Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel

Apr 1, 2026 - 22:11
 0  0
Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel

Dariya Shu'aibu ya kwashe da ita yana cewa, "Wallahi ina ma ni ne , ai ko ita ce zaka samu wani abu agunta kana ganin yarinya cikakkiya , ai wallahi dani take so tuni an wuce gun , kuma wallahi babbar karuwa ce , domin ko kud'in yaharta bani da shi."

Dogon tsaki Uncle Yahaya yaja yana cewa, "Dama dai sona take da gaske shi ne , amma kana ji fa , wai gayyatata take na kwana a d'akinta fa."

Kafin ya rufe baki ya hangota tana tahowa inda suke kawai Uncle Yahaya ya juyar da kanshi yana tsaki , 

hakan yasa Shu'aibu kallon inda take yana sakin baki , riga da wando tasa wanda suka kama jikinta sosai , tun daga nesa Shu'aibu yake jin kamar ya rungumota , bari ma lokacin data 'karaso bada ban ya daure ba da Fa'iza taji wani abu😂.

,"Haba Yahaya, sai ne manka nake a cikin garin nan ."

Uncle Yahaya ya yi mata shiru ko kallonta bai ba , ta sake cewa, "Na yi maka girki jazo muje ."

Kallon wayarta tai dake hannunta sakamakon kiran da ya shigo, Abdul Salim , kawai ta kashe wayar tana cewa, "Da kai fa nake magana Yahaya."

Uncle Yahaya yaja dogon tsaki yana cewa, "Ke ni fa babu inda zani , baza ki ta'ba samun abin da ki ke so ba , kawai dan kinga kirjinki dam -dam shi ne za ki tunanin za ki rud'eni."

Ya sake jan dogon tsaki ya bar waje , shi kuwa Shu'aibu ya tsaya yana kallonta dama shi ne .

Fa'iza cikin ranta tace, "To wallahi matukar na cika karuwai gaske sai na jawo Yahaya jikina, mu zuba mu gani ." A'a ni ko na ce Allah ya ba mai rabo sa'a .

Uncle Yahaya a yau ya shirya ya baro legos, lokacin da dare ya yi tazo ta sami Shu'aibu, yake tabbatar mata da Uncle Yahaya ya koma Kano , aiko ta yi takaici , kawai ta amshi numbarsa ta koma.

Zainab da Mahmud ne a kan hanyarsu ta zuwa asubiti, Mah.mud ya kalli Zainab wanda duk hankalinta yake kan had'uwarsu da Harun yana cewa, "Kin san wazan dubu ."

Zainab tace, "A'a Yaya Mahmud."

Mahmud ya jawo hannunta ya ri'ke , hakan yasa Zainab tsayawa tana kallonshi , shi ma ya kalleta yana cewa, "A haka zamu taafi."

Tai ajiyar zuciya suka ci gaba da tafiya badan taso ba .

Sisters kar a manta comment dina a private za a ajen.

Files

What's Your Reaction?

Like Like 0
Dislike Dislike 0
Love Love 0
Funny Funny 0
Angry Angry 0
Sad Sad 0
Wow Wow 0