Complete Hausa Novels

Farrah Complete Hausa Novel

Reading file: FARRAH COMPLETE.txt

Chapter 19 of 32

EPISODE 2️⃣0️⃣
Side din Mami suka wuce, Mami na zaune a falo tana magana da Mama awaya suka shigo ganinsu tare yasa ta hararesu tacigaba da wayanta zama kusada Mami Alhaji yayi yana kallonta sabida tai kyau taci gayu sosai cikin kace kai kyau, katse wayan tayi takalleshi tace “ne kake kallona haka” cikeda tsokana yace “wai ke baki tsufa ne jibeki saikace ba kene kika haifi wannan gansamemen saurayin ba” yanuna Zayn, dan dariya Mami tayi tace “I take that as a compliment” “ina Farrah”? Alhaji ya tambayeta anatse, murmushi tayi tace “tana sama nabarta cartoon take kallo a IPad dina, you need to see yanda maganan ta ke improving Alhaji, one thing I like about her is she is fearless tanada kwazo da jajircewa” murmushi Alhaji yayi yace “kiramin ita” tashi Mami tayi tai sama bata wani jimaba suka shiga saukowa tareda Farrah, tana sanye da doguwan riga na atampa brown dinkin yamata das das ajiki sai dan kwalinshi data daura aka kanta na kasa wani kunya taji tanaji ita Mami tafiso da Mami kawai tasaki jiki saukowa kasa sukayi Mami ta zaunar da ita kan kujera kusada ita kasa zama tayi tazame jikinta ta zauna akasa da sauri kanta na kasa tashiga wasa da yatsunta Dan dariyan manya Alhaji yayi yace “Farrah yaya jikin? Wajen dinkin yadaina zafi”? Gyadama Alhaji kai tayi ahankali cikin zazzakan muryanta tace “eh…..Ab….ba” jinjina kai Alhaji yayi yana murmushi yace “Masha Allah, ga muryanki nan Tubarkallah Allah kara sauki” “Farrah” yasake kiranta anatse hakan yasa ahankali tadago kanta ta kalleshi, ajiyan zuciya Alhaji yasaki, yace “kingan ni nine mahaifin Zayn, mijin Mamin ku, da Mariya da Fatima da Maryam, Zayn kadai Allah yabani, rana daya kuma Allah yakawoki cikin rayuwan mu, akwai abinda yasa nasaka aka kiraki, inaso na tambayeki ne naji amsanki kafin nai komi” yasakeyin shiru sanan ahankali yace “Farrah kawunki ya sanar damu ke marainya ce, matata nan Maman Zayn likita ce, itace tamiki aiki a operation, taga tabo da dama ajikinki wanda yake nuna na alamun duka ne, yanzu inaso namiki wani tambaya banso kimin karya kinji” gyadama Alhaji kai tayi ahankali, anatse Alhaji yace “wanene yasamiki garwashin wuta abaki?” Shiru tayi gabanta nafaduwa dum dum, dafata Mami tayi ahankali tace “kada kiji tsoro ki yayi gaskiya kinji” gyadama Mami kai tayi sanan takalli Dad, batasan ya akayiba kasa karya tayi ahankali tace “In…na” “Matar kawunki”? Gyadama Alhaji kai tayi tace “eh””ita ke dukanki ma”? Gyadama Alhaji kai tayi takai bayan hannunta dasauri tashare hawayen daya zubomata, shiru dakin yayi Alhaji na kallonta, murya chan kasa yace “akwai abinda ake cema adoption aturence, yana nufin zaki dawo diyata ni da Mami da kotu tabamu mune custodian naki, kula dake yafita daga hannun su kawunki yadawo hannunmu dundundun ki dawo yarmu musaki amakaranta da sauran su, nakira lawyer na halama ya iso yanzu, yanzu hakama kawunki da matarshi na gidan nan chan bangaren baki, amman so naki nafara jin bakin ki kafin nasa akawo kowa nan, Farrah” Alhaji yakirata ahankali murya chan kasa tace “Na’am” ahankali yace “kin yarda ni da Mami muzama iyayenki?” Wasu kalan hawaye ne suka cika idanunta, tunda take baa taba bata daraja da mahimmaci dahar za’a zaunar da ita atamabayi yardanta Awani abu ba sai yau, tunda tahadu da mutanen nan sunada kirki sosai, batada kowa aduniyan nan banda kawu shi kadai gareta amman shima baya sonta baya kaunarta agabanshi aka kashe mata yar uwa baice komiba, dafata Mami tayi dasauri ta kalli Mami, Gyadamata kai Mami tayi alamun tace “eh” ahankali tace “eh Abba” rungumeta Mami tayi tana share mata fuska tace “daina kuka to” sai alokacin Zayn yadan saci kallonta, fuskanta na jikin Mami tana goge hawayen dasuka zubomata kaman ance ta kalleshi hada idanu sukayi da Zayn din hararanshi tayi tareda dauke kai.

Dauke kai shima Zayn yayi dasauri yana regretting kallonta ma dayayi waya Alhaji yayi sanan ya katse wayan yakalli Mami yace “tafi da ita sama”.

Wani Babban lawyer Alhaji ne yashigo falon tareda Uncle, sai Malam da idanunshi sukai zuru zuru da Inna da itama idanunta sukai zuru zuru, Malam yay mamaki dahar gida aka shigo aka daukesu suka shiga jirgi, Inna ihu tadingayi a helicopter wai zata mutu hanjin cikinta zasu zube.

Malam na ganin Alhaji da gudu yataho gabanshi ya tsugunna yahade hannayenshi biyu yace “Alhaji dan girman Allah kayakuri kada ka karbe kudaden daka bani, wlh wlh shairin shaidan yasa na gudu nakoma kauyenmu, to inbama shairin shedan ba ai nasan Kunsan kauyen kuma nakama nagudu, Alhaji dan Allah kayakuri wlh bazaka gane bane, Alhaji nima diyata daya rak, ina fama dakai na, kanwata tazo ciwon datayi shine ya tsiyatar dani tatas banda ko kwandala matata ce keda awakai suma awakan ranan da Farrah ta ceto dan gidan ka duka ta batar dasu, wlh ashirmena naso nagudu ne kawai nahuta inje na karata da matata da diyata guda amman nai kuskure kuya kuri” tunda yake maganan kowa ke kallonshi, cikin fushi Uncle yace “ina miliyan goman damuka baka bamu kayanmu ku dauki yarku amaidaku kauyenk……” tsayar da maganan datakeyi yayi ganin Alhaji yadagamai hannu, nuna kanshi Alhaji yayi yace “kai tun kana dan kankanin ka kataba ganin nai kyauta sanan nadawo na amshe kyautan danayi” sunnar da kanshi kasa Uncle yayi yace “a’a Yaya” maida hankalinshi kan Malam Alhaji yayi da Inna da itama ke zube gaban mijinta jikinta na rawa tunda take bata taba ganin aljannan duniya irin gidan nan ba, murmushi Alhaji yasakin musu yace “ku zauna da kyau dan Allah ni bakamin komi ba kuma bansa adaukoka sabida kudin danabaka ba nariga nabaka gonakin suma nariga nasa anma mai garin ku magana shi gwamnan Adamawa duk sanda ka koma zaka amsa koba komi yarinyar da bakaso yarinyar daka gudu a asibiti kabarta kaga kaci arzikinta” Alhaji yakara murmushi jikin Malam yay sanyi yakoma ahankali ya zauna hakama Inna, gyaran murya Alhaji yayi yace “abinda yasa na nasa akawomin kai nauyin dake kanka kake kokarin gudun mawa nakeso nacire maka shi daga kanka gabaki daya, diyarku Farrah nakeso nazama mahaifinta a shar’ance, cinta shanta, suturanta karatunta duka yadawo kaina, zai zamto Farrah tadawo diyata shine kawai abinda yasa na nemoka zaka bani”? Alhaji ya tambayeshi dasauri Malam jikinshi har bari yake yace “eh eh wlh nabaka Alhaji” Inna ma dan sosa keya tayi azuciyanta tanaji inama ace Rakiya ce ta taimaki yaron, kaman ta chakama kanta wukan bakin ciki takeji, kallon Lawyer Alhaji yayi yace “give him the papers” tashi yayi zuwa wajen Malam dan yabashi papers din yakuma nunamai inda zaiyi signing, dan yatsine fuska Zayn yayi yamike tsaye hanyar stairs yayi yay sama abinshi, shi kanshi baisan mesa yazo saman ba kujeran dakenan falon sama ya zauna yana kallon kofan dakin da yake tunani nan ne dakin Farrah dan shine dakin dake kusada na Mami, yadade yana kallon kofan, kaman akwai abinda ke controlling nashi tashi yayi zuwa gaban dakin yay jimmm yana kallon kofan, ahankali yadaga hannunshi yakai zaiyi knocking kofan dan cizan lips dinshi yayi yasauke hannun kasa ahankali, sake daga hannun yayi zaiyi knocking daidai nan aka bude kofan Farrah ce tabude kofan da saurinta dan ana kiran IPad din Mami dake wajenta zata kaimata saura kadan tafada jikin Zayn ta tare kanta ta hanyar kai hannunta daya ta daura kan kirjinshi daidai saitin zuciyanshi as kariya daidai lokacin kirjinshi ya buga dumm!💫 FARRAH 💫

✍🏻M SHAKUR

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.