Complete Hausa Novels

Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 14 of 17

Prof Ridwan Matarsa ɗaya yaransu biyu rak, mace da namiji kuma suna zaune a ƙasar Faransa har wa yau kasancewarsa Ambassador.

Haka ma Eng. Khamis da Alhaji Tasi'u duk matansu É—aiÉ—ai kuma kowannensu Allah ya azurtashi da yara.
Sai kuma Alhaji Dauda Mijin Mommy matansa biyu Mommy ce ta biyu yayin da Hajiya Saima da ake kira da Ammiey ta kasance ta farko, Mommy yaranta biyu Asma da Fahat sai kuma Junaidiya da Sudais da kuma Firdaus yaran Ammiey.
Tsayawa ƙiyasa adadin familyn SAL ba abu ne mai sauƙi ba mu dai afka gadan-gadan cikin labarin a hankali za'a san kowa kuma halin kowa ya bayyana mu dai ci gaba da gashi kawai....🔥

*FAƊIME...💋🌸💕*
_(Dangin Jinnu)_

©By Nainarh KD & Zahrah Royal Star

*Dedicated to Salma Ahmad Isah (Candy)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*A love & Laugh story that will capture your heart and soul.*

09

*FAD'IME POV*

Inna Lami dake kallon Fad'ime shirye take domin yau aminiyarta Inna Zubaida ita ke dillancin kai Yara aikatau tunda sanyin asubahi tayi mata a gidan su Fad'ime. Jikin Inna Lami har yana rawa wajan zuwa k'ofar d'akin Inna Fatuh domin taso k'eyar Fad'ime su wuce.

"Wai nikam Lami wannan sammako haka tunda uwar safiyar nan, miye kike buk'ata ne?".

Fad'in Inna Fatuh tana kallon Lami data fad'o masu d'aki tunda uwar safiya.

Sosa k'ayarta Inna Lami tayi tana inina wajan fad'in.

"Uhum uhum....da...dama...dama ga wacce zata tafi da Fad'ime can ta zo domin tafiyar wuri take".

Wani kallon rashin gaskiya Inna Fatuh ke bin Lami dashi d'an tashi tayi tana kallon Fad'ime dake bacci hankalinta kwance ta b'ararraje akan gadon Inna Fatuh sai baccinta take.

"Wace irin tafiya ce haka tunda sanyin asubahi?, to gaskiya bada ni ba wallahi domin sanin kanki ne kin san ba'a tayar da Fad'ime idan tana wannan baccin nata, idan ko tsautsayi yasa ka tayar da ita wallahi kaine masha wuya".

Wani duba Inna Lami tayi ma Inna Fatuh a zuciyarta zai dannk'ara ma Inna Fatun zagi take, a fali kuma ta saki murmushin yak'e tana cewa.

"Haba Inna Fatuh ai ke babu abunda take miki idan kika tayar da ita d'in, kawai ki tada ta ko sun wuce kar waje ya k'ure, karma ta ce ta fasa kaita wajan aikatau d'in".

Inna Fatuh zatai magana Fad'ime ta saki hamma mai sauti had'e da wata mik'a ta bud'e idonta, domin tun d'azo take jin y'ar hayaniya a cikin d'akin, maganganun su ne suka tayar da ita.

D'an tashi tayi tana duban Inna Fatuh da Inna Lami dake tsaye a tsakiyar d'akin d'an sak'o k'afarta tayi k'asa tana duban Inna Lami ta kalli Inna Fatuh tana turo baki gaba ta ce.

"Inna Fatuh sai hayaniya kuke min har kun tayar dani, Fisbilillahi basai ku fita waje kuyi firar tak'u ba".

D'an murmushi Inna Lami ta saki tana maganar zuci.

"Kaji y'ar iskar yarinya, ai insha Allahu idan na samu kika tafi keda gidan nan har abada wallahi, domin ba wani aikatau d'in da zaki je inda za'a wargaza rayuwarki can zakije, ai dama nayi rantsuwa bazan tab'a bari ki zama wani abu ba Fad'ime, ba aljanu ba, ko kuka ce a kanki inda za'aje dake yau sai kin Gwammace kid'a da karatu, ke saima kinyi danasanin zuwanki duniya Dan........
Maganar da Inna Fatuh ke mata ce ta katse maganar zucin da take fad'a tana yi ma ta kallon Fad'ime tana jefanta da murmushi, mai cike da gugar zana.

"Wai ke Lami tunanin miye kike haka?, sai magana nake na jiki Shuru, sai kallon Fad'ime kike kina murmushi, shin wai ko dai akwai muguntar da kike k'ullawa ne?, nifa tun farko ban yarda dake ba dama".
Fad'in Inna Fatuh tana k'arema Inna Lami wani kallon tuhuma sosai.

Cike da d'an firgice ta maze tana cewa da sauri

"Haba Inna Fatuh ki daina min irin haka mana, miye zan k'ullama Fad'ime ne, da duk da banyi mata mugunta ba sai yanzu kuma".

Tab'e baki Inna Fatuh tayi tana cewa

"Yo waye ya sani abu a duhu, kuma ai waye bai sanki ba da can baya, idan banda ido na, da bana raye Allah kad'ai yasan abunda zaki yima wannan marainiyar Allahn ai wallahi ke kima yi istigfari Lami waye bai san baki k'aunar Fad'ime ba"

A fakaice Inna Lami ke hararar Inna Fatuh dake maganar.

Fad'ime ta saki wani murmushin gefen baki tana duban Inna Lami ta ce.

"Nifa Inna Fatuh nama fasa tafiyar nan wallahi, domin wani mafarki nayi akanta, dan haka bazanje ba".

Baki a bud'e hankali a tashe kuma Inna Lami ke saurin fad'in, sai dai tun kamin ta fad'i abunda ke cin ranta, Inna Fatuh ta tari hanzarinta.

Da fad'in "shikenan falin lahil amdu, ai ni dama can ban wani ji tafiyar nan a raina ba, saboda nasan bak'in hali irin na Lami, tana iya kai ki inda za'a datse lumfashinki".

Baki na rawa Inna Lami ke fad'in.

"Haba Fad'ime wai kuwa kin san irin gidan da za'a kaiki kike fad'in baki zuwa, gida ne irin na y'an gayu mai bene sama da k'asa, gashi har makaranta za'a sakaki, kiyi kallon abubuwan duniya, amma kina zaune a k'auyen nan miye zaki sani a duniyar nan, da abunda ke cikinta, koni nan da dai basa son Manya ai ni ce zanje bake ba wallahi, ki dai yi shawara Fad'ime kar ayi tafiyar nan babu ke".

D'an shuru Fad'ime tayi, tana tunani, hak'ik'a tana son birni ita mayiyar son zuwa cikin birni ce, da son ganin abunda ke cikin birnin, to amma kafin tashinta tayi wani mafarki wata mata tazo mata tana jaddada mata cewa karta sake ta yarda da tafiyar da Inna Lami take ta matsawa tayi, tana gama fad'a mata haka ta b'ace shine ita kuma ta farka kawai ta iske Inna Lami a cikin d'akin, suna magana akan tafiyar da aka gama gargad'inta da kar taje a cikin baccinta.

Inna Lami dake kallon Fad'ime tana d'an murmushi ganin maganar tada fad'a mata kamar tayi tasiri a cikin ranta, domin ganin yadda ta fad'a duniyar tunanin.

"Uhuhmm kuma fa hakane Inna Lami tabbas ina son ganin yaya birni yake, domin idan na dawo naba K'awaye na labari, domin garin nan mutane d'ai-d'ai ne ke zuwa birni".

Fad'in Fad'ime tana duban Inna Lami dake murmushi sosai a yanzu.

"Yawwa ashe kin gane, kuma idan kece kika fara zuwa birnin nan kamin su, ai kin wuce da ajinsu nesa bama kusa ba, zaki dawo y'ar gayu a k'auyen nan namu, ki dawo kinfi kowa iya d'aukar wanka".

Dariya Fad'ime ta saki tana sakkowa ta kalli Inna Fatuh data saki baki da hanci tana duban Inna Lami dake murmushi kamar ta Allah.

"Inna Fatuh ki had'a min kayana zanje birnin aikatau d'in yanzu".

Rik'e baki Inna Fatuh tayi ta dafa kafad'ar Fad'ime tana ji gabanta na d'an fad'uwa da tafiyar Fad'imen, domin Allah ya sani har cikin ranta bata aminta da tafiyar ba, bata kwanta mata a rai ba.

"Fad'ime miye ya canza miki tunanin a d'an k'ank'anin lokaci haka?, ke nan yanzu har Lami zata gaya miki magana ki yarda lokaci d'aya, har tayi sanadiyar canza tunaninki a d'an lokaci haka?".

Turo baki Fad'ime tayi tana ji itafa Allah wallahi saita je birnin nan, domin Inna Lami ta gama saka mata rai da abubuwan k'aryar data shinfid'a mata.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.