Complete Hausa Novels

Farrah Complete Hausa Novel

Reading file: FARRAH COMPLETE.txt

Chapter 16 of 32

EPISODE 1️⃣7️⃣
Ganin ko motsi batayiba yasa yay dan gajeren tsaki yaduko yana kallon fuskanta, hannunshi yakai ahankali yadaura kan wayan yaja cikin bacci itama taja tarike wayan gam tanadan gyara yanayin zaman datayi cikin baccin taredayin hamma, fuskanta ya tsaya chak yana kallon yanda take hamman tareda yin dan nishi ahankali, she looks super cute baisan mesaba hakanan kawai yatashi batare daya karbi wayan ba yawuce yafita daga dakin zuwa motan shi bodyguards biyu biyedashi, shiga motan nashi yayi da Dad yasa aka kawomishi danshi yafita danashi dasukazo dashi, zamanshi yayi cikin motan tareda lumshe idanu, anytime yayi yunkurin lumshe idanu mutanen nan yake gani, ko jiya is because Dad ya kwana dashi ya iya yay bacci, the whole experience yadameshi yahanashi sakat, dan tsaki yaja yasa hannu a aljihun shi yadauko kwalin taba daya yazaro sanan ya kunna da sauri yashiga sha tareda kwantar da kanshi jikin kujera, he’s feeling so dull the only thing dayake bukata yanzu is to be extremely high and have a wild sex.
Kiran sallan zuhur akayi a masallacin dake nan cikin hospital din, dan yatsine fuska yayi kaman yay ignoring karyaje saikuma ahankali yadan yunkura yana tunanin maganan Mami “this is a second chance Allah yabaka Zayn” bude kofar motan nashi yayi ahankali yasauko dasauri bodyguards dinshi suka tsaya agabanshi, wani kalan daura hannu yayi agoshinshi cikeda takaici yace “for f**k sake i wanna go to the mosque” kallonshi duka bodyguards din sukayi cikeda mamaki, dan gajeren tsaki yaja ya bangajesu yawuce mosque abinshi suka bishi dayake su arna ne gaban masallacin suka tsaya kaman an bishiyoyi suna jiranshi.

Shigowa dakin Mami tayi wajajen zuhur ganinta tana bacci kan kujera rikeda wayan Zayn yasa tadan ware idanu, Zayn haryasoma jin maganan tane wanan daya bama yarinyar wayanshi tarikemai does that mean yama yarinyar godiya, dan murmushi tayi takaraso ciki basuda wani kaya hakan yasa kawai after dress daya sayama Farrah tadauko tazo inda take tabata tayi tace “Farrah Farrah” gently tabude idanunta takalli Mami, murmushi Mami tayi tace “tashi mutafi gida kinji” gyadama Mami kai tayi sanan tamike tsaye ahankali, abayan ta warware da taimakon Mami ta iya daga hannu Mami tasa mata ta makala boturan sanan takai hannunta ta gyaramata hulan dake kanta daya zamiye baya tana kallon gashinta Mami tace “kikaji sauki sosai zan kaiki saloon a gyara gashin nan ko” ahankali tace “to” ita kanta saida tai mamaki datai magana this time bai breaking ba Mami ma murmushi tayi tace “masha Allah, Beautiful Farrah is talking now, muryanki dadi Alhamdulilah” handbag dinta Mami tadauka bayan tahada komi nata ciki sanan tabama Farrah wayan Zayn tace “rikemai wayanshi mukaje sai kibashi” karban wayan tayi sanan suka fito tareda Mami ahankali take tafiya sai kallonsu ake, duk Dr dazaisa Mami saiyace “is she your daughter Mrs Ganuwa she’s so Preety” murmushi Mami take tana cemusu yes, waje suka fita suna tafiya zuwa parking space daidai shima Zayn nafitowa daga masallaci, kallo daya Mami tamai tadauke kai amman ba karamin Dadi taji ba, hanyar motanta tayi dake kusada motan Zayn, takalli Farrah dake tsaye kusada ita tace “ba Zayn wayanshi kizo muje” Mami tai maganan tana shiga bayan motan, ahankali Farrah tajuya, ganin Zayn harya shiga bayan tashi motar yazauna yasa takarasa wajen ahankali tadaure fuska dan bata manta stupid din daya kirata dazu ba, ganinta tsaye gaban motanshi yasa yadan kalleta kaman baiso yakalleta, daure fuskanta tayi tamau sanan tamikamai wayanshi dake hannunta, kallon hannunta yayi dake rikeda wayanshi sanan yadan kara kallon fuskanta, ganin kallonshi take still fuskanta adaure yasa ahankali kaman baiso yakai hannunshi zai karbi wayan, haryasa hannunshi kan wayan zai zare daga hannunta tawani fizge wayan ta nakamai wayan akan kujera sanan ta watsamai harara a idanu tajuya fuuuuuu tawuce tashiga motansu bodyguard din Mami yarufe motan yakoma gaba yana tada motan Mami kuma hankalinta nakan wayan datakeyi.
Tsayawa chak Zayn yayi da hannunshi dakenan a position din dayake na karban wayan sanan yakalli wayan data ijiyemai kan kujera, wani kalan zafi yaji aranshi daya kasa daurewa yadanyi giggling cikeda mamaki yace “Wowww!” Bodyguard dinshi dake tsaye gaban motan ya kalla sanan yanuna kanshi yace “did you see what that village little gurl did just now?” Saukar da kanshi kasa bodyguard din yayi dasauri, cikin fushi Zayn kaman bodyguard dinne yamai laifi yace “shut the door get into the damn car and drive me home motherfucker!” Ya dannamai rude rich kids zagin nan kirjinshi na tafarfasa.

“Just tell me what exactly kikeso nayi? Eh” cikin tsantsan masifa tace “you are the root of this whole mess damuka shiga, inda ka yarda muka bama Oga order akashe dan iskan yaron nan da tuni yatashi aiki” wani kalan dan dariya Uncle yayi more of dariyan dazaka kira da dariyan takaici, saida yayishi ya koshi sanan yadago idanunshi dasukai jajir yace “tayaya zan taba bada order akashemin nephew? How do you guys even think zan iya haka for god sake dandan yayana wanda nake uwa daya Uba daya dashi how?!” Yay ihu, wani kalan mugun tsaki Hajiya Fatima taja, Hajiya Mariya da takaici yagama kasheta tace “thank you Fatima da wanan tsakin, wlh ko kadan bakasan ciwon kanka ba, kace nephew? Nephew din dabaisan darajan kaba, baisan amfanin ka ba all u are to him is dan boyi boyi” wani yunkurowa Uncle yayi daga kan kujeran dayake zaune kaman zai mari Hajiya Mariya, Hajiya Fatima tace “dukanta zakayi, yo karya tamaka, kai har kanada bakin kace dandan yayanka uwa daya Uba daya, to wlh bari kaji in fadamaka indai har aka ake yaya aduniya to Allah karya bani irin yayanka na yamaida ni dan aike, ta yanda zakasan ko tunanin ka bama yayi yatashi gabaki dayan dukiyan shi yabawa danshi batare daya baka ko kwabo ba” baki Hajiya Mariya tabude zatai magana Uncle da idanunshi sukai jajir yabuga table tareda daka musu tsawa yace “enough! We are here to discuss solution idan lecturing dina zakuyi ne sai kuyi kugaji, ni abinda nakeso kudin Yaya nakeso gabaki dayanshi, wanda nake gani idan nasamu zan iya rabamana shi gida uku, kowa yadauki daya, inda kun yarda ahakan na tabbatar da mutanen nan da tuni sunsa Yaya yarubuta komi yabasu takardan in exchange ma rayuwan Zayn babu abinda bazai iyayi akan Zayn ba, amman ku kukaki ku duka biyun kukeso akashe Zayn sanan akarbe kudi, yanzu dai kunsan an kama Lamba ko, luckily for us Oga yay assuring nawa baisan komi kan mu da muka basu kwangilan ba, so kozai fadi wani abu idan yaji azaba saidai kansu bamuba, so for now asirin mu arufe, he’s demanding abashi kudin aikin shi koya fasa kwai, sai magana tabiyu what’s the way forward yanzu kowani security na gida da waje Yaya yayi doubling komi, tayaya zamu cimma burin mu” jaka Hajiya Mariya tabude taciro wasu bandir bandir na 100 dollars ta ijiye guda biyar kan table tace “nidai ga payment dina, banda wata matsala data wuce Zayn, nasan kudi baya isan mutum aduniya mukaci nasara muka sami kudin Alhaji inaso, amman Zayn dai sainaga bayan yaron nan aduniya, duk sanda na ganshi nakanji wani abu ya tsayamin awuya na bakin tsanan shi uwa na lumamishi wuka aciki ya mutu nakeji, I think the easiest way dazan iya kashe yaron nan is da taimakon diya mace tunda shi Allah yayishi bunsuru ne” wani dan murmushi Uncle yayi yace “aikam kinada aiki, Zayn abaiban mutum ne dazakiyi shekaru aru aru baki gane kanshi ba, miskilin mutum ne na karshe, haryau banga wacce Zayn yakeso aduniyan nan ba, kowace mace yasamu kawai kawad da sha’awan shi yakeyi da ita yabarta anan, I believe ki chanza plan” wani kalan murmushi Hajiya Mariya tayi sanan takalli Hajiya Fatima tace “kin tuna Layla Fatima”? Wani kalan makirin murmushi Hajiya Fatima tayi tace “natuna ta” Uncle dabai gane me ake cewa ba yace “waye kuma Layla”? Murmushi sosai Hajiya Mariya tayi ta gyara zama tareda wani kalan juya kujeran datake kai tace “let’s just say Layla is a girl I picked on from the street lokacin iyayenta na kangin talauci, infact irin buzayen nan ne dasuka zo from chadi, suna bara kan titi, long story short I sponsored education nata a England ta karanta Mass com, yanzu haka tadawo nasan tanama gida tana jirana, iyayenta sun mutu I am morethan iyaye awajenta, bantaba ganin yarinya mai kyau kaman ita ba, kowaye Zayn yayi kadan yay resisting yarinyar nan, I will use her to get to throat din Zayn” tabe baki Uncle yayi yace “good luck with that” yasa hannunshi ya tattaro kudaden da Hajiya Mariya ta daura akan table din yace “bani kudin ki Hajiya Fatima” itama same amount da Hajiya Mariya ta ijiye ta ijiye Uncle ya tattara ya kwashe ajaka sanan yatashi yana rataye jakan yace “good luck Ladies, do your path while I do mine” yawuce yafita daga dakin, juyowa Hajiya Fatima tayi tace “are you sure Layla zata iya aikin nan karyazo instead of tasamo miki throat na Zayn, Zayn ne zai sami throat nata you know what I mean just look at Zayn, yaron nan yahadu my god, ga kyau ga gayu ga body da mata keso ga shagwaba” wani kalan murmushi Hajiya tayi tace “bakisan waye Layla ba saisa kike magana haka” dariya suka dan yi, Hajiya Mariya tace “I want to see Mami tai kuka na bakin ciki kaman yanda ta kwacemin miji na, i want her to suffer tai experiencing pains danayi arayuwan nan ta dalilinta, kiri kiri yanzu idan Zayn na bukatan Alhaji zai hakura da Kwanan mu yaje wajen danshi, muyi kishi da Zayn muyi kishi da uwarshi, jiya adakina yake amman sabida wanan wayward son of his na tsoro ya kubuta yaje ya kwana dashi, I hate hate extremely hate that drug addict yaron nan nashi” tabe baki Hajiya Fatima tayi tace “ni wlh da Allah yabani d’a irin Zayn gwara ma na mutum nan haihu ba, babu kalan kwayan dabaya sha, tun kafin ya balaga Nany shi nakeji take gayama ubanshi takama shi da mace, yaro haka har abin sone” “saisa nake addu’a Allah ubangiji karya shiryashi yakare haka a wulakance ja’irin yaro, tashi kiwuce kafin nima nafito yanzun nan kada aga duk mun dawo thesame time, ni tausayi ma amaryan shi Mariya kebani” ta kwashe da dariya tace “tunda Zayn yadawo billahillazi Alhaji baimasan yanada wata Amarya ba” tashi Fatima tayi tace “shag ya manta da ita, kinji Bari na wuce saikin shigo kema” key motarta tadauka tana tabe baki tace “mu sauran matanshi mune bamu da bodyguard, Maman dan iskan danshi tanada shi hakama danshi” dan dariya Hajiya tayi tace “karki damu komi yazo karshe” wucewa Hajiya Fatima tayi tafice wata arniyan mota tashiga taja tabar gidan dasuke ciki wanda yake karamin sabon gida, almost one hour sanan itama Hajiya Mariya tafito tashiga tata motar tabar gidan.💫 FARRAH 💫

✍🏻M SHAKUR

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.