Complete Hausa Novels

Farar Taska Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Farar Taska Part 1 Complete Hausa Novel.docx

Chapter 12 of 14

" yi haƙuri aminina kasani duk duniya babu wanda zai maka shaida irin wacce zan maka, a ruɗe nake da kai ne baka saba zomin kana hawaye ba dole na ruɗe, wai menene a zanin kake boyewa? Audi ya buɗe jinjirin yana nuna masa, "yaron da ummy ta haifa ne babu rai, ka duba ka ga irin magajin da na samu sak Irina, baƙi Mai kamanni kamar ni amma sun kashe mani shi Shamwilu" (ya cigaba da zubar da ƙwallah cikin ƙunci) Shamwilu ya karbi jinjirin yana kallo, yace

"abokina tabbas ba dan ina cikin bacin rai na Yasira ba da na taya ka kukan wannan rashin da kayi, amma zuciyar tawa a bushe take yanzu saboda dukan ta na gama duk raina a bace yake, Kaga yaron sak Kai wannan zaa ce Kaine ka haife sa amma banda waÉ—ancan matan, yanzu Ina ita Ummy? "

Audi yace" tana asibiti na sake ta". Shamwilu ya zaro idanu yana kallon sa, yace "da gaske ka saki Ummy ko wasa kake min? Yace "baƙin cikin kashe wannan yaron ya saka na sake ta, babu wani amfanin zamana tare da ita tun da bata so na da khairi, amma wancan tsohon mai gari yana cewa babu sakin wai har yanzu matata ce ita, shine na kyautar da ita ga Wadata"

Cikin ƙunar rai Shamwilu ya dube sa, yace "shi wadata ka bashi kyautar Ummy to ni menene amfani na, Ina abokin ka kaje ka baiwa wani banza gani meyasa ni baka bani ita ba sai wani shashasha".

Audi yayi Jim kaÉ—an kafin yace "kasan kuÉ—in da ya kashe na nema mata lfy Sam bazan iya biyan sa ba shiyasa na bar masa ita, kana da mata irin Yasira ina zata bar ka kayi wani aure yanzu, ni bama wannan ba, wai yanzu Shamwilu babu ta yanda zaa yi yaron nan ya tashi?

Cikin takaici shamwilu yace "ina ne ka taba jin an mutu an dawo, waye yake bayar da rayuwar idan ba Allah ba kuma ya karbe kayansa ko gurin boka kaje bazai tayar da wannan yaron ba" idanun Audi suka yi jawur ya karbi yaron yana ƙara kallon sa yana jin wani shauƙin son sa, da kyar aka rarrashe sa mutanen unguwar aka karbi yaron aka je aka masa wanka da sutura, kukan da yayi akan yaron bai yi akan rasa iyayen sa ba yanzu ne ya san zafin mutuwa, a wannan ranar yayi addu'a sosai ya saka iyayen sa tare da istighfari akan abinda ya aikata masu, yana tunanin ko haƙƙin su ne ya kama yaron, daren ranar ya nufi mashaya batare da ya ƙara waiwayar asibiti ba.

TWO WRITERS EMPIRE ✍️✍️

Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su É—ebe muku kewa,

FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH

ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA

Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira É—ari shidda shidda, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya.

[8/3, 9:11 PM] J💕: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt?mode=ac_t

*FARAR TASKA*

Fertymerh Zarah

12

Gwargwado Mutanen garin sai zuwa jajen rasa jinjirin suke masa sanin Audi wani gefe mutumin kirki ne, duk wani abu ya sami mutum na farinciki ko akasin sa idan har yaji lbr ya kan je wa mutum shiyasa rashin wannan jinjirin ya sami masu zuwa masa ta'aziyya sosai, bayan mutane sun lafa ya tashi daga ƙofar gida ya shiga cikin gida, kallon ko ina yayi duk a hargitse da kayan yaran dana mahaifiyar su, cikin takaici da bacin rai ya soma tattara su duka yana jefa su ta katangar wadata, duk wani tsumma nasu haka ya tattara ya fitar dasu daga gidan acewar sa tun da ya rabu da matar komai nata baya son gani kona ƴaƴan ta acikin gidan sa.

Bayan farfaɗowar Ummy babu abinda take sai kuka idan ta tuna auren ta da Audi ya ƙare, mutumin da take gani duk duniya shi kaɗai ne ɗan uwa daya rage mata, shine suturar ta kuma rufin asirin ta, ta shafa cikin ta tana kallon Saratu, tace "Dan Allah Malam wadata yaje ya bashi haƙuri Saratu ko dan yarannan ya mayar dani". Saratu ta zauna tana faɗin "Maigari da kansa yayi masa magana bai ji ba bana jin yanda yake jin haushi da takaicin mu ni da Malam wadata saboda mun taimake ki ya saurare mu. balle yanzu da yake cikin fushi ki barshi ya sauko, kiyi hakuri Ummy kowane ɗan adam da irin tasa jarabawar, Zaki cigaba da zama damu kada ki damu". Ummy ta rumtse idanunta a hankali kafin ta buɗe cikin hawaye, "ina son shi Saratu, wallahi har cikin raina ina son mijina, ban gane hakan ba sai a yanzu da bana tare dashi, duk wannan azabtar dani da yake ina da yaƙini akan zai daina shiyasa bazan gaji da yi masa uzuri ba nasan wata rana zai dawo hanya madaidaici ya sharrin giya da Shamwilu ne" Saratu ta bata rai wannan karon, tace "haba Ummy ta yaya namijin dake wulakanta ki, yake dukan ki, babu ci, babu sha, babu sutura, sannan babu magana mai daɗi, baya kaunar ki keda ƴaƴan sa har kike ikirarin kina son sa kina son zama dashi, wannan dukan da yayi maki da ace yazo da ƙarar kwana fa? da yanzu fa babu ke a duniyar amma saboda kina da sauran numfashi a gaba Allah ya ɗauke jinjirin ya barki, duk wannan bai saka ya tausaya maki ba lokacin da kike cikin neman taimako ya sake ki a bainar mutane kuma kice kina son zama dashi, me yake damun ki Ummy? Tace "wallahi Saratu ina son shi a haka, na tabbata Audi yana sona ina ganin haka a kwayar idanuwansa, da zai nutsu ya daina shan wannan giyar zan sami soyayyar sa, kin sani tun iyayen sa suna da rai itace babbar matsalar da suka so ganin sun raba shi da ita hakan bai yiwu ba har Allah ya karbi rayuwar su, kuma dukan da yazo yayi min wallahi sharrin Shamwilu ne shine ya haɗa ni dashi, Shamwilu shine na biyu a babbar matsalar dake tare da Audi dan Allah ku roƙa min shi ya mayar dani".

Tsaki Saratu tayi cikin takaici kafin ta tashi ta fice batare da tayi magana ba, tana fitowa suka haɗa ido da Malam wadata dake sauraren su, murmushi yayi yana faɗin "banda abin Saratu waye yake ƙoƙarin shiga tsakanin mata da miji, ai ko naman jikin ta yake gutsira tunda take son sa zata iya zama dashi, ki daina faɗa da fushi da Ummy ki rarrashe ta a yanzu kafin ta sami lafiya".

Shiru kawai Saratu tayi batare da tayi magana ba saboda bacin ran Ummy da take ciki, tana fitowa ta sami Feenah tare da Huzaifa wanda tun kwanciyar Ummy asibiti kusan kullum yana gurin, wata shaquwa mai tsananin gaske ta shiga tsakanin su biyu, a shekaru irin na Safeenah shekara goma sha biyu kuma tashin ƙauye ya saka Huzaifa bai furta mata kalmar so ba ko da wasa, ya boye hakan har zuwa sanda zata san menene so da kuma Auren, Ummy ma duk lokacin da ta buɗe ido ta gansu tare wani sanyi take ji a ranta ta tabbata Huzaifa zai iya riqe mata amanar Safeenah kuma ba irin riqon da Audi yayi mata ba. Daren ranar sai ga Shamwilu ya zo, ya saka sabon yadin sa sai faman murmushi yake yi, yaran suka gaida shi ya amsa da sauri fuskar sa a sake yana ƙara kallon Ummy da ta tsuke fuskar ta, ya ajiye leda gefen Saratu yana faɗin,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.