Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 7 of 9
AKIN CIKI 2***14 Ya soja ya dubi Ya
abdulrahman, yace je ka kawo mana ita nan! Ya
miki cikin hanxari, ya nufi dakinta, tana kife bisa
gado aikin kuka kawai takeyi. Ya sa hannu ya
fisgota, ba karamin tsoro ya bata ba, ta kwala
ihu, wani BAKIN CIKI ya kara turnuke shi, bai
san tymda yasa hannu ya doke bakinta ba, yace
rufe mana baki shashasha. Da sauri ta kame
baki, wanda take kyautata xaton hakoranta xasu
iya xaxxagow idan bata dafe shi ba. Ahaka ya
ciga da jan ta har dakin abba. Gaban babban ya
direta, ta xube har tana karo da guiwarsa. Ya
xuro mata ido kamar zasu fado kasa. Yace
matsa kdaga kusa dani, xan iya tokarinki, ki
mutu idan baki matsa ba. Ta janye jikinta baya,
ahankali hawaye na ambaliya, sunfi minti 5 babu
wanda tanka saboda takaici, kafin Ya abdulkrm
yace, gaba daya kin rusa rayuwarki Mama kin
lalata cikar asalinki da martabar iyayenmu.
Yanxu wa ya isa ya kankare bakin fetin da kika
shafawa kanki? Wa ai daura miki aure da ciki?
Wa kuma xai jagoranci kisan kai? Wannan cikin
dole ki haife shi, domin yunkurin xubda shi, ya fi
yinsa barna da tarin xunubi. Kin ga tun daga nan
idan kinyi tunani cikin hankalinki, xaki gane
babu soyayysa tsankaninki da Danliti. Burinsa
dama ya ruguxa rayuwarki, burinsa kuma ya cika
tare da hadin kanki. Saboda haka dabara ta rage
wa mai shiga rijiya, sannan karki xargi Danliti,
idan ya tsallake auranki, gaba daya abinda yake
bukata ya samu, abinda yai saura shine ki haife
masa wannan ckin, in ya ga dama ya karbi dan,
idan bai yarda ba ya kyaleki da shi, ku wulaknta.
Dama wannan shine karshen son xuciya. Babu
uwar kudi balle riba ga mai cinikin son xuciya.
Kuma duk wanda ya hau motar kwadayi da son
xuciya, babu tantama tashar kunya da nadama
xata kaishi ta aje. A koda yaushe karshen
danasani, ina fatan wannan xai xama darasi
gareki, ki gane cewa abinda Babba ya hango,
yaro ko ya hau gwauron dutse ba xai hango ba.
Ya goge 'ya kwallan da suka xubo bisa kuncinsa
sannan ya sauke numfashi ya dubi sauran, yace
yanxun mene abinyi? Abba yace abinyi babu shi
abdulkrm, tunda maganar aure ta rushe a halin
yanxun. Ya Soja yace duk da haka, dole ya san
tana dauke da cikinsa, bayan ta haihu xa a daura
musu aure, su tare da yaronsu! Su karata can da
abin kunyarsu! Ya abdul rahman ya kara sanyaya
muryarsa mai taushi, yace wannan dole ne,
amma abu na farko shine, ina xata xauna? Ta
kula da kanta? Umma dai ba xata jure ganinta a
wannan yanayin ba, ya soja ya gyara zama yace,
gaskiya ne, kuma waje na ya kamata ta xauna,
sai dai ba xan iya daukarta ba saboda xan iya yi
mata dukan mutuwa yadda nake jin na tsani
ganinya. So a cikinku, wanda yake ganin xai iya
hkr da ita, yana iya tafiya da ita Allah ya
shiryeta, mu kuma kullum addu'a muke mata,
idan ta dauki wannan mtsayin darasi a gareta,
xamu fi kowa farin ciki. Ya Abdulrahman, yace ni
xan tafi da ita, no ka bari ni in wuce da ita
Minna. In ji Ya abdulkrm. Abba yace ba xata biki
ba nan da xata xauna... ban ce mata yin ku za
su yadda ta ba amman yau da gobe sai Allah.
gara ta zauna anan, domin anan ne suke aikata
abin kunyar u kun ga ganinta da juna biyu ba zai
girgiza kowa ba sanin cewar daman can
sakamkon da zai biyo baya kenan. in ba wani
gyaran Allah ba. saboda haka ku kwantar da
hankalinku kuci gaba da yi mata addua sannan
ku kwantar da hankalinku ku tallafa wa
mahaifiyar ku ta kowace fuska don ganin ciwon
BAKIN CIKIN bai tagayyara ta ba, dukkan su
suka jinjina kai alaman uban dawaki gaskia ne.
yaya soja yace da yardar Allah umma ba za ta
tagayyara ba, idan mama bata son ki mu bamu
da wacce ta fi ki. bamu da wani buri. da ya wuce
mu rayu tare da ke. kar bacin ran mama yasa
mu dakatar da dukkan farin cikin mu. mu ukkun
nan mun ishe ki kallo ki samu sanyi a ranki ko
umma? hawaye na suka malalo mata yaya abdul
yayi maza ya rungumota ya na share mata
hawayen ki daina kuka umma in kina kuka
mama ba zata taba ganin haske ba, duk adduar
da zamu mata tace ba komai wallahi bana
jayayya da ikon Allah amman ku sani BAKIN
CIKIN ba zai goge cikin raina ba, domin FARin
ciki da bakin ciki duk halitta ce cdaga Allah fata
na kawai Allah ya bamu ikon cinye jarabawarnan
Allah yayi maku albarka Kowa ya numfasa, yace
amin, abba ya dubi mama da hawayenta yaki
yankewa yace, ina fatan kin ji abubuwan da 'yan
uwanki suka fadi, idan kinyi anfani da su, ki ga
daidai, idan kuma kin ce ba haka ba, mu babu
abinda xamu iya yi, sai mu kyale ki, ki ci gaba
da rayuwar da kika xaba. Ko dama kin riga kin
ruguza ta, karashe ne kawai. Allah ya shiryeki,
ki na iya bamu wuri mu sha iska, ki jira dawowar
Danliti, amma ki sani auran ku ba shi yuwuwa,
sai bayan kin haihu. Tashi ki bamu wuri. Ta kara
makurewa, kukanta ya karu, duk suka xubo mata
ido. Ya soja yace wa yace kiyi kuka? Cewa akayi
mun gaji da ganinki, ki koma dakinki. Ta
yunkura kamar xata tashi, amma ta kasa, da
sauri ta rarrafa jikin Ya abdulrahman, ta
kudundune ta rushe da kuka. Nan da nan ta
karya masa xuciya, ko dama shi akwai sanyi da
saurin jin tausayin mutum. Idanuwansa suka cika
taf da kwalla, tun baya son kulata har ya kai
hannunsa, bisa knta muryarsa na rawa yake
fadin, imani kawai xai sa akalleki Mama, amma
ke ba abar tausayi bace, tunda baki tausaywa
kanki ba...... Ya soja ya katse shi, pls
abdulrahman, fita da ita, Umma tace sai ma ya
fita da ita? Gata kenan, ya kyaleta, ta tashi da
kanta ta wuce. Ya tarairayo ta suka mike tare,
ya janyo ta xuwa dakinta ya xaunar da ita bakin
gado. Ya tsugunna gabanta yace, dube ni Mama.
Da kyar ta dube shi, hawayen ta na xuba, yace
kukanki bai da wani anfani, muddin ba nayin
nadama bane. Nadamar ma ta gaskiyya, tsakani
da Allah. Saboda haka ina shwaratar ki da ki
kama kanki, wannan ya xama na farko kuma na
karshe. Ba soyyaya vace wannan, ki dauki jikinki
ki ba da ga namiji, daga ranar da ya sanki a
waje. Wlh kin gama yawo, duk wulaknci da ya ga
dama xaiyi miki, ko da kinyi sa'a ya aureki,
abanxa xai rika kallonki, sannan wulakanci ba
xai daina shi ba, a karshe ki ga auran ya
bantale, tun ba aje koina ba. Kuskure ne, kin
riga kin yi Mama, irin wanda bamu taba xato ba,
babu yadda xa muyi mu gyara shi, sai dai kiyi
tuba wajen Allah, sannan ki nemi afuwarsu Abba,
kin jini? Ta xura masa ido, hawaye na ta bulbula
ta kasa fadin komai, domin ita kanta bata san
ainihin abinda ke damunta ba, cikin ranta agame
da samun ciki ba tare da aure ba. Saboda haka,
sake fado masa tayi, ta kankame shi, kukan ta
kamar xai fasa xuciyarta. Ba karamin rikita shi
tayi ba, domin nan take ya goce da kukan shi
ma. Da kyar ya banbare ta ya mike da sauri ya
bar dakin, ya dawo falo ya cigaba da gugar
kwalla, xuciyarsa na masa ciwo. Kai! Sun
dandani BAKINCIKI, da akwai yadda xasuyi su
goge wa Mama wannan bakin fentin da sun goge
mata shi, ko da shi xasu rasa komai nasu. Sai
dai kash! Babu hali, shi ya sa ko abinci
tsakurarsa sukayi suka ci, ba don yayi musu dadi
a baki ba. Haka suka juya bayan sallar la'asar
makare da BAKIN CIKIN da baya misaltuwa.
Haka zalika sun bar Mama cikin wani yanayi na
kunci rayuwa, wanda ya wanxar mata da
cututtuka masu dama ajikinta. Kafin yamma ta
fadi, kamar ba ita ta dawo Legos dambasheshiya
ba. Sati 2 kenan yau babu labarin Danliti, yayin
da rashin lfyar mama ke cigaba da yaduwa
tamkar yadda labarin samun cikinta ya gama
baza gari, ta bakin Hajiya Gaje. Amma don
tsabar yaudara su suka matsawa Mazajensu su
akan su kai ta asibiti ko ta sami dan taimakon
da xai rage mata larurar jikinta. Da kyar abba ya
amince. Alh. Basir ya kaita babban asibiti da
garin Kagara. Suka ga likita, yayi gwaje gwajen
sa ya gano, lalurar shigar ciki ne ke wahalar da
ita. Saboda haka ya bata 'yan taimakon da xasu
rage abubuwan da take ji a jikinta, sauka dawo
gida. Sun wuce kofar shagon Danliti shi kuma
yana karasowa wajen. Yayi fakin ya fito tare da
yin daguwar mika mai isar da sakon gajiya.
Ayuba ya fito ya tarbe shi, sai dai fuskar sa
babu fara'a ko alama. Yaya dai mutumina? Naga
kamar kana ciwo? Ya numfasa, amma bai tanka
ba har suka shige shagon. Ya dube shi da kyau,
yace ina magana ka kyaleni, lfya nace? Ya kara
sauke numfashi. Yace ina fa lfya, magana ta
cika gari..... Ya katseshi Mama na da ciki ko?
Gabansa ya fadi ya saki baki yana masa kallon
Mamaki, Dan liti ya kece da dariya, kwalla na
gangara bisa kuncinsa kafin yace, shiege ni, dan
buzu mai shayi. Raina kama gaiyya, ka tabani ka
ga tsiya. Watau labari har ya bazu ko? Kaga
burina na farko ya cika, amma har yanxun akwai
saura, don na san dan xagin kalilan za'ayi mata.
Ido jajur! Ayuba yace, kaji tsoron Allah Danliti,
ka kyale yarinyar nan haka. Tunda ba xaka
aureta ba, ka barta taji da wannan bala'in! Ai ka
gama ruguzamata rayuwa, babu sauran
wulakanci da yafi wannan..... Ya ja Kujera ya
xauna, yace haka kake gani, nasan akwai saura,
sai dai ba xan shanye maka dadin labarin ba,
idon ka nake son ka gani kamar yadda ka ga
wannnan. Ya bishi da kallo, yana kada kai.
Murmushin keta Danliti yayi, ya sake fadin, babu
wani abu mutumina, kai kanka kasa ramuwar
gayya, tafi gayya xafi. Dadin abin a gabanka
mama ta xageni, ta xagi Mahaifina, ka manta
kawai! Yace wannan ba hujja bace Danliti, ina
gaya maka barnar da kakeyi tayi yawa. Allah ba
xai kyaleka ba. Ya ja dogon tsaki ya mike tsaye,
kai wannan ya dameka, ni yanxun gidan ma xani
kuma lfy lau xaka ga na dawo, see you! Ya juya
ya daga kanta ya fice abinsa, ayuba ya koma a
hankali, ya xauna ya dora tagumin mamaki da
takaici. Danliti ya sake gani ya dire masa bakar
leda tare da kwalin juice kato bisa kanta. Yace
ga sauran kazar da na ci a mota nan, idan ka
gama laulayin, ka ci. Ya juya ya wuce mota, yayi
tafiya sa ya bar shi da tagumi. Kansa tsaye yayi
fakin kofar gidan Uban dawaki, akwai yara gidan
suna wasa, don haka bai yi wahalat neman yaro
ba, take nan ya aika yana kiran Mama. Yarinyar
ta shiga, jim kadan ta fito ta gaya masa tana
xuwa. Yana nan jingine da mota yana kada
makullai. Abba ya fito. Nan da nan ya tsuguna
kai sunkuye, mummunin kare kenan. Yace, ah!
Sannu abba, ina yini? Abba ya bishi da kallo,
amma kash, ya kasa ganin bakinsa balle ya gaya
masa bakaken maganganu. Ya amsa gaisuwasa,
sannan yace mike ka biyoni. Ya wuce kofar falon
bakinsa, ya murda ta bude suka shiga, xauna, ya
nemi waje ya tankwashe kafafuwa. Abba ya
xauna ya dube shi da kyau yace, yanxun saboda
Allah Danliti abinda kayi, ka kyauta kenan? Me
ya sa duk abinda xakuyi baku sa tsoron Allah a
xukatanku? Ya xa kace kana son yarinya da
aure, sannan ka aikata mata abinda ba shine ba?
Danliti ya kara sunkuyar da kai, kamar xai tsaga
kafet din falon ya shige don gulma, abba ya ciga
da cewa, to ta faru takare, ahalin Yanuxn Mama
juna 2 gareta, kaga xancen auranku ya rushe
kenan dole tayi zaman istibra'i xuwa tym da xata
haihu. Wannan abu ya bani kunya kuma kun
xubar min da mutunci da kima a garin nan.
Hannaye 2 Danliti ysa ya rufe fuskarsa yayi
xugum, ko mtsi ba yayi. Abba ya numfasa ya
kada kai ya cigaba, ni bani da abinda da xan
iyayi, tunda kaddara ta riga fata, abinda kawai
nake soka sni, shari'a ce ta tsara haka, saboda
haka dole ku kauracewa juna, don gudun karku
kara maida hannun agogo baya. Ina fatan kaji?
Sai ka koma jira ranar da xata haifamaka danka,
kaga kun sami dan aike, ba sai kun nema ba.
Kana iya tfiya, mu jira abinda Allah xaiyi.
Shawara da xan baka kawai, ka nemi tuba wajen
Allah, domin ka saba masa, ka keta rigar
mutuncin yarainya. Shiru yayi ya kasa tashi,
abba yace tashi mana, ni nakare magana, ya
dago kai da kyar, amma bai kalli fuskar abba ba,
cikin sanyin murya yace, abba kayi hkr ka yafe
min? Wlh sharrin shaidan ne. Ya goge kwalla,
abba na kallonsa kafin yace, haka ne, amma
wani tym har da son xuciya. Si yasa nace ka
nemi tuba wajen Allah, don ta ni mai sauki ne.
Ya kara rankwafawa yace, je ka kawai. Ya tashi
simi simi ya fice babu ko waige. Abba ya raka
shi da ido, sannan ya numfasa ya kada kai, yace
Allah ya shirya mana. Shi kuwa Danliti yana fita
yayiwata 'yar girgiza ta jin dadi, ya wuce
motarsa cike da farin ciki ya koma shagonsa.
Ledar kazar da ya ajewa ayuba suna nan bisa
kantar bai taba ba. Wai don ya ba ayuba haushi
sai ya dage kantar kayan suka watse kasa.
Ayuba ya bishi da kallon kafin ya ce ni baka ban
haushi ba don ka xubar kudinka ne, ba nwa ba,
gaskiyya ce dai ba xan daina gaya maka ba,
watakila ma baiji shi ba, domin bai tsaya ya
saurare shi ba, cikin daki ya shigr. Yayi kwance
yana tunanin shirinsa na gaba akan mama. Abba
kuwa ys jima falon xaune yana tunani rayuwa
kawai. Sannan ya mike da kyar ya koma cikin
gida, ya maida wa Umma yadda sukayi da
Danliti ta kada kai tace , shikenan, Allah yasa ta
nutsu ta xauna gidan. Yace amin, amma ina mai
tabbatar miki muddin tace ba xata nutsu cikin
gida ba, xan bata mamaki, domin, dole ta xaba
ko mu ko shi. Umma tace gaskiyya ne, ace
wannan abu ya sameka, baka yi nadama, ai
kuwa sai a sallama mutum asa masa ido. Allah
yasa mu dace. Ya amsa da amin. Tunanin uwar
gayyar ba anan yake ba, domin kuwa jin ga
Danliti yana kiranta, ya tabbatar mata da cewar
ya dawo kuma taso ta ganshi, su Abba suka
taka mata birki. Duk da haka taji karfi a jikinta
kwarai da gaske, har wasu daga cikin
cuttuttukan da ke damunta suka yaye nan take.
Sai dai tana ganin babu adalci a hukuncin dasu
abba suka yanke. A zaton su zan iya zama
tsahon tym banga masoyina ba???????? Ta tabe
baki tana daga kwancw tace, ba xan iya ba
gaskiyya, sai dai suyi hkr wlh. Ai dai maga juna,
ya san halin da nake ciki, ya tausaya min. Ta
goge kwalla ta cigaba da sakar xuci. Ana ta
sallar magriba, tym ne da ita mama ta sami
damar satar jiki ta sulale ta isa shagon danliti.
Shi kuma kaida ke xaune cikin shagon. Ayuba ya
shiga sallah. Yana ganinta ya dafe kirji ya wani
lumshe ido. Yace wayyo Allah na gode maka! Ta
daga kanta ta shiga, ta nemi t barma ta zauna,
saboda bata jure tsayuwa. Tana xama ta hade
kai da guiwa ta fasa kuka ya kare mata kallo, a
dage yana dan murmushi, sannan ya taso ya
dawo gunta yace haba bebina! Meye abin kuka?
Ya xauna gefenta ya rungumota jikinsa, bana son
kukan hakan nan....... Ta cira kai da sauri ta
dube shi, ba xanyi kuka ba? Ciki fah gareni,
kowa ya tsaneni ana ta zagina. Shine xaka ce ba
xanyi kuka ba? Yayi dan murmushi yace, bebi
kenan, to don kowa ya tsaneki shine me?
Bayanni ina son ki kuma ina son ciki na! Kina so
yi kukan ne, wata kila kuma na dadi ne yayi
miki yawa. Ta mako masa harara tace, jin dadi?
A zageni, a tsaneni shine jin dadi? Son ka ne
kawai yake sawa bana damuwa, amma kai ina
ganin abin baya damunka, daya dame ka, da
baka wanke kafarka ka bar garin ba, tsawon sati
2, alhalin an ce ka turo a daura mana aure. Da
ka maida hankali ka turo din, ai da duk hakan
bata kasance ba, koda cikin xai bayyana
adakinka xai fito. Tunda ni ban ma taba nuna wa
akwai wani abu tskanin mu ba. Sannann.... Ya
da ka mata tsawa, ya ida don Allah! Haba!
Wannan maida xancen na menene? Ko kuwa turo
ki akayi ki zo ki batan rai? Ko dan kinga ina ta
rarrashinki? Babu fah dole, kin ganne? Abban ki
cewa yayi ba dole bane ya bani ke, ko bayan kin
haihu. So pls ki daina damu na da irin
wadannnan surutun banxan, ban son jinsu, idan
har kin son mu shirya! Kin gane? Ta xura masa
ido hawaye na xuba, ta ma rasa me zata ce?
Ayuba yayo sallama ya shigo ya riske su cikin
wannan halin. Shi ma yayi tsaye yana kallon su,
jim kadan Danliti ya buga tsaki ya tashi ya
shige daki ta goge hawayen itama ta tashi ta
bishi, ayuba yaa kada kai ya ja kujera ya xauna
yana fadin Allah ya kwaci yarinyar nan. Tana
shiga ido ya xubo mata. Yace au biyo ni kikayi?
To ranki xai baci kuwa, gara ki koma. Ta
marairaice tace, kayi hrk Danliti, ba don ranka
ya baci bane ya sa na gaya maka abinda ke
damuna. A xatona xaka tausaya min a halin da
nake ciki. Bani da wani gata wajen iyayena. Tun
ranar da na nuna kainake so Danliti, ka tausaya
min. Yayi lum da ido ya bude, ya cigaba da
kallonta tana tsiyayar hawaye kusan 3mins
sannnan ya yafito ta da hannu, yace xo nan! Da
sauri ta isa gunsa, ta fada jikinsa ta kara fashe
da kuka. A'a, kinga ni fa kukan ne bana so.
Yanxu menene damuwarki? Ta goge hawaye, tace
kullum in rinka samun kulawarka, hakan shi xai
tabbatar min da kana sona kana son abinda ke
cikina. Yayi dan murmushin nan nasa, ya kara
janyo ta jikinsa, yace, kin samu bebi, karewa ma
da kewarki na dawo. Kin ci abinci? Ta kada kai,
saboda me? Bana iyawa ne, jikina gaba daya ya
canza, sai amai kamar xai kasheni. Yace ayya
sorry ko? Amma duk da haka ba za a rasa
abinda kike sha-awa ba, gaya min in nemo shi,
na kosa in kore kishirwata. Ta mako masa
harara, ya kyalkyale da dariya, meye na harara
ta? Ko ke ma xaki min BAKIN CIKI ne, irin na
'yan sa ido? Masu shiga tsakanin masoya suna
son suga bayansu. Haushi su nake ji wlh. Tace ai
ko ni din ma haushin su nake ji, ah haba? Wlh
kaji na rantse. Ya cacume ta tana dariya tana
fadin, ban da lfya Danliti, bai saurare ta balle ya
tuna ya nemo mata abinda take son ci. Karfe 8
ya fito ya barta can kwance tana murkukusun
ciwon ciki, ya wuce waje wani mai suyan nama,
ya karbi danyan naman da yasa ya aje masa. Ya
dawo ya bade shi da magani, ya maida cikin leda
ya nade. Yana xaune bakin shgo bisa benci, yana
tunanin tafiya yayi wanka ko ya samu yayi
sallah. Mama ta fito tana yafa mayafinta, ya bita
da kallo yana murmushin keta, ya cikin? Tace
yayi sauki ni xan koma gida sai gobe. Haba haka
da wuri? Yanxun fa 8 ta wuce? Kar a neme ni ne.
Wa xai neme ki? Don Allah xaumna muyi hira, ba
wanda xai nemeki, bayan sun san kina nan. Bata
da xabi, don haka ta xauna kusa dashi, ya shiga
bata labaran banxa. Jimawa kadan wani kare ya
xo gilmawa nan take ya hau kiransa, tace me
xakayi da kare kake kiransa. Kasan karen
okundiri fada gareshi ko? Yace bai sami nama
bane don ubansa okundiiri, ya kece da dariya,
okundirin ne ubansa? Lallai ka samo shi. Yacee
to da waye ubansa? Kinga bude ledar nan nama
aciki dauko ki ba shi. Yana magana yana shafar
kan karen. Tace, taf ya cafke min hannu? Kai
dai ka bashi kai da ka siyo masa,don raka
asara. Yace karki bani kunya mana, me xai sa
ya cije ki, bayan yasan ke bebina ce, ko kare? Ai
ka santa ko? Sweetheart dina ce kar ka cije min
ita. Tuni kanta ya fasu, ya jawo leda ya bude ta
dauko katon yanka ta mika masa tana fadin,
abin har da yaji? Sangarta! Ya kwashe da dariya,
yace ina ruwanki? Ke dai mika masa gudan. Ta
dauko ta mika masa, ya cafke, Dan liti ya runtse
ido yace yes! Ya xarce da dairya. Ta xuba masa
ido tace, menene abin dariya har da wani cije
labe? Yace ji nayi kamar ya hade da hannunki ya
gartse. Takai masa bugu a kirji tace amma kai
mugu ne! Yace sosai ma ashe baki sani ba
yarinya, to tashi kije gida an gama hirar, kinga
karen yayi tafiyarsa. Ka gaida okundiri kaji? Ta
ci da kyakyata dariya. Yace, ah! Tashi karki sa
yarona ya fito yana fito yana kyakyatawa kamar
dolo. Ta shi kije gida sai safe. Don Allah kiyi
hkr, so nake nayi wanka inyi sallah. Ta fido lah
nima har ka tuna min banyi ko magriba ba. Ta
juya da sauri tana cewa, sai da safe! Yace Allah
ya kaimu. Ya bita da kallo, yace yarinya kin
gama yawo kin shiga 3 kin lalace, ya daga
murya ki fa sami abinci ki ci. Ta juyo ta amsa,
kar ka damu xanci. Suka ja hankalin mutane,
don haka yama didi ya biyo baya, masu tsinuwa
nayi, masu addu'ae shiriya nayi. A tsakar gida
ta iske su Abba na jiran dawowar ta, shi da su
Alh. Basiru. Tana shigowa tasha jinin jikinta, ta
shiga bin bango, tana so ta shige falo. Alh.
Basiru ya daka mata tsawa, ke dawo nan! Simi
simi ta matso gun su ta durkusa guiwa 2, batayi
aune ba, taji saukar wani wawan mari. Gaba
daya ya ratsa kanta, ya gigita ta, ta dunkule ta
fasa kuka. A cikin ba tace ga wanda ya xabga
mata wannan marin mai tsanannin xafi ba. Sai
dai taji muryar Abba na fadin wannan shine
gargadi na karshe da xanyi miki, shi ya sa na
tara kowa su xama shaida! Idan har ba xaki bi
umarni na, ki xauna a gida ba, to wlh sai dai ki
xaba, ko mu ko Danliti! BAKIN CIKIn nan ya ishe
mu mama. Gara in sallama ki, in tabbatar da
kinfi karfina xaman kanki kikeyi. Saboda haka
daga yau kika kara sa kafarki kika fita kikaje
gun yaron nan, to kar ki dawo, ki yi zaman ki
can wajensa ku sha shagalinku yadda kuke so.
Duniya ce Mama, mai dauke da axuxuwa babu
adadi! Ina fatan kinji kuma kowa ya shaida! Alh.
Basir ya karbe karuwa kike so ki xama ko? To
Allah ya baki sa'a, mu dai ba xa mu hana shi
ba, duk ranar da koreki. Alh. Adamu yace dama
saboda me xamu hana shi? Cikin shege ne fah
ajikinki, amma bai sa kinyi nadama ba, to me
xai sanya ki kuwa? Karkiji da wai, mun tsame
hannun a kanki, haka xuri'ar gidan nan kaf! Kar
ki ce kin san daya daga cikinsu, duk ranar da
wuya ta koro ki! Ta shi ki bace mana da gani
shashasha sakarya. Ta mike da gudu ta fada
dakinta, ta dasa kukanta, a fusace abba ya bar
wajen kowa ya kama gabanmsa, suka cigaba da
yada xancan a sasan su. Daren nan su ma Umma
basuyi barci ba, musamman Umma da tabbatar
wa kanta ciwon xuciya ya kamata. Da safe ta
atashi xuru-xuru baki daya idanuwanta sun
xurma, shi kansa Abba ya rame ta maxa kawai
yakeyi yana wa Umma fada kar ta salwantar da
rayuwarta akan Mama. Ita Mama ba wannan ta
aje ranta ba, kawau burinta kasance tare da
Danliti, don haka take ganin kowa ya tsangwame
ta saboda kiyayya. Kafin safiya ma ta mance
duk kalaman su Abba da kawunninta. Allah Allah
takyi ta sami saukin laulayin safe dake damunta
ta lababa taje ta gano Danlitin ta. Xuwa 12noon
ta iya shiga kicin, ta dan tsiyayi ruwan lipton, ta
dawo ta shanye. Xufa ta keto mata, danji dadi
ajikinta, kana ta shiga bayi tayi wanka da
sabulun wanki maras kamshi. Ta kimtsa, tsaf,
duk da tayi haske sosai, ta kuma rame kwarai,
kana iya gane kyanta na asali mai daukar
hankali. Ta koma ta kwanta yana kllon agogo
1:00 ta tashi tayo alwala tayi sallah, ta dauko
gyalemnta ta xura takalma ta leko falo bataji
motsin kowa ba, ta kwahi sauri ta fice abinta.
Yara suna ce mata sai kin dawo aunty Mama!
Jin haka yasa Umma yanke sallah, ta fito da
sauri ta tambayi yaran ina maman? Sukace
yanxun ta fita. Tabi xauran, yaran suka biyota ta
tura su tace, ku kira min ita. Yara suka fice da
gudu suna kwala mata kira, Aunty Mama, ki zo
Umma na kira! Haka suke ta gudu suna fadi har
suka isketa, ta dube su tace, sai na ci ubanku in
kuna kwala min kira haka! Ni sa'ar kuce don
Ubanku? Ku tafi ku ban wuri kafin in fallawa
yaro mari! Mts..... Taja tsaki, ta wuce abinta,
yara suka dawo a guje suka iske Umma a xaure
sukace, wai sai ta ci ubanmu idan muka sake
kiranta! Ta dafe kirji tace, ta kyauta, kuje wasan
ku. Ta dawo cikin gida a salube tare da mamakin
taurin kai irin na Mama, me take nufi kenan? Ta
xauna a falo tana juyayi. Da kyar ta sake mikewa
ta shiga dakin Abba, ta tashe shi barcin ramakon
da yakeyi. Ya farka yana kallonta...... Yace,
azahar tayi ko? Tace tayi alhaji. Ya yankura ya
tashi yace menene na ganki a salube? Tace
tasake fita, wa? Mama mana. Cike da mamaki
yace ta fita? Yanxun nan kuwa, kamar fako na
takeyi, har yaran nasa su kirata, ta dinga
kunduma musu xagi, taki dawowa. Ita Maman ta
zage su? Tayi murmushin takaici, tace kana
mamaki ne? Bai kamata kayi ba alhji. Ta kuwa
tafi kenan, kinsa Allah ba zata dawo ckin gidan
nan ba. Kiyi hkr, duk abinda ke ranki na so da
kaunar Mama, ki cire ki dangana da ita, nima na
hkr da ita. Umma ta fasa kuka, ta tashi da
asauri ta bar dakin. Hankalin Abba ya kara
tashi, ya taso ya biyota dakinta, tana xaune
bakin gado kukan kawai takeyi. Ya tsaya kanta,
yace saboda Allah ya kike so nayi Halima? Ta
cira kai murya na rawa. Tace har ga Allah ba
korar Mama ke sanya ni kuka ba, tausayin
rayuwarta ke bani, yadda ta ka sa gane cewar
mu ba tsangwamarta mukeyi ba, saboda tana son
Danliti. Yanxun shikenan ba xata gane cewar
alabarkar mu itace kwanciyar hankalinta ba, duk
tsananin son da Danliti ke mata, shikenan ta
xabi cigaba da xaman shashanci akan ta nutsu,
dn tym kankani a daura masu aure? Wannan
rayuawar tana cike da tausayi da ban Mamaki,
kamar Ya asirce Mama? Ta kada kai ta ciga, ba
haka Mamar mu take ba alhji, ta sauya saboda
soyayya, kenan ta fi son shi a kanmu? Ina xan
samo amsoshin nan Alhji? Ina xan..... Ya rufe
bakin da sauri, ya ace ya isa haka! Kar ki jefa
kanki damuwar da xata tada miki ciwo, ki kauda
kanki ki akan komai, sannan ki nisanta xuciyarki
ga irin wadannan tambayoyin da kike wa kanki.
Xaki xautu saboda yarinyar da bata damu da
lfyarki ba, xamani ne Allah ya kawo mu da yara
ke rufe idanuwan su akan abinda suke so. Suyi
ta fada da iyeyensu har xuciyoyin iyayen su fara
xargin asirce su akayi. Xan ji dadi da farin ciki
idan xa'a ce, duk wannan abubuwan da suke
faruwa, ki dauke shi amatsayin mafarki mai
wucewa, tamkar baki taba haihuwar wata mai
suna sakeena ba. Ta dube shi xai yuwu ko? Mai
hana? Idan har zaki dage da adduoi, ubangiji ba
xai barki haka ba, ta goge hawayenta ta sauke
gwauran numfashi tace, xan yi iya kokarina Alhji.
Ya jinjina kai. Yace haka nafiso sadiya, kin san
ina jin dadin xama dake, kuma tun ina saurayi
ban taba son wat 'ya mace ba sai ke. Ban fatan
abinda xai salwantar min da rayuwarki, ya
kasance wata kaddara tasa kin fara barina cikin
duniyar nan. Kullum nayi sallah, sai na roki Allah
ya fara daukar raina saboda ba xan iya ganin
gawarki ba halima. Idanuwanta suka kara tara
hawaye. Tace ka daina fadar maganar nan
Alhji..... Ya katse ta, ni ma ba ason raina na fadi
ba, domin sirri nane wanda nake xaton shi kdai
ne ban taba gaya miki ba, sai yau, dole ce ta
sanyani, don ina son ki sami nutsuwa sadiya. Ta
matse ido kwallatana suka kwararo ya mika
hannu ya goge mata yace, sha kurkuminki
Maman abdul 3, gwarazan samarin nan masu
takama da baiwar Allah. Ta numfasa tace, Allah
yayi masu albarka baki dayansu. Kina nufin har
da sakeena ko? Ta amsa da kai, kafin tace, ai
mu na mata fatan shiriya ko? Yace haka ne, toh
Allah ya shiryta. Amin ta amsa. Haka yayi ta
rarrashinta, ta samu nutsuwa, sannan sukayi
sallah suma mika kukan su ga Allah. Na san
kilan kuyi musu ko mamaki idan nagaya muku
Mama bata dawo gida ba, sai bayan sallar
magriba. Abu na farko da ta fara cin karo da shi
a kofar sasansu dake kulle, shine akwatin
kayanta. Taja cak! Ta tsya ta xura masa ido
tsawon tym, kana ta matsa ta tura kofar taji ga,!
A kulle. Ta tabe baki tare da jan tsaki, ta figi
akwatin ta juya tana fadin a ranta, sai aga na
kwana a titi. Kai tsaye Danliti ta dosa, yana
xaune kofar shagonsa, inda ta basa. Yana
hangota da akwati, ya mike ya shige daga ciki
yana gayawa Ayuba ga mutuniyar can tafe da
akwati, ko maganarta tace ta tabbata? Ayuba ya
murtuke fuska yace ni xaka tambaya? Au haushi
kaji? Amma dai kana ji na gaya mata kar ta
kuskura ta bari su koreta, don bani da wurin
ajeta, ko ban gaya mata ba? Yace oho! Wai kai
wani irin banxa ne? Yace Ni banxa bane, ai
rainin wayau yasa ka gaya mata hakan. Wa ke
jan ragamar rayuawarta, in ba kai ba? Ai sanin
bata da xabi shi yasa ka raina mata hankali. To
ya isa malam, sai gata tsaye gaban kanta, tana
kokarin dagawa, duk suka xubo mata ido, ta
karasa shigowa, ido waje ya dubi shirgegen
akwatin, ya ce ya dai? Bata saurare shi ba, kofar
dakin ta tasarmawa xata shige. Yayi azama ya
shawo gabanta, magana fa nake yi, kona kokarin
shigewa kamar gidanku? Ta xubo masa ido a
marairaice tace, me na gaya maka? Ni kuma me
na gaya miki? To yaya xanyi? Ina komawa na
iske akwatina akofar gida sun kulle gidansu. Ya
gayara tsayuwa, da yake kuma ke sakarya ce sai
kaka kamo hanya kika taho baki tsaya kika nemi
sulhu ba! Yanxun menene nufinki? Anan xaki
xauna? Cikin shago? Lallai kin cika dakikiya,
Jaka! Kuka sosai ya kwace mata, ta tsugunna ta
rungumi kafafwansa, murya na rawa tana fadin,
karkayi min Haka Danliti! Saboda kai suka
koreni, ina kake so naje, idan ba nan ba?
BAKIN CIKI 2***15 Ayuba ya daga kanta, ya fice
hankalinsa tashe, shi kuwa ko gezau beji ba
ajikinsa, a dage yake kallonta, tsawan tym
sannan ya fizge kafarsa ya kama hanya xai fita,
da sauri ta mike ta cukuikuyo rigarsa, fadi take,
kayi hrk don girman Allah. Wasu samari 2 suka
iso wajen siyen taba sigari, ai sai suka buge da
shari'a, kaya-kaya hayaniya har waje Danliti na
daga murya shi ba xai aje ta cikin shagonwa ba,
ta koma ta nemi sulhu da iayeynta. Kan ka ce
kwabo jama'a sun cika makil a gun. Kai Mama
ta sha zagi da la'anta, Allah shi kara kwando-
kwando. Kalilan ke cewa Allah ya shiryeta, Dan
liti ya gacciye banci kofar shagoin ya xauna yace
yaga uban da ya tsaya mata agarin nan, wnada
xai sashi ya ajeta. Baiwar Allah kuwa na tsugene
gaban akwatinta, tana ruasar kuka har karfe
10pm. 'yan ganin kwakwaf suka gaji suka koma
gidajen su dauke da labari mai ban al'ajabi.
Wasu suna ganin bai kamata Uban dawaki ya
koreta ba a matsayin sa na Uba, kuma babban
mutum mai sarauta, wasu kuwa suna ganin
hakan shine daidai, imna xai sa BAKIN CIKI?
Idan bai sallame ta ba, tunda ta tara masa, ya
cika masa xuciya, tana neman fashewa ta
hallakashi? Ai gara da ya sallamata duniya ta
koya mata hankali. Ga darasi na farko nan ta
fara gani, duk iskancin Danlitim yace baxai aje
taba. Alhalin saboda shi aka koreta. Wannnan ya
nuna a fili ita ta nace masa kamar sauran 'yan
mata marasa xuciya. Mutane na mamaki abinda
Danliti yake da shi wanda yake tsonewa 'yan
Mata ido. Su mutu cikin soyayyar sa. In bata ga
kyau me yake da shi? Shi babu hali babu
kwakkwaran asali. Amma duk wacce ta fada
tarkonsa sai gagari iyayenta. Ko don kudi da ya
ke kashe mus ne? Shiya sa suka dauki laifi
kacokan suka dorawa 'yan Matan masu biye
masa don kwadayi da kyalekyalen jikinsa. Wayyi,
kai bai san dawan garin ba, dai bai yi tunanin
kutsa kansa ciki ba. Tun ciki dare surutai kala-
kala suka fara baza gari. Shi kuwa gogan da ya
ga kowa ya watse sai ya matso ya xunguri Mama
da kafa, ta dago kai da sauri ta dube shi, matso
mana nan kiji, ta matsa gareshi, tana hawaye.
Ya dubeta da kyau yace, ke banxa ce wlh, shi ya
sa kika bani haushi. Nace ba xaki xauna anan
ba. In banda hauka irin naki, ya xa'ayi ki xauna
tare da mu cikin shago? To ina sane da abinda
nakeyi, kin gane? Saboda haka ki koma ki nemi
wani wurin ki xauna, ki bani nan da sati xan san
abinyi. Murya dushe tace, ni bansan inda xani
ba, a'a ko gidan 'yanwanku ba xaki je ba? Ko
baku da su ne? Sai dai inje gidan su Baraka,
yace ko gidan su Mubarak xaki, sai kinm dawo
matsalar kice. Amma ba xaki kwana shagon nan
ba. Yauwa, tashi ki sungumi akwatinki, ki wace
kar su kulle gidansu. Tace to nagode, sai da
safe, Allah ya kaimu 'ya bebine. Muyi fada mu
shirya ko? Kar ki damu xan ganki goben. Tayi
murmushi, dadi ya rufeta, ta mike tana kara
masa godiya, taja akwatinta ta nufi gidansu
Baraka. Ya mike janye da benci yana kyalkyala
dariya, ya shige shago. Kai mugu dan gidan buzu
mai shayi! Yayi wa kansa kirari ya shige daki.
Ayuba na kallonsa yana kada kai. Gidan su Bara
akulle yake, saboda sha dayan dare tayi ma. Ta
shiga bugawa har aka xo aka bude mahaifin
Baraka ke tsaye cikin xauran, ya dubeta da kyau
yace, Mama ce? Daga ina haka? Ta fara kuka
yace shigo shigo ciki! Ta wuce da uban akwati
ya maida kofa ya rufe. Tana gaba yana biye da
ita yana fadin, subhanalillahi! Dakin Inna saude
suka shiga tana tsaye tsakar daki, lfya? Ta xube
sharaf! Cikin kuka tace, abba ne ya koreni.....
Ina saude ta nemi waje ta xauna, yayin da
malam kasim ke fadin, me ya sa Uban dawaki
xaiyi hak? Inna saude tace BAKIN CIKIN ta ne ya
ishesu. Ace kamar Mama ta gagari kowa duk
abinda ya sameta da abinda ake gaya mata ba
su isheta nadama ba, idan ba su koreta ba me
kike so suyi miki? Ba shashanci kike sha'awar yi
ba? To sun baki hanya, meye kuma na kuka?
Mal. Kasim yace hakan ba hujja bace, duk
abinda xatayi, gara tana gabansu suna tsawata
mata, yau da gobe ana hada mata da addu'a, sai
Allah ya taimaketa ta gane illar abinda take
aikatawa. Saboda haka ta xauna, gobe Allah ya
kaimu lfya, xanje in ganshi. Ke kuma je ki
kwanta kiyi tunani, meye amfanin lalata
rayuwarki da kikeyi? Har jikokinki sai an yi musu
gori, wannnan abinda kika aikata! Kina da
babban laifi mama, sai kin tuba kin bi Allah kin
bi iyayenki sannnan xaki ga daidai a rayuwarki,
kinji ni? Ta amsa da kai, yace ta shi ki shiga
wajen 'yar uwarji kafin Allah ya kaimu goben. Ta
mike simi-simi ta ja akwatinta, inna saude ta
xuba mata ido tana mamakinta. Ta kada kai,
taca baka ce xata aikata ba, yarinya kyakkyawa,
ta lalata rayuwarta. Allah ya shirya mana, yace
amin albarkar annabi. Atsakar gida taga Baraka
tsaye tana share hwaye, ta matso ta kama mata
akwatin suka shiga dakin, kowacce ta nemi wuri
ta xauna bakin katifa. Baraka ta dubeta.........
Tace anya mama abubuwa da kike yi kanki
kalau? Ke bakijin kinya? Baki tunanin gaba daya
idanuwan garin nan sun dawo bisa kanki? Baki
da martaba da darajar Abba agarin nan? Haba
Mama, kamar ba tare muka taso ba? Tarbiyarmu
iri daya, nutsuwa da kamun kai, kowa na yabon
mu. Mutane na rububin mu, da son hada xuri'a
tagari. Ta daga kai sama, idanuwa cike da
hawaye ta cigaba, Allah ya isa tsakaninmu da
Danliti! Ta dube ta sukayi ma juna xuru kafin
Mama tace kar ki sake xagin Danliti Baraka,
alhakin sa xai kamaki, laifin mune? Tun tym din
da mukace muna son juna, ya kamata su Abba
su rungume mu hannu 2 amma suka ki, suka
gwammace in kwashe kayana in bishi. A tunanin
ki wane sakamako ya kamata su gani? Bayan
wannan dake jikina? Baki sake take kallonta,
kafin tace, maganar Banza ce, idan duka jina
kunnuwa ne xai taba sauraronki ba, wa kika
burge don kin aikiata wannnan sakarcin? Shi
kansa Danlitin adage yke kallonki. Kin dawo an
yi miki afuwa, cikin nman ya bayyana, duk sun
hkr, sun shanye, amma ki ntsu xuwa tym din da
xaki haihu, a daura maki aure, kar fa ki manta
xaman nan naki agida ibadane tunda Allah ya
shifida hakan, sai ki ga dalilin xaman, duk
xunubunku sun kankare, auran ku yayi karko tare
da xuria masu albarka. Ki kwanta kiyi tunani
mama, ko asiri Dan liti yayi miki, xakewar taki
tayi yawa. Ta sualala kafita ta kwanta, tace, na
kwanta shekiya Baraka, sai da safe ko? Ta bita
da kallo ta numfasa, tace Allah ya sa ki gane.
Amin, ta amsa da gatse ta juya baya abinta.
Baraka ta mike ta rufe daki ta dawo ta kwnta. Ta
jima bata sami barci ba, saboda juyayin halin da
'yar uwarta ta shiga. Da farar safiya M.kasim ya
usa gidan Ubban dawaki yasa aka yi masa
sallama da shi, jin cewa shine ke sallam ya sa
yace ya shigo cikin gida. Bayan su gaisa. Umma
ta fito suka gaisa. Sannan ya maida jawabinsa, a
karshe yace, alhaji kar bacin rai yasa ka yanke
wannan hukunci, ni ina ganin gara yarinyar nan
ta xauna agaban ku, kuna tsawata mata, sai
Allah ya taimakemu ya shiryar da ita. Don
girman Allah ka yafe mata dawo gida, tunda tayi
tunani taxo wajenmu, ta kawo mana kukanta.
Abba ya gyara xama yace, a tunanin ka a kashin
kanta, ta yanke shawara taje wajen ku? To ba
haka xancen yake ba, kila ba xaka sani ba ne,
saboda kuan cikin lungu. Amma ni tun jiya na
sami labarin wulakancin da yaron nan yayi mata,
ya tara mata jama'a, ya tozarta ta, ya kuma ce
ba xata xauna masa a shago ba, kaji dalilin
nemanku, amma ba nadama tayi ba. Yace, duk
da haka ina son ka duba girman da martabar ka
agarin nan. Kayi hkri ka amshi rokona, ba don ni
ba, sai don girman Allah da darajar iyaye. Ya
sunkuar da kai yana kadawa, kafin yace,
M.kasim ban ki ta taka ba, amma ba xan iya
xama da yarinyar da ban isa in bata umarni ta bi
ba. Ta fita tayo shashancinta, ta dawo min gida
ta wanke najasa ta kwanta. Mts! Ban jin
idanuwana xa su iya jure gainin wannan kaxanta.
Gara ta tafu su cikashe. Wlh na hkr da ita, kuma
ina rokon Allah ya sanya mana dangani nida
Mahaifiyarta, ba kuma xamu gaza ba wajen yi
mata addu-ar shiriya. Watakila wata rana taga
uwar bari, ta dawo da kanta ta neme mu. Kaga a
tym din xan tabbatar da tayi nadama. M. Kasim
yayi shiru, jawabin Uban dawaki na cike da
tausayi, ya numfasa, yace, na yarda da kai Alh.
Sai dai har yanxun ina rokonka, da ka sake bata
dama ta karshe, mu gani.idan bata daina ba, to
muma sai mu tsame hannayen mu. M. Kasim ya
cikwa Abba ido kwarai da gaske, ya jima kafin
ya numfasa, yace, shikenan ba komai nagode.
Yace nima nagode, Hajiya akara hkr, a bata
damar karshe, tace babu komai M. Kasim, Allah
saka da alkhairi. Yace amin, barin in koma in
turo saude ta dawo ita. Tace to ka tsaya kaga
abin kari akawo maka mana, ya mike cike da
fara'a, yana fadin alhmdlh, kar ki damu nagode,
to nabr ku lfya, Allah ya shige mana gaba, suka
amsa amin. Yaka hanya fice. Bayan tafiyarsa
kamar da hadin baki, jama'a sukayi ta xuwa
suna ba uban dawaki hrk tare da rokonsa ya
daure ya maida 'yarda gabasa xai fi kyau
agareshi. A cikin su har da abokansa da yaron
gidansa, watau kalla. Duk ya karbi rokonsu,
kuma yaji dadin kulawar jama'a gareshi tare da
tausaya masa akan kaddarar da ta fada wa
iyalinsa. Karfe Tara saura, Inna saude ta taso
Mama xuwa gida. Bata ma biyo da ita ta shagon
Danliti ba, balle ya gansu, haka suka taru da
matan gidan kamar zasu cinye ta danya, sannan
matza suka shigo suka dasa nasu. A gaban kowa
suka tilasta, ta dauki alkawarin ba xata sake
xuwa ko ina ba, kidan kuwa ta saba, to a yanke
mata hkunci da yafi wannan. Kwana 2 hatsaniyar
nan ta kwnata, mama na xaune cikin gida bata
fita daidai da tsakar gidan sasansu. Muna iya
cewa Danliti bai murda kambunsa bane haka?
Saboda haka xuciyar Mama ta sami 'ya nutsuwa.
Bata ita kadai ba, su abba ma sun sami 'ya
nutsuwa har tana debo 'ya'yan itatuwan da Abba
ya ka siyo ta kawo mata, tace ta sha saboda
rashin cin abinci da take fama da shi.....
***************** A wannan asabar din ma
abdulkrm ya xo daiyalinsa duka. Su ameera nata
murnar ganin auntynsum domin sun jima basu
ganta ba. Dr. Na ta dabo, yana son ya taka, sai
'yar banxar kuiyam shi ya sa yaki yarda Mama
ta daukeshi. Aunty Rabi ta tasa ta da nasihohi,
ayoyi, hadisan Manxo SAW akan ta dage ta yaki
xuciyarta ta dawo kan kanya, sannan ta nuna
mata wannan ba shine soyayya ba, duka
saurayin da ya nemi lalacewa da yarinyar da
yake so, a hakikanin gaskiyya ba son gaskiyya
yake mata ba. Sha'awar sassan jikinta kawai
yakeyi. Haka yayanta ta tsatsagge mata
gaskiyya, har yayi mata alkawarin idan ta nutsu
ta xauna gida kamar yadda aka umarceta, to
bayan ta haohu za'ayi bikinta, duk abinda take
so, shi xai sayo mata. Mama ta wani kuka tana
ba su ameera tausayi. Anann suka kwana,
washegari lhadi karfe 12noon suka juya. Su
ameera nata tambayar antyn su yaushe xata xo?
Tace kar su damu tana nan xuwa nan bada
dadewa ba, suna isa gida, yayan ya kira 'yan
uwansa, ya labarta musu abinda ya gani game
da Mama, idan har ya dore a hakan, alhmdlh!
Ana iya cewa an fara samun nasara. Kowa yayi
farin ciki jin wannan labarin da fatan Allah ya
shige mus gaba. Allah, da ikonsa a yammacin
yau din, tun bayan sallar la'asar mama ke cike
da kewar Danliti, kafin 5pm ra mance kaf! Da
alkawuran da dauka, babu abinda take so face
gain Danliti, kewarsa ta gigita kwakwalwarta, ta
birkita ta. Kamar an tsikare, kawai ta tashi ta
suri gyale da takalmi ta fito kanta tsaye ta fice
abinta. Dan gogan ta samun cikin dakin
barcinsu, tana shigowa yana xubawa wani
kaskon rushi ruwa, ya dago ido ya dubeta, yace
ba xan miki sannu da xuwa ba. Ta xaune gefensa
tana murmushi, saboda me? Ya xubo mata
harara, yace kwanaki nawa rabon ki da nan?
Sabo da nayi miki fada ko? Ta rungomoshi tana
dariya, ayya nawan ba haka bane, kowa yasa
min ido, sai surutai sukeyi kamar ni kadai na
fara soyayya agarin nan. Amma kana cikin raina,
kaima ka sani, bani da burin da wuce in kasanxe
tare da kai, ta bae baki yace tsarani, au baka
yarda ba? T yanxun ba ni na xo ba? Dana kiraki
ba? Ka kirani? Kamar ya? Ya ture kaskon ba
xaki gane. Sai dai na yarda kina sona, tunda
kika amsa kiran. Ta xura masa ido tace ngode,
tunda kasan hakan, me kake yi da kasko? Ke
duk xamanki a dakin nan baki taba ganinsa ba?
Da shi fah muke turaren daki. Kai amma wannan
bai hadu ba, kauri gare shi, kin kuwa san
tsadarsa? Ai ku maza ba gwabe bakin ku ake
wajen siyayya? Kabari xan kawo maka mai kyau,
idan ka sanya shi sai makwabta sun tambayeka
ina ka samo. Ko? To sai kin kawo din. Yanxun
mu ake maganar turare, ina kuka kwana da su
Abba? Ta tabe baki, me ma? Wai an bashi hkr
ya kyaleni, amma idan na sake xuwa nan, dole in
tafi. To kice kin karya doka, tunda gaki kin sake
xuwa, ni kuma da har nayi cinikin wani gida can
bayan tasha, ina fasa kenan? Bakinta har kunne,
tace ka fasa kuma? Ai xai mana anfani idan
munyi aure ko? Ya shafa kai, gaskiyya ne, xan
biya kudin in sa a gyara shi, ai sau muje ma ki
ganshi ko? Ya xama dole, yaushe xamu? Duk
tym din da kika shirya. Ko yanxumn a shirye
nake, mu tafi kenan? Bismillah. Ta sumbace ta
yace, amarya ta kenan, maman bebi! Ta rausaya
da kai tana dariya. Tare suka fito yana rike da
hannunta, har gaban motarsa. Ya bude mata ta
shige, ta dawo maxauninsa yaka suka tafi. Gidan
ginin kasa ne mai dauke da dakuna 2 kicin da
bayi, tsakar gidan turbayar kasa ce, haka ginin
babu digon siminti ko kadan, zallar kasar ce
kawai, illah iyaka cikin dakunan anyi masu dabe,
suna tsaye kafada da kafada, ya dubeta yace,
kinga gidan, ina fatan yayi miki? Ta yake baki
ta makalo wuyansa tace, ya fiye min kowannne
irin gida muddin da kai xan xauna cikinsa. Kar
wani abu ya dameka,a hankali na gyara shi,
kyau xaiyi fa, yayi dan murmushim ya falla ido
sannan yace, toh shikenan, tunda yayi maki, yau
din xan nemi dillalin in bashi kudin. Ta kara
kankame shi tace, ina tayaka murna. Ya xubo
mata ido yace ni xaki taya murna, ko ke xan
taya murna, gidan ki ne fa? Tayi dariya sosai. To
dukkan mu Congratulations! Ya sumbaci labbata,
tace thnk U! Sun jima cikin gidan suna
sharholiyar su, ana kiran magriba, suka fito, ya
kulle kwadaon gidan suka koma shago, maimako
ta koma gida sai ta rashe nan, tana nishadantar
da shi, kamar yadda ya bukata, ya siyo mata
abubuwan da take so, tace, tayi hani'an, kai
barci sace ta mana, ta yada kai bisa filo tai tayi
kuwa...... 11pm za su kulle hsago, ayuba yayi
juyin duniyan na Danliti ta tashe ta, ta tafi gida
amma yaki, ya kuma hana Ayuba ya tasheta. Da
ita suka kulle shago, ayuba ya kwana tsakar
shagon, shi kuwa dan gogan yana tare da
gimbiyar. Tsakar dare ta farka da ganta tare da
mutum. Ta tashi xaune ta bubbuga shi ya tashi,
menene? Tace dama ban tafi gida ba? Yace ga
shi nan kin gani, ai da ka sani ka tasheni
Danliti. Yace waya gaya miki ana tashin mai ciki
barci? Kiyi kwanciyarki kawai da safe kin koma,
Abba xai koro ni Danliti, yace akwai gida na biya
kudinsa, baki da haushin wannan. Idan kina
kwanciyarki, ki kwanta ida kuma yanxun xaki
fita 2am ga hanya nan babu ruwana. Bebi na
kawai nake ji. Ta watso masa harara ni banda ni
ko? To! Na ga kin wani hakikance ne, meye sabo
idan kin kwana anan? In banda gulma! Ta dare
ruwan cikinsa ta kai masa duka, ni ce
magulmaciya? Kai din fa? Todama mai neman
kuka ne aka jefa shi da kashi awaki, sai yaya?
Washegari, yadda bata sallaci magriba da isha
ba haka batayi asuba ba, karfe 7am ta dauko
hanya. Gata nan ga nan har gida, salalau-
salalau ta karaso ciki, ta iske duk sammakonta
Abba ya riga ta tara jama'am don haka tana
xuwa tsakar falo, tayi sanrada. Gwiuwa 2 ta xbe
ta fara kuka. Kowa ya saki baki yana kallonta,
M.kasin ya fara magana, yanxun saboda Allah
Mama duk maganganun da aka gaya miki ta
bayan kunnunwaki suka wuce? Ashe haka kike
da taurin kai? To mu babu ruwan mu, dama
rokonsa mukayi, ya ga girman mu ya hkr, tunda
ke baki gani ba. Shikenan ga hanya na, ki bi duk
wacce kika xaba. Abu yaya kamari har da
kwana? Ke Mama kiji tsoron Allah ki tausayawa
iyayenki. Ba xata suka ji tana magana, wlh Baba
bada niyyara kwana ba na fita, Danliti ne ya sayi
gida, yace muje na gani, mun dawo ina hutawa,
ban tym din da barci ya kwasheni ba, abba ya
xaburo yana fadin, kunaji Maganar Banxan da
take fadi ko? Kun tabbatar da cewa abinda nake
fadi gaskiyya ne? To ya isheni haka! Ya isheni
haka!! BAKIN CIKI ba xai akshe mu ba. Daga nan
ki juya ko koma, idan har ki na son kanki da
arxiki, wlh! Wlh!! Babu wanda ya ya sake roko
na in kyaleki cikin gidan nan! Duniya ce da fadi,
karki saurara wajen bin ta kwararo-kwararo har
ki gano iyakar ta! Tashi ki bace min da gani,
kafin in kusa kashe ki da duka. Gaba daya falon
yayi tsit, sai shasheshekar kukan Mama, jim
kadan muryar abba ta kara gauraye falon, kai
Jama'a! Ina xan kai takaici da BAKIN CIKI? Me
nxan yi wa yarinyar nan a dniya na huce, banda
in sallama ta, tamkar ban taba haihuwarta ba?
Ki tashi fice min nace, in daina ganinki a
gabana..... Ki ta... Kawai sai ya yanke jiki ya
fadi, gaba daya suka mike da sallalami sukayi
kansa...... Toh masu karatu, wannan fa shine
wasa farin girki. Nayi iya kar kokarina ace nayi
muku sallama anan. Amma ina abin ya faskara,
kuyi min hkr karshen badakalar wannan littafi
yana cikin 3, ku biyo ni, kada ku gajiya nayi
gaba....................THE END!!!