Complete Hausa Novels

Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 2 of 17

“mene ne kikaga Jaririyar ta yi?”

Iya Suwai ta tambaya da mamaki.

Muƙut Lami ta haɗiye yawu don ta tabbatar ita kaɗai ke ganin wannan tashin hankali.

Cikin sanyin jiki dana murya ta furta. “ah ba komai ai batayi komai ba kawai dai na tambaya ne?”

Ta faɗa tana ƙoƙarin miƙa ma iya Suwai Jaririyar.

Takaici ya sa Iya Suwai ta girgiza kai tana faɗin. “kema dai Lami halin ki saike wasu lokutan sai kike abu kamar mai shafan jinnu ina ce ɗazun kika gama roƙona a kan ke zakiyi ma Jaririyar wanka shi ne yanzu kuma kike miƙomin ita...”

“zakiga shafan aljanu ganin idonki lokacin da kika karɓe wannan dangin Jinnun daga hannuna ai.”

Lami ta faɗa ƙasa ƙasa lokacin da ta samu Iya Suwai ta karɓi Jaririyar bayan ta gama sababi.

Cikin ƙanƙanin lokaci a ka gama shirya mai jego da jaririyarta yayin da Lami da Iya Suwai suka gyara Ɗakin tsaf a lokacin kuma dangi da maƙota suka fara cika gidan cike da murnar samun ƙaruwa da Malam Yahayah ya yi kuma cikin amincewar Ubangiji a ka sama ɗiya Mace a abin da ya daɗe yana nema ke nan domin duka ya'yan Lami maza ne su uku, sai wannan karon da Ummah ta haifo masa Mace ga jaririyar jajur da ita tayo mahaifiyarta a haske yayin da kamanni tas ta kwaso na Mahaifinta malam Yahayah ai kuwa zo kuga rawar ƙafa wurin Malam Yahaya abin dai ba kama ƙafar yaro, yayin da gefe guda tsaban baƙin ciki da takaici ya taru ya yi ma Lami cunkus a zuciya, ga wannan ɗan banzan kyau da Jaririyar take da kamar wata ƴar larabawa ga kuma baƙin ciki na rawar ƙafar da Malam Yahaya yake yi sai kace ba'a taɓa yi masa haihuwa ba, gefe guda ga alhinin yadda zata sama Malam Kasan komai da wannan mummunar labari na kwaɓewar aiki da kuma abin da ya fara biyo baya a Ranar dai bata samu ta bar gidan zuwa wurin Malam kasan komai ba saboda mutane masu ganin mai haihuwa da jaririya da suka dingi shigowa haka ma washe gari ayyuka suka taru suka yi ma ta yawa a taƙaice dai har Ranar suna Lami bata samu ta fita zuwa wurin Malam kasan komai ba duk kuwa da yadda taso sai dai inda ta gode Allah shi ne tun daga wancan Ranar Jaririyar bata ƙarayi ma ta wani abu da zai firgita ta ba hakan ne ya ɗan kwantar ma ta da hankali amma kaɗan.

Jaririya taci sunan mahaifiyar Malam Yahaya wato Fatima hakan kuma ba ƙaramin ƙauna yaja ma ta ba a cikin dangin da ma wurin ita kanta Mahaifiyar Malam Yahaya wato Iya Fatuh yayin da hakan ya ƙara wutar ƙiyayyar wannan Jaririya a zuciyar Lami domin taci burin Malam ya sakama Yarinyar da zata haifa wannan suna sai dai hakan bai faru ba sakamakon bata taɓa haihuwar mace ba.

A taƙaice dai a Ranar sunan Lami ta samu ta faki ido ta bar gidan zuwa wurin Malam kasan komai domin neman mafita na wannan al'amari domin so take daga Jaririyar har uwan nata duka su baƙunci halira.

Sai dai sosai jikinta ya yi sanyi lagwas lokacin da ta ƙari sa wurin Malam kasan komai tun kafin ta sanar da shi abin da ya faru ya rufe ta da masifa kamar zai cinye ta ɗanye sakamakon kuskuren da ta tafka ya kuma tabbatar ma ta ba shi ba koda wurin wani Malamin tsubbu ko boka zataje to fa ba mai iya kashe ma ta wannan Jaririya Muddun ba Allah ne ya so hakan ta kasance ba.
Sai dai duk da haka bata karaya ba ta buƙaci a yi aikin da zai sa Malam ya dena bawa uwan da Jaririyar kulawar da yake basu a saka yaji duk Duniyar nan babu waɗan da ya tsana kuma bai san gani fa ce Ummah da ƴarta. Anan ne kuma Kasan komai ya tabbatar ma ta da aiki zai yiwuwa muddun zatayi biya mai kyau kuma ta cike da wasu matakai, ba musu ya yarje masa a taƙaice dai kafin ta bar wurinsa sai da suka yi abin da suka saba muddun ta kai masa ziyara to fa sai sun kusanci juna....

_______
________
_______

TO FA! ANA DARA GA DARE YA YI. GA DAI DA YADDA LABARIN NAMU MAI TAKEN FAÆŠIME (DANGIN JINNU) YA FARA. YA KUKE GANIN ZATA KASANCE? TO MU DAI HAÆŠU A FEJI NA GABA, KAR A MANTA DA YIN LIKE, SHARE FISABILILLAH

ZAHRAH ROYAL STAR CE TARE DA NAINARH KD SUKA TSARA KUMA SUKA RUBUTA ✍️🤍

*FAƊIME...💋🌸💕*
_(Dangin Jinnu)_

©By Nainarh KD & Zahrah Royal Star

*Dedicated to Salma Ahmad Isah (Candy)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*A love & Laugh story that will capture your heart and soul.*

02

*ƘAUYEN KINKIBA, KADUNA STATE.*

*GIDAN MALAM YAHAYA*

*Five Years later*

"Haba Auta miye Fad'ime tayi maka ne da zaka kai mata wannan dukan haka, ai K'anwarka ce".

Cewar Umma ta k'are maganar tana jawo Fad'ime dake zaune a k'asa tana wasan k'asa irin na yara duk da dukan da Auta ya kai mata batai kuka ba bare tari sai ma wasan data ci gaba tana kallonsu da idanuwanta masu haske cikinsu kamar na mage.

"Baki ga miye tamin bane?, nifa na tsaneta bana sonta haka kawai duk ta zo tafi y'an gidanmu kyau k'ila ma ba y'ar gidanmu ba ce can akaje a ka samo mana ita a ka k'ak'ubama Abbanmu ita"

"Kaii Auta ubanwa ya gaya maka wannan maganar"

Umma ta idasa maganar tana neman kai masa mari a fuska. Wuffff Lami ta fito daga d'aki har zanin dake d'aure a k'ugunta na neman kwancewa tsabar masifa har bakinta na kunfa wajan cewa.

"Lahhh karki kuskura ki ce zaki tab'a min Yaro, bamu kwashi y'an kallo dake ba yanzun nan ehee"

"Amma Iya Lami kina jin abunda yake fad'a min, kuma kin san hakan bai dace ba ina a matsayin matar ubans......

Lami ta katseta da hanzari tana cewa

"Kee kinga bana son jin soki burutsinki. Kuma ai Yaro gaskiya ya fad'a duk cikin dangin Malam babu mai kyan wannan d'iyar taki mai kama da Iskokai ai Yaro ya fad'i gaskiya yo wa ya sani ma ko cikinta akaje aka yo daga waje aka zo aka k'ak'uba Malam shi"

Umma tayi shuru tana jin zuciyarta na zafi sosai bata san sadda hawaye suka cika mata ido ba. Batai aune ba taga Fad'ime ta gangaro har inda take tana tab'a mata k'afa, jiki a sanyaye tasa hannu ta d'auki d'iyarta, ga mamakinta sai taga Yarinyar tasa hannunta tana d'an share mata hawayen dake mata zuba.

Wani dogon tsaki Lami ta saki tana juya ga Auta ta dafasa tana cewa.

"Kai da'aAllah rabu da ita je abunka ka ci gaba da wasanka, naga ubanda ya isa ya hanaka watayawa a cikin gidan ubanka".

Umma bata sake cewa komai ba kusan a tare zasu juya domin barin wajan Auta dake wasa kawai suja ji ya fasa wata gigitacciyar k'ara ya fad'i a k'asa yana shure-shure.

Habawa ai a haukace Lami tayo kansa Umma ma ta aje Fad'ime a k'asa tana yo wajan.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.