Complete Hausa Novels

Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 10 of 17

Dariya FaÉ—ime ta É—an yi sannan ta kallesu gaba É—aya ta ce.

“a tunaninku zan bari hakan ta faru ne? Ai ba zata taɓa saɓuwa ba Bindiga a ruwa...”

“to yanzu mene ne abin yi?”

Laure ta faÉ—a cike da damuwa.

“ai tuni na samo mana mafita, ku matso kuji.”

Cewar Faɗime tana sakin dariya ba musu suka ƙari sa ƙasa-ƙasa ta sanar da su shirin da ta ratsa ai kuwa a tare suka saki murmushi cike da farin ciki Faɗime ta ce.

“kun ga dama yazo mana a daidai ke nan ko?”

Gaba ɗaya suka ce E, Laure ta ƙara da faɗin. “lallai Faɗime ƙwaƙwalwarki na ja.”
“hhhh to an faɗa miki ni ɗin jahila ce, ku ƙara matsowa ma kuji wani abu...”

FaÉ—ime ta faÉ—a cike da fariya sannan ta ci gaba da sanar da su yadda shirin nasu zai wakana basu suka rabu ba sai da suka gama tsara komai da zasuyi sannan suka rabu bayan FaÉ—ime ta gama jaddada musu a kan gobe su shirya da wuri sannan ne kowacce ta wuce gida.

______
Ba sallama ta faɗa gidan abin ta tana ƴar waƙarta cike da nishaɗi tana lura da irin kallon da matan gidan ke yi ma ta suna gulma ƙasa-ƙasa amma ta yi kamar bata gani ba sai ma dariya da take yi ta shige Ɗakin Inna Fatuh sai dai bata tarar da ita ba da alama bata dawo ba daga Anguwan da ta tafi hakan ya sa Faɗime ta yi kwanciyarta ba abin da ya dameta ba'a jima ba kuwa bacci mai daɗi ya yi awon gaba da ita duk da lokacin yammaci ne kuma ko can anjima da Inna Fatuh ta dawo ta tarar da ita bata yi yunƙurin tashin ta ba domin a Ganinta hakan babu amfani sai ma tashin hankali da zai biyo baya dan kuwa fitan da ta yi ta sama labarin da ya girgizata a kan batun Auren Faɗime da Ɗan Abba ta kuma fusata da yadda labarin ya zagaye ƙauyen amma ita bata da labari yanzun ma ta dawo ne tana jiran Malam Yahaya ya dawo daga kasuwa ta turkeshi sai ya sanar da ita dalilinsa na ɓoye ma ta batun auren Faɗime da ya yi.

Ai kuwa an yi sallar isha'i ba jimawa Malam ya shigo gidan kuma har lokacin Faɗime bata tashi ba dan so take ta yi bacci ta darje dan akwai abin da ta shirya zata yi a daren yau shi ya sa ta nutsu tana bacci cikin kwanciyar hankali domin ta rantse yau babu mai rintsawa a gidan tun da har a ka munafurceta yau ba zata kyale kowa ba kowa sai yaji a jikinsa tun da har ita za'a ɓoye ma ta magana a kan aurenta ke nan da sai dai taji labarin an ɗaura aure...

Kai tsaye Ɗakin mahaifiyarsa Inna Fatuh Malam Yahaya ya wuce a nutse ya Gaishe ta tare da fara kama kame a kan ta yadda zai sanar da ita maganar dake tafe da shi dan ya yanke shawarar sanar da ita maganar auren in yaso ya lallaɓata ta yarda ita kuma Faɗime zuwa da asuba zai zaunar da ita ya yi ma ta nasiha mai ratsa jiki sannan ya sanar da ita maganar auren.

Da ƙyar ya samu ya iya zayyanewa Inna Fatuh kalaman dake bakinsa.

Tun da ya fara maganar har ya kai aya Inna Fatuh ta zuba uban ta gumi hannu bibbiyu tana saurarensa ba tare da ta katse shi ba har sai da taji ya kai aya sannan a fusace ta ce.

“ka gama? Nace ka gama surutun banza da wofin e mana banza da wofi mana domin ba zan lamunce ba, amma yahayah ka bani mamaki har lalacewar taka ta kai haka ban sani ba?”

Sai kawai Inna Fatuh ta saka kuka tana ci gaba da faÉ—in.

“shikenan zama bai sameni ba, Lami ta gama dani Lami ta mallakemun ɗa wayyo ni Fattuh.”

Shi dai Malam Yahaya yana zaune gefe abin duniya ya haɗe masa goma da ashirin domin ji yake muddun bai aurar da Faɗime ba a gobe to fa Akwai matsala, da ƙyar ya iya furta.

“dan Allah Inna kiyi shiru ba fa abin da kike tunani ba ne kawai dai ni ne naga hakan ya dace shi ya sa na yanke aurawa Faɗime wannan yaro amma idan na ɓata miki rai bisa ɓoye lamarin da nayi a gareki kiyi haƙuri....”

“Yahaya ka tashi ta fitarmin daga ɗaki tun muna mumu biyu.”

Inna Fatuh ta faÉ—a a fusace tana nuna masa hanya ba musu Malam ya tashi cikin sanyin jiki ya fice.

Sai Inna Fatuh ta mayar da dubanta wurin da FaÉ—ime ke kwance kamar mai bacci sai dai tun shigowar Mahaifin nata É—akin ta farka sai dai bata yi motsi ba.

“Allah sarki Baiwar Allah marainiyar Allah ta'ala muddun ina raye ban ga meyi miki Auren dole ba.”

Inna Fatuh ta kai maganar tana ƙara fyace majiya wai duk cikin tausayin Faɗime sannan ta miƙe tsaye tunawa da ta yi bata yi sallahr isha'i ba ta fita domin ɗauro al'wala.

Hakan kuma ya bawa FaÉ—ime damar sakkowa daga gadon na Inna Fatuh da ake kira da mambari ta tsaya tsakiyar ÆŠakin tana tunanin ta inda zata fara, murmushi ta saki dan bataso duk abin da zai faru a daren yau Inna Fatuh ta sani tun da ita tana goyon bayanta.

Aljihun doguwar rigar jikinta ta saka hannu ta ciro abin da ta siyo É—azu kafin ta shigo gidan ta yi saurin barbaÉ—awa cikin miyar tuwon dare a ka kawo ma Inna Fatuh bataci ba, sai da ta juye duka sannan ta yi ma za ta fito daga ÆŠakin ai kuwa suka buga karo da Inna Fatuh da gata É—auro al'wala tana shirin shiga ÆŠakin.

Washe baki Inna Fatuh ta yi tana faɗin. “ƴar albarka Faɗime na kin tashi ke nan? To ma za kiyo al'wala kiyi sallah sannan kizo mu ci abinci kinji?”

Inna Fatuh ta faɗa tana kamo Hannun Faɗime domin tayar da ta yi komai amma ban da abubuwa guda biyu su ne; ƙin yin sallah da kuma zama da yunwa.

Turo baki Faɗime ta yi cike da shagwaɓa ta ce.

“Ni Inna Fatuh bana jin yunwa kuma zan yi sallahr amma sai anjima yanzu zan je wurin ƙawata Sa'ade ne akwai abuna dana manta ban karɓa ba a wurinta.”

“amma kuma ba zaki bari sai zuwa da safe fa Faɗime gani nayi dare ya ɗan yi...”

“karki damu Inna ai zan iya kare kaina kuma ba zan daɗe ba yanzu zan je na dawo.”

Faɗime ta faɗa tana yin gaba Inna Fatuh ta jijjiga kai sannan ta shige Ɗakin ta gabatar da sallahr taso ta jira Faɗime ta dawo su ci tuwon tare amma ƙamshin miyar kukan dake dakar hancinta ya sa ta gaza haƙura ta buɗe kwanon tuwon ta loda abin ta har da tanɗe hannu a fili ta ce.
“yau kuma su Salaha an yi abin kai kome ta sakama miyar nan ta yi wannan maganaɗisun daɗi ohoo.”

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.