Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 6 of 9
BAKIN CIKI 2***13 hasalima rashinki yasa na
aure ta koda yaushe ki kace da ni kule da sauri
xan ce cas mama don son ki ya zauna a raina,
tayi yar dariya tace yaya ali ke nan kar kasa
amaryar ka ta tsane. Ni daga wasa sai ka hau
jera zance!ba haks nake nufi ba yaya ali muje
kawai naga amarya in na dawo na ci abincin
bata jira yace wani abuba ta yi gaba abinta tilas
ya biyo bayanta yana kada kai!Amare kam
masha ALLAH suna dauke da tasu baiwar da
ALLAH yayi masu musamman aminar yaya ali
har mama na masa tsiya wai ya kamata ya
maida sunan sa aminu dan su kara dacewa da
juna kallon ta kawai yake yi cikin ransa shi
yasan babu wacce tafi dacewa dashi face ita
kanta maman,bata wani dade ba ta dawo sasan
su ta dauko leda cike da kayan garar amare
bayan ta gama cin abinci ta zauna gaban madubi
tayi wa fuskar ta kwaskwarima tayi zaman jiran
Danliti har barci ya fara dibarta bataji aiken yaro
ba,ta kwana zullumi da juyayin abinda ya hana
Danliti zuwa alhalin ya sami izinin yin hakan ko
har yanzu bai amince wa ransa bane?ya gudun
kar yazo ya fuskanci wulakanci!wannan
tambayar taso ta hana ta barci domin ta kai
sama da karfe dayan dare bata sami barci ba,Da
sassafe ta tashi da ciwon kai wanda ya haddasa
mata jiri akai akai duk da haka ko karyawa bata
yiba karfe bakwai da rabi tasa kai ta fice babu
wanda ya sani ta nufi wajen Danliti dauke da
ledar kayan garar amaren da aka bata jiya ita ta
tashe shi barci ya tashi a gigice yana tambaya
lafiya kika bugo sammako haka?tace nayi zaton
zaka zo jiya hira me ya hana ka zuwa. ya ja
dogon tsaki ya kauda kai jim sannan ya juyo ya
dubeta wai me ke damun kine?ba kinzo nan ba
sai bayan magariba kika tafiba?to kuma me
zanje in yi maki saboda ALLAH ta zura masa ido
ya kare mata kwakwazo nan take idanuwanta
suka tara kwalla murya na rawa ta ba haba
Danliti laifi ne don ban gan kaba na biyo in duba
ko lafiya?ya bita da kallo tana ta gugar kwalla
ya kece da dariya kamar mahaukaci hakan yasa
ta daina hawaye ta zuba masa ido yayi dariya
mai isar sa sannan ya natsu shima ya bita da
kallo to meye abin kuka ni ina can ina ta billayin
neman mana waliyai ai banga ta zaman fira ba
sakeena"nan da nan ta hadiye tashin hankalinta
ta fara murmushi duk kin wani daga hankalinki
don baki ganni ba jiya kawai " kawai ne? In gaya
maka dai dai da sakwan daya bana son zama
babu kai,yayi wata budurwar dariya yace ko to
na kara baki tukuicin kaina ta kwanto masa tana
dariya kasan ALLAH da ciwon kai na tashi ga
wani jiri na diba na amma na kasa daurewa na
fito ko karyawa banyi ba, yace ai ya bebi na
sannu ko ya kamata mu karya ki sha magani
bari inzo. Ya fice ya bar ta kwance bisa katifar
wucewar minti ashirin ya dawo da soyayyun kwai
da naman kaza da doya itama hade da kwai ta
hada masu shayi suka batse cikinsu harda ayuba
anan ta yada kafada daga fira barci ya kwasheta
Danliti ya dawo shago ya zauna tare da ayuba ya
zura masa ido yace don ALLAH ka tasheta ta
koma gidan su yayi banza dashi ya fito yana
zuba fito kamar katon arne. -Ayuba ya kada kai
yace karshen alewa kasa Danliti idan an ciza a
rinka hurawa ya ballo masa harara ya ce ba
ruwanka malam ka kyale ni in ci lokacina ya
tabe baki yace na barka zaifi kyau suka yi shiru
kowa na harkan gabansa, a gida kuwa tunda
suka shafa babu mama a dakin ta suke ta
kwasar BAKIN CIKI don sun tabbata tana can
shagon Danliti karfe tara uban dawaki ya gama
shirin sa zai fita ko karyawa bai yi ba saboda
tsabar takaici yasa umma ta fito masa da jakar
kayan da mama ta shigo dasu ya sunkuta yayi
waje da ita kalla ya tarbe shi da sauri ya amsa
ya bude but ya saka Abba yace minna zasu tafi
amma zasu tsaya shagon Danliti, kalla yaja
mota suka wuce yayi fakin kofar shagon abba ya
umarci daya fito masa da jakar nan kai tsaye ya
wuce shagon lokacin da su Danliti ke ta
harkokinsu yayi tsaye babu sallama har
hankulansu suka juyo gareshi Danliti ya matso
yana fadin sannu alhaji ina kwana yace nasan
mama na nan tare da kai ina take baki sake yace
tazo amma ta tafi yayi jim yana kallonsa kafin
yace ba shi ya dame ni ba wannan ya rage kuda
ubangiji ina fatan. Ta gaya maka yace ta gaya
min kokarin da nakeyi ke nan na samu na turo
yace kar ka bata lokaci domin na kosa na kauda
kazantar da nake gani ya dan sunkuyar da kai
yana murmushin izgilanci naji abba in ALLAH ya
yarda zuwa anjima ko gobe zan turo yace shike
nan ina sauraronka amma ga kayan ka nan ka
aje idan ta tare gidanka sai ka bata ba na
bukatar komai daga gareka sai sadakin da
ALLAH ya wajabta ga jakar nan bai saurari wani
abu ba yasa kai ya bar shagon ya fada motarsa
kalla ya ja suka dauki hanya Ayuba ya matso
gare shi yace, Allah na tabaka dama, don ka
gyara kuskuran ka Danliti, kar ka bari ta subuce
maka, ka dawo kana cizo yatsa. Ya watsa masa
harara yace bana bukatar wa'azinka alaramma
karfa ka manta da ni da kai duk daya ne. Na ma
dai san abinyi, ayuba ya xuba masa ido ya rasa
ta cewa babu abinda ya sami Danliti, yasa
hannu ya dauki jaka ya shige da ita. Hannu 2 ya
rike kugu, yana kallon mama xucyarsa na masa
sake-sake. Kusan 5mins yana tsaye, sannan ta
tsugunna ya bubbugata. Ta farka tana yamutsa
fuska, menene? Tashi kiji? Ta yunkura ta tashi
xaune, yasa hannu ya kara janyo jakarta, don ta
ganta sosai. Cike da mamaki tace waya kawo ta?
Yace, abbanki mana! Wannan kadai ya tabbatar
min baya sona, baya kaunta. Bai dameni ba,
amma me yasa zai uzzura min dole sai na turo
magabata na yanxu-yanxu? Hankalinta ya tashi,
ta matso a hankali ta dafa kafadarsa. Don
girman Allah kar hankalinka yatashi Danliti....
Cikin sababi. Yace ki daina gaya min wannan
maganar! Kora da hali abba ke min, saboda
haka ki hkr, kije su baki wanda suke so! Tashi
ki bar dakin nan, kar kuma ki sake xuwa, ni
babu ruwana! Ta narke da kuka, murya na rawa
tace, karka yi min haka Danliti, ina mai tabbatar
maka xan kashe kaina idan ka juya min baya.
(Kuji banza mtsw :(). Ya cire hannunta daga
jikinsa yace, ni ban aikeki ba ya kamata ki gane
ki gane ba dole bane na aureki. Don me xa a
daga min hankali akan magabata? Banda su,
uban wa xanje na tura idan ban nema ba? Kinga
ki tshi kije ki gaya musu na fasa. Ta marairaice
kamar ranta xai fita ni ina sonka Danliti ba xan
iya rabuwa da kai ba, ai dai ni xa'a daurawa
aurenko? Xan gaya musu su kyaleka, sai ka
shirya. Shikenan? Ya kara murtue fuska, yana
kallonta bai tanka ba. Takara matsarsa sosai
taci gaba da fadin, muddin suka ki yarda da
uxurinka wlh na yi rantsuwa xasu sha mamaki
dan wlh nan xan dawo na tare..... Ok, ki sa a
daureni kenan? Tace wa xai daureka? Don Allah
ki kyaleni ni bana son surutu, tashi ki tafi kawai,
sai na nemeki! Dan..... Ya daga mata hannu,
idan baki so raina ya baci to ki tashi kawai ki
bar dakin nan! Ta cigaba da share hawaye, ta
xura takalmi ta dauki mayafi ta mike xata wuce,
amma ta kasa, tayi tsaye tana kallonsa, don
Allah kayi hkr Danliti. Ya dago ido ya dubeta,
hawaye keta ambaliya, yayi dan jim, kafin yace
nayi hkr, amma kije tukunna xan nemeki. Xaka
xo gidanmu? Eh xan xo ki share hawayen, ba
wani abu. Ta share da sauri ta duro bayansa,
Nagode Danliti na! To kayi dan murmushi mana
ko naji dadi mana. (mayya :() Ya banbare
hannayen ta ya mike tsaye, karki damu da
murmushina, muje in rakaki, kafin tace wani
abu, ya fice, dole ta biyo bayansa, bakin shagon
kawai ya tsaya, yace sai nazo ko? Tace, daga
nan xaka tsaya? Xan wuce neman wadanda xan
turo din ne. Nan da nan sanyi ya ratsa mata
xuciya, baki har kunne. Tace, Allah sarki nawan,
to sai mun hadu anjima. Ya daga gira yana
fadin, sai mun hadun, yana sakin tsaki. Tana
shigowa dakinta, ta shige, motsinta kawai Umma
ta jiyo ta biyo ta dakin, tana kokarin cire kaya,
don shiga wanka. Umma ta kare mata kallo, ta
kada kai, tace don girman Allah mama ki rinka
xama a gida. Tunda Danliti na sonki kuma
abbanki ya bashi dama ai shi xai biyoki. Kullum
inaga ya miki babu mutunci ga 'ya mace ta rinka
bin saurayi har makwancinsa. Ko bai aikata miki
komai ba jama'a ba za su dube ki da mutunci
ba. Me yasa Danlit ya sauya miki tarbiya.? Tayi
shiru tana ciccika tana batsewa, Umma tacigaba
ni rokonki nakeyi, ki taimakemu ki taimaki
kanki, don mu tsira da 'yar martabar da tareg
mana a idon jama'a. Kinji? Ta amsa da ka, kafin
tace, Umma idan abba ya dawo ki fada masa ya
daina matsawa Danliti akan turo
magabatansa...... Ta katseta kamar ya? To
umma tunda an gayama sa kuma ya amsa xai
turo din, ba sai asa masa ido ba? Ta mako mata
harara, bangane asa masa ido ba? Shi daman
can bai shirya auran ba, ya hanaki sauraron
wandan ya shirya? To baku isa ba, mu ba wasa
mukeyi ba, tunda ya hure miki kunne dole ya
gaugauta turowa, ya raba da mu da bakin ciki da
muke gani, kinji nagaya miki. Tayi ta tashi tana
fadin, to shikenan ai matsa masa ba shine xaisa
ya turo din ba. Me kikace? Ta shige bayi da sauri
ta rufe kofa. Mama ni kike wa rashin kunya?
Lallai kin rika, kina gab da tsinka min mari akan
Danliti. Sallamar da jiyo, shi yasa tayi shiru. Ta
mike ta fito tana amsawa. Inna saude ce da
Baraka, saude sannunku da xuwa. Duk suka
amsa, yayin da Baraka ta tsugunna ta cigaba da
gaisawa. Bayan sun nutsa a falon, inna saude
tace, tun jiya naso fitowa, wani axababben ciwon
kai ya addabeni. Tace ayya ina fatan yayi sauki.
A'a da sauki, ina maman? Tana ciki ta shiga
wanka.... Wai dama saboda ita kika zo? Ai da
kin yi kwanciyar ki kin huta, domin al'amarin
Mama ya zama jiki. Tace, ya xama dole in taso
yaya. BAKIN CIKI kuwa baya taba zama jiki sai
dai imani. Allah dai ya bamu ikon cinye
jarabawar, ta nisa tace amin. Tace, yanxun me
kuke ciki? Ta fada mata yadda al-amarin yake,
ta cire tagumi. Tace haka shi yafi dacewa, in ma
banda sakarci ba ita xata taimaka mana ya turo
da wurin a huta ba. Tace ina fa, ai ina mai
tabbatar miki tafi son shi akan mu. Allah dai shi
kyauta. Ta amsa da amin. Suka ci gaba da hira
har suka ji motsin fitowar Baraka ta tashi ta
shige dakin. Ba suyi wata hirar kirki ba, domin
ra'ayinsu yasha bambam yanxun. Duk mai zagin
Danliti Mama bata ganinsa da kima haka ta fada
ma baraka, shiyasa ta shiga taitayinta, tafito
daga dakin tace xata ganin amare. Mama dataga
shirinta can ta sameta dakin amaryar Ya Ali, nan
suka shantake, sama da 2hrs sai da Inna saude
ta shiryo tafiya tasameta can, ita ma bata yi ma
Mama maganar komai ba akan abinda ta aikata.
Domin a tunaninta babu wata bakuwar kalmar da
xa agaya mata wacce bata sani ba. A wannan
daren mama tasa ido taga xuwan Danliti shiru
kakeji yasa ta jin haushin rashin dawowar abba.
Al- amarin nata cizon ta taga ba xata daure ba,
karfe goma harta goa, ta fito ta bude kofar ta
fice abinta. Ko kafin Umma ta fito taga wanda
ya bude kofar mama har ta kai kofar gidan,
ganin bata a dakin ya tabbatarma da Umma ita
ta fita. Ta nemi kujera ta xauna hannunta a
kunci BAKIN CIKI ykamar ya kasheta. Take nan
taji xuciyarta na ciwo, wani abu dum! Cikin
kanta kamar xai makantar da ita, tasbihi ta
shiga jerawa ko ta samu saukin kan. Ita kuwa
mama Tunda ta kwashi sauri bata sausauta ba
sai da taje shagon mutumin nata ta ja birki.
Ayuba na xaune daga ciki, taga kanta ta shiga
tare da sallama. Ya amsa mata ta wuce tana
fadin sweetyna naciki ne? Da sauri ya amsa
mata ai bayana nan bai gaya miki bane? Ta
tsaya cak dauke mamaki, ina yaje? Ya amsa
gaskiya bai gaya min ba, cewa yayi xaiyi tafiya
kawai. Na xaci ya gaya miki daxun. Ta kada kai,
bai gaya min ba wlh, amma xai dawo gobe ko?
Yace watakila, ta danyi shiru sannan tace to
shikenan sai goben. Allah ya kaimu. Taga kanta
ta fice, ya bita da kallo. Duk tasuayinta ya lullbe
shi, aransa yace Allah ya kubutar dake daga
sharrin Danliti. To nima nace AMEEN! Da babbar
murya. Tana tafe tana sakar xuci, wai duk fushin
ne yasa Danliti yatfi ba sallama? Ina xansa
kaina idan kalaman Abba suka korar min
Danliti? Bata samo amsa ba taji ann fige
mayafinta, 'yammata ji mana! Firgigi ta waigo
hankalinta ta dubi gungun samarin da suka kai
kusan shida, kowanne su dauke yake da tabar
wiwi. Ta dora hannu bisa kai wayyo nashiga uku,
duk suka fashe da dariya, ina kika nufa mu
rakaki? Ta durkusa kuyi hkr dan Allah, dariya
kwai suke kyakyatawa, 2 daga cikinsu suka
kawo mata cafka. Ta xabura ta mike, Allah ya
taimaketa ta kutsa ta cikinsu ta xura aguje,
dawa Allah ya hada su ba da ita ba, ta watsar da
takalma, ko daman gyalen yana hannunsu, taci
gudun fitar rai, ta rufta cikin gida, yayin da alh.
Adamu, ke kokarin rufe gidan, bakara min figita
yayi ba, amma yayi axama ya maida kofar ya
jefa sakata. Mama kuwa tuni tana sassansu, ta
fadi warwas! Tana maida numfashi tamkar xata
mutu, Alh. Adamu ya biyota, ya isketa daidai
kasa, ya xura mata ido kafin yace, wai daman
mama ce kartin Maxan nan suka biyota? Me kike
a waje har 11pm? Umma tayo waje tana sallami,
ganin mama a kasa yasa ta dafe kirji lfy? Ya
dubeta ido waje, yace, yanxun saboda Allah me
yarinyar nan take a waje cikn duhu? Kinga kartin
da suka biyo sunyi su 10, wannan ai diban
albarka ne da iskanci. Jiri ya soma dibar Umma
tana fadin me? Innalillahi Wainna ilaihir raju'un
kasan Allah, Alh. Adamu har na rufe kofa naji
motsin fitarta, xaune nake kawai narasa inda
xansa kaina dan BAKIN CIKI! Ban san yadda
mama ta maida rayuwarta ba......... Tana rufe
baki, tayi kasa da dafe kirji, saboda ciwon da
yake tsananin yi mata. A hankali hawayenta ke
fita tana fadin, BAKIN CIKIN ki zai kashe ni
Mama.... Alh. Adamu ya daga murya yana
masifa, kin shiga 3 mama! Kin maida kanki 'yar
iska da karfi da yaji, to ki bi a hankali, muddin
kika bari BAKIN CIKI ya kashe mahaifanki, kin
buga babbar asara, tashi ki ba mutane wuri,
kafin in taka ruwan cikinki. Ta yunkura ta tashi
da kyar, amma ta kasa mikewa tsaye, a
duddauke ta shige falo a tym din har mutanen
gidan sun fara taruwa, don ji me ya faru, Alh
Adamu ke daga murya cikin dare? Nan take ya
maida yadda akayi har ya dora karya, wai kartin
har sun turmusheta, tsawat da yayi masu, yasa
suka gudu. Kowa tafa hannu yakeyi yana salati,
kusan 12am suna xuba magana. Sannan kowa ya
koma sasansu, aka bar Umma kwance da ciwon
abubuwa barkatai. Ya ali ne kadai bai tanka ba,
don BAKIN CIKIN sa na gaske ne, tamkar yadda
UMMa takeji cikin xuciyarta. Dakin amaryarsa ya
koma yana kuka da hawayensa. Amina tayi
rarrashinsa tana nuna masa addu'a Mama tafi
bukata ba kuka ba. Mts!.... Amina ba zata gane
ba, BAKIN CIKIN dake cin angonta ba xai iya
jurewa ba, tilas sai ya matse shi. Hasalima ba
zai iya zama yana kallon irin wadannan
abubuwan ba, gara ya koma bakin aiki ko ya
kauracewa idanuwansa ganin abinda ya fi komai
daga masa ciwon xuciya. Saboda haka yacewa
amina ta shirya kayansu gobe zasu koma birnin
gwari da yardar Allah. Al'amarin ya daure mata
kai, kuma tayi tambayoyin da bata sami
amsarsu ba. Washe gari da suke shirin tafiya,
taji fashin baki na bakin Haj. Hajjo. Eh lallai biri
yayi kama da mutum. Nan take kumallon mata
ya taso mata, ya dasa mata kyamar Mama cikin
ranta har tafi Ya ali kosawa su bar garin. 12pm
kuwa ya samo shatan mota suka damki hanya.
Mama bata ma san anayi ba, tana can tana
murkususun ciwon ciki ita kadai a daki. Don ko
daya shigo yin sallama da umma bai shiga
wajenta ba. Sai wajen azahar barci mai nauyi
gaske ya dauke ta. Haka ita ma Umma ke ta
gyangyadin takaici bisa kujera. Rabonta da
abincin kirki tun jiya da daddare motsi taji a falo
ana shigowa da kaya, ta taso da sauri ta leko
falon. Kalla ta gani da tsirin kwalaye ya aje gefe
yana gaisheta. Ta amsa da fara'a ta karfin hali.
Bai karasa ficewa ba, abba ya kawo ka falon
tilas ya rabe gefe ya bashi wuri ya shigo, sannan
ya fice. Alhajin yana fadin, agaida Iyali, yace
xasu ji. Kallo daya yayi wa Umma gabansa ya
fadi, ya amsa sannu da xuwan da tayi masa. Ya
xauna falo. Yayi da ta shiga kitchen dauko masa
ruwa ta kawo masa ta xauna gefe tana kara
masa sannu da xuwa. Bayan yasha ruwa ya
numfasa. Tace an dawo lfy? Ya amsa lfya lau,
duk suna gaisheki, ni ne har abuja, daga can na
xarce kd yau da safe. Tace, wai kunsha hanya,
ina fatan duk lfya ka baro su? Yace kalau,
amma sai naga kamar kin rame, ina fatan ba
ciwo ne ya tashi ba? Ta kada kai. Kai dai bari
Alhaji, ciwo na ba zai taba warkewa ba, idan ban
ga yarinyar nan dakin miji ba. Kaci abinci
tukunna, kaji abinda ya faru jiya. Yayi dan shiru
har ta mike xata dauko abinci kafi, yace ki gaya
min kawai Halima, nasan babu bacin ran da
xanji wanda ya wuce na baya. Ta dawo ta xauna
ta fede masa abinda ya faru. Ya kada kai. Yace
ya rage nata, ba burinta ta fita duk tym da ta ga
dama ba? Jikinta xai gaya mata, xata gane
akwai wadanda suka fita iskannci. Yanxun tana
ina? Tana daki, ni yau ko kalarta ban gani ba.
Bata xo ta gaisheki ba ke nan? Tace ni a suwa?
Bana ma bukatar gaisuwarta, amma tun jiyan na
gaya mata idan na mutu, ta sani BAKIN CIKIN
tane ya kasheni. Yace, ba xaki mutu ba Halima
da Yarda Allah mama ba zata salwantar min da
rayuwarki ba. Karki manta, su hudu kika haifa,
kuma Allah ya albarkace su dubi tsibin kwalayen
nan, duk sakonki ne, kowa na da sa nau'in
tsarabar, zabi kalar abubuwan da kika fiso.
Bayan haka, jibi asabar duk zasu hadu anan,
don su share mana hawayen kukan da Mama ta
samu. Don kuwa zau tsaya tsayin daka dole
Danliti ya turo wakilnsa a daura masu aure a
cikin satin nan. Saboda haka ki kwantar da
hankalinki, ki na dasauran 'yal3an da suke
bukatar ki kusa da su a koda yaushe. Kinji ni da
kyau? Ta goge 'yar kwallan da suka xubo mata,
tace naji alhji, Allah yayi musu albarka baki
dayansu. Yayi murmushi yana fadin, amin kina
iya dauko abincin yanxun. Ta tashi da saurinta,
ta wuce, ya raka da ido tausayinta ya kwarara
cikn ransa. Ya numfasa yace, mun gode maka
Allah da wannan jarabci. Ta fito masa da abin,
ya gaugauta ci, domin gab ake da kiran la'asar.
Ya kammalawa kuwa tym yayi, ya mike yana
fadin, ki shiga ki tasheta tayi sallah. Ta amsa da
to, ya wuce dakinsa. Umma ta kwashe kayan ta
maida kicin, sannan ta nufi dakin Mama, don
tashinta. Tana kife ruf da ciki, Umma ta dada
mata duka ta tashi a firgice. Umma ta xura mata
ido, tace, in kin ga dama ki tashi kiyi sallah!
Tayi waje ta bata wuri. Da kyar ta mike zaune,
kanta ya sara mata, ta dafe shi hannu biyu, gaba
daya miyan bakinta ya kafe. Makoshin ta ya
bushe. Tana daga xaune, amma jiri ne ke dibar
ta.... Idanuwanta na ganin duhu, don haka ta
runtse su tamau! Tana maida numfashi, ta wuce
minti sama da goma ahaka, sannan ta iya tashi
a daddafe ta shiga bayin. Tunaninta kawai tayi
wanka ko tafi jin dadin jikinta. Nan da nan ta
kwashi ruwa a bokiti ta fara wanka. Kamshin
sabulun( Joy) Ya gauraye bayin, ba xato ba
tsammani taji xuciyarta ta tsani kamshin, kan ka
ce kwabo ta goce da amai. Ta kwarara mai
isarta, wai don ma babu komi cikin nata. Tana
gamawa ta dauki bojitin ta juye ruwan ajikinta,
tun daga kai. Ta jefar da shi ta yayo xani ta
daura, ta banko kofa ta dawo daki, ta bar bayin
face face da amai. Ruf da ciki ta sake fadwa
gado fadi take, wash! Wayyo Allah xan mutu! Tun
daga tym din al'amura suka kwance mata, ta
rasa kanta ta rasa meke damunta tana rashin
son abinci da yawan tashin xuciya, ga wani cikin
safe da jiri wani tym din jikinta yayi xafi, don
kansa kuma ya sauka ba tare da tasha magani
ba. Duk ba wannan bace babbar Matsalarta ba,
Ina Danliti ya shiga kwana 2 babu labarinsa? Me
kuma yake nufi da tafiyarsa? Duk da cewar tasan
dole ya dawo, idanuwanta da xuciyarta sun gaza
jure rashin sa na 'yan kwanakin 2. Shi yasa koda
yaushe tana kunshe a dakin matsalolinta masu
yawa na neman xautar da ita. Umma da kanta
bata gane kanta ba, musamman rashin xuwanta
neman abinda xat ci. Amma yawan xaman daki
umma ta jingina da rashin ganin Danliti da ta
rataywa xuciyarta, balle ayi maganar jingina shi
da wanccan Matsalar. Ta kan kada kai, tace,
kaico! Abincin wani, gubar wani! Allah ka raba
mu da muguwar kaddara... A yau asabar ake sa
ran xuwan yayyin Mamma, ga shi babu magana
mai kwari ko kuma muce uban gayyar baya gari,
shi da kansa abba xaune yake shiru dakin ta
same shi, ta xauna gefensa tace, kana xaune
baka shiga wanka ba? Yayi gajeran tsaki, yace
maganar nan ke damuna, da yarinyar nan xata
gane da ta amince cewar Dalinti ba xai turo kowa
ba. Banda aikin rashin gaskiyya, menene na
kama hanya kabar gari, kai da aka ba damar ka
aiko a baka mallakar abinda kake so. Wane bata
tym xakayi saboda Allah? Ta numfasa, tace
yaushe xata fusknaci hakan yadda ta makance
gaba daya, bata ganin kowa sai shi? Ai na gaya
maka ko abinci bata ci, duk ta fige saboda
bala'i, ni yaran nan ma dasu wahala suke nake
tausayawa ba su gama warware gajiyar biki ba,
ga aikinsa mai dan banxan wahala, da da halin
da xa'a ce da su dakata, wlh da ance suyi
xamansu. Ya gyara xama kyale su suzo ko hira
mukayi, ai maji dadi, ko ba haka ba? Haka ne,
Allah ya kawo su lfya. Amin ke ki kira min
Mama ta zo yaushe, dan liti xai dawo? Ta mike
ta nufi daki Mama ta tura kofa kakarin amai ya
fara dibar hankalinta, cikin fargaba ta nufi kofar
bayin ta murda ta bude, Mama! Tana durkushe
kame da ciki, kamar xata mutu. Kan Umma ya
kara daurewa, domin bata taba ganin Mama na
kwarara amai haka ba. Ko rashin lfya takeyi,
bata amai, sai dai xafin xaxxabi. Don haka ta
nufe da sauri ta dafe ta, me xan gani haka
Mama, baki da lfya ne ko yaya ne? Bata iya
amsa mata ba, tana tsaye kame da haba, tagama
kakarinta, ta kuskure baki hade da fuska, tayo
waje abinta, ba tare da kula Umma ba. Bisa gado
ta fada ta datse ciki tana numfarfashi. Umma ta
biyo a fusace tasa hannu ta birkito ta, ba kyajin
ina magana ne? Nace lfya kike sheka amai? Ido
jajur! Cike da kwalla tace, cikina ke min ciwo,
tun yaushe? Yau 3days. Ta jawo ta waje cikin
haske sosai, ta kama hannayenta ta dudduba,
sannan ta gwale idanuwanta, ta duba cikinsu, a
tsorace ta tambayeta ke, kina yi al'ada kuwa?
Tayi shiru tana xaxxare ido, baki na rawa tace,
nima ban sani ba Umma. Ba ki sani ba? Ke xaki
gaya min ko sai na farfasa bakinki? Ta goce da
kuka, don ita ma ta kideme, ta mance rabonta
da a'alada. Umma ta xura mata ido, jinin ta na
kara hauhawa, da sauri ta wuce ta bar mama
tsaye. Dakin abba ta koma ta xauna, ta rike kai
tana maida salati. Me akayi? Tace alh. Magana
takare ka dauki mama ka kaita asibiti ayi mata
gwajegwaje! Gabansa ya fadi gwajegwaje? Name
kuma? Na komai Alh. Ina shiga na sameta tana
sheka amai a bayi, wai cikinta ke ciwo, amma
alamu a bayyane sun nuna Mama juna 2
gareta........ Tsaye ya mike tare da fadin me?
Hawaye suka kara tsunke mata, ya koma a
hankali ya xauna bakin sa na karanto salatin
Manxon rahma. Gaba dayansu tsit! Sukayi
tsawon lokaci sai Umma ke shatatar hawaye,
baiyi aune ba kawai ya ga ta dungura ta fadi a
sume. Ya xabura ya tarairayota, yana kiran
Halima! Halima!! Don girman Allah karki kara
min tsahin hankali akan wanda nake ciki, ya
jawo goran ruwa ya xuba a hannunsa, ya yarfa
mata, ya cigaba da shafa mata ruwan bisa
fuska, ahankali har ta dawo hayyacinta. Ta bude
ido, jim tana kallonsa, sannan ta sake fashewa
da kuka, nan take tausayinta, yasa kwallan
Ubandawaki suka fara sauka bisa kuncinsa.
BAKIN CIKI kamar ya aika shi barxahu. Kiyi hkr,
ki kwantar da hankalin ki Halima, wannan
jarabawa daga Allah Ubangiji take, babu wanda
ya isa ya kankare mana ita, bana son tsanin
damuwar nan da kikeyi, tana jefa ni mummunan
matsayi, ko dogara da Allah Halima shine xai
magance mana komai. Ta goge hawayenta tayi,
iyayinta don ta tashi xaune amma ta kasa. Yace
kar ki damu da sai kin tashi yanxu kiyi
kwanciyarki ki huta, bari in kwaso magungunan
ki in duba wanda ya dace kisha. Ya mike da
sauri wani duhu ya rufe masa idanuwansa, bai
ganin komai face wasu miliyoyin taurari kanana,
tilas ya dawo ya xauna ya fadin Hasbinallahu wa
nimal wakil. Yayi ta maxa ya sake mikewa.
Umma tace ka xauna Alhaji kar kaje ka fadi ka
nakasa. Bai tanka ba, ya fice. Jimawa kadan ya
dawo da kwanndon magungunan ta ya xauan
yana bincikawa, jikinsa na rawa saboda bacin
rai. Sallama sukayi daga falo kuma babu
tantama muryar Ya abdurahman ce, abba Ya
amsa, ya kara da fadin gamu nan, ku karaso
ciki. Ganinsu jugun2, Yaya take ya rasa
kuzarinsa. Yaya dai Abba? Jikin nata ne ya
tashi? Yace shine abdulrahman, nan da nan ya
xube gabanta, da dauko kanta ya dora bisa
cinyoyinsa, sannu Umma! Sannu! Ta matse
kwalla, ta dube shi, kaxo lfya? Ina safiyya? Ya
amsa lfya lau take, tace in gaisheki. Ina
amsawa, me yasa baka xo da ita ba? Ya goge
mata kwalla, tayi nauyi ne Umma bata jin dadi,
idan tayi doguwar tafiya, koda muka koma,
bayan daura aure sai da tayi xaxxabi. Ta dan
kada kai, tace Allah sarki, Allah ya raba su lfya.
Amin. Ya amsa sannan ya dubi Abba suka gaisa.
Kafin su kama wata maganar, muryar Manyan
yayin ta gauraye cikin falonm. Abba ya gaya
musu suna ciki, kowa ya shigo da kuzarinsa, ya
ga Umma a kwance sai yayi turus! Bayan sun
gaisa tasha magani. Abba ya kwashe abinda ke
faruwa kaf, ya gaya musu, kowa yayi shiru,
kawunansu sunkuye tsawon tym kafin Ya soja,
yace, yanxun Ina Maman take? Oho inji Abba,
gaba daya sukace oho? Ta bar gidan nne, Umma
tace tsakar gida na barya tsaye, ban sani ba ko
ta koma daki ko ta fice don ba sani xamuyi ba.
Duk tym din ta so fitarta, ficewa ta takeyi.