Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 3 of 9
BAKIN CIKI 1***10 Wannan soyayya ta su Al-
ameen dasakeenar sa ko a film ba'a taba nuna
irinta ba. Sannua hankali bikin abdulrahman
yana ta kara matsowa, a'yan tsakanin ne
jarabwar su Mama ta fito. Allah daikon sa
sakamakon ta yayi kyau matuka, domin
tanadaya daga cikin ajin farko. Tsalle da murna
wajen Mama abin ba'a cewa komai, ba ita kadai
ba, kowa yataya ta murna musamman dan gaban
goshin nata,daga can yake gaya mata a halin
yanxun yana tare daabokan karatunsa, suna
liyafar taya ta murna. Donhaka kowannen su dai
tayi magana da shi, tayi masagodiya. Babu bata
lokacu Abba ya fara bincikar mata makaranta a
zariya, amma aka ce ba'a fara siyar daform ba
tukunna, jin haka yasa hankalin Al-ameen
yatashi, sam baya so Abba yayi wahalar karatun
mamakuma, ai cewa akayi a gidan sa xatayi
karatunta. Nantake ya kira wayar gidansu, ya
kuma yi sa'a dadinsana gida, saboda haka ya
marairaice ya bayyana masalarsa, Dady yace,
wai me ke damun ka neAminu? Haba Aminullah!
Menene a ciki, idan ta farakaratun? Yace, ni dai
Dady nafi so ta fara bayan aure,kamar yadda
aka shirya tun farko. Yace, wanan yarorigimarka
tayi yawa, saboda Allah ya kake so inyi?Kaje
wajen Abban, kui magana. Kai tsaye ya bashi
amsa, ba xan iya ba, gaskiyya sai dai ka hk,
bakasan nauyin da nake ji na uban dawaki ba.
Sabodahaka ba inda xani, wannan karon dole ka
hkr. Kuma niban ga wani abin xafi ba, idan
sakeena ta fara karatuyanxi. Cewa xatayi ta fasa
auranka? Kamar zaiyikuka yake fadin, ba haka
bane, Dadyi amma ina tsoron mata a jami'a,
yace, ban son shirmen ka, kayarda Da Allah shi
daya ne mai xartar da komai,sannan ka rike
sakeena da xuciya daya, na tabbataba xa ta ci
amanar ka ba. Ya numfasa yace, shikenanDady,
na gode. Sukayi sallama ya aje waya.
Dukjawabin da dady yayi masa, hanlainsa bai
kwanta ba, don haka yake sake kiran waya gidan
Yaya Abdul.Mama ce kuma ta dauka. Bayan sun
gaisa, ya faratambayarta, yaya maganar
makaranta? Tace, tananan, form din ne har
yanxun ba su saki ba, yace,saboda Allah menene
na wahalar da Abba, yanayawon neman makai
makaranta? Hakki na ne sakeena, don Allah ki
taimake ni, ki gaya wa Abba yabari in dawo,
bayan auranmu, sai ki tsundumamakaranta. Tayi
'yar dariya tace na tsunduma kamarwani kogi?
To menene idan na fara yanxu? Gaskiyyaban so
my princess, pls ki rushe maganar nan sai
nadawo. Ta yaya? Ki na cewa sai na dawo. Babu
mai tilasta miki, tace wa xan gayawa? To sai dai
in gaywaAunty Rabi, tunda ka nace da alama
kana da watamanufa. Yayi murmushi yace,
manufar kenan gudadaya, xallar kishinki, bana
so wani ya san cewa bakida aure, ya lallabo
yace xai miki magana. Aikomuryarki yaji, wlh ya
cuce ni. Ta kama baki tanamasa dariya, a
gaisheka. Dariya kike yi? Dagaskenakeyi, kina da
kyau sakeena, ba karamin jarumi bane xai kalle
ki ya dauke kai. So pls kic gaba daxama gida
har na dawo, in maida ki tawa, ni kadai, aikin
gane? Tace, ba dole ba, ya na iya da Maigida?
Yafara dariya yana fadin iye! Dan sake fadi inko?
Tace,Maigida takobi. Kaina xai fashe uwargida,
in dainafadi? Yace, a'a ci gaba madam. Idan kan
nawa ya fashe, kin san yadda xakiyi. Tace ya
xan yi? Hakanan xa'a sha bikin. Kina fa dada
tunxura ni. Ji nakenakfi kowa awajen nan. Tace,
sa ranka a inuwaAmeer da Ameera suna tafe....
Me kikace? Me nacekuwa? Don Allah ki
maimiata. Allah na manta. Yamarairaice,
gaskiyya ba haka akeyi ba, ba haka akeyi ba
sakeena. Ai dai banji ba sai ki maimaita ko?
Tanata masa dariya tace, sai da safe. Yace, a'a
rufeidonki. Kin rufe? Ta rufe tana fadin, uhm.
Yace, kingansu? Su wa? Ameer da ameera. Suna
tsakiyar mu.Ameer ya cire min hula ya sanya a
kansa. KingaAmeera? Wayyo, kamar ku daya my
princess, shagwaban ta kawai takeyi a ajiki na.
Oh ma Godmwhat a lovely family. I lobe U
sakeena, I really meantit. Murya sanyaye ta
amsa, me too dokta. Tayi saurita kife wayar ta
ruga dakin ta, tayi sufa bisa shimfida,ta datse
ciki ta rasa duniyar da xa ta sa ranta tajisanyi.
Haka ta raba dare tana juyi, bata san lokacin da
barawon ya sace ta ba. Kamar yadda ya
tsaramata haka ta aikta, domin bata bata lokci
ba, ta samiAunty Rabi ta gaya mata, abinda
dokta ke bukta. Taxura mata ido jim, kafin tace,
wannan dan nawa yafiye rikici wlh, menene
banbancin fara karatunkiyanxun da kuma lokacin
da ya bukta? Kar fa yayi miki sakiyar da ba
ruwa, ki shiga gidan yayi mirsisi!Da saurinta
tambaya, kamar yaya aunty? Tace, ayiauran ya
ce bai san maganar karatu ba. Tayimumushi da
bai kai ciki ba tace, Haba anti kamarwani jahili,
ai dokta baiyi xubin irin wadannan mutanenba.
Tace, oh haka ne? Idonki ya rufe kina son sa ko?
Ai shikenan, ni 'yar sako ce kuma ko an tambaye
nishawara ba xance a'a ba. Tace, kinyi daidai
antina,kin kuma san Yaya na ji dake, idan kika
ce eh dinnan, babu sauyi. Tace, banson zakin
baki, inda yakexuwa neman 'yan matansa sani
zakiyi? Ya ya mutsfuska tace, wannan kuma
sharrin kine. Ta dada mata duka. Ai gaskiyya ne
anti, dan Abba sadauki ne,bawan Allah bai yi
xubin shaidanu ba. Ke da kanki, kikace idab
bashi ba, sai rijiya. Tace, a'a sai masai barijiya
ba, meye ajikin Yayan naki da za'a fada rijiya?
Ta gwalalo mata idanuwa tace, ayi kurumaunty,
kar ayi 'yan tone-tone, don ni har na hango ki
agidan Zoo! Tace, kan biki! Lallai yarinyar na ki
gagadon barcina, to ko ke din suke kwakwaxo a
kanki,ma zaki gwada min? Ta kece da daroya
tana fadin, aidama ni ban fadi ba. Aunty ke ce
xaki raina min yaya, alhalin koda mai kwado, ya
dara gaya. Tace, naji saikije wajen kwadon ki
gaya masa da kan ki, a kyalegaya agefe. Ta
rungumo ta, ayya my Aunty ba ma'yar haka dake
surukuta ta kaina! My lovely wife! Tatabe baki
tace, haka naji masu kyau ke da Al-ameendin
naki hakane? Tace ban so surutu, sai in fasa ta
kara kankakme ta, yauwa my swthrt, ke kadai ce
harabada. Tace, ko baki fadi ba. Haka ta lallaba
ta sukasasanta, don ta san halin Aunty Rabo, da
wasa xatace ba xatayi abu ba, amma sai sai ki
sha mamaki,taki ai watarwar da gaske. Ba yaya
Abdulkareemakadai, su Abba kan su sun sha
mamaki da wannan sako da yazo kunnuwansu,
sai dai Abba baiyi jayayyaba, du da yana shakku
cikin ransa, yana jin kamar Al-ameen ba zai bar
ta yin karatun bane. To amma idanya dubi
iyayensa, sai yayi saurin kauda wannantunanin.
Yanxun bikin abdulrahman shi suka gaba,sun
kyale fafutukar makarantar mama. Shi dai dadi
bai san yadda akayi ba kawai an masa ne
makarantarce bata samu ba, sai wata shekara.
Tun sati biyun sasuka wuce aka fara gabatar da
shirye-shiryen biki tahanyar kai kayan lefe
kaduna. Tun daga lokacin sumama babu xama,
kusan kullum fita sukeyi xuwakasuwa, domin
yawancin abubuwan bukata, daga nan minnar xa
su taho da su. Satin daya shigo shine yakama
kwana shida biki, don haka a gobe su mama
damutan gidan za su wuce Fandagori. A daran
ranarraba dare sukayi suna hira da Al-ameen,
saboda xasukwana biyu basu motsin juna ba.
Washegari dasassafe yaske bugowa. Sai da
kalamansa suka sa Mama kuka, don kalamai ne
masu ratsa xuciya, suhana ta sukuni, shi ya sa
bakinta gum! Tana tunanitare da kewar Doktan
ta, ji take kmar tace su sauketa koma gida. Ta
dai ya daurewa sannu a hankali tatattaro
nutsuwarta wuri daya, ta dauki dangana. Sunisa
kuma, ganin Ummanta ya debe mata kewar
masoyinta. Bayan sun ci abinci, sunyi sallolin
su,sannan suka ci gaba da tattaunawa akan
shirye-shiryen biki. Karfe biyar dai-dai lokacin
ne rana tayisanyi. Mama ta sheko wanka tayi
shafe- shafe, bayaga hoda bata karawa fuskar ta
komai ba, ta daukowata atamafa 'yar ingila
ruwan bula ta sanya, ta daura dan kwalin ta, ta
ziro bakaken takalma, ta yafo bakingale ta
rataya jaka. Duk wannan shirin na tafiya
wajenBaraka ne, wai nan ma ba kwalliyya tayi
ba, kawaiyanayin jikinta ne baya boye kyan da
kaya ke mata.Ta sallami Umma ta kama hannun
Ameera suka fitotare A kofar gida suka ci karo
da Ameer, yanaganin gari shi ma yace zaije.
Tace yaje ya fadi a gida,don kar a neme shi.
Daga nan ya kwaso takalman sa.Ya sheka a guje
cikin 'yan dakikai ya fito suka wuce.Suna gaba
tana biye da su, suna xuba mata labari,iya ko
jinsu bata yi, don tayi nisa a tunanin Doktan ta,
kalamansa ke shiga suna fita a kunnuwanta,
"kwanakigoma banji muryarki ba sakeena? Ai
yayi yawa, kitaimake ni kar ki sa asiri na ya
tonu a makarantarnan. Xauntuwa xanyi cikin aji
in kasa gane komai".Idanuwan ta suka tara
kwalla, tayi sauri ta shanye su,tana fada aranta,
ba xan xauna ba, ana gama biki xan koma......
Sannu 'yam mata! Muryar ta fito. Samaribiyu ke
xaune bisa benci a kaofar wani katon shagodaf
da bakin titi. Daya fai sol! Ga dogon hanci
damatsakaitan idanuwa, duk da cewa a xaune
yake, kana kallon sa zaka gane dogon gaske ne.
Gashinkansa kuwa mai santsin gaske ne, har
yana nannadewa duk da cewa bai da yawa
akansa, watauyayi aski. Kwalli ram! Ya xauna a
idanuwan kamarmace. Ga kuma alamar gashin
baki baki wulik! Akwance, guda kuwa wankan
tarwada ne kuma zamansa kusa da na farkon, ya
dushe gaba daya kyan sa.Gaba dayansu, ta san
su, amma tuni suka bace a kwakwalwarta, domin
shekaru masu yawa rabon ta dasu. Sannan ko a
wancan lokacin babu wata alakantsakanin su.
Shi yasa a yanxu take masu kallonmamaki,
yayin da farin yake kara fadada murmushinsa,
sannu ko? Ya sake fadi. Wani guntun tsaki
tayi,ta wuce abinta, sukayi sa'a babu wata mota
mai xuwa, don haka ta rike hannun yaran suka
tsallakatitin. Ka gani ko? Na gaya maka karka yi
matamagana, ba zata saurare ka ba. Yayi
murmushi yace,ko bata suarare ni ba, dole ne ma
ta so ni, domin irinwadannan su ne ke nema
kuma ban taba daga ido nadubi yarinya nace ina
son ta ba, tayi min kallon banza ta xubar ba.
Yace yau ka samu, saboda haka dukabinda kake
takamar ka na dashi, yau ka hangowacce ta fi
ka, kar ka kuma ka mance, bikinta sauran'yan
watanni suka rage, mijin da xa ta auran ma
bashianan kasar, kaga kuwa yafi ka komai. Ya
ja dogontsaki, aikin banxa, to meye ruwa na
dashi? Kasan Allah yarinyar nan sai dai in ban
so ta bi ra'ayi na ba,cikin dan kankanin lokaci
zan birkita ta, ko? Wlh, kajina ranste, yace
hakan dai babu kyau, tunda na gayamaka bikinta
ya kusa, sai ka hkr. Yace, kai ba xanhkr ba,
yanxu ma na fara sonta. Yana dariya yace,sai ka
shirya yaki da manyan kasa, na lura har yanxu
ba ka hankaltu ba. Yace, bar maganar nan tun
kafinran ka ya baci, don Uban ka! Yace, nayi
shiru. Zai fimaka kyau. Ya tashi daga kantar
shagon sa ya komaciki ya xauna a kujera. Bai
kara tankawa na wajen ba,haka shi ma bai sake
cewa da shi komai ba. Yayin daita ma mama ke
tafe tana sakin tsaki kamar tsaka. Ranta bace
tayi sallama gidan su baraka. Barakar ketsakar
gida tana wanke- wanken yamma. Tayi
tsallesama ta runtuma a guje suka runguma
juna. Inna taleko daga daki da sauri tana
tambaya lfya? Sai tagansu rungume da juna, tayi
dan tsaki tace, Ammadai Allah ya shirya ku,
kunji yadda gabana ya fadi? Suka nufo gunta
suna dariya, wayyo Inna, kinsankwana biyu ba'a
hudu ba. Tace, ku rika nutsuwa,girma kuke
karawa. Mama tace, to Inna. Suka shigedaki,
suka gaisa da Inna, sannan suka dawo
indaBaraka ke wanke wanke ta baro su Ameera
wajenInna. Ta kawo wa Mama kujera ta xauna
tana wankewa. Mama na mata dauraya. Ina
mutuminki?Tayi dan murmushi tace, karki sani
kuka don Allah,yau da kyar zan iya barci baraka.
Ko? Kuna da abindariya ke da likitanki nan, tace,
baiki tausayinmukenan? Tace shagwabar kawai
ke damunku, shi yamarairaice, ke kin
marairaice,, to wa zai rarrashi wani? Da kan mu
muke rarrashin junanmu. To yaza'ayi, ke kuwa
soyayya. Tace, baku da laifi, in gayamiki nima
na kamu. Ta mika mata hannu, ban mukashe,
don Allah, a ina yake? Suka tafa suna dariya
kafin tace, danKagara, wani dan aiki ya kawo shi
na garin, na yiniguda, in gaya miki ashe rabo na
ne. Muhammadsunan sa, yana aiki a sakateriyar
nan ta kagara. Tajuya idanuwa tace, ba shakka
ta muhammad. Allah yatabbatar da lkhairi. Tace,
amin. Suka kara tafawa, ai zaki ganshi, dan
kyakkyawa shi ga addini. Tace, baikai Aminu na
ba dai. Ta tabe baki tace, naki kikasani, ni kuma
nawa na sani. Kowa da gwaninsa.Tace,
gaskiyarki, kuturu ma sarki ne a gidan sa.
Shikika raina ma wayau? Tace, ba haka bane
wlh, aimisali ne kawai. Tace, na gane kowa jin
kamsa yakeyi a inda yake takama? Mama ta
gyara zamatace, har kin tuna min, wai yahse
wannan me masunansa? Wannan da aka jefe
babansa wajenkwartanci? Tace oh! Kina nufin
Dan liti? Yauwa shimyaushe ya dawo gain? Tace,
ai ya jima zai kai satibiyu. Ta tabe baki, na gaua
bude wani shago ne? Kai mutane ba su da
tunani, menen na barin Dan liti yaxauna garin
nan har da ba shi hayar katon shago?Tace,
manyan gari ma basu kore shi, wai zai koreshi?
Wai kin san ma wani abu? Yanxun nana xan
wuce,wai sannu 'yan mata yace dani. Tace, haka
yake,anyi gadon banza ido a mata. Shi jinsa
yake mai kyau, marasa tunani na binsa yana
lalata su. Kingashekarunsa shida rabonsa da
garin nan, amma yanadawowa 'yan mata na
masa layi, yana tijara su. Takaici ya ishi mama
tace, kwadayi, ba an ga ya dawo daabin duniya
ba? Ai mata mun shiga ciki, kwadayi kekai mu
ya baro mu. Allah ya shiryemu, tace ameen dai.
To wai shi da yayi miki magana menene nufinsa?
Ido waje tace oho! Shi ya sani, ke da baki wajen,
idankin tanka, nima na tanka masa. Allah ya isa
ma nayimasa, daya katse min tunanin dokta na.
Suka tafa,Baraka ta mike ta dauki kwandon
kayan ta shige dashi kicin. Mama ta dauki
tsintsiya ta sa ruwa ta kora wurin, ta share tas!
Suka koma dakin Baraka. Hirar takoma can tare
da tsara shagalin biki. Gab da akekiran magriba.
Mama ta baro gidan Baraka tayo matarakiya,
suna rike da hannauen yaran har bakin titi.Anan
Baraka ta tsaya tace, to sai na zo goben ko?
Tace, ina jira, don Allah ki zo da wuri. ISA, lah!
Kinga mutumin naki da zai rufe shago, ya hango
ki ya fasa.Kar ki bi ta wajen sake hanya. Kinsan
Allah bai isaba, bazan dauki nisa saboda shi ba,
idan ya matsamin sai ya sha mamaki, don xan yi
masa wnkinbabban bargo, kafin nan bar garin
nan. Ina son kimatar likita, amma ki tsaya bata
lokacinki wajen danliti asara ce, ki wuce kawai,
shi ya fi. Allah kokawata? Don dai ba ke yake
wa magana ba, shi yasahaushin bai damunki.
Tayi 'yar dariya, haka ne, ammaina rokon ki,
karki kula shi, ba don ni ba sabodaDokta. An
gama, kinsan wani abu? Cewa yayi idanwani yaji
murya ta kawai, ya cuce shi, abinda na tuna
kenan. Saboda haka kwalelensa, ba zaiji ba. Suyi
'yardariya. Kuje, yanxun xa'a kira sallah, sai
goben. Allahya kaimu. Ta sallamu su ameer, ta
tsaya sukatsallaha, sannan ta juya ta koma. Kai
tsaye mama tazao zata wuce. Dan liti bai
daddara ba, ya sake yimata magana, 'yan mata
an dawo? Ko kallo bai isheta ba, wannan karon,
ya daga murya ya sake fadin,Haba 'yammata ai
rika sauraran masoyi mana, don ba'a san inda
rana zata fadi ba! Kai, Dan liti yayi sa'atayi
alkwarin ba zai ji muryarta ba, amma da
yajiamsar da ba zai sake marmamrin kula ta ba.
Dawannan haushin ta iso gida. Suka yi alwala da
yaran sukayi sallah. Dare ya raba barci, yaki
zama cikinidanuwan ta saboda zafi biyu suka
hade mata, gakewar muryar sanyin ranta, ga
kuma takaicin rashinba Danliti amsa, har yanxun
yana mata kaikayi axuciya. Idan ta tuna kalaman
sa na karshe, ta kanjikamar zata mutu. Wai ba
'a son inda rana zata fadi ba? Ta kan kuta, ta
shanye hwayen idanuwanta. Hakata wayi gari da
ramar rashin barci, shi ya sa take jinkasala.
Xuwan Baraka ya sa ta gyagije ta mike
sosai,suna ta aiki. Ba'a jima ba, ango ya iso.
Gida ya karagauraye wa da shewa da guda.
Bayan sallar la'asarmutanen Abuja suka iso.
Sannu a hankali gida ya cika da 'yan biki na
nesa da kusa. Tundaga lokacinake ta dora
tukunya ana saukewa.... Ranar juma'a akwai
dinner a kd. Don hakaango ya kwashi su mama
da baraka tare da su danDanlami ya wuce da su.
Mama kam sai da mucetsarki ta tabbata ga
Allah gwanin halitta, ka ranste daAllah itace
amaryar. Tana gefen Yayanta, ya na ji daita.
Samari kowa idonsa na kanta. Cikin abokansa
kuwa babu wanda bai taya ba, amma ya ce mus
ansanya mata ranar 'yar watanni suka rage
bikinta.Kash! Duk wanda yaji sai ya numfasa.
Lallai Al-ameen gaskiyya, sai ma yanxu take
kara jinjinwatunanisa. Bata gama shan mamaki
ba, bayansundawo daga diner, misalin goma na
dare, suna sashin baki a gidan ango, inda aka
xubawa amarya kayandakinta. Suna tare da
Baraka hirar dinner kawai sukeyi. Dan lami ya yi
sallam ya shigo yace wa mamayaya Ali na
kiranta. Tace lfya? Yace kalau, yana canbaya. Ya
fice abinsa. Ta dubi Baraka tace, kinji
watasabuwa kuma. Tace, wata tsohuwa dai, ai
kun jima da Yaya Ali. Abin ne ta motsa, kin san
gyambo ne, tace,Allah ya ba shi sauki. Ameen
dai. Ta figi gyale ta yafata same shi a bayan
gida yana xaune bisa dakalinsokawe da fara'arta
ta tayi sallama, ya amsa. Ganinfusakar ta sake
ya sa shi ma jin sanyi cikin ransa,tace wai kana
kirana? Yace eh ina kuma fatan xaki saurare ni,
ta kara matsowa tana fadin me hana yaAli? Meya
faru? Ya mike daga inda yake yace ga gurixauna,
tace a'a yay Ali kayi xamanka kawai, no kixauna
ai ni nace ko? Ta xauna tana murmushi sannanta
dube shi suka hada ido, ya akayi? Yace
babukomai Mama, kawai so nake muyi hira. Ta
sunkuyar da kai tare da numfasawa. Yace nasan
tuni kin mantada ni cikin ranki, amma ni na kasa
mama, waccesahwara xaki bani? Ta dago kai ta
sake dubansa,tace me xaisa na manta da kai Ya
Ali? Karfa kamanta jininmu daya, dubi
fuskokinmu kamar mu daya,don me xan manta
da mutum kamar ka? Ashe lallai xan iya
mantawa da su Ya abdulkadeer. Ya
saukenumafshi yace, haka ne, amma kin san ina
miki waniso na daban ko? Sao dai ke kinyi nisa
da soyayyarwani, har kun kusa aure. Ba wai ina
masa ynaka bayabane, so nake ki gane har
abada ni mai sonki ne, bakuma xan taba fidda
rai da ke ba, sai ranar da na ga an shafa fatihar
auranki. Xanyi farinciki, idan har zakiyarda mu yi
hira koda labarin Al-ameen zaki rika bani,wlh
xan saurareki. Ta runtse ido, tausayin Ya Ali
yaryfeta, sai dai runtse idanuwan da tayi bata
ganinhotunan kowa face na Al- ameen dinta. Tayi
sauri tabude, idanuwanta suka kada, a sanyaye
take cewa, kayi hkr Ya Alli, komai mukaddari ne
daga Allah. Kayiaddu'ar Ubangiji yayi maka
sauyi na alkhairi. Sannankuma ina so ka sani,
ban taba kin ka cikin raina ba,kuma ba xan taba
kinka ba, shi aure nufi ne na Allah.Shi ne yake
shirya abinsa yadda yaso. Ina fatan kafahimce
ni? Ya gyara tasyauwa yana kallonta, yace, na
fahimce ki mama, na gode da gudunmawarki.
Toamma bana so kana damuwa. Yayi dan
murmushi, nadaina kanwata. To kai sai yaushe
zaka yi auran? Sairanar da na daina ganin Mama
a matsayin budurwa.Ta kalle shi tana 'yar dariya,
ka tsufa Ya Ali, ka fagirmi ya Abdulrahma. Kana
so a fara maka kiran gwauro ko? Hakan bai
dameni ba. Ni ya dameni, aceyayana gwauro.
Yayi dariya, nace ki bari na tabbatarna rasa
wacce nake so, sai in rufe ido in kwaso kowace
ce inyi maneji. A'a yayana, tsakani da Allahzaka
aureta, ai sunnan ba'ayin ta da maneji. Iba
dace,ibada kuwa akwai hakkoki cikinta.
Gaskiyane, amma kin san shan kojo kwanciyar
rai. Kuma kowane soyana da mizaninsa a xuciya,
ni na san babu macenda xan so tamkar yadda na
ke sonki. Ya Ali kenan,ka bar maganr nan don
Allah, na yi karya ne? Banfada ba. Bari na shiga
ciki, kin gaji da surutu na ko?Ta kada kai, a'a
wlh kawai barci na ji ya soma kama ni. Kindai
gajin kena. Eh, toh da xak duba agogonkakila ka
ganr dare yayo. Ya duba agogon ya dubeta,sha
daya da rabi ne kawai. Tayi sauri ta mike, wuu!
Aikuwa na kawai bane, dare yayi yaya. Kai
kankaidanka ganni da wni a wannan lokacin,
dole ka koranigida. Uhm hakane, amma banda
Al-ameen, don ban isa na rabaki da shi ba, do
ne? A matsayinka nayayana, idan bayi dai-dai
ba, dole ka hukunta ni kotare da wa nake. Yayi
dan murmushi, to na gode. Saiwani lokacin
kenan? Uhm..... Sai da safe. Allah yakamu lfya,
Ameen. Ya wuce ba tare da sake waigowaba. Shi
kuwa kallonta yake tayi har kule ya sauke
numfashi, ya koma inda ta tashi ya xauna, shiru
jimsannan ya kada kai cike da damuwa.
Damuwar mamaba a kan tausayin Ya Ali kawai
ta tsaya ba. Ji takekamar tayi abinda ba dai-dai
ba ga Al-ameen. Shi yasa xuciyarta ta rasa
sukuni ta rika korafo wajenBaraka. Allah ya sani
ba tadi tayi da Ya Ali ba, illa ta saurare shi ne
kawai don ta kwantar masa da hankali.Yaushe
rabon da yayi mata magana irin wannan?Tabbas
ta gane yana cikin matsala, dalilinsa da ya
sakenan ta tsaya ta saurari kalaman bakinsa,
wadandatake ganin amayo su xasusa ya sami
sukuni aransa.To ita gashi ta shiga matsalar,
gani take tamkar taci amanar doktanta. Ta
runtse ido hotunan sa sukabayyana gareta, yana
ta cuba murmushi muryarsa nafadin.. Shema
Alqali "Manufar kenan guda daya, zallar
kishinki.Bana so wani ya san cewa baki da aure,
ya lallaboyace xai miki magana, ai ko muryarki
yaji, ya cucuniwlh." A bayyane take magana
batare da sani ba, kayihkr dokta, Allah bada
wata manufa nayi ba. Barakadake kallonta, ta sa
hannu ta bubbuga ta. Ta mike firgigi dafe da
kirji, Innalillahi wa inna ilahir raji'un!Baraka
tace, wlh xaki xautu! Sambatu kikeyi, idanbaki
sani ba, ki sani yanxu. Ta numfasa tace,
barakaDokta na baya so kowa ya ji muryata. Har
'ya uwanki?To kunyi karya, dole aji muryarki,
musammamn su YaAli, domin dan uwanki ne,
kuma tare ya ganku. Shima ba irinsu yake nufi
ba, karki maida kankimahaukaciya mana. Ta
koma ta kwanta shiru,idanuwanta suka kawo
kwalla. Kada ki shiga rudun daxai dagula
lissafinki, a aikin baxa har karshenrayuwarki, ba
xaki daina magana da Yaya Ali ba, Al-ameen ba
zai hana ba, don ya san dolenkine. Dama kin
kwanta kinyi barci da ya fiye miki alkhairi. Ta
maida kai bisa filo taja mayafi abinta. Mama ta
saukenumafshi, ta gyara kwanciya bata san
lokacin dabarci ya sace ta ba. Tun safe suke
shirin tarbar 'yandaurin aure, karfe daya dai-dai
kafar gidan ango babumasaka tsinke da motoci,
bayan anyi sallah. Abokan ango tare da angon
kansa suka jagoranci tawagarxuwa gidan iyayen
amarya inda aka daura auranFadila ta ma
mallakar Abdulrahman halas malak!Daga cam
liyafar cin abincin rana akayi ta maza
zalla.Komai ya ji. Masha Allah! Babu bata lokaci
motocindaukar amarya suka koma, yayinn da
Mama da Baraka suka koma motar Abba. Anata
kirana sallarmagriba, amare suka suka
Fandagori, kebabban wurida aka gyara musu
cana aka sauke baki. Washe garisuka sha
gagarumar walimar da aka jima ba 'yikamarta ba
a Fandagori. Xuwa la'asar baki suka komakd,
aka bar amarya da lainta. Mama da baraka ke
tare da ita, suna ta tslkanarta, karfe biyar da
rabi ango yashigo, saboda haka suka fito suka
basu wuri. Daganan Baraka tayi sallama da
kowa, ta kwasokayayyakinta. Mama ta daukar
mata wasu suka kamohanya, tana yi mata rakiya
sun atafe suna hirar susuka doso shagon Danliti.
Da saurinsa ya fito ya xauna, yana jiran
karasowar su, suna xuwa kuwa yatanka, 'ya
mata ran gari! Ko kuna jin gaisuwa? Su kaba
banxa ajiyarsa, suka wuce. Sun dan jima bakin
titi,suna sallama kafin Baraka ta tsallaka, ta
kamahanyar gida. Mama ta juyo ta dawo, 'yan
mata ji manadon Allah! Dan liti baiyi xuciya ba,
ta kyale shi, ta wuce. Kawai ganinsa tayi ya sha
gabanta, haba 'yanmata, tunshekanjiya na ke
gaishe ki, me yasa bazakiamsa min ba? Bakin
ciki ya turniketa, kamar ta kurmaihu bata san
lokacin da ta amsa masa ba cikinxafinta. Tace,
wai dole ne? Ko ka ganayi kama dashirginka?
Yace Ya salam! Maida wukar 'yan mata, ba fada
bane, A zato na so bai taba zama laifi ba.Taja
dogon tsaki ta wuce shi. Ya daga murya ya
sakefadin, a daina fada da masoyi, don ba 'a san
inda ranaxata fadi ba! Taf! Yayi biyu kenan.
Kamar xata daure,amma ta kasa, cak!!!! Ta ja ta
tsaya, ta juyo ta dubeshi har ya koma maxaunin
sa, kusa da bokinsa, na rannan. Ta tako a nutse
taxo gefensa, ta tsaya sukakarewa juna kallo.
Yayi dan murmushi yace, ko ke fa?Ai idan kace
so an gama magana 'yan mata. Ta gyaratsayuea
fuska daure, " wai ba kai bane danliti? Ni ne.Dan
wajen buzu mai shayi ko? Ya
hadiyemurmushinsa, kwarai nine. Ta kara
kankance idanuwa, ta cigaba, wanda yaje
kwartanci din nan akakama shi, ya ci dan banxan
duka, wuya ta kashe shi,ko bashi bane? Wani
irin kallo yake mata, bai iyacewa komai ba, ta
kara karkacewa tace, ai kodamuke yara ba mu
da wayau sosai, tarihin bai bacemana ba na
munana ayyukansa, muna ganinsu cikin
idanuwan mu. Hijira a gudu bayan 'yan shekrau
adawo, ba shi xai goge rubutun ba. In bnda
abinDanlita, ai bindin rakumi yayi nesa da kasa,
kumagaskiyar hausawa da suke cwa kwarya bai
kwarya.Dube ni da kyau, kai kanka ka sanni ba
abokiyarhadin ka bace. Don Allah a rika nutsuwa,
ana tunanin abinda ya dace. Taja tsaki ta wuce
su, suna kallonta.Baby wanda ya motsa. Sun fi
sakwan uku bayantafiyarta. Babu wanda ya
tanka baokin yace, kaga irintako? Sai da nagaya
maka wannan yarinyar ba xatasaurare ka ba,
gashi ka jawo ta zagi baba.Idanuwansa sukayi
ja! Yace, ta kuma debo ruwan dafa kanta ba. Xan
nuna mata tabbas ni dan gidanbuxu mai shayi
ne. Ai ni dama irin wadannan 'yan jinkan nake
nema, inyi maganinsu. A'a dan liti baka
dagaskiyya. Tun farko na gaya maka yarinyar
nan an samata rana, bikin ta ma ya matso. In
banda iskanci irinnaka, menen na yi mata
magana? Mu da muke gari ma, bamu ce xamu
neme ta ba sai kai da ka dawokwanan nan? Mu
ma ai mun sa cewa tana da kyau,amma mu ka
basar. Dahskiyara da tace kwarya tabikwarya. To
wannan karon xa ta hau akushi, kuma taxauna
daram dam!!! Yace, wlh kayi karya.
Billahillazi,yarinyar na sai ta dauki cikina
kuma.... Ya tsohe masa baki. Babu ruwana
danliti, idan ka jawo bala'inda yafi karfinka. Ka
ga muna xaman lfya, ba uwa bauba a garin nan,
gara ni bani da tabo... Amma kai kana ganin
abnda ya faru zamangarin nan ya ggareka ,
yanxu ka samu ka dawo harankarbe ka , don
Allah kayi kokari ka zauna damutane lfy. "Ai ba
saboda Allah bane da shiri na,nadawo, shi yasa
kaji bakin kowa gum! Sai itace maibakin rashin
kunya. To zanyi maganinta , wadanda ma suka
fita taurin kai, na gama da su balle ita.Kasan
Allah yarinyar nan sai ta raina kanta ..." Danliti!
Karka fara wannan danyen aikin , ina ba
kashawa. Kasan tana da yaya babban soja ko?
Wlh yakwashe ka ya kai bariki, kai kanka idan
aka aje kagaban mirrow baza ka shaida kanka
ba".. Ya ja dogon tsaki, "Aikin banza, kai ka ke
tunanin soja, sojanbanza. Sojan wofi" da kwalli
kake takama Dan liti,gashi nan kuma a idon ka
ban ga yayi tasiri ba, bansoka matsa da yawa
Dan Liti, watakil rabon whla kejanka" Ayuba na
ce ba ruwan ka, nkna sha alwashinzanyi maganin
yarinyar nan. Kasa ido za ka ga abinda zai
faru"... Ya zura masa eyes yana mmakin sa,
dazaiji shawarar sa daya kyale yarinyar nan
tunda Harda Allah ba ajin sa bace, idan aka bi
salsala. Ammashi Dan Liti ko ajikin sa, watakil
ajali ke kiransa,kamar yadda ya faru da
tsohonsa...
BAKIN CIKI 1***11 Washegari anti amina da anti
rabi suka shiryatafiya. Tun dare mama ta hada
kayanta tace ita mazata bi su,fasa karin
kwanakin da tace zata yi.Gabadaya suka rufe ta
da tsokana wai sbda alamin zatakoma.Tace eh
sbda shi din ne haramun ne? Ita kadaita san
abinda ke damunta. Duk da ta ba danliti amsa,ji
take kamar amsar tayi kadan ko alama batason
ganinsa balle tahi munanan kalaman
bakinsa,shiyasa ta zabi data koma minna tayi
zamanta canhar lokacin da alamin zai dawo.
Allah da ikonsakuma,anti amina ta kafe tare
zasu tafi wannan karon.Gaskia hankalin ta zai fi
nutsuwa a minna sbda tana gani bebi alamin
tana renon sa yana mata dariya idanta kira shi
dokta.Ita kanta anti rabi bata so hakanba,sai dai
ba yadda ta iya dole mama ta bi anti aminata
nace.Suna ta zuba kayan su a mota.Yara
damanya na taya su,bayan sun kare suka kara
sallamada kowa duka suka yo musu rakiya har
da marya da ango.Mama ta shiga bayan mota ita
da malami.Yayaali ya tsaya jikin tagar ya zuro
mata ido "wai damadake za'a wuce? Tace eh
mana."Na zaci zaki yiwaumma kwana biyu".Tayi
murmushi,naso hakan ammaai zan dawo,yaushe
kenan? Ni ma sai inzo mugaisa.Tayi er
dariya,gaskiya ba zance ga lokacin ba,watakila
ma sai alamin ya dawo,"Ke don Allah,kusan
wata uku kenan ashe zaki iya tafiya ki barumma
tsawon wannan lokacin? Tace ba haka bane Sai
ga yaya soja ya fito tare daabba,shi yakatse
musu zancen.Abba ya leko,toauta na a kula
dakai kin ji? Tace to abba",yayanyace "abba har
wanirarrashinta kake yi,jaririya ce? Yaceitace
mana,damaina son gaya maka ka
dainarankwasar min ita'.Yawaigo gidan bayan
yanafadin,rankw ashi abba?Irin wannan?Abba ya
bude murfin motaryace,"auta nafito! Fito ki bi
abdulkareem. Tafito dage da kai har dakukan
shagwaba,masu dariyanayi.Shi ma ya fito
dasauri,sorry abba,sorry! Ya kamakunnuwansa
yarike,"na rantse ba zan sake ba" tacuno baki
tamakale kafada,ni ba zan bi suba.Yaya yace,"za
ki tsallen kwado awajen nan,I'm telln you,ki
shigamotamu tafi!Ta kara turo bakin,abbayace
'yi hakuri komaki kyale shi".Har ta tura kai
zatashige ta sakedagowa ta dubi umman ta
tsayekofar gida tanadariya,ta ruga wajenta ta
rungumeta,umma zan dawonan ba da dadewa
ba.tace wuce kutafi". To Allah ya tsare. Ta
saketa,ta kwaso sauri bata san yaddaakeyi ta
dawo ta bangaran inda yayaali yake
tsayeba,kawai ganinsu tayi daf dajuna,ta bi shi
da kallokafin tace,ba zan dade ba,zandawo."
Jikinsa yayi mugun mutuwa yace,adawo
lafiya"'amin".Ta bude mota ta shiga yataimaka
ya rufe kofaridanuwansa na kallonta,Ta
sunkuyarda kai,ita kantabata san abinda ya
kashe mata jikiba,sannan batasan me take
tunani ba,Ji tayi motana tafiya ta dagoda sauri
tana daga wa kowa hannuhar suka bace.Ta
maida kanta jikinmota ta jawo malami
tarungume.suna isowa daidai shagondanliti,daga
muryayayi yace "Allah ya kiyaye hanya!Ta ballo
masaharara,yaya nta na
fadin,"amin""amin".Tana harararsayana mata
murmushi har da dagamata gira,ta sakidogon
tsaki,"ke da wa? Anti aminata tambaya,tace
mantuwanayi.Yayanta yace 'ba zan koma ba!
tacenima bance ba yaya ai ba waniabun damuwa
bane namanta". Suka fada titi,komadamuwar ne
ba zankoma ba lazy girl"tace "lazy soja"ya
kyalkyale dadariya yana kallon
motarabdulkareem tana bin su abaya yace,ni ko?
Za ki shiga guardroom yarinya,jikin ki zai
gayamiki".Suka kalli juna ita da
malamisukatintsire da dariya haka suka
cigabada tafiya. Har suka iso minna anan suka
tsyasuka karayiwa juna sallama
sannanabdulkareem ya daukihanyar unguwar
su,su kuma sukacigaba da tafiya.Sun isa abj
lafia,sojoji biyu kegadin gidan suka budemusu
get. Bayan sun yi sallolinsukowa yaci abindayake
sha'awar ci daga nan mamada anti amina suka
shiga gyaregyaren wuri.Karfe tara na darelokacin
neda mama ta gama shirin barcibayan wankan
datayi.Suna kwance da malami wanilittafin
labarin yaratake karanta masa,anti amina
tashiga dakin tace,gadoktan ki can akan layi
dama yasan yau zaki dawo?Ido waje ta kada kai
tace a'a kilasun yi waya da anti rabi ne ta
gayamasa,ba mamaki je ki dauka.Tasauko kayan
barci ne jikin ta rigada wando ta rugafalon kasa
ta dauki kan wayar dakeaje gefe,tayimasa
sallama,ya amsa muryarsa nabayyanar dafarin
cikin zuciyarsa.Watau abj kikagudo ko?me
kikenufi da kika baro dokta acan?'Yardariya tayi
tace,shi ma yaji yaddanake ji.Baki da hujja
yarinya kikomagun sa kafin mami taci ki
tara.Zankoma yallabai,toya karatu,ya rasha?To
ba laofoamma rasha kin sansai maneji da nake
yi,zuciyata nagun ki myprincess.Tana murmushi
nima inatuhumar kadokta,waya gaya maka ina
nan?Yace kawai na kira ne inji ko suanti sun
dawo,inyi musu barka dadawowa.Sai take gaya
min kemakina abj,ta dannumfasa tace ta
kyauta.Ko?Allah,dama ina tatunanin ina zan ji
ka?Allah sarkisakeenta,to ya biki? Tace anyi an
gama lafiya amarya na can tare daangonta.da
kyau,saura namu ko? Tayi murmushi batace
komai ba,ba zaki amsa min ba? Me zan ce?
Bayankasan hakan?yace to Allah ya nuna
mana,ki karahakuri na kusan dawowa kin ji?
Idanuwanta suka kawokwalla.Na kosa dokta,baki
kai ni ba sakeena,ni kadai na san yadda nake
ji,kin san irin son da nake miki kekanki kin san
ina wahala anan tsawon watannin danayi ban
ganki ba sakeena yasa idanuwa na sunmakance
alhali lafiyar su lau,dul abinda na kalla
bayagamsar dani my princess hakuri kawai nake
yi. Tagoge kwallan bisa kuncinta,ta numfasa,no
sakeena,pls kar ki gigita ni,stop crying,please!M
uryana rawa tace dole in yi hawaye dokta,domin
na fi kafuskantar kalubale shiyasa na kosa ka
dawo ayi takare,Yace kalubale? Wane iri sakeena
ta?kowa zuwayake nema na,kare da doki
ma,shiyasa na gudo abjdon inyi musu nisa.Yayi
hucin zafi,ya fahimci ta shiga damuwa,kar ki
saurare su sakeena kullum ki rikakallon zoben
alkawarin mu sannan kar ki manta akwairanar
auran mu a kanki. Nauyi ne babba a kan ki
myprincess pls,kar wani kalubale yasa ki qi
saukewa,kitaimake ni dom girman Allah". Ta
kara goge hawaye,ka daina roko na doktadomin
kai ma kasan cewa ban iya rayuwa da kowaface
kai,idan kana roko na sai in ga kamar baka
yardadani bane.Da sauri ya amsa na yarda dake
sakeenakema in har kin amince da magana ta to
ki sharehawayenki ki daina kuka zuciyata ta
daina konewa. Ta share fuska tare da kokarin
tsaida hawayenta,nadaina dokta,yace good girl!
To bani labari me kikashirya a bikin mu? Tace
me zan shirya baka nan? Nikuwa kinga list din
nan anan rubuce,karanto min inji?Da farko
akwai immunization day,wasu manyamanyan
allurai ne na tanadar don amarya.....Dariyarta ta
katse shi shima ya fara dariyar,ki tsaya kiji
mana!me zan ji?Wannan shirin naka almara ce
kamasake.Na riga na gama shiri na ba zan sake
ba,yarinyaallura biyu da safe,biyu da rana,biyu
da daddare,shidakenan.Sosai ma,duk a jiki na,ah
to,sa wasa kiga aiki.Ta cigaba da dariya
hankalinsa na kara kwanciya,kokari nsa ta
manta da waccan maganarshiyasa ya dage da
bata dariya har dare ya fara nisabasu sani ba,ai
kuwa yayi nasara don ko data je takwanta bata
yi tunanin komai ba,tace labarin dayarika bata
har tayi barci mai rai da koshi ne. Kwanabiyu
cif!yau zuwanta abj kuma ko a daren yau
alameen ya kira sun sha hira tana ta kewar
bebialameen ta kwanta barci,sosai take son
ganinsashiyasa ta kwaso hotunansu ta tsibe tana
kallo hakata bata lokaci tana kallon doktan ta
sannan tasumbace shi,ta tattara hotuna ta maida
cikinjakarta,ta dawo ta kwanta ta zurawa
malami ido amma a zahiri ba shi take kallo
ba,wani tunanin candaban take yi,bata san
lokacin da barci ya sace ta ba Tsintar kanta tayi
tare da danliti bisa benci akofar shagonsa cikin
wani irin nishadi na banmamaki.Wani abu suke
ci wanda bata tantance komenen ba.Ta sanya
masa a baki ya cinye,shi ma yadauko yasa
mata?Ta sake daukowa ta kai masa bakishi ma
ya kara mika mata sai ta hade da yatsun sa ta
cije,ya rika yarfawa yana fadin,"wash! Sakeena!
Wlhda zafi! Ita kuwa dariya take yi har da kama
ciki,yakawo mata duka ta tashi da gudu ta mika
hanyargida,tana gudu tana waigensa tare dayi
masadariya.shi kuwa kwala mata kira yake mai
karfi yanaamsa kuwwa "sakeena! sakeena!!
sakeena!!! Ta yunkura ta tashi zaune dafe da
kirji tana fadin,innalillahi wa inna ilaihir rajiun!
sharkaf tayi da zufa kumatana ta numfarfashi
tamkar wacce ta sha gudunfamfalaki. Ta lalubi
fitilar tebur ta kunna ta cigaba dazare ido tana
dube dube,mamaki ya isheta tanatambayar kanta
'me ya hada ta da danliti? Barcin da bata sake
komawa ba kenan har gab da asuba alokacin ne
wani sabon barci ya dauketa,ji tayi ana
tabubbuga ta,ta bude ido a natse ta dubi mai
tashi Malami ne a tsaye yana mata dariya,gari
yawaye anti ki tashi mu yi sallah.Ta tashi da
sauri tadubi agogo karfe shida daidai,ta duro ta
fada bayi tayoalwala tayi sallah,wani abinda ke
daure mata kai shafta mance da mafarkinta,a
zahiri ta san tayi mafarkiamma ta kasa tuna
irinsa. Haka ta wuni tunani babu kuzari a jikinta
kuma ta kasa gayawa kowa. Hattaalamin da bata
iya boye masa duk wata damuwartayau ta kasa
gaya masa mafarkinta mai ban mamakiballe ya
taya ta addua.Dare yayi sosai lokacin dabarci ya
sake dauketa kamar jiya haka ta sakeganinta da
danliti. Babu bambanci da mafarkin jiya,ta farka
a firgice hankalinta ya tashi,gaba daya kanta
yayamutse tana jin muryarsa yana kiran sunanta
cikinkunnuwanta,shiya ta zuwa yatsunta,ta tashi
ta runtseido tamau!Tana fadin inna lillahi wa
inna ilaihir rajiun!Sannu a hankali ta daina jin
kiran. Ta makure a gadota rasa abinda ke mata
dadi a duniya,gab da asuba wani barcin ya sake
sace ta,yadda take zaune amakure gefen
gado.Malami ke tashinta ta bude ido tadube
shi,yace a zaune kika kwana anti? Da kyar
tatashi sosai ta zauna,wuyanta yayi mugun
rikewa,yakage,ta kasa motsa shi,tace ya aka yi
na tashizaune?Yace oho nima ynzu na tashi na
ganki a zaune. Ta jujjuya wuyanta tace,wash!
wuya na ya rikemalami ban iya motsa shi.yace in
kira momi? Tace aa kyaleta, yanxu zai warware
in na tashi,yana tsaye yana kallonta tana ta juya
wuyan har tasamu ya saki, ka yi alwala ne? Ya
ce aa . To jekayimana ka fito, ya wuce ya yayo,
ya dawo itama dashiga toilet, ta kama ruwa
tafara alwala, Sakeena! Tajian kira ta. Ta waigo
da sauri, bata ga kowa b, tayi jim, a tsaye
sannan ta ci gaba da alwala ta kare ta fito
taysallah. Wannan yinin tayi tunanin Dan Liti,
gaba 1mind dinta, ta koma fandogari. Har Anti
Amina ta lurabatab cikin sukuni. Yau da wuri Al-
Ameen ya kirawaya 8:30 ma bata gama yi b,
tana daki ta idar dasallar isha. Malami ya shigo
ya gaya mata yaya Al Ameen ya kira, takalleshi
up n down tace kace masaina zuwa.. Ya juya ya
fice, shi kansa da yake yaro,yaji mamaki , don
bai saba gani b, Da taji waya harrige rige sukeyi
wajen rcvng. Tay guntun tsaki ta tasorai bace ta
sauko falon suna ta hira da malami yanabashi
daria. Tayi tsaye, tana kallon sa, kafin yace gata.
Ya miqa mata , ta amsa ba fara'a, tace
hello.Yace Amincin Allah ya tabbata gare ki my
princess...Kai ma hak. Yau kuma yanga kike ji,
kika barni damamaki? Ko amarci ne ya fara tun
yanxu? Tayatsuna face tace " sallah na ke," Oho
yau na bugoda wuri ko? Na kosa inji ki ne my
wife.. Tayi far da eyez tace ka kyautah wa
kanka...... Banda ke? Watakila, banson gulma.
To yakike? Kalau, aa ba kalau b, kamar
sakeenata batacikin walwala, waya taba min ke?
Wa zaitabani kuwa? To ai ban saba jin ki haka b
my princess ko bakida lfyne? Lfy lau nake. Ina
shakku gaskia, karki boye minsakeena, gaya mi
meke damunki? Ta danyi shiru, hawaye suka cika
eyez dinta,murya na rawa Lnibansani ba Dr.
Kayimin pryr raina yana baci nekawai"jikinsa yay
sanyi karki damu mama in shaAllah zan miki,
kinsan Dan Adam ajjizi ne, 9 yake baicika 10 b,
dole wata rana kaji ba daidai b. Haka lyftake,so
karki damu, ok? Nagode, ki manta kawai. Kinsa
wani abu? Kishin kishin naji wai skul dinnansuna
son rike ni, kamar yaya? Wai in zauna anan
inyimasu aiki.... Banjin zan iya ko da sunyi man
tayin.Don me? Ke kingoyi baya ke nan. Baci
gaba bane? Niban ga wani abu a cikin sa b.... Ni
nagani, wayau nekawai suke mana , a haifi
mutum a kasar sa, yayi girma ya gama whlar
studyng a kasarsa, tashi 1 watakasar ta gwada
masa money ya bar kasar sa. Alhalinal umar sa
na matukar buqatar gudunmuwarsa. Ni banda
sha'awar wannan, na fi so inyiwa kasa ta bauta,
badon kudi b sakeena , sai don tai mako ga
masubukata kin gane????? Uhm.... Uhm?? Haba
sakina ta, na ce ki sakiranki, ko naji dadi, kina
so in shiga damuwa ne? Tayihamma,gaba 1 taji
slp ya rufe mata eyez, yayi yardariya ya ce,
wannan uwar hamma, ai sai ki cinye ni,barci
kike ji? Wlh kuwa gaba 1 eyez dina sun rufe,.
Aikuwa ya kamata ki kwanta kiyi slp, in kyale ki
ko? Tadan nunfasa, kuma bana son kwanciyar.
No pls kijeki kwanta, Allah na yafe, ok? Sai
2mrw zankira inAllah ya yarda, sai da 2mrw ko?
Shi ke nan. Ki fa yibarcin, kar ki tsaya tinkng
komai. Ta amsa,to. Gudgirl I lov U my prncess. A
hnkli ta ce Me too... YaceSo much? Tace So
much! Murmushin sa ya kari yace to ayi slp lfy.
To. Ta fadi tare da aje kan wayar ta jimatsaye
tana tunanin iska, ta tako ta dawo daki
9pmdaidai. Malami har yayi slp. Bata sauya
komai jikin taba ta kwnta,shirun da tayi, bawai
Al amin take tnkba , fandagori kawai take
tink,can mind dinta ta koma,tana matukar son
ganin Dan liti. Yayin da shima al amin yake
zaune bisa bed yana tinkn yanayn sakinarsa take
ayau,don hka ya roki Allah daya yaye
mataabinda ke bata mata rai. Dukkansu sun raba
darebasuyi slp b... Yau mafarkin mama ya sauya
salo,domin a yau kiran da ya kwala mata yasa ta
tsayacak,! Tana kallon sa, tafiya zakiyi ki
barni??? Ta kada Kai.. Ya ware hnds dinsa yace,
Kizo nan don Allah. 2acigaba da kallonsa bata
motsa b, kizo mana nace,! Taruntumo da gudu ta
rungume sa, ta fasa kuka, ya riqeta tamau! Yna
fadin, ko ke fa? To kidaina cryng, donbanga
dalilin yin sa ba... Ya dago fuskarta yana
sharemata hawayen, ya isa haka, ki daina bata
hawayen ki? Kuka take yi sosai, tana kwance
rashe rashe bisagadon, ta jima tana kuka kafin
ta yunkura ta tashizaune,taja jikinta,ta jingina
da akanta kan gado tacigaba da tsiyayar hawaye
ana sharewa. Bata sakekomawa barci ba har aka
kira asalatu. Ta sauka tafada bayi tayo alwala ta
bada faralo,ta zauna shiru bisa sallaya.
Zuciyarta tana azalzala mata son ganinDan
liti...... Muryar malami taji yana fadin, har
kinkinyi sallah ne anti? Shine baki tashe ni ba?
Tadanruntse ido, ta bude,yi hkri malami,na
manta ne. Je kayo alwala,. Ya wuce bayi yayi
alwala ya fito yayisallah. Yana idarwa, wanka
yaje yayo yayi shirin skul. Bisa gadonsa ya
koma ya kwnat.jim yayi shiru cankuma ya dago
kai yace anti kifa tashe ni karki manta.Tace
bazan manta ba,ya koma ya kwanta.ya
bartazaune bisa sallaya. Anti Amina ce ta
shigo,karfebakwai da rabi wai barci ne ya dauke
ku? KaiMalami!... Ta bubbuga shi,yayin da
mama tay firgigi ta bude ido, skul din fa? Ka
kwanta kana ta slp?? Yasauko a firgice yace ,
nace anti ta tashe ni fa! NAGA ALAMA BAZAKU
IYA KARANTA WANNAN BAKIN CIKIN BA, gara
kawai a samu wani book, INA jiran ra'ayin ku,
masu so a cigaba suyi COMMENTS masu son
sabon littafi suyi LIKE.