Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 15 of 17
Ganin rigimar da take son farawa yasa Inna Fatuh cewa da sauri.
"Allah ya baki hakuri bari na had'a miki, indai birni ne gaki can kinje ai, ni bana son ganin b'acin ranki ai. Duk dai inda kike ai k'aryar mutum ya iya cutar dake a'ato, idan ma mutum ya manta gara ya tuna".
Ta k'are maganar had'e da gogar zana da take ma Inna Lami.
Inna Lami kuwa tana jinta sai ma jawo kayan Fad'ime tayi ta cewa bari ta had'a mata da kaina ma, ba sai Inna Fatun ta had'a ba.
Abunda Inna Lami take da zumud'in tafiyar nan ta Fad'ime fa, k'ara ba Inna Fatuh mamaki yake had'e da tsoron wani abu take shiryawa wallahi.
Auta ne yayi sallama a k'ofar d'akin Inna Fatuh yana cewa.
"Inna ki fito ga Haj Bintoto can fa ta fara gajiya da jiranki. Ita kuma Fad'imen da ake jira dan ubanta bata fitowa ne ita zatai jira ne?".
Fad'ime data dawo d'akin yanzu bayan ta wanki idonta tayi tsakar tsaka tsami tana saka kaya da sauri sai zumud'in tafiyar take sosai. Turo baki tayi tana murgud'a ma k'ofar d'akin Inna Fatuh baki had'e da harara kamar Auta ne take gani wajan.
Inna Lami da sauri ta jawo hannun Fad'ime da k'ullin kayanta ta ce.
"Kai Auta ina ruwanka da ita, bana son irin haka fa tom".
Auta dake murmushin gefen baki shima yabi Fad'ime da harara yana cewa.
"Kai yau dai zamu huta da kawo k'arar shaid'aniyar yarinyar nan, haba mutum yana mutum amma kamar Aljani tsabar jaraba da rashinji, anya Fad'ime ba rabi aljan rabi mutum aka haifeki ba kuwa?".
Dak'uwa Inna Fatuh tayi masa tana binsa da wata uwar harara tana cewa.
"Kai Auta ka fita ido na, na rufe na rantse da Allah ka kiyaye ni fa".
Gaba Auta yayi bai tankama Inna Fatuh dake masa masifa har lokacin ba.
Inna Lami dake cikin d'akinta bayan ta fito da Fad'ime ta barta waje ita dasu Inna Fatuh da Auta.
Ta kalli Bintoto a hankali tana cewa.
"Bintoto kin tabbatar gidan yankan kai zaki kaita?".
Bintoto dake murmushin cin nasara da samun kud'in da zatai idan ta kai Fad'ime wajan Alhaji Bukhar, ba k'ananun kud'i zata samu ba, harma da ita Inna Lami za'a bata wani abu daga ciki, shi yasa ma ta amince.
Kallabin dake kanta ta k'ara turo shi gaba, domin daka kalli yanayin Bintoto zaka shaida y'ar duniya ce ta gidan gaba, sai wani taunar chingum take idonta kansa an baura masa kyalli, ta ce.
"Haba Lami sai kace baki sanni ba, ai nake gaya miki idan Fad'ime ta tafi ta tafi kenan bazata tab'a dawowa ba, kuma nake sanar dake ba gidan yankan kai zan kaita ba, kamar suna anfani da mata ne suna tsafi dasu, kamar k'ungiyar asiri dai haka, ai kina jin labarinsu ko?".
"Eh tabbas muna jin labarinsu, dama duk masu kud'in nan dake cikin birni ai da yawansu ba kud'in Allah da Annabi bane, na tsafi ne".
"Yawwa, tun da kin gane mubar maganar a nan saina dawo zan taho miki da naki kason, domin Alhaji Bukhar ya dad'e yana neman yarinya budurwa mai shekaru irin na Fad'ime ba'a samu ba, sai ni ya ba cigiyar ya ce idan har na samo masa zai bani kud'i masu yawan gaske, dan haka kema dole ki samu kud'i masu yawa daga ciki".
Wani kalar murmushi Lami ta saki tana kallon Bintoto kamin zatai magana suka ji muryar Inna Fatuh na cewa.
"Wai Ina Lamin ne, da ita Bintoton miye kuke k'ullawa ne cikin d'akin, idan ba rashin gaskiya ba ai sai ku fito waje kuyi maganar da zakuyi mana".
Da sauri Lami ta kamo hannun Bintoto suka fito tana fad'in.
"Haba Inna Fatuh miye zamu shirya kuma?, kawai fa ina sake gaya mata ne ta kula da Fad'ime sosai".
Wani kallo kawai Inna Fatuh tabi su dashi tana tab'e bakinta ta ce.
"Hmmmm Ohho maku dai, idan ma akwai abunda kuke k'ullawa gara tum wuri kuma daina, kuje tun wuri ku warware abunda kuke shirin aikatawa domin dai Fad'ime ba mutum ce kamar kowa ba da......
Da hanzari Inna Lami ta tari hanzarin Inna Fatuh tana cewa.
"Inna Fatuh mi ya kawo duk wannan canzan Kuma?".
"Uhuhmm ai kin san miye nake nufi dashi Hajiya".
Inna Fatuh ta k'are maganar tana b'alla masu harara su duka.
Bintoto data gaji da maganar ta su ta kalli Fad'ime dake tsaye sai murna take ita ta ce.
"Fad'ime muje ko gari na haske bamu bar cikinsa ba kuma, na so iyanzu mun kusa cikin garin Kano wallahi".
Rik'o hannunta Bintoto tayi. Inna Fatuh kamar zata fashe da kuka tayi saurin cewa.
"Baza'a bari Babanta ya dawo suyi ban kwana bane?, kofa K'awayenta basuyi sallama dasu ba".
Inna Lami da sauri ta ce "a'a Inna Fatuh indai Malam ne zan sanar dashi da kaina, dama kuma ai yasan da tafiyar tasu a yau d'in, K'awayenta kuma ai Inna Fatuh nake ganin kin san tun jiya ta sanar dasu, ai sunyi bankwana tun jiyan ko Fad'ime?".
Ta k'are maganar had'e da duban inda Fad'ime take rik'e da hannun Bintoto.
"Eh munyi sallama dasu idan sunzo sun tambaye ni Inna Fatuh ki ce na tafi birni saina dawo, zanyo masu tsaraba idan zan dawo".
Wasu y'an hawaye Inna Fatuh ta share tana fad'in.
"Ai shikenan Fad'ime Allah Ubangiji ya tsare ki da tsarewarsa, za'a gaya masu hakan".
Inna Lami ta tab'e baki a fakaice tana dannama Inna Fatuh harara.
Har k'ofar gidan Inna Lami da Auta suka raka su Bintoto Inna Fatuh kuwa k'in fita tayi.
___________________
Tafiya suke sun mik'e hanya domin zuwa inda zasu hau mashin domin fitar dasu daga K'auyen, babu yawan mutane a hanyar sai y'an tsiraro suma sai a d'auki lokaci basu had'u da wani ba.
Fad'ime kamar ance ta waiga ta hango matar nan da tayi mafarkinta d'azo cikin bacci, yanzu ma tana nesa da ita take ce mata.
"Fad'ime karki sake kibi Matar nan zuwa birni, bana fad'a miki ba karki sake kije?".
D'an sake waro ido waje Fad'ime tayi, kawai saita sami kanta da d'aga k'afad'arta tana cewa.
"Ni sai naje wallahi, haka kawai nayita zama a K'auye nida nake so na zama y'ar gayu na auri mai kyau d'an gidan y'an gayu, wallahi saina naje".
"Karki sake ki bita zakiyi nadama Fad'ime".
Turo baki gaba tayi ta sake d'aga kafad'arta alamar bazata ji maganar abunda take gaya mata ba.
Bintoto dake rik'e da hannun Fad'ime jin tana magana ita d'aya yasa Bintoto juyowa a zabure tana kallon inda Fad'ime ke kallo tana magana, sai dai bata ga komai ba, hasali ma maganar Fad'imen ce kawai take ji.
D'an girgizata Bintoto tayi tana cewa.
"Ke Fad'ime kanki d'aya kuwa kike magana ke d'aya".
Da sauri Fad'ime ta juyo inda Bintoto take tana murmushi ta ce.
"Babu komai wata mata ce fa na gani take ce min wai kar na biki zuwa birni".
A haukan Bintoto bata kawo komai a ranta ba saima cewa tayi.
"Hhhh so take tayi Miki bak'in cikin zuwa birni ne, manta da ita kawai muje waje na k'ure mana".........âœï¸
*FAƊIME...💋🌸💕*
_(Dangin Jinnu)_
©By Nainarh KD & Zahrah Royal Star
10
Last Free Page.
*ABUJA CITY*
Tun da suka shigo garin Abuja bakin Fad'ime yake a washe tun kafin su fito daga motar ta baza idanu tana ƙare ma ko'ina kallo irin na ƙauyanci. Ta juya bakiwashe domin ta yi ma Hajiya Bintoto magana sai dai kafin ta kai ga furta komai Hajiya Bintoto ta yi wuff tare da fesa ma ta wani abu kamar turare a fuska, galala Fad'ime ta yi tana dubanta da mamaki sai dai kafin ta yi wani yunƙuri tuni idanunta sun fara lumshewa wani nannauyar bacci ya yi awon gaba da ita, sai ta faɗa jikin Hajiya Bintoto.
Shu'umin murmushi Hajiya Bintoto ta saki suna haɗa ido da drivern Motar suka sake sakin murmushi a tare dama iya su kaɗai ne a motar tuni sauran mutanen sun fi ce, tada Motar drivern ya yi da dama shi ne abokin cin mushen Hajiya Bintoto duk wata bak'ar harƙalla da take yi tun daga kan safaran ƴan mata da yara ƙanana da take yi duka da taimakonsa ne.
Hanya É—oÉ—ar ya É—auka yana tsala gudu tun suna kan titi har suka fara shiga daji-daji sai da suka yi tafiya mai tsawon gaske tukunna suka iso bakin wani kogo da bazakayi tunanin akwai wani abu ciki ba.
Fitowa suka yi daga Motar Hajiya Bintoto tana riÆ™e da Fad'ime ita da drivern suka Æ™ari sa bakin kogon sai dai basu shiga ba suka tsaya sannan Hajiya Bintoto ta ciro waya tare da dannawa Alhaji Bukhar kira bugu É—aya ya É—auka yana zuba ma ta kirari da. “sai ke uwar mata kuma uwar duk wasu masu harÆ™alla kinci dubu sai ceto mai faÉ—a da cikawa Hajiya Bintoto ikon Allah kin faÉ—a kuma kin aikata.â€
Yanayi mata kirarin ne yayin da kan Hajiya Bintoto yake ƙara girma ɗan kwaran gwan tanajin ita ɗin ta kai, yayin da ta gefan Alhaji Bukhar tsananin farin ciki ne ya sa yake yi ma ta wannan kirari dan ya san in yaji kira daga gare ta to fa tabbas ta samu ne bare kuma yanzu da suka yi za su haɗu ta bashi Yarinyar da a ka samu shi kuma ya bata cikon kuɗin dan kuwa ya bata adibas.
“ni dai yanzu ba wannan ba Alhaji Bukhar gamu fa a bakin kogo nasan kuma a daidai wannan lokaci kana ciki shi ya sa nace da Rabilu Driver mu taho nan kai tsaye.â€
Hajiya Bintoto ta kai maganar tana taunar cingum har da bada sautin. Tiss! Tass! Toss!!
Dariya Alhaji Bukhar ya yi ya ce.
“kwarai kuwa ina ciki ko zaki Æ™ari so ciki ne?â€
Ya tambaya da sigar wasa.
Hajiya Bintoto ta zaro tana faÉ—in.
“wa? Ni wai? Allah sitira ai in ka ganni a lahira kaini a ka yi kai dai ka Æ™ari so kawai ga Yarinya lafiyayya an samu sweet 16 to 17 years da ita.â€
Wata uwar dariya Alhaji Bukhar ya yi tare da amsa ma ta da faÉ—in. “gani nan tafeâ€
Ta katse kiran ba'a jima ba sai gashi ya fito daga kogon da in za'a kashe Hajiya Bintoto da Rabilu Driver basa ce ga taƙamaimai ta inda ya fito ba.
Koda ya ƙari so Hajiya Bintoto ta nuna masa Fad'ime da ke sharar bacci, ya yi dariya yana suɗe baki ganin kyakkyawar yarinya haka. Ta ke a wurin ya tura ma ta cikon kuɗin ta asusunta miliyan uku dama miliyan biyu ya bata, cike da farin ciki Hajiya Bintoto ta miƙa masa Fad'ime sannan suka yi sallama ta shiga mota Rabilu yaja suka bar wurin yayin da shima Alhaji Bukhar ko minti guda bai sake bayan ya karanto wasu latsumai daga shi kar Fad'ime suka ɓace daga wurin.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.