Farar Taska Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Farar Taska Part 1 Complete Hausa Novel.docx
Chapter 11 of 14
TWO WRITERS EMPIRE âœï¸âœï¸
Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su É—ebe muku kewa,
FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH
ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA
Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira É—ari shidda shidda, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya.
[8/3, 8:45 PM] J💕: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt?mode=ac_t
*FARAR TASKA*
Fertymerh Zarah
11
Duk suka zubawa Malam Audi idanu kafin su dubi mai gari cikin mamaki, ɗaya daga cikin ma'aikaciyar asibiti ta muskuta tayi wa mai gari bayanin komai tun daga farko zuwan su har kawo yanzu, kana ta ƙara da cewa saboda yaron bai isa haihuwa ba da kuma an bar ta gida har kwana biyu tana naƙuda ya saka Allah bai yi mai numfashi bane" Mai gari yace "ina ita mai haihuwa? Saratu tace" tana can kwance bata san inda kanta yake ba saboda babu jini a tare da ita, an gayawa mijin ta yaƙi ya bayar da komai sai mijina ne yaje ya siye jini aka saka mata" mai gari ya dubi Audi dake ta rarraba idanu yace "ko da ka sake ta alhakin ciyar da ita da nema mata lafiya yana kanka saboda ta dalili ka ta haɗu da wannan jarabawar, ballantana babu saki irin wannan sai na bidi'a dan haka ka biya malam wadata kuɗin sa saboda har yanzu ita matar kace" Audi ya soma ƙoƙarin tashi da gawar yaron sa yana faɗin "wannan haɗin baki ne Sam babu adalci a wannan zaman, matar da nace na sake ta kuma zaa ce na kula da ita, ta yaya ciyar da ita da nema mata lfy yake ƙarƙashi na bayan na sake ta, kai da na zo mak da zancen an kashe min magaji ka bimin haqqi Sai ka buge da wata magan can, tukunna ma waye yace ba'a saki dan tana cikin jinin haihuwa? Mai gari ya dube sa cikin bacin rai yace" ka zauna Ina magana da kai ina zaka je, nace kuɗin da Wadata ya kashe ka maida masa domin bashi yake da alhakin kula da ita ba kai ne kuma Ummy har gobe matar ka ce babu wannan sakin" ran Audi ya baci, yayi jim kaɗan kafin ya dubi mai gari yace "ina cikin wani hali na alhini saboda rasa ɗana, a bar ni naji da mutuwar a yanzu idan anyi masa sutura zan biya shi" Wadata ya muskuta kaɗan yana kallon mai gari, yace
"ranka shi daÉ—e maganar kuÉ—in saka jini a bar shi nayi saboda Allah, kawai ya bada kuÉ—in maganin da zaa siya mata"
Audi ya dalla masa harara yana faɗin "duk zan biya ka ragin ko sisi bana so daga gurin ka, in har da gaske saboda Allah kayi matarka bazata zo nan bainar jama'a tana maimaita mijin tane ya siye jini aka saka mata ba, dan haka zan biya gudun gorin wata rana Kuma Ummin na bar maka ita bana so" ya tashi da gawar da sauri kafin mai gari yayi magana ya fice ransa matuƙar bace, Kai tsaye gida ya nufa inda Shamwilu.
Yasira fitowar ta bayi kenan yayi dai dai da shigowar sa, ta É—aure fuska tana faÉ—in "Sai yanzu kake dawowa gida? Yace
" Afuwan abar ƙaunata kuɗin ne basu samu da wuri ba, gasu da ƙyar na samu" ta fisge kuɗin daga hannun sa tana dubawa, dubu biyar ne kana ta saki fuska ba yabo ba fallasa tace " karbi kaje da su inda Azumi ka bata kuɗin zubin adashe ne da nake yi, ka tunasar da ita kada ta aiko min cewa ban zuba a wannan watan ba" ya haɗiye wasu yawu da ƙyar yace
"Wai dama yasira saboda ki zuba kuɗin adashe ne kika saka ni cin bashi har dubu biyar, ni ne zan maki zubin? Ta bata fuska tana masa wani kallon raini tace" me kake nufi, ko ban isa ka bani kuɗin ba ne? Yace "a'a yi haƙuri gimbiyar mata ki saki fuskar ki bakya kyau idan kika bata fuskar, wasa nake wallahi na haƙura" ta ja ƙaramin tsaki tana faɗin "ka da ka manta da mgnr da muka yi shekaranjiya, ka siyar da gona ɗaya ko ka karbe ta gurin Audi ka siyar ka bawa yaran nan jari za su je can kudu su yi sana'a ba aikin noma zasu zauna yi a gida ba". Yace "duk yanda kika ce haka zaa yi, ai dukiyar taku ce keda yaran ki Kinga bazan ji asarar siyarwa na biya buƙatun ku ba, zan duba naga wacce zaa siyar"
batare da tayi magana ba ta nufi ɗakin ta da hanzari ya bi bayan ta da sauri yana waiwayen bayan sa idan babu yara a gida, kafin ya washe baki ya ƙarasa shiga ɗakin, ta juyo tana kallon sa "lafiya sai bibiyata kake? Ya sosa kansa yana dariya yace" haba yasira yanzu duk wannan hidimar da nayi na bada dubu biyar na adashe bai isa ya saka nima a ɗan bani na lasa ba, ki taimaka yau kusan wata takwas kenan ina bibiyar ki kina hanamin yau kaɗai sabida Allah ki bar ni nayi". Kallonsa tayi galala baki a buɗe kafin tayi wani shu'umin murmushi tana taba hannayen ta tace
"Shamwilu ko na baka dubun ka biyar ne, naga sai mita kake a kansu zan iya fita naje na nema da kaina ka sani". Yace "aa babu inda zaki je neman kuɗi bayan gani, ba mitar kuɗin nake ba naga nayi abin a yaba min ne a saka min da wani abin? Tace" to ka fice min daga ɗaki kafin raina ya baci" yace "ki taimaka ko sau ɗaya ne, abin nan tana cikin yunwa idan ba wata kike so naje na nema a waje ba? wata irin dariya tayi mai cike da shaƙiyanci kafin ta juyo tana kallon sa ƙasa da sama a wulaƙance tace
" shege ka fasa, ka je ka kwanta da wata mace a waje ka dawo ka same ni gidan nan " zai yi magana suka jiyo muryar Audi Yana sallama, da hanzari ya fita baya so ko kaÉ—an Audi yaji suna sa'in'sa da Yasira, a zauren gidan suka yi kicibis yace
" Wai Kai da Sai ka faÉ—omin kawai a gida bazaka jira na fito ba, idan ka same ni akan matata fa? Audi yayi baya jiki a sanyaye yana faÉ—in "fito abokina fito ka ga babbar asarar da ta same ni a yau" wannan karon sai ga hawaye a fuskar sa wanda ya sanyaya jikin Shamwilu yabi bayansa ba kuzari, kallon abinda ke hannun sa yayi yana faÉ—in
"Audi menene ka ƙunso haka a zani, kada dai ba abin wani kaje ka ɗauka aka ganka kazo kana min kuka ba, dan Allah kada ka saka ni a matsala". Audi ya sharce majina yana faɗin
"kasani duk acikin hali na marar kyau giya ce kawai da nake sha, bana sata, bana caca da zina kuma ina sallah biyar a rana kullum ko da na buge, dana farfado nake ramakon sallah, meyasa kake bina da sharri a maimakon alheri? Shamwilu ya washe baki kaÉ—an yana dafa kafaÉ—arsa yace
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.