Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 11 of 17
Inna Fatuh bata yi minti biyar da gama cin tuwon ba bacci mai nauyi ya É—ibeta ai kuwa ta jingine a Wurin tana kwasar bacci.
Ita kuwa Faɗime kai tsaye sashen Inna Lami ta nufa ta kuwa yi Sa'a ƙofar a buɗe da sauri ta ƙari sa ciki ta jiyo motsin Lami a bayi, hakan ya sa ta yi wuff ta shige Ɗakin Auta domin muguntar ta kansa za'a fara kwanon tuwonsa ta gani a gefe da alama bai ci ba, murmushin ƙeta ta yi dan kuwa ta san yadda Auta ke muguwar son tuwo ba abin da zai hana shi cin tuwon nan ɗayan maganin dake aljihun ta ta ciro tare da barbaɗewa gaba ɗaya a cikin miyar tuwon Auta ta saka hannu ta juya cike da mugunta tana shirin miƙe wa taji alamun za'a shigo Ɗakin ai da mugun sauri ta ƙari sa bayan ƙofa tare da ɓuya, Auta ne ya shigo yana danna waya da alama chatting yake sai faman sakin murmushi yake yi, da sauri ganin ya juya baya Faɗime ta yi wuff ta fice daga Ɗakin, shi kuwa Auta zama ya yi tare da buɗe kwanon tuwonsa ya naga abin sa yana ci gaba da chatting ɗin sa hankali kwance.
Faɗime fitowa ta yi daga ɓangaren Inna Lami duk da bata gama da su ba amma zata fara komawa shashen sauran mutan gidan Matan yayyi da ƙannin mahaifinta duk ta yi musu abin da ta shirya dan ta rantse yau dai babu mai yin Bacci a gidan....
*FAƊIME...💋🌸💕*
_(Dangin Jinnu)_
©By Nainarh KD & Zahrah Royal Star
07
Inna Khande ce ta fito daga band'aki, Matar K'anin Malam ce, kamar ance ta waiga taga iniwara mutum tsaye a kanta.
Zaro ido waje tayi y'an cikinta suka hautsina, bata san lokacin data saki butar dake rik'e a hannunta ba.
Wata shegiyar dariya mai amsa kuwwwa Fad'ime ta kece da ita, wadda tasa Inna Khande idasa rud'ewa had'e da sakin wani marayan kuka.
Domin ta gefen idonta take ganin wata mace sanye da farar kaya sai ta zama fatalwace tsaye a gefen nata.
"Na shiga uku na lalace ni Khande, yau kuma miye nayi gamu dashi a tsakiyar daren nan?".
"hhhhhhh Inna Khande kike kowa?".
"It....ita...ita ce wallahi Khande nake".
Ta idasa maganar jikinta na d'aukar rawa kamar mazari.
"Dan girman Allah kumin rai wallahi tallahi ban san miye nayi maka ba kuyi hakuri ku kyale ni na tafi".
"Hhhhh yau gaba d'aya gidan nan sai kun gane shayima ruwa ne, ubanwa yasa a had'a munafurci daku ace za'ayi ma Fad'ime auran dole shine ku kuma munafikai, kukayi shuru to yau jikin kowa sai gaya masa mun rantse"
"Innallihi wa'inna alaihir raju'o..
Wani uban bugu da aka kaima bakinta ne yasa Khande datse salatin data d'akko. Dafe bakinta tayi da take jin lokaci d'aya ya haye yayi suntum, ga wani azababben zafi da yayi ma Kwakwalwar kanta dirar mikiya, wasu sabbin hawayen ne ya sake b'arke mata akan fuskarta.
Bata san lokacin data fasa k'ara had'e da rugawa da gudu ta shige d'akinta har tana bangaje k'ofar d'akin ta bada wani sauti karauuuuu.
"Innallihi wai Inna miye haka Kinga yadda kika fad'o d'akin nan kuwa?".
"Ke da'aAllah can rufe min baki ki.....
Dariya ce ta sarke ta tana nuna Inna Khande da hannu harda rik'e ciki.
"Bura'uban can, ni kike ma dariya Halima?, dan kund'in ubanki".
"Hhhh Inna baki ga yadda bakinki ya haye yayi suntum bane shi yasa, wallahi abun gwanin ban dariya fa, dan Allah Inna miya Koro ki haka ne daga zuwa bayi".
Sauk'e lumfashi kawai Inna Khande keyi tana kallon K'anwarta wacce yau suka zo bikin Fad'ime da ake shirin yinsa gobe.
"Na rantse da Allah Halima gamo nayi a hanyar band'aki".
"Gamo kuma Inna Khande?, ko dai kawai tsoro ne kika sama kanki, yanzu baka babu abunda kika gani".
Inna Khande zatai magana su duka suka fara jin wasu maganganu sama-sama had'e da ihu yana fitowa daga sansa na gidan.
Wata zufa ce ta yanke koma Inna Khande ba shiri ta ruga a guje tana matsawa sosai inda Halima take, itama tayi mutuwar tsaye.
K'ank'ame juna sukai suka cure waje d'aya.
Zaro ido Halima tayi tana duban Inna Khande a hankali kamar mai tsoron magana ta ce.
"Inna Khande mun shiga uku, dama gidanku nada aljanu ban sani ba?".
"Na rantse da Allah nima yau na fara ganinsu"
"Amma gaskiya kin cuceni Inna Khande miye yasa kika bari na taho bikinga baki gaya min, akwai Tanbotse a wanga gida naku ba na shiga uku nahh ni Halima".
Ta k'are maganar jikinta na d'aukar rawa domin wata iska suka ji tana busosu had'e da wani irin kuka irin na aljanu irin kamar kana cikin mak'abartar nan haka suke juyowa.
Wani mugun duka suka ji an kaima bayansu ba shiri suka saki juna suna sakin ihu.
Kamin su gama dawowa dai-dai suka ji an gwara kansu waje d'aya ji kake gummmmmm.
"Wayyo wayyo Allah na shiga uku kaina zai fashe".
Kusan a tare suka fad'i hakan.
A d'akin Inna Lami ma a kwance take sai nishari take kawai bata san hawa ba bata san sauka ba taji an zuba mata wani gigitaccan mari akan kumatunta.
Wani uban ihu ta saki had'e da tashi a haukace tana cewa.
"Na shige su ni jikar mutum hud'u, mafarki nake ne ko gaske wannan ne irin Mari ne haka aka d'auke ni dashi a cikin bacci?"
Duk maganar da take a rud'e take yinta, tana faman dube-dube, da kuma dafe a k'uncinta.
Saukar bulala taji a gadun bayanta wadda tasa ta d'auke numafashi had'e da wata irin gantsarewa, na azabar zafin da ya kewaye kwanyar kanta.
Ihun data saki ma ciki-ciki tsabar yadda bulalar nan taji ta.
Bata ga wadda ya zuba mata bulalar ba sai wata murya dake mata amsa kuwwwa a cikin kunnanta.
"Hhhhhh Lami wato ke muguwa ko?, kin zuga Malam yayima Fad'ime auran dole ko?, ai ko yau sai kin gwamce dama baki je kika had'u wannan tungun naki ba, daga yau bazaki sake marmarin shiga gonar god'iyarmu ba hhhhhhhh".
Dariyar da aka idasa maganar ce tasa Lami zubewa k'asa tana fashewa da wani kukan tausayi tana had'e hannunwanta waje d'aya murya na rawa take cewa.
"Dan girman Allah kumin rai na rantse da Allah ni banyi abun nan dan na musguna mata ba, ai gani na gata nayi mata kawai bawai bana sonta bane ai".
Wata bulalar aka sake zubama Inna Lami wacce tasa Lami sakin fisarin dole tana sake fashewa da kuka.
Abunda ya k'arasa Inna Lami rud'ewa kuwa shine d'agowar da zatai taga wata mace sanye da wasu kaya farare tass dogowa tsawonta har ya wuce misali ga bakinta dake zubar da wani irin jini bak'ik'k'rin dashi, kwarin idonta kuwa fari ne tass babu d'igon bak'in nan idonta cikinsu fari tass.
Wani uba-uban ihu Inna Lami ta saki tana furta.
"Wa'innahu sulemanu wa'innahu biss..... Bata idasa maganar da take son fad'a ba taga matar na nufo inda take haba wa, tuni Inna Lami ta zube a sume a wajan.
Wata dariyar aka kece da ita matar ta b'ace bat kamar ba'a tab'a wanzuwarta a wajan ba.
_______
Auta dake chatting d'insa sai murmushi yake hankali kwance. Wata zabura yayi yana sakin wayar dake hannunsa ya mik'e tsaye ba shiri jikinsa na d'aukar rawa.
A cikin wayar yana cikin chatting d'insa kawai a fuskar wayarsa yaga hoton Fad'ime tana masa wani mugun kallo na gargad'i.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.