Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 3 of 17
Lami ta kamasa tana faman jijjigasa tana tabbayar miye ya sameshi miye yake masa ciwo duk ta rud'e ta fita hayaccinta. Ganin Umma na neman b'atasa yasa Lami a haukace muryarta har tana shak'ewa ta dubi inda Umma take ta d'aga mata hannu tana cewa.
"Karki sake ki tab'a min d'ana karki sake ki k'araso inda muke. Kuma wallahi komi ya sami Yaro na to wallahi wannan y'ar iskar yarinyar taki ce sila domin naga ana tab'a ta aljanunta ke d'aukar mataki to ni dai nafi k'arfinsu nan gani nan bari, yo waye ma yasan k'ila aljana kika haifa ba mutum ba ce".
Wata dariya Lami taji an b'ab'b'ake da ita a zabure ta kai dubanta wajan Fad'ime inda take jiyo dariyar, wani zaro ido tayi waje tana kallon yadda yarinyar ke kallonta tana mata dariya harda tab'a hannu.
Sakin Auta tayi tana murza idonta da k'arfi ta bud'e again dai dariyar take mata had'e da gwalo ma take gani.
"Innallihi wa'inna alaihir raju'on na shiga uku na, Wallahi Malam an haifar maka masifa a cikin gida, wallahi wannan d'iyar taki masifa ce a cikin jama'a"
Umma ta waiga inda Lami ke kallon ita dai D'iyarta ta gani zaune hasalima wasanta take irin na Yara.
Tsaye tayi kawai tana kallon ikon Allah.
Zuwa can Malam ya fad'u gidan kamar wadda akai ma kiranye.
Shima a rud'e kamar wadda akace ma Auta ya mutu ya nufi inda yake.
Ai Lami na ganin Malam ya shigo ta fashe da kukan munafurci tana cewa.
"Ni dai wallahi Malam na gaji, na gaji wallahi gara na bar maka gidanka dana zauna bak'in cikin matarka ya kashe ni, ita da aljanar yarinyar can tata, Fisbilillahi yanzu nan suna wasa da Auta yarinyar nan kawai mukaji Auta ya fad'i yana shure-shure, kuma na rantse da Allah ita ce tayi masa wani uban, dan haka wallahi idan Yaro na bai dawo yadda yake ba, na rantse da tsarkin mulkin Allah yau koto ce zata rabani dake wallahi".
Lami ta k'are maganar tana kallon Umma data daskare waje d'aya.
Gani tayi Malam ya mik'e ya nufi inda Fad'ime take kawai sai dai taji saukar k'arar Mari, ba shiri ta zabura ta nufi inda Malam yake ganin yadda ya Mari y'ar yarinyar da bata san miye duniyar take ciki bama.
Ido a waje Umma ta warce yarinyarta tana shafa fuskarta yarinyar ko tari batai ba bare tayi kukan Marin da Malam d'in yayi mata, hasali ma dariyarta take masa tana wangale masa bakinta wadda ba hak'ora cikinsa.
Shi kansa Malam d'in mamakin yarinyar ya fara kashe zuwa yanzu, kwata-kwata ji yake ba wadda ya tsana irin uwar d'iyar nan da ita kanta yarinyar.
Umma cike da tsananin mamakin Malam d'in a kullum da yake k'ara kashe mata jiki ta ce
"Malam yanzu dana barka saika ci gaba da dukan wannan y'ar yarinyar?, da bata san miye ma take yi ba, yanzu komai aka fad'a maka sai kawai ka hau sama ka zauna ka yarda, miye wannan yarinyar zatai ma Auta Fisbilillahi kawai saboda anga ina hakuri kuma bana magana, kai kuma baka son gaskiya yanzu sa.......
Tasssss
Rauntse idonta tayi da k'arfi had'e da dafe k'uncinta, bata san hawa ba bata san sauka ba kawai taji an d'auke ta da Mari, Abun bai sake bata mamaki sai da taga ashe Malam ne da wannan aiki yana tsaye kanta sai huce yake kamar wani Zaki kamar ace masa takk ya rufeta da duka gaba d'aya.
Lami tana daga gafe sai sakin dariya take had'e da jin dad'in yadda yanzu ta gama malke Malam gaba d'aya sai abunda ta ce shine yake yi, idan aka tab'a ta da ita da yaranta kuwa yi yake kamar ya yanka mutum tsabar yadda yake mugun tsoronta a yanzu.
Wasu zafafan hawaye ne suka shiga zarya akan fuskar Umma ba abunda take sai kallon Malam. Tunda take dashi bai tab'a daga hannunsa da sunan ya dake ta, sai a yanzu duk da tsawon shekarun nan taga abubuwa na wulakanci daga garesa da Matarsa Lami wacce abun ya samo asali ne tun washe garin da aka haifi Fatima, Lami ta fita ita ce bata dawo ba sai wajan dare kuma tunda ta dawo Umma taji gabanta na fad'uwa sosai saboda ganin yadda Lami ke sakar mata wani irin murmushi mai kamar gugar zana.
Tun wannan lokacin shikenan zaman lafiya da jin dad'i ya k'are ma Umma da ita da abunda ta haifa yau bak'i gobe fari. Gashi gaba d'aya Yaran Iya Lami sun raina Umma rashin kunya babu wacce bata gani bare Auta yafi kowa iya rashin kunya sai ya gaya mata maganar da ko a mafarki bazaka ce shine yayita ba, garama sauran su sun zama manya ba wani zama gidan suke ba sosai.
"Malam......
"Kimin shuru, ki sauk'e d'iyar nan taki ta warware abunda tayima Auta idan ba haka ba ranki daga ke har ita sai yayi mummunan b'aci wallahi"
Nuna kanta take Umma tana kiran.
"Malam yanzu miye wannan yarinyar zata yi ma Auta, duk fa wannan abun canfi ne fa ni yarinyata mutum ce kamar kowa bata da wani abu wallahi".
Ganin Auta ya mik'e sai raba ido yake yasa Lami rungumesa tana kallon Umma ta mik'e dashi rik'e a jikinta tana cewa.
"Barta Malam sa'arta d'aya D'ana ya mik'e, bance kuma ka sake ta ba har sai lokacin dana ga damar ta bar min cikin gidana daga ni sai Yara na, ai tunda kika ce zakiyi kishi da Lami shige ka fasa wallahi".
Ko a jikin Malam kamar wadda ake ba umarni haka ya fara gyad'a ma Lami kai sai ka ce wani Yaronta wadda ta haifa da cikinta.
Ta sake kallonsa tana cewa.
"Muje ciki Malam"
Sumi-sumi ya bi bayanta suka shige d'akin Lamin Umma na tsaye tana kallon ikon Allah.
A hankali taji ana share mata hawaye, k'aro ma d'iyar tata ido tayi tana mamakin yarinyar indai zata ga tana kuka to tabbas ita ce zaka sameta tana share mata hawayen dake zubo mata, wayonta bai kai tasan hakan ba, kallonta take tana so ta gano miye yasa Mutane ke mata kallon wacce ba mutum ba, bare su Iya Lami dake hurara abun a wajan mutane suna muzanta mata yarinya. Wani irin taji a jikinta tana jin tausayin yarinyar tata a yau d'in, haka nan taji a jikinta ba lallai suyi rayuwa mai tsawo da yarinyarta, wani irin tsananin tausayin d'iyarta ne ya rufeta, ya rayuwarta zata kasance idan bata nan?, miye zai faru da ita idan bata gidan Mahaifinta?, tana gidan ma ya aka k'are inaga kuma ace bata nan babu idonta a cikin gidan...........
*FAƊIME...💋🌸💕*
_(Dangin Jinnu)_
©By Nainarh KD & Zahrah Royal Star
*Dedicated to Salma Ahmad Isah (Candy)*
*بسم الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…*
*A love & Laugh story that will capture your heart and soul.*
03
*One week later.*
“Innallihi wa'inna alaihir raju'on, jama'a ku kawo É—auki gini ya danne Umman FaÉ—ime da ita kanta FaÉ—imen ku kawo agaji jama'a!â€
Iya Lami ce ke wannan kururuwar ta ɗaura hannu a ka cikin tashin hankali yayin da take tsaye gaban gidan Malam Yahaya dake ta faman rushewa yadda ka san an kasa motar rushe gini ana rusawa haka ginin gidan ta ko'ina yake ci gaba da rushewa yayin da Iya Lami take ci gaba da kururuwar neman taimako, ai kuwa lokaci ƙanƙani jama'a suka cika ƙofar gidan kowa yana tambayar abin da yake faruwa, ita kam Iya Lami ta ruɗe ba abin da take iya faɗa fa ce a kawo ɗauki gini ya rufe FAƊIME da mahaifiyarta, ai kuwa hankali tashe jama'a suka fara neman yadda za'a ɓullo ma lamarin kar a rasa rai biyu ana cikin haka sai ga Malam Yahaya ya dawo hankali tashe domin labari ya kai masa ai kuwa da ƙari sowarsa bai kula Iya Lami dake ƙoƙarin yi masa bayanin yadda al'amarin ya kasance ba, gadan-gadan ya nufa cikin gidan da ya gama rushewa faɗi yake.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.