Complete Hausa Novels

Farar Taska Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Farar Taska Part 1 Complete Hausa Novel.docx

Chapter 6 of 14

TWO WRITERS EMPIRE ✍️✍️

Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su É—ebe muku kewa,

FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH

ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA

Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira É—ari shidda shidda, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya.

[8/2, 9:00 PM] J💕: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt?mode=ac_t

*FARAR TASKA*

Fertymerh Zarah

6

Audi bai motsa daga wurin da yake zaune ba har sai da ganin Shamwilu ya bacewa idanun sa, ya sauke numfashi kaɗan kafin ya tashi, ya ɗauki kayan nomansa jiki ba ƙwari saboda yunwa ya shiga cikin gida, zaune suke tsakar gida kowacce tana tsefe gashin kanta, Deejah ce kawai mamanta take mata, yaji wani yarrr gashin jikinsa ya tashi ganin irin yalwar gashin dake tattare da kowaccen su, da sauri ya ɗauke kansa daga kallon su har wani tsoron yake ji, yaji Muryar Ummy tana faɗin " Barka da dawowa mai gida" bai amsa ba yayi shigewar sa ɗaki, kayan sa ya ajiye ya dawo da sauri yana faɗin " kowaccen ku ta rufe min kanta kafin naci kutumar uban ku yanzu" da sauri Ummy ta soma basu kallabin su jikinta na rawa tace " ku yi sauri ku ɗaura a kai kun ji" suka karba suna tunzure baki ƙasa ƙasa, ta ɗaure na Deejah ta riƙa hannunta suna ƙoƙarin barin gurin yace " dawo nan ina magana zaki tashi ki tafi saboda kin raina ni, sai na fasa maki baki yanzu kinsan halina" ta sunkuyar da kanta ƙasa batare da tayi magana ba, ya dubi yaran tare da nuna su da ɗan yatsansa yace " wallahi summa tallahi kun ji na rantse ko, duk ranar da ku ka sa ke na ƙara shigowa gidan nan baku gaidani kamar mahaifiyar ku ba sai fatar jikin ku ta gayamaku, na fita neman abinci na dawo a gajiye sai ku zuba min shegun idanun ku kuna kallona" Ummy tace " Ayi masu afuwa mai gida, zasu gyara" ya ja ƙaramin tsaki yana faɗin " ina abinci na" ta ɗago daga sunkuyen da take wannan karon tana kallon sa, kallo ne mai cike da ban mamaki, to ko dai baya hayyacinsa yaje yaa sha ya bugu ne idan ba haka ba ta yaya zai tambaye ta abincin sa bayan ba shi yake ciyar dasu ba ita take ciyar da kanta da yaranta, duk aikin noman nan da yake zuwa har ya gama ya cire yaje ya siyar bai taba bata ko gwangwani na gero ba, rabon da ya ciyar da ita tun bata haifi Deejah ba tun iyayen sa suna da rai....kin min shiru ina magana saboda kin raina ni sai kallona kike, mayya namana bazai ciyu a gurin ki keda ƴaƴan ki ba" ta lumshe manyan idanuwanta a hankali kafin ta sunkuyar da kanta tare da faɗin " babu abinci su kansu yaran maƙota suka je suka ciyo" yayi jim cikin takaici kafin yace " kowacce mace tana nemawa mijinta abinda zai ci har da nama amma banda ke, babu ta inda kike kyautatawa mijin ki, wani lokacin sai na zauna nayi tunanin menene amfanin ki a gurina babu banda ki haifa ƴaƴa mata, to wlhy nagaji idan har bazaki ciyar dani ba to dole zaki bar gidannan ke da yaran ki naje na nemo wata na aura" ƙwallah ta cika idanunta, cikin rawar jiki tace " idan na bar gidan ni da su a ina kake so mu je mu zauna, waye zai bani gurin zama da yara uku haka, bani da wani sauran gata a duniyar nan banda kai, kai kaɗai nake dashi sai waɗannan yaran, kuma Allah ne gatan mu kaine gatan mu, bani da iyaye bansan ƴan uwana ba ina kake so naje, kayi haƙuri duk abinda naje na samu zan riƙa ajiye maka dan Allah" yayi ƙwafa batare da yayi magana ba ya nufi ɗakinsa, cikin sa sai ƙugi yake alamar yunwa, har ya kwanta ya sake dawowa har lokacin tana zaune dirshan a ƙasa cike da damuwa, yace " ƙuɗin gida da nace ku riƙa biya duk wata ki bani yanzu" tace " babu kuɗin Mai gida wallahi bani da ko sisi a hannuna, abincin da zamu ci da dare shi nake tunanin ta inda zan samu yanz.....tayi shiru sakamakon ɗauke ta da mari da yayi, duka yaran sai da suka razana, yace " wallahi sai kin bani kuɗina yau ko ki bar gidan, ni zaki raina wayau ki maidani mahaukaci, ina yi magana kimin ƙorafi, ko dan saboda ina ɗaga maki ƙafa ne, baki da lbrn Yasira matar Shamwilu har kuɗin ta take sakawa ta siye nama ta saka a girki saboda ta faranta ran mijin ta amma ke dussa wannan ta dabbobi kin kasa bani sai ƙorafi da bani haquri, haquri zan ci...... ta lumshe idanuwanta cikin ƙunar zucci, hawaye suka zubo, Meelah ta nufe ta da sauri tana faɗin "innar mu kiyi hak'uri wata rana idan ya dake ki da kaina zan rama maki kinji" a kufule yace " wallahi daga ranar da kika ɗaga hannu da sunan zaki dake ni daga ranar zan tsinke duka hannayen ki guda biyu, mtsew banzaye ƴaƴan Farar Taska kawai", sake juyowa yayi da sauri yana faɗin zaku zo ku fice min daga gidana ko zaku biya ni ne, cikin rawar jiki Ummy ta tashi tana gyara zanin jikin ta dake son faɗuwa tace " maigida Dan Allah ka bar su bari naje na nema yanzu amma kada ka dake su ko fito dasu daga gidan dan Allah" ya ja guntun tsaki yana kallon ta da yaran a wulakance kafin yace " Ina jira kada ki bata min lokaci" ya nufi ɗakin sa, ta juya tana kallon su da murmushi a fuskar ta dake jiƙe sharkaf da hawaye tace " Feenah ki ja hannun ƙannen ki ku shiga ɗaki ku jira ni kada ku kuskura ku fito har sai na dawo baya son ganin ku kun sani" Meelah tace "Innar'mu ni zan biyo ki muje kin ji" tace "aa Meelah ku zauna bazan jima ba zan dawo nima" ta juya da sauri ta bar gidan, sai tafiya take batare da tasan inda zata je neman kuɗin da zata bashi ba, wani tunani yazo mata kai tsaye gidan da take aikatau ta nufa, cikin rashin sa'a basa nan, duk inda take saka rai zata sami aikin da zata yi a bata wani abu duk taje basa bukatar aiki a ranar, ga yaron cikin ta sai juyi yake alamar yunwa, ga hankalinta yana gida gurin yaran, haka ta nufo gida jiki a sanyaye cike da fargaban yanda zasu yi dashi, tana tafe tana sharar ƙwallah, kicibis suka yi da shamwilu, yace "Ummy Ina kika fito acikin wannan ranar, ga ciki, kukan me kike haka? tayi ƙoƙarin haɗiye kukan dake son taso mata tace" An yini lfy? Yace " lfy lau, Ina shi Audi ya shiga da zai bar ki, ki fito haka? tayi murmushin yaƙe kafin tace" Yana gida tare da yara suna kula dashi baya jin daɗi" Shamwilu ya bata fuska kaɗan yace "Kai Anya kuwa, yanzun nan fa muka rabu dashi mun dawo daga gona, ko kansa baya ciwo kawai dai yana so ɗaga maki hankali ya wahalar dake, anya kinci abinci kuwa, yanayin ki ya nuna akwai yunwa a tare dake" ta girgiza kanta batare da tayi magana ba, yace "gsky Audi bashi da mutunci ka bar santaleliyar mace haka a wahala, ga juna biyu babu abinci, kinsan ko yau ya sami kuɗi sosai wani da yake biya bashi ina tsaye yazo ya kawo masa kuɗin amma kuma ya kasa siya maku ɗan abinda zaku ci keda yara, ni a gidana komai faɗa na bana hana iyalina abinci ina basu har nama su ci su ƙoshi shiyasa za ki ga yasir hankalin ta a kwance bata da wata damuwa, taci ta qoshi tayi barci ni na fita neman kuɗi, sai qiba kawai take ai" batare da tayi magana ba ta saka gefen mayafin ta tana share wasu ƙwallah, shamwilu ya rage murya kaɗan yana kallon ta, "wallahi Ummy Aisha Audi baya son ki ya sha faɗa keda yaran ki, har zargin ki yake da yaran a wani guri kika yi shegen su, wani lokacin ji yake kamar ya saka maku shinkafar bera ya kashe ku yake ji, Kinga wannan cikin idan kika haife sa lafiya kada ki kuskura ki ƙara bari kiyi wani cikin duk yanda zaki kashe auren ki kashe ki zo ni zan aure ki kuma na kula maki da yaran, saboda tausayin ki ya dasa min ƙaunar ki a zuciya ta, xan kula maki da yaran na ciyar dasu batare da kin fita nema ba, ki yarda dani" har lokacin batayi magana ba saboda tsanani mamaki zancen sa na cewa Audi zai iya kashe su ita da yaranta, shamwilu yace "wannan fararen yaran naki su suke ƙona ransa har yake kiran ki da farar Taska, saboda mahaifar taki bata iya ajiye komai ba sai haifo masa fararen ya'ya mata, ni ko goma zaki haifamin bani da matsala ina son su kuma da zuciya ɗaya zan riƙe ki da ƴaƴan ki". A sanyaye tace "Nagode" kafin ta soma tafiya jiki a sanyaye yabi bayan ta da sauri ya ciro dubu guda biyu ya bata yace " ga wannan kije keda yara kuci abinci nasan Kuna buƙata" kallon kuɗin tayi ta haɗiye wasu yawu da kyar kafin ta dube shi tana girgiza kanta, "nagode akwai abinci a gida da zamu ci" yace "aa wlhy Sai kin karɓa, ko da ace bana son ki ina so ki tuna ni fa abokin mijin kine tun ƙurciya da muka taso tare, ta yaya zan baki kyauta kiƙi karɓa Ummy Aisha? Ai shaiɗan kaɗai yake mayar da alheri shi kansa Audi idan yaji ba zai ji dadi ba" batare da tunanin komai ba ta saka hannu ta karɓa tare da sunkuyawa kaɗan tana masa godiya, da sauri ta fice har tana jin wani kuzari a ranta, yana tsaye yana kallon ta cikin murmushi har ga Allah yana kwaɗaituwa da Ummy Aisha shi yasa yake da burin auren ta ko da hakan zai sa ya rabu da yasira, har yanzu Audi ya kasa gane cewa duk faɗin garin jere babu mace kamar irin Ummy Aisha, da ba zai taba wulaƙantar da ita ba, ji yanda take haihuwar kyawawan ƴaƴa, ya girgiza kansa cikin murmushi ya fice yana addu'a a ransa ranar da zai ji auren su ya mutu da Audi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.