Farar Taska Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Farar Taska Part 1 Complete Hausa Novel.docx
Chapter 4 of 14
[8/2, 6:56 PM] J💕: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt?mode=ac_t
*FARAR TASKA*
Fertymerh Zarah💕
4
Shigowarsa ya saka duk suka yi shiru suka qara ƙanƙame Ummy, ya ja dogon tsaki cikin takaici yana faɗin " wai har ni zaa tare a hanya akan waɗannan mayun yaran naki ace ana so, har ana kirana da baban turawa, an mayar min da gida a garin nan gidan turawa saboda jajjayen fatar ku, na soma gajiya wallahi ta Allah zaku barmin gidana, na gayamiki ba tun yau ba ki nemi uban su ni ba yarana bane, iyayena basu taba haifar mace ba har suka bar duniya, ta ina nake da gadon haifar ƴaƴa mata, sannan kaf dangin mu bamu da masu jajjayen fata, ta ina nayi gadon haifar su, ƴaƴan da na dasa acikin ki ai sai dai su fito a irina ba irin ki ba" cikin karkarwar murya jin yana maganar zai kore su tace " kayi haƙuri maigida" ya ƙara turo baki yana hararar su kafin yace " wallahi ta Allah aka sake tare ni a hanya ana son waɗannan yaran sai nayi masu duka, sai na bata wannan fatar jikin tasu, saboda haihuwar su komai nawa yake lalacewa, saboda su na rasa iyayena duka da ban haifesu ba da yanzu ina tare dasu, da ace maza ne kika haifamin Allah kaɗai yasan inda suna na zai kai saboda tarin arziki, ga ƴaƴan Shamwilu nan kullum sai ya saka su a gaba yaje dasu gona, shiyasa duk lokacin gona yazo yake cin gajiyarta ni bani da wani magaji da zai kama min". Duk suka yi shiru ba wanda yayi magana sai ƙwallah da suke sharewa, ya nufi hanyar fita kome ya tuna ya dawo yana nuna ta da yatsa " Kin ga wannan cikin wallahi kinji na rantse ba gudu ba ja baya idan macece ki danneta kada ki taba haifarta kai ko ta fito ki mayar da ita ko kuma kije ki jefar da ita, wallahi bayan wannan matan guda uku da na haqura nake zaune dasu bazan ƙara zama da wata macen ba, idan har bakiyi yanda nace ba zaki tattara ƴaƴanki ki bar min gidana kai garinan ma zaki bari gabaki ɗaya ai saboda ni aka kawo ki kike zaune kuma zan kora ki" yana gama mgnr ya fice yana faɗa sosai, Deejah tace " Innar mu ki kaimu inda baban mu ai shi bazai riƙa dukan mu yana dukan ki ba" tayi murmushin yaqe tana goge hawayen fuskarta tace " ban taba baku labarin illar shan barasa da abinda take haifarwa ba? Duk suka jinjina kansu, tace " to wannan yana ɗaya daga cikin ilollin duk mai shan barasa shiyasa na hane ku da santa kada ta taba Baku sha'awa ko lasawa kuyi Idan kuka ga ya ajiye kwalbar domin tana saka mutum mantuwa ya manta komai da kowa nashi, kuma haramun ne shanta, shiyasa kuka ga mahaifin ku yana irin wannan halin ba yin kanshi bane duk barasar ce take saka shi haka, amma shine mahaifin ku kuma yana son ku har zuciyarsa, idan ya daina shan barasa a rayuwarsa zaku ganshi ya dawo dai dai kamar Malam wadata" Safinah tace " Innar mu meyasa bazai daina sha ba tunda haramun ne? Tace " zai daina ai ya kusa ya daina dana haifa masa yaron cikina" Meelah tace " idan kuma macece kika haifa kenan bazai daina sha ba innar mu? Tayi jim tana kallonta cikin mamaki kafin tace " zai daina ku daina wannan maganar a yanzu, kowa yaje ya cire kayan jikinsa na ajiye maku abinda zaku ci idan kun gama ku huta haka" suka fashe da kuka suna faɗin duk jikin su ciwo saboda zafin duka, haka ta riƙa rarrashinsu da basu baki har ta samu suka daina kukan. Bayan wani lokaci anyi hutu daga makaranta sai gasu sun shigo gidan a guje kowacce tana so ta fara zuwa ga Ummy, jin hayaniyarsu ta fito daga ɗakin tana faɗin " kuyi sannu kada ku zame kuji ciwo, murnar me kuke yi haka" Meelah tayi caraf tace " Anyi hutu Inna kuma kowa yaci jarabawarsa" Ummy ta nemi guri ta zauna da ƙyar tana murmushi suma suka zauna kusa da ita kowa na ƙoƙarin nuna mata sakamakon jarabawar sa, Safeenah tace " Innar mu kinga a ajin mu nice nayi ta biyu, Meelah ce tayi ta ɗaya a ajin su, Deejah ma ta biyu tayi a ajin su kowa sai faɗa yake munyi ƙoƙari, kinga harda kuɗi wani malamin mu ya bamu a makaranta" taji wani farinciki a ranta, sai murmushi take tana duba jarabawar su duk da bata gane komai, amma farincikin da take gani a tare dasu yake saka ta wani nishaɗi a zuciya, tace " Allah ya nuna min watarana kun zo min haka kuna farincikin sanar dani kun zama wasu da Al'umma zata amfana daku tayi alfahari daku" Deejah tace " Innar mu ni kinsan dame zan amfani al'umma? Ummy ta girgiza kanta tana kallon ta da murmushi, tace " ni ina so na zama Malamar makaranta na riƙa koyar da yara irin yanda Anty Nabila take koyar damu, na riƙa saka kaya irin nata masu kyau ina yin kwalliyar kamar nata ko kuma na zama lecturer a babbar makaranta, Innar mu ance sai anyi karatu mai zurfi sosai ake kai wannan matakin" Ummy tace " babu laifi a wannan Hadeeza wasu su sami ilimi a ƙarƙashin ka domin kuma a ƙarƙashin wasu kuke nema a yanzu, Allah ya cika maki wannan burin naki har ki kai ga matakin riƙe makaranta gabaki ɗaya bama Malama kaɗai ba ". Safeenah tace " Innar mu ni kuma ina so na zama ƴar Jarida, bansan dalili ba amma abin yana burgeni idan naga ƙawaye na suna bayar da labari akan ƴan jaridu" Ummy tace " baki da ra'ayi sai na wasu kenan, nikam menene acikin aikin Jarida Safeenah? Tace " shikenan tunda bakya so, zan zama ƴar kasuwa zanyi karatu akan Business, na riƙa fita ƙasashe ina kasuwanci, malamin mu ya bamu labari masu kasuwanci har jirgi suke shiga suje wata ƙasa saboda kasuwanci, Innar mu idan na sami kuɗin zan gina maki ƙaton gida ki bar wannan, kuma bazaki ƙara yiwa kowa aikatau ba" Ummy tayi murmushi idanunta cike da ƙwallah ta shafa kan Safeenah tana faɗin " Allah ya tabbatar da hakan kasuwanci ma wani abu ne mai kyau shima dogara da kaine, amma shima karatun sa ake yi ne? Safeenah ta gyaɗa kai tana faɗin " Sosai kuwa Inna" Ummy tace " Allah ya cika maku wannan burin naku, ta dubi Meelah tana faɗin, saura ke baki ce komai ba". Ta yatsina fuska kaɗan kamar bazatayi magana ba kafin tace " ni Inna ina so na kasance tare da ke har ƙarshen rayuwata, idan na girma bazan ƙara bari Baba ya dake ki ba". Hawayen da take maƙalewa suka zubo, ta saka hannu da sauri tana goge su kafin tace " Jameelah suma ƴan uwanki zasu kasance dani har mutuwa ko da kunyi aure muna tare babu abinda zai raba mu, bana so ki kasance dani kawai batare da kin taimaki al'umma daga cikin ilimin da kike nema ba" ta tunzuro baki kaɗan tace " to zan zama ƴar sanda saboda kawai idan Baba ya dake ki na kama shi" Ummy tace " Mahaifi mahaifi ne komai lalacewar sa, ki daina tunani akwai ranar da zaki iya rama min duka a gurin wanda ya haife ki, ki ɗora hannun ki akan mahaifin ki kar na qara jin wannan banzan tunanin ki ko a mafarki, yanda kuke sona kuke son ganin farincikina haka nake so ku nunawa mahaifin ku, bana gayamaku duk abinda yake yi ba laifin sa bane kuma zai zo ya daina, ku daina ƙullatarsa ko tsanarsa ko da naman jikin ku yake yanka, kuma ko da ace mugun halin sa yafi na kowa a duniyar nan shi ɗin Mahaifin ku ne bazaku iya goge shi a rayuwar ku ba". Meelah ta ɗauke kanta tana tunzuro baki, Ummy tace " ki gayamin naji dame zaki taimaki al'umma? Tace " ki zaba min kome kike so nayi". Ummy tace " ina burin naga ɗaya daga cikin ku ta zamo unguzoma a ƙauyen nan ko dan mata irin mu da suke haihuwa a gida da waɗanda ake kai asibiti babu ma'aikaciya mace sai maza ne suke karban haihuwa suke duba kowacce mace da matsalarta, tunda su sun faɗi nasu ra'ayin ke kuma kin bani zabi wannan nake so kiyi Meelah" Meelah ta jinjina kanta tace " shikenan zan yi Innar mu" tayi murmushi tana kaallon su cikin farinciki, tace " Allah yayi wa rayuwar ku albarka ya raya min ku cikin aminci ya kuma baku mazaje nagari da zasu riƙe min ku hannu bibbiyu bisa amana da ku..ma....bakinta ya ɗauki rawa saboda wani baƙinciki daya zo ya tokare zuciyarta, tasa gefen zani tana goge wasu ƙwallah, Meelah tace " ni bazan yi aure ba innar mu kidaina saka ni a irin wannan addu'a, zan zauna na kula dake" Deejah ma tace " nima bazan yi aure ba ina tare dake innar mu" Feenah ma tace " nima bana son auren, bana so a dinga dukana kamar yanda Baba yake dukan ki" bata da ƙarfin magana a wannan lokacin saboda zuciyarta ba daɗi, sai tayi shiru tana sauraren su tana kallon su cikin shauƙi irin na uwa ga ƴaƴanta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.