Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 7 of 17
"Yo ka barsa mana tunda ai uwarsa ce take d'aure masa gindi yayi ma mutane rashin kunya ai".
Inna Lami ta katse Inna Fatuh tana d'aga mata hannu ta ce.
"Kinga Inna Fatuh tunda aka fara wannan kicimulin baki ji baki na ba, dan haka kar a sake saka ni a ciki a'ato".
"Ai kawai ki fito fili ki ce zaki zage ni Lami, dama ai kema ba k'aunar Fad'ime kikeyi ba wallahi, bakik'i ma Fad'ime zuwa yanzu ta mutu ba ai, to Fad'ime dai nan gani nan bari ajiyar Allah ce wallahi".
Lami zata sake magana ranta a b'ace Malam ya d'aga masu hannu zuciyarsa babu dad'i ya kalli dandazon jama'ar dake wajan ya ce.
"Kowa ya fad'i kud'in da tayi masa asara da wadda zasu je asibiti sukai Y'ay'ansu. Dan Allah kuyi hakuri kuma, Yaro ne ka haifesa baka haifi halinsa ba".
Jama'ar wajan tausayin Malam ne ya kamasu dan haka da kyar wasu suka hakura nan take yasa aka kamo Akuya har biyu aka saida, aka biya kowa kud'in da ya kamata, sai mutum d'aya ce bata karb'a ba, wacce Yaronta jinsa ya d'auke ita ce tsaya a wajan yanzu tana cewa.
"Babufa kud'in da zan amsa naku, iyakaci a fito min da Fad'ime ta bud'e ma Yaro na kunnansa, idan ba haka ba kuma nima wallahi wajan Y'an Saddan zan kai k'ara, domin ni kud'inku babu uwar da zasu min".
Inna Fatuh zatai magana ta hango Fad'ime dake tafe ita da zugar K'awayenta.
Ganin Ibrahim zai nufi wajanta Babban Yayansu ta d'aga masa tsawa tana cewa.
"Na rantse da Allah karka sake ta tab'a min Jika, karka sake na ce".
Duk maganar da take yi hakan baisa Ibrahim tsayawa ba, sai da ya kamo hannun Fad'ime dake zare ido waje y'an cikinta na k'ara, domin tasan an kawo k'ararta tun kan ta iso gida, tana jin tsoron Ibrahim shine kad'ai duk cikin familynsu take d'an shakka shima kad'an.
Sai da ya d'auketa da Mari har sau biyu, yana zare mata ido yana cewa.
"Dan Ubanki abunda aka ce kije kiyo kenan?, kin san iyayen mutanan da suka zo kawo k'ararki? Ke wai wacce irin y'ar banzar yarinya ce ne?, shegiya kamar shaid'aniya, ke kullum kece y'ar kawo k'ararki wajan mutane, dalla wuce min a nan karna karya miki k'afafu yanzu nan wallahi".
"Karyata mana, ai kawai ka idasa min ita na ce kaji Ibrahim?"
Cewar Inna Fatuh data warce Fad'ime daga hannunsa yanzu tana b'alla masa uwar harara.
Banza yayi da ita ya kalli sauran K'awayen yana zare masu ido ya ce.
"da'aAllah can kuma kubar wajan nan".
Aje nik'an sukai da sauri suka juya da gudu suka bar wajan.
Sake fisgo Fad'ime yayi a hannun Inna Fatuh ya matso da ita inda Matar nan take da Yaronta yana cewa.
"Kiyi Maza-maza ki bud'e ma Yaron nan kunne idan ba haka ba kuma na rantse miki na lahira sai fiki jin dad'i".
Matsowa Inna Fatuh tayi wajan tana cewa.
"Wai kai Ibrahim wane irin abu ne wannan kake haka, kana ma yarinya tsawa sai ka ce ba ubanku d'aya ba, ai ku duka ba k'aunarta kuke ba, shikenan kullum ace cikin hantarar kuke, to wallahi ranka zaiyi mummunan b'aci ne".
Nan d'in ma ba tanka mata yayi ba.
Sai k'ok'arin bugu da yake son kaima Fad'ime domin yaga yadda ta wani tsaya bata niyar yin abunda ya ce.
Yasa Inna Fatuh kallon Malam dake tsaye cike da jin haushinsa shima ta ce.
"Idan har ni ce na haifeka to kaba Yaronka umarnin cewa karya sake ya sake tab'a min Jika, idan ban isa dashi ba, ai kai na isa da Kai".
Ba dan Malam yaso ba ya dakatar da Ibrahim daga dukan da yake son kaima Fad'ime.
Malam ya matso a hankali cikin kwantar da murya ya ce.
"Fad'ime y'ar albarka ki bud'e ma yaron nan kunnansa kinji".
D'an sakin fuskarta tayi domin da tun farko da lallami aka bi da ita da tuni tayi abunda suke so. Dan a duniya Fad'ime ta tsani a d'aga mata murya.
A hankali ta juya wajan Inna Fatuh tana cewa.
"Suje gida Kunnan nasa zai bud'e".
Tana fad'ar haka ta shige cikin gidan.
"Kutumar uban can, ni Lami naga takaina, ace yarinya tayi laifi amma ko a jikinta, ko da yake d'aurin gindi ta samu ai, dole tayi abunda take so ai, ta taka wadda take so ".
Inna Lami ta fad'a cike da bak'in cikin Fad'ime, yau so tayi a tafi Police teshin d'in da ita ace ubanta sosai.
"Ohhh dai ba kuma yadda za'ayi da ita kuma ba".
Cewar Inna Fatuh.
Lami ta shige gida tana jin bak'in cikin dawowarsu wannan gidan, da ace suna can gidansu ai da sai yadda tayi da wannan aljanar yarinyar.
Kamin su wuce ga mamakin Matar nan uwar yaron nan sai ji tayi Yaronta na cewa yanzu yana jin komai cike da murna yake fad'ar haka.
Inna Fatuh ta kallesu tana cewa.
"To daga yau sai kiyi ma D'anki gargad'in cewa karya sake Jan Jikata, dan k'ila a gaba zai iya rasa idanuwansa ma".
Itama ta k'are maganar tana d'aukar nik'anta dasu Laure suka aje, ta shige cikin gidan.
Malam ne ya tsaya ya sake ba Matar hakuri sosai...........
*FAƊIME...💋🌸💕*
_(Dangin Jinnu)_
©By Nainarh KD & Zahrah Royal Star
*Dedicated to Salma Ahmad Isah (Candy)*
*بسم الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…*
*A love & Laugh story that will capture your heart and soul.*
05
*BAYAN SATI ÆŠAYA*
Abin Duniya da halin FAD'IME ya gama isar Malam Yahaya hakan ya sa ya yanke shawarar aurar da ita domin ta kai minzalin Auren har ma ta wuce domin shekarunta goma sha shida tana gab da shiga na sha bakwai sa'anninta ma zalla duk an aurar da su sai waɗan da ba'a rasa ba irinsu Sa'ade ƙawayenta da suka addabi ƙauye. Da wani mutumi mai suna Ɗan Abba Malam ya yanke shawarar aurar ma FAD'IME kuma hakan ya biyo bayan maganganu ƙarya da gaskiya a kan FAD'IME ne da Lami ta faɗa masa kuma ita ta nema da ya aura wa Ɗan Abba FAD'IME kuma ba musu Malam ya amince domin ta riga ta gama da shi sai abin da take so shi yake yi ba tare da musu ba koda kuwa hakan shi bai kwanta mishi ba sai dai ganin Ɗan Abba mutumin kirki ne a idon kowa na ƙauyen, kuma ma har Mata yake da ita da yara biyu shi ya sa ba tare da wani dogon bincike ba Malam ya yarda zai aura masa FAD'IME dama kuma sara ne a kan gaɓa domin Ɗan Abba ya daɗe da mutuwa a kan son FAD'IME sai dai bata ma san yanayi ba kuma ko yanzu da Mahaifinta ya bashi ita sai wani farin ciki ya cika shi shikenan zai sama muradin ransa FAD'IME ba tare da ɓata lokaci ba a ka tsayar da lokaci da Ranar Aure nan da sati ɗaya kuma a ka fara shirya shirye sai dai a ɓoye ba tare da FAD'IME da Inna Fatuh sun sani ba, gudun abin da zai je ya dawo ya sa Malam ya ɓoye musu batun don ya san muddun FAD'IME ta ce bata so to fa ko sama da ƙasa zata haɗe ne Inna Fatuh ba zata taɓa yarda a ɗaura Auren ba.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.