Complete Hausa Novels

Farar Taska Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Farar Taska Part 1 Complete Hausa Novel.docx

Chapter 13 of 14

"ga wannan a rabawa yara, sauran na mai jinya ne" ya dubi Ummy,

"Ummina ya jikin? tayi kasafe tana kallon sa jin sunan daya kira ta dashi bama ita ba har saratu mamaki take, yace

"dan Allah kice su bamu wuri ina son magana dake ta sirri Ummina". Saratu ta tashi tana faɗin "ai dole zan tashi na fita Shamwilu amma kafin nan idan zaka fito ka ɗauki kayan ka bama buƙata" kafin yayi magana ta tattara yaran suka fito, yace

"kamar wacce take baƙin ciki da zuwa na gurin ki Ummy, da alama zamu fuskanci maƙiya a auren da zamu yi, nikam da so samu ne ki tattara saratun nan kiyi watsi da ita domin bazata barmu zaman lfy ba" tace

"ina ji sai da kasha giyar kafin kazo nan ko, to bara kaji wallahi ko maza suka ƙare a jere bazan taba auren ka ba Shamwilu, ko kana tunanin bansan munafurcin da kaje ka ƙullamin a gurin Audi ba, saboda kai nake kwance a wannan asibitin a yanzu kuma saboda kai Audi ya rasa jinjirin sa, saboda kai na rasa Aure na, da baka je ka gayamasa qarya akai na ba da bai zo ya dake ni ba wallahi tsakani na da kai Allah ya isa Shamwilu" ya sassauta muryarsa cikin sanyin hali, yace

"naji duka laifina ne amma kiyi haquri saboda ina matuƙar son ki ne Ummy, wallahi ni kaɗai zaki aura a duk faɗin jeren nan ki kasance acikin farinciki, ina son ki da gaske Ummy" tace

"Wallahi bana son ka, duk duniya babu wanda na tsana kamar kai" ta tashi da sauri ledar da ya ajiye ta dauka ta jefa masa a jiki tare da nuna sa da yatsan ta, tace

"Maza ka ɗauki tsiyar ka tun kafin raina ya baci ka fice min da gani, bazan karba ba ballantana kaje ka gayamasa duniyar dake cikin jere ka kawo min na karɓa, kuma ka sani sai na gayawa Audi abinda kazo kayi a yau, sai na gayamasa cin amanar sa kake wallahi". Yace

"Shikenan naji zan fita, kin ga wannan abin da kika min wallahi sai na rama.....ya juya cike da bacin rai ya fice, fitarsa ke da wuya Saratu ta shigo da sauri saboda tana labe tana jin komai, tace

"kin kyauta, dama ko Audi haka kike rufe fuska ki ci masa mutunci da tuni kin daÉ—e da kwatarwa kanki Æ´anci". Ummy tace

"Raina baci yake idan na ganshi Saratu duk wani farin cikina shine yake gusar dashi, shine yake da kaso tamanin na ƙiyayyar da Audi yake min da yarana, ina addua watarana Audi ya gane hakan ya gane Shamwilu ba mai ƙaunar sa bane" Saratu ta zauna tana faɗin "akwai lokaci yana zuwa.

Bayan kwana huɗu aka sallami Ummy jikinta yayi ƙwari sosai, Audi na ƙofar gida suka dawo daga asibiti da yaran, kallon ta yayi acikin kwana huɗu kacal duk ta canza kamar ba wacce take cikin jinya ba, haka yake ji a ransa kamar ya shekara bai saka ta a ido ba, idanun daya kafe ta dasu ya saka shamwilu kallon inda yake kallo, Ummy ta karaya daga kallon da Audi yake mata, ji take kamar taje ta rarrashe sa ta bashi haƙuri ya maida ta a gidan sa, ta tuna labarin da saratu ta bata na cewa ko da suka zo ya jefo duka kayan su daga gidan sa, ta ɗauke kanta da sauri daga fuskarsa ita da yaran suka shige gidan Wadata.

Shamwilu yace "Amma yarinyar nan ta gama raina ka abokina, har ta iya shigewa wani gida batare da ta gaida ka ba kamar fa bata ganka ba". Audi yayi Jim kafin ya sauke numfashi kaÉ—an yace

"Ni fa zan dawo da Ummy" "Meyasa? Shamwilu ya tambaya a razane yana kallon sa cike da fargaba, Audi yace" saboda mata ta ce, bangane tana da muhimmanci a rayuwa ta ba sai da bata gidan nan na kwana huÉ—u rak, kasan Allah idan tayi wata bata gidan nan zan haukace saboda ina son ta sai ynzu na gane hakan" Shamwilu ya bata ransa,

"kai haba kada ka bayar da maza, duk yaushe aka yi sakin, kwana huÉ—u Kacal me ka iya ganewa acikin sa yaushe ma ka gama hukunta ta har ta gane girman laifin da ta aikata maka, wallahi karya kake ba son ta kake ba kuma baza ka mayar da ita ba, saboda wane dalili ka saki mata shekaranjiya kace har kayi dana sanin da zaka mayar da ita". Audi ya dube sa da mamaki yace

"mata ta ce ba matar ka ba, menene damuwar ka? Yace" babu, amma ina so ka sani gona ta da take hannun ka zan karɓa na siyar zan bawa ƴaƴa na jari zasu je can kudu kasuwanci" Audi yace

"Shamwilu menene haɗin mgnr Ummy da gona, Naga kamar ka ɗauki zafi dan kawai zan mayar da ita, na ɗauka kai abokina ne da zaka ƙarfafa min gwiwa akan na mayar ita saboda ta cancanci haka, kai ne fa ka saka na sake ta". Da jin haka sai Shamwilu ya hau bakin sa, ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba sai fada yake yana zage zage wanda ya saka audi saukowa yana bashi hakuri, Shamwilu ya tashi ya fice cikin bacin rai, Audi ya shiga gidan sa zuciyar sa a dagule, yana jiyo dariyar yaran a gidan wadata suna wasa wanda basa samun damar yi a gidan sa tun suna yara ya hana su wasa da sake wa a gidansa, kullum idan ba suna taya maman su aiki ba to suna zaune suna hira sama sama, duk sai yaji babu daɗi, ya ɗauki turmi ya kai gun katanga da yake ba mai tsayi bace irin na ƙauye ya hau ya taka yana kallon yaran, sai ga Ummy ta fito daga wanka tun da ya ɗora idanunsa akan mazaunan ta yaji yana neman nutsuwar sa, jikin sa ya ɗauki karkarwa gab da zata shiga ɗakin Saratu ya ɗaga murya sosai yace

"Wallahi na mayar da aure na, dama can sakin ba har zuciya nayi shi ba..... Jin muryarsa ya saka ta juyowa tana kallon inda yake leqen su, yaran ma kowane ya tsaya yana kallon sa cirko cirko, ya cigaba da faÉ—in

" eh na mayar da aure na, maza maza ki tattaro yaran nan ki dawo dasu É—akin ki, (ya dube su) kai maza ku shiga ku É—auko duka kayan ku, ku dawo gidan uban ku ai nine uban naku saboda me zaku je ku zauna a wani gida.

Meelah tayi caraf tace" Malam Wadata ne baban mu kai kuma ba baban mu bane dan haka bama son gidan ka mun fi son wannan gidan "

Cikin bacin rai ya ciro takalmin ƙafansa ya jefe ta dashi da sauri ta kwace, yace" ungo nan, shegiya mai shegen iya yi, to ko zaki mutu nine uban ki nina haife ki baki isa ki canza ni ba, zaki dawo ki same ni gidan nan sai na yanke wannan bakin naki da kike turomin, ke Hadiza maza ɗauko min takalmin nan ki kawo min yanzu" da sauri Deejah taje ta ɗauki takalmin zata kai masa Meelah ta riqe ta "idan kika je zai riqe ki ya hana maki dawowa, bani nan", ta karɓa tare da jefa masa tsakiyar gidan sa, wani haushi da takaici ya taso masa a zuciya kafin yayi magana Ummy ta saka yaran duka ɗaki suka barshi nan tsaye yana leqen su, a zuciye ya sauko ya saka takalmin ya fita daga gidan kai tsaye fadar mai gari ya nufa, ya zauna yana faɗin "Ranka shi daɗe na kawo ƙarar Malam Wadata ne saboda ya ɗauke min mata ya boye a gidan sa bansan me yake nufi ba" Mai gari ya dube sa da mamaki yace "ba dai Ummy kake magana ba ko? Yace" Ita mana duk duniya bani da wata mata bayan ita kai ma shaida ne" mai gari yace "eh tabbas ni shaida ne akan ka saki Ummy, kuma da bakin ka kace ka barwa Wadata" ya sassauta murya yace "Ranka shi daɗe duk acikin bacin rai ne nayi hakan, Ina neman afuwa tun da na mayar da mata ta ya bani abata, ayi mashi magana ya bani mata ta ranka shi daɗe kum..... Yayi shiru sakamakon ganin Wadata yazo a fusacce, bayan ya gaisa da Mai gari yace" Ranka shi daɗe Ina ƙarar Audi Akan leƙen gidana alhali bana gida, kuma ko da ina nan bai kamata ya leƙamin mata ba" a firgice Audi ya dube sa yana faɗin "Matata na leqa ni ko matar ka idanuwana basu nuna min ba kuma banji ƙamshin ta ba" mai gari yace "laifine babba kaje ka leqa gidan wani...... ya katse sa da hanzari" ranka shi daɗe na karbi laifina abawa Malam Wadata haƙuri Akan kuskuren da nayi amma ya maida min mata, ya gayamin duka nawa ne kuɗin sa da ya kashe a asibiti zan biya sa yanzu" Wadata ya dube sa yana faɗin "Ummy bata son zama da kai a yanzu, kuma da zarar ta gama Idda ni ne wanda zai aure ta".

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.