Complete Hausa Novels

Farar Taska Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Farar Taska Part 1 Complete Hausa Novel.docx

Chapter 1 of 14

[8/1, 9:02 PM] J💕: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt?mode=ac_t

ﺑِﺴْـــــــﻢِﷲِﺍﻟﺮَّﺣْﻤَﻦِﺍلرَّﺣِﻴﻢ

©️Fertymerh Xarah💞

*FARAR TASKA*

1

Gudu gudu, sauri sauri haka take haɗa tafiyar ta, tana yi tana waigawa bayanta tana hango yanda yara suke biye dashi suna mashi waqa, wasu ma riƙe da babbar rigarsa suna jansa sai tangaɗi yake kamar zai faɗi ƙasa, tana shiga gida ta nufi inda mahafiyarta ke ƙoƙarin kunna gawayi domin ta ɗora girki, ta ajiye mata markaɗen gari a gabanta da sauri ta juya zata fice tace " Saurin me kike haka, ina zaki je, ba yanzu kika shigo ba? ta shagwabe fuska kamar zata yi kuka cikin damuwa da bacin rai, tace " Innar mu yanzu na hango yara suna bibiyar baba da waqa ina tunanin yaje ya sha wannan abin da bakya so yana sha a kullum" batare da tayi magana ba taja dogon tsaki ta juya tana cigaba da gyara wuta, ganin haka yasa yarinyar yar kimamin shekara goma da haihuwa fita da sauri ta nufi inda mahaifin su yake, yaran suna hangota suka soma gudu suna faɗin " ga Meelah ta zo kowa ya gudu kada ta fasa masa goshi" duk suka gudu suka barshi, cikin takaici bayan ta ƙaraso inda yake tana kallon sa tace " Baba kasan Innar mu Bata so kana shan wannan abun meyasa bazaka daina ba, baka jin kunyar yanda yaran ƙauye suke biyo ka kullum da waƙa, innar mu ta gayamana wannan abin da kake sha ba mai kyau bane, hassalima addinin mu ya hana kuma tace yana taba lafiyar ɗan adam muma kada mu kuskura muce watarana zamu sha, meyasa kai bazaka daina ba ko dan saboda Allah da ya hana? ya buɗe idanunsa da ƙyar tare da nuna ta da ɗan yatsa yace " zan ci uban ki yanzu idan kika sake min magana irin wannan, maza matsa bani hanya kar nasa ƙafa na shure ki nayi maki illah bani da kuɗin magani" ta riƙa hannunsa suka soma tafiya tana addu'a a ranta Allah yasa kada ya daki Inna, wani lokacin duk ya sha ya fita hayyacinsa haka yake zuwa yayi ta dukanta a gabansu, tun suna yara har suka taso yake wannan halin bai daina ba, sanda suka iso gidan ko kaɗan Inna bata tayar da kai ta dube su ba, ta cigaba da aikin da take tana kiran Safeenah, da sauri ta fito daga ɗaki tana faɗin " Innar mu sai ƙwalla min kira kike kamar zaki fasa kaina, sallah fa nake yi" cikin takaici ta dube ta tana faɗin " yanzu fisabilillah Safeenah sai yanzu kika Asr? tace " kiyi haƙuri kada ki dake ni Inna wallahi barci ya ɗauke ni bansan lokaci yayi ba" tayi ƙwafa tana faɗin " zo ki gyara kayan miyar yanzu kafin tuwon ya nuna" tace " to innarmu" ta ƙarasa wurin ta da sauri, Audi ya dube ta cikin maye yana faɗin " ke Ummy baki ganni bane kika yi kunne uwar shegu dani" a raunane ta ɗago tana kallon sa, tace " kayi haƙuri sannu da dawowa" yace " saboda kin raina ni sai da nayi magana zaki min sannu, to ki riƙe sannun ki bana so amma jikin ki yau zai gayamiki tunda har yanzu baki hankali ba baki san yanda ake tarairayar miji ba" gaba ki ɗaya duka ɗiyan suka buɗe ido suna kallonsa, Meelah tace " dan Allah Baba kada ka dake ta yau kayi haƙuri ka barta" yace " yi min shiru kafin na fasa maki baki yanzu" ya nufi inda yake ajiye bulalar sa ƙatuwar gaske, Innar mu na ganin haka ta tashi ta nufi ɗaki ba dan komai ba saboda bata so maƙota su jiyo dukan da yake mata, yaran suka soma kuka sosai suna bashi haƙuri bai saurare su ba, suna ji yana dukan mahaifiyar su da ƙarfi babu yanda zasu iya taimakonta, suna jin yanda take nishi alamar dukan yana shiga jikinta sosai amma bazata iya buɗe baki tayi kuka saboda ta ɗaga hankalin ƴaƴanta ba, har ya gaji dan kansa ya fito daga ɗakin ya nufi nasa, da sauri duka su ukun suka faɗa ɗakin suka nufi mahaifiyar su, a tare suka faɗa jikinta suna wani irin kuka gwani tausayi ganin yanda take kwance hawaye na fita gefen idanuwan ta, ga shatin bulala a jikinta da cinyoyinta, suka rufe mata cinyoyin suna ƙara rungumeta cikin tsantsan so da tausayi ga mahafiyar su, Tace " Safeenah kije ki ƙarasa girkin, ai zaki iya ko? Safeenah ta gyaɗa kanta tana share wasu ƙwallah, kafin ta tashi ta fita jiki a sanyaye, Meelah tace " Innar mu zaki sha ruwa na kawo maki? ta gyaɗa kanta a hankali, Meelah ta tashi da sauri ta fita daga ɗakin bata jima ba sai gata ta dawo ɗauke da Cup ɗin ruwa ta zauna gabanta tana faɗin " tashi kisha innar mu" ta tashi da ƙyar tana rumtse idanunta tare da dafe ɗan matashin cikinta ta zauna, Meelah ta kai cup ɗin ruwa bakinta ta soma sha, sai da taga ta ɗauke kanta gefe kafin ta ajiye cup ɗin tana faɗin " Innarmu inje in ɗora ruwan zafi na gasa maki jikin ki? ta girgiza kanta a hankali tace " ki bari idan na huta kaɗan zanje nayi wanka". Haka suka yi ta ɗawainiya da Mahaifiyar tasu cikin so da kulawa duk da suke yara hakan bai sa sun gane mahaifinsu baya kyautawa mahaifiyar su.

Malam Audi ɗan Asalin jere, mashayin giya idan nace mashayin giya ina nufin komai zai iya akan ya sami giyar, yana shekara ashirin ya tashi da ɗabi'ar shaye shaye ga rashin ji, dalilin haka iyayen sa suka je suka samo masa mata mai kyau buzuwa suka aura masa ko da Allah zai sa ya gyara ɗabi'un sa, tun bayan auren sa da Ummy Aysha maimakon su ga canjin da suke fatan samu sai suka ga sabanin haka, sun yi faɗa sun yi rarrashi bashi da niyar canzawa, duka kayan ɗakin da aka kawo Ummi dasu ya siyar gurin shan giya, idan bashi da ko sisi zai je duk inda zai nemi bashi yaci bashi yaje ya siya, duk garin babu wanda bai san Malam Audi da Aminin sa Shamwilu saboda barasa ba, wanda yawanci duk abubuwan da yake yi shine yake saka shi komai, iyayensa su suke kula da Ummi yarinya mai kyau da kirki ga nutsuwa amma bata yi dacen miji nagari ba, bayan ta sami cikin farko ta haifi Safeenah, tun a lokacin ya ke ƙara cusguna mata na ta haifa masa mace ba namiji ba, acewar shamwilu ƴaƴa mata basu da wani amfani a rayuwa, hakan ya ƙara hasala Audi wanda yaji sam baya son a haifa mace, ya faɗa ya ƙara faɗa da babbar murya baya son ƴaƴa mata kada ta kuskura ta ƙara haifa masa, tun da ta sami ciki na biyu ta shiga tsoro da zullumi tayi tattaki har inda iyayen ta taje ta sanar dasu irin halin da take ciki game da mijin da suka aura mata, sosai sun ji babu daɗi kuma sun nuna bacin rai ganin yanda duk ta rame wannan hasken nata mai ban sha'awa duk ya soma gushewa, suka riƙe ta suka hanata tafiya har sai da iyayensa suka zo suka bada haƙuri sosai sannan iyayenta suka yarda ta koma, bayan dawowar ta aka zauna dashi aka masa faɗa sosai da nasiha akan ya gyara zamantakewar sa da matarsa kai har da rayuwar sa ma idan ba haka ba zata koma gaban iyayen ta yaje ya nemawa kansa wata matar ya aura, sosai ya tsorata da fushin iyayen nasa, sai ya sassauto ya rage hantarar ta da dukan ta, yana siyo mata abinci da kayan maƙulashe irin na masu juna biyu da addu'a Allah yasa namiji zata haifa masa, ranar da ta haifi Jameelah yaji duk duniyar tayi masa baƙi, da masu karban haihuwar suka fice haka ya same ta cikin jego da raɗaɗin zafin haihuwa yayi mata duka sosai akan ta haifa masa mace, maƙota sai da suka shiga tsakani kuma kowa yayi Allah wadarai da hali irin na Malam Audi na rashin tausayawa, sanda iyayensa suka ji labari sai suka ɗauke ta suka maidata gidan su, dama mahaifinsa ba wata lafiya ne dashi ba kuma shi ba mai ƙarfin arziki bane, haka ya samu ya siyawa Ummi rago da ƙyar, suka saka mata suna Jameelah saboda kyawun nata har ya zarce na Safeenah, bayan haihuwarta da kwana goma Allah yayi wa mahaifin rasuwa, ko kaɗan mutuwar bata taba Malam Audi ba babban burin shi akai mahaifinsa makwancinsa azo a raba gado a bashi haƙƙinsa ba sai an gama addu'a kwana uku ba kamar yanda Shamwilu ya bashi shawara, idan ba haka ba zai wayi gari ya tarar mahaifiyarsa.ta cinye gadon ta barshi, sai yaji hankalinsa ya tashi ya sami mahaifiyarsa da mgnr gado kafin a gama adduar kwana uku, tun daga lokacin daya furta wannan maganar hankalin mahaifiyarsa ya tashi ta fashe da kuka, ba dan mutuwar mijin ba sai dan mamaki da irin ɗan da ta haifa, mahaifinsa ko kau dashi baa yi ba yana mgnr gado, da ƙyar mutane suka rarrashe ta suka bata haƙuri akan kukan da take, sai tayi ta masa addu'a Allah ya shirya mata Audi ko bayan ranta ya kula da Ummy, aka yi masa sallah aka je aka kaisa, sun dawo abokan mahaifinsa sun zauna yace duk su tashi su bar ƙofar gida babu uban da ya isa ya zauna yayi masa zaman makoki a gidan sa, duk ya korasu suka bar wurin kowa da irin abinda yake faɗa akan sa, yana shiga gidan yace da mahaifiyarsa " siyar da gidannan zanyi ina buƙatar kuɗi ki tattara komai naki da kike so kije can ƙauyen ku ki zauna da ƴan wanki, nayi maki alƙawari ziyartar ki akai akai kina saka min albarka, kuma ko na siyar da gidannan zan baki haƙƙin ki kija jari bazan ci ko ƙwandala a kuɗin ki ba" Ummi na gefe kanta sunkuye tana hawaye, tana roƙon Allah ya raba ta da wannan mugun mutum, mahaifiyarsa ta cira kai da ƙyar ta dube sa duk idanunta cike da ƙwallah ta buɗe baki zatayi magana sai ta kasa nan take ta faɗi gurin ko da aka duba rai yayi halinsa zuciyarta ce ta buga, wannan karon yaji mutuwar mahaifiyarsa kaɗan ba kamar ta mahaifin sa ba, har akaje aka kaita itama baiyi magana da kowa ba yana tunani a ransa menene laifinsa da mutanen gari suke zaginsa akan ya kashe mahaifiyarsa, shi fa maganar gado kawai yayi kuma musulunci ne ya yarda da hakan. Iyayen Hafsatu sun sami mummunan labari akan mutuwar sai suka shigo mota daga maiduguri zuwa jere ta'aziya akan hanyar su suka sami mummunan hatsari duk suka mutu a tare, Ummi ta shiga ruɗani matuƙa sosai da wannan abun fiye da zaton mai karatu, tayi kuka har ta gode Allah tayi addu'a da rungumar jarabawar ubangiji, haka tana ji tana gani ya mayar da ita gidan sa ya kuma siyar da gidan mahaifinsa ko ƙwandala bai bata ko siyawa yaranta wani abin ba, yaje yana siyan barasa da kuɗin shi da shamwilu, sai suyi kwana biyar basu saka shi a ido ba da haka har ya canye duka kuɗin gadon sa da duk abinda ya mallaka na iyayensa, ita take zuwa wankau gida gida ana biyanta kuɗi tana ci da kanta da ƴaƴan ta guda biyu, da haka har ta sami ciki na uku, shima sai daya ja mata kunne idan ta kuskura ta haifa masa mace wannan karon kashe jaririyar zai yi bazaa masa rainon ɗiya mata a gidan sa ba.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.