Farrah Complete Hausa Novel
Reading file: FARRAH COMPLETE.txt
Chapter 11 of 32
EPISODE 1️⃣1️⃣
Cikin tsananin fushi dakuma tashin hankali Oga yace “Duk inda zaku shiga ku shiga kufito min da yaron nan, that boy life is our golden ticket to paradise” baisan ya akayi ba but jiyayi yasa hannu yakama hannun Farrah gam gam atsorace jin maganan da Oga keyi kirjinshi na bugawa dum dum dum! Ahankali Farrah takalli hannunta dataji ya kama yarike kafin gently tadago manyan idanunta takalli fuskanshi, ko kadan hankalinshi baya kanta fuskanshi na kallon sama dan asaman kansu yakejin maganansu gani yake kaman zasuyi missing step kawai su taka reshen mangwaron su fado cikin ramin dasuke su gansu su kasheshi, zufan dakebin gefen fuskanshi ta kalla dan murmushi tasaki tunda tai wayau yaune rana na farko data taba haduwa da namiji matsoraci, ko Baffa dayake nan siriri baikai Inna kiba ba baida tsoro, rashin mutuncin yake surfafama Inna dudda idanma duka ne zata iya zauneshi ma amman baya tsoron ta balle uban kowa, su Moddibo dabama sukai wannan girma ba suma basuda tsoro amman jibi wanan katon yanda jikinshi ke rawa, tabe baki tayi tadauke kai batare data cire hannunshi daga kan hannunta ba ta jingina da bangon ramin hankalinta kwance ta lumshe idanu dan wani kalan baccin gajiya takeji ko minti uku batayi ba bacci yay awon gaba da ita azaunen, minsharin dayaji taja yasa dasauri yajuyo da kanshi ya kalleta bacci take azaune bayanta jingine da bango tadan dukar da kanta hakan yasa bama ya iya ganin fuskanta sai saman hulanta, mamaki ne ya kasheshi how can she sleep comfortably acikin rami akan wanan dattin? Yana nan inda yake yanajin duka neme nemen shi dasukeyi aka wani kalan tsuge da ruwan sama dayasa yaji sun kwasa dagudu, kalan azababben kishin dayakeji yasa yabude bakinshi ahankali yanajin wani iri but ji yake idan baisha ruwan nan ba zai iya mutuwa, ruwan dake tsiyaya daga ganyayyakin nashiga bakinshi yana hadiya ahaka, saukan ruwan dataji kan fuskanta yasa tabude idanunta ahankali kafin taja hulanta baya tadago kanta ta kalleshi ruwa na fesowa a fuskanta shima kallonta yake, saikuma chan yamaida bakinshi yarufe ganin kaman yanda takeshan ruwan yake kallo, dan yunkurowa kadan tayi taja reshen gefe ta lelleka ganin basanan yasa ta matsar dashi gefe tafito sanan ta tsugunna gaban ramin tamikamai hannu ahankali yakalli hannun nata sanan gently yasaka mata nashi aciki yafito ahankali da taimakonta, mangwaron su ta katse daga jikin reshen sanan tamikamai guda daya kallon mangon yayi sanan yakalli reshen da bolan da aka rufe dasu yanajin amai na zuwan mai tuna ruwan dayasha amman aman yaki zuwa sanan ya girgiza mata kai, maida mangwaron tayi tarike tafara shan nata dan rawa yafara na sanyi dan ruwa ake mai karfin gaske ita ko ajikinta, tafiya tafara da sauri shima yabita yana tafiya da sauri har zuwa gaban dutsenta hawa sukayi sanan suka shiga kogon, waje tanunamai hakan yasa ya zauna akasan ahankali fita gaban kogon tayi sai yanzun nema gabanta yafadi duka tumakan su Shanu daya kawai tagani awajen yana yawo, wani irin kalan mugun faduwa gabanta keyi, dawowa ciki tayi ta zauna sanan ta kalleshi kaman yanda yake kallonta batace mai komi ba.
Ahankali yana kallonta yace “do you have phone please”? Kallonshi ta tsaya tanayi kuri hakan yasa gently yace “kinada waya”? Girgizamai kai tayi alamun batada shi, shiru yadanyi saikuma yasake dago kai yakalleta still tana kallonshi murya chan kasa yace “wani gari ne nan?” Da demonstration tagayamai ganin yanda ya tsaya kuri yana kallonta bai gane abinda take cewa ba yasa tamai alamun tana zuwa tamike tsaye tafice daga kogon bayan riganta yabi da kallo duk jini yabata dutsen da aka buga mata, sauka tayi daga kan kujeran ta kwasa da gudun bala’in sa’i karkaransu ana ruwan nan, direct gidan su Shafa tayi tana shiga taga Shafa ita kadai a kitchen tana soya manja zatai girki, ganinta yasa Shafa tasaki baki tace “yanzu da girmanki kika shiga ruwa kika jike haka Kurma?” Karasawa gaban Shafan tayi tasa hannu ta dagata daga kan kujera sanan tafara gayamata komi a kurmance Shafa nabin labarin tundaga farko har zuwa yanzu, saida tagama tass sanan Shafa ta zaga ta bayanta riganta ta daga ganin taji ciwo sosai yasa tace “waike Farrah maisa bakijin…..” Farrah bata bari takarasa magana ba ta girgiza mata kai sanan tamata alamu itadai tabata wayan, jim Shafa tayi tana kallonta tanason Farrah sama da tunanin Farrah but bataso Farrah taje tasa kanta a matsala, wucewa tayi ta shiga dakin Baban su, wata tsohuwar waya taciro wayan ma akashe tabama Farrah karba Farrah tayi tana murmushi sanan takama hannun Shafa suka fice daga gidan, suna fita ta tuna yanda yakeji tadawo cikin gidan dasauri dakin shafa tashiga ta dauki bargon Shafa dake kan gadon tafito Shafa tabita da kallo sanan tai shiru, gudu sukahauyi nan da nan sukakai wajen, shiga ciki sukayi yana zaune inda Farrah ta barshi sanyin gaske yakeji ya kankame jikinshi warware bargon Farrah tayi ta lullubamai ya sauri yarike bargon sanan tamikamai wayan da Shafa tabashi karba yayi dasauri yana kallon wayan yana dannawa ganin akashe, kugu Shafa tarike tace “kaga Farrah Kurma ce, kuma marainiya ce batada Baba batada Mama, yarinyar nan dakake gani batada gata akauyen nan wahala take, Allah ne kadai gatanta koma wa zaka kira ka kira sabida kafita daga hannunta banson kasamin kawa a matsala” tunda take maganan yake kallonta harta gama, kallon Farrah yayi da itama kallonshi take yanzu daman kurmace, juyowa yayi yakalli Shafa ahankali yace “inane nan?” “Kauyen kudiri” tafadi kai tsaye, murya chan kasa yace “awani gari”? Ahankali tace “garin adamawa” kunna wayan yayi cikin ikon Allah ta kunnu saura one bar, ga service ma kara daya itama rawa take, number Papa yasaka yay dialing yaji ana you have one minute remaining shima ana maganan tana breaking wayan yafara ringing dauka akayi yaji muryan Mami hakan yasa dasauri yace “Mami” muryanta na breaking sosai tace “Hello, Hello” dasauri shima yace “Mami, Mami, is Zayn” duk tsayawa kallonshi suke yanda yake maganan yana fama da wayan yakaita baki yakaita kunne, Shafa tace “ka karamata volume haka Baba keyi idan kawu yakirashi daga binni” da sauri yasa a speaker shima da kyar yagane sabida bai iya amfani da wayan ba “Zayn is that you, muryanka nakej………”. Muryan Mami shi yafito ras awayan daidai wayan ya katse kati yakare, gyadama wayan kai yayi ahankali saiga hawaye sharrrrr yazubo daga idanunshi, ware idanu daga Shafa har Farrah sukayi suna kallonshi, dama kattan maza na kuka, ringing wayan yashigayi hakan yasa dasauri yadauka yasa a speaker wanan karan murya Baban shi yaji kaman ma kuka Alhaji yake dan baya iya magana da kyau yace “Zayn dina kana ina are you okay”? Girgiza kai yayi kaman yana gabansu cikin tsantsan shagwaba yace “I am so scared Papa, please come and get me, I am scared” cikin wani kalan lallashi da so naban mamaki Alhaji yace “stop crying where are you tell me zanzo na daukeka” ahankali yace “kauyen kuduri adamawa state” “adamawa state Innalillahi we are coming with choppers gamunan, kafin nakaraso I am calling the governor na Adamawa stay with this phone okay, wherever you are they’re going to provide you with security, I am coming for you Zayn dina, your father is coming okay” gydamai kai yayi ahankali wani kalan zazzabi na rufeshi jin muryan iyayen shi, suka katse wayan hannunshi yasa akan fuskanshi ya share fuskan nashi tass, sanan ahankali yadago kanshi yakallesu hawaye yagani sun taru a idanun Farrah sosai tana kallonshi, hannunta Shafa takama tace “wuce mutafi tunda za’azo daukanshi wayan idan zai tafi ya ijiye mana anan zamuzo gobe mu dauka” dan kallonshi Farrah tayi kaman yanda shima yake kallonta kafin ahankali tafara tafiya tanabin Shafa dake janta suka fice daga kogon.
This is not a free book chat me up directly by clicking on this link;
wa.me/+2347012181461💫 FARRAH 💫
✍🏻M SHAKUR
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.