Complete Hausa Novels

Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Faɗime Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 1 of 17

*FAƊIME...💋🌸💕*
_(Dangin Jinnu)_

©By Nainarh KD & Zahrah Royal Star

*Dedicated to Salma Ahmad Isah (Candy)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*A love & Laugh story that will capture your heart and soul.*

01

*ƘAUYEN KINKIBA, KADUNA STATE.*

*GIDAN MALAM YAHAYA*

Lami ta saki shewa a karo na barkatai zuciyarta cike fal da zallar farin ciki na ganin halin da Abokiyar zamanta Ummah ke ciki na tsananin azabar naƙuda, amma hakan bai sa Lami ta tausaya ma ta ba, sai ma ƙari sa shiga cikin Ɗakin da ya haɗu daidai gwargwado kuma kana gani kaga Ɗakin Amaryar da bata shekara ba, wani irin kallo take jefa wa Ummah dake tsakiyar Ɗakin tana faman nuƙurƙusu cikin halin naƙuda, kafin ta ƙari sa wurin da take tare da durƙusa wa a gabanta ta ce.
“kin yi kaɗan kuma kin tafka Babban kuskure da har kika yarda kika kasance matsayin kishiya a gareni wannan azabtar ma kaɗan kika gani sauran a kan abin da zaki haifa zai koma domin nayi miki alƙawarin ɗaiɗaitawa da tarwatsa Rayuwar koma wane ne jaririn da zaki haifa tun da duk irin abin da nayi domin cikin ya zube tun yana ƙaraminsa amma abu ya gagara, to ya fito ya haɗu da uƙubata domin sai ya zama abin tausayi sanadiyyar uƙubar dana tanadar masa.”
Tana gama maganar ta miƙe tsaye tare da kwance ɗaurin zanin jikinta ta ciro wani garin magani ba imani ba bare tausayi da ganin halin da Ummah ke ciki haka Lami ta daddage ta juye wannan garin maganin a gaban Ummah cike da rashin tausayi sannan ta koma gefe tana jiran sakamako tana kuma tuna maganar Malam Kasan komai da ya tabbatar ma ta da muddun ta zuba garin maganin a gaban Ummah lokacin da take tsaka da naƙuda to fa abin da zata haifa ba lallai ne ya zo a raye ba in ma ya rayu to fa zai kasance mara amfani domin zai kasance banbancinsa da matacce shi ne numfashi, baya da haka Ummah ba zata ƙara haihuwa ba tsawon Rayuwarta, duk wannan za su biyo baya ne muddun Lami ta aikata komai yadda ya umarce ta, a ka sin haka kuma to fa abin da zai biyo baya ba zai haifar musu ɗa mai ido ba daga shi har ita shi ya sa kafin ya bata maganin sai da ya zuba ma ta kakkausar gargaɗi na yadda zata yi amfani da maganin ta aiwatar da komai yadda ya buƙata....

Zuwa yanzu kuma da ta kammala sai ta ja gefe tare da naÉ—e hannu tana jiran tsammani.

Ai kuwa a take a wurin naƙuda ta ƙara tsanani ga Ummah gadan-gadan haihuwa ta taho a daidai lokacin kuma mai gidansu wato malam Yahayah da ya fita kiran Ungozoma ya dawo afujajan yayin da Matar mahaifinsa kuma ungozoma ta garin take biye da shi ganin haka ya sa da sauri Lami ta ƙari sa wurin Ummah tanayi ma ta sannu tare da ƙoƙarin taimaka ma ta daidai lokacin da ungozoma Iya Suwai ta shigo Ɗakin ne kuma jaririya ta faɗo ai da azama ta ƙari sa ciki domin taimakawa da abin da ba'a rasa ba.

Bayan wasu mintina jaririyar tana hannun Lami ta zuba ma ta ido tana ƙare ma ta kallo cike da takaici na ganin jaririyar tubarkallah ma sha Allah ƴar dumurmur da ita.
Kamar almara haka Lami taga kamar Jaririyar ta gifta ma ta ido.
Zaro ido Lami ta yi cikin son tabbatar da abin da idonta ya gani ita ma ta zaro ma Jaririyar nata idanunta, sai kawai taga jaririya ta fashe da dariya sai ga haƙora sun bayyana a bakin Jaririyar tashin hankali ya sa Lami ta kwaɗa ihu tare da miƙe wa tana ƙoƙarin jefar da jaririyar ta ranta a guje sai ji ta yi tamkar an saka gam an manne Jaririyar a hannunta haka kuma ta kasa tashi tsaye jikinta ne ya shiga rawa na tsananin tashin hankali da dabara ta waigo da dubanta saitin Jaririyar wai don taga ina Jaririyar take duba ai sai taga Jaririyar ta kafeta da manyan idanunta tana turo ma ta harshe waje.

Muƙut! Lami ta haɗiye yawu na tsoro cike kuma da tashin hankali bata kai ga motsi ba taji Jaririyar ta ce.

“Baabaah Lami ba zakiyimin wankan ba ne so kike sanyi ya kamani?.”

Lami da sai lokacin ta tuna dalilin É—aukar Jaririyar da ta yi shi ne don ta yi ma ta wanka, sai taji gaba É—aya jikinta ya saki bata da sauran kuzari saboda tsananin tsoro take ta fara tunanin ya a ka yi a ka haihu a ragaya ne, bayan kuma Malam kasan komai ya sanar da ita a Macce jaririn zai zo in ma bai zo a matacce ba to zai kasance da shi da mataccen basu da bambanci ne.

Lokaci guda ta fara tuna yadda ta aiwatar da komai lokacin da zata zuba maganin ta fara nazarin ta ina ne a ka sama matsala.

Dam-du-dum dam! Kirjinta ya buga da sauri lokacin da ta tuna kwaɓar da ta yi domin ta yi Magana kafin ta saka maganin in bata manta ba har shewa ta yi da hakan ke nufin aiki ya ɓaci kuma kamar yadda Malam Kasan komai ya faɗa abin da zai biyo baya ba zai yi musu kyau ba muddun aikin ya ɓaci.

Lokacin da Lami ta zo nan a tunanin tashin hankalinta ya ƙaru sai kawai ta fashe da kuka domin ji take shi ne abin da ya kamace ta a wannan taƙin.

Kukan nata ne ya jawo hankalin Iya Suwai da ta shigo ÆŠakin É—auke da bahon da za'ayi ma Jaririyar wanka.

“Ke Lami lafiyarki kuwa wannan kukan fa?”
Cewar Iya Suwai tanayi ma Lami kallon mamaki.

Lami ta fyace majiya tana faɗin. “ba komai Iya Suwai ai wannan kukan duk a cikin farin ciki ne wai yau dai Allah ya nufa ƴar uwa Ummah ta haihu, ta haifowa Malam wannan Jaririya kyakkyawa da ita ma sha Allah.

Lami ta ƙare maganar tare da ƙara sautin kukan tana ɗan gantsarewa sakamakon wani azaba da ya ziyarci gadon bayanta ji ta yi kamar an mintsineta aikuwa tana dubawa taga Jaririyar ce ta mintsineta a baya.

Tsananin mamaki ya sa bakinta ya fara rawa tana so ta yi magana amma ta kasa sai dai tana mamakin ya a ka yi hannun Jaririyar ya kai har gadon bayan ta ga É—an banzan zafi da ta ji a bayan tamkar an saka allura mai tsini, da sauri ta kalla Iya Suwai dan son tabbatar da ita kaÉ—ai take ganin wannan tashin hankalin ko kuwa dai ita ma Iya Suwai ta gani, don son ta tabbatarwa sai ta ce ma Iya Suwai.

“wai Dan Allah Iya Suwai kina lura da abin da wannan Jaririyar take yi kuwa?.”

Murya a raunace ta yi maganar domin ta gama sadaƙarwa da lamarin wannan Jaririyar tasan wannan Jaririya dai ba Dangin Mutane ba ne sai DANGIN JINNU domin ba yadda zatayi Jaririya daga haihuwa ta yi magana kuma take yin irin wannan abun haka dole dai akwai wata ƙasa ai ya zamar ma ta dole anjima ba sai gobe ba ta koma wurin kasan komai domin lamarin yafi ƙarfinta ita ɗaya.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.