Farar Taska Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Farar Taska Part 1 Complete Hausa Novel.docx
Chapter 8 of 14
TWO WRITERS EMPIRE âœï¸âœï¸
Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su É—ebe muku kewa,
FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH
ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA
Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira É—ari shidda shidda, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya.
[8/2, 9:34 PM] J💕: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt?mode=ac_t
*FARAR TASKA*
Fertymerh Zarah 💕
8
Daren ranar sun gama cin abinci kenan Audi ya shigo da hanzari sa har tuntube yake kamar zai kife a ƙasa saboda tsabar sauri, "ke ɗiyar farar taska, Ina Ummy ne nake ta faman kira kika min banza" da ƙyar ta fito daga banɗaki saboda nauyin cikin ya soma damun ta, muryarsa kaɗai ta tabbatar da ba lafiya ba, yace "Ina yaran naki suka shiga" tace "suna ɗaki lafiya maigida? Yace" fito min dasu duka kafin na saka ƙafa na take cikin nan naki, daga yau ba zasu ƙara zuwa wani boko ba tunda soyayya take kai su ba karatu ba" taji hankalinta ya tashi, soyayya kuma yaushe yaran suka san wani abu soyayya? Yaran da basu da ƙawaye mata balle samari, yaran da bata bari suna zuwa ko ina daga makaranta sai idan aiken su tayi.....tayi firgigit saboda tsawar da ya daka mata, "Ina magana kin min shiru saboda kin raina ni ko" ta ɗaga murya kaɗan hankalinta a tashe tana kiran sunan yaran, ba bata lokaci duk suka fito a gaban sa suka tsaya cirko cirko, ya tofar da yawu gefe yana kallon su cikin bacin rai, "wace shegiyar ce acikin ku take bibiyar maza? Duk suka zaro ido suna kallon sa cikin rashin fahimtar maganar sa, da ƙyar Ummy tace" Mai gida me yayi zafi haka zaka shegantar da ƴaƴan cikin ka, kuma ma ta yaya waɗannan ƙananun yaran suka san s..... bata ƙarasa ba ya ɗauke ta da mari cikin bacin rai yace " ke har kin isa ina magana kina ƙaryatani? ƙarya nayi ba shegu bane ko ƙarya nake basa bibiyar maza, Meyasa ake yawan tare ni akan yarannan ko su kaɗai ne mata kaf a ƙauyen nan, wallahi ina magana kika sake sakamin baki sai na fasa shi, shegiya mayya, da maza ne kika haifamin da yanzu hankali na a kwance bani da wata damuwa" ya dubi yaran "mu je ya nuna min wacce yake magana acikin ku domin wannan karon bazan bar ku ba sai na maku mugun duka da ko sunan namiji aka ambata a gaban ku sai hankalin ku ya tashi" ba musu suka nufi hanyar waje a tsorace, yana biye dasu, ganin haka ya saka Ummy ta bi bayan su a sanyaye kada ya illa ta mata yara, cikin bacin rai ya dubi Huzaifa dake tsaye a gefe yace "nuna min wacce kake magana aciki". Shiru Huzaifa yayi yana kallon matan guda uku masu matuƙar kyau da kama da junan su, biyu ne tsawon su yazo ɗaya kuma suke matuƙar kama da juna kamar twins, Meelah da Deejah, ya dubi mahaifiyar su babu shakka a gurin ta suka sami wannan kyawun duk da jikin ta ya nuna tana cikin mawuyacin hali, Safeenah ta fashe da kuka tana faɗin "wallahi Baba Sai da na gaya mashi kada yace yana sona dukan mu zaka yi, kuma kayansa ma naki na karɓa...... Yace" au kece Kenan? Kai samari itace wannan? Yayi tambayar yana kallon Huzaifa, ganin tsoro sosai a idanun feenah da ƴan'uwanta ya saka shi nemo nutsuwar sa, yace "Baba babu wacce nake so acikin su, wannan ma sau ɗaya na taba ganin ta.... Ya katse sa cikin bacin rai " to me kake nema a guri na idan babu wacce kake so acikin su? Huzaifa yace "ni malamin makaranta ne kamar yanda na gayama sanda na zo, ɗaya daga cikin su ce naga bata da takalmi a ƙafa, a matsayina na malamin su na siya na bata taƙi ƙarba tace iyayen ta sun hana ta karɓan komai a gurin namiji, naji ta burgeni kuma hakan ya nuna ta fito gidan tarbiya da mutunci naji ina so nazo na haɗu da iyayen da suka tsaya akan tarbiyarta na kuma basu takalmin da kaina sai su ba ta " Audi ya washe baki jin ɗan boko mai gayu sai yabon su ya ke, ganin haka ya saka hankalin Huzaifa ya kwanta ganin dabara sa tayi aiki akan sa, yace" yauwa yaro an gode, bani takalmin ya faɗa yana fisgo ledar hannun Huzaifa, ya fito da takalmin yana juyawa kafin ya bashi yana faɗin "baza mu karbi wannan takalmin ba". Cikin mamaki Huzaifa yace "Meyasa Baba? Yace" saboda ƙa'ida ne duk wanda zai siyawa yarana ko menene nima sai anyi min tawa Leda, shine ribar haihuwar ai, dan haka kaje da takalmin duk sanda ka siyamin nawa sai ka kawo mana tare" Huzaifa yace "in dan wannan ne babu matsala nayi maka alƙawarin siya maka takalmi gobe zan kawo maka amma kayi haƙuri ta ƙarbi wannan saboda kada ta sake fita babu takalmi a ƙafarta, ga wannan canjin ka riƙe kafin gobe" ya faɗa yana ƙoƙarin ciro kuɗin aljihunsa, dubu uku ne ya bashi, Audi ya karɓa yana washe baki sai godiya yake sosai wannan ne karo na farko da aka taba bashi kuɗi akan yaran, duk masu cewa suna son su ko kwandala basu taba bashi ba, Huzaifa ya juya ga Ummy itama ya bata dubu biyu yana faɗin "gashi ayi haƙuri da wannan". ta girgiza kai alamar bazata karɓa ba, ran Audi ya baci suna haɗa ido ya jefe ta da wata harara wanda ba shiri ta miƙa hannu ta ƙarbi kuɗin, ta tattara yaran suka juya suka bar gurin, Huzaifa yayi masa sallama har zai bar gurin ya tsaida shi, yace "yaro ya ya sunan ka kuma waye uban ka a garin nan? A wannan lokacin Huzaifa bai shirya sanar dashi ko waye mahaifin sa ba, saboda sananne ne a Maiduguri ɗan kasuwa ne, bautar ƙasa ta zo dashi garin, yace da Audi "mahaifina ba wani sananne bane ko na faɗa ba lallai bane ka san shi, ni sunana Huzaifa Kuma ni talaka ne, nazo yin bautar ƙasa a wannan garin" yace "shi mahaifin naka aikin me yake? Huzaifa yace" baya aikin komai a yanzu ni nake taimako sa da albashina " Audi ya jinjina kansa, yace" Naji a jikina Kai yaron kirki ne, idan hankali na ya gama kwanciya da nutsuwar ka zan baka auren Safeenah bada jimawa ba" murmushi Huzaifa yayi "Kamar yace shi bai shirya aure a yanzu ba domin akwai abinda yake jira ya kammala ya bar ƙasar gabaki ɗaya yaje yayi masters ɗinsa, Kuma ya tabbata mahaifin sa ma ba zai masa aure a yanzu ba amma yana tsoron hali irin na Audi, yana tsoron ya hana masa taimakon yarinyar, yace " nagode sosai da wannan karamci Baba" Audi ya nufi gida da sauri batare da ya qara magana ba, kai tsaye ɗakin su ya nufa, "ke bani kuɗin nan har kin manta ina da sauran canji a hannun ki da baki cika min kuɗin gida ba, naga har baƙin ciki kika so ki mana ki ƙi karɓan kuɗin wlhy da yau jikin ki ya gaya miki". Babu musu ta miƙa masa kuɗin ya karɓa zai fice, Meelah tace " Baba to me kake so mu ci da safe idan ka karbe duka kuɗin, ai ya raba ya baka naka itama ya bata nata" ya juyo Yana nuna ta da ɗan yatsa, "ke kin gan ki wlhy ki kiyaye ni, ina ɗaga maki ƙafa ne saboda ina jin ki a raina duk acikin su da tuni na daɗe da zubar da haƙoran bakin ki duka" Meelah tace "to ka bamu kuɗin mu mana idan dukan mu zaka yi ka dake mu amma kada ka hana mana kuɗin mu zauna da yunwa, idan ba haka ba gobe idan ya dawo kawo maka takalmin zan gaya masa ka karbe kuɗin innar'mu.... bata ƙarasa ba ya saka hannu ya bige bakin nan take ya fashe da jini, "shegiya farar mayya dama kece yace yana so a goben zan aura masa ke ya tafi dake na huta" ya jefa masu dubu ɗaya ya fice yana balbalin faɗa, kicibis suka ci karo da Shamwilu a ƙofar gida, yace "Audi Kai da waye kake faɗa a wannan daren, ko farar taskar kace? Tsaki Audi yayi kafin yace" baƙar taskar dai ai idan ka ganni cikin bacin rai ka sani babu mai ƙuntata min kamar Ummy da yaranta, gabaki ɗaya sun gama raina ni kuma duka babu irin wanda bana yi masu". Shamwilu ya ja hannun sa suka zauna nan dakkali yace "Wai har sai yaushe Ummy zata daina saka ka a ƙunci ne? haka zaka ƙare rayuwar kullum da bacin rai abokina, gashi shekarun ka kaɗan amma fitinar matar nan da yaranta sai tsofar da kai suke, wai baza ka ɗauki mataki bane? Yace" wallahi Shamwilu babu wani mataki da ya rage wanda ban yi ba nayi dukan nayi dukan har na gaji amma duk a banza daga ita har yaran". Shamwilu yace "Ai yanzu mafita ɗaya ce kawai ka yarda ka sake aure, ka auro mafaɗaciya Kuma hatsabibiya ka haɗa su zama a gida wlhy zata gyara maka Ummy, idan zama ya gagare ta zata tattara ita da yaran su bar maka gidan ka" Audi yayi shiru cikin tunani kafin ya girgiza kansa, Shamwilu ya buga kirjinsa kaɗan yace ka sami lokaci kayi tunani Audi ni mai son ka ne shiyasa duk abinda zai saka ka farin ciki nake kokarin nemo maka shi, yanzu sanar dani me Ummy tayi maka a wannan daren ya fusata ka haka? Audi yace "yaron kirki ne yazo yana son Safeenah ya bamu kuɗi taqi ƙarba Sai da na zare mata ido, bayan ya tafi naje na same ta na kwace kuɗin shine Jameelah ke gayamin magana....Shamwilu ya buga wani uban ashar, yace "amma duk duniyar nan babu munafuka irin Ummy a gaban ka zata nuna bata karɓan kuɗi a hannun maza, bayan a idon ka zuwa take tana roƙona kuɗi? Audi ya zare idanu yana kallon sa cikin mamaki, yace "me kake son cewa shamwilu, wai kana nufin ita ummy tawa dai take zuwa roƙar ka kuɗi? Shamwilu yaja ƙaramin tsaki yana gyara zaman sa, yace "ko jiya ta tare ni a hanya na bata dubu biyu, ta zage ka sosai akan rashin ciyar dasu da baka yi kake barin su da yunwa, ta tsinewa giyar da kake sha, ta kira ka mashayin banza, Ummy da bakin ta take sanar dani ta jima tana sona saboda yanda nake kula da iyalina nake ciyar dasu da basu farinciki, kuma kudin da na bata ne kazo kake nuna min kyale ka kawai nayi a jiya, nan da bakin ka kake cewa ka yarda da ummy bata neman maza amma a jiyan tace idan zan jure bata kuɗin da zata ciyar da yaranta babu abinda zan nema a jikinta ta hanani k.....bai ƙarasa jin zancen shamwilu ba ya tashi a fusacce ya shiga gidan, kansa har wani sarawa yake ga duhu dake mamaye idanun sa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.