Complete Hausa Novels

Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 4 of 17

“Mata ta! 'yata! Jama'a ku taimaka ‘yata da Matata suna ciki gini ya rushe da su.”

Ganin da gaske dai ƙoƙarin shiga ciki yake ne ya sa maƙocinsa Malam Idi ya yi saurin riƙo shi yana bashi haƙuri.

Ita kam Iya Lami tsabar baƙin ciki da ganin halin ruɗani da Malam Yahaya ya shiga ya sa ta dakata cak daga kukan munafurcin da take yi duk da ta wani bangaren zuciyarta fal domin tasan koba komai FAƊIME da Mahaifiyarta sun mutu sanadin wannan rushewar ginin da ita ce sila.

Curko curko kowa ya yi cike da alhini na wannan abu da ya faru sai da ƙyar ma wata ta sama zarafin faɗin.

“amma garin ya ya wannan lamari ya kasance?”

Ta kai maganar tana kallon Iya Lami da ta yi nisa Duniyar tunani a kan yadda zata ɓullo wa lamarin malam dan ta lura aikin baya ya fara sakin jikinsa dole yana buƙatar sabon aiki.

“ah eh uhm! E dama fa, dama...”

“dama me?”

Malam Idi Mijin Matar da ta yi tambayar ya katse Iya Lami da faÉ—in hakan sai kuma kallo gaba É—aya ya koma kanta, Iya Lami ganin asirinta yana shirin tonuwa ta yi saurin faÉ—in.

“dama daga maƙota nima na fito kwatsam naga gidan yana rushewa kuma FAD'IME da umman ta duk suna ciki....”

Ƙoƙarin zubewa ƙasa da Malam Yahaya ke yi ya sa ta kasa ƙari sa maganar ta yi saurin kamo shi tana kiran sunanshi.

Sosai jikin mutanen wurin ya yi sanyi ganin irin halin da malam yahaya ya shiga domin sambatu ya shiga yi faÉ—i yake.

“Allah Sarki Rayuwa shikenan kuma na rasaki Umman Fatima matar kirki duk irin cin kashin da nakeyi miki da wulaƙanci keda ‘yarki baki taɓa buɗe baki kin yi ƙorafi ba kullum cikin haƙuri kike dani gashi yau na rasa ku gaba ɗaya wayyo rayuwa kaico...”

“haba mana Malam me ya sa kake faɗin hakan ne ai wani sai ya ɗauka Mugun wuya kake bawa Umman FAƊIME ka gyara kalamanka dai”

Cewar Iya Lami tana zazzaro ido kamar wacce ta yi ma sarki ƙarya.

Malam Yahaya bai kulata ba sai ma miƙe wa daga zaunen da yake da ya yi tare da nufar hanyar gidan nasa da ya gama rushewa zuwa yanzu.

Yayin da wata cikin matar unguwa dake wurin ta katse Iya Lami da faÉ—in.

“ke dai Lami kiyi shiru kawai in ba so kike ayi 'yar tone-tone ba domin kam wuya dai Umman FAƊIME tana sha a hannunki dan ma Allah yayi ta mai haƙuri ne da kuma kauda kai shi ya sa kawai...”

Shiru kakeji Iya Lami bata tanka ta ba domin ji take tana ƙara magana asirinta ne zai tonu, a ka ce mara gaskiya ko'a ruwa gumi yake.....

Buguzun buguzun haka take tafiya irin nasu na tsofi har ta ƙari so Anguwan da 'yan kullin kayanta a hannu sai dai tun daga shigowarta layin take hango mutane tsai-tsaye bata gama mamaki ba ta hango har da ɗanta Yahaya tsaye a wurin ta buɗe baki da mamaki sai kawai ta hango saitin gidansa da ya zama fili sai bulon ginin da ya rushe ai ba shiri a tamanin ta ƙara sauri tana faɗin a bata hanya ta ga abin da yake faruwa da kyau ko dai makuwa ta yi ba gidan ɗan ta Yahaya ba ne.

“Iya kece anan kuma?”

Malam Yahaya ta tambaya murya sanyin ƙalau yana ƙoƙarin ƙari sawa wurin da Mahaifiyar nasa take.

“ni ce ɗan nan ka ganni da safen nan gajiya nayi ina so naga Takwarata mai sunan manya kwana biyu ana yi min rowarta shi ne nazo da kaina na ganta ka ganni harda tsaraba nayo ma ta ita da mahaifiyarta mai kyawun hali dana fuska ba irinsu oh oh ba, sai dai gashi na ƙari so gidan naga lissafin ya canza kamar na rikice a toh Fisabilillah ban da na rikice me zai sa na dinga ganin fili a wuri maimakon naga ginin gidan ka...”

Wani kuka ne ya taho ma Malam Yahaya jin kalaman da mahaifiyarsa ke yi sai ya daure amma ya rasa ta inda zai yi ma ta bayani domin bai san ta inda zai fara ba, ita kuma taƙi shiru sai tambayar abin da yake faruwa take.

Da ƙyar dai ya samu ya buɗe baki ya ce.

“Fatima da mahaifiyarta...”

Kasa ƙari sa maganar ya yi sakamakon hango FAƊIME da ya yi ta shigo layin a guje fuskarta ta yi futu futu da ƙasa da alama daga wasar ƙasa take sam bata lura da mutanen dake tsai-tsaye curko curko a wurin ba kai tsaye ta wuce wurin gidansu. Sai dai cak ta ja ta tsaya tana ƙare ma yadda gidan ya koma da kallo tashi ɗaya sai kawai ta fasa ihu tare da juyawa gadan-gadan ta nufa wurin da Iya Lami take tana gwarancinta tun kafin ta ƙari sa Malam Yahaya ya yi saurin riƙo ta ya haɗa da jikinsa yana sauke ajiyar zuciya da hamdala ga Allah na ganin ashe FAƊIME bata cikin gidan.

Sai lokacin ya sama zarafin yi ma Iya Fatuh bayanin abin da yake faruwa, ai kuwa ta yi matuƙar girgiza da jin wannan al'amari ta kuma fusata jin kalaman da matan unguwan ke yi na irin zaman haƙuri da Ummah takeyi a gidan kuma bata ƙara tabbatarwa ba sai ganin ƙiri-ƙiri FAƊIME taƙi zuwa wurin Malam Yahaya duk kuwa da yadda ya so, ai kuwa kunyar Duniyar nan da kuma dana sani ya cika shi.

Daga ƙarshe dai an samu an sama wasu sun fito da gawar mahaifiyar FAƊIME daga cikin gidan yayin da Iya Fatuh ta wuce da FAƊIME can gidan gado da take zaune da sauran iyalanta dama Malam Yahaya ne kawai yake gidansa daban dan bashi da ra'ayin zama a gidan gado sai dai sanadin wannan iftila'in da ya faɗa masa na rushewar gida da ba'a san mene ne sila ba ya sa ba shiri ya koma gidan gado shida Lami da sauran yaransa, a ranar a ka yi ma mahaifiyar FAƊIME sallah da komai a ka wuce da ita gidanta na gaskiya, yayin da kacokan raino da riƙon FAƊIME ya koma hannun Iya Fatuh dama taso tun ya ye a bata ita to Malam Yahaya ne yaƙi yarda yanzu kuma bashi da bakin musu haka Rayuwar ta ci gaba da gangarawa yayin da Malam Yahaya suke zaune a gidan gado da sauran dangi gefe guda kuma riƙon FAƊIME ya koma hannun Iya Fatuh gaba ɗaya dan ta rantse koda Aure malam yahaya ya ƙara to fa ba zata bashi FAƊIME ba bare kuma ace bai ƙara aure ba kuma ya yi zaton zata bawa Matarsa Lami Matar da batasan mutunci ba dan sam Lami da Iya Fatuh basa ga maciji tsakaninsu kuma hakan ya samo asali ne tun lokacin da Malam Yahaya zai Aure Lami ita Iya Fatuh bata so amma haka Malam Yahaya ya kafe dole a ka yi auren.

WANNAN KE NAN.

*Eleven years later*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.