Complete Hausa Novels

Farar Taska Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Farar Taska Part 1 Complete Hausa Novel.docx

Chapter 3 of 14

[8/2, 6:56 PM] J💕: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt?mode=ac_t

*FARAR TASKA*

Fertymerh Zarah 💕

3

Suna gama cin abinci, Safeenah ta haɗa duka uniform ɗin su ta zauna ta wanke duk da ba wani iya wankin tayi sosai ba, Hadeeza da Meelah suka fita ɗebo ruwa, haka Ummi ta tashi jiki duk ba daɗi ta ɗauki mayafi ta fita ba dan ta san inda zata je ba sai dan nemawa yaranta abinda zasu ci da dare, bata jima da fita ba ta dawo a gajiye ta sami guri ta zauna tana kallon su inda suke zaune suna wasa, tace " lokacin islamiya yayi ku zo ku tafi bana so kuna makara ana dukan ku" duk suka tashi a tare kowa ya ɗauki abin karatun sa suka fita, ta zauna jugum da uban tagumi yaron cikin ta sai juyi yake alamar yunwa, tun karin kumallon da tayi bata ƙara saka komai acikin ba sai ruwa, bata da abinda zata ci balle ta bawa yaran da dare idan sun dawo, ta share wasu ƙwallah cikin tausayin halin da ta tsinci kanta aciki, tana ƙoƙarin fita daga gidan sai gashi yana dawowa a buge saura ƙiris ya ture ta tayi saurin kaucewa, kallonsa tayi yana tafe yana rangaji har ya shige cikin gida ta girgiza kai, kafin tayi wani laifin da zai dukanta ta sa kai ta fice da sauri, a ƙofar gida yara ne da alama su suka rako shi gida suna masa waqar da taji kamar hayaniya ake a waje, duk gidajen da take wankau haka tabi ɗaya bayan ɗaya tayi aiki su bata wani abu, da haka ta tara wajen ɗari takwas sai murna take da kuɗin ta nufo gida, ta hango su tsaye su uku a kofar gida da alama ita suke jira, tun daga nesa ta soma yi masu murmushinta mai ƙarawa fuskarta annuri, tace " meyasa kuka tsaya anan maimakon ku shiga gida ku jira ni" Deejah tace " Ai Baba ne ya hana mu zama a gida wai muje gidan uban mu shi ba uban mu bane". Taji hankalinta ya tashi ainun ta dubi Feenah da Meelah dan son tabbatar da zancen Hadeeza, suka tabbatar mata da gaskiya ta faɗa, ta shiga gidan suna biye da ita a baya yana zaune da alamar ya soma dawowa hayyacinsa sai sigari yake zuƙa kamar wani mayen zaki, tayi sallama bai amsa ba, ta kai gwiwowinta har kasa cikin tsoro ta soma gaida shi, wani kallo yayi mata na tsana yace " daga ina kike" cikin rawar murya tace " naje aikatau babu abinda zamu ci da dare" yaja dogon tsaki yana tashi daga inda yake zaune, yace " ina abinda kika samo" jiki na rawa ta kwanto daga zaninta tana nuna masa babu tsammani ya warce kuɗin yana faɗin " na samu na barasar gobe, ciko kawai zanyi, kije idan baku ci abinci ba ku mutu keda buzayen yaran naki" ƙwallah ta cika idanunta jikinta ya ɗauki karkarwa tace " Malam dan Allah kayi haƙuri ko kaɗan ne ka bamu mu sami abinda muka ci da dare" yace " kada ki harzuƙa ni yanzun nan jikin ki ya gayamiki, banda iskanci da kin raina ni har kin isa na karbi abu a hannun ki kice na maida maki, da kike zama a gidana keda shegun ƴaƴan ki na taba maki magana, ke bari kiji ma daga yau duk wata zaku riƙa biyana haya, bazan yarda na baku gurin zama a kyauta ba wallahi duk wata sai kin bani dubu biyu na haya ko kibar gidannan ke da yaran ki, mtsew aikin banza" ya sa takalminsa ya fice daga gidan, ta fashe da wani irin kuka gwani tausayi, yau duk juriya irin nata ta kasa wani irin abu take ji ya danne ƙirjin ta, yaran duk suka rungume ta suna taya ta kukan, har aka soma kiran sallar magrib suna tsugunne a guri ɗaya, idanunta sun yi jawur saboda kuka ta dube su tana faɗin kuje kuyi sallah, bara naje ko zan samo maku wani abun" Meelah tace " innar mu ina zaki je da wannan daren, ki bari kiyi sallah tukunna sai mu raka ki duk inda zaki je" bata yi musu ba haka tayi sallah tayi addu'a tana roƙon Allah, bayan sun gama suka fito a tare suna cikin tafiya suka haɗu da Malam Wadata yace " ina zaku je haka da dare Ummy" ta share hawayen fuskarta tace " bazamu jima ba zamu dawo nan ne kusa" kafin yayi magana Hadeezah tace " zamu je ta nema mana abinda zamu ci, tayi aiki ta sami kuɗi baba ya ƙwace duka kuɗin" cikin tausayi Wadata yace " ai da sai ki faɗa min Ummi, ki ɗauki ƴaƴa da ciki kina yawo dasu haka, maza maza ku juya zuwa gida yanzu zan aiko Saratu ta kawo maku abincin da zaku ci ku kwanta" suka hau yi masa godiya sosai kafin su juya, basu jima da zama ba sai ga Saratu ta shigo da sallama a bakinta, duk suka amsa Deejah ta tashi ta nufe ta tana ƙoƙarin karbar abincin hannunta, duka a jiraye suke jikinsu har rawa yake lokacin da duk suka kai hannu su huɗu a abincin, ba yaran ba kuma ba uwar mai juna biyu ba, Saratu taji wata ƙwallar tausayin su har ga Allah tana son bayin Allah nan kuma tana tausaya masu, ta ajiye ledar gero tana faɗin " innar su ga gero Malam yace a kawo maku kuna kunu dashi" cikin sauri Ummi tace " ki mana godia sosai saratu Allah ya qara maku arziki ya qara rufa maku asiri" saratu tace " Amin" kafin ta juya ta bar gidan. Daren ranar tana cikin barci taji kamar ana zungurin ta da ƙafa, ta buɗe ido tana kallon sa ta hasken wata daya hasko ɗakin, yace " buɗe min ƙafafun ki" gabanta ya faɗi ta juya kaɗan tana kallon yaranta dake gefe suna barci, acikin su yake son kwanciya da ita, ta juyo tana kallonsa tace " acikin yaran? Yace " to sai me, kada ki bata min lokaci yanzu jikinki ya gayamiki, ki buɗe min ƙafafu nace" ta tashi da ƙyar tana cije bakinta saboda bayanta dake ciwo, cikin rawar murya tace " mai gida dan Allah kayi haƙuri ko ɗakin kane sai muje amma acikin yaran nan idan wata aciki ta tashi fa? Yace " ni zan kai ki ɗakina dan kin raina min wayo, ɗakina ne zanje dake ki kwanta min ml katifa, aiko darajar ƙasan ɗakina baki cancanci kwanciya ba balle ki hau makwancina, maza buɗe min qafa idan bazaki iya ba na buɗe ta ƙarfi da kaina" idanunta suka cika da ƙwallah ta tashi da ƙyar tana ƙoƙarin fita, yace " gidan uban wa zaki je ki barni anan? cikin rawar murya saboda kuka tace " zan kwanta ƙasa a waje ne, zai fimin akan gaban ƴaƴana" yayi ƙwafa yabi bayanta, da ƙyar ta kwanta a ƙasa yasa ƙafa ya hangame ƙafarta a fusacce yana cire wandon jikinsa, ban da hawaye masu ƙunar zuciya babu abinda take, yayi iya yinsa ya tashi ya fice yana babbatu tare da tsine mata albarka ita da yaranta mata, ta kasa ko wani ƙwaƙwaron motsi daga inda take kwance a ƙasa, barcin ma ya ƙauracewa idanuwanta, kasancewar sa uban ƴaƴanta ya saka duk wata muguwar addu'a take kasa yi masa, tana ji an soma kiraye kirayen sallah ta tashi da ƙyar ta lallaba ta shiga bayi tayi wanka, washe gari bayan fitar su makaranta ta nufi inda Saratu ta jima zaune a gidan suna hira ba dan komai ba sai dan ta kaucewa ganin ta dashi, babu abinda ta tsana a duniya irin ta buɗe ido ta ganshi a gabanta, yanda take jin tsana da tsoronsa a zuciya har tana hasashen shine ajalinta wata rana, muryarsa kaɗai idan taji ji take kamar ana fisgar numfashinta, sai da lokacin dawowar su makaranta yayi kana ta nufi gida, bata jima ba sai gasu sun shigo duka suna kuka a tare su uku, hankalinta yayi matuƙatar tashi har ta manta cikin jikinta saboda tsananin ruɗewa ta nufe su tanaa tambayar su meya faru, " baba ne ya tare mu a hanya yayi mana dukan tsiya" suka cire kayan jikinsu suna nuna mata bayan su, abinka da farar fata duk shatin bulala ruɗuɗu a bayansu, dukan da aka masu irin na mugunta kamar ana bugun babban mutum, jikinta ya ɗauki rawa iya ruɗewa ta ruɗe ga hawaye dake ta ambaliya a fuskarta, ta taba jikin wannan ta taba jikin wannan tace " me kuka masa yayi maku wannan duka haka" Safeenah tace " wai mu ba ƴaƴan sa bane mu shegu ne baya son mu, innar'mu ki kaimu inda mahaifin mu ai shi bazai dake mu haka ba" duka su ukun ta haɗa a jikinta ta rungume, wannan karon sautin kukan ta ya kasa boyuwa saboda zafin dukan da ta gani a jikinsu, kuka take ba kakkautawa wanda ya saka su shiru da nasu kukan suna saurarenta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.