Farar Taska Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Farar Taska Part 1 Complete Hausa Novel.docx
Chapter 5 of 14
[8/2, 8:40 PM] J💕: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt?mode=ac_t
*FARAR TASKA*
Fertymerh Zarah 💕
5
Tafe suke suna hira sama sama, zuciyarsa a jagule yau kamar ko yaushe, ganin yanda yaran shamwilu suka yi aikin gona sosai yau shi ko rabin rabi bai samu yayi ba kuma acikin su babu wani wanda yake taimaka masa, kallon shamwilu yayi yace " Shamwilu kai abokina ne na amana kasani, mun taso da kai tun muna yara kuma muka girma a tare har muka zo muna makwabtaka da juna saboda abotar mu, na ɗauka yaran ka yara na ne ko ban fito nayi magana da fatar baki ba zaka iya basu umarni da su taimaka min a tawa gonar, banda haka ma acikin su huɗu ko ɗaya ne ai zaka iya bani muyi aikin tare". Shamwilu ya kece da wata dariya kafin ya dubi Audi yace " ka manta yaran yanzu ka haifesu baka haifi halin su bane, ni kaina ba sai nayi da ƙyar ba kafin na samu su zo min gonar balle har kayi tunanin su taya ka taka gonar, ni bazan hana ba idan zasu taimake ka, gobe ka gwada yi masu magana kaji" Audi yayi jim kaɗan kafin yace " idan na haifi yaro dole yabi umarni na domin ni nake ciyar dashi na tufatar dashi kuma yake zaune a qarqashin inuwa ta, tabbas Shamwilu da nine nake da ƴaƴa maza kake da mata ko basa so dole sai sun taya ka aikin gona albarkacin ƙawancen mu" Shamwilu ya bata fuska kaɗan yace " Audi me kake nufi yanzu kana son gayamin nayi ma ba dai dai ba saboda basu taya ka aikin gona ba, nace ka barsu gobe idan mun fito zan masu mgn su taya ka, menene na fushi kuma" Audi yace "Allah ya kaimu goben" suka cigaba da tafiya har suka iso gida, ƙofar gida suka zauna suna mayar da numfashi cikin gajiya, basu jima da zama ba sai ga su Safeenah sun dawo daga ɗebo ruwa, suka gaida su kafin su shiga cikin gida, Shamwilu ya tabe baki yana jinjina kansa kafin yace " wallahi abokina waɗannan yaran guda uku da ace akwai wani bature a garin nan tabbas zaa ce ƴaƴan sa ne ba naka bane, kai ni har yanzu bani da tabbas akan Ummy ba fita take wani guri tana haɗuwa da wani daban ba". Audi yayi jim kaɗan kafin yace " Ummy Salihar macece zan yi shaidar hakan akan ta, kuma duk inda zata je baya wuce aikatau da take zuwa sai nan gidan Wadata maƙocin mu, amma nima kaina idan na dubi yaran wani lokaci har ƙoƙonto nake idan jinina ne su kaf zuri'ata kasani bamu da farare kyawawa irin yaran nan, wani lokacin kyawun nasu ruɗani yake naji na tsane su nayi ta dukan su batare da laifin komai ba, ko kuma nayi ta dukan uwar tasu kamar yanda ka bani shawarar laifi kaɗan tayi min nayi mata duka kada ta raina ni, kuma fa duk kyawun nan nasu ai Uwar ta fisu kyau ko ka manta, kawai wahala ne da yanayi na cikin nan da take ɗauke dashi ya gusar da komai nata" cikin takaici Shamwilu ya ja tsaki yafi kowa sanin Ummy tana da kyau domin ya jima da son ta a zuciyarsa bashi da buri na ganin Audi ya rabu da ita shi kuma ya samu ya aure ta ko zata haifa masa kyawawan ƴaƴa masu kama da ita, ya muskuta kamar gaske yana kallon Audi, yace " Matar nan idan ta sake haifo maka wata macen wlhy kayi gaggawar rabuwa da ita domin babu ƙashin arziki a tare da ita kuma ita ɗin ba alheri bace a rayuwar ka, kowane gida yana buƙatar magaji yanzu da ace ta haifa maka ƴaƴa zaka dinga wahala a gona ne? Audi ya girgiza kansa, Shamwilu ya cigaba da faɗin " mutanen gari sai su fara maka kallon wani golobo kamar ba cikakken namiji ba, ka kasa haihuwar ɗa namiji raini ya zo ya shiga tsakanin ka da zawarawan garin nan su ɗauka baka da ƙarfin haifo ɗa namiji matarka ta fika ƙarfi". Audi yaji wani bacin rai sai gumi yake haɗawa saboda damuwa, Shamwilu ya cigaba da faɗin " sai kaje neman aure a hanaka akan wannan idan baka sani ba, saboda kowa kallon raggo yake ma kamar bazaka iya aikata komai a shimfiɗa ba sai matar ka, kai ni fa ko kaɗan bana sassauta wa yasira saboda kada ta raina ni, wlhy duka nake mata sosai ko gyaran murya nayi a ƙofar gida zaka ganta durqushe tana gaida ni cikin tsoro, balle kai mai mace irin ummy kace ba zaka kara aure ba" Audi ya dube sa cike da damuwa yace " gayamin menene abin yi yanzu ina cike da damuwa, ina buƙatar magaji, ba dan komai ba sai dan Allah ya saka min son haihuwar namiji a yanzu, mu'amalar ka da yaran ka tana burgeni musamman a gona" Shamwilu yayi wani shu''umin murmushi yana jan gemun sa, yace "abokina kasani nayi maka ƙoƙari wajen ara maka gonar nan tawa da kake juyawa, kasani baka da komai a duniyar nan banda wannan gidan da kuke zaune komai ka siyar kasha giya, sanda ka rasa iyayen naka babu shawarar da ban baka ba akan kada ka banzantar da kuɗin ka siye gona sai ka ƙi zance na gabaki ɗaya ka tare gidan giya inaji sau uku rak ka taba siya min giyar, sai da kuɗin suka ƙare ka neme ni, to magana ta gsky na kusa na karbi gonar bada jimawa ba domin siyar da ita zanyi na haɗa kuɗin da wanda ke hannuna na ba yaran zasu je can kudu neman sana'a". Audi ya dube sa jikinsa ya ɗauki karkarwa yace " Shamwilu idan ka karbe gonar ya kake so nayi da tawa rayuwar, a ina zan nemi abinci? Shamwilu ya ja gajeren tsaki cikin takaici yace " da kake neman abinci a gonar ina ce saidawa kake kana shan barasa da kuɗin, iyalinka kake ciyarwa da abincin ne da zaka damu? Ƴaƴana duka maza ne kasani kuma dole zan basu jari su je su nemi sana'a". Audi yayi shiru cikin tunanin mafita sosai yake ƙaruwa da gonar duk da ba wani abin kirki yake nomawa ba, Shamwilu yace " ko menene abin damuwa kai da kake da manyan jari a gaban ka" Audi ya dube shi da mamaki batare da yayi magana ba, Shamwilu yace " eh mana, kana da ƴaƴa mata irin wannan me kake jira, ai kawai ka bayar da su aure ka huta kowacce acikin su zaka sami alheri" cikin rashin fahimta yace " Shamwi bangane ba, waye zai yarda ya aure su kuma wane alheri zan samu a tattare da waɗannan fararen mata? Shamwilu yace " ai kawai muje can mashayar giyar tamu ka sami wani ka haɗa shi da wannan babbar, dama ƴaƴa mata ai jari ne saboda jarin ake haifarsu, ka bayar da ita akan kuɗi dubu ɗari uku zuwa sama, idan ka sami kuɗin ka siye wata gona ƙarama ka riƙe sauran canjin kasha barasa, nima ka bani wani abu na saka a aljihuna". Audi yayi shiru cikin tunani kafin yace " Allah ya shaida ya sani ina son ka shamwilu sosai saboda duk na shiga matsala kana da hanyar fitar dani, hakan zanyi tun da dama basu da wani amfani a gurina ga mahaifiyarsu sai wahala take wurin ciyar dasu, idan lokacin siyar da gonar taka yayi zan mata aure da duk wanda na samu zai bani kuɗin". Shamwilu ya tashi ya nufi cikin gidanshi ya bar shi gurin a zaune, da shigar shi ya ajiye kayan shi inda ya saba ajiyewa ya nufi ɗakin Yasira, " ranki shi daɗe na same ki lafiya". hararar sa tayi kafin taja tsaki tana faɗin " tun ɗazu ina ka tsaya har yaran nan suka dawo baka dawo ba? Yace " ai ina tare da Audi a waje tun ɗazu kiyi haƙuri masoyiya ta" tayi mashi banza, ya washe baki yana faɗin " ina abincin nawa? Cikin takaici tace " baka shigo da wuri ba na bawa yaran sun cinye". yayi shiru cikin bacin rai yaje gona yayi aiki ya dawo gidansa ace baa ajiye masa abinci ba bayan shine mai nemo wa, ta juyo tana kallon sa tace " kayi min tsaye akai ko akwai wani abu" ya haɗiye wasu yawu da ƙyar tare da girgiza kansa, ya juya har zai bar ɗakin sai ya dube ta yace " baki yi ajiyar ko ɗan wani abu ba na saka a bakina ko ruwan kunu ne, yunwa nake ji sosai Yasira" cikin bacin rai tace " to ko ni zaka ɗauka ka cinye ne? ya girgiza kansa yana faɗin " tuba nake ranki shi daɗe kiyi haƙuri" ya juya zai fice tace " ji mana" ya juyo da sauri yana kallon ta, tace " ni kaina ban samu naci abincin ba na bawa yaran sun dawo gona duk sun gaji ga yunwa sai nace su cinye duka, kaje kasuwa ka siyomin gasashen nama mai ruwa ruwa shi kaɗai nake son ci a yanzu kazo ga ruwan kunu na ajiye maka kasha", yace " kiyi haƙuri babu kuɗi hannuna a yanzu, amma nayi maki alƙawari anjima idan na fita zan zo maki dashi" tace " yanzu nake so kaje ko bashi ne ka nema ka siyomin yanzu kafin raina ya baci kasani kuma bazan maka da kyau ba, kuma kasani na saka yarannan sun samo min bulala (geza) idan ka sake anjima ka dawo min a buge sai jikin ka ya gayamaka wlhy". Yace " ai na daina shan barasa tunda bakya so Audi kawai zan ra ka" tayi ƙwafa tana girgiza ƙafafunta tace " naman nake jira yanzu kada ka bata min lokaci" ya fice da sauri jikinsa har rawa yake saboda yunwa, bai yi tunanin zai sami Audi a zaune inda ya barshi ba ya ɗauka ya jima da shiga gida, yana fitowa suka haɗa ido, yace " baka shiga gida ba kenan? Audi yace " ina zaune ina ta faman tunani, lafiya na ganka kamar a hargitse? Shamwilu yayi murmushin yaƙe yace " yanzu na gama dukan yasira shine ka ganni haka, inace kaji tana ihun neman taimako ko? Audi yace kunnena ba a can yake ba, ni tunani nake akan rayuwar nan tun ɗaxu, amma me tayi maka da dawowar ka zaka dake ta yarinya tana maka biyayya sosai". Shamwilu yace "girki tayi min babu nama aciki, na gayamata ko ban bayar da kuɗin nama ba dole zata saka kuɗin jikinta ta siye naman ta saka min ko da tsoka ɗaya ce idan ba haka ba duk ranar da ta sake ta min girki ba nama tabbas jikin ta zai gayamata" Audi cikin mamaki yace " yanzu saboda wannan ka dake ta" shamwilu yace " ƙwarai kuwa ai gobe bazata sake min girki ba nama ba ko bata da kuɗin zata je taci bashi ta saka min, ai shiyasa nake gayamaka idan baka dukan mace raina ka take sosai kuma bazata taba ganin ka da girma a idon ta ba". Audi ya jinjina kansa cikin gamsuwa tuna yanda Ummy ke tsoron sa kuma tana masa biyayya akan komai yace, Shamwilu ya soma tafiya yana faɗin " sauri nake yunwa nake ji zanje na siyo naman na dawo, ba dan mutanen gari su zage ni idan suka ganta a yanzu ta fito ba da tabbas ita zata je ta siyo naman, duk na yiwa jikin ta tabon duka shiyasa bana son ta fita a yanzu" Audi yace " shikenan sai ka dawo nima zan shiga daga ciki na nemi abinda naci".
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.