Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 12 of 17
"Kai ko dai ba gani nayi ba sosai, ya za'ai naga aljanar yarinyar can a wayata, kai gizo kawai take min ai hakan bamai yiyuwa bane ma".
Hannunsa ya kai zai d'auki wayar yaga an zanye wayar daga inda take, an matsar da ita daga inda take.
Zaro ido waje Auta yayi nan take ya sake shiga wani yanayi tsananin rud'ani, had'e da wani masifaffen tsoro da ya mamaye masa zuciya da ruhi.
Curewa Auta yayi waje d'aya yana kallon wayar, koda gigi bai k'ara kai hannunsa domin tab'a wayar ba.
Gani yayi wayar na matso shi tana nufo inda yake, yanzu wayar a sama take, ita ba sama ba ita ba k'asa ba.
Matsawa ya rink'ayi tana matso shi haka suka rink'a yi yana zagaye d'akin.
Tun yana yi a hankali ya rink'a gudu a cikin d'akin, tun yana yi ta dad'in rai har ya fara gajiya, sai zufa ke yanko masa.
Wani gigitaccan mari aka d'auke Auta dashi ne yasa shi damtse bakinsa da k'arfi yana hana ihunsa fitowa fili.
K'ara d'aukesa akai da wani marin a d'ayan kuncinsa nanma da k'arfi ya rufe bakinsa da tafin hannunsa.
Ba abunda yake sai hawaye dake zubo masa.
Wata irin murya ce ta cika masa kunne wacce zai iya rantsuwa da Allah muryar nan zata iyasa ma mutum sumewa nan take tsabar rashin dad'inta da ban tsoro.
"Hhhhhhh Auta kayi kuskuren marin Fad'ime god'iyarmu, saida tayi maka gargad'in hakan, amma kai mai kunnan k'ashi baka ji ba ko? Sana harda kai ake bada shawarar aurar da Fad'ime ko?"
"Na rantse da girman Allah ni babu ruwa na a cikin auran da za'ama Fad'ime, wallahi Inna Lami ce ta fara kawo shawarar"
"Shine kai koma ka biye mata kuka zuga Malam ko?"
"Wallahi a'a hi.... Ni... Ni babu ruwa a cikin wannan abun, kuyima girman Allah ku kyale ni karku cutar dani".
Ya k'are maganar had'e da fashewa da kuka. Domin wata inuwa ya fara hangowa ta gefensa tana nufo inda yake tsaye jikinsa na sake d'aukar rawa..
_______________________
*SAL Estate, Shehu Shagari Way Abuja Nigeria*
Haj Saratu ce zaune tana kallon Firdausi dake zumin d'in had'a kayan abinci da za'a tarbi Young SAL.
Rawar kanta wajan SAL tayi yawa hakan yasa Haj Saratu ta kamo hannun Firdaus dake ba y'an aikin gidansu umarnin su gyara wajan sosai.
"Amma Miya faru?"
Cewar Firdaus.
"Ya kamata Firdaus ki rage yawan rawar kan nan da kike akan SAL d'in nan haka nan"
"Amma, bazaki gane bane ina bala'in son Young SAL"
Tab'e baki kawai Haj Saratu tayi tana sake kallon Firdaus zata sake magana suka ji shigowar Sudas K'ani ga Firdaus d'in, wadda su biyu ne a wajan Haj Saratun.
Kallonsa Haj Saratu tayi tana cewa.
"Kai kuma lafiya da shigowa ba sallama?".
"No Amma am sorry, naga motocin Young SAL ne sun shigo, kawai sai na tsaya har ya kama fitowa, abun mamaki kawai na gansa da wasu yara guda biyu, kamarsu d'aya da juna kamar y'an biyu, kuma wallahi Amma kamarsu d'aya da SAL, duk wadda ya gansu gaya jinin Young SAL na asali, tabbas kamar shine ya haife su".
Wata irin zabura had'e da mik'ewa tsaye Haj Saratu tayi, ba shiri. Firdaus kuwa da gudu ta fice harabar gidan domin gane ma idonta abunda Sudas ke fad'i.
"Sudas kana da hankali kuwa? Ya za'ai ya tafi shi d'aya k'asar waje kuma ace yau rana tsaka an ganshi tare da Yara har biyu, kuma masu kama dashi? Inahh koda Sudas baka gani sosai bane?".
"Na rantse da Allah Amma da gaske nake, zo ta bakin window ki gani".
Kamo hannunta yayi ya matsar da ita bakin window tana iya hango harabar estate d'in motoci ne jere sai kace wani d'and'an shugaban k'asar ne ya dawo.
Gaban Haj Saratu ne ya bada wani sauti dummmm dummm dummmm.
Sakamakon tozali da tayi da wasu y'an biyu mace da namiji sunsha kaya iri d'aya da SAL d'in, kamarsu dashi harta b'aci, kowa waye yaga wa'innan Yara tabbas nan take zai iya rantsuwa da Allah nashi ne na cikinsa.
Sauke wani irin huce Haj Saratu tayi tana dafe kanta dake take ji lokaci d'aya na sara mata.
Rik'eta sosai Sudas yayi yana d'an tab'e baki yana kallon window yadda SAL ke tafiya cike da izzarshi wacce ta riga da ta zame masa jiki.
Da kyar suka kai kujera Sudas yana kallon Amma a hankali ya ce.
"Nifa dama na tsani wancan Safiuddin d'in can, saboda Jiji da kansa yayi yawa, yana d'aukar kansa wani shege ni shi, ni kuma nake ganin duk matsayi d'aya muke".
Tashi tsaye Haj Saratu tayi tana cewa.
"Dole ne naji a ina ya samo wa'innan yaran, Allah yasa ba zargin da nake yi bane ya zama gaskiya, idan ko haka ne magauta na gidan nan namu zasu samu yi mana dariya, saboda akwai y'an matan family d'in nan dake tsananin sonshi, amma aka hanasu aka y'ata, itama kuma Saida na dage na mik'e tsaye har Alhaji Sa'id Ahmad Lamid'o ya yarda Young SAL ya auri Y'ata, dole ne na riga jin miye ya kawo wa'innan yaran a tare dashi".
Shuru Sudas yayi domin ya lura Amma tayi nisa tama manta da wadda take magana.
______________
"Kee koma miye kika sakko kina murmushi haka"
Kallon Mahaifiyarta tayi tana idasa sakkowa k'asa ta zauna a kusa da ita ta nuna mata wani photo dake cikin wayarta.
Zaro ido waje tayi ta mik'e tana cewa.
"Kee Asma ina kika samu wannan pic d'in, na SAL da wa'innan Yaran?".
"Hhhh Momy kenan ai tunda Alhaji ya ce ya zab'i Firdaus a matsayin matar SAL nake addu'ar Allah ya kawo abunda zai sama tarwatsa wannan had'in, sai gashi rana tsaka anga SAL ya dawo da Y'ay'anshi shegu daya je yayo cikinsu a k'asar waje, ya dawo da abun kunya a cikin Family"
Zama Momy tayi tana d'an jin wani abu a zuciyarta kamin ta ce.
"Ai tunda Haj Saratu ta tari gabana to tabbas itama tasan bazamu wanye lafiya ba, duk da tana matsayin Ƙanwar mijina, tasan abunda na dad'e ina burin Y'ata ta auri SAL shine tayi min d'aurin goro taje ta had'a mugun abu har Alhaji Sa'id ya amince yaba ɗan ɗansa Magajin dukiyarsa ita, hmmm lallai naji dad'in wannan labarin saura kuma mu tsaya jin miye zai biyo baya".......
*FAƊIME..💋🌸💕*
_(Dangin Jinnu)_
©By Nainarh KD & Zahrah Royal Star
08
Dawowarsa ke nan daga masallaci sallahr asuba har ya yi gaba sam bai lura da ita ba ganin haka ya sa ta ce.
“Baba!â€
Da sauri ya juya sai kuwa ya yi ido huÉ—u da FaÉ—ime tana tsaye har ta so ma ta ba shi tsoro, domin sam bai lura da ita ba.
“Fatima me kike yi anan?â€
Malam ya tambaya da mamaki.
FaÉ—ime tana shirin magana ta hango fitowar Auta daga banÉ—aki yana dafe bango cike da gajiya domin kwana ya yi yana zarya zuwa bayi.
Gimtse dariya Faɗime ta yi gudun kar Malam ya ɓaro jikinta shi kuwa Malam ganin inda take kallo ya sa shi mayar da dubansa zuwa wurin.
“Zubair! Lafiya kuwa kake riÆ™e bango kamar mai naÆ™uda?â€
“Ba..ba bakomai Baba dama gudawa nakeyi tsawon dare shi ya sa duk nabi na galaÉ“aitaâ€
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.