Complete Hausa Novels

Farrah Complete Hausa Novel

Reading file: FARRAH COMPLETE.txt

Chapter 15 of 32

EPISODE 1️⃣6️⃣
Dudda yana sanye da black glasses bata ganin kwayar idanunshi amman wani kalan cika mata idanu yayi gashi yana wani kalan kamshi da takeji kaman kada tasakeshi tunda take aduniyan nan bata tabajin irin kamshin dayakeyi ba Subhanallahi kamshin dadi, ganin yanda yabata rai yana jiranta ta sauka daga jikinshi yasa ahankali tashiga dagashi tana satan kallon lion din dataga yarike a hannunshi, komawa gefen kujeran tayi ta nannade kanta cikeda tsoro tana kallon hannun nashi dake rikeda lion din sai yanzu ma taji inda aka mata dinki namata ciwo, tashi Zayn yayi ranshi bace, kayan jikinshi ya kalla ganin yanda suka yamutse dudda bawani yamutsewan kirki bane amman jiyayi ranshi yabaci kallon Farrah yayi da itama daidai lokacin tasaci kallonshi wani dan iskan tsaki yaji. “Mtswwww stupid girl” yafadi ahankali ware idanu Farrah tayi jin yazageta bata wani jin turenci but tasan stupid tun a kauyen su wucewa yayi fuuu yafita daga dakin da teddy a hannunshi daidai bodyguard din daya aika siyomai taba nadawowa teddy yamikamai cikeda masifa yace “donate this teddy to children ward, apparently the stupid girl na tsoronshi” yay maganan yana fizge kwalin tabanshi yawuce waje jikinshi har tsuma yake yakosa yasha taban.

Shigowa dakin Mami tayi ganin Farrah zaune kan kujera yasa tace “Iyye kin sauko”? Kai Farrah tadaga zata gyadama Mami, Mami tai mata kallon no, hakan yasa tadan runtse idanunta tace “e……h” murmushi Mami tayi sanan yawo wajenta gefen kujeran ta zauna hannunta takama tace “nasan yanda kikeji, but idan zaki magana, relax, take it easy, kiyi maganan a sannu akuma hankali batare dakinyi tunanin komi ba, once kika koyama kanki kina amsawa da maganan nan da 2days zaki fara magana lafiya lau kinji” wanan karan bata lumtse idanu ba ahankali tace “ehhh” murmushi Mami tamata tace “ina Zayn, Dr shi na jiranshi” ahankali tana kallon Mami tace “f…….iiii…ta” “okay yafita waje, bari naje nakirashi muje ganin Dr, I am coming idan nadawo zamuje gida, zakije gidana”? Mami tamata tambayan cikeda so, wani cute smile tama Mami ahankali tace “eh” wucewa Mami tayi tafita daga dakin tana murmushi she so much love Farrah bama tasan mesaba.

Tana kaiwa gaban entrance din Zayn na zuwa wajen shima daidai yana yarda karan taban hannunshi wani kalan mugun kallo Mami tamai sanan kawai tajuya cus da mutane awajen binta abaya yayi zuwa office din babban likitan idanun wanda yake bature ganin Zayn yasa yau murmushi yace “Mrs Zayn I really like this your boy he’s so cute” murmushi Mami tayi tana kallon Zayn dako gaidashi baiyiba yawuce yay zamanshi kan gadon duba patient, tashi Dr yayi yazo yacire plasta idanun yana kallon idon yace “can you see me”? Kallonshi Zayn yayi yana ganinshi da idon amman ba sosai ba, murya chan kasa yace “I can’t see clearly with it” murmushi Dr yayi yadagashi yace “I expect that to happen, I made a glass for you dagakai amfani dashi for 3month, zaisa idanun su warke” yay maganan yana kawomai fararen glasses din, yasamai sanan yace “can you see me now” gyadamai kai Zayn yayi yana kallonshi Dr yay murmushi dan glass din yanamai kyau sosai kaman wani professional Dr dinan, Dr yace “that’s all” kaman jira Zayn yake yasauka daga gadon yafice, Mami ne ta kakalo murmushi tace “thanks Dr OP” murmushi yamata yace “you are welcome” fitowa Mami tayi Zayn haryadanyi nisa tace “Zayn” juyowa yayi jin Mami takirashi, anatse tace “to my office” tajuya tawuce, dan yatsine fuska yayi sanan yabiyota abaya, shiga cikin wani hadadden office tayi ta tsaya gaban kofan tana jiranshi shigowa yayi hakan yasa tamaida office din tarufe tasa key sanan tawuceshi taje ta zauna, agaban table dinta wasu kananun photo frames guda uku ne gaban table dinta daya na Zayn ne yana jariri, daya dayay graduating daga university dayan kuma hoto ta ne da Alhaji da Zayn tareda su, kujeran dake gaban desk din nabaki ya zauna ahankali tareda dan sosakai irin na yan iskan nan dan yasan fada Mami zatamai, Mami takai kusan 1min tana kallonshi yanda yakeyi tasan cewa yasan fada zatamai, tasowa tayi ahankali ta zagayo inda yake, dayan kujeran dake gaban desk din dake facing na Zayn din taja ta zauna ahankali tana kallon fuskanshi, cikin wata kalan tattausan murya tace “Zayn” dan dago idanunshi yayi yakalli Mami ahankali yace “Yes Mami” hannu Mami tadaura kan bakinta kaman tana kokarin taushe kuka ne komenene ma takeji oho kafin ahankali ta zare hannun tace “Zayn is this how you show Allah you are grateful daya ceceka yay saving rayuwan ke eh? Two days ago Zayn you were kidnapped, this is Abuja aka tafi dakai chan wani kauye wai kuduri a Adamawa inda badadan Allah yasa that girl” tanuna kofan office dinta, tace “that girl, dake kwance akan gadon chan ta taimaka maka tasamo maka waya munyi magana dakai ba hankalinmu ko tunanin mu bazai taba kawomana kanachan wata duniya Adamawa ba” Mami tai shiru sanan ahankali tace “Zayn you almost die, you almost lost your life, look at your hand” tanunamai hannunshi dake nan akarye an daure, tace “look at your eyes” tanunamai idanunshi dake sanye da glass, tace “look at your whole body an zaneka blue black, Zayn u remembered you were crying danai waya dakai kana fadamana you were scared Zayn harka manta” Mami tai maganan ahankali tana kallonshi, dan lumshe idanunshi yayi kana ganin yanayin shi kasan maganan ta shige shi, ahankali Mami tace “Zayn tunda kataso bakasan menene wahala ba but rana tsaka within just 48hrs Allah ya nuna maka akwai rayuwan da ita sunanta wahala, ukuba da tsantsan azaba, sanan yanuna maka dukiyarka is nothing bata isa ta ceceka ba alokacin dazai kamaka, sanan yanuna maka shi kaskantaccen mutum dabaka dauka a komi ba zai iya maka abinda babu wanda zai iya maka shi aduniyan nan, Zayn badadan this incident ba someone like that girl Farrah can not even come close to you cewa zakayi she looks scary sabida Yar kauye ce bata da kudi irin na gidan Baban ka, Zayn did you know cewa second chance Allah yabaka” Mami tai maganan tana dafa knees dinshi, ahankali tace “Allah has given you second chance amman harka fara misusing nashi, kafara shaye shayen ka, mutum bai isheka da kallo ba, ba salla ba salati, babu wanda yakai matsayin kacemai kagode or thank you, did you thank that little girl that saved your life and took a bullet for you”? Mani tai maganan tana daga murya, shiru Zayn yayi kanshi akasa hakan yasa Mami ta dakamai tsawa. “Zayn did you thank her”? Ahankali ya girgizama Mami kai alamun no, wani kalan murmushi tayi tace “Baban ka nada kudi kafi karfi kama mutum godiya ko Zayn, you feel idan taji sauki u can give her money, jirgi and just send her off that’s your thank you” Mami tai shiru tana kallonshi, takai kusan 2good minute kallonshi take idanunta sunyi ja kaman kai shirin kuka, ahankali tace “all this behavior naka Zayn is my fault, lokacin dazaka fara JSS1 da zaakaika outside I had the chance nace baza akaimin yaro wajeba anan gida agabana zai karatu but nai shiru nabiyema Allah kiri kiri inaji ina gani kaki dawowa Nigeria tundaga nan kana makale da baturiyan Nany dinka dake kula dakai achan look at you now Zayn at 26yrs old you can’t differentiate between right and wrong, ba salla ba salati, ba komi, rayuwa kawai kake mara amfani magana ma sai anyi da gaske kakeyi, Zayn why why Zayn hmmm? Kataba tunanin inda munrasaka in this incident yaya zamuyi da rayukanmu dagani har Baban ka, why don’t you wanna be a better person for the sake of son damuke maka eh” Mami tai maganan hawaye na gangarowa daga idanunta sharrrr, wani iri Zayn yaji dasauri ya kauda kanshi gefe tunda yake baitaba ganin Mami na kuka ba sai yau, sanyi jikinshi yayi ahankali yace “s……sorry Mami” girgiza kai kai tayi tace “I don’t want you to tell me sorry, I want you to start doing the right thing, amend your ways ka koma ga Allah, kafara rayuwa kaman wanda yakeda hankali yay girma, someone of your age, kasakama wayanda suka maka hallaci da alkhairi Zayn, I believe in you, you are a very good boy Zayn I know that cus ni ne mahaifiyar ka kaji” kasa daurewa yayi yanda yaji Mami na kuka ahankali yatashi daga kan kujeran juyawa yayi ahankali yace “Mami I am sorry” hannunta tasa dasauri kan idanunta tashare fuska nata dan murmushi tayi tace “zonan Zayn” juyowa yayi ahankali yakalleta ganin ta share fuskanta yasa ahankali yaje gabanta, murya chan kasa tace “promise me you will change” ahankali yace “I promise Mami” murmushi tamai sanan tai pecking goshinshi tace “tashi kaje I am coming” tashi yayi yawuce yafita daga office din tabishi da kallo.

Ahankali yake bude kofan dakin da Farrah take, zaune yaganta yanda yabarta dazu akan dogon kujeran nan tana bacci ga wayanshi daya gani tarike a hannunshi, dawani kalan sauri yataba aljihun shi jin babu wayanshi yasa yadan yatsine fuska probably dazu ne ya manta dashi adakin, maida kofan dakin yayi yarufe sanan yazo gabanta ya tsaya hannunzhi ya mika mata yace “ke give me my phone”.
😘💫 FARRAH 💫

✍🏻M SHAKUR

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.