Complete Hausa Novels

Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 16 of 17

*FAD'IME POV.*

A hankali take motsa manyan idanunta da take jin sun yi ma ta wani irin nauyi, tarr! Ta ware su tana kallon saman ceiling na saitin da take kwance. Lokaci ɗaya abin da ya faru ya fara dawo ma ta ƙwaƙwalwa. Ta zazzaro ido tana ƙoƙarin tashi miƙe a razane sai dai ji da ta yi ta kasa ya sa ta yi saurin kallon jikinta zaro ido ta sake yi ganin ba kayan da ta baro ƙauye da su ne a jikinta ba, wannan wata doguwar riga ce ta yadi kamar irinta ta asibiti sai dai wannan launin baƙi mai ratsi-ratsin ja ne, ga ƙafafunta ɗaure da wata kakkaurar igiya hannunta ma haka, tashin hankalinta ya ƙaru fahimtar abin da ke shirin faru da ita duk a tunaninta ma sace ta a ka yi hakan ya sa ta daddage iya kar ƙarfinta ta kwala ihu wanda ba iya Ɗakin ba gaba ɗaya duka gidan ma sai da ya amsa, ihu take zubawa wai don ko wani zai kawo ma ta a gaji sai dai har ta gaji bata ga kowa ba, maganar da taji ta gefanta ne ya sa ta ɗan juya a razane, ai kuwa idanunta suka yi kyakkyawan gani da santalelan kan Budurwar dake a aske irin rigar jikin Fad'ime shi ne a jikinta ta saka hannu ta toshe kunnenta sakamakon ihun Fad'ime.
Shiru Fad'ime ta yi tana ƙare ma Budurwar kallo duk da ga halin da take ciki amma sai da dariya ta kwace ma ta lokacin da wannan Budurwar ta ɗa go fuskarta ashe ba iya gashin kanta ba hatta da gashin girarta ma ba'a kyale ba, sai da Fad'ime ta yi dariya san ranta sannan ta tsagaita tana duban Budurwar da ta zuba ma ta idanu ba tare da ta ce ma ta ƙala ba duk da tasan da ita take wa dariyar.

“Wai Dan Allah Baiwar Allah na tambayeki ya a ka yi kika koma haka ne kin ganni ki kuwa caɓɗi-jan sai kace Sule almajiri wai ma ina ne nan wurin?”
Fad'ime ta ƙare maganar tana ƙare ma Ɗakin kallo. Tare da ƙoƙarin kwance ɗaurin da a ka yi ma ta.

‘lallai yarinya baki da hankali wato ma baki san ina ne nan ba sai dai nayi miki uzuri dan da gani daga ƙauye kike'
Budurwar ta raya hakan a ranta, kafin a fili ta furta.
“Gidan ƴan yankan kai ne”
Ta faɗa a taƙaice tare da yin tsitt.

Lokaci ɗaya wutar Fad'ime ta ɗauke na ƴan daƙiƙu kafin ta duba Budurwar cikin tsananin tsoro da zaro ido ta furta.

“Gidan ƴan yankan kai dai? Kamar fa haka kika faɗa wai kuma da gaske kike?”

“ni abokiyar wasar ki ce da zan yi miki wasa?”
Budurwar ta faÉ—a cikin gatse a zuciyarta kuma tana dariyar ganin yadda Fad'ime ta koma lokaci guda daga jin an ambaci gidan yankan kai.

“wayyo Allahna wayyo Inna Fatuh wayyo ni Fad'ime tawa ta sameni”
Fad'ime ta dage ta fashe da kuka tana faɗin hakan kuma bata dena ƙare ma Ɗakin kallo ba da babu uwar komai ciki domin hatta su a saman tayar tiles suke.

Banko ƙofar a ka yi a fusace wani jibgegen mutumi ya shigo yana zazzare ido ya duba Fad'ime da bata dena kuka ba ya ce.
“idan baki rufemin wannan wawwaran bakin ba sai na ƙari so wurin na yankaki na kaima dodo”

Yadda kasan an yi ruwa an É—auke haka Fad'ime ta yi tsitt da jin kalamansa.
Ya kyaɗa kai ganin barazanarsa ta yi aiki ya juya domin komawa ya ci gaba aikinsa na tsaro, sai dai ji ya yi Fad'ime ta ƙara fashewa da wani kukan da ya fi na baya tana kiran sunan Inna Fatuh. A mugun fusace ya juyo domin ya ƙari sa ko kifa ma ta mari ne ya yi kota dawo hayyacinta sai dai juyowar da zai yi ya ganta tsaye a gabansa kamar wata aljana, gabansa ne ya yi wani irin mummunar bugawa ganin yadda idanunta suka sauya kala jin ƙarar abu na ɗiga ya sa ya yi saurin kallon ƙasar wai ashe fitsari ne ya suɓuce ya fito masa dan tsabar tsoro ɗagowar da zai yi ya sake dubanta Fad'ime ta shammace shi ta hanyar kai masa wani rikitaccen naushi a tsakiyar kansa domin sai da ta wani daka tsalle kamar yar wasan ƙwallon kwando dake shirin jefa kwallo.
Take a wurin ya zube ƙasa sumamme.
Juyawa Fad'ime ta yi tana dariya ta duba Budurwar data miƙe tsaye tana bin ta da kallon tsoro cikin rawar murya Budurwar ta furta.
“wa..wace ce ke? Kuma me kike shirin aika tawa?”
Fad'ime ta yi dariya sannan ta ce.
“Fad'ime suna na kuma ni Mutum ce sai dai a ƙauyenmu anai mini laƙabi da DANGIN JINNU, kefa mene ne sunanki?”

“Jiddarh”

Cewar Budurwar cikin sanyin murya.

Fad'ime tana shirin magana taji muryar wancan Matar ta mafarkinta a gefenta da sauri ta juya ai kuwa taga matar tsaye a gefanta tana faÉ—in.

“ki gudu muddun kinaso ki tsira da ranki ni zan taimaka miki ki kuɓuta daga sharrin wannan gidan”

Da mamaki Fad'ime ta ce. “wacece ke kuma me ya sa kikeson taimaka min?”

“zan faɗa miki amma ba yanzu ba kedai ki yi sauri tun kafin su cim miki ki bar gidan nan.”

Shiru Fad'ime ta yi tana nazari duk da gefe guda na zuciyarta tsoro ne fall musamman dataji ance gidan nan na Æ´an yankan kai ne, amma kuma tana tsoron ta yarda da wannan matar ita kuma ta cutar da ita.

Ido kawai Jiddarh ta zuba ma Fad'ime tana bin ta da kallon tsoro ganin yadda take magana ita É—aya sai dai batajin abin da take faÉ—a.

“na amince zan biki domin ki fitar dani daga gidan nan sai dai da sharaɗin zaki sanar dani wacece ke”

Cewar Fad'ime ba musu Matar ta ce ta amince.

Kallon Jiddarh da tsoro ya cika ta Fad'ime ta yi sannan ta ce.

“in kinga zaki biyo ni mu gudu a tare tohm, in kuma kinga zaki tsaya har zuwa lokacin da za'a raba kanki da gangar jikinki ne sai dai nace miki bissalam”

Shiru Jiddarh ta yi tana nazari ba so ɗaya ba kuma ba biyu ba ta sha ƙoƙarin guduwa daga gidan amma ana kamota wani lokacin ma sai ta sha tafiya sosai sai ta fahimci wuri ɗaya kawai take zagayewa wato bakin kogon, gashi gobe ne kwananta zai ƙare a gidan shi ya sa a ka aske ma ta gashin ta domin gobe ne za'a sadaukar wa da dodo jininta.

Ganin Fad'ime tana shirin fita daga Ɗakin ya sa ta yi saurin bin bayanta cikin ƙasa da murya take faɗin.

“ki fa yi a hankali domin Akwai hatsari abin da kike shirin aikatawa.”

“muke shirin aikatawa dai tun da gaki kin biyoni”

Cewar Fad'ime tana dariya shiru Jiddarh ta yi da yake tasan hanya ita take nuna ma Fad'ime inda za su bi kuma sai ya zama na duk inda ta faɗa ya yi daidai da inda wannan matar take nuna wa Fad'ime sun yi tafiya mai nisa sosai cikin gida kuma Allah ya taimaka ba wanda ya gansu, Fad'ime ta yi mamakin irin shegen girman da gidan keda ga wani irin malkwataɗaɗɗen gini da ta rasa gane kansa ita har ta fara gajiya da tafiyar ma suka ƙari sa wani ƙaton fili na gidan da suna iya hango makeken gate ɗin sai kace na wata Masarautar mai shegen girma. Sai dai me zai faru?
Wata iriyar Mahaukaciyar dariya suka ji an kece da ita kuma ba Muryar Mutum guda ba ne da alama na mutane da yawa ne. Cak! Suka dakata zuciyoyinsu na bugun lugude Fad'ime da Jiddarh suka cure wuri guda jin dariyar bata ƙarau ba ce.
Ai kuwa take mutane da maza da mata suka fara bayyana a wurin suna zagaye su Fad'ime da hakan ya da É—a, É—aga hankalin su Fad'ime. Mutanen sanye suke cikin wasu jajaye da bakaken dogayen riguna wurin su goma sha ne mafi yawa daga cikinsu jajayen doyayen riguna zumbula zumbula ne a jikinsu ga wata uwar hula dake jikin rigar da suka rufe fuskokinsu da shi.
Cikin Wata kalar murya mai cike da amo su Fad'ime suka ji an fara faÉ—in.
“wato kune tauraƙaƙu ko muna tsaka da shagalin bikin shekararmu goma sha biyar da kafuwa shi ne kuke ƙoƙarin guduwa ai kuwa kun tafka Babban kuskure domin a yau ba sai gobe ba zaku sama hukunci na daidai da abin da kuka aikata a yau jininku zamu sadaukar da shi ga dodon tsafi.”
Bayan muryar mai amon ta gama wannan bayani duka mutanen suka sake fashewa da dariya kafin su fara karanto wasu latsumai.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.