Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 4 of 9
BAKIN CIKI 1***12 Tace, Ita ma aunty ai ta
bingire, dube ta aza zaune take yinsa. Ta so kayi
breakfast dadin kana jiranka. Ta juya inda Mama
ke xaune tana famanxuba mika, Yayan ki zai fita
ne, ki fito ku gaisa. Tace,Gani nan. Suka fice da
Malami, ita kuwa mama bayita shiga ta wanko
Fuska ta fito. Suna bisa tebur ta same su fuska
ba walwala, ta ja kujera ta xauna, inakwana
yaya? Yace kalau, ya lazu Doktan ki?Murmushin
bai kai ciki ba tace, ai ni ban shi ba Yaya.Yace a
Yau kuma? Zamuyi waya ai, zan gaya
masaabinda kikace. Tayi shiru Aunty amina tace,
me yasami idanuwanki? Kamar sun kumbura? Ai
ba sa min ciwo, tace, to meyasa? Da alama dai
sun kumbura.Ta murje idon. Yayanta na cewa, ke
me zai dameki?Ita da take tare da lazy Dr. Suka
fara dariya, ita kuwayake takeyi. Ta sa abincin,
sai juya masa cokalitakeyi, ta kasa ci, da alama
tana son tayi matamagana ne. Amma ta kasa,
aunty amina ta kare mata kallo, tace wai
menene? Ta dago ido ta dubeta, tadubi yayanta,
jim kafin tace, Fandagori nake sonxuwa.
Fandagori? Me zakayi? Yayan ta ya
tambaya.Idanuwan ta suka yi rau- rau! Da kwalla
tace, ina sonxuwa ne kawai. Ya xura mata ido
yace, xo nan bebi.Ta taso a hankali ta zo gaban
sa ta tsaya. Ya kamo hannnayenta biyu yace, me
zaki yi a can? Bayan yaukwanan mu bakwai da
dawowa? Tace Umma na keson gani. Ya dubi
Aunty amina, yace kinji shagwabarbanza! Ke
kadai ke da Umman nan ne wai? To ba zaiki ba
ki ba, nan zaki zauna sai karshen wata. Ta
karamurtuke fuska. Don Allah yaya kayi hkr ka
bari in tafi. Ni wlh ko a motar haya xan iya
tafiya, ba sai direbaya kaini ba. Yace, motar
haya? Baki a tunaninki bebi,banso in sake jin
wannan maganar, karshen wata inada hutu zamu
tafi tare. Is dat clear? Ya fadi tare damatse
yatsunta da karfi. Tayi tayi ta kwace amma
takasa. Ya kara girgiza ya, ya kara fadin Is dat
clear? Ta kara cunno baki ta kauda kai. Ya saki
hannun yace je ki ci abinci, ta juya da gudu ta
haye sama.Aunty amina ta kwala mata kira,
Mama! Ya dagamata hannu, a kyaleta! Iya shege
takeji kwana biyu,ko baki lura ba? Tace haka ne
fa, ni ma ban ganemata ba kwana biyu. Ya dubi
malami yace, lazy man ayi sauri mana. Yace na
gama Dadi. Mu tafi kenan?Ya ce eh. Suka bar
tebur. Madam ta kwaso masajakar sa da hularsa.
Malami ya goya, ta sa jakar suka fito tayi musu
rakiya xuwa mota. Sai da suka fita,ta dawo cikin
gida. Kai tsaye wajen mama ta nufa,tana xaune
bakin gado ta kumbura suntum! Idanuwan ta sun
kada jajur! Ta kare mata kallo, sannan taxauna
gefenta, wai Mama me yake damunki ne?
Komunyi miki laifi ne? Ta kada kai. To me zai sa
ki tashihankalinki haka? Wajen Umma nake son
inje. Ai bahana ki akayi ba, tunda yace ki bari
karshen wata kutafi, sai kiyi hakr xuwa tym din.
Tayi shiru ba tace komi ba. Ta rungumo
kafadarta, wannan abu na banimamaki, kamar
yau kika fara xuwa garin nan? Dabakinki fa kika
ce kin fasa kara kwanankin da kikacexakiki,
balle ace matsa miki akayi. Tace sai da na
zokuma naji bana son zaman. To kiyi hkr,
tundaYayanki yace ba xaki motar haya ba.
Shikenan, yauwa autan Umma. Ni bari in je inyi
wanka, in dankwanta kafin rana tayi. Tace to,
auntyn ta bar dakin takoma nata. Ta aiwatar da
duk abinda take son yidaganan tabi lfyr hafo.
Bata jima ba, ta sunkuci jakarhannu ta rataya ta
yafa mayafi ta debo takalman tarike a hannu ta
sadado ta sauko kasa. Shigar ta falon ke da
wuya, wayar Al-amen ta shigo falon, gabanta
yayanke ya fadi, ta tsaya cak! Tana zare
idanuwan.Tsoron ta Allah, tsoronta kar karar
wayar ta tashi antyamina. Saboda haka tayi
azama ta nufi wajen wayar,ta daga kan taaje
gefe, ba tare da tayi magana ba,balle ta san
waye akan layi. Ta dan kara tsayawa, jim shiru
bata jin wani motsi ba, tayi hamdala ga Allah.
Taaje takalmanta ta xura tayi waje abinta.
Babufargaban komai ta doshi gate har tana
gaida masugadi. Suka amsa tare da fadin a dawo
lfya. Taceameen. Tayi waje cikin sauri ta bar
sashin unguwar tafito a sarari a inda ta samu
shatan tashi ta kai ta tasha. Tayi muguwar sa'a
fasinja daya akejira motarta tashi xuwa Minna.
Inda daga can zata sami MotarFandagori. Sha
biyun Rana Aunty amina ta farkabarcinta, ta
sauko falon kasa, tin daga nan ta faraganin
abinda bata sa ba ba, kayan abinci na aje
bisatebur yadda ta barsu. Mama ta bata kwashe
ta gyara wurin ba. Cikin ranta take fadin, lallai
yau Mama tsiyatakeji. Haushi ya isheta ta nemi
kujera tsakar falo taxauna ta shiga kwala mata
kira. Shiru bata amsa ba.Mamaki ya isheta, t
yunkura zata tashi idanunwantasuka kai bisa
waya, Ah ji wani sabon iya shege. Sumama! Ta
nufi kan wayar ta dauka ta mayar yadda take.
Tana jan tsaki. Ta hawo saman ta fada
dakinmama cikin zafinta. Ganin babu kowa a
dakin yasatayi turus! Cikin sanyin murya take
kiranta, mama! Kokina toilet ne? Shiru? Wai
malam yaci shirwa. Tabude bayin vata ciki.
Hankalinta ya tashi ta sauko dasauri tana kiran
Mama! Har waje. Daya daga cikin masu gadin
yake gaya mata ai ta jima ta da fita.Al'amarin
ya daure mata kai. Ta dawo falo..... Tana
mamakin mama. Karar waya yadawomata da
hankalinta, ta tashi taje ta dauka, hello! Muryar
aunty Rabi taji ta amsa. Hello aunty amina,Rabi
ce, tace nagane ai ya yara? Lfya lau wlh. Waime
ya smu wayar ku ne? Al- ameen ya kirani, wai
tunsafe yake neman layin, amma yana engage.
Tace, uhm.... Ke dai bari, ina nan ina ganin abin
mamaki.Kamar yaya? Tace, Mama ce daxun da
safen tacewaYayanta ita gida zata koma, yace ta
bari karshenwata ya kaita. Nima na rarrasheta,
har fa ta amince,wai kuma na tashi barci
yanzun, bata ba dalilinta cikingidan nan. Sannan
ina zaton ita ta cire mana kan waya ta aje gefe.
Cikin al-ajabi tace, to saboda me? Oho! Kuma
ba ayi mata komai ba? Wai zai yi mataRabi? Ko
da ma anyi matan ai be kamata tayi hakanba
ko? Tace gaskiya ne ka, ah to, ita da yayanta
ne.Ni ba babu ruwan. Tace, amma ai mama bata
dawannan halin, me yasa za tafar shi yanxun?
Wlh bakiji ba duk Al-ameen ya damu, nace masa
ya barizanyi tryn inji. Tace watakila don taga
kowa na rawarjiki ne da ita, shi yasa take son ta
lallace. Zata kuwayiwa kanta sakiyar da ba ruwa,
idan ta bari yaron nanya kubce mata. Aunty Rabi
ta numfasa tace, to yanxumenene abinyi? Tace,
yayan nata zan kira Yanxun in gaya masa ta
gudu, Allah ya sawwake. To ameen. Taaje waya,
sannan ta sake dauka ta lallatsa
lambobinmaigidan na Ofis, jimawa kadan ya
dauka, ta zayyanemasa kaf, abinda ke faruwa.
Nan take haushi ya rufeshi. Ya mike cikin fushi
ya fito daga Ofis, ya fadamota bai zame ko ina
ba sai tasha, jami'an union ya samu ya bayyana
masu kamaninnta, nan take sukabashi tabbacin
ta zo tashar ta shiga motar xuwaMinna tun safe.
Ran maza ya kara baci kwarai. Yafada motar sa
yana tambayar kansa, dama mama taiya irin
iskancin nan? Lallai zasu gauraya, zatayabawa
aya zakinta... Karfe uku da rabi mota ta aje
taabakin titi, ta fito ta gangagro saitin shagon
danliti, saidai shagon a rufe yake. Babu kowa
wajen. Ta tsayatana kallon kofar shagon kafin ta
wuce, tana tafe tanawaige ko zata ga Danliti ya
dawo, amma har ta dainahango shagon. Babu
alamun kowa. Taci gaba da tafiya ranta bace na
rashin ganin Danliti, xuciyartacike da tambayoyi,
tana hasashen menenemusababbin rashin xuwan
Dan liti shago? Tun dagakofar gida yara ke
kwala ihun mama oyoyo! Shi yasaUmma ta fito
har kofar sassan dauke da mamaki bisafuskar
ta. Suna hada ido tace ke kuma dga ina haka?
Ta kwaso da sauri ta rungume ta, Umma na!
Tayisauri ta dago ta, ta xura mata ido, meya faru
ne? Mekuwa Umma? Na dawo ne kawai. Ta wuce
uwar tabiyo bayanta, bata yarda da ita ba. Cikin
falo yara sunrufeta, tace, kuyi hkr ban siyo muku
komai ba, gakudin nan kuje ku siyo biskit. Ta
dauko Naira Hamsin ta basu., duk suka watse da
murna. Har yanxunUmma kallonta takeyi, tayi
dan murmushi tace, saikallona kike yi Umma?
Tace dole in kalle ki, kin shgokamar an koro ki.
Ni bawanda ya koroni, ke nake tamafarki Umma,
nace gaskiyya ni xan dawo. To inajakar kayanki?
Tana can, kamar yaya? Yaya ne yace baxan taho
ba, ni kuma na silalo na gudo. Ta daukisalati ta
sauke, kika yi me? Kanki na lfya kuwa?Mama ki
gaya min gaskiyya dawa kuka yi fada?
Taceumma ni ina fada ne? Da wan xanyi kuwa?
Umma kiyarda da ni, wurinki nazo. Ba zan taba
yarda dake baMama har sai Yayanki ya zo naji
ta bakinsa. Kuma wlh naji akasin abinda kika
fadam sai na bata miki raifiye da zatonki, kinji
nagaya miki. Na yarda, shikenan,Ina abbana? Ya
tafi kd, tayi 'yar dariya, Allah sarki inaango da
amarya? Yau kwanan su uku da komawa.Kije ki
zubo abinci ko sai kinyi sallah? Tace bari infara
cin abincin, yunwa nakeji. Ta tashi ta shiga ta
xubo abincin ta dauko ruwa ta dawo falon ta
xauna.Bata wani ci sosai ba, saboda cikinta ya
cushe dayunwa, don ko karin safe batayi ba,
bayan ta gamatayi sallolinta tayi wanka, cikin
kayayyakinta, dakegida ta dauko tasa. Ta fito
tace zata shiga sasa tagaishe su, daga nan zata
wajen Baraka. Umma tace daga xuwanki? Ba
inda zakije sai Yayanki ya zo najidalilin
dawowarki gida. Ta ya mutsa fuska, tace
kaiUmma! Barakara kamar wata bare, kuma wlh
damada xan tafi bamu sallama ba, na wuce, hkr
zanje nabata. Tace, tazo nemanki kinbi 'yan
abuja, amma bainda zaki, kinji na gaya miki. Ta
bata rai sosai. Ta jefar da gyele bisa kujera ta
koma dakinta. Ummatace, in kinso kiyi bindiga,
ba fushi ba. Ta shige natadakin. Jimawa kadan
mama ta fito cikin sanda ta lekafalon, daga nan
tana jiyi sautin Umma tana karatunQur'ani. Tayo
sanda takalmin ta a hannu, ta daukigyalan tayi
waje. Bata shiga sassan ba, kai tsaye waje tayi,
sauri take kar wani ya ganta. Yaran natakaratu
ta gaida Malam ta fice. Ga ta nan ga ta nan
harkofan shagon Dan-liti, farin ciki ya lullubeta
da tahango shi a bude. Sai dai kash! Tana isowa
ta iskeayuba ne a cki. Tayi masa sallama, cike
da mamakiyake kallonta har ya kasa amswa,
gaba daya tsigar jikinsa ta tashi. Ya xura mata
ido kafin yace, sannuko? Me za abaki? Tace ba
komai, don Allah ko danlitina nan? Ya kara
matsowa ido waje yace, a'a bayanan. Tayi dan
shiru jim, kafin tace yayi nisa ne, eh to,kano ya
tafi siyo kaya, amma watakila xuwa anjimako
gobe ya dawo. Ta numfasa cikin rashin jin dadi,
tace, shikenan nagode. Zan dawo xuwa goben. Ya
nadan murmushi yace Allah ya kaimu. Ta wuce
ta komagida. Ayuba bai gasgankanta idonsa ba,
sai da ya fitoya bi bayanta da kallo. Ya dora
hannu bisa kai yace,na shiga uku, amma Dan liti
anyi mugun dan iska! Baikoma cikin shagon bisa
benci ya xauna yana jimami! Mama kuwa tana
tafe har tuntube tayi saboda takaicinrashin ganin
Danliti. Ta shige gida can sassan sukawunanta.
Hajiya Gaje tace, a'a saukar yaushe? Tace daxun
nazo. Lfya dai ko? Tace kalau. To yamutan
Abuja? Suna lfya, ina su Dan lami? Ko sunsami
makarantar? Tace ai kuwa makrnta ta samu,
shekaran jiya ya tafi, ana can sakkwato. Allah
yataimaka. Amin. Umma tayi sallam sassan
suka amsata dubi Mama tace, Abbanki ya dawo
yana kira, tamike tana fadin to. Hajiya tace,
ashe autan Umma andawo? Tace eh wai hankalin
ta ne ya dawo gida.Sukayi 'yar dariya, Haj. Gaje
tace, ah shagwaba! Sai da auran yazo ake kwa
xucin gida? Kina wasa neyarinya. Suka fice suna
dariya. Abban yana falo azaune, ta shigo da
fara'arta, Allah ya taimaki maimartaba! Yace zo
nan. Ta matso jiki babu kwari tazauna akasa
gefensa. Mama me ya faru kika baroAbuja ko
jakar kayanki baki dauko ba? Tayi kasa da kai
tace, Allah abba babu abinda ya faru, cewa
nayizan dawo wajen Umma, shine yaya ya hana,
ni kumana gudo. Ya xura mata ido, yace, me ya
sameki? Kina ma gani kamar ba laifi kika aikata
ba? Haka kawaiki kamo hanya ki taho ke kadai,
ba tare da saninkowa ba, idan wani abu ya faru
dake, ya kike so mutane suyi? Wannan rashin
hankali ne, irin wandaban taba sanin ki da shi
ba. Ina fatan kuma daga shiba zaki sake ba? Ina
fatan kinji da kyau? Ta kara kasa daidon tace, yi
hkr Abba Insha Allah ba zan sake. Yanumfasa
yace yanxun saboda Allah kinsan awane
halisuke? Zaki gamu da Yayanki ai, kala bazan
ce masaba, yayi miki duk abinda yayi niyya.
Umma tace ni faabin daure min kai yakeyi. Wai
mama ta gudo? Ta kuta tana zuba mata harara.
Abba yace, tunda daiAllah yasa ta ido lfya,
mungode masa, sauran magankuma sai yayanki
yazo. Idanuwanta suka kwalla tana,duban abba
tace, Allah abba bada gangan nayi ba,kullum
mafarkin gida nakeyi, shine nace ni dai zandawo
in ganku. Yace, to kin ganmu ko shi kenan?
Tace ka gaya wa yaya idan yazo kar yace zai
bigeni.Umma ta karbe, ai ko shi bai ce ba, ni
zan sashi.Kuma tunda abin naki ya zama tsiya
anan din zaki tazama, na ga inda zaki samu ki
dauki wayar. Karyartsiya kikeyi! Ta turo baki tayi
shiru. Abba kuwa 'yardariya yayi yace, dama
kinyi shiru da bakini, da kanta zaki ji tana
neman hanyar komawa. Ba kuma zatanba,
yauwa! Ki ma sani. Ta shiga murza ido ko
alamarbacin rai bata ji ba, tayi shiru tana
sauraren suna tazazzaga mata tsiya. Ita bama
wannan ce matsalartaba, kusan ma da za'ace ba
zata koma din ba, ita adadinta. Damuwar ta
daya, tayi tozali da Danliti ko hankalinta ya
kwanta. Domin ko a daren yau ma takuma yin
mafarkinsa irin na jiya. Ya kira ta amsakiransa
har taje gunsa. Da wannan azalzalar songanin
Danlitin ta wayi gari. Allah-Allah takeyi, abba
yabar gidan, ta sulale taje ta duba ya dawo.
Kafin lokcinfitar sa tayi har tayo wanka ta chaba
ado. Yayan kuwa sammako ya bugo mata, karfe
tara dai-dai yanaparkin kafar gidan. Ya bude ya
but, ya kwasokayanta, da ganin yaddayake ya
wurgo jakar kasa zaitabbatar da afusace yake
kalla ya iso wajen dasurinsa yana masa sannu
da xuwa, ya amsa, kalla yakwashe kayan ya
shige da su cikin gida. Yaya abdulqadeer ya biyo
bayansa, sallamar sa hade takeda kwala wa
mama kira, Ina bebi? Abba da Ummasuka fito
falon. Yaya Babba sammako kayo haka?Abba ya
tambaya, yace ina fatan Bebi nan na. Yace ,ta
iso tun jiya, zauna mana! Yace ina take
tukunna?Umma tace tana dakinta tana jinka. Ya
wuce dakin abba ya bishi. Mama na makure
karshen gado, kaitsaye ita ya dosa, kafarsa daya
ya dora bisa gadonya mika hannu zai janyota.
Abba ya riko shi yanafadin, yi hkr Yaya babba ka
dubeni ka saurareni. Yadubi abba ransa bace
yace, abba yarinyar nan tana dahankali kuwa?
Ban iya barci ba fa saboda bacin ran abin da
tayi min jiya! Tana nufin tayi girman da ba zaa
gayamata taji ba? Saboda muna wasa da ita?
AbbayaCe, Allah ya huci zuciyar Soja. Zauna
kaji, zaunanace ko? Ya zauna yana kallonta
xuciyarsa natafasa. Umma tace, wlh da ka kyale
shi ya tattabajikinta ko hankalinta ya zl jikinta.
Abba yace ya dai karya ta kike so, kinsan irin
dukan da zai yi mata?Yadda ya hassalo din nan?
Ya juya kan Yaya yacigaba. Dubani nan Babban
Yaya, kayi hkr don girmanAllah, ni kaina na san
Mama bata kyauta ba, kumatun jiya na nuna
mata kuskuranta. Ni tunani na ma kowani abu ne
ya faru tsakaninta da maidakinka. Kayi hrk
babban Yaya da yardar Allah ba zata sake
ba.Idan kuwa har ta sake, duk hukuncin da ka
yankemata kayi daidai. Ke kuma bashi hkr,
maras kunyakawai. Tuni hwaye ke ta kwaranya
bisa kuncinta,murya na rawa tace kayi hkr yaya
don Allah. Ya ballomata harara yace, ga
komatsanki can na kwaso miki, idan na sake
ganin kafar ki cikin gida na, sai na karyaki.
Kuma daga yau mun bata, kar sake min magana!
Abba,Yace Allah ya huci xuciyar Soja, ai ba
zatasake ba. Ta ma sake! Ta rarrafo da sauri, ta
rungumebayansa, Allah yaya bazan sake ba kayi
hkr. Abbayace, Allah sarki tsaknin babban Yayya
da bebinsa, ai ba ajin kansu. Ko? Zuciyarsa ta
fara sauka, sannua hankali ya huce, ya jawo ta
gefensa ya zura mataido, ban sanki da rashin ji
haka ba Bebi na, sabodahaka kar ki kara idan ba
ki so mu bata. Ina fatan kinjini? Kwallan ta suka
wuce da gude, tace Allah ba zansake ba Yaya.
Ya share mata hwayen, ya wuce, shikenan, ki
zauna wajen Umma, shi kuma lazy Dr.Din me
zan gaya masa? Tun jiya yake damun mu.Tace ai
zan dawo. Haka xan gaya masa? Ta amsa daka,
yace an gama. Ya dubi Abba yacigaba,
munshirya abba, Umma ki yi hkr idan ta kara
guard roomxan sata. Tace yayi kyau. Abba yace,
Allah ya so ki 'yar nema, da kin jigata. Suka
fara dariya, yace dukda haka sai na dan tabata.
Ya duma mata dundutsakar baya, ta fasa kukan
shagwaba, tana susarbaya. Ya mike yana dariyan
mugunta, yayin da takefadin wayyo Allahna. Ka
dai jibgeta da wayau, injiAbba, yace ladan
sammakon da nayi, ta hana min xuwa ofis. Suka
koma falo suka gaisa. Karin safekawai yayi a
gurguje ya shiga sauran sassan ya
gaidakawunansa, ya fito ya sake dibar hanya.
Yau maAbba kd ya sake tafiya bin wata kwangila
da yakenema. Bayan sun gama ayyukan gidan.
Ummakwanciya tayi, ba dadewa barci ya
kwasheta. Nan da nan Mama ta kwashi takalma
da gyale tai waje ta nufishagon danliti, amma
kash! Ayuba ta sake samu.Dan liti bai dawo ba
kamar zatayi kuka, ta tsayadauke da tagumi.....
Ayuba yace, karki damu xuwaanjima, ninasan
bazai wuce yau ba. Tanumfasa muryasanyayetac
e, zanzo anjiman, Allah ya sayadawo
lokacin.Yace, amin ta juya ta fito ta danjima a
tsaye batasan abinda ke mata dadi ba.Salalau-
salalau ta komagida, ta fada dakinta, ta
kwantaranta na mata daci kamar tayitsuntsuwa
tabi shi kanon. Ta juyanan, tajuya can duk inda
ya jefa idonta,shi take gani yamiko hannayensa
yana murmushi.Yana fadin zomana! Jikin ta
gaba daya ya hauciwo, zazzabi naneman rufeta.
Har cikinkasusuwanta take jin ciwontamkar mai
sanyin kashi. Karfehudu bayan tayi sallar
la'arsar tasake sabon wanka ta sauya
kayatacewaUmma zata wajen Baraka.
Ummabatayi musu ba,saboda sun warware
matsalaryayanta. Cike da farinciki ta bar gidan
kuma xuciyarta najaddada matatabas taga
Danliti. Wayyo Allah! Ranta ne kawai kesaka
mata haka, saboda ta zaku tagashi, ayuba, ne
cikin shagon ahain yanxun kam ya rasa kalmar
dazai gaya mata. Ta zura masa ido,tace, kodai
guduyakeyi idan ya hango? Ya kada kaiyace, wlh
baidawo ba ne Mama. Ashe kasansuna na nan?
Yayidan murmushi yace, haba kamarwani bako a
garin?Asalin sunanki sakeena, ko banfada daidai
ba? Fuska sake taamsa, haka yake, amma
abokin kayacika yawo, dama haya yakedadewa.
Yace, kin sansha'anin kasuwa, watakila ma
bakano kadi ya tsayaba. A fada nan ne, a fada
can ananeman halali. Tacegaskiyya ne. Barin in
tsallakawajen kawata, may bekafin in fito. Allah
ya taimakeni yadawo. Yace, Allah yasa. Kin
damuda yawa, neman me kike masa ne?Ta gyara
tsayuwa tace, a'a tsakanida shi ne, so kake
kaji? Ya kada kai yana 'yardariya yace, wane
niinji sirrin ku? Sai dai in ce Allah yadawo miki
da shilfya. Tace amin, barin in je indawo. To
shikenan. Tabar wajen ta tsallaka titi.
Al'amrinkara daurewa Ayua kai yakeyi, yama
rasa yadda zai fassara shi.Kamardaga sama
wata mota (ToyotaCarina) tayi fakin akofar
shagon, me ayuba zai gani?Mutumin na sa nea
ckinta. Yayi azama ya fito dashgo, yayin da shi
maDan liti? Yace, siyo ta nayi. Motar?Ya
tambayadauke da mamaki. Yace, eh mana.Ya
bashi hannu suka tafa, ka tsulana tsiya mutumin
na a bayankasa, ya akayi? Yace yadda
akayikenan? Kasan itamota akwai kara aji, shi
yasa nashiyo, kada yarinyarnan ta dauke ni wani
gara. Yacekai! Don Ubanka dalabari, shigo dai
daga ciki! Yayi dangutun tsaki, tanata xuwa
nemana nakoa? Ya sakibaki ya na son kallonsa,
ka ma sanikenan? Ahaf! Kana wasa danine.... Ya
wuce ya bude but, yasake juyo wa ya kalleshi,
ka na nan tsaye? Ga kaya kazoka taya ni
cirewamana. Ya tako a hankali ya tsayagabansa,
kana bantsoro Danliti. Wlh kabi a hankaliMalam
mu kwashikaya in ka na kwasa! Mts.. Ya jatsaki
ya shigo fito da kaya yanashigewa da su shago.
Ayuba natayashi har suka kwashe. Tsakar
shagonya baza 'yartabarma ya zauna. Ayuba na
bisakujera, kofin ruwaguda ya shanye, ya aje
kofinsannan ya dubi Ayuba,duk kayi wani
la'asar, kai banza newlh, yace ai doleabin nake
da ban tsoro. Tsoro?Tsoron me xanji? In gaya
makayadda kasan Tv haka ake nuna
minitaakofar shagon nan. Sakeena a tafinhannu
na take,sai yadda naga dama da ita. Yacigaba
da kada kofardamarsa. Ayuba yace, xan
bakashawara mutumi na,tunda ka nace, ka
matsa sai da kabirkita hankalinyarinyar nan, kuyi
aure kawai kahuta da kwashe- kwashe.
Sakeenakarshe ce wajen kyau, ni ban mataba
sanin haka ta hadu ba, sai danatsu anan
tanamin magana. Kaga idanuwan takamar
madara!Mts.... Ya dan kada kai. Yaci
gaba,yarinyar nan inaiya ma cewa idan ka aure
ka hutamutumi nan. Adage yake kallon sa
tsawon lokacinkafin yace, aure? Wa zai aureta?
Kana hauka ne? Idan na aure ta,insiyo mata
kima? Yadda tageni,haka kowa sai yazage ta a
garin nan. A'a danliti! Karika sayan tsoronAllah
a ranka... Ya daga masahannu, ya isa
hakaAyuba! Naga alama kai ma sai nasaan
daure minbakinka, kar kaje kana min
shegensurutu a gari. Domin daddawa bazata
gayawa manda baki ba. Saidai ni bana zurfi
shige-shige irinnaka. Shi yasa nakeba ka
shawara ka aureta. Malamba ruwanka! Ni
banshakkar Uban kowa, irin ta irin tamasu taurin
kai biyuna baro da ciki a garinsu. Daya akano,
daya a zariya.Zaman da nayi a can kafin in
dawonan. Ido waje yace, iye! Kwarai!Me zai
danne ni? Kila ma yanxuduk sun haihu, wa ya
sani? Ayubaya kara la'asaryana kallon yadda
yake kadakafarsa, ko ajikinsa.Wata 'yar fulani ta
leko tana fadin,hannun ku dai! Adama fura? Dan
liti yace, dama tahamsin. Ta sauketa shiga
damun fura. Dan liti yafito ya zauna bisa benci
yana hirada 'yar fulani ya bar Ayuba.
AwadayaMama tayi a daddafe wajenBaraka, duk
hankalin tayana can tunanin ko Danliti ya iso?
Suka fito tare zasu wuce Baraka tace, Yau ba
zakishiga wajenkishiyar taki bane? Ta ya
mutsafuska, tace, kullumnazo sai na shiga
wajenta? TaceHala Dokta yayi laifi ne, ni nagako
maganarsa baki min ba. Tace ninadaina yayinsa.
Tayi 'yar dariya tacemama kenan.Ashe Dr, zaiyi
laifi har adainayayinsa? Dakata, kina nufin kin
warwareranar da akasanya miki? Tabbas haka
ne,domin hankali na ya fikwanciya da kai.Yayi
wani saurayinmurmushi cikinnishadi, nagode
sakeena, kin cetorayuwa ta, ban sanirin godiyar
da xan miki ba. Dadiya rufe ta, ta rausayakai,
nima na gode, kin gode? Menayi na godiya? Dole
ka godewa wame sonka. Ya kara jingina da
motayaxura mata ido, kamar na sace kisakeena,
kalaman kina gigitani, gashi banzo miki dakomai
ba, balle inbaki tukwici. Ta kada kai
tanamurmushi, ban sankomai naka. Ba kiso nake
na, al bahaka bane nufiba, so na gaskiyya baya
bukatarkudi. Allah ko? Eh mana. Kin
finigaskiyya. Amma duk da hakayakamata ace
na zo miki da waniabu, hausawasunce yaba
kyauta tukuici. Kar ki jikomai kyauta saikin ture
sakeena, tunda kika zabeni. Tace gaba
damurmushi tana fadin, to Allahyasa. Awa daya
da rabisuna tare, sannan sukayi sallama,ya
wuce, ta shigo cikin gidan.Umma na kwance bisa
doguwarkujera afalon, ta shigo simi-simi
zatawucem umma tace zonan Mama! Ta dawo
gunta zaunabisa kafet. Ummata tashi zaune ta
dube ta tsaff!Kafin tace, ke da akece kije ki gaya
masa an sanya mikirana, me ya kaikidadewa. Ta
sunkuyar da kai, batatanka ba, ban gane miki ba
Mama,kina so a zage mu a garin nan ne? Bikinki
fah saura wata uku ko kinmanta ne? To muba
kananan mutane bane, ko kingaya msa ko
bakigaya masa ba, ba zaki kara fita ba! Kinji na
gayamiki! Ba zaki kawo mana sakarciba, dan na
lura taketaken ki kenan. Idan kuma ba hakaba,
abbanki zai maida ki minna koabuja, tashi ki ban
wuri! Ta mikeda kyar fuska kumbure, ta
wucedaki. Umma ta bitada kallo ganin yanayim
fuskarta yasa ta kama bakicike da mamaki. Ta
jima zaunesannan ta tashi tarufe ko ina ta kashe
fitulu ta samiabba a daki. Waikasan yarinyar nan
sai yanxun tashigo? Ni fah ban gane
sauyinyanayin ta ba, ina mata fada tanabatarai,
yace ai na leka ta falon bakina hango su
sunawasu dararraku, ni ban ganewanene ba,
amma yayishigarsa tsaf harda motarsa. Kajiba?
Allah ya sagobe da kanka zaka fita ka
bashilabarinta. Ai kamarkin shiga raina,
kwanciyar nan danayi abinda nake ta tunani
kenan,karta hadu da romon baka, yajikirtatunani
nta. Ya kamata ka hanzartayin wani abu.
Yazama dole kar girma na ya fadi.Haka suka
kwan daabin cikin xukatansu. Ita kuwaMama ba
nantunaninta yake ba, hankalintakwance tayi
barci cikinshaukin son dan Liti. Da safe Abbaya
xaunar da ita yayi matanasihohi tare da jan
hankali, akankuskuranda take neman aikatawa.
Har yayi,ya gama batacekala ba. Abinda bai sani
ba, shinebabu kalma dayada ta shga kanta,
domin kuwa tananan akan bakanta,duk ta inda
za'a bullo mata. Danliti ne, ba sauyi.Bayan sun
gama ayyunkan su, tayiwanka Umma tayi barci
ta sadadata fice kamar jiya. A shago ta
samiDanliti, koda ganinta, sai yai tsayea kofa,
bakinsahar kunne ya mike, ah! Sanyinraina
kamar kinsantsundum nake cikin tunaninki.
Tatsaya rungume dahannaye ta zuba masa ido.
Tace,hum! Haka naji.Baki yarda ba kenan? Dubi
lissafinda nakeyi dole na aje shi don
banafahimta. Tayi dan murmushi, to yaka
kwana? Ya amsa barcin nan baiyidadi
basakeena, ko'ina najefa ido ke nakegani, kamar
zanzautu nake gaya miki. Tayi dariyafasa min
kai. Saiga Ayuba ya shigo, manya manyainji
kanana! Tadubi Danliti tace, ka yarda mugaisa?
Ku gaisa sanyin raina badamuwa. Ayuba ya saki
baki au saima kayarda zamu gaisa? To matar
kace?Ya kada kai,wane ni? Tafara dariya tana
fadinkadai ina kwana?Yace baxan amsa ba. Dan
liti yaceto idan bazakaamsa ba, ka fita ka bamu
guri,yace ai ko baka ce ba.Ya juya ya fice mama
na dariya,tace wlh baka da dama korarsa
makayi? Ah to yadawo ne? Ta kadakai a'a, yace
to shigo daga cikimana kya ta tsayuwaanan, tace
wlh karka damu datsayuwata. Yadan batarai me
yasa? Tace dan Allah karkabata ranka, yasaki
fuska nima na hkr banso natakura ki. Ammadole
kici wani cikin shagon nan,me xan miko miki?
Ta kada kaidon girman Allah ka barshi.
Yaceanan nezamuyi fada idan har baki sa
minalbarka ba. Me zanbaki? Ta sa hannu cikin
wani katontire ya dauki mintguda daya tace, na
dauka Allah yakawo kasuwa. Yazura mata ido
kawai, bai ce kalaba. Tayi murmushi tabare mint
din ta ajefa baki, kaganinama sha. Yace yanxun
duk girmanshagon nan ki rasa abinda zakidauka,
sai banzan sweet. Ta rufebaki tana dariyakafin
tace, baka gane manufa ta bakenan. Na
daukisweet ne saboda mahimmancinkalmar, kai
sweetheart dina ne, dole in sweet ashagonka.
Yayi 'yardariya yace, shagon mu zakice.
Toshagon mu. Yauwa yanxu najimagana. To ki
kara sweet dinmana, tunda ita kika fiso, zan
karabari sai zan tafi.Yace nabari sakeena ta. Sun
jimasuna hira, sai datakin taci tashin mama
daga barci,sannan tace masazata koma gida. Ya
dauki leda yacika mata da kayanzaki, ya bata.
Ta sa hannu ta amsatana ta xuba godiya. Ya
dago kantaya fito, barin in dan taka miki.Tace ka
barwa shagon wa? Bayanka kori Ayuba? Aiko
bakin kwata na rakaki ko? Ta fito waje tana
dariya, kawai saiga Barakata tsallako titi. Ido
sukayi da junabakinta har kunne,ta bar Dan liti
tsaye tayi gunta,kawata! Ta tsaya tanamata
duban da yafi gaban mamaki? Tace ban ganeba?
Kamar yaya? Daga shagonDanliti naga kin
fito,eh menene? A tunani na kodasiyayya ce,
ajinki ya wuce ki yi ta ashagon Danliti. Amma
sai nagakamarkun fito tare kina dariya. Ko
idonane? Tace kemuguwar 'yar sa ido ce wlh,
bamaganar sa ido bane,wai da gaske daga
shagon kika fito?Daga can nake.Amma dai
siyayya kikayi? Barakake kika haifeni ne?
Wannan irin tambayoyi, me yadame kine? Ta
fizge ledarhannunta, ta duba idan sweet kikeso
ai gara kitsallaka shagon Okundiri ki siya, yafiye
miki mutunci.Arnan? A waje na Okundiri ya
fiDanliti mutunci. Tagyara fuska tace, ni kuma
wajenabai fishi ba. Fadazamuyi Mama? Yaushe
kika faragood time daDanliti? Ban sani ba, ta
nuna tace,kina nufin yayi nasara kanki?
Baikamata ba, domin a iya sanina, bayaudara Dr.
Kike ba. Yaushe kikacanza? Ban sani baBaraka.
Haba mama, ai ko laifi Dr.Yayi miki bagirmanki
bane ki huce haushinkiwajen Danliti. Kigayawa
manya mana ayi masafada. To Ummamtsw.....
Ta fige ledar ta, ta dawotana kara zuba tsaki.
Baraka kuwatsaki tayi musamman da tagaMama
ta sake komawa wajen Danliti. Allah kadaiyasan
me sukace. Ta dai ga Mamata wuce, tanadariya.
Gabanta ya kara faduwa, tadafe kirji
tanaInnalillahi wa Inna ilaihi raju'un!Wlh sai
Umma tajimaganar nan...... KARSHE SAI MUN
HADU A NA BIYU
So Ko Kauna?
Go to Home
BAKIN CIKI (TRUE LIFE STORY) 2***1 Ta wuce
inda aka aiketa kamar zata tashi sama sbda
saurin ta dawo gida.Ta zube wa inna cefane,ko
zama bata yi ba ta fara fadin "inna mama na
cikin hankalinta kuwa? Tace,me tayi? "Kin san
danliti ya dawo....""Danliti?" Waye shi? Dan
gidan buzu mai shayi fa inna."Oho ,ina jin ki me
yayi? Lokacin da aka yi bikin yaya Abdulrahman
danliti yaga mama ya nuna yana son ta wlh a
lokacin ko kallonsa bata yi amma ban san yadda
aka yi ya shawo kanta ba,ynzun nan na gamu da
ita Ta fito shagonsa leda cike da kayan sweet."
Inna ta dafe kirji ido waje,mama fa kika ce? Wlh
inna ni kaina mamaki ya kusa kashe ni.Danliti
dan iska!"Inna tace,mun shiga uku ni saude wai!
Ban ga ta zama ba dole in bincika na tabbata
gidansu ba'a sa ni ba! Kai mama kamar mai
hankali,me zai tsone mata ido a wajen yaron
nan?Kai Allah ka shirya mana yara.Bari babanki
ya shigo Insha Allahu yau din nan za ni gidan
gara a yiwa tufkar hanci,kar ya kai mu ya baro!"
Ya kamata inna,ni ina ganin ma kamar fada
suka yi da Al-ameen don tun dawowar ta bata so
ayi maganar sa."To ba sai ta fadi ba,ko yayyinta
sun isa su kira shi su sasanta su balle ga
iyayensa a gari."Ni ma dai hakan na gaya mata.
Tace min babu ruwa na" "ita mama din ta fadi
hakan? "Ko yanzu ta maimaita min kiris ya rage
mu yi fada a titi,inna ta kuta,ta numfasa,kai
jama'a yara halin su sai su,Ita fa ta kawo shi ba
dole aka yi mata ba?Ta zabga tagumi bakin tana
maimaita salatin Manzo,Da azahar mahaifin
baraka ya shigo gida,inna saude ta maida masa
halin da ake ciki.Nan da nan ya bata umarnin
taje ta bincika,ai bata bata lokaci ba,cikin
tsakar ranar nan ta kama hanya ta nufi gidan
uban dawaki.Umma na daki tare da abban shi
ma shigowarsa kenan gidan aka gabatar masa
da abincin sa yana ci.-Inna ta shiga suka gaisa
sannan suka koma dakin umman.Bayan sun
gaisa da en hirarrakin zumunci kafin
tace.magana ce tafe dani yaya amma ki duba ko
alhaji ya gama cin abincinsa zan so in fade ta a
gabansa."Nan take jikinta ya mutu,tace me ya
faru saude?"To magana ce data shafi mama na
rashin jindadi shiayasa nace ba zan bari ta
kwana ba dole in zo in bincika,sai dai alhaji shi
yafi dacewa ya sani,tunda nayi sa'a yana
nan.Tayi dan tagumi......Subhanalillahi!Bari in yi
masa magana.Ta mike jiki a salube ta shiga
dakin abba ta iske ya kammala tace,wai magana
ce tafe da saude idan ka gama ka taso muje,To
muje gani nan".Ta gyara zama ta maida musu
abinda baraka ta gaya mata umma ta shiga tafa
hannu,abba kuwa sai daya mike."Kar dai ace shi
ne yazo jiya da daddare?Lallai biri yayi kama da
mutum,ina maman take? Umma ta dube shi ido
taf da kwalla,tana daki. Kira min ita!Ta mike ta
fita,har suka dawo tare babu wanda ya tanka
sbda tsabar mutuwar jinin jikinta,a darare ta
karaso dakin tana fadin,inna sannu da zuwa."Ta
zuba mata ido,ke ma sannu."Ta gaishe da abba
da umma na mata kallon mamaki,ta dube shi
suka hada ido,tace abba ga-ni" yace,wanene
yazo gun ki jiya?Ta sunkuyar da kai,tayi
shiru,ya daka mata tsawa,ko baki ji ne?Nace
waya zo gun ki jiya? Tana rawar lebe tace dan-
liti?"Kin kuwa san ko waye danliti a garin nan?
Tayi shiru,mama ni kike so ki mayar tsohon
bnza,ki tozarta?jiya me na gaya miki?To ni ba
hayaniya na kira ki mu yi ba domin a iya sani na
ke mai hankali ce,kin san abinda ya dace,kin fi
kowa sanin cewa saura 'yan watanni suka rage
bikin ki.Sannan idan kika nutsu kika yi tunani ba
mutuncin mu bane daga ke har mu ace an gan
ki,kina karakaina a shagon wani ma,balle danliti
sbda haka nake umurtar ki daga rana mai kamar
ta yau,bana son in sake jin wani labari
makamancin wannan!Ina fatan kin fahimce ni?Ta
kara sunkuyar da kai yayin da idanuwanta suka
fara tsiyayar ruwan hawaye,umma ta muskuta ta
karbe "kin bani mamaki ba kadan ba mama,wai
ma in tambaye ki,me kike nufi da bin sa har
shagonsa? Shiru babu amasa,umma ta
cigaba,wannan katon sakarci da me yayi kama?
A zaton ki abin birgewa ne yadda 'yan mata ke
tsayuwa kofar shagon samari suna amsar abin
hannun su?Ban taba zaton hakan zai fito daga
gareki ba mama kuma mun saurara miki ne
kawai sbda wannan shine karo na farko da irin
haka ta faru!" Inna tace,kin ga gidan nan da
dukkan jama'ar gidan dake cikin sa ana ganin
girma da mutuncin su musamman mahaifnki,don
girman Allah kar ki bari wani ya rusa wannan
ginin,ya hure miki kunne ya kai ki ya baro,kin ji
mam? Ta goge kwalla bata ce uffan ba,abba
yace,to mun ci mun rufe anan bana son ki sake
aikata wani abinda zai sa ayi miki zama irin
wannan,kin ji ni? Ta amsa da kai tana goge
kwalla.umma tace tashi maza muje ki dauko min
ledar kayan da aka ce ya baki,a iya sani na dai
baki da yunwar su,maza tashi muje!Ta mike da
kyar umma ta tasa ta suka je dakin ta dauko
ledar.Umma ta fizge cikin zafi tace,Allah yasa in
sake gani ko ji sai kin sha mamaki!" Ta fice ta
bar dakin,ta bar mama cikin tashin hankalin da
bata taba jin irinsa ba,har inna ta gama zamanta
ta bar gidan mama na aikin kuka a daki domin
dai tamkar sun kara debo soyayyar danliti ne sun
kara antayawa cikin zuciyarta.Ita wannan ranar
da suke kwakwazon an sanya mata ta jima da
manta saurayin ma balle ranar,ba shi a idon ta
ko birnin zuciyarta.Al'amarin ya daurewa
iyayenta kai,shin wai me mama take nufi da
kukan ta? Tambayar zukatan su kawai suke yi
amma basu da tabbacin amsa.Karfe takwas da
rabi cif! Lokaci ne da motar danliti ke fakin a
kofar gidan uban dawaki,kai tsaya ya aiko yaro
a kira masa mama,abba na nan a falo yana
gadin zuwansa don haka yace da yaron yaje yace
tana zuwa. Umma ta fito masa da kullin ledar
kayan kwalamar da ya ba mama Abba ya karba
ya bi bayan yaro kamar jiya,yau ma yana harde
jikin motarsa yana kada mukullai sai dai yau
kananan kaya ke jikinsa,gaba daya ya firgita
kofar gidan da kamshin turare.Yana hango uban
dawaki tilasa ya gyara tsayuwa yana 'yan kame
kamen gulma ko kafin ya karaso ya tsugunna
yana fadin,sannu alhaji,yace yauwa sannu,ya
sake fadin ina wuni? Lafiya kalau,mike abin
ka,magana zamu yi,ya mike a hankali yana
sunkuyar da kai kamar muminin gaske.Abba
yace magana guda daya ce nake so zan gaya
maka danliti,'ya ta sakeena na riga nayi mata
miji,tuni aka sa musu rana har ma lokacin ya
kusan zuwa da yardar Allah sbda haka ina rokon
ka da girman Allah kayi hakuri ka nemi
wata,daga yau kar ka sake zuwa gun mama don
tana da miji,ina fatan ka ji ni? Ya dan yi shiru
jim kafin yace naji alhaji amma nima ina roqon
arziki ka bar ni in rinka zuwa muna gaisawa,tnda
ba'a daura ba.Wlh..."Abba ya katse shi,ba zai
yiwu ba danliti domin koda babu alkawarin wani
akan mama kai kanka ka sani zai yi wuya ka
sami auranta,sanin kanka ne kaf garin nan babu
wanda ya san tushenka,kaje kayi tunani
mana.Ya saki baki yana kallon abba ran sa a
bace,abba ya mika masa keda yace ungo
nan,yasa hannu ya karba kafin ya cigaba da
fadin,abubuwan daka bata ne dazu tunda ba
auranka zata yi ba bai kamata ta amshi kayan
ka ba.Don Allah kayi hakuri ka nemi daidai
kai,sai da safe.Ya juya ya shige gida abinsa ya
bar danliti a tsaye. )Ya kara harde kafafuwansa
yana irin murmushin mugunta,sannan yace ko
banzo ba ita zata zo wajena,koda kuwa kasheta
zaku yi ta dawo.Dama ai zuwan nawa na hure
kunne ne ba wai neman nake da gaske ba."Yayi
er budurwar dariya ya bude motar sa ya shiga ya
sake fadin,sai ni dan gidan buzu mai shayi taba
ni kaga tsiya da bala'I!Ya ba mota wuta yaja ya
bar harabar gidan hankalinsa kwance.Sabanin
mama da take ji kamar ta saci jiki cikin daren
nan taje wajen danliti shiyasa tayi ta leken
falo,amma kash!Abba da umma sun ki tashi har
dare yayi sosai suna tattauna zancenta.Daren
nan bata yi barcin kirki ba sbda bakin cikin an
hana ta fita ganin danliti.Gari ya waye ko alama
umma ta ki sakar mata fuska,sam abin bai
dameta ba Allah- Allah take yi kowa ya kama
gabansa,itama ta samu ta sulale,ai kuwa abba
na fita karfe goma umma ta gama abnda take
yi,ta dare gado kamar yadda ta saba barcin
safe,mama ta gama caba kwalliyarta ta sadada
ta bar gidan.Ta kwarara sallama kofar shagon
danliti,ya taso cike da fara'a yana amsawa kafin
yace,a zatona ke ma zaki juya min baya ne,har
na fara shiga damuwa,jiya sam ban yi barci
ba.Ta dube shi cike da tausayi tace nima haka
danliti ko gyangyadi ban runtsa ba,me zai sa na
juya maka baya alhalin na san cewa nima zan
cutu? Ya zura mata ido a marairece yace,abbanki
ya nuna baya so na ban san yadda zanyi da
rayuwata ba sakeena,kar ki bari ciwon zuciya ya
kama ni.Kwalla suka taru cikin idanuwanta tace
ka daina fadar wannan maganar don Allah,in ka
ga na rabu da kai to sai dai su kashe ni in daina
numfashi,zuciya ta kai take so kuma bana
ra'ayin auran kowa face kai." Kwalla suka zubo
bisa kuncinta.Da sauri ya tauko sabuwar téÂÂ泂hu
kware ta ya yago ya miko mata,"share
hawayenki, ki daina kuka.Na yarda dake
sakeena,amma mece ce mafitar mu? Ta dan
kada kai tace, "zanyi tunani,ka ban dan lokaci
kadan,zan samo mana mafita.'ya daga kanta ya
fito ya gyara zaman benci.Yace zauna kiji Ta
zauna gefe shi ma ya zauna ya fuskanceta sosai
yace,me zai hana ba zaki gaya musu ni kike so
ynzu ba?Ta daga ido ta dube shi,jim,amma ba
tace komai ba,yace "kar kiji tsoron komai kai
tsaye ki gaya musu ke kin sauya ra'ayi ni kike
so,za'a yi miki tilas ne?Dole a baki wanda kike
so,don babu wanda zai zauna miki da shi,idan
kuma kina son in rasa raina ne shikke
nan........Ta kada kai tace,"nace ka daina fadar
rasa rai danliti idan ka mutu nima mutuwar zan
yi.Ka kwantar da hankalinka insha Allahu a yau
zan gaya musu na sami sauyi wanda hankalina
yafi kwanciya."Ya dafe kirji,ya lumshe ido
yace,kin sa naji sanyi cikin raina sakeena.Ya
bude ido ya bi ta da kallo ya cigaba,idan kika yi
min haka kin gama min komai sarauniya ta,ba
zan cika baki ba sai mun yi aure zaki ga tsantsar
son da nake miki,bana jin akwai wata 'ya mace a
fadin duniyar nana da zata sami irin gatan da
zan nuna miki." Tayi dan murmushi tace,Allah ya
nuna mana,yace amin.Ya dan gyara zama ya
sake gadin,"wai sakeena kin san cewa kin fi
kowa kyau a duniyar nan?Ta saki baki,ido waje
tace,duk duniya? Wlh duk duniya babu mace mai
kyau irin naki,ta kada kai tana murmushi
tace,"ka daina fasa min kai danliti,ni na san ban
kai ka ba,ya washe baki ya nuna kansa ya9e "ni
kuma? A'a ni dai kike son ki fasawa kan,ina ni
ina ke? kin gan ki kuwa?kin ga wannan dan
bakin naki dagwas ba karamin kashe min jiki
yake ba."Ta sunkuyar da kai tana 'yar dariya ya
bita da kallo yana shafo habarsa."Mama!"
Muryar kawai taji anyi mata wani gigitaccen
kira,gaba dayan su suka kalli mai magana,ta bi
shi da kallo babu tsoro ko wata fargaba tace,ah!
yaya ali! saukar yaushe?"Ya kara tsuke
fusk,yace me kike yi anan?"Tace me kuwa?Ba
komai,taso muje gida,kaje ina zuwa,"ina wasa
dake ne? nace ki taso mu wuce." "Ta dubi danliti
suka hada ido yace,tashi ku tafi sai wani lokaci
ko?Ta dan numfasa ta mike ta wuce,yaya alin
dake tsaye,ya bi ta da sauri ya
sameta,"mama,wai mafarki nake yi ko kuwa
gaske ne?Ta yamutsa fuska "da aka yi me?"
Zaune na gan ki kofar shago kina hira da
wani...." 'Wani? Ba ka ma san danliti ba?"Shut
up don Allah!waye danliti kike gaya min magana
ba dadin ji?Hauka kika yi?Ina mutunci ga'ya
mace tana hira da maza a kofar shago gaban
jama'a? Ban san ki da wannan ba,yaushe kika
canza mama? Ta ballo masa harara ta ja dogon
tsaki ta kwahsi sauri ta wuce shi,shi ma ya biyo
ta yana fadin,ban gane nufin ki ba?"Ta juyo ta
dube shi tace,wai menene yaya ali?"Shi kike
so?" 'Ai kaji,menene na sake tambaya? ya kara
cika da mamaki,'Ban fa gane shi ki ke so ba
mama.Ina Al-Ameen din?" Ido jajur! Ta dube
shi,"kai ka san wannan sunan,don girman Allah
ka kyale ni da tambayoyin nan." "Ba zan kyale ki
ba Mama,hasali ma sai na gaya wasu
Abba.Wannan ai zubar da mutunci ne da cin
amana!Me ya tsone miki ido a wajen Dan-Liti?Ke
ma kin shiga sahun 'yan matan da yake ruda da
kyan sa ne?Kai na ya daure Mama.Allah yasa
abinda na ke gani da ji ba gaskiya bane." Da
gaske ne yaya Ali! Kuma ko baka gayawa su
Abba ba,ni da kaina zan gaya musu."Ta zura da
gudu ta bar shi tsaye, shakare da
mamakinta.Kafin ya iso gida kansa,ya kusa
fashewa sbd tunani da al'ajabi.Rokon Allah
kawai yake yi Allah yasa mafarki yake yi. Kai
tsaye sasan su Mama ya zarce.Suna tsakar falo
umma ta tirke ta da tambaya,"Idan biki gaya min
inda kika je ba sai na sumar dake yau a gidan
nan!"Yayi sallama.Umma bata iya amsawa
ba,sbd bacin ran da take tare dashi.Ya-ce,'yanzu
na koro ta daga shagon Dan-Lati suna zaune
bisa benci suna hira Umma.Yaushe Mama ta
sauya haka? Tuni Umma ke sallallami,ta dafe
kirji ta-ce "shagon Dan-Lati ki ka koma Mama?
Mu kike so ki zubarwa mutunci a garin nan? Ai
kuwa baki isa ba,ba ki isa ba Mama!'Ji ka ke
tim! Ta rufe ta da duka ta ko'ina.kafin yaya Ali
ya kawo mata dauki,ta sha dan banzan
duka.Kukan ta ya watsu cikin sassa,matan gidan
da kananan yara suka sheko don ganin meke
faruwa?Al'amarin ya daure masu kai,ganin
Mama na birgima tsakar falo tana ture hannayen
Yaya Ali dake kokarin rarrashinta
BAKIN CIKI 2***2(TRUE LIFE STORY) Wa ya mutu
Ali? "suka tambaya,yayin da umma ta fito daga
daki dauke da wayar rediyo kafin su yi aune,ta
fara tsula mata.Haba gaba daya matan suka
cafke hannun Umma, 'Hajiya Halima! Lafiya
wannan abu haka?Me ta yi da zafi irin wannan
duka?" Umma na haki tace wai yarinyar nan ita
ce zata siyar mana da mutunci? Ta rasa wanda
zata tsaya da shi, sai Dan-Liti? "Dan-Liti? Waye
Dan- Liti?"Dan gidan Buzu mai shayi mana! Yau
kwana uku kenan muna fama da ita ta rabu da
yaron nan,ta ki! Jiya yazo kofar gidan nan.Alhaji
da kansa ya same shi ya gaya masa tana da rana
a kanta.shine don dibar albarka ta bi shi shagon
sa,yanzu Ali ya ganta ya koro ta! Wace irin tijara
ce wannan sbd Allah! Tuni suke kallon juna suna
tafa hannu,hajiya hajo tace "danliti kuma?Waye
bai san tarihin su ba a garin nan?Yaron da tun
tasowar sa garin nan basu da aiki sai bata
'ya'yan mutane koda baki da wayau sosai ai kin
yi dan hankalin da zaki gane buzu mai shayi
kasurgumin kwarto ne,shi kuwa danliti kananan
yara sau nawa ana kama shi dasu?Ko kin mance
ranar da dubu ta cika suka ci shegen
duka.Danliti ya sha da kyar shi kuwa buzu ya
shura barzahi?Me ya dawo da shi kike kwadayi
da har idon ki ya rufe kika kasa duban kazantar
dake tare dashi?Hajiya Gaje tace "duk ba ma
wannan ba kina nufin zaki fasa auran Al-ameen
ne?Umma tace,karya take yi sai dai bayan ran
mu,bari kuma alhajin ya dawo,yau din nan zai
maida ta minna tnda zaman naki anan abinda ya
haifar kenan!Ta tashi da gudu ta fada dakinta
har da danna sakata ta bar su nan suna maida
yadda aka yi. Shi dai yaya ali tunda ya sunkuci
jakar sa ya fada dakin mahaifiyarsa bai sake
kyakkyawan motsi ba sai tsabar tunani.Muryar
mahaifiyarsa yaji a kansa tana fadin,"kai kuma
yaushe ka shigo garin?"Firgigi ya dube ta
na'am!"Ta zura masa ido,nace yaushe kazo?Ya
sauke gwauron numfashi yace,"zuwa na kenan
inna".ciwon daya sami mama,ai ya same ni
domin jinin mu daya......"Gafara can sakarai kai
ka san wannan,da su ma sun san cewa jinin ku
daya ba'a hana ka auranta ba ai sbda haka ban
ga dalilin dogon tunanin da kake yi ba,don daga
ita har iyayenta basu san ka na yi ba!Gara tun
wuri ka halkantu ka gane cewar alhakinku ne ya
kamasu!Idan ba haka ba,ina mama,ina danliti?
Marasa asali da tushe ga tarin abin gori da na
kunya a jikin sa?"Ya dafe goshi idanuwansa suka
kara kadawa,yayi hucin zafi ya dubeta,"duk
wannan maganar bata taso ba inna abinda nake
so ki gane shine muddin mutuncin mama ya
zube,to martabar gidan nan gaba daya ta
fadi,ashe kuwa dole in damu tnda nima dan
gidan nan ne,ga shi kuma mama ta dauko
hanyar bada mana kasa a ido. Tace can dai zata
badawa iyayenta masu kwadayi,ban sa aka ba
balle ya dameni wahalar banza kake yi dama
ruwa da abinci ka samu ka ci,daya fiye maka
wannan sakarcin!Ya sake dafe goshi yana kada
kai,me yasa innar sa baza ta gane ba?Takaici ya
kara kama shi ya sunkuci jakarsa ya koma
dakinsu.Haj Gaje ta shigo saboda gulma ta
cigaba,sharri kala kala suka yi ta jifar uban
dawaki da su.La'asar sakaliya abba ya dawo
gida ya iske idanuwan umma sun jirkita jajur!Ga
kumburi sun yi,ko bai tambaya ba ya tabbatar
akwai abinda ke damun ta,don haka ya kasa cin
abincin data kawo masa,ya zura mata ido yace
kamar akwai abinda ke damunki sadiya? Tace
akwai matsala alhaji amma ka ci abincin sai mu
san abin yi."Fuska ki ta bayyana tashin hankali
dake tare da ke ban jin abincin nan zai iya wuce
min ba tare da naji damuwae ki ba.Gaya min
uwargida,ni kadai gareki wanda zai saurari
kukan ki."Ta dan yi murmushi karfin hali tace
mama zata siyar da mutuncin mu a garin nan
gara ka dauketa ka maida minna ko abj ta zauna
can har zuwa lokacin bikinta."Gaban sa ya fadi
yace,me tayi?Bata daina zuwa shagon yaron nan
ba,yau ali da kan sa ya koro ta tana zaune bisa
benci suna hira,benci fa a kofar shagon bakin
titi?Kamar mama yadda muke a garin nan take
zama tare da danliti?Ta goge kwalla,ina zan sa
BAKIN CIKI Alh,anya kuwa mama ce ke aikata
wannan abu?Hankalin alh yayi mummunan tashi
ya fuskanci umma da kyau ya sanyaya murya
yace,ki daina zubda mata hawaye halima ke
mahaifyarta ce,sai abin ya kara wargaje
mata......" "Ba yin kai na bane alhaji,hawayen ke
tilasta wa kansa zubowa."Yace duk da haka ki
rinka daurewa kina mata addu'a,insha Allahu
gobe zan maidata minna ko ta ki ko ta so dole
ta zauna.Ni abinda ban gane ba shine,tana nufin
ta fasa auran Al-ameen ne?Idan wani abu yayi
mata ai sai tayi bayani,ba wai ta nemi ta maida
mutane sakarkaru ba!Ina take ne?"Tace tana
daki a kulle tun safe daya koro ta,haushi yasa
nayi mata duka har ynzu bata fito ba."Ya mike
cikin fushi ya nufi dakin ya buga da karfi yana
fadin,"tashi ki bude kofar nan!"Tana budewa ya
cafko hannunta ya jawo ta zuwa falonsa,hakan
ya sanya mama cigaba da tsiyayar hawaye,ya
cillata tsakar dakin ta zube gefen ummanta.Ya
zura mata ido yace,"ashe wani lokaci zai zo da
zamu ce ki bar abu ki ki bari mama?Kin dai san
maganara auren ki da al-ameen ko?To ynzu nake
so ki gaya min manufarki ta bin danliti
shagonsa.Gaya min inji tun kafin mu tara 'yan
kallo!Tayi kasa da kai kukan ta ya karu.Abba ya
daka mata tsawa,"kuka na tambaye ki? Ki gaya
min dalilin bin sakaran yaron nan nace?Ta
cigaba da share kwalla tana mutsu mutsun rashin
gaskia,leben ta na makyarkyata tace,"shi....shi
na ke......na..na...ke so ab...."Umma ce ra doke
ta da bayan hannu tace rufe mana baki mara
kunya!"Ta dubi abba dake tsaye sake da baki
tace,"ka ji ko?Ni na san take-taken ta kenan!"Ya
matso ya cafki kunnenta cikin tsawa yake
magana."Idan barci kike yi to ki farka ki bude
kunnuwanki da kyau ki saurare ni! Ni ba tsohon
banza bane,in har kin ga ki auri yaron
nan,tabbaci hakika ni uwaisu na mutu an binne
ni cikin kabari na! Ya girgiza kunnen kamar zai
tuge shi,kin ji ni! Wannan itace magana ta
karshe da zanyi akan danliti kuma gobe ki shirya
kayanki zan maida ki minna!"Ya shirga mata
dundu tare da fadin,"tashi ki bani wuri!Ai bata
iya tashi ba nan ta baje ruf da ciki sbda tsananin
zafin dundun da yayi mata abnda bata saba
ba,sai ta ji shi har cikin kayan cikinta sun dau
zafi ba kadan ba,Ta fasa kara mai shiga zuciya
tace wayyo Allah na shiga uku! Na shiga uku!
Yaya ali ya mike a firgice,gabansa ya yanke ya
fadi ya fito da sauri yana tsinkayar kukan
mama,ya nufi sasa.Umman ke fadin,'ba ki shiga
uku ba mama sai nan gaba muddin baki dauki
nashihar da muke yi miki ba!"Hannu biyu yaya
ali yasa ya ciccibe ta ya mikar da ita,zafin duka
da tsananin BAKIN CIKI dake dankare cikin ran
ta yasa ta kwakume.Yaya ali bakin gado ya
zaunar da ita ya dago fuskar ta hannu biyu yake
share hawayenta,yayin da nasa kwallan ke
neman sauka,yace "haba mama ki yiwa kan ki
fada mana!"Murya na rawa tace,me nayi masu
yaya ali!Sbda Allah me nayi?"Me kika yi? ynzu a
wajen ki wannan ba laifi bane?Haba mama!Ba
haka kike ba,kin sauya da yawa kar dadin bakin
danliti yasa hankalin ki ya gushe,laifin me al-
ameen yayi miki kike so ki yi masa wannan
sakayyar?A zato na koda babu Al-ameen nine
mutum na farko daya kamata ki fara kawowa ran
ki don na dade ina yawo da ciwon son ki
mama.Ki tausaya mana me zai sa ki canza
kyawawan halayen ki? Ya Girgiza kunnen kamar
zai tuge shi. Kin ji ni! Wannan itace maagana ta
karshe da xanyi akan Dan-liti, kuma gobe ki
shirya kayan ki, zan maida ki bani wuri. Ai bata
iya tashi ba, nan ta baje ruf da ciki, saboda
tsanannin xafin dundun da yayi mata. Abinda
bata saba ba, sai taji shi cikin kayan cikinta sun
dau xafi ba kadan ba. Ta fasa kara mai shiga
xuciya. Tace wayyo Allah na shiga uku! Na shiga
Uku! Yaya Ali ya mike a afirgice, gabansa ya
yanke ya fadi, ya fito da sauri yana tsinkayar
kukan mama, ya nufi sasan. Umma ke fadin baki
shiga uku ba Mama, sai nan gaba muddin baki
dauki nasihar da mukeyi ba miki ba! Hannu biyu
Ya Ali ya sa ya ciccibeta ya mikar da ita, xafin
duka da tsananin BAKIN CIKI da ke dankare cikin
ranta ya sa ta kwakume Ya Ali. Bakin gado ya
xaunar da ita ya dago fuskar ta hannu biyu yake
share hawayen ta, yayin da nasa kwallan ke
neman sauka. Yace, haba mama kiyi wa kanki
fada mna! Murya na rawa tace, me nayi musu Ya
Ali? Saboda Allah me na yi? Me kikayi? Yanxu a
wajenki wannan ba laifi bane? Haba mama! Ba
haka kike ba, kin sauya da yawa kar dadin bakin
Danliti ysa hankalinki ya gushe. Laifin me Al-
ameen yayi miki, kike son ki masa wannan
sakayyar? A xato na koda babu a alameen, ni ne
mutum na farko daya kamata ki fara dawowa
ranki, don na dade ina yawo da ciwon sonki
Mama, ki tausaya mana, zai sa ki canja
halayenki? Ta xuba masa kwala- kwalan
idanuwanta da suka kara fitowa waje jajur! Tace,
Yaya Ali ina ganin girman ka, ka kyale ni da
wadannan surutan, don ba xa suyi tasiri ba. Ni
nace ina so Al-ameen, yanxun kuma bana son
shi Danlilti nake so. Ra'aryi nane, ba sai a kyale
ni ba, ko akwai wanda zai zauna min da shi? Ya
bita da kallo, ta sa aya kafin yace, ki daina
tunanin wannan ra'ayin na ki mai yuwuwa ne,
kin dauko katon aikin da xai rushe martabar
gidan nan a idon jama'a. Idan baki son Al-
ameen, ki musanya da ni Mama, zai fi miki kyau
a bisa shirmen da kie sonyi. Ta runtse ido tace,
yaya Ali je ka kawai! Ba ki son gaskiyya? Ta
kauda kai kwalla na tsiyaya. Ya sanya murya
yace, xan bar ki ki kwanta kiyi tunani sosai,
cikin kan ki. Ina rokon ki girma da Allah, ki
manta da kudirin da kika dauko. Bata tanka ba,
haka bata dube shi ba yace, A bakin tofa ya
tsaya ya kare mata kallo kafin ya sake fadin,
bana so ana taba jikin ki mama, tamkar ni ake
tabawa nakeji. Pls ki sauya tunaninki. Haushi ya
kara kuma ta, ta juya masa baya. Ya fice yana
kara waigen ta. A daren nan daga ita har Yaya
Ali babu wanda ya iya cin abincin balle barci.
Tunanin Mama shine xata ga yadda za'ayi a raba
ta da garin nan. Cikn xuciyar ta tasha alwashin
ko sun maida ta, zata dawo, dole su gaji su
kyale ta da wanda take so. Dalilin da yasa ke
nan, yau kwata-kwata taki bude kofar ta, kowa
yayi bugu, iyayinsa har kawunninta, sai dai
kalaman bakin su suka kare. Amma mama taki
bude kofarta. Duk wanda ka duba ransa bace
yake, musamman Abba, fuska kamar gobara ya
dubi Umma yace, dauko min tabarya! Ta mike a
salube ta shiga kicin ta dauko masa tabarya, ta
mika masa. Alh basiru yayi caraf! Ya karba.
Yace karka balle kofar nan yaya, asara biyu
xa'ayi..... Yace yarinyar nan dole ta bar garin
nan, ba xata xauna tana jawo min xagi ba, ana
kallo na tsahon banza, bansan abinda nake yi
ba! Buge min kofar nan, ko ka ba ni da kaina, in
sauketa! Kowa yayi cirko-cirko. Alh. Basiru ya
kai wa kofa duka da tabarya, sai ga sallamar
Yaya abdul- kareem. Basu gama amswa ba, yaci
gaba da tambaya, lfya? Me ya faru da kofar?
Abba yace, nayi farin cikin xuwanka, don ni ma a
yau nayi niyyar tafiya gunka. Me ya faru abba?
Umma ya naga kamar kina kuka? Yace, mama
ce.... Me ya sameta? Ya kwashe kaf halin da
suke ciki ya gaya masa. Kai! Bai gaskanta
kunnuwansa ba, shi yasa yace, abba ban yarda
da wannan maganar ba, ya kamata asake
bincikawa. Abba ya xuba masa ido jajur! Yace,
wannan maganar ni Uwaisu nake gaya maka ita.
Abdul kareem kasan kuwa ba za ayiwa mama
kage ba, domin ni na haifeta. Saboda haka gidan
ka xata xauna can har xuwa lokacin bikinta!
Yace, ya xama wajibi, don ganin nan da kuka yi
min xuwa nayi in tafi da ita dama. Al'ameen ya
damu kwarai har yana ganin kamar wani abu ne
ya faru da ita ake boye masa. Wlh jiya ya turo
mahaifiyarsa da yamma wai ta zo ta bincika
masa lfiyar mama, shine nace shi kwantar da
hankalinsu Insha Allah da kaina xanje in dawo
da ita. Wannan al'amari ya daure min kai.
Yaushe mama ta canza haka? Kawu Basiru yave
xancan banza takeyi, tunda ita ta kawo Al'ameen
har aka sanya musu rana, bata isa tace ta canza
shi ba! Wannan karya take yi. Haushi ya kara
kure yayanta, ya mike ya suer tabarya ya kaiwwa
kofar duka sau biyu kofar ta balle, bata a dakin.
Ya nufi kofar bayi ya murda can ma garkamen
yake, bai tsaya wata-wata ba, ya maka mata
tabarya. Bugu daya kofar ta wangem, sai ga
mama jikin bango ta fita hayyacinta saboda
tsabar kuka. Al'amarin tamakar mafarki yayana
yake gani. Ya xura mata ido, yace hauka kikayi
mama! Me Al-ameem yayi miki? Iye? Yayi miki
laifi ne da ba zaki fada ba! Sannan ki rasa
wanda zaki bi, sai dan liti! Kinji abinda nace?
Kin yi karya ki xuabar mana da mutunci a garin
nan! Zo mu wuce, ban son jin komai daga gareki!
Ta sulale kasa hannaye biyu bisa kanta, ta kara
fasa kuka mai tsananin gaske. Matan gidan suka
kutso kai cikin bayain suka tarairayo ta, suka
fito da ita dakin. Yaya yana fadin ko mutuwa
zakiyi yau, sai na tafi dake mu je can idan Al-
ameen ya kira waya, in tambayehsi a gabanki,
muji abinda ya hadaku! Amma yaro na sonki
yana tattalinki. Iyayeynsa na ririta ki, tashi guda
kice ba kiyi da shi, aikin san wannan karya
kikeyi. Ina kayan ta suke umma? Hada mata si
don baxan bata lokaci ba! Gaba daya suka
yanyame ta da fada kowa na fadin albarkacin
bakinsa, su Umma na hada mata kaya. Su
Hajiya Hajjo na rarrashi ta suna bata baki tare
da gyara mata jiki da fuska. Yaya Ali kuwa yana
xaune gefe rayuwa tayi masa bakikkirin! Ana
janta, tana togewa suka saka ta gabn motar
yayanta. Ya jefa jakar ta gidan baya, daga nan
yayi sallama ransa bace, ya ja motar yayi gaba
da mama. Dole ne ya saurar daidai shagon
Danliti, domin akan mahada shagon yake.
Tsayuwar su wajen, ya jawo hankalin Danliti
xuwa garesu. Ya xuba wa Mama idanuwan sa
suka sha kwalli rangadau! Haka ita take kallonsa
kwalla fal! Suna neman sauka. Ya daga kanka ta
fito kofar shagon, irin duban da yake mata ya
bayyanar da damuwarsa karara bisa fuskarsa.
Tausayinsa ya lullubeta, nan da nan hawayen
suka fara bulbula. Yayanta bai kula ba, kokarin
sa, duk motocin da suka kawo, suka wuce shima
ya samu ya haura. Yawanci duk manyan motoci
ne, kamar yadda akansan babban titi ne, wanda
ya mike ya tafi har lagos. Suna tsagaitawa ya
cilla tasa motar ba tare da ya fahimci Danliti da
mama sun ruga sun gama magana da
idanuwansu ba. Kawai ji yayi ta kara gocewa da
kuka mai karfi. Ya dan dubeta, ya kada kai.
Yace, Al'amarin ki na bani mamaki, look kina
jina? Saurare ni muyi magana ta fahimta. In
tambayeki xaki bani amsa? Hankalinta sam ba
awajen sa yake ba, balle ta saurare shi. Fuskar
Danliti take gani, irin yadda ya shifa damuwa
yana neman xubar da hawayensa, shi ya kara
dagula mata lissafinta. Yace, saboda Allah zaki
gaya min Al- ameen yayi miki da zaki juya masa
baya? Tayi shiru, danliti na cigaba da yawo a
idonta. Yace, kin kuwa san tun ranar da kika
dawo garin nan. Al-ameen ya rasa nutsuwarsa?
Ban iya kirga yawon wayoyinsa ba, tunaninsa
kina cikin wani matsanancin hali ne aka boye
masa. Kar ki saki reshe ki kama ganye Mama,
domin kowa yasan Danliti lalata rayuwar ki
kawai zai yi, ya kai ki ya baro ki tashar
danasani. Ki ga ya min idan Al- ameen yayi miki
laifi ne, ni da kaina xan masa magana in ja
masa kunne. Kinji? Bai yi aune ba yaga ta balle
murfin motar ta dire waje. Ta mulmula cikin
ciyayi. Cikn tashin hankali ya take birki.... Allah
yasa ba babu mota a bayansa, yayi fakin gefen
titi, ya fito. Can ya hange ta tana kokarin tashi,
amma ta kasa, kafin ya gangara wajen 'yan
tsirarrun jama'ar wajen sunyi caa! Kanta. Suka
ciccibota, suna sallalami tare da mamakin yadda
aka yi abin ya faru. Gaba daya gwiwowin ta
sunyi mugun kurjewa ta xura da gudu amma bata
je ko'ina ba mutane suka cafke masa ita. BAKIN
CIKI yasa ya dauke da wani mahaukacin mari
daya tilasta mata xubewa kasa. Wani dan dattijo
cikinsu ya kama shi. Yace, haba malam yaya
haka kuma? Baka ganin kaddarar da ta sameta?
Da ta mutu fa? Ku rinka kulawa da murafen mota
mana don gudun irin hakan! Idanuwan sa ajuye
yake magana, kyaleni da yarinyar nan baba! Da
kanta ta bude murfin ta fito! Iskanci ne kawai,
dama kin mutu, mu huta da wannan BAKIN
CIKIN da kike son jefa mu! Saboda haka xan
koma in gayawa abba kin bude mota ki diro, ni
kuma ba xan tafi dake ba, ki xauna kiyi duk
abinda kika ga dama agarin nan, tunda lalacewa
kika xaba. Allah ya shirye ki! Ya shura
takalmansa ya koma mota ya tayar yayi kwana
ya koma gida ya bar Mama anan tana faman
kuka, jama'ar dake wajen suna mamakin wannan
abu har sun kasa fassara shi. Dan dattijon nan
shi ya riko ta hankali suna tafe tana bashi
labarin wai auran dole ake son yi mata. Kwarai
kansa ya daure jin cewar ita 'yar gidan Uban
dawaki ce, don haka ya tasa ta har gidan. Amma
me? Suna xuwa kofar shagon Danliti ta xarce can
tayi xamanta bisa benci. Dan liti ya fito aguje da
ayuba, mamaki ya rufe ayuba, shi kuwa dan
gogan munafuncin ne yasa gaba, sai yazo ya
narke a gabanta. Yace, saboda me sakina,
kinaso ki rasa ranki ne? Tace gara in mutu da su
raba ni da kai, ya dubi Ayuba a gigice. Yace,
kawo min mukullin mota ayuba! Ya shige shagon
da surinsa, shi kuma ya juyo gunta ya marairaice
yake fadin, aure na Allah ne sakeena, ina so ki
yarda da wannan. Duk iya son da muke juna idan
Allah bai nufi auran mu ba, babu yadda xamuyi.
Don me xaki nemi halaka kanki? Bata bashi
amsa ba. Ayuba ya mika masa mukulan. Bai jira
tace wani abu ba, ya kamo hanninta taso muje
asibiti asa miki magani. Dattijon nan ya bisu da
kallo, duk tausayi ya rufeshi. Rashin sani kenan,
ya fi dare duhu, domin shi gani yake irin haka ke
jefa yara yawon banza..
BAKIN CIKI 2***3 (TRUE LIFE STORY) Wasu
iyayeyn na da ra'ayin rikau, idan kuma ka
bibibya kwadayi ne, wata kila wancan yafi
wannan kudi ne? Sai dai kuma ai uban dawaki
mutumin kwarai ne, me xai sa ya aikata haka
akan yarsa? Duk da cewar dan dattijon nan
talaka ne, ya doshi gidan uban dawaki, don ya
bashi shawara. Fuskar Umma a sharkaf da
hawaye take muryar ta har rawa takeyi, bai
kamata ka baro ta can ba abdul... Yaya xanyi
umma? Kona cusata cikin, sake fitowa xatayi.
Mama ba zata mutu a hannu na ba, umma ta tafi
inda take son xuwa, kanta tayi mawa. Fatana
kwai Allah ya yaye mata abinda ke damunta.
Kuyi hkr ku kyaleta anan domin ina mai tabbatar
muku xata xauna can ba dawowa xatayi ba.
BAKIN CIKI ya hana abba magana, sai A. Adamu
ya iya fadin, gaskiya, gara ta xauna a cigaba da
yi mata nasiha watakila a dace. Kuyi hkr Yaya
mu dauki wannan a matsayi kaddara. Kai abdul
idan ka koma Al-ameen ya kira ka kwantar masa
da hankali ka... In ce masa me kawu? Gaskiyya
xan gaya masa shi ma ya hkr da ita tunda ba ita
kadai bace 'ya mace. Allah xai bashi wata. Ko
kuwa? Abba ya dube shi, sai yanxun ya iya cewa,
karka gaya masa haka abdul, da yardar Allah sai
inda karfina ya kare akan mama. Indai ni na
haifeta kuma ni ne xan daura mata aure Insha
Allahu shine xai aureta. Kawai ka bashi hkr kayi
masa wannan bayanin da naga ya maka yanxun.
Ya dafe goshi yayi huci zafi kafin ya dubi
Umma. Yace ki share hawayenki, umma ki yi
mata addu'a Allah ya shiryata. Ni xan koma sai
yadda ta kama. Basu amsa ba, ya mike kawu
Basir da Adamu suka yo masa rakiya kuma suna
gaya masa kalaman da suka dace ya gayawa Al-
ameen. Da dan dattijon nan sukayi kicibis yana
sallam cikin xaure suka amsa nan take. Yace
baka shaida ni ba ko yaro? Nine wanda yaga
lokacin da yarinyar gidan nan ta bude murfin
mota ta fito, tayi min bayani ita 'yar mai girma
Uban dawaki ce, shine nace ai mai martaba yana
da saukin kai xan xo in bashi shawara game da
auran dole, yayan ya dube shi da kyau. Yace
hakan ta gaya maka? Yace, kwarai hakan ta
fada. Yace to tayi maka karya, kawu ka na iya yi
masa bayani, don na tabbata abba baxai iya
fitowa ba ahalin da yake ciki. Alh. Basiru yace
yanxun ina take? Yace tana can ta tsaya wani
shago har sun tafi, zai kaita asibiti. Suka dubi
juna, yaya yace, kunji ko? Mama ta tafi, bata jin
kira saidai addu'ar Allah ya shiryata. Ni na tafi.
Ya fice ya barsu nan tsaye. Alh. Basiru ya dubi
tsoho yace mun gode baba, amma kayi hkr,
bazaka ji komai daga gareni ba, saboda ban
sami izinin yin hakan ba. Maganata gaskiyya da
nake so ka gane shine karya yarinyar ke maka,
tare da shegantaka irin ta yaran yanxun. Mun
gode da kulawarka. Tsoho yace, shikenan nima
na gode, amma don girman Allah abi a hankali
asamu a sulhunta. A. Basiru yace ba komi baba
mun gode. Sukayi sallama ya shige gida. Tsho
ya kama gabansa cike da wasi-wasi cikin ransa.
Falon Uban dawaki A. Basiru ya koma ya
xayyane masa labarin da tsho yaxo da shi, da
kuma shawarwarin da ya bayar. Abba bai iya
cewa komai ba saboda tsabar bacin rai. Sun jima
suna tausar xuciyar Abba sannan suka koma
sasan su, inda matan suke xaune dirshan suna
xuba gulmace gulmace. Suna zagin mama da
iyayenta. Basu hanasu ba, hasalima zama sukayi
suka dora xancan babu dadin ji, ita kuwa baiwar
Allah mama, tana tare da Danliti cikin mota,
bayan fitowarsu asibiti, yana ta faman
rarrashinta, don ta daina kuka ta kwantar da
hankalinta, da kyar ya samu ta nutsu ta daina
xubda hawayen. Yayi fakin kofar shagon sa ya
juyo ya fuskance ta. Yanxun ya xamuyi mu
fuskanci juna abba ya gane cewar idan ba mu
auri juna ba, komai zai iya faruwa da mu? Tace,
ai ga misali nan na fara nuna masu kuma ba xan
fasa ba, ina nan akan baka na. Ya marairaice
yace wannan misalin bana son irinsa sakeena,
don bana son na rasaki. Gaba ki daya kin fita
kamanninki kin kuwa ci abinci yau? Ta kada kai,
abinci ba xai iya wuce min ba Dan liti ina cikin
wannan masifar meye illar ka? Da abba xai ce
samm baka dace dani ba? Ya lumshe ido, ya
bude kafin yace, saboda suna ganin ni bako ne,
bani da kowa agarin nan..... Ta katse shi, hakan
shine xai nuna daga sama ka fado? Wannan ba
hujja bace Danliti, son rai ne kawai irin na iyaye
ni kuwa ba xan yarda ba, sai dai muyi ta ba juna
wahala. Ya ja gwauron numfashi ya sauke, ya
lalubo yatsun ta ya runtse su cikin nasa, ya xuba
mata ido yace, nasan ki na sona sakeena, amma
ki daina damuwa ko sun hana ki xuwa wajena,
sannan ki daina wasa da rayuwarki, don tana da
muhimmanci aguna. Abu da gaba, ki daina zama
da yunwa, ita ma zata iya illata minke. Yaunxu
abinda nake so dake, ki zo muje shago in hada
miki tea ki sha, sannan kije gida ko sun zage ki,
kar ki ce dasu komai, don kar su sami damar
dukanki. Kinji bebi na? Ta amsa da ka. Tace,
yauwa mai kyau, to dan kalle ni mana, ta dube
shi suka yiwa juna xuru, jim kafin ta kauda kai,
tana dan murmushi, shima murmushin yayi yana
mata kllon kwadayi, ya ja yatsunta xuwa bakinsa
ya sumbata. (kuji dan iska). Ta kwace da sauri
ta kara sadda kai. Yace, bebi na kenan, sarkin
kunya. To muje ko? Zaki iya sauka ko in zo in
fito dake? Ta balle murfin batare da tace wani
abu ba ta fito, shima yayo waje yana kallon
yadda take dingisawa har cikon shagon sa. Ya
ba za mata tabarma ta zauna. Ayuba na mata
sannu. Akwai wani labule jikin wata kwana a
shagon, sai alokacin ta gane daki ne. Cikinsa
Dan liti ya shiga ya fito da filas da kofi da cokali
ya aje gabanta. Yace ga ruwan zafi, ki daga
idonki, ki duba duk irin madarar da kike so, ki
zaba na dauko miki. Tana murmushi tace, kai
wacce iri kake sha? Yace ai bana shan madara a
tea, ganye kawai nake sha. Kinsan buzaye ai?
Tayi dariya tace, ba'a raba su da jiko. Yace shayi
dai. Ta ciga da dariya tana fadin, to shayi, wai
menene sirrin shayin nan ne? Yace xan gaya miki
amma da farko wacce madara kika zaba, in
dauko miki? Na kowa ki sawa cikinki abinci.
Tace, bani peak ta ruwa. Ya mike ya dauko hade
da katon bread ya hada mata tea mai kauri,
domin duka ya juye peak din. Tana sha, suna
hira ya gaya mata ire-iren shayin su. Bayan ta
kammala, ya matsa gareta yace, yanxun ya
kamata ki koma gida kiyi barci, ki huta kinji?
Karki damu ko an hana ki xuwa nan, wane tym
zamu hadu. Ke dai kiyi addu'ar fatan samun
nasara. Tace, Insha Allahu zanyi. Yana
murmushi ya mika baki ya sumbaci kuncinta. Ta
sunkuyar da kai tana murza yatsunta. Ya zura
mata ido, gaba daya jikinsa yai la'asar, sannan
ya dago habarta, suka dubi juna, yace I love U!
Tace me too, yace, to ki tashi kije gidan, zaki
iya ko? Tace xan iya. Ta yunkura ya taimaka
mata mikewa suka fito tare ta sallami Ayuba, ya
dan taka mata kadan ya dawo, yana zuwa ya
kwashe da dariya, ya mikawa Ayuba hannu suka
tafa. Ayuba yace, baka da kyau dan iska. Yace
raina kama gayya! Gaskiyya ta gurzu, na
tausaya mata wlh. Shegiya akwai taushin fata,
baka ji ba kamar auduga, duk ta susuta ni. Ya
zura masa ido yace, tunda kuka shiga, na
karance ka, shi ya gaba na yayi ta faduwa, kar
ka sata labulan nan. Yace, ko na sata ba zata
hani ba, nake gaya maka kuma babu abinda zai
faru dani. Kawai dai ban yi niyya bane yanxu, ni
nasan abinda nake hari. Yace a dai rika tuna
Allah Danliti, shagalinka yayi yawa kuma ina ma
kwadayin cin ubanta nakeyi, ai har uanxun
duniya bata fara zaginta ba. Kaga da sauran
mutuncinta. Ya bishi da kallo, bai ce komai ba,
yayi tsaki ya tashi ya koma shago abinsa. Tana
tafe tana dingishi, ta iso gida, kanta tsaye bata
fargabar komai ta fada zaure, kicibus suka yi da
Ya Ali sabe da jakar sa zai bar garin. Ko kallon
sa batayi ba ta wuce, ya biyota yana kiranta bata
waigo ba, balle ta amsa, ta shiga sasan su har
falo yana binta. Su abba na kallon ikon Allah,
domin dai Mama bata saurara ba, cikin dakinta
ta shige. Ya Ali na shigowa ya gansu, ya ja birki
amma ransa na son ya shiga wajen mama, yayi
magana da ita, abba ya dube shi. Yace, Ali ka
daina wahalar da kanka abanza, mama bata
bukatar komai sai addu'a. Saboda haka ka kama
hanyarka ka koma bakin aikinka. To amma, kayi
hkr Abba, don girman Allah karku daketa, kamar
yadda kace nayi mata addu'a kuma kuyi mata
addu'ar. Yace, na yarda da kai Ali, amma ban
yarda auran kowa ba, sai wanda na aminta da
shi. Zan gani idan ita zata daura wa kanta aure
ko mune? Yace, haka ne Abba don Allah ina
rokon 2mins in ishiga in dayi mata nasiha, koda
bazata saurere ni. Ya suke numfashi yace, shiga
Ali, Allah ya sa taji abinda zaka gaya mata. Ya
aje jaka ya wuce cikin dakin. Tana kwance
niyyar barci ma takeyi, kamar yadda Danliti ya
umarceta. Yana shigowa ta runtse ido ta juya
baya, ya tsya kanta yace, komai zakiyi, dole in
gaya miki gaskiyya, tunda kunnuwanki naji.....
Fadan hakan yasa tai sauri ta toshe kunnuwan
nata da yatsunta. Yace aikin banza kike yi
Mama, kuma rayuwar ki na cikin hatsari, muddin
baki daina jefa su abba cikin BAKIN CIKI ba.
Menene anfani abinda kika aikata yanxu? Ki
kashe kanki a banza da wofi, ba asarar Danliti
bane, don na tabbata duk tsananin son da yake
mi, ba zai hallaka kansa ya biki ba. Ki nutsu kiyi
tunani. Akwai abinda magabatan mu ke hangowa
kan wannan ra'ayin naki. Ni zan koma kuma ina
fatan zanji canji daga gareki? Ya juya ya fice
bata re da ta daga kai ta dube shi ba. Wani
dogon tsaki ta raka shi da shi, wanda ya tilasta
masa juyowa ya dubeta ji, sannan ya karasa
ficewa. Ya dauki jakarsa ya kara yiwa su Abba
sallama, ya bar gidan ciki da Al'ajabin maras
misaltuwa a zuciyarsa. Bayan tafiyarsa, su
Umma suka shigo gunta ta tana kudundune ta
dunkule wuri daya, ko 'ina jikinta ciwo. Umma ta
zauna gefen gadon shi kuma Abba n atsaye
kanta, yace Mama barazanar kashe kanki ba zai
sauya abinda ke cikin raina ba, idan ma baki
sani ba, ki sani gara ki mutu da mutunci na ya
xube a idon duniya. Saboda haka fadowar ki a
mota bata girgiza ni ba balle ta cire daidai da
kwayar zarra na alkawarin da na daukarwa Al-
ameen da iyayensa. Mu zuba ni dake, duk wani
matakin rashin kunyar da kika hau, ni na fi ki
hawa matakin karshe! Ya juya ya bar dakin.
Umma ta kura mata ido, hawaye suka cika
idanuwanta, tace Mama zaki iya tashi ki saurare
ni? Ta shiru bata motsa ba, ta sake fadin, idan
har ni na haifeki kuma na isa dake, to ki tashi
zaune ki fuskance ni. Ta jima kafin ta yunkura ta
tashi fuskar ta sharkaf da hawaye, kamanninta
sun sauya, saboda fitinar da ta daukarwa kanta
a tunanin iyayenta. Umma ta zura mata ido,
kafin tace, nasiha xan miki, idan kiji ki dauka
wahala ta kare miki, idan kuma kince ba haka ba
to rayuwa zata cigaba da yi miki kunci, domin
Allah ne ya wajabta miki yi mana biyayya,
muddin ba mu sa ba masa. Ban jin akwai wani
dalili ko hujja da xaki gayawa ubangiji da ace
kin mutu sakamon bude murfin motar da kikayi,
ki fado lasa. Wannan ya nuna muraran kin kashe
kanki ne da gan-gan. Ma'ana kin mutu kafira.
Me zai jawo miki wannan masifar da hankalinki
da komai? Ko kuwa kina so ki nuna mana kin fi
karfin mu cikin dan kankanin lokcine ne? Kina
nufin mu sanya miki ido ki zubar da mutuncin ki
da mu a garin nan? Ban taba tunanin Mama, ke
din nan zaki zama kaza kici share baki a game
da irin so da Kaunar da Al-ameen da iyayensa
syka nuna miki. Haka kuma ban taba mafarkin
ke din nan zaki iya hango wani da namiji ya rufe
miki ido har kice kin fo sonsa akan Al-ameen.
Kina nufin daman can yaudara sa kike yi ba
tsakani da Allah kike sonsa ba? Har yanxun
mafarki nakeyi Mama, don ba gaskanya abinda
yake shirin fitowa daga gareki nake ba. Ki yiwa
girman Allah kir ki bari wannan magana ta zama
gaskiyya, ba ke kadai za'a zaga ba har damu
iyayenki. Na mu ma zai fi yawa saboda mune
muka isa dake. Yanxun abinda na rokonki shine,
ki share hawayen ki ki gaya min, laifin me Al-
ameen yayi miki kike son ki katse masa rayuwa?
Gaya min daga ni sai ke ce a dakin nan kuma
share hwayenki, muddin shi ne baida gaskiyya.
Ta shre hawayneta wasu suka xubo mata,
kalaman ummanta masu taushi ne dashiga
xuciya, amma kash Danliti ya riga ya gama da
ruhinta. Allah ya bashi sa'a ya kamata ahannu,
idanuwanta ba sa ganin kowa sai shi,
kunnuwanta ba sa sauraron kowa face kalaman
yaudarsa da izgilanci. Dalilin da yasa kenan
kalma daya bata tasiri a hrt dinta, a duk tsahon
jawabin da Umma tayi, da ka dubi fuskarta, zaka
gane bata yarda bane kawai. Murya cunkushe
tace, ni babu abinda Al'ameen yayi min Umma,
kawai raina yafi kwanciya da Danliti kuma shi
nake so na aura. Haushi kamar ya kashe Umma
ta mike tsaye. Tace, to baki isa ba! Mu dan Liti
baiyi mana ba, idan kina da wasu iyayen da za
su dauta miki auran to bismillah! Ya ci gaba da
fadin, ai kuwa bata isa ba, ni zanje in dauko ta
kuma dole ta auri wannan yaron tunda itace tace
tana so tun farko! Yace, Yaya duk yadda kake
tunanin al'amarin nan ya wuce nan, amma ka
gwada ka gani, kilan kai tafi jin tsoronka, sai
dai kafin nan xance Al-ameen din ya kira ka,
kuyi magana, don ni gaskiyya ban san me xance
masa ba. Yace ba wani abu xan rarrasheshi, ya
kwantar da hankalinsa, kaima yaunxun nan ka
kama hanya kaje ka yiwa Hajiyansa bayani, kace
kar su damu ba wata matsala bace babba. Ya
numfasa ya amsa da to kawai. Lallai babban
yaya yana dau kara abin wasa ne. Suna aje waya
Aunty amina ta nufo shi, me ya faru ne wai? Nan
take ya labarta mata abinda ke faruwa. Tun
kafin ya kare idanunwanta ke waje, wai kana
nufin Mama ta fasa auran Dr? Yace gara da
kikace wai, don bata ida ba. Ni xan je na dauko
ta, cikin gidan nan zata zauna sai ya dawo. Ta
kada kai cikin damuwa, tace amma mama ta ban
mamaki, me Dr? Yayi mata? Babu abinda yayi
mata, wani ta hango saboda rashin hankali irin
naku na mata da butulci! Tace wlh na yadda sai
dai matsalar banyi zaton haka ba daga wajen
Mama ba ganin yadda take nunwa Dr. So mai
tsanani, duk yaudara ce, kai gani kuma a zahiri
ai ta nuna. Amma ai tayi kuskure ni zan gyara
mata zama, don bata isa ta zubda mana mutunci
ba! Tace gaskiyya ne. Allah yasa ta gane. Ya
wuce tebur don cin abinci. Shi kuwa
abdulkareem, bai sami zaman cin abincin ba
gidansu Al-ameen ya nufa ba tare daya san wane
irin bayani xai iya yi masu ba, don hankalinsu ya
kwanta. A haka ya isa gidan. Nan da nan aka
tarbe shi da girmamawa da abubuwan kusa da
baka, marafa baya gari, saboda haka mami ce ke
tare da shi, ina fatan dai kaci abinci? Yayi dan
yake yace, Alhmdlh Hajiya, nagode. Tace amma
dai ko Juice kasha ko? Haba, kamar wani bako?
Yanata murmushin rashin nayi, yana kallo ta
xuba masa ta mika masa, Ungo sha don Allah.
Kuma maimakon kazo min da surukartwa, yau in
riketa cikin gidan nan sai tayi min sati. Ya aje
kofin lemo ya kara gyara zama, Yace Hajiya, hkr
na zo in baki, domin ban sami dawowa da Mama
ba,... Saboda me? Kodai maganar Al-ameen
gaskiyya ce, sakeena na cikin wani hali? Bata da
lfya ko? Ya karkada kai.... Tace karka bote min
komai Baban ameer, duk tsananin da sakeena ke
ciki, nasan yadda xan rarrashi Al-ameen don
hankalinsa ya kwanta. Gaya min me ya faru da
ita? Jikinsa ya kara sanyi, cikin taushin murya,
yace Matsala ce babba Hajiya, wacce ni kaina
ban da ita ba, sai da naje daxun. Ashe tun
komawar ta gida, wani yaro ya hure mata kunne,
shi ya hana ta dawowa. Su abba na ta fama da
ita kuma suna kan kokarin su don ganin raba ta
da shi. Na yi nayi ta biyo ni, taki hajiya, shine
Abba yace in zo in baku hkr kafin yazo. Insha
Allahu za'ayi maganin abin. Gaba daya hankulan
mu atashe suke, al'amarin yana daure mana kai.
Idanuwanta xuru akansa, hannunta bisa kunci.
Tace, wyyo Allah! Wayyo Allah! Me xanji yau mai
kama da almara? Ta goce da sallalami, yanxun
baban ameera kana nufin sakeena tace amanar
Al-ameen kenan? Idanuwanta suka cika da
kwalla, yayi da yaya Abdul ya kara kasa da
kansa. Yace, kiyi hkr Hajiya, a gaskiyya ban san
yadda xan fassara wannan al'amarin ba, amma
abinda nake so ki gane Abba ba xao rungume
hannayensa ya sanya mata ido ba. Haka muma
'yan uwanta. Muddin kuwa tana son albarka dole
tabi umarnin mahaifinta. Shi yasa ya fara turo ni
kafin ya zo da kansa ya ga alhaji. Haka kuma ku
rarrashi Al-ameen ya kwnatar da hankalinsa
komai zai daidaita cikin hukuncin Allah da
yardarsa. Ta cire tagumi. Tace, a gaskiyya ba
zan iya fuskantar Al-ameen da wannan maganar
ba, in katsa masa karatu. Na san ya damu
kwarai ya san halin da sakeena ke ciki, amma
ba xan iya gaya masa wannan mummunan
labarin ba, kuma na rokr ku don Allah ku
kyaleshi kawai. Gara abar shi cikin duhun da
agaya masa sakeena ta sauke alkawarin da ta
daukara masa. Na tabbata komai nasa zai tsaya
jarabawar su gab take da xuwa. Ni da kaina xan
iya xuwa na roketa, ta tausaya wa Al-ameen
karta kashe masa zuciya. Kwalla masu zafi suka
xubo bisa kuncinta bata re da saninta ba.
Hankalin Abdul ya kara tashi, BAKIN CIKI ya
dada lulluba shi. Don girman Allah Hajia karki
xubda hawayenki akan maganar nan. Da yardar
Allah komai zai gyaru. Kamar yadda kika ce kar
agaya masa ba, ba za'a gaya masa ba. Gara ace
masa bata da lfiya ne, xuwa lokacin da xa'a
shawo kanta. Ta goge kwallah, tace ina ganin
hakan zai fi sauki iyaka dai yayi tunanin jikinta,
mu kuma nan mu rinka gaya masa tana samun
sauki. Yace, to shkienan, Allah yasa mudace.
Don girman Allah hajiya kuyi hkr, sakarci ne
kawai irin na yara. Tace, ya za muyi baban
ameer? Dole mu rungumi kaddara. Ya mike babu
isasshen laka a jikinsa, yayi mata sallama ya
fice, batare da hajiyar ta kara ko motsi ba.
Wucewar awa daya da rabi tana zaune xuciyarta
cike da sake-sake iri-iri. Ji take kamar a
mafarki abdul yaxo mata da wannan mummunan
labari, wanda take ganin zai iya salwantar fa
rayuwar dant tilon danta da takeji da shi. Duk
fadin duniyar nan bata hada shi da kowa. Yaya
marafa zaiji, idan wannan labari yake kunnen
sa? Tabbas xai fita shga damuwa, domin yafi ta
sanya Al-ameen ransa, ko alama baya son yaga
ya nemi abu. Waya ta dau ruri a falon, ita ta
katse tunaninta tare da haddasa mata faduwar
gaba mai tsanani. Ta mika hannu ta dauka ba
tare da tayi hasashen mai kiran ba. Tayi sallama
cikin raunin murya. A raunane taji muryar Al-
ameen ya amsa mata kafin yaci gaba da cewa,
mami na, ashe sakeen ba ta da lfiya shine aka
boye min? Ni ban ma yarda bata da lfiya bane
Mami, kawai ku gaya min idan mutuwa tayi, xan
hana Allah ikonsa ne? Ai nasan yafi ni sonta,
kuma ta shi ce ban isa in hana shi amsat
kayansa ba.... Tace saurareni Al-ameen, kar
hankalinka ya gushe.idan baka yarda ba da
maganar yayun sakeena ba, ai ni mahaifiyar
kace, ba xan rufe maka komai ba, ka yarda ko
baka yarda ba? Murya na rawa ya amsa, Na
yarda mami, tace to sakeena bata mutu ba,
rashin lfya ce ta sameta aka maida ta gida.
Bana so ka damu da yawa, domin sosai take
samun sauki, gobe ma xan sake xuwa in dubo ta,
kaji? Ya numfasa yace, amma Mami me yasa
za'a ajiyeta gida? Akaita asibiti mana, ko can
xariya xanyi magana da abokina, na tabbata xai
kula da ita tamkar ni. Pls mamy ki basu shawara
idan kinje goben. Tace ba ciwon asibiti bane,
shedanu ne suka tabata, kuma su iyayen nata
suna tsye neman magani. Kai ma kasan xa su
xauna ba. Ni dai rokona gareka shine ka nutsu
ka kwantar da hankalinka, ka fuskanci jarabawar
ki mai xuwa. Ka zama mai imani da Allah, shi
xai sa ya karbi addu'ar ka idan kayi mata. Ka
jini? Ya goge kwalla, yace naji mami don Allah
idan kinje ki dafa kanta ki karanta mata ayatul
kursiyu, falaki da nasi. Idan har gane ki ko da
baxa ta iya miki magana ba, ki gaya mata Al-
ameen dinta na gasheta, kuma xan ciga ba da yi
mata addu'a har xuwa lokacin da xanji muryar ta
a waya. Idanunwanta suka tara kwalla. Tace,
Insha Allahu xan gaya mata, tare da dukkan
abinda kace, muddin kayi min alkawarin zaka
kwantar da hankalinka. Da sauri ya amsa, Allah
nai miki alkawari mami, kinsan bani da wani
buri daya wuce in faranta maku rai. Tace, Allah
yasa dalilin alkawarin da kayi min Ubangiji ya
yayewa sakeena abinda ya sameta! Yace, ameen
Mami na! Dadina bai dawo ba ko? Bai dawo ba
sai zuwa jibi. Yace Allah ya dawo da shi lfya. Ta
amsa da ameen. Yace ki gayawa su iya su taya
mu da addu'a, Allah ya taimake mu. Tace, xan
gaya musu. Al-ameen, karka damu kaji? Murya
raunane ya amsa, to mami sai kinsake jina. Bata
iya kara komai ba ta aje wayar, domin muryarsa
kawai ta isa jefa mutun cikin damuwa. Taci gaba
da xama dauke da tagumi tunani na cin xuciyarta
fiye da tunanin mai kallonta. Haka al-amarin
yake wajen Al-ameen, domin dai rayuwa tayi
masa tsauri kuma hasashen rashin lfiyar Mam
yafi koma zama cikin ransa. Ba don yayi wa
mamy alkawari ba, da babu makwa zai iya baro
abinda yakeyi ya dawo ya ganewa idon sa
Mama, tana cikin mummunan hali. Kafin kace
kwabo, kowa ya fahimci samun sauyin sa, domin
ya yamutse ya wayi garim duk kuzarin da
nutsuwar sa basu jikinsa. Yana zaune addu'a
yana tafe addu'a, haka acikin aji, hankalinsa
yafi rinjayea ga addu'o'in da yakewa mama cikin
ransa. 12pm washegari lokacin ne motar Mami
ke fakin kofar gidan Uban dawaki. Yayin da
mama ke kwance rankas ciwon jiki, sakamakon
fadowar da tayi daga mota. Can da nan bata iya
motsawa, Baraka ke tare da ita tana zazzaga
mata nasihohi, duk da ta san bata sauraron ta,
sai dai ya zama wajibi gareta, ta kara gaya mata
gaskiyya. Mami tayo sallama falon ta shigo,
gaban Umma ya yanke ya fadi. Ta amsa tana
fitowa daga dakinta. Yake baki kawai takeyi,
amma zuciyarta ta shake take da takaici tare da
BAKIN CIKI mai tarin yawa. Ga wata kunya da ta
yo wa idanuwanta dirar mikiya, mai alaka da
ciwon dundumi. Sannu da xuwa Hajiya! Ta amsa
mata da fara'ar karfin hali. Ta nuna mata kujera
ta xauna, tana kara yi mata sannu da xuwa.
Sannan ta debo mata abubuwan sanyi masu
ruwa. Ruwan ta fara xuba mata, ta mika mata ta
sha. Suka gaisa cikin girmama juna. Ta kara
gyara xama, tace, sai kika ganni da rana tsaka
ko? Fuska kunshe da tashin hankali. Tace ke dai
bari, nasan kin sami sako maras dadin ji. Ta
kada kai dauke da damuwa. Tace naji sakon da
ya hani barci jiya, wanda ya sanya ni rama kafin
safiya. Ina jajantawa shi kansa Al-ameen da ya
sallama rayuwarsa kaf kan sakeena. Nayi kuka
da wadannan idanuwan nawa, don na tabbatar da
amsata ba alkhairi bace a gareni, domin komai
zai iya faruwa ga tilon da na, farin ciki na kuma
sanyi idona. Shi ya sa nace xama bai ganni ba,
tilas inxo in rarrashi sakeena, ta tausaya min kar
in rasa Al-ameen. Wadannan kalami sosai suka
sanya hawayen Umma suka tsinke nan take, ta
rasa me zata ce wa Mami ta sanyaya mata rai?
Dole tayi kuma domin dai bata da kwakkwarar
mafada, mama na nan akan bakanta babu sauyi.
Da kunnunwata ta, taji lokacin da take gaywa
Baraka tabbas zata iya kashe kanta, saboda
Danliti. Mami ta cigaba da fadin ki daina kuka
Hajiya, Baban ameer ya gaya min tashin
hankalin da kuke ciki, kukan bashi da
alfanu.......
HAUSA
BAKIN CIKI 2***4(TRUE LIFE STORY) umma ta
hare kwalla ta katse ta Tabbas mama bata da
lafia ciwon daya kamata mai tsanani ne maganin
Allah, dole kuwa in yi kuka , don mama ta dasa
mana BAKIN CIKIN da ban taba tunani ko
mafarkin irinsa ba daga ni har Abban ta mu na
cikin rudu tare da mamakin yadda wannan
alamari ya kasanze haka, hakuri zakuyi hajia
sannan ku taya mu addua mama kam ko ta so
ko taki doke ta auri Alamin, tunda zabin ta ne na
farko bamu muka cusa mata shi ba. Hasali ma
bamu san lokacin da suka hadu ba. tsabat rashin
kunya ce irin t yayan zamani da rashin sanin
mutuncin mutane. saboda. haja hajia karki damu
kuma dabarar da kikayi wa alamin tayi daidai
sai dai akwai sauran rina akaba domin fadar
kalmar ciwon ma ba zai bar shi yayi sukuni ba.
Tace zaifi sauki akan a gaya masa gaskiar
magana ni na dauki dawainiyar kwantar masa da
hankali kullun ya kira waya. Tace to shikenan
Allah yasa mu dace ta ce ina sakinar take mu
gaisa Ta mike tana fadin Taso muje in kaiki
kwance ma take bata iya tashi. Ah me ya faru?
ina fatan ba dukanta kukayi ba, ta ce Baban
Amira bai gaya maki bude mota tayi ta diro kasa
ba? ido waje ta dafe kirji ta diro daga mota?
tace ya wuce wai! zo muje ki ganta ta tashi
dauke da mamakin tana fadin naga abinda ya
ishe ni ni yasu, sakina da gaske take bata son
Alamin. suka cusa kai dakin, baraka dake zaune
bakin gado ta mike tana gaishe su. umma ta
nuna wa mami wurin zama a bakin gadon tace
zauyna hajia kinga idanuwan maras kunya ta
juya kan mama taci gaba ga hajia nan tazo da
kanta inkinga dama ki bude ido ta kudundune
kai cikin pilli mami ta dube su tace ku bamu
wuri hajia ita baraka suka bar dakin mami ta
karasa matsowa tasa hannu ta birkito ta kuka
taga tanayi tasa hannu biyu ta tallafo kuncin ta
ta sanyaya murya tace sakina dan dubeni kinji?
ta dago idanuwa jajur ta dube ta hawaye suka
wuce bisa kuncinta. mami ta kara goge su . ta ce
na san ba'a siyan so mama da yau nayi cinikin
sa ko nawa ne na siya wa alamin, koda zai
kasance zani daya zai rage min a fadin duniya.
amma kash hakan ba zai taba yuwuwa ba, sai
nayi imanin ko dan yaya ne kin san mahimamcin
rike alqawari me yasa kika dauki alqawarin da
ba zaki iya cikawa ba? me yasa kika yaudari shi
kika bari tsananin son ki ya zauna a zuciyarsa?
kina so ki kashe shi ne sakina? ki tausaya min
ana gaya masa sakon nan zuciyar sa zata iya
bugawa ya mutu mama. shi kenan na rasa shi
kuma ban da wani alamin na sonki mama sai dai
ayi zancen dan adam ssaboda haka ki gaya mani
abubuwan da yake miki wadanda baki so har
suka sanya ki tunanin fasa aurensa. wallahi nayi
maki alqawarin zan masa fada tare da lallashi in
kuma. gargade shi kinji? gaya man matsalarki da
alamin. hawaye suka ci gaba da ambaliya bisa
fuskar mama domin ko sunan alamin bata son
ana ambatowa tsawon lokaci bata tanka ba sai
kwarara ruwan idonta kamar zai kare mami ta
sake fadin da alama alamin dai bai maki komai
ba sakina tsuntsun son sa ne kawai ya tashi
daga kansa ya koma wa wani ko? ta kara aje ido
kasa mami tai wawan ajiyar zuciya idanuwanta
suka kawo kwalla baki man halacci ba sakina a
iya tunani na mutuwa ce kawai zata raba ki da
alamin shi yasa gaba dayan mu muka dora burin
mu a kanki. bamu da wami buri face Allah ya
nuna mana ranar da zki zama mata danmu sai
gashi dare daya kin juya mana baya. A tunani ki
kinyi daidai? baki gudun kar amana ta ci ki
sakina? kiyi tinani cikin natsuwa duk wanda ya
ha'inci wani Allah ba zai kyale shi ba. zan barki
kiyi tunani kan magana ta. idan kin canza ra'ayi
ki koma minna zuwa gobe Alamin yaji ki
hankalinsa ya kwanta kinji? yace in gaishe ki
kuma yace inyi maki addu'a. Ta taimaka mata ta
kwanta a hankali idanuwanta rufe suke yayin da
mami ta dafa kanta tayi mata addu'oi da alamin
yace tayi sannan ta kirata ta bude ido. nizan
koma sai najiki a minna karki bari shaidan ya
rinjayeki ki bar mai tsananin sonki cikin kunan
zuciya nakasa zaiyi kinji? ta lumshe idon a natse
mami ta wuce ta bar dakin umma ta shiga tare
da sallama ta nemi wuri ta zauna yayin da
baraka ta fice. ta basu wuri ta saurareki? tace
to! bata dai tanka ba sai kuka da zan fito. ma
nayi mata addua' kallo na ta dinga yi. da alamun
za'a dace tace kwarai da gaske bari in lallaba
hajia zan shiga wajen gwaggo sannan mu wuce .
to a gaishe ta da kyau Allah ya kiyaye hanya
Suka wuce suna fadin"Amin"har kofar gida tayi
mata rakiya,motarsu ta daga ita kuma ta dawo
gida dakin mama a koma suka taru da baraka
suka ci gaba da yi mata nasihohi tana
kudundune bata tanka ba,balle su gane me take
nufi,Awa guda bayan tafiya mami yaya. Abdul-
kadeer ya iso gidan daidai lokacin kuwa Abba ya
dawo gidan,yayan tare yake da dakarun sojoji
guda uku,duk suka fito,suka toge suna sarawa
abba,sannan suka gaishe shi tare da yayan suka
rankayo yana ruwan masifa, maganar banza
yarinyar nan take yi,mu makace ta kawo shi ko
mu muka hadasu wannan ai iskanci ne yanzun
nan zan wuce da ita shiya na dauko kuratan nan
su yi min gadinta a mota na ga ta inda zata
fito,Nonsense kawai" Abba yace kayi daidai
domin ni mama ta ginsheni ko ganinta bana
sonyi cikin gidan nan,saboda "BAKIN CIKI",abu
kamar al'mara yana so ya zama gaske yarinya
ta bamu kunya ta zubar mana da mutunci basu
ma san sun shigo falon ba sai da umma tace
maraba da babban yaya yace sannu umma
bamuyi sallama ba ko?raina bace yake ina
mama?tana daki ina fatan tafiya kazo yi da ita
sosai kuwa umma akwai kurata uku nazo dasu
wadanda zasu gyara mata zama muddin tayi
yunkurin bata mana lokaci tace yayi kyau wallhi
yanzu ma hajiyar al-amin ta bar gidan nan
bakaga uwar kunyar da ta lullubeniba na rasa
inda zansa kaina Abba yace tazo kikace"tana ma
cikin garin nan bata wuce ba"Abba ya nemi waje
ya zauna ya kama kai,shi kuwa yaya babba
dakin ya nufa kina jina baza ki fito ba"umma
tace da wace kafar zata fito bayan ta kusan
kashe kanta,yace kadan ta gani amma yau sai
kin bar garin nan ko za ki mutu!Useless girl!kina
nufin ki zubar mana da mutunci ko,baki. Kai
wannan matsayinba,I swear,kin ji na rantse"yasa
hannu ya fisgo ta da karfin sa yana fadin"stand
up my friend"ta tsandara kara mai garfin gaske
saboda gaba gabobain ta suka amsa suka kaiwa
kwakwalwar ta zuwa falon dole gabobin suka
loma aiki ashe dama wuri suka samu. Ya
dankwafar da ita bisa kujera tace wayyo na shiga
uku yace"No lokacin bai zoba tukuna sai kin ci
gaba da bijire wasu umma I'am telling you! yau
abuja zamu wuce ki zauna can, sai lazy doktan
ki ya dawo ai ke ki ka zabe shi tun farko so now
you have no reason ki ce kin fasa bayan kun
kusa aure ya dubi umma yaci gaba karki ji
tausayinta ta umma ki fidda ta a ranki har sai
tayi biyayya a gareku, Ta kada kai tace tuni
mama ta fice min a rai balle tausayinta ko alama
babashi cikin raina ka tafi da ita duk abinda ya
dace kuyi mata don ta gane kuskuranta yace
wannan dole ne Abba bari mu wuce umma ta
fara magana bari in hado mata kaya yayin da
abba da babban yaya kamar zasu cinye mama a
falo kuka take tamkar za a zare mata rayuwa
umma ta fito da jakar kayan ta wurga mata gyale
bisa jiki,yaya soja ya mike tashi karki bata min
lokaci taki mikewa yasa hannu ya maketa
sannan ya cafko. ta yana fadin zan iya karya ki
u know dat! gara ki shiga hankalinki bai sake
taba har kofar gida ita kuwa umma cikin sasa ta
shiga ta gayo masu za a wuce da mama don
haka suka yo waje ganin yadda za a yi saboda
suji dadin karaars wa. A gaban su ya cilla wa
kuratan daya zo da su ya ce kusa min ita a
mota! kan kace kwabo mama na cikin mota,
suka sanya ta tsakiya yayanta na gaba sanda ya
jefa jakarta a but yaya ya juya da sauri ya zauna
matsayin driver babu bata lokaci ya murza
mukulli mota ta tashi ya bar wajen, idanuwan
baraka suka cika da kwalla nan da nan ta fasa
kuka ta koma cikin gida da gudu. sauran matan
na ta fadin Allah ya kiyaye hanya ubangiji yasa
a dace. umma ta juya ta shiga gida su suka biyo
bayanta . ganin hankalin umma yayi mummunan
tashi yasa hajia gaje ta janye hajia hajo cikin
gida ta mika hannu suka tafa sannan ta tallafe
haba ido waje tace Ashe abin har ya girman
haka? wanan sojoji kamar an zo kama
gagararren barawo? ta ce ai kamar hakan ne
tunda ta gagari iyayenta. zamuga ikon Allah
yarinya na neman tayi wa iyayenta bakin cikin
daula, sun ga samu zasu ga rashi ai kinga haj
halima kamar ranta zai fita sai kace dole suka
sake tafawa haj hajo tace Hakki ne nake gaya
miki kadan ma suka gani badai danliti ta jajibo
masu ba? Allah dai ya kiyaye lalacewa! ta tabe
baki Nayaushe kuma? wai ance wa kuturu Allah
ya laance ka! shagonsa fa take zuwa tsinancewa
ai ba sai an tambaya ba! hajia hajo tace Allah
shi kyauta haj gaje ta amsa na gaba domin dai
wannan ya riga ya faru anyi abin kunya maga
yadda za ayi! sun jima suna yada labaran banza
da karairayi kai duniya ina zaki da mu? rayuwa
kenan uban dawaki da umma suna kallon ikon
Allah suna fama da BAKIN CIKI sai fatan Allah
ya musanya masu alkhairi Mama kuwa tun
isowarsu Abuja take kudundune cikin daki duk
hargagin yaya soja baisa ta dauki lomar abinci
tasa wa bakinta ba,al'amari ya daure wa anti
amina kai ta zauna ta siga yayyafa mata
nasihohi da rarrashi ko Allah yasa ta gane amma
ina Alla bai nufa ba tukuna shi kuwa soja babu
abinda ya dame shi cewa yayi zai fi kyau da
zata bari yunwa ta kasheta a yau hakan kuma
shi zai tabbatar masa ta cika mai kunnen
kashi,yasa kai ya bar gidan amma kuratan
sojojinsa na nan tsare da gidan bayan masu gadi
mutun biyu ke nan yanzu sun zama su
biyar,kafin yamma mama taci kukan daya fidda
ta daga hayyacinta bama ta jin tarin yunwar da
ke cikin ta saboda tsananin tashin hankalin da
take ciki domin ita kanta ta san ta shigo kurkuku
zai yi wuya ta kara ganin dan liti sai dai tunanin
ta bai yanke ba duk tsananin da zata shiga baza
ta taba auren wani ba dan liti ba.
BAKIN CIKI 2***5(TRUE LIFE STORY) Saboda
haka taci gaba da zama cikin kunci da yunwa
har bayan sallar isha'I yayanta ya shigo gida
kamar shi alamin ke kira wayar sa ta hau
bugawa falon kai tsaye kan wayar ya nufa ya
dauka yayain da malami ya sheko da gudu don
yi masa oyoyo.anti Amina ta biyo bayansa daga
jin muryar al'ameen kasa yana cikin farin ciki da
doki cike da zuciyarsa ina yini yaya,yace lazy
dokta ya karatu?"Yana yar dariya ya amsa
Alhamdulillahi ai na kira can minna don in
tambayi jikin mutunniyar sai aka ce min ta sami
sauki harma ka taho da ita, yace haka ne amma
kasan yana yin rashin lafiyar sai a hankali cikin
dan kankanin lokaci sai ta birkice bari in turo
maka ita,koda kaji sauyi daga gare ta kar ka
damu haka yanayinta ya sauya,jikin sa yayi
mugun sanyi duk a lokaci guda gabansa ya ci
gaba da faduwa murya dishe yace to yaya Allah
dai ya bata lfy,ya amsa da amin ya aje kan
wayar gefe ya amsa gaisuwar iyalinsa sannan ya
haye sama ya fada dakin mama yana shiga ta
kara kudundinewa cikin bargo yasa hannu ya
kwashe bargon ya watsar gefr yace tashi zaune
sai ga antin ta shigo ta matsa bisa shimfidar ta
birkito ta tana fadin yi mata a hankali ke mama
tashi kinji! Ta ciccibo ta ta tashi zaune kamar
wacce ta shekara tana ciwo saboda tsabar fita
hayyacin da tayi Tausayi ya lullube antyn a
hankali tace kinaji na? Ga alamin cen ya kira
waya don Allah ki fidda mu kunya ki tashi ki je
ki saurare shi badon mu ba sai don girman
Alkawarin da kika daukar masa kafin ya tafi
tashi kije kudinsa na bin iska kinji? Tamkar
antyn na magana da dutse don ko motsi batayi
ba sai idanuwa ta ke ambaliyar ruwan hawaye .
Haushi da takaici suka rufe yayanta ya daka
mata tsawa mai tsanani sai ta zabura bazaki
tashi ba? Alamarin ya kara kure su cikin
mamaki sukaji wannan kalmar ta fito bakinta
Nifa yaya ba zanyi magana da kowa ba Gaba
daya suka ware ido baki sake sai dai shi soja
baya tsayawa yana kallon raini don haka ya cira
hannu ya tsnke ta da wawan marin da yayi
sanadiyyar daukewar numfashinta karkaf,ta zube
sumammiya ya nuna cikin zafi yace ni zakiyi wa
rashin kunya ba na wasa da ke ni zan iya karya
ki wallhy anti amina da tuni take kwasar salati
tace ai maganar karyawa ta kare tafa suma
yallabai yanzu me za a cewa Al'ameen din Yace
ta mutu ni tayiwa rashin kunya bata isa ba
wallahi!Mtsw"ya ja dogon tsaki ya bar dakin
falon ya sauka ya dauki kan wayar ya kanga wa
kunnensa hello al'ameen naji na ya amsa ina
kinka yaya yace kayi hakuri da mama al'ameen
ya katse shi me ya faru yaya ina take yace ta
suma al'ameen kayi hakuri da ita domin mama
ta riga ta sami matsala....". Ya sauke salati ya
katse shi yaya bazan iya hakura da sakeena ba
kowane irin hali ta shi ina son ta haka koda
kuwa ciwon hauka ne ya kamata,Roko na gare
ku shine ku taimake ni ku kai ta asibiti don
Allah ko nawane zan kashe yaya please ku
taimake ni ya goge hawayen dake zuba bisa
kuncinsa yayin da jikin yaya soja yayi mugun la
a sar cikin taushin murya yace kar ka damu
al'ameen zamu kaita kar ka damu kaji sai da
safe. Ko kamin ya gama amsawa ya kife kan
wayar al'ameen sai da ya lalubi wuri don baya
gani yadda ya kamata sauran abinda ke zuciyar
sa kuwa biro na ba zai iya rubuce shi ba domin
al'amarin gagarumi ne maras misaltuwa sai dai
muce Allah ka kiyashemu sharrin masu sharri
amin summa amin Anti amina keta faman
neman ran mama shi kuwa yayanta bai sake
komawa ta kanta ba dakin sa ya shige don yin
abubuwan da yake ganin suna da muhimmanci a
gare shi ita kuwa mama zafin. Mari da tsananin
yunwa tare da tarin damuwa su suka taru suka
jefa ta cikin doguwar suma awa daya da rabi ta
kwashe babu motsin rai sannan ta dawo
duniya,ta fasa kuka tana fadin wayyo Allah na
zan mutu wayyo Allah! wayyo!" Nan da nan
hawaye suka tsunkewa anti amina saboda
tausayin da ya kamata murya na rawa ta
tarairayo ta tana fadin mama ki tausaya wa
kanki wannan mugun halin da kika jefa kanki
kin kuwa ga yadda kamannin ki suka sauya wane
irin masifar so ne wannan na bala'I. Akan da
namiji kike wahalar da kanki a banza a wofi ki
mutu ya nemi wata ya aura,wannan sakarci ne
mama kiyi wa kanki fada tun dare bai miki ba
sannan ki sani idan kika ci amanar al'ameen
Allah ba zai kyale ki ba,ta fizge jikin ta ta sake
faduwa bisa shimfida ta kara fasa kuka, malami
ya budo kofa ya shigo cikin sanyin jiki ya karasa
gun su yace mami uncle al'ameen ya bugo waya,
kafin anti amina tace wani abu tuni mama tayi
wuf ta tashi zaune cikin sababi take fadin ba za
a zo ba kaje ka gaya masa bazan dauki wayar ba
dole ne sai na aure shi nace. Ba zan aure shi ba
duk ku taru ku kashe ni kowa ya huta ta sake
komawa ta dase ciki anti amina da malami suka
saki baki suna kallon ikon Allah. Jimawa kadan
ta dube shi tace,Mu je falon." suka fice jiki babu
kwari,musamman Malami da sababin ya bashi
tsoro ba kadan ba.Anti Amina ta dauki wayar
tayi sallama,suka gaisa kafin yace, Ya jikin
sakeenar? Ta farfado kuwa? 'Ta farfado Al-
Ameen, har ta samu barci. Ya sauke
numfashi,'Allah ya kara mata lfy. To amin.yace
Anti,don Allah ki taimaka ki tuna wa yaya tafiya
asibitin.Ni ina ganin babu abinda zai gagari
asibiti koda matsalar junnu din ne, akwai ta su
irin gudumawar da zasu iya badawa. Please Anti
a kai ta asibitin a gwada." Idanuwan ta suka
kara tara kwalla,jin yadda muryar sa ke rawa,ta
tabbata hawaye ne ke zuba bisa kuncin sa.Ta
numfasa tace "karka damu Al-Ameen,duk wani
iya kokari ana yinsa.inshaAllahu Allah zai dube
mu ya yaye mata wannan lalura.ka kwantar da
hankalinka kaji? Ya amsa,Hankalina ba zai
kwanta ba Anti,har sai naji muryar sakeena da
bakinta ta gaya min tabbacin samun saukin.Ban
san halin da sakeena ke ciki ba Anti,kowa cewa
yake tana samun sauki,amma ni ban ji alamun
ba a jiki na.zuciya ta tana min sake-sake iri-iri
akan sakeena kuma tana nuna min ita acikin
mummunan hali.jin muryar ta ne kadai zata
warware min rudun dana fada.....Anti Amina ta
amshe,komai yayi zafi mgnin sa Allah Dokta.ka
tsaya wa addu'a kawai ita ce kadai zata taimake
mu.shi kenan Anti,ngd.Idan Allah ya kaimu gobe
zan sake kira ko na dace jin muryar ta.Tace To
Allah ya yasa a dace.ameen Sukayi sallama ta
aje waya ta koma bisa kujera ta kama kai hannu
biyu ta matse kwallan ta tace wannan masifa
Allah ka yaye mana,muryar mai gidan taji yana
fadin kema zai zauna kina bata lokacinki yau mu
ma bazamu ci abinci ba ke nan Ta share fuska
ta dube shi yallabai ba ka ki kalaman dokta bane
su suka kara dafani wallahi ya ya zamuyi da
yarinyar nan ne yace oho!ni kizo ki ban abinci
ina jin yunwa ta mike ta nufi kicin shi kuma ya
wuce ebur yana kiran malami ya sauko da gudu
yana amsawa gani dadi kaima yau baza kaci
abinci. Bane yace ai na ci dadi to koma daki
kayi barci sai da safe,ya juya ya haye saman
yayin da anti amina ta fito da jerin kayan abinci
bisa tire ta jera bisa tebur sannan ta zuba masa
taja kujera ita ma ta zauna yana ci tana maida
masa kalaman al'ameen sai da ta kare ya kurbi
ruwa ya dube ta, Yace ni kinga duk wannan
shiriritar ina yi ne kawai saboda hajiyar sa ta
roki a rufe masa amma ni ban ga dalilin yawo da
hankali ba yanzu ina fa'idar yin shirun tunda
hankalin sa da ake so ya kwanta bai kwanta ba?
mama ko zata mutu shi zata aura to me ne ne
abin jin tsoron gaya masa matsalar da ake ciki
banda shiriritarku ta mata,ta ce ai ba haka bane
yallabai kaga kuma shi kansa marafa ya goyi
bayan hakan"shi ke nan sai ki yi ta rarrashinta
kafin gobe idan ta amince yin maga da shi shi ke
nan idan kuma taki kya nemi wata karyar ki
shirya masa kinga sharo karya ya same mu ke
nan sai abinda Allah yayi ina amfanin sa Ta
numfasa tace al'amarin hakuri zamuyi tayi
rokona gare ka don Allah ka daina dukanta
wallahi taurin kai zai kara mata ido waje yake
magana muddin tayi min rashin kunya zan
tabbatar da na hukunta ta yadda ya kamata don
ni ba sa'an ta bane,you know that so ba zan
dauki iskanci ba kina iya hawa sama idan kin
kare maganar,tace ran maza ya huce yallabai ba
ina nufin wani abu bane yaci gaba da cin
abincinsa bai tanka ba ta zura masa ido tana
dan murmushi ta san halin yan kayan ta idan
kayi magana kaji yayi shiru to kaima ka tsuke
dan bakin ka ka kama kanka shi zai fi zama
alkairi. Garin Allah ya waye,baya ga sallah babu
abinda Mama ta aikata,ta yada kai bisa kafet
tayi lamo kamar sumammiya.Gaba daya ta
rame,fuskar ta ta tsuke duk ta bushe idanuwanta
sun kode sun firfito waje, sbd tsabar
kuka.Malami ya fito wanka ya tsugunna gabanta
yace "éÂÂæ²¶a kwana Anti?Tayi banza dashi,ya zura
mata ido,Baki da lafiya ne Anti? Tunda ku ka zo
da Daddy baki min mgna ba. Ta ballo masa
harara,sai na tsinka mka mari ka sake min
magana! Ta ja tsaki,ta juya kan ta wani
gefen.Haushi ya kama shi,ya tashi ya ci gaba da
shirin sa. Wannan karon kam bai gane kan gadon
Antinsa ba. Me ke faruwane? Karfe bakwai daidai
Anti Amina ta shigo,tana shigowa Mama ta
rintse ido. Anti Amina ta dauko bisa kanta,ta
dan dafa ta na san ba barci kike yi ba,ki tashi
don girman Allah ga Dokta can ya kira. Kamar
yadda na gaya miki jiya so yake yaji muryar
ki,hankalinsa ya kwanta ko da gaisuwar sa ki
amsa,zai ji dadi Mama.
BAKIN CIKI 2***6(TRUE LIFE STORY) Ku da baku
wurin in kun amsa.To Mama ta amsa. Haushi
kamar ya kashe anti Amina.ta mike tsaye tace,
kar ki tashi Mamaa,idan kin sake jin nayi mik閾�
mgn akan Al-Ameen,duk abinda kika so kiyi
min! Mts....... Ta ja tsaki ta wuce. Mama ta
rakata da nata dogon tsakin anti amina ta waigo
rike da kugu ta zubo mata ido,lallai mama,ni
kike yiwa tsaki? Yayi miki kyau! Taja kofa ta
fice.kan wayar ta duka rai bace. Tace, hello!
Yace hello anti,ta tashi? Bata tashi ba dokta.
(nace"dokto ka fiya nace dolene?) "ba matsala,ai
barcin ma yana da amfani a gareta.zan sake
kira,ngd ant閾�. Cike da tausayinsa ta amsa,kar ka
damu sai anjima. To suka aje waya. Ta haye
sama shake da haushi,amma bata nuna wa
yallabai ba,don ta san ita zai tsatstsage danya.
Iyaka tace da shi bata tashi barci ba Wasa wasa
mama fa har ta sake kai bayan la'asar batasa
kwayar abinci a bakinta ba hankalin anti amina
ya tashi kwarai da gaske mama kam bata cikin
hayyacinta gaba daya ta galabaita yunwa na
neman tayi mata illa koma in ce tayi
matan,shiyasa tana jin waya na ta bugawa taki
dagawa don tasab mai kiran kuma bata da
abinda zata gaya masa a hakikanin gaskiya ma
hankalinta yafi rinjaye akan mama dake ta zama
da yunwa tun safiyar jiya Tayi fada tayi rarrashi
duk a banza misalin karfe biyar ta hada tea ta
shigo da shi dakin wai ko Allah ya bata sa'a ta
dan kurba me zata gani mama ke ta madedewa
tsakar daki wata irin farar kuffa na hauhawa bisa
bakin ta,tasaki kofin tea ta tarairayo ta tana
sallalami kinga irinta ko mama nayi nayi dake
kice abinci kin ki kina so ki kashe kanki a banza
a rude ta sake bazamowa falo ta dauki waya ta
kira wayar ofishin yaya abdul kadeea ta shaida
masa halin da mama ta shiga Amma yanzu za a
fara wucewa da ita asibiti nan take ya bata izini
yace zai same ta asibitin babu baa lokaci soja
daya ya sakata mota anti amina na tare da ita a
gidan baya tana shafa mata ruwa a fuska sojan
na jan motar an bata gado ga ledar ruwa na aiki
a jikinta, wucewa minti talatin yayan ya iso ya
same su jugum jugum,suna kallon ta rai bace ya
watsa hannaye aljihu yace dama haka take so ba
kuma shi zai taimaketa ba muddin tana motsin
rai al'ameen ne mijinta so idan ta farfado ki fara
gaya mata kafin na dawo zan koma ofis muna da
mitin,tace to adawo lafiya ya wuce cikin
kuzarinsa kuratan sa na biye da shi har bakin
mota suka koma sannan guda ya bude masa ya
shiga direban yaja suka wuce,anti amina ta ci
gaba da zama dauke da tagumi zuciyar ta na
mata saka iri iri haka wayar al'ameen ke ci gaba
da bugawa cikin gidan ba a dauka ba malami ya
shigo gidan dawo war sa ke nan daga maka
ranta,kicin ya wuce kai tsaye saboda yunwa ce
ta koro shi ya debo abinci ya zauna ya fara ci
waya ta sake daukar ruri ya mike da filet din a
hannunsa yana kara lomar shinkafa da salad ya
dauki waya baki cike da abinci ya ce hello hello
malami al'ameen ne ba kowa ne a gidan yace eh
nima yanzu na dawo school mai gadi ya gaya
min sun tafi kai anti mama asibiti wai ta suma.
Jikin al ameen Ya kara mutuwa ya ce gaskiya
Uncle duk ta rame kamar ba ita ba bata magana
sai kuka Tunda suka dawo da dadi ba ta ci
komai ba ko ni bata. Yi min magana ba sai yau
ta ce za ta mare ni idan na sake gaishe ta wane
irin ciwo take yi uncle hawaye suka tsunke wa Al
Ameen. Bai san lokacin da ya kife kan wayar ba
malami yabi ta hannunsa da kallo. Bai gane
komai ba dan haka shima ya aje ya dauki
abincinsa ya cigaba da ci yayi sallar magariba
dadinsa ya shigo yayi masa sannu da zuwa ya
amsa ya haye sama ya cire kaki yasa kana nan
kaya jaket da wando ya sauko ya shiga kicin ya
hada kayan abinci cikin dan matsakaicin kwando
ya kira malami yace kai mota ya jirashi can su
tafi asibitin,yace dadi yauwa uncle al'ameen ya
kira waya dazun me kagaya masa na gaya masa
anti ta sume kunje kai ta asibit to ke ka kirani a
mota ya dauki kwando yayi waje jim kadan
dadinsa ya fito suka tafi har zuwa lokacin mama
bata gane kowa yayan ta ya zauna nan zuwa
goman dare sannan suka koma gida da malami
Anti amina ta kwana tare da ita kiran asubahin
farko ta dawo hayyacinta ido ta zurawa anti
amina kafin ta fasa kuka anti amina ta matsa
gare ta ta dafa ta saman goshinta tace me yasa
kike wahalar da kanki bayan ki na sane da cewa
aure tsakaninki da al'ameen babu fashi,ta goge
hawaye wallahi wallahi anti bazan. Taba cin
abinci ba har sai yaya ya maida ni inda ya
dauko ni kinji kuma na rantse bazan kaffara
ba,baki sake take kallonta tama rasa ta cewa
mama ke ci gaba da fadin na gwammace na
mutu da a raba ni da dan liti sabo da haka mu
zuba nida yaya idan jan idonsa zai sa in daina
son dan'liti anti amina tace gadkiya ne kuma
yanzu kika tabbatar min kinyi nisa ka kya jin
kira To abinda zan gaya miki shine ki guji bacin
ran iyaye rayuwa ki ba zatayi kyau ba muddin
kika bar mahaifanki da BAKIN CIKI sannan dole
ki fuskanci kalubale tunda kika ci amanar dokta
bazan rufe miki ba mama koda nan gaba in ta
Allah ta kasance zaki tuna dani kice na gaya
miki a asibitin nan wallahi yadda kika sanya
al'ameen kuka da radadin zuciya kema sai dan
liti ya dandana miki fiye da hakan Da namiji ne
fa ki bari ya gama shanye romon da yake hange
a jikin ki kisha mamaki daidaiku ke da rikon
amana su ajiye ki ke kadai suna girmamaki a
matsayin matar sunna mai tsananin kamanta
gaskiya shi ne zai ce kik zai kara aur amma
sauran shagalinsu suke sha a waje su barki hoto
a gida balle wannan Dan'liti daya sami shaidar
banza don haka kibi a hankali mama so ba
hauka bane tace na ji kin fada amman yarda ba
dole bane ko ashe kin gane domin ni duk abinda
mutun zai fadi akan Dan'liti ina daukar sa a
matsayin hassada ina abin hassadar ga Dan'liti
koda ban san shiba labarinsa ya gamsar dani
kuma na tsane shi idan kin tsane shi ki daina
maganar sa don zai sanima in tsane ki Ta ware
ido sosai tana kallon ta ban yi mamakin jin
kalamanki ba tunda kika iya shafawa idanuwanki
toka ba kya ganin mahaifanki ki balle ki saurari
nasihohinsu gareki kin ban kunya mama ban
taba zaton wata rana mai kamar wannan zata
zoba in sha Allahu zan rarrashin dadin malami
ya kyale ki duniya ta koya miki hankali,ido cikin
ido ta bata amsa zaifi kyau idan kika yimin
wannan kokarin haushi yasa anti amina ta mikie
ta fito babban falon asibitin tayi zaune har aka
kira asalatu tayi alwala tayi sallah ta je ro
addu'o'I tare da rokon Allah ya sanya wa
al'ameen dangana idan har ya rasa mama Cikin
shigar kakinsa tsaf ya shigo asibitin tare da
malami shi ma sanye da kayan makaranta
kuratan sojoji biyu na take masa baya dauke da
kwandon kayan karin kumallon safe a babban
falo ya same ta zaune bisa dardumar
sallah,malami ya fara isa gun ta ya gaisheta ta
amsa sojojin dake biye suka kwashi gaishuwa
yayin da ta miki ta tarbi yallabai amma fuskarta
babu walwala sannu da zuwa tace dashi ya amsa
yauwa ya dai jikin na ta, tana ciki shiga ka
ganta ai ta farfado tun asuba,ko?suka jera zuwa
dakin tana gaishe shi jin muryarsa yasa mama ta
runtse ido ya tsaya kanta yace ki daina matsr
ido nasan kina ji na ina fatan amina ta gaya
miki sako na saboda haka ina son ki gane
wannan sakarcin bazai firgitani ba abinda na
sani kawai al'ameen ya dawo a daura maku aure
middin kina numfashi sauran shawara ta rage
gare ki, Anti amina dake ta kallon ledar ruwa
tasa hannu ta dago igiyar tabbas abinda take
zato shine din. Ruwan ba a jikin mama yake ba
cirewa kikayi mama, ta juya kan yallabai tayi
masa kuri ka gani ko ta cire ruwan yaya ya kawo
iya wuya kamar ya nannausheta yake. Ji cikin
fushi ya juya ya fita anti amina tace da kanki ki
ka kama drip din ki ka tuge,sau dubu aka samin
sau dubu zan cire me ruwanku dani tunda baku
kauna ta tana rufe baki yayan na shigowa da
wasu nosis biyu amma abin karin haushin mama
taki yarda su mai da mata ledar ruwan nan basu
san lokacin da yayanta ya cire hannu ya tsinka
mata mari ba,sai da bakinta ya tsatso jini
saboda haushi da takaici kafin ayi haka ya bar
dakin anti amina ta biyo bayan sa ta bar nosis
na rarrashin mama yana shiga mota ita ma ta
fada ciki tace kayi wa girman Allah yallabai
karkayi fushi ka tsaya ka saurareni kar ki min
magana akan wannan wawayar yarinya," I have
finish with her, dama munyi waya da abdul-
kareem sun ce za su zo harda abdul-rahman so
suna zuwa zasu wuce da ita daga can su bata
kudin mota ta wuce fandogari zan iya kashe
yarinyar nan idan ina ganinta, tace wallahi ni ma
shawarar dana ke son in ba ka ke nan idan kaji
maganganun da mama ke fadi zaka tabbatar da
tayi nisa bata jin kira sai addu'a kawai zamu
zauna ne tana bamu wahala koda yaushe mu ma
asibiti a aikin banza?ba zai yuwu ba a irin take
taken ta tana gab da fara sufa mana zagi ku
kyale ta da dan-litin shi ne zai koya mata
hankali,yace ai an gama dokta zuwa kice ya
sallame ku kawai zan sake kiran abdul- kareem
din in ce su dame mi gida ta numfasa don murna
kafin tace,"!58,naji dadi yallabai Allah shi
taimake ka ita kuma ya shiryar da ita amin ga
break fast can kije kici ki kyale ta bari mu kai
malami school gada can zan shiga ofis to a
dawo lafiya amin,ta fito sannan sojojin suka
taso daga. Inda suke tsaye tare da malami suna
jiran su babu bata lokaci suka bar harabar
asibitin anti amina ta koma ciki tace wa nosis su
kyale ta su tafi abinsu guda tace oga zaiyi fada
madam idan ya shigo. ni nace ku tafi kawai abin
ku ba mu muka kawota ba,kuma mu zamu biya
bill ku wuce kwai ba wani abu"nosis suka wuce
da mamaki anti amina ta hada abin kari ta hau
ci bata sake komawa ta kan mama ba har likita
ya shigo misalin takwas da rabi na safiya anti
amina ta maida masa bayanini yallabai likita
yace a'a baza ayi haka ba nan ya ja kujera yayi
ta rarrashin mama,tayi shiru kamar da gaske
sauraronsa takeyi da kansa ya nemo jijiya ya
maida mata ruwan amman me yana gamawa bai
ko bar dakin ba ta sa hannu ta zare ta aje masa
robobin sa haushi ya shake likita ya jima yana
kallon ta sannan ya dauki (file)din ta yayi
rubutu,ya dubi anti amina yace kuna iya tafiya
gida madam da alama ba zamu shirya da
sakeena ba tace ai dama na gaya maka kayi
hakuri dokta kan ta tayi mawa tace ba wani abu
shawa ta kawai ia ce ku kyale ta ta auri wanda
ta zaba may be rabon wahala ke kiranta,tace
sosai kuwa dokta mun gode ji suka yi mama taja
wani shegen tsaki duk suka bita da kallo likita
yace I'am sorry for yau,a tunaninki kinyi abu Mai
kyau ke-nan? NO,ba hk rayuwa take ba. Ya
kamata ki rinka kulaw. Ya sa kai ya fice.Nosis
din sa suka take masa baya,kowanne su babu
wanda bai shakéÂÂ� taikacin Mama ba. Tana hada
kaya direba na shigowa, yaya ya turo shi,idan
anyi sallamar ya kaisu gida. Shi ke nan kaya sun
tsunke karkashin kaba. Ya kwashe kaya,ta dubi
Mama tace, ki na iya tasowa muje gida,idan kin
so.Ta yunkura ta tashi,Anti Amina bata
saurareta ba ta wuce abin ta. Da kyar ta sauko
daga gadon,wani mugun jiri yayi tafiyar ruwa da
ita,ta koma dabas! Ta zauna.(maganin mara jin
magana,yarinyar nan tana ban haushéÂÂ�! Mts!) Tafi
minti uku dafe da kai,sannan ta sake mikewa ta
daddafa bango ta fito tana layi. Kowa kallon ta
yakeyi,musamman Noisis din da komai ya faru a
gaban su,ai nan take aka shiga maida labari. A
mota ta same su. Anti Amina na gidan baya,duk
ta kulle sakatun kofofin biyu,saboda haka dole
Mama ta bude murfin gaba ta zauna tare da
direba. Ko a cikin gidan ma,babu mai kula
wani,hasalima Anti Amina kwanciyar ta tayi
tasha barci,bayan ta yi wanka ta sauya kaya.Ita
kuwa Mama taci gaba da sanya tsananin kunci
cikin ranta,ji take kamar ana hura wa zuciya ta
wuta.Tsananin son ganin Dan-Lati da kewarsa
suka hana ta sukuni. A yadda jiri ke dibar ta,sau
uku tana fitowa waje ta tsaya wai ko zata ga
lakwa-lakwa ta sulale ta gudu.Amma ina,ko
fuska babu a wajen kuratan nan,balle ta sami
hanyar fita.Don haka ta kifa ciki tsakar falo,tayi
ta sharara kuka har azahar,bata san lokacin da
barcin wuya ya sace ta ba. Anti Amina ta sauko
tayi girki ta gama bata farka ba.Dawowar
Malami ya kwarara sallama',shi ya tashe ta,tayi
doguwar mika tare da hamma mai kunshi da
yunwa da wahalar duniya. Ta tashi zaune taja
jikin ta,ta zauna ta jingina da kujera,wucewar
'yan mintoci.sannan idanuwan ta suka kwalli
agogo.karfe daya hard a rabi. Da kyar ta yunkura
ta tashi ta haye sama a wahale,tana shiga dakin
ta zube a kasa,sbd babu karfi a jikinta.Malami
da ke cire kayan makaranta,ya zubo mata
ido.yana so ya gaisheta yana jin tsoran mari. Ya
sauya kaya,ya fice daga dakin,wajen Momin sa
ya shiga idanuwan sa cike da damuwa. Ya zauna
kusa da ita,tana kallon yadda ran sa ke bace,don
hk ta rungumo kafadun sa tace, "Yaya dai,yunwa
akeji? Ya kada kai yace, Momi Anti fa zaa
mutu,ku maida ta asibiti.Allah bata warke ba. Ta
zura masa ido,tace,Ba laifin mu bane Malami,a
gaban ka ai kana kallo taki yarda asa mata Drip.
To ya take so muyi?" Yace, kawai ku kira mata
abba yayi mata fada. Wlh bana son Ant閾� ta mutu.
Ina son ta MoméÂÂ�,me yasa take ta wannan ciwon
ne? Ta kara rungume shi tace, kowa ma nason
Antin ka Malami,kuma babu mai son mutuwar
ta,Matsalar taki cin abinci ne,shi yasa ka ganta
haka. To sbd me? Tace kaga ka yi shiru da bakin
ka,kai yaro ne ba ruwanka da maganar
manya.kai daéÂÂ� idan ka yi sallah ka roki Allah ya
bata lafiya. Yace, To Momi,tace. Maza kicin ka
zuba abincin ka.'ya fice tana kallon sa. Zuwa
karfe biyar Mama ta sake fadawa cikin
mummunan hali,bata gane kowa. Anti Amina ta
rasa inda zata sa ranta,domin ta rasa yadda
zata yi da Mama don ta ceto ran ta. Ta sauko
falo da nufin kiran wayar ofishin yallabai.
Shigowar mota harabar gidan,shi ya dauki
hnklnta ta zage labulan taga ta daga.Motar
Abdulkareem ke fakin a harabar aje motoci,ta
dawo da sauri ta nufi kofa cike da farin ciki da
baya misaltuwa. Ta bude kofar tayi waje,farin
cikin ta ya karu,ganin har da Abba acikin su.
Sannun ku da zuwa! Ta isa wajen tana fadi. Duk
suka amsa,sannan suka rankayo cikin gida.
Malami ya rugo ya rungume Abba. Bayan gaishe
gaishe suka tambayi Mama. Tace,tana daki babu
kyan gani,nama fito ne,in kira dadin Malami ko
za mu sake komawa asibitin ne,sai gaku. Wlhy
Abba taki cin komai tunda suka zo garin. Ban jin
tasa ruwa a bakinta,wannan masifa dame tayi
kama? Duk suka yi shiru sbd takaici,babu wanda
ya tanka har Anti Amina ta mike ta kawo musu
abincin da ababen sha. Ruwa kawai suka sha
Abba. Ya-ce, muje mu ganta. Duk suka rankaya
saman. Yanayin da suka riski Mama,ba karamin
daga hankulan su yayi ba. Abba ya zura mata
ido,idan da zai hadu da ita a hanya,ba zai shaida
ta ba,sbd sauya kamannin da tayi,sbd tsananin
son cikawa al-ameen alkawari ko alama bai baréÂÂ�
tausayinta ya rinjaye shi ba. Don hk ya dubi
sauran yace,wannan ba shi zaisa mutuncin mu
ya zube a idon duniya ba.sbd hk zamu koma da
ita asibiti,ta farfado.sannan mu wuce da ita
fandogari. Farin ciki na Mama ta mutu a dakin
nauran al-ameen wanan shne kwanciyar hnkli na.
Ku dauko ta mu tafi.
gaskiya ne abba shi kuwa yaya abdul-rahman
abin ne ya zame masa banbarakwai don bai taba
zaton labarin da yakeji abin ya kai haka ba duk
da yana jin zafin abinda mama tayi ,halin da
idanuwansa suka gane masa mama a halin yanzu
kwarai tausayinta ya kwanta a zuciyar sa shi ne
ya fara kai hannu ya ciccubo ta suka taimaka
suka sauko da ita kasa kamat matacciya,da kyar
likita ya karbe ta sai da yan uwanta suka yita
rarrshinsa sannan ya bata gado yayi mata duk
abinda ya dace. Acan yaya abdul- kadeer ya
same su bayan sallar magariba kafin ayi issha'I
suka rankaya gida akabar anti amina tare da
ita,kusan kwana sukayi shawarwari akan
al'amarin,kwana daya da wuni mama na kwance
magashiyan ledar ruwa goma sha tara ta
shanye,ana shirin daura mata na ashirin sannan
idanuwanta suka fara washewa ta gane inda take
hada ido da abba tare da karkaf yan'uwanta bai
haifar mata da wata nadama ba illa kuka da ta
fasa wai don su tausaya mata babu wanda ya
tanka mata wannan itace shawarar da suka
yanke babu wanda zai sake bata bakinsa don yi
mata fada amma zata sha mamaki ranar da
Allah ya yasa al'ameen ya dawo kasar nan,babu
wanda yace cikanki har ta gaji da shashekar
kukanta. A zaton ta shirun na su alamma ce ta
saduda ma'ana sun rasa yadda zasuyi da ita dole
suu sa mata ido anti amina ta fara bata ruwan
lipton tana kurba da kyar take iya hadiye shi
gaba daya Makogwaronta ya farfashe kafin gari
ya sake wayewa mama ta samo kanta misalin
goma da rabi kawai ganin su tayi sun shigo suna
gaya wa anti amina an sallame ta zasu wuce
yanzu bata yi mamakin jin haka ba don haka ta
amsa da to,Allah kara lafiya ita kuwa yar gigalar
murna ce fal cikin ta jin za a wuce da ita
fandogari nan da nan suka kwashe kaya,yaya
abdul-kadeer ya dauki matarsa,mama kuma tabi
ayarin komawa gida a minna suka yada zango
suka ci abinci tare da yin sallolin azahar da
la'asr in banda su ameera babu wanda mama
tayi magana dashi domin anti rabi ma ta sauya
fuska al'ameen dintama bai sami kulawa ba
suna idar da la'asar yaya abdul-rahman ya jawo
matarsa daga inda ya aje ta aka maida jakar
mama ciki ita ma ta fito ta shige gidan baya
abba na tare da karamin yaya a gaba Shi ya jasu
a hankali xuwa fandagori. tun daga kan kwana
hankalin mama ya soma kwantawa, domin dai
idanuwan ta sun hango wanda take son gani.
yana zaune bisa benci a kofar shagonsa, yayi
murmushi itama ta sakar masa nata. har motar
ta wuce, ba su daina leken juna ba. sai da ta
daina hangensa, sannan ta zauna sosai kirjibta
nata bugawa, ji take kamar ta balle murfin motar
ta fice taje gunsa. ya mikawa ayuba hannu suka
tafa. yace baka da kyau! Yace karya kak don
ubanka, kalle ni sama da kasa! ba kyawun sura
ba, ina nufin.... ya kai masa naushi a kafada, shi
ya katse shi. zan ci..... kai! ka kiyaye ni fa wlh!
me na gaya maka? yadda suka dauke ya ahaka
za su dawo min da ita. wahalar banza sukeyi
sakeena mallaka tace. yace ranar da Allah kuma
zai kama. ayuba baya wajen, duk ka gama
iskancin ka. ya ballo masa harara yace, to ko ka
na wajen me zakyi? kai ma ka ji da naka, don
ubanka. Menayi? ni nakai ka iskanci a garin
nan? dama wane kai, amma sannu a habkali
xzaka biyo ni mujera hanya watakila ma ka xarta
ni. ya tabe baki yace Allah ya sawwake, kai din
ma so nake na janyo ka baya. ka auri yarinyara
nan, ka manta da kudinrinka na wulakantata. ya
dafa shi yace ka dan kula da shagon, bari na je
nemo gasasshiyar kaza. kasan dole anjima ta zo
鎷� ya xuba masa ido kawai, bai ce masa komai
ba. yayi dan saurayin murmushin. ya mike ya
fada motar sa yayi birnin gwarin tsinke. kai
tsaye mama dakinta ta shige. umma bata
gasganta idonta ba, irin yanayin da taga mama
saboda haka tatashi tabi bayanta. Kallo daya
tayi mata taji kanta ya ci gaba da sarawa, wani
kululu ya daure xuciyarta, idanuwanta suka tara
kwalla, saboda tsabar BAKIN CIKI. Ta jima kafin
tace, Mama kina da hankali da tunani kuwa? Ji
tayi an dafata ta biyu, muryar Yaya abdul rahma
ke fadin, baki da lfya Umma, karki daga
hankalinki, abba yace ki fito ki kyale ta. Ya
kamo ta suka fito, jiri na dibarta, shi ya sa tace
yawuce da ita dakinta. Abba ya taso ya biyo su,
yayin da take kwanciya a gado. Gefen gadon ya
xauna yace, bai kamata ki bar ciwon ki ya tashi
ba halima, kin ji dai abinda Dr. Ya fada, jininki
ne ke hawa saboda damuwar da kika sanya a
ranki. Ki hrk kawai. Tace, ba alamun yin nadama
a wajen Mama, ni kaina, nasan haka,amma
shawarar da mu ka yanke da 'yan uwanta shine
mu sanya mata ido tayi shirmen ta, sai ranar da
Al-ameen ya dawo xata gane mu ma ba muyi
nadama ba. Abdul yace saboda haka ki kwantar
da hankalinki, ISA sai dai mama ta mutu a dakin
Al-ameen, ba zamu ji kunya ba. Su Yaya babba
da Iyalnsu duk sunce gaishe ki, sai sun xo. Tace
ina amsawa, Allah ya taimake mu, suka amsa
ameen. Abba ya dube shi ya cigaba, kai ma ya
kamata ka hanxarta wucewa yamma tayi sosai.
Umma ta amshe, ba xai bari xuwa gobe ba?
Yace, akwai aiki Umma, yanxun nake so na
lallaba. Ta dan kada kai. Tace, to Allah ya Tsare
agaida min safiyya da kyau. Zata ji, ki daina
damuwa Umma, komai xai wuce da yardar Allah.
Ta amsa da kai, tana fadin shikenan abdul, Allah
yayi maka albarka. Yace amin. Ya wuce cikin
hanzari. A tsakar gida ya hadu da su Haj.Hajjo.
Ashe da gaske ne kun dawo? Yara ke fada mana
yanxun. Yace eh, nima xan wuce kd kenan. Gaba
daya suke to Allah ya tsare! Ya amsa yayi gaba
abinda, su kuwa ciki suka kutsa kai dakin
mama. Kwakwazon surutun su ya sa Abba ya ta
so fito. Sannuku da dawowa Yaya. Yace yauwa,
ga haliman can a dakin ta. Haj. Hajjo tace, muna
nan mun ganin ikon Allah. Mama ta dawo kashi
ba rai? Yace haka take so, ai ku daina bata
bakinku, kowa ya sa mata ido. Haj. Gaje tace,
lallai kam wannan al'amarin sai ido. Allah ya
kyauta. Ameen. Suka fice tare suka koma dakin
Umma, suka isheta da surutu. Duk iya kokarin
mama na son fita a wannan daren abin ya
faskara, domin dai Abba ya kasa ya tsare a falo
har goman dare ya garkame kofar ya shige
dakinsa barcinsa. Allah da ikon sa, abba bai
xare mukulin ba, domin bai taba tunanin Mama
xata iya aikata wani abu a wannan tym din ba
lallai abba bai san Mama ta wuce tunaninsa ba.
Yana bada baya, taji motsin rufe kofarsa ta yi
wuf ta mike, takalmanta a hannu tare da
mayafinta. Tayo sanda ta fito jim, tsakar falon
bata ji mtsin kowa ba, sannan ta karasa kofar ta
bude ta cikin nutsuwa ta sulale ta fice. Can ma
kofar sassan hka ta bude ta, ta wuce zaurukan
gidan, ta zare sakatun ta bude ta fita ta maida
kofar ta sakaya. In bakayi bani wuri! Ta callah
da gudu bata ko jin rashin karfin jikinta, sai da
tayi rabin tafiya, sannan ta tsaya ta sa
takalmanta ta yafa gyalen tana ta xuba haki, ta
dau hanya babu jama'a sosai. Gata nan ga ta
nan har kofar shagon dan gogan. Ya tare da dije
a kofar shagon bisa banci, ta cukuikuye shi
kamar na goye fadi yake, wai dan Ubanki dole
ne? Kin fa matsa min da yawa, xan ci ubanki a
daren nan, in ga mai kwatar ki! Kawai ganin
mama yayi akan su. Ya banbare dije ya ture
gefe, bai bata lokacin ya daga kanta ya shige,
shagon yana jan tsaki. Mama ta daga itama ta
bishi. Dije kuwa mikewa tayi ta kakkabe jikinta
ta wuce tana kwafa. Ya hade rai a kujera, bai ko
kalle ta ba. Ta matsa gare shi murya sanyaye
tace, fushi kayi danliti? Ni ban yi fushi ba sai
kai? Ina can naki ci na ki sha saboda kai. Ashe
ka na nan ka tare da wata? Dubi yadda na rame
na sauya kamanni, saboda tunanin ka Danliti.
Bai kamata ka yi min haka ba. Ya dago
idanuwansa farare sol! Sunji kwalli ya dubeta, ko
mai nai miki ai kekika jawo, kinbi 'yan uwanki ki
manta da ni, ba dole in sami wata ba! Tun
yaushe kuka shigo garin nan? Nayi ta xuba ido,
amma ban ganki ba, me kike tunanin xan dauka?
Kafin tace wani abu ya fizgo hannunta xuwa
daki, yana kara fadin, idan karya nake yi, xo
muje ki gani! Ayuba dake kwance bisa katifa
yayi firgigi ya tashi yana kallon ikon Allah.
Ledar kaji ya janyo ya xaxxage su. Yace me kika
gani nan? Saboda ke na tafi har birnin gwari na
siyo miki gashin xamani kajin turawa. Dubi nan
juice ne kala-kala har sanyi su ya fita, baki xo
ba. Ba dole in yi fushi ba, in saurari mai so na!
Ta sauke numfashi, idanuwan ta taf! Da kwallah,
ba laifina bane Danliti, baka san irin bakar
wahalar da na sha ba, don kawai su dawo da ni.
Sau biyu ina kwanciya a ascibiti, dube ni da
kyau, kai kanka kasan ba haka nake ba. Amma
kayi hkr, tunda kana ganin kamar da gangan
nayi, ka hkr? Ya xura mata ido jim, sannan yayi
dan murmushi ya ware hannayensa yace, to
oyoyo! Ta sa hannaeyanta ta rufe fuska. Yace
kunya? Ashe baki so na, lallai na yarda ni kadai
nake haukan sonki. Yana rufe baki ta matso da
sauri ta rungunme shi. Ayuba, yayi gyaran
murya. Mama tayi wuf ta rabu da jikinsa. Ya
dubi Ayuba, yace malam ka fita ka bamu wuri!
Yace, ai ku ya kamata ku koma daga waje anan
nake so mu xauna, fita ka bamu wuri don Allah,
shago fah abude yake, ya yankura ya tashi yana
fadin, gaskiyya kuyi sauri ku gamacin kazaraku,
barci nakeji. Ba ruwanka wannan. Ya fice yana
waigen Danliti yana masa ishara da idanuwansa
dauke da gargadu, wanda shi kansa ya gane
nufinsa, shi yasa yake wani irin mur0ushin na
iya shege. Yana fita ya dubi Mama suka hada
ido dukkan su sukayi murmushi, sannan ya
kamo kafadunta yace, gashi dare yayi, amma
dole ki xauna ki cinye kajin nan, domin saboda
ke na siyo su. Ba tace komai bam ya xaunar da
ita gefen katifa, ya jawo kayan kwalama, ya baje
mata kajin, yana bata abaki, tun tana jin kunya
har ta saki jikinta, tana amssa sosai tana ci,
suka ci suka sha suna hirar bayan rabuwa. Bayan
sun kare. Danliti ya dubi agogonsa ya ce
shadaya da kwata yanxu, ya kamata kije gida
ko? Sai gobe, ina fatan xaki rika cin abinci don
ki gyagije kyanki ya dawo kamar da. Kinji ni?
Tace, naji kuma xan kiyaye, amma don Allah ka
daina bari 'yan mata na xuwa gunka, watarana
xamuyi dambe da su wlh, kaji na rantse. Ya
kyalkyale da dariya son ransa kafin yace, xaki
kuwa sha duka, don dai nasan sunfi karfinki.
Wannan jikin naki rugu-rugu babu kwari. Ya fadi
yana mammatsa hannayenta da kafafuwanta. Ta
yankura ta tashi tana cewa, haka kake gani, ka
maida abin wasa, zaka sha mamaki. Shima ya
mike ya kamo yatsunta, yace karki damu, ke
kadai nake so, ko da damben ya kama kuyi, xan
shigar miki balle ma banda lokacinsu. Ke me xai
dameki? Tayi murmushi, tace, to shikenan sai da
safe. Ya sumbaceta yace, muje na rakaki. Suka
fito yana rike da hannunta, tayi wa ayuba
sallama suka wuce. A kofar gida suka fuskanci
juna, tallafo kuncinta ya xura mata ido, yace
karfa ki damu da ganin Dije tare da ni, wlh ba
sonta nake ba, kawai ta matsa min ne dole muyi
soyayya, amma xan dauki mataki akanta, tinda
ta fara bata miki rai. Tayi murmushi, tace,
nayarda da kai, ina fatam Allah ya yarda mana,
ya bamu nasara abinda muka sa gaba. Da sauri
ya amsa amin sakeena. To sai da safe nagode,
wannan karon abin ya cigaba akan labbanta ya
sumbace ta. Ta juya da sauri, ta tura gida ta
shige ta maida sakatu. Danliti ya runtse ido ya
jinjina hannayensa, shege ni! Ya juya yana
takawa dda+dai kamar wani kasaitaccen
basarake. Mama kuwa sanda takeyi, kamar
barauniya ta turo kofar fa'aar dshigo ta mayar d
hankali ta kuleta, ta fada gado. Tana jan mayafi,
taji a; ttay bude kofa, tayi tsaye jim, sannan ya
mayar ya rufe. Muryar umma taji tana fadin,
menene alh.? Yace kamar motsin naji ana taba
mukulli.. Tace Innalillahi an shi ne? Yace amma
ban ga kowa ba. Ya dubi agogo, karfe sha biyu
saura kwata, dare ma bai yi ba sosai, to Allah
yai mana tsari da sharrin masu sharri. Yace
amin, je ki kwanta. Cikin fargaba suka bar falon.
Mama ta gyara kwanciya tana gyatsar naman
kaxa. Dan kanta tace kwanta naman kaza. Tayi
tunani Danliti har barci ya kwashe ta, shi take
marfi yana sa mata naman kaza abaki. Da safe
tayi wanka, duk 'yan ciwukan da suka rage ba su
warke ba, ta goga musu mai, ta shafa hoda ta
sa atamfah riga da xani, nan da nan ta dan yi
fasali, duk da cewa akwai rama sosai a jikinta.
Yau kam tayi dan kyan gani, ta fito falo wajen
Umma cikin kicin inda take aikace aikacenta,
tace sannu Umma ina kwna? Ta juyo da sauri ta
dubeta sama da kasa, tace kalau na kwana. Ta
kara matsowa tace, bari in gaida Abba, sai in xo
in tayaki aikin. Bata amsa ba ta fice, ta bita da
kallo sannan ta kada kai tace, Allah ya shirya.
Dakin Abban tayi sallama, ya amsa ya bita da
kallo, ta karaso gunsa ta tsugunna, ina kwana
Abba? Yace Kalau, ta dan dube shi, amma bata
kara komai ba, ta mike tayi waje ta koma kicin:
Umma me xan tayaki? Tace ban so, koma
dakinki kawai. Saboda me Umma? Ai ban isa na
fadi ko saboda mene ba, tunda kin xama
shafaffiya da mai. Je ki kawai ki sha xamanki.
Kai tsaye kuwa ta wuce daki abinta. Tana fadi
cikin ranta, kya gama girkawa, mu zo mu jajja
(hmmm mama tayi nisa walle). Kan Umma ya
sara ganin yadda mama ta wuce ko ajikinta,
bata damu ba. Mamaki bai gama kashe Umma
ba sai da ta hange ta kicin din tana diban abinda
take son ci. Tana kallo ta koma dakinta ta cinye,
ta maida kayan kitchen ta fito. Haushi ya kume
Umma bata san tym din da tace, Uban wa kika
ajewa kayan ya wanke miki? Tabbatacciya! Ta
dan bata rai ta juya ta kwaso kayna ta wanke.
Karfe 9 abba ya fita harkokinsa. 9:30 mama figi
gyale tayi waje, Umma nace na wanka. Ta sha
hirarta wajen Danliti har 12pm sannan ta
tsallaka ta gangara wajen Baraka. Sosai taga
sauyin fuska wajen Inna saude. Sam abin be
dame ta ba. Suna kebewa da Baraka tace.
Kawata ban gane ba, sai da nayi miki kallon
kurulla. Yanxun saboda Allah dawowa kikayi?
Tace ga ni kuma kina ganina. Matsala tace,
babu ruwan kowa. Mutane masharanta ne kawai,
saboda Allah yayi wa Danliti kyau da farin jini,
ga shi ya Rufa masa asiri, shi ya sa ake masa
hassada.... Ta katse ta, idan hassada ce, ai
kuwa kem kinyi masa da. Menen baki fada ba
akansa? Tace, Rashin sani ne, duk surutan da
akeyi wai dan Iska ne dan guguwa. Dan wata
tsiyace, ni har yanxun Danliti bai taba furta min
maganar banxa ba balle ya nemi aikata wani
shashanci. Rashin fahimta ne kawai yasa ake
masa zargi, kisan mutum mai farin jinin
'yammata (Kuji fa wai bai taba mata komai ba?)
baki ganin ko mace ce ta fiye samari sai arinka
mata wani irin kallo? Baraka ta sauke fuska,
tayi guntun tsaki, baki jin kira Mama. Allah ya
shirye ki. Ameen, ni bari in koma gida, dama
lekowa nayi mu gaisa kisan na dawo. Tabita da
kallo, ki na san kin dawo wajenki xano? Menene
anfani kawancen mu? Bayan ko na gaya miki
gaskiyya bakyaji. Allah ko? To Allah ya bamu
alkhairi ki gaida mohd dinki, in yazo. Yaushe
xasu kawo gaisuwane? Ko bai shirya aure bane?
Wlh ban masa zargin komai ba, amma sonsa bai
rufe min ido ba, ina bukatar in gama sanin ko
shi waye tunda ba gari daya muke ba. Ta tabe
baki, Baraka ke nan, Miss kakale! Ba kakale
bane, gaskiyya ce kawai, daga kinta sai bata.
Shi ya sa nake nuna mikita, don banson ki bata.
Ta mike hannu daya kame da kugu, tace,
nagode, ni nayi gida, kar Umma ta neme ni. Tasa
kai tafice. Baraka ta biyota, ta sallami Inna ta
rako ta iya zaure ta juya. Ta shige gida, tabar
mama dauke da mamaki. Tai kwafa tace, kiyi da
gwana yarinya. Ta kama hanya ta koma wajen
Danliti, wasa-wasa sai da ta bata mini talatin
anan, sannan ta karasa gida. Umma na zaune
tskar falo ta sha tagumi, ta gaji Mama ta shigo
babu ko tsoro ko fargaba tace, sannu da gida
Umma. Inna saude na gaisheki. Ta zura mata ido
ba tare da cire tagumin ba, jima kafin tace, da
izinin wa ki ka bar gidan nan Mama? Ta
mimmike kafa sosai akujera. Tace ai kinshifa
wanka ne Umma shi yasa banyi miki magana ba.
Umma ta numfasa, tayi hucin BAKIN CIKi tace,
lallai kin isa mama, duk son danliti ne yasa kika
zama maras kunya? To kibi a hankali, duniya
zata koya miki hankali, muddin kika dauke ta
kika goya. Ta figi gyalenta, ta mike cikin sauri
tana fadin, Uhm.....! Ta wuce ta fada dakinta,
tayi kwanciyarta. Umma ta kada kai, kwallah
suka xubo mata, ta share tace, Allah kana kallo,
munyi iya yinmu, amma shiriya na wajenka, kayi
mana gaji Ya Allah. Nan Umma taci gaba da
zama tana shan BAKIN CIKI tare da takaici mai
tarin yawa har aka kira azhar, ta tashi tayi
sallah. Abba ya dawo ta labarta masa, hannaye
biyi ya kama kai, takaici kamar ya kashe shi,
bai niyyara kara yiwa Mama wata magana ba
akan Danliti, amma dole tasa ya kira tazo
dakinsa ta xauna. Yayi mata kaca-kaca, sannan
ya sa mata dokar fita ko'ina, duk da yasan ba
dole bane tabi umarninsa. Tabbas hakan ne,
yadda Mama ta fito dakin bakin nan nata ya kai
wani gari wai shi ZUNTU. Shi kasna ya san
rashin kunyta Mama ta kai wani mataki na
kololuwa kwatance, ta xauna bakin gadon ta
tana fadin a fili, wannan shine bature ke kira
Impossible! Tunda kuka hana shi xuwa guna,
dole inje gunsa mu ga juna. Ta saki wani
lafiyayyen tsaki, ta yada kai bisa filo.........
Maganar mama dutse. 7days kenan babu abinda
ta fasa, muna iya cewa al'amarin kara haukata
yayi. Domin a halin yanxun Mama bata shayi,
agaban Umma zata dauki mayafinta, ta fice.
Umma na kira, tana fadin tana xuwa yanxu xata
dawo. Sau uku Umma na xuwa da kanta kofar
shagon Danlinti, tana taso keyarta. Jama'a na
kallon su, gwanin ban kunya. Sai da Abba ya
hanata xuwa. Yace tasa mata ido, tunda ta zama
gagararriya. Wannan abin kunya ya zama abin
yayatawa awajen su hajjo, duk inda suka xauna
xancan kenan. Babu abinda bai dawowa kunnen
Umma ba, sai dai tayi kuka ta share hawayenta
ta barwa Allah komai. Mama fa ta gagari kowa,
suna ji suna gani mummunan labari na ta
yaduwa har gidan Gwaggo Hausi. Daga can
labarin ya mika gidan Marafa. Nana take mami
ta tsani auran mama da Al-ameen. Shi kuwa
Marafa nuna mata yake su daina kama jita-jita.
Aure dai nufi ne na Allah, idan sakeena matar
Al- ameen ce, bbu makawa xai aureta, idan kuwa
ba matar sa bace si barwa Allah yayi masa zabin
alkhairi. Duk da haka al'amarin yana jefa Mamai
cikin tunani ba kadan ba, kuma da Al-ameen zai
ji shawarar ta, da ta umarace shi daya hakura da
sakeena, tunda shasahnci tasa gaba. Sallar
la'asar ta kammala, amma bata bar sallayar ba,
saboda gabatar da lazimi takeyi. Wata tasi tayi
fakin kofar gidan, direban ya fito ya bude but,
yana fido jakar kaya. Yana rufe but din, idanuwa
na suka nuna min Al-ameen a tsaye ya cusa
hannu gaban riga ya zaro kudi ya mikawa
direban, yace, ka rike chanji. Ya sunkuci jakarsa
ya wuce. Direba na xuba gdoiya. Ya tura karamin
gate ya shiga, bakin mai gida har kunne ya taso
da gudu ya amshi jakar yana fadin Maraba da
oga! Fuskarsa babu walwala sosai, yace ya
kuke? Lafiya lau oga. Ya shige masa da kaya
falo. Al-ameen yayi sallama, muryar sa ta dauki
hankalin duk wanda ke cikin gidan. Iya ta riga
kowa fitowa, wa nakehi kamar dan Iya? Ya nufo
ta fuska sake, ni ne iya, surprise ko? Ya dan
rungumo tana fadin, ai kaki koya min turancin
nan, da yanxun na gane nufinka. Yana murmushi
ya rabu da jikinta, ya dubi Ladi, Hajiya Ladi ina
fatan kunje kun duba min jikin sakeena ta? Tace
muna dai shirin tafiya da hada tsaraba. Ya ce,
baku da tsraaba? Gaskiyya kunyi min babban
laifi. Tace, mun san hakan amma tuba muke. Ta
ya kuke? Ta amsa lfya lau ya hanya? Yace,
Alhmdlh. Yana juyo wa sukayi ido hudu da mami
tana masa kallon mamaki. Ya nufe ta da sauri
ya rungumeta, Mami na! Idanuwanta suka tara
kwalla, ta kasa cewa komai har ya dago ya
dubeta, yayi dan murmushi. Yace, nayi muku
laifi Mami, kuyi min hkr na kasa daurewa ne.
Tace nagode Allah da ya kawo ka lfya. Amma
banji dadin xuwanka ba Al-ameen. Yace, na tuba
Mami, ki duba halin da nake ciki, kiyi min uzuri.
Ta dan kada kai. Tace, muje ciki ka sha ruwa ka
yi sallah. Suka wuce yana tambayar Dadinda.
Tace, xai dawo anjima daga kd. Yana xama Ladi
ta shigo masa da ababen sha masu sanyi. Bayan
ya jika makoshi, ya dubi Mami yace, ya jikin
sakeena? Na daina kiran waya, don kunnuwa na
ba za su jure jin mummunan labari ba, koda
yaushe. Dalilin da yasa kenan, nace ya xama
wajibi in xo inga halin da take ciki da idanuwa
na. Dan hutu muka samu na sati daya, shine na
yi anfani da wannan damar. Yaya yanayin jikin
nata yake? Ta numfasa sosai kafin tace, jikin ta
har yanxun a rikice yake, xan so ace Allah ya
saka maka hkr, da dangana akan sakeena,
domin kwakwalwarta ta jirkita Al-ameen.....
Hauka Mami? Kina nufin sakeena ta haukace?
Inna- lillahi wa Inna-illaihiri Raji-un!
Idanuwansa suka tara kwalla, ba xan iya hkr da
ita ba Mami, ko ba zata taba warkewa ba, sai na
aureya. Alkawari ne wannan Insha Allahu ba xan
karya wa sakeena ba. Tana ina ne yanxu? Ita ma
nata idanuwan suka kawo kwalla. Ta ce, tana
Fandagori, kuma ni ma xan so hakan Al-ameen,
domin duk abinda kake so, nima shi xuciyata
take matukat so da kauna. Amma al-amarin ya
sauya salo, ka dauki kaddara kayi hkr da ita,
hankalina zaifi kwanciya Al-ameen. Da gudu
hawayen sa suka wuce bisa kyakkyawar
fuskarsa, ya matso ta a hankali, ya dauko
hannayenta biyu ya matse, ya dubeta ido cikin
ido. Yace, har abada bana fatan in saba umarnin
ku mama, amma ina rokon alfarma ki ban izini
in cikawa sakeena alkawarin da daukar mata.
Zan tafi samun nutsuwa, idan ina kallonta a
matsayin mata ta kowane irin yanayin take. Ina
rokon ki Mami ki taimaka min. Ya jingina
goshinsa bisa kafadar ta, ya matse hawayensa
tare da ajiyar zuciya mai karfin gaske. Haka
maminsa ke cikin irin wannan yanain. Ta jima
shiru tana tunanin zuci, tana son gaya masa
gaskiyya, amma bakinta ba xai iya furtawa ba,
saboda tausayin dan tilon dan ta. Ta yi ajiyar
zuciya. Tace, nayi maka Umarni akan duk
abinda yafi xama alkhairi Al-ameen. Mike ka je
kayi sallah kaci abinci. Ya dubeta yana share
kwalla. Yace, nagode Mami. Ta danyi murmushin
dole. Jeka yi sallah. Ya tashi da sauri ya dauki
jakarsa, ya fice. Mami ta raka shi da kallo,
hannunta a kunci. Ta nunfasa kafin tace, Allah
gamu gareka. Yana shiga, bangarensa ya isa ya
yar da jakar hannunsa ya xauna gefen gado Ya
kama kai hannayensa 2 yana yiwa Allah tasbihi.
Jim kdan ya tura hannu aljihunsa, ya xao wallet
dinsa ya bude ya xurawa dan karamin hoton
Mama ido, nan da nan hwaye suka goce masa,
bai ma san tsaninin kukan da yake ba har da
shassheka, kamar xuciyarsa zata tsago kirjinsa.
Allah da ikonsa, tamkar mami na da masaniya ta
taso ta biyo shi dakin, don ganin a wane yanayin
yake? Da sauri ta karaso ta zauna kusa ta shi ta
rungumo abinta, idanuwan na tara kwalla. Komai
ya sami bawa daga Allah ne Al- ameen, bai
kamata ka xauna ka rinka kuka ba! Jin muryarta
yasa hankalinsa ya dawo jikinsa, sannu-sannu
hawayensa ya tsane. Ya dago ido jajur! Ya dubi
Mami, yace mami ki amince min inje in dubo
sakeena Yanxun. Ta goge masa guntun kwallan
dake bisa kuncinsa. Tace, na baka izini Al-
ameen, fargaba na kawai dare. Yace, kar ki
damu Mami. Allah xai tsare. Shikenan, Ubangiji
Allah ya sa ganinka ya xama waraka gareta,
hankalin kowa yakwanta. Yace, Ameen Mami.
Tace , To kayi sallah Maza-maza, don Allah kar
ka zauna dogon tunani. Yanxun xan fito Insha
Allahu. Ta mike ta bar dakin. Al-ameen Ya
sauke numfashi, shima ya mike ya fada bayi,
nan da nan ya watso ruwa ya dauro alwala ya
fito. Bayan yayi sallah ya kimtsa, ya fito Mama
ta matsa yaci wani abu, amma bai iya zama ba,
gaba daya hankalimsa ya koma Fandogari. Sai
dai ya sha Mamaki daya ga Mami ta nace dole
ya tafi da direbanya, bai yi musu ba. Kai tsaye
ya shiga mota direba ya ja shi suka dauki hanya
suka bar Mami cike da damuwa tare da tunanin
yaya al'amarin zai kasance idan Mama ta juya
wa Al-ameen Baya?
BAKIN CIKI 2*** 8 Ba su ido Fandogari ba, sai
karfe 8pm, babu bata tym gidan Uban dawaki
suka dosa. Ya shige sassan sa tare da sallama.
Umma ta amsa ba tare da ankara da mai muryar
ba. Sannu Umma. Ta dube shi da kyau, gaban ta
yayi mugun faduwa, ta mike tsaye tana fadin,
Al- ameen! Saukar yaushe? Yace, yau din nan
Umma. Ikon Allah. Sannu da xuwa! Zauna mana,
ya zauna yana amsawa. Kafin yace, ina yini
Umma? Ta amsa, lfya lau ya karatu? Mun gode
Allah, ya jikin sakeena? Tayi dan shiru, kafin
tace wani abu. Abba yayi sallama ya shigo, duk
suka amsa amsa Abba! Yace, ah! Al-ameen!
Saukan yaushe? Yace daxun da la'asar Abba. Ya
xauna suka gaisa, sannan ya sake tambayar jikin
mama. Abba yace ciwo na nan Al-ameen. Halima
kawo masa abinci ya ci, kafin muyi magana.
Abba bana jin yunwa, domin na riga na saba da
ita, tun tym din na sami labarin tashin hankalin
da kuke ciki. Abin daya hana ni jurewa kenan,
nace dole in xo inga halin da Mama take ciki.
Abba yace, gaskiyya ne. Mama na nan cikin
lularar da ta sameta sai dai al'amuran zai ba ka
mamaki idan na gaya maka alabari ya sha
bambam Al-ameen, nasan an boye maka komai
coz of karatunka, amma yanxun dole ka sani,
tunda ka zo. Jikinsa ya kara sanyi, yayi xuru
yana sauraron abba, al-ameen rayuwa ta
sauyawa mama, wanda muke ganin sa tamkar a
mafarki, daga ni har 'yan uwanta kaf! Babu
wanda ba shi ckin alhinin wannan abu. Balle
kuma kai da soyayyah ta hada ka Mama, kuma
ita da kanta takwo mana kai cikin gidan nan. Shi
yasa nayi rantsuwa, idan mama xata mutu, sai
dai ta mutu a dakin ka tunda tun farko ita ta
kawo ka. Ashe kuwa babu wani dalili ko uzuuri
da xata kawo mana mu saurare ta. Nasan har
yanxun kana jina a hagunce ne, baka gane inda
na dosa ba. To bari na fito maka a mutum kada
ka wahalar da kanka, Magana daya ce, mama ta
gano wani kuma idanuwanta sun rufe ta manta
cewar tayi xafin farko kuma na karshe a
swajena. Ka fahimce ni? Gaba daya kansa ya
kunce, daga yadda yayi kuri idanuwan sa kafe
yana kallon Abba, suka gane bai fahimci su ba.
Saboda haka yace, dole ka shiga rudu fiye da
wanda ka shuga a baya, amma ina so ka sani,
mu muna tare da kai, ba mu san kowa ba face
kai, ba don komai ba sai don tun farko kai tafara
kawo mana. Abinda nake son ka gane shi ne,
xuwanka ya sanya ni farin ciki. Domin kai kadai
nake jira in tabbatar wa Mama cewa lallai ni ba
tsohon banxa bane, kuma bana magana 2. Ina
mai tabbatar maka ba xaka koma ba sai na
daura auranka da sakeena da yardan Allah. Na
gama magana ta, ka tashi hankalinka kwance,
kashiga wajenta tana nan cikin dakinta. Ya mike
ya bar falon. Umma ta dube shi tace, Al-ameen!
Murya dishe ya amsa, na'am Umma tace kayi
hkr, ka kwantar da hankalinka. Mama bata isa ta
xubar mana da mtunci ba. Kai zata aura da
yardar Allah, domin da kai ne akayi mata baiko.
Tashi ka shiga wajenta ku fahimci juna. Ta mike
tabashi guri, don yaji dadin tashi......... Me
kunnuwan Al-ameen ke ji yau? Ya runtse ido
tamau! Ya girgiza kai wai ko barci yakeyi ne?
Abba ya xo masa a mafarki. Ya bude idanuwan
ya ware su sosai, tabbas zaune yake cikin falon
su Mama. Kenan dagaske ne maganganun da
Abba ya gaya masa? Kirjinsa ya soma bugawa ji
yake kiris! Yarage ya zare masa rai, saboda wani
gagarumin ciwo da yaji cikin xuciyarsa, nan take
ya kama shi. Motsin kirki ya kasa yi har Umma
ta sake fitowa da nufin dauko wa Abba
abincinsa. Ta danyi jim, tana masa kallon
tausayi, sannan ta matso tayi kiransa, ya dubeta
firgigi idanuwa sun juye jajur! Tace, ka na xaune,
baka shiga ba? Tashi ka shiga mana, ka kwantar
da hankalinka, komai xai wuce Insha Allah, ya
mike a kasale, ya nufi dakin ba tare da yasan me
xai je yayi ba. Tana zaune tsakar daki ba ta hade
kai da guiwa, tsiyayar hawaye kawai takeyi,
domin tana jin duk kalaman da Abba ke fadi.
Daf! Da ita ya tsugnna, bai san lokacin da yasa
hannu ya dago fuskarta ba. Sukayi wa juna xuru
tsawon lokaci kafin yace, kin ganeni sakeena?
Al-ameen ne, kin gane ni? Ta kau da kai abinta.
Da sauri ya kara juyo da ita, kiyi min magana
sakeena ko na sami nutsuwa saboda ke na dawo
kasar nan, don na duba jikin ki. Ina can tunani
da xulimmi sun addabe ni, idan kin gane ni, ki
amsa min, ya jikin ki? Ta watso masa harara,
hawaye na kwarara. Tace waya gaya maka banda
lfya? Yace, haka kowa ke gaya min tun tym din
da na daina jin muryarki a waya, komai nawa ya
tsaya sakeena, radadin ciwon daya sameki, ya
hanani sukuni. Ina fatan gani na ya zama
sanadin samun saukin ki. Ta goge kwalla. Tace
duk wanda ya gaya maka banda lfya, ya maka
karya, kalau nake, gani kuma kana kallo na
xaune, sai dai na tabbata dawowar ka zata iya
zame min cuta! Ya kara xura mata ido , kina
nufin abinda Abba ya gaya min yanxun gaskiyya
ne? Tace ka daina kokwanto. Ya langwabe kai
gwanin ban tausayi. Yace dole nai kokwanto
sakeena, don nasan akwai alkawarin a tsakanin
mu, kuma bana tunanin zaki yaudare ni, wannan
ya tabbatar min da tsantsan son da kike min.
Ban taba kallonki da xuciya 2 ba sakeena.
Shiyasa har halin yanxun da nake magana dake
ban yarda kin karya alkawarin mu ba. Ta kalle
shi a dage, ta watsar tace, ya kamata ka amince,
tunda gashi da bakina ina gaya maka, tsutsun
soyayyarka yayi fiffike yayi dogon tashi. Ya dafe
kirjinsa a natse idanuwansa tam! Da wahaye,
yace, bai tashi ba sakeena, nayi rantsuwa kina
so na. Akwai miskhila dai a wani wuri, ki gaya
min laifin da nayi miki. Wlh da kaina xan
hukunta kaina, koda da jinin jikina ne xuba, idan
har zai zama fansar tarin laifin da nayi miki.
Gaya min da sauri inji. Ta ya mutsa fuska,
hawayen ta ya bushe tace, Al-ameen ka farka
daga barcin da kakeyi ka saurareni, ni sakeena
na gaya maka a da naso ka, amma yanxun ban
son ka, ba kuma zan aure ka ba, idan sama da
kasa za su hade! Kaji ni ko? Sai na maimaita?
Ya matse ido, kwalla masu zafi suka yo waje da
gudu, ya dan kada kai murya shke yace, kin
xuba min dafi, kin xuba min dafi sakeena. Baki
tunanin amana? Yasa hannu ya kamo yatsunta,
ya kura wa zobensa ido, ya ciga, baki kallon
zoben alkawarin mu? Me yasa kika mance da
dimbin kalaman da kika sha gaya min? Wadanda
suka jaddada imani na akan son da kike min? Ta
kwace yatsunta a hankali ta zare xoben, ta jefa
masa, ga tsiyarka nan, idan shi kake kallo a
matsayin alkawari, ni ma cire min nawa ka bani.
Yaci gaba da kallonta, kafin ya dauko zoben
yace, kiyiwa Girman Allah ki maida zoben nan
sakeena.... Bazan karba ba! Idan ma ka aje shi,
zan jefa shi masai! Kuma nima dole ka ban
nawa! Yace sai dai ki kashe ni, sannan ki zare
shi, wannan din ma zan ciga da boye shi, har
xuwa tym din zaki sami nutsuwa dakin auranmu.
Ta kwada masa harara, sannan tayi wani dan
murmushi na kaico, ta kauda fuska, y mika
hannu ya kamo habarta, ta sa nata da karfi ta
doke nasa, kafin tace, karka sake tabani, idan ba
haka ba kuma sai na kurma maka ihun dan iska!
Ta mike da sauri ta bar wajen, kai tsaye bayi ta
shige, ta maida mukulli ta kulle. Yayin da Al-
ameen ke cigaba da kiranta. Ya tashi ya tsaya
kofar bayin yana fadin, ki fito ki saurare ni
sakeena, ya kamata mu fuskanci juna, mu gane
inda matsalar mu take. A zatona har duniya ta
nade ba zaki taba juya min baya ba! Tana daga
ciki ta amsa, bazan fito ba. Daman kasan inda
dare yayi maka, yace ki tuna alkawari sakeena,
don Allah karki bari ayi min dariya. Idan na
rasaki zan iya rasa komai nawa, ki tausaya min
sakeena, kar damuwa ta kasheni. Tace, kan ka
akeji! Ni na gama magana da kai. Ko za'a kashe
ni ba xan sauya ba, dama ka kama gabanka zai
fiye maka alkhairi. Ya tsaya jim, shiru goshin sa
jingine da kofar ya rasa inda zai tsoma ransa
yaji dadi. A hankali ya soma karannto Innalillahi
Wa inna ilaihir Rajiu'un. Ya fi 10mins tsaye.
Sannan ya juyo da sauri ya fito yana share fuska
da hankaci. Kawai arba yayi da su Abba zaune
falon. Ya rage sauri ya nufi gunsu ya tsugunna,
abba zan koma. Gab dayan su ido suka xuba
masa, jim Abba yace, amma dai ba minna zaka
nufa ba yanxu ko? Ya dan kada yace, kuma ka
kwantar da hankalinka Insha Allahu Mama matar
kace. Kar ma ka bata tym din wajen xuwa goben,
kai tsaye ka wuce gida, ka gayawa Marafa ina
tafe da kaina, muyi magana. Yace to, Abba na
barku lfya. Ya mike ya fice suka raka shi da
kallo. Ummma kam bata sami cewa komai ba,
saboda tsabar tausayinsa. Yana fitowa Gambo
direba ya balle murfin mota ya fito, ya tarbe shi
ganin ogansa na ta share fuska, yaya jikin nata?
Ya dube shi ido jajur yace ba sauki Gambo. Mu
shiga mota, ka maidani gida. Yace yallabai ai
dare yayi sosai, nayi zaton gidan gwaggo xamu
kwana. Ya miko hannu yace bani keys, kai ka
wuce gidan Gwaggon ka kwana! Ya dan sunkuyar
da kai, yace yi hkr yallabai Allah ya sauke mu
lfya. Shi tuni ya bude gidan gaba ya fada.
Gambo ya xauna mazauninsa da sunan Allah ya
murza mukulli yaja suka wuce, a tym din agogon
motar yana nuna 09:45pm. A daren nan nake son
ganin Dady na. Gambo yace Allah ya yarda
mana, ita kuma Allah ya bata lfya. Ya kama kai
ya runtse ido, ya jingina sosai da kujera yana
fadin amin Gambo. Direba na ta tsula gudu cikin
dare. Shi kuwa Al-ameen kurwarsa na can cikin
tunanin baya. Itin tsantsan son da Mama ke
masa, shi yake gani cikin idanuwansa, har xuwa
ranar da ya xo sallama da ita a sch, kawai
gambo ji yayi Al-ameen na sambatu, sosai
kikace kina sona sakeena, dama yaudara ce? Me
yasa sakeena? Me yasa? Hnkalin Gambo ya
koma gunsa yayi kiransa sau uku, kafin yaji
kiran. Ya xuba masa ido yayi da direba ke fadin,
kayi hkr yallabai, yace sakeena ta yaudareni
Gambo, ta xuba min dafin da xai wuya na sami
maganinsa. Xan iya mutuwa Gambo, domin gaba
daya na sallama kaina gareta. Ko kasan inda
nake da mishkila ka gaya min in gyara? Gaba
daya tausayin sa ya lullube gambo, ya kada kai
da sauri, yace babu inda kake da mishkila
Yallabai, sai dai ko ajizanci na dan adam. Ni
kaina ban yarda sakeena bata sonka ba,
watakila ciwo ne rudata yace, kai ma ka yarda
bata da lfya ko? Amma kowa yace kalau take, ni
nasan sakeena bazata ki ni haka kawai ba,
zuciya na wasi-wasi. Gambo yace , kar ka damu
Yallabai, Allah zai warware komai, sakeena zata
zama matarka. Ya sauke numfashi mai karfi
yace, wannan shine babban burina a duniya,
komai Allah ya bani na gode masa, saura
wannan burin ya rage min. Shima zaka sameshi
Insha Allahu. Yayi dan shiru, sannan ya kada kai
yace, laifi nane, rashin kasancewa ta kusa da
sakeena, shi ya jawo shaidani ya shiga tsakanin
mu. Lallai mata na da rauni Gambo, ba taba
tunanin sakeena zata iya hango wani har ya
rikita ta amince dukkan amanar da muka damka
ma juna. Al'amarin na daure min kai, na rasa
yadda xan fassara shi. Yace, haka ne yallabai,
amma idan ka barwa Allah komi na tabbata xai
maka zabin alkhairi. Ka sani ko wata jarabawa
ce Ubangiji yake yi ma don ya gwada imanin ka.
Kar ka damu Yallabai, Allah ba zai hana ka
sakeena ba, idan har kayi imani shine mai
hanawa da badawa. Ya sake jingina da kujera,
ya runtse ido ka fadi gaskiyya Gambo, na gode.
Bai sake tankaea ba haka kuma bai daina
tunanin xuci ba, ma'ana sakeena bata daina
xuwa cikin idanuwan sa dauke da lallausan
murmushinta mai sanyaya masa rai, tana tura
hularasa gaban goshi bakinta na fadin, so much!
Shi ya sa baya aikin komai face ajiya xuciya.
Gambo na jinsa tausayinsa nakara zama cikin
ransa. Karfe daya dai-dai na dare motarsu na
tsayuwa kofar gate din gidansu. Gambo yayi
hon, nan da nan Mai gadi ya shaida hon din
motar mami ne, ya taso a guje ya bude kofar,
motar ta shige kai tsaye kofar shiga ya tsaya.
Al-ameen ya fito, sannan ya wuce ma'ajiya
motaci. Tun kafin ya kwankwasa, yaji ana
kokarin budewa, don haka ya dakata hannayensa
biyu cikin aljihu. Marafa ne da kansa ya bude
kofar, suka zuba juna ido, daga bisani ne mami
ta bayyana wajen har ta riga marafa magana, Al-
ameen . Idanuwansa suka yi tam da kwalla, ta yi
azama ta jawo shi ciki, daddynsa ya maida kofar
ya rufe. Don me ka iyo daren nan Al-ameen? Sai
kace babu inda zaka raba ka kwana! Ya zauna
dabas! Ya kama hannaye biyu, Marafa ya xauna
kusa shi. Ya rungumo kafadunsa, yace baka
kyauta min ba Al-ameen, da ka dauko hanya
cikin daren nan dan kuskure kadan za'asamu,
shikenan ka ajwo mana tashin hankali, karfa ka
manta, kai ke nan guda daya muke kallo zukatan
mu na wankewa daga radadin rashin da. Ya dube
shi ido jajur! Yayin da Mami itama ta xauna daya
gefen suka sanya shi tsakiya. Yace, na kosa in
ganka Dady, sakon Abba xan gaya maka, yace
gobe yana nan tafe maganar aure na sakeena,
kafin in koma yake so a daura shi. Mami tace,
kun daidaita da sakeenar ne? Ya dan kada kai
yace, sakeena ba warke ba Mami, hasalima bata
gane ni ba, shiyasa tun farko nace a kaita
asibiti, kowa yaki amincea da ni, ga shi nan
kwakwalwarta ta tabu. Sakeena ta kasa ganeni
Mami, ni kuma bazan fasa auran ta ba, domin
shine babban buri na a duniya. Su abba sun goya
min baya, kuma ku taimaka min buri na ya cika
don girman Allah. Gaba daya ya kara daga musu
hankali babu kamar Marafa da ko alama baya
kaunar yaga dansa na kukan neman wani abu,
shi yasa nan take ya ji ko ana ba maza ha mata,
sai Al-ameen ya auri mama. Amma ita Mami
bata an ta dosa ba, don haka tace. Al-ameen
bania ron hankalin kanan, na ga alama baka
yarda Sakeena lfy lau take ba.... Ku kuka gaya
min ai Mami... Yanxun kuma ni na gaya maka
lfya, kawai cin amanar ka tayi, tunda kaje bata
saurare ka ba, kai ma ka manta da ita kawai, ka
roki Allah ya musanya maka da mafi alkahiri.
Bafa sakeena kadai ce ta yalwatu da dukkan
abubuwan da kake so ba. Saboda haka ka kama
kanka, ka nutsu ka gane cewa ko an daura
auran, ba zaku zauna lfya ba, tunda idon ta ya
bude, tana takamar tana da kyau, kowa na
kallonta, kajini? Ya girgiza kai, idonsa xuru yana
kallonta, tace au baka ji ni ba? Menene nufinka?
Marafa ya amshe don Allah, don Annabi ki kyale
shi, ba yace Uban dawaki na taf ba? Allah ya
kaimu goben lfya, shi aure ai nufi ne na Allah.
Yanun kaje ka kwanta mu saurari goben, kaji?
Yace naji dady, don Allah ku tayni da addu'a
sakeena kadai nake so. Yace na sani, addua
kuwa kullum munayi, kayi alwala ka sami koda
raka'a 2 ne kafin ka kwanta, na tabbata zaka
sami nutsuwa ok? Ya amsa da kai ya dan
bubbuga kafadarsa yace, yau dan Dady, Allah ya
bamu alkhairi. Bai dai tanka ba, ya mike ya bar
falon. Mami ta cire tagumi tace, sai Allah yayi
wa yaron nan sakayya! Yadda tai masa haka
Allah zai mata. In banda idon Al-ameen ya rufe a
kanta, me zaici da ita? Yarinyar da gwaggo tace
shagon saurayi take su raba dare suna.... Marafa
ya katse ta, don son Annabi, ki bar wannan
magana haba. Ki yi masa fatan alkkhairi kawai.
Cikin bacin rai ta mike ta koma daki. BAKIN
CIKI kamar ya kasheta. Shi kuwa Al-ameen yana
can yana nafilfili kamar yadda dadinsa ya
umarce shi. Da safe ya fito gaba daya ya zabge,
kallo daya za kai masa ka tabbatar da hakan.
Gaban mami ya fadi ta kwala wa Ladi kira ta zo
a gigice. Tace, to hajiya. Ta juya da sauri ta fice.
Mami ta dube shi tace, matso nan kusa da ni. Ya
kara matsowa yace, ina kwana? Ta amsa tana
shafar kansa. Ina dadina, bai tashi bane? Tace,
kwana yayi baiyi barci ba, sai bayan sallahr
asuba barcin ya sace shi. Tana rufe baki ladi na
sallama da tiran abinci ta dire gabansu. Tace ga
shi hajiya dr, Iya tace in gaida ka, yanxun xata
shigo. Yace ina amsawa. Ta fita ta bar dakin.
Mami ta jawo tiren ta hada masu shayi ta mika
masa, ungo nan dan iya. Daute ka sha kaji karfin
jikinka. Ya sanya kofi a baki ya kurba kadan.
Wlh daci mami ba xan iya sha ba. Tace don me?
Ka cigaba da sha za kaji bakin ya washe. Ga
kuma farfesun, bude bakin in xuba maka. Ya
bude 'yar kular ta debo a cokali ta mika masa,
karbi ka gani mana. Ya bude bakin ta xuba masa
tace, yauwa ko kai fah? Yanxun idan Abba ya zo
maganar auranta kankama, haka za'a ga ango a
rame? Dadi ya lullubeshi yayi wani lallausan
murmushi yace, mami na rame ko? Kai baka ji
ajikin ka ba? Bana so kayi angwanci a rame, don
haka ma za ka kama abinci ka ci. Nan da nan ta
ga ya gyara zama ya hau shan farfesu yana
kurban shayi, kinsan wani abu Mami? Sai ka
fadi, shayin nan ya daian min daci. To yi sauri
ka shannye. Ya kuraba ya sake kallonta, yanxu
Mami idan aka daura auran anan xan barta? Eh
mana, ko ba xan iya kula da ita bane? Yayi dan
murmushi, a'a mami na, amma ni na fison mu
tafi tare can, kin ga kafin mu dawo ta mance da
sakaran Yaron da ya hure mata kunne. Ko ma
muyi xaman mu can tana karatunta ina aiki na,
ko kuwa? Ta dafa kafadarsa, gaskiyya ne, ina
goyan bayanka, sai dai in ta haihu ka kawo min
maigida ko kishiya. Ya kyalkyale da dariya,
kwalla suka cika idanuwan mami ta bisi da kallo
tana gyada kai. Yayi gyatsa kafin yace, ina son
twins mami, ko? Sai dai an mai son su baya
samun su? Da sauki ya katse ta, no duk canfi ne
Mami, ni dai ina so kuma Allah xai bani ameer
da ameera. Tayi 'yar dariya tace, duk naji, idan
ma 'yan hudu ne Allah ya kawo masu albarka,
yanxun tunda ka koshi, kaje ka yi wanka kafin
dadin ka ya tashi. Xai ji dadi idan ya ga ango
shar! Yace haka ne mamina. Ina xuwa, ya tashi
da sauri ya fice. Mami ta ta tallafe kunci ta ce
nikam tawa.... Nikam tawa ta sameni, ni Ya su,
Allah ka duba mana. A bakin kofa suka hadu da
iya suka gaisa. Sannan ya wuce bangarens, ya
fada bayi ya sheko wanka, ya kimtsa jikinsa da
wani lafiyayyen farin boyel mai taushin gaske.
Ya fesa turare, ya dawo dakin Mami, ita ma
wanka yi ta sauya kaya. Ta dube shi tana fara'a
tace, haba yanxu na ga daidai. Ina ganin ma dai
daga yau aka angwancin nan. Ya xauna kusa da
ita yana dariya. Tsokanata kike sonyi Mami, me
kika gani yanxun? Sai ma ranar kenan. Ki gane
Mamina, ranar ba zaki shaida ni ba. Ta ware ido
tana 'yar dariya zai hana? Sai dai ko amarya ta
kasa shaida kai, amma ina mami zata mance da
dan tilon dan ta. Dadi ya kara lullube shi, ya
rungumo ta yana fadin Allah sarki mamina, Allah
ya bar min ke tare da Dady na. Dadin ne kansa
ya amsa, amin amin. Ya kara sa shigowa suna
masuayar fara'a. Dadyna ya tashi lfya? Na tashi
lfy Doktna. Suka gaishe shi cikin annushuwa,
duk da bai san sirrin ba, xuciyarsa tayi masa
dadi. Don haka ya xauna aka kawo masa
abincinsa su ka fara ci tare suna kara kwantar
masa da hankalin. Sosai kuwa hankalinsa ya
kwanta, yana ganin tamkar an daura auransa da
mama, tunda yana da magoya baya ta kowanne
bangare