiya bane domin naga fitar Audi hankalinsa a tashe yana waige waige, me ya aikata maki Ummy? Sai ta fashe da kuka mai tsanani, cikin kukan tace "ya dake ni Saratu, kuma yace na fice masa daga gida, ina Audi yake so naje da wannan daren kuma ina yake so na zauna da yaran nan, me na aikata masa haka da zafi, ya manta bani da kowa a duniyar nan bayan shi? Saratu ta girgiza kanta idanunta cike da hawaye, tace" daɗi na dake Ummy kina manta Allah a al'amuran ki, kina manta shine gatan ki a duniya ba Audi ba, kina manta acikin ikon sa kike zaune a gidannan ba ikon Audi ba, dan haka Allah kaɗai yasan inda zai baki ki zauna kuma shine zai maki gata ke da yaran ki, bara naje na kira Baba Shatu ta duba ki idan haihuwar ne sai ta taimaka, idan bashi bane sai mu jira zuwa wayewar gari muga hukunci irin na ubangiji". Ummy bata yi magana ba saboda zafi da raɗaɗin da take ji, Saratu na fita yaran suka yo kanta sai sannu suke mata cikin tausayawa, bata jima da fita ba sai gata tare da dattijuwar aka fitar da yaran ta duba ta ga ba haihuwar bane tayi tafiyar ta, cikin ciwo da azaba ta kwana a wannan daren ko kaɗan bata yi barci ba, yaran duk sun kwanta a waje sun yi barci, Saratu ma ta kishingiɗa daga gefe, tayi kuka har ta gode Allah kuma tayi addu'a har babu iyaka, yanda taga dare haka taga safiya babu wani canji, Saratu da sassafe ta bar gidan taje tayi jiqe jiqen su na gargajiya ta kawo mata duka babu wani canji, ciwo sai gaba gaba yake yaran kowanen su idanu sun yi luhu luhu sun kumbura saboda kuka, Audi kuwa shima yanda yaga dare haka yaga safiya bai runtsa ba tunanin sa ko ta mutu, washe gari yana jiran yaji an sanar da mutuwar ta yaji shiru hakan ya tabbatar masa tana raye, ya tashi a fusacce ya nufi gidan da zumar ta haɗa komai nata ta bar mashi gida, halin da ya same ta aciki ya tabbatar masa da haihuwa ce zata yi, ya zauna ya soma lissafi a iya tunani sa ya san bata isa haihuwa ba, ko ma dai menene ta haifa masa yaro sak irin sa zai yafe mata ya cigaba da zama da ita, ganin har lokacin babu wani cigaba Saratu ta fice tana hawaye taje ta sanar da Wadata, a tare suka fita nema mata magani gurin wani malami da mutanen ƙauyen ke karɓan taimakon haihuwa, Audi ya ƙarasa ɗakin yana faɗin, kin ga wannan wahalar da kika yi na yafe maki na yarda ki cigaba da zama ke da ya'yanki, ki haifamin yaro namiji sak Irina bazaki ƙara zama da yunwa ke da yaran ki ba ke ko kallon banza wata tayi maki a maƙota sai mai gari ya raba ni da ita, dan haka maza maza ki fiddo min shi ina son sa ko da hasken fatar ki ne zan haƙura na barwa Allah amma ya kasance namiji, idan kin san mace ce kada ki kuskura ta zo duniyar nan wlhy zan azabtar dake fiye da baya" yaran suka ɗago suna kallon sa, Ummy kuwa babu abinda ta ke fahimta domin ta daɗe da fita hayyacinta, ya dube su yana faɗin "eh na yarda da mahafiyar ku zaku cigaba da zama anan gidan kuma ku yi addu'a ta haifi ɗa namiji albarkacin sa zan ciyar daku, amma ku sani ko da wasa wani acikin ku ya kuskura ya taba sa da sunan duka wallahi sai na karya yaro, ya tashi jin motsin kamar zaa shigo ɗakin, Saratu ce da magani a hannun ta ko kallon sa bata yi ba taje da sauri ta ɗaga kan Ummy tare da kafa mata magani a baki tana bata tana sha, ya fito gidan dai dai lokacin Shamwilu zai shiga nasa gidan, yace "abokina lafiya na ganka sai gumi kake haɗawa, ba dai zafin rabuwa da Ummy kake yi ba kai da zaka yi aure? Audi yace" Ai na amince ta cigaba da zama a gidan Shamwilu saboda kawai tausayin halin da take ciki saboda nace ta bar gidan ne ta shiga wannan halin" annurin dake fuskar Shamwilu ya kau, yaji wani ƙunci a ransa batare da yayi magana ba yayi shigewar sa, Audi bai kula da yanayin sa ba saboda babu nutsuwa a tare dashi, yini ranar ana abu ɗaya gabaki ɗaya ta ƙarasa fita hayyacinta ta galabaita ainun, har zuwa washe garin ranar again haka ta kwana, Sai a lokaci suka yi tunanin ko zasu kai ta asibitin nan ƙauyen, yace "shi ko ƙwandala bazai kashe a kanta ba" Wadata da matar sa suka nemi taimakon wasu maƙota mata aka riƙeta da ƙyar take takawa duk nisan asibitin haka aka je da ita, Audi yana biye a bayan su sai mita yake ba wanda ya kula sa, yana kallo Wadata yake bayar da kuɗin sa idan aka buƙaci wani abu, sau biyu yana leƙa ɗakin haihuwa tare da sanar da ita kada ta kuskura ta haifa masa mace idan ba namiji ba, kowa sai kallon sa yake da mamaki, cikin hukunci na ubangiji da taimakon nurses ɗin aka samu ta haihu da ƙyar bayan wahalar da ta sha.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.