Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 13 of 17
Auta ya faÉ—a tamkar ya fashe da kuka.
Juyawa gefe Faɗime ta yi tana sakin dariyar ƙeta tana ji Malam yana yi ma Auta faɗa a kan yawan ciya-ciye daga ƙarshe ya yi masa sannu ya kuma taimaka masa ya koma Ɗakin.
“ƙari so ciki dama ina so nayi magana dake.â€
Malam ya faÉ—a lokacin da ya dawo da kallonsa kan FaÉ—ime.
Ba musu tabi bayansa har zuwa sashensa ta zauna saman tabarma tana jira taji ta yadda sai fara.
“wato Fatima wani babban laifi nayi miki ban kuma san ta yadda zaki karÉ“a al'amarin ba.â€
Faɗime ta ɗa go tana yi ma mahaifin nata kallon ƙasan ido, wato ya ɗauka batasan komai ba ke nan.
“Wani abu ne ya faru Baba?â€
Ta faɗa cikin ladabi kamar ba ita ba dan ta ƙosa ya yi ya gama ta fice ta aiwatar da ƙudirinta.
“dama...â€
“ai Bama abin da ya faru kawai dai ni ce na yanke shawarar kaiki Birni aikatau ai kina so ko?â€
Lami da ta yi wuff ta shigo ÆŠakin ta katse Malam da yake shirin magana da faÉ—in hakan.
Da kallon mamaki Malam ya bita, yayin da FaÉ—ime ta saki murmushi a zuciyarta ta ce.
‘lallai su Inna Lami anji Uwar bari an canza taku.’
A fili kuwa sai cewa ta yi.
“Birni kuma ni ba zan je baâ€
Ta faɗa tana miƙe wa tsaye ta fice daga Ɗakin tana sakin dariya domin kuwa ita a nata tunanin faɗuwa ce tazo daidai da zama.
Gidan ta fice gaba É—aya kai tsaye ta wuce zuwa gidansu Sa'ade, a hanya suka ji karo da Sa'ade dake ta faman sauri tana waige-waige ga tumin kaya a hannunta.
“laa FaÉ—ime ashe kece ni wallahi har kin ban tsoro amma ina naki kayan ne kodai ba zaki tafi da komai ba?â€
Sa'ade dake ta faman zuba ta yi shiru ganin FaÉ—ime tana dariya.
“ke ni barni da wannan zancen dan ya zama tsoron labari yanzu dai batun aure babu...â€
Sa'ade ta zazzaro ido waje sai kuma cike da zumuÉ—i ta ce.
“amma naji daÉ—i sosai hahaha cike su Inna Lami an ji uwar bari ke nan bani labari yadda ta kaya.â€
“hmmm ke dai bari kawai domin labarin da tsayi a taÆ™aice dai yanzu ta ce Aikatau zata kaini Birni....â€
“Aikatau kuma?â€
Sa'ade ta katse FaÉ—ime tana zazzaro ido.
“matsalata dake Sa'ade bakyajin ribar zan ce ki bari mana na kai aya.â€
Cewar FaÉ—ime, sannan ta ci gaba.
“eh kuma da fari zan nuna banaso sai da Æ™yar zan amince idan kuma naje ba aikin zan yi ba zai dai kasance na sama hanyar zuwa birni domin cika burina na zama MawaÆ™iâ€
FaÉ—ime ta kai maganar tana lumshe ido cike da zumuÉ—i bata jira Sa'ade da mamaki ya sa ta kasa magana ba ta ci gaba da faÉ—in.
“saboda haka yanzu kije tun kafin Laure ta fito ki faÉ—a ma ta labari ya sauya ba batun guduwa.â€
FaÉ—ime tana gama maganar ta juya abin ta zuwa gida domin zumuÉ—in zuwa birni take.
_____
DA RANA
Inna Lami ce durƙushe gaban Inna Fatuh tana faman yi ma ta magiya a kan ta bari a tafi da Faɗime Birni aikatau a gobe.
Yayin da FaÉ—ime take zaune gefe tana faman kai loma kamar batasan abin da ke wakana ba.
“ke Lami nafa san ba mutunci ne dake ba ki faÉ—a min abin da kike shiryawa da kike wannan magiyar a kan na bar FaÉ—ime taje Birni aikatau salon ki cutar min da ita ko to kuwa ba zata saÉ“u ba ehe wato saboda kin ga auren bai yiwu ba shi ne kika É“ullo ta nan.â€
Inna Fatuh ta ƙare maganar tana bin Inna Lami da kallon banza.
Wani takaici ya cike Lami amma ta daure domin ita kaÉ—ai ta san abin da take shiryawa a kan zuwan FaÉ—ime Birnin, hakan ya sa ta ce.
“wallahi Inna Fatuh ba abin da nake shiryawa kawai dai nayi nadama ne da irin abubuwan da nake yi ma FaÉ—ime a da.... ouchâ€
Ta kai maganar tare da sakin ƙara na azaba sakamakon wani tsunƙuli da a ka yi ma ta a baya.
FaÉ—ime ta saki dariyar mugunta a fili da hakan ya sa duk suka dubeta sai ta ma ze da faÉ—in.
“Inna Fatuh kawai ki yarda kika sani ma ko na samo zuÆ™eÆ™en miji a can Birninâ€
Washe bari Inna Fatuh ta yi jin kalaman FaÉ—ime sai kawai ta duba Lami dake sakar ma ta harara a fakaice.
“to ai sai ki tashi ki bani wuri tun da ta amince kuma kada ki kuskura na gano kina shirya wani abin ne dan ba zan kyaleki ba.â€
“ai Inna Fatuh ba ma abin da nake shiryawa.â€
Cewar Lami sannan ta bar wurin cike da farin ciki ta lalubo ƙaramar nokiya ɗin wayarta ta kira Dillaliya ta sanar da ita halin da a ke ciki.
_____
“wai FaÉ—ime shikenan yanzu tafiya Birnin zakiyi?â€
Laure ta tambaya lokacin da su ukun suka haÉ—u a wurin da suka saba haÉ—u wa.
Sai da FaÉ—ime ta gwagwiyi goribar hannunta sannan ta ce.
“da gudu ma, ke Laure ko dai baÆ™in ciki kike min ban sani ba?â€
Da sauri Laure ta ce.
“Ni a wa Allah baki haÆ™uri kawai ina jajatawa ne zamuyi kewarkiâ€
Sai FaÉ—ime ta yi dariya tana faÉ—in.
“mu je nayi É“arna na Æ™arshe kafin na tafi birni domin ban san ranar dawowata ba.â€
ÆŠunguma suka yi suka nufa hanyar fadamar mai gari da suka É—ibo rake jiya.
____________
Hajiya Saleema uwar gidan Alhaji Sa'id Ahmad LamiÉ—o tana da yara huÉ—u sun haÉ—a da Alhaji Ahmad da shi ne Babba sai kuma mai bi masa Eng. Khamis sannan sai Alhaji Tasi'u da kuma Prof. Ridwan sai kuma Auta wato Hajiya Saratu...
Sannan sai Hajiya Haleema yaranta biyu, Alhaji Dauda sai kuma Hajiya Laraba.
Duka suna zaune ne a SAL Estate tare da iyalansu baki É—aya.
Hajiya Saratu wato mahaifiyar Fidaus ta kasance mace ce da bata yarda wani yafita da komai ba zata iya aikata komai muddun wani muradi nata da ta saka a gaba na son duniya zai cika sam bata yarda da faɗuwa ba al'amarin ta shi ya sa sam basa shiri da Mommy Matar Alhaji Dauda kasancewar Mommy ita ma halinta kusan ɗaya ne dana Hajiya Saratu na son abin duniya sai dai ta wani ɓangaren sun sha bamban. Kowacce tana Burin ganin tafi ɗaya a komai shi ya sa har yaransu sun taso a haka sam basa wani ga maciji tsakaninsu kuma hakan ya samo asali ne daga iyayen nasu mata, domin su iyayen maza kullum burinsu bai wuce ganin kan yaran nasu ya haɗu ba.
Alhaji Ahmad SAL yana da mata biyu Hajiya Zakiya da ake kira da Mamy sai kuma Hajiya Lubabatu da a ke kira da Nur.
Mamy yaranta huɗu curr, Salim, Maryam, sai kuma Muhammad da Saddika, yayin da Hajiya Lubabatu take da yara Biyar duk da kasancewarta mace ta biyu a gidan Alhaji Ahmad SAL sai dai ita ce macen da ya fara so tun ƙuruciya yayin da Hajiya Zakiya ta kasance auren haɗi a ka yi musu sai daga baya ne ya Aura Hajiya Lubabatu wato Nur, kuma ita ce mahaifiyar Safiuddin, Safiya ita ce ƴarta ta fari sai kuma Safiuddin mai bi ma ta sannan sai Jalil da Jalila twins sai kuma Auta Shaheeda.
Shekarun baya Mahaifan Safiuddin suka yi hatsarin mota lokacin suna tare da Jalilah a motar gaba É—ayansu babu wanda ya yi rai. Zo kuga tashin hankali wurin waÉ—an nan Ahali sosai suka girgiza da wannan mutuwar musamman ma Safiuddin da Æ´an uwansa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.