Complete Hausa Novels

Farrah Complete Hausa Novel

Reading file: FARRAH COMPLETE.txt

Chapter 22 of 32

EPISODE 2️⃣3️⃣

The Wellness by Oriflame routine is designed to support your intake of protein, dietary fibre and micronutrients, in the right proportions, every day.

A = ACTIVATE
Set the foundation of your routine with vitamins, minerals and omega-3 fatty acids. These are needed every day to fill the nutritional gaps in your daily diet. You find them in our Wellness Multivitamin and mineral.

B = BUILD
Boost your defence system, and even build it over time, with the amazing Astaxanthin, together with bilberry extract and protein. Antioxidants are your active defense against environmental pollutants and help your body cope with a hectic lifestyle. Proteins help your body build new cells. You can find these in our Wellness Shakes.

C = CUSTOMISE
We all have individual needs depending on our age, lifestyle and general wellbeing. That’s why you should top up your routine with additional nutrition to feel and look your best. This includes using products like our Wellness soups and bars.

Meanwhile lemme all introduce you to supplement da I think we be solution to all problems na jikinmu.

Dukanmu nan munsan ORIFLAME is a reputable brand da aka sansu wajen wallafa abu mai kyau yanzu sunyi Supplement mai suna WELLNESS by ORIFLAME.
Kowa dakuka gani mata da maza muna bukatan some mineral, vitamins da sauransu dazai helping jikinmu da system namu, supplement dazai karama defense mechanism namu karfi to protect us from ciwake ciwake, sanan dazai taimakawa organs dinmu yin aiki da kyau.

Idan kina shan wellness zaki kyau, zai karamiki lafiya, zai taimakawa organs naki sosai, akwai so many reviews, wata tace tunda tasha wellness tafara samin ruwa gaba, wata tace skin nata yay fresh, wata tace gashinta daya karairaye yadawo, wata tace nonon ta yakara cikowa, banda haka wellness na bada kariya against cancer.

Wellness is the best supplement da ake dashi right now wanda kasashen duniya da dama sukasha kuma suke recommending ma mutane.

I have good news! Supplier wellness dinan tace namuku albishir duk wanda yasaya akwai FREE DELIVERY to duk inda kake a Nigeria. You will never regret buying wellness, zaki saya sanan kisaima maigida nshi shima.
Don sayan wellness contact her by clicking on this link;
wa.me/+2349133427208
***************************
EPISODE 2️⃣3️⃣
Bala’in faduwa gaban Layla yayi ganin yanda idanun Zayn sukayi ga hannunta dahar wani kalan zugi yafara sabida yanda Zayn ya damke hannun, fizge hannun nata tayi da karfi sanan tawuce inda ya jefar mata da riga ta dauka tasaka sanan tazo tafice saida kofan yarufe sanan Zayn ya kalli Farrah dake kuka sosai har lokacin kokarin kwace kanta daga jikinshi take, hannunshi yasa yacire hannunta daga kan fuskanta cikin dan kakkausan murya yace “ke open your eyes” juyarda fuskanta gefe tayi dasauri tana kokarin fizge hannunwanta daga nashi amman takasa, dan gajeren tsaki yaja yanajin yanda take kuka aranshi cikin dan fushi ya jijjigata yace “why are you crying now meke saki kuka eh”? Yasake shiru yana kallon gefen fuskanta da shine saitin fuskanshi dan tsaki yaja ahankali yace “what’s your business with my life? Damn it stop crying Farrah!” Yadaka mata wani uban tsawa da har zuciyanta saida taji yakada tsayawa kukan datakeyi yayi chak, sakin hannayenta yayi cikin kakkausan murya yace “kalleni nan” juyoda fuskanta tayi ahankali sanan gently tabude idanunta kaman mai tsoron bude su ta daurasu akan fuskanshi idanun har sundanyi ja gashin idanun sun tattare da hawaye, wani irin yirrrrr yaji data kalleshi da moist idanun, ajiyan zuciya tasauke ahankali dayaji saukanshi akan fuskanta, dan kauda fuskanshi yayi kadan sanan yadawo da fuskan yadaura idanunshi kan nata daure fuska yayi yace “goge fuskan ki” hannunta takai ahankali ta goge fuskan tass kaman yanda yasata, yatsine fuska yayi yakalleta from head to toe yace “go” juyawa tayi dasauri tafice daga gym din hartana neman tuntube, har lokacin jikinta yaki dawowa daidai, sai ganin abinda tagani just now take Ya Zayn yakama ma Layla dasuka gani jiya tareda kishiyan Mami nono zaisha, wani kalan abu taji acikinta yataso mata tareda tsigan jikinta kaman zatai amai yamata wani warrrrrer ajiki, dasauri tabude kofan dakin Mami tashiga, Mami dake cikin kitchen jin anbude kofa tace “Farrah kene” ahankali tace “eh Mami” daga kitchen din tace “yauwa imaza jeki shirya mutafi saloon nafito miki da kayan dazaki saka” ahankali tace “to” sanan tawuce sama.

Saida yaga fitanta sanan yawuce yakoma kan machine din dayake kai dazu ya zauna, dan gajeren tsaki yaja sai kawai yatashi safan hannun yacire ya Yar awajen ko kashe wakan gym din baiyiba yafito yawuce side nashi wanka yayi dagashi sai towel a waist kawai yazo yafada gado sai bacci yau tun asuba yatashi.

Yanda tafado falon da bala’in fushi yasa Hajiya Mariya tace “ke lafiya”? Cikin tsananin fushi tace “Mommy wai waye wanan yarinyar tajiya”? Dasauri tace “Meya faru tell me everything”? Cikin fushi Layla tace “son ta yake Momny” kwashewa da dariya Mommy tayi sosai tace “so anya kinsan abinda kike fadi kuwa Layla? Zayn ne zaiso mutum, please leave that just tell me what happen” fadama Hajiya abinda yafaru daga farko zuwa karshe tayi Hajiya ta jinjina kai tace “Alhaji ne wai yay adopting yarinyar, kinsan tun farko farkon aurena dashi babu kalan rokon Alhaji da banyiba kan muyi adopting yara yaki Amma kinga ai yanzu yayi dayayi kuma sai yabawa favorite wife dinshi, komi yakusan zuwa karshe wannan alkawari, just duk yanda zakiyi kiyi kisami kan yaro ya yarda dake kinjini ko that’s my only hope” Gyadamata kai Layla tace “don’t worry Mommy I can do anything for you” murmushi tayi tace “jekiyi wanka kizo kiyi breakfast” tashi tayi tawuce sama.

Wanka fara tayi tafito daure da towel kowani motsi tayi sai abinda yafaru dazu yafado mata, inda aka mata aiki Mami harta cire bandage din jikinta nada kyau sosai, shiryawa tayi cikin kayan da Mami ta ijiye mata Riga da skirt na atampa ja, sun bala’in amsanta, gyale tadauka a hannu tafito afalo tasami Mami tana waya ganin Farrah saida tai murmushi tace “kinyi kyau sosai My baby Oya muje” tashi tayi tacigaba da wayan datake suka fito mota suka shiga bodyguard din Mami yajasu wani babban saloon Mami takaita, wanke Mata gashinan dakeda uban dauda akayi, akai blowdrying sanan Mami tasa aka mata kitso shuku yan kanana ana mata pedicure itadai Farrah kallonsu kawai take, tsaf aka gama komi tsayin gashinta har waist, ciki suka wuse Mami tasa aka mata facials sanan tasayamata wani set na cream da sabulun wanka damai spa din tamata recommending, Mami tasa aka mata waxing nanne fa Mami na zaune a falo amman taji kukanta dan murmushi Mami tayi, saida aka gama sanan tafito idanunta sunyi zuru zuru, Mami tace “sannu” akunyace ta gyadama Mami kai sanan suka fito ita kanta jin jikinta tayi daban, wani babban super market sukaje, shopping Mami tamata na mamaki Farrah sai kallonta take bata taba sanin akwai wayanda basune suka haifeka ba amman zasu soka da zuciya daya ba sai awajen Mami saida suka gama aka loda komi a mota sanan suka shiga Mami tace “kinaso kiga Mama na”? Dasauri ta gyadama Mami kai tace “eh Mami” dan murmushi Mami tayi tace “itama ta kosa taganki yanzu zamu”.

Tunda suka shigo layin su Grandma take kallon layin shi layin ba kaman na irinsu Mami bane, parking sukayi a kofar gidan aka bude musu kofa, kayan da Mami tasayama gidan Bodyguards suka shiga fitowa dashi itakuma Mami da Farrah sukai ciki, da sallama suka shiga gidan, Mama ce tafito daga dakinta tana rikeda charbi a hannu tace “oyoyo oyoyo oyoyo jikalle na” wani kalan murmushi Farrah tayi ganin yanda tsohuwan dake kama da Mami sosai tamata oyoyo har gabanta Farrah taje ta tsugunna ahankali tace “ina kwana Mama” dasauri Grandma tace “tashi tashi Allah kadai ake tsugunnamawa, Allah yamiki albarka taho muje daki” taja hannun Farrah suka shiga daki Mami kuma tai murmushi tana biyosu abaya, zaunar da ita Mama tayi akan kujera sanan tace “yau kaf Mutan gidan nan sun fita sunje bikin saude ni kadai bari nakawo miki abinci” dasauri Farrah tace “a’a Mama bari na dauko miki” “je uwar daka na zakiga kula ki dauko” gyadamata kai Farrah tayi da sauri sanan ta ijiye gyalenta kusada Mama tawuce dakin data tabbata nanne uwardakan kulan datagani tadauko sanan tafito takawo takara komawa plates data gani takawo, Mama tace “ci abinci iya cinki kinga Maman nan taki bata son cin abinci ita Zayn yabiyo” dan murmushi tayi tadan dagakai takalli Mami gani tayi Mami na kallonta, ahankali tace “Mami zakici abinci”? Gyadamata kai Mami tayi ahankali tanajin wani sanyi aranta Zayn baitaba tambayanta taci abinci ko zataci abinci ba yara mata daban ne kawai duk wanda Allah yabamawa yace Alhamdulillah.

Yanda Mami tace “eh” yasa dasauri tabude kulan tuwone da miyan karkashi dayaji nama da man shanu, fara zubawa tayi ahankali Mami dake kallonta tace “ki zuba mana tare” dagokai tayi takalli Mami saikuma tai murmushi sosai itama Mama dake kallonsu duka biyun murmushi tayi, zuba musu tayi sanan tadauka takai gaban Mami, saukowa Mami tayi kasa sanan suka faraci feeding Farrah tadingayi abaki har suka cinye, kwashe kwanukan Farrah tayi tafita dasu waje inda taga makwarara, kwanukan data gani na datti ta hada tass tashiga wankewa daga daki Mama tace “mekikeyi Farrah” “wanke wanke Mama” murmushi Mama tayi takalli Mami tace “Allah yabaku ladan abinda kukayi, sanan Allah yatayaku riko” murmushi tayi tace “Ameen” Mama tace “yanda kika taimaketa ubangiji Allah Ya taimakawa Zayn dinki haka Ya shirya dashi yakuma natsar dashi” murmushi Mami tayi tace “Ameen Mama, kin shanye magungunan ki” tabe baki tayi tace “nifa nagaji da shan magani fa Mami ki kyaleni” tashi Mami tayi dasauri tashiga uwar dakinsu gaban drawer tana dudduba magungunan Mama tace “Mama wai mesa bakishan magani, sune fa zasu dinga controlling da regulating BP dinki eh Mama dan Allah kidinga sha” naji.
Sai gab da magrib sukabar gidan Mama, har atampa Mama tama Farrah kyauta dan Farrah ta gyara gidan tsaf ta gyara dakin Mama ta share harda cire duka yanan gidan dana zaure sai dariya suke itada Mama suna tambayanta ya akayi tacire yanan Xauren nan abokanen Zayn ne wai tsoronsu yake da gizogizo, babu kalan labarin tsorace tsorace Zayn dabata jiba, suna kaiwa gida sukai Magrib anayin isha’i Mama tasata tai bacci dan gobe monday zaa kaita school.💫 FARRAH 💫

✍🏻M SHAKUR

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.