Farar Wuta Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Farar Wuta Book 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 9 of 9
BABI NA SHA BIYAR.
~~~~~~~
This could be the start of something new.
-High School Musical
"Ina zamu je?"
Aminah ta tambaya lokacin da Ma'aruf yayi wata kwana data dauke su daga titin da ta kula cewa tun da suka shigo cikin garin Jifaywan a dazu shi suka yi ta miƙewa, muryarta a hankali ta fito yayin da take kallon hanyar.
"Wani waje." Amsar tasa ta fito a gajarce ba tare da ya kalle ta ba.
Sai ta juyo a hankali ga barin kallon titin da suke kai ta kalle shi ita, idanunta na shaida rashin fahimtar zancen, a can ciki kuma ruÉ—anin da take ciki, kamar ba zata ce komai ba amma sai muryarta ta sake fitowa.
"Nayi zaton gida zamu tafi."
Kalaman suka fito tare da nauyin yadda a yau bakinta ya furta wani waje daban da sunan Gida, saɓanin wajen da ta taso da rayuwarta a ciki. Ya girgiza kansa sannan ya juyo ya kalle ta, nauyin idanunsa suka sa taji kamar ta sunkuyar da kanta amma ta daure.
"Dare yayi kuna bana son tuƙin dare a babbar hanya, so anan garin zamu kwana sai gobe tukunna."
Yadda sautin muryarsa ya fito a cikin motar da kuma yadda yake kallonta yasa ta haɗiye wani abu a makogwaronta da bata san meye ba kafin ta gyada kanta alamun ta fahimta sannan kuma ta sunkuyar dashi ƙasa ta shiga wasa da karshen mayafinta, tattaunawarsu da Amma bata kare ba sam zuwansa ne ya katse su, wanda ta san haka ne, da tun a can ta roƙe shi fa ya barta ta kwana tare dasu idan yazo da safen sai ya koma ya ɗauke ta, wani abun ya sake zarcewa makogwaronta tuna cewa a yanzu bata san ina zai kaita su kwana ba ma.
Amma duk da haka sai taji wani ɓangare a cikin zuciyarta na washewa, zuciyarta na rage nauyin da take ɗauke dashi a ɗazu mai cike da taraddadin rashin sanin abinda zata yarda dashi a al'amarin Hajiya Kilishi, ko ba komai yanzu ta san tana da babbar hanyar da take da yakinin zata samawa kanta mafita kamar yadda Amma ta fara gaya mata, Har a yanzu tana jin tasirin kalamanta da ya cika kanta taf! Yana ƙara buɗe wasu sababbin shafuka da a iya zagayen tunaninta gabaɗaya ita bata hango su ba.
Tana jin yadda amon kalaman nata ke zagaye cikin kanta, ma'anarsu na bi ta cikin jijiyoyinta suna taso da ƙarfin gwiwar da ta nemi ta rasa, kuma duk da taraddadin da take ji, koina a cikin kanta dama jikinta yana gaya mata cewar yanzu ne komai zai fara, don kamar yadda Amma ta fada ne babban kuskuren da Hajiya Kilishi tayi, ya riga ya bude musu ƙofar nasarar su.
"Mafitar ta riga tazo hannunki Amina, buɗe idonki kawai zaki yi ki kalle ta, kina da rabin maganin wannan matsalar yanzu a hannunki, wanda babban abun shine sanin halinta da kikayi, ita kanta bata sani bane amma tayi babban kuskure wajen bayyana miki sirrinta duk kuwa da na san cewa iya abinda take so ki sani kawai ta faɗa akwai sauran ƙurar da dole na san ta lulluɓe. Amma tun ana na fara raina lissafinta Amina, don da ace tayi bunƙasar da zan sara mata, da zata sami tarin hanyoyin da kema zata juya ki ba tare da kin san sirrinta ba..."
Wasu daga cikin kalaman Amman kenan da suka ƙara saka ta yarda cewa mahaifiyarta na cikin irin daidaikun matan da ake misali dasu a duniya, masu halayen da dimbin jama'a zasu gani tamkar a mafarki, da kowacce kalma da ta gaya mata a yau, zuciyarta ta ƙara yarda cewa mahaifiyarta itace babban makamin da zata iya tunkarar komai dashi a duniyar nan bayan addu'a.
Sai dai akwai wani abu guda daya a cikin kalaman nata dake fassara abinda zuciyarta bata taɓa lissafawa ba, abinda har yanzu da ta tuno yake rikita lissafinta yana sa hannayenta rawa, har yanzu bata gama sanin tunanin Ma'aruf game da ita ba, don haka ba zata taɓa iya ɗorar da komai ba a wannan fannin.
Ta rufe idanunta tsawon wasu sakanni kafin ta sake buɗe su tana ƙoƙarin saita kanta. Amma ta gaya mata cewa lokacin wani rauninta ya kare, kar ta yarda wani abu ya gaya mata cewa an fi ƙarfinta ba zata iya ba, tace mata itama macece, duk wani abu da take taƙama dashi itama tana dashi, kawai ita tana amfani da nata wayon ne ta mummunar hanya, don haka idan ita zata ɓullarwa gaskiya, a lokaci kadan ne zata kawo karshenta don gaskiya itace sama da komai a duniyar nan.
"Kilishi bata fi kowacce mace ba a duniyar nan Amina, yadda take takama da wayo da kuma dabararta, haka Allah ya halittawa ƙwaƙwalwar dukkan mata don ita mace uwa ce, an halicci mutane da yawa da zasu rayu a ƙarƙashinta wanda kowanne da irin ƙalubalen rayuwarsa, shi yasa Allah ya buɗe ƙwaƙwalwarta ta yadda zata iya samar da mafita kala-kala a fannin rayuwa.
Wasu matan basa gane hakan ne har suyi yunƙurin sanin abinda zasu iya, matan kuwa da kika ga suna zaune lafiya tare da mazajensu ƴaƴansu harma da duk wanda zai raɓe su, sune wanda suka iya buɗe wannan baiwar tasu, Mata irin Kilishi kuma sune wanda suke amfani da wannan baiwar ta hanya mai munin da har suke ganin cewa sun fi kowa.
Yanzu girma yazo kanki da gaske Amina, kin fara ganin hakan tun daga ranar da kika bar karƙashinmu, kuma hausawa sun ce aure yakin mata, yaki ne da kowacce mace akwai kalar nata, don haka kema dole ne ki bude ƙwaƙwalwar ki, ki karɓi wannan girman sannan ki fuskanci naki yaƙin Amina..."
A daidai wannan lokacin suka shigo harabar wani haddadden gini mai tarin fitulun dake ta haske suna maraba da daren da bai kai ga ƙarasowa ba. Ma'aruf ya tsayar da motar a jerin motocin dake tsaye a wajen daidai lokacin da idonta ya zare akan sunan wajen.
Haseenah Guest Inn.
***
"Mene ne total charges for Adjustment and Uncollectables?"
Ma'aruf ya tambaya a cikin wayar da yake yi daga cikin dakin, yana zaune ne akan wani dan karamin dining table dake can karshen dakin yayin da hannunsa ke rubutu a cikin notepad din dake kan teburin. Kayan jikinsa wata loose T-shirt ce da ya siyo da kuma wani gajeran wando kalar grey.
"Next..."
Ya sake faÉ—a bayan mai maganar na ciki ya gaya masa wani adadi da ya rubuta a cikin wayar.
"Ka gaya min Net Patient Revenue din?"
"Na gaya maka yallabai, shine na biyu bayan total charges na Patient Care gabaÉ—aya."
Mai maganar daga cikin wayar ya fada, sai ya gyada kansa yana bude shafin baya, ya karanta abinda ya rubuta sannan ya sake dawowa inda yake yace.
"Operating Expenses din fa?"
Mutumin na ciki ya sake faÉ—o masa wani adadi da ya shifa rubutawa.
"Sannan sir akwai Bad debts É—in wancan..."
"Sai kuma Natural Expense É—in?"
Ya katse shi ba tare da ya saurari abinda yake cewa ba, mutumin ya É—anyi shiru kafin ya faÉ—o wani adadi na makudan kudin da saida Ma'aruf ya jinkirta kadan yana saurarar sa kafin ya rubuta.
"Yallaɓai ka saurare ni akan zancen bashin nan, bamu da wata hanya ne dole..."
"Just tell me the total Sadiq." (Kawai ka gaya min jimlar komai gabadaya Sadiq.)
Muryarsa ta fito a hankalin da take tun bayan sallar magariba da yayi buda baki.
"Wallahi yallabai zai fi kyau ka duba Report É—in gaba É—aya tukunna gabadaya 42 pages ne, idan ka karanta komai you will realize that..."
"Ka gaya min total din kawai Sadiq."
Yadda sautin muryar tasa ta fito wannan karon ita tasa Sadiq din sarewa daga dukkan ƙokarin da yake fanin zai iya shawo kansa, yayi ajiyar zuciya a hankali sannan ya fadi wasu makudan kudade da shi kansa Ma'aruf ɗin ya sani idan za'a bincike account dinsa na bankuna tsaf a tattaro komai baza 'a taba samun wannan adadin ba, don haka bai ma rubuta ba, wani guntun murmushi ne ya suɓuce a lebbensa yayin da yayi baya ya jingina da kujerar da yake kai yana kallon gabansa tamkar Sadiq ɗin ne a wajen.
"Wallahi yallabai..."
"Sadiq"
Ya katse shi, sautin muryarsa can ƙasa amma kuma a kausashe.
"A rufe asibitin, a tsayar da komai, kwana kaÉ—an na baku, I'm coming in few days, ku san yadda zaku gyara wannan abin in a reasonable way kafin zuwa na. Idan ba haka ba, na rantse da Allah wasu ne zasu ci muku abinda kuka É—iba ba ku ba, and just dare me and see.!"
Yana faɗin haka ya kashe wayar, ya cilla ta kan teburin da karfi har sai da screenguard ɗin dake kanta yayi wata katuwar tsaga guda daya, sannan ya cusa hannayensa duka biyu a cikin gashinsa yana ƙoƙarin saita numfashinsa, ransa ne yake shirin baci ya sani, amma yana kokati da dukkan iyawarsa ya danne hakan kamar yadda ya saba yanzu a kwanakin nan. Bakinsa ya shiga karanto hasbunallahu wa ni'imal walkil daidai lokacin da kofar toilet din dakin daga can gefe ta buɗe bayan abinda zai iya kira aƙalla minti talatin.
Ya sauke hannayensa daga fuskarsa kafin ya juyo ya kalle ta, tana tsaye daga kofar kamar zata koma ciki ne ta sake rufewa, babu shiri yaji dukkan abinda ke cikin kansa na sulalewa yana bin iska, rigar da ya siyo ita ta saka, kusan iri daya ce da wadda ya taɓa gani ta saka a gida ranar da tashi cikin daren nan, me tsawo daga baya amma ta gaba kuma iya gwiwa take kawai, kuma yadda idanunsa suka riƙe hoton siraran kafafunta a wancan lokacin shi yasa kai tsaye yace a mayar da wanda ya ɗauko a ciro masa ita.
Daga yanayinta kawai ya san ta saka ne don bata da wani zaɓi, tunda wani mai wanki da guga na Hotel ɗin yasa yazo ya karɓi kayansu don ya wanke zuwa gobe, idanunsa kallonta kawai suke tun daga nan, ta yafa bakin mayafinta da bata bayar dashi ba akanta amma duk da haka gashinta na fitowa kamar ɗazu da safe.
Daga inda Amina take tsaye, cakuɗa yatsunta kawai take yi cikin junansu saboda rawar da hannayenta ke yi musamman a yanzu da take ƙara ganin wautarta na fitowa a haka, amma ya zata yi, har tawul a cikin toilet din ta ɗauko ta ɗaura taga abin bai dace ba ta cire shi.
A ajiye ma zancen ƙafafunta dake waje a gefe, tunda take bata taɓa lissafawa cewa zata yi kwanan hotel a rayuwarta ba idan har ba wai Makkah ko wata kasar taje ba, wanda shima ba'a irin wannan yanayin take hango shi ba, shi yasa tun da suka shigo zuciyarta ke rabewa gida biyu tana sake haɗewar da har a yanzu ta kasa samun sauƙi duk kuwa da ƙarfin halin da ta tattaro a ranta.
Ganin yadda yake kallonta yasa ta juya da sauri ta ƙarasa jawo ƙofar toilet ɗin ta rufe sannan ta shiga tahowa cikin ɗakin. Wani abu ya zarce maƙogwaron Ma'aruf da yake kallonta tana tahowa sai mutstsika yatsunta take yi cikin junansu yayin da siraran ƙafafun nata ke tafiya.
Tare da Ruƙayya yasha tambayar kansa meye babban interest dinsa game da mace, sai dai a lokacin ya kasa tsaida zuciyarsa akan komai banda kyawunta don ita ɗin kyakkyawa ce, amma a yanzu ya samu wannan amsar da ya daɗe yana nema, don yadda zuciyarsa ke sake ɗaukan hoton ƙafafun Amina tana masa kyakkyawar ajiya, a wani yanayi ne da wataƙila ko bayan ransa ba zai manta ba.
Ta ƙaraso kamar mara gaskiya ta wuce shi ta nufi wajen wani ɗan ƙaramin table da ma'aikatan wajen suka kawo musu abinci kamar yadda ya basu umarni.
Kuma sai a sannan tayi magana, tun bayan da suka idar da sallar isha da ya bata wayarsa ta sake kiran mahaifiyarta ta shaida mata cewa basu bar garin ba sai gobe tukunna.
"Wanne abincin zan zubo maka?"
Yaji ta tambaya daga bayansa inda taje ta tsaya, sai kawai ya ture komai a ransa ya taso ya taho inda take, ta juya bayan nata kamar yadda ya zata tana ƙoƙarin buɗe plates ɗin masu wasu irin manyan-manyan murafe kamar na abincin sarakai, a hankali ƙafafunsa suka tako ta kan carpet ɗin dake shimfide a wajen ya ƙaraso ya tsaya dab da bayan nata idanunsa na nazarin ɗan karamin jikinta dama siraran hannunta, bayan haka tsawonta ma gabadaya iya kafaɗarsa ne, ya san yana da tsawo don shi da Jamal ana cewa duk tsawon Hajiya Maimuna suka yi, amma bai taɓa tsayawa yayi nazarin yadda yafi wani tsawo irin haka ba sai akanta, don ko Ruƙayya ya sani ne cewa da kaɗan yafi ta.
Kuma wataƙila shirun da yayi ne yasa ta juyowa a hankali hannunta rike da murfin da ta ɗauko guda ɗaya, idonsa ya sake kaiwa kan kafafunta a yanzu data juyo, sai yanzu ya lura cewa akan farcen kafafun nata akwai kalar baki alamun lallen da bai gama fita ba, kuma yadda farcen ya rabu kala biyu fari da baki yasa shi kasa daina kallonsu.
Amina ta sunkuya kalli ƙafafunta da yake kallo tana son ta nemo abinda ke wajen amma bata ga komai ba, yadda yake tsaye dab da ita kaɗai ya isa yasa zuciyarta rabewa gida biyu, amma tunda bata rabe tun a lokacin data fahimci cewa yau zata kwana daya daki daya dashi ba, bata jin a yanzun ma zata yi. Ta sake haɗiye wani abu karo na ba adadi a maƙogwaronta tana son kore ɗimbin tunanin dake kanta kafin ta sake yin magana.
"Zaka ci abincin?"
Muryarta ta fito ne kamar tana son tuna masa cewa ba'a kafarta fuskarta take ba, kuma hakan yayi aiki don a lokaci guda ya É—ago da idonsa ya kalle ta.
"Naci abincinki, kin manta?"
Ta yaya zata manta, da wannan busashshiyar doya da ƙwan data soya tun safe yayi buɗa baki, tea ɗin wajen kawai yasha ya cinye doyar gabaɗaya, a lokacin tana waya dasu Amma, tana daga karshen ɗakin kallon yadda yake buɗe-bude a cikin labtop ɗinsa yana cin doyar, wani abu da ya kara nutsar da zuciyarta a cikin kirjinta tana jin dama abinda tayi yafi doyar kaɗai, sannan kuma wani abu da ya fara buɗewa kalaman Amma dake sa hannunta rawa kofa a zuciyarta.
Sai ta girgiza kanta a yanzu tana ƙoƙarin cigaba da kallonsa.
"Ai wannan ba zai isa ba, idan mutum yayi azumi gwara yaci abinci da yawa."
Ya gyaÉ—a kansa shima yana kallonta.
"Na sani, amma raina ne ya fara ɓaci yanzu, bana jin zan iya cin abincin."
Kawai sai ta samu kanta da tambayar.
"Me ya faru?"
Kuma fitowar tambayar yasa taji kamar ta fara yin nisa da taraddadin dake zuciyarta.
Hannunsa ɗaya taga ya zura cikin gashin kansa kamar abinda zai faɗa zai yi masa wahala kafin wucewar sakan biyu yace.
"Ina da abubuwa da yawa a gabana, so mutane na using wannan opportunity É—in suna cuta ta, Annual report din MMB- 6 aka aiko min yanzu, kuÉ—in da suka ce sun kashe a shekarar nan Amina ko ni bani dasu yanzu."
Ba maganganun ne suka daki zuciyar Amina ba, sautin muryarsa ne yadda ya fito cike da wani rauni da idan za'ayi musu da ɗimbin mutane zasu kwana suna rantsewa cewa ba daga muryar Ma'aruf wannan raunin yake ba, ba shiri taji ta hadiye wani abu a makogwaronta kafin tace.
"Meye MMB-6?"
Wataƙila idan ta fara sani meye shi din zata fahimci abinda maganar tasa take nufi.
"Asibiti na ne da yake Abuja."
Sai ta sake gyaÉ—a kanta tana jin kamar maganar tafi karfinta, amma kuma kai tsaye sai tace.
"Ance idan hankali ya ɓata hankali ake sawa ya nemo shi, yanzu ko ranka ya ɓaci babu abinda zai canja, kamata yayi ka samu nutsuwa mai kyau, sai kayi amfani da hakan ka gano koma wane irin akasi ne aka samu."
Maganganun suka tafi har ƙarshen zuciyar Ma'aruf, suna fito da irin kwanciyar hankalin da yake ji a duk lokacin da ya gayawa Mami damuwarsa kuma ta bashi ɗaya daga cikin shawarwarin ta, Amina bata sani bane amma itace mutum ta farko daya dangance shi bayan Ishaq da suka san da zancen asibitin nan.
Abu ne da ko Mamin bata sani ba, kuma shi yasa dama yake damuwa duk sanda aka samu matsala akansa don ya san babu wanda zai iya bashi shawara mai kyau akan hakan tunda ko Ishaq baya yiwa zancensa. Kuma haka kurum ya zaɓi boyewa kowa sanin da zaman asibitin don so yake yi da gaske ya binne duk wata halayyarsa ta baya tare dasu kamar yadda yayi wa kansa alƙawari.
Zama likita yana daya daga cikin burinsa na farko a duniya, don haka nacin da zuciyarsa ke masa shi yasa shi tsallakewa zuwa garin Abuja ya gina ƙaton asibitin guda inda ya danka amanarsa a hannun wani likita mai suna Sadiq, shi yake jagorantar komai na asinitin don hatta tarin likitocin dake musu aiki shi yake biyansu, shekaru biyar kenan da kafa asibitin, kuma tun bayan shekaru biyun farko aka fara samun matsala a annual report din da suke bashi duk ƙarshen shekara, ya zama kudin da suke cewa duna amfani dashi duk shekara ya fara fin karfin tunaninsa.
Sai gashi yanzu minti ɗaya kawai gaban Amina duk dauriyarsa ya kasa riƙe wannan sirrin ya fallasa mata komai, amma kuma da ta bashi sai tasa bai ji yayi nadamar sanar da itan ba, hasalima zuciyarsa gode masa ta dinga yi don aƙalla abinda ta faɗa ɗin ya sama mata wani sauƙin.
Sai kawai ya gyaÉ—a kansa yace.
"Thank you."
Sannan ya zagayo ta gefen table É—in yace.
"Me zaki zuba mana?"
Tambayar tasa ta juyowa itama tana jin nauyin abinda ya faÉ—a, plates din ya shiga budewa gabadaya yana tara murafansu a hannusa É—aya.
"Wanne kafi so a ciki?" Ta samu kanta da tambaya babu wani dalili.
Ya girgiza kansa shima.
"Ni zan ci ko meye kika zuba, favourite abinda nake so baya cikin wadannan."
Ya fada yana kokarin ajiye murafan a gefe, sannan kai tsaye ya shiga gaya mata irin abincin da yake so wanda kusan duka na gargajiya ne, sanda yace mata har da É—anwake sai da ta tsaya tana kallonsa, don ita a tunaninta mutane kamarsa basa É—aukar abincin gargajiya da muhimmanci.
Ya tambaye ta abinda take so itama kuma sai ta samu kanta da ture komai a ranta ta shiga gaya masa, kuma da kowacce kalma data faÉ—a tana ji kamar tana karkaÉ—e ragowar taraddadin dake ranta ne.
"Ina son chocolate, sannan zan sha lemon zoɓo a koina kuma a kodayaushe."
Ta fada lokacin da yake tambayarta abinda take so na kayan kwaÉ—ayi.
Ya gyada kansa.
"Naga alama, cox naga zoɓo da yawa a fridge dinki."
Ta gyada kanta a hankali itama.
"Ina ga ba zan taɓa iya dadewa babu shi ba a koina."
"Wow, I like the enthusiasm."(ina son kwarin gwiwar nan.)
Muryarsa ta gito da slamun cewa shima ya fara jin dadin sakewarta.
Sai tayi wani guntun murmushi da bata san daga ina ya fito ba tana kallon abinda take zubawa.
"Wane kalar chocolate kika fi so?" Da alama so yake hirar ta cigaba da yin nisa.
"Kowanne."
Wannan karon muryarta ta sake fitowa kamar silin gashin dake faɗowa ƙasa a hankali ba tare da ta dago ba.
"Chocolate bai dame ni ba amma I always enjoy Ferraro Rocher." (Ina jin dadin Ferraro Rocher.)
Bata taɓa jin ko sunan ba, kuma sai Allah ya taimake ta kafin tayi tunanin abinda zata faɗa, wayarsa dake can kan table ɗin daya baro ta ta shiga ƙara, don haka ya karbi plate din da gama zubawa ya tafi wajen, ya ajiye plate shi akan table din sannan ya kara wayar a kunnensa ya shiga magana da wani cikin Pidgin english, irin tsantsar Pidgin din da ita bata taba ji ba ma, amma kuma sai yayi mata dadi, yadda sautin muryarsa yake haɗewa cikin accent ɗin da kana ji ka san ya fito ne daga Jinsin Hausa/Fulani.
'Matar Æ´an gayu.'
Haka Aminu yayi ta tsokanarta ɗazu, kuma ita kanta duk da hargitsin yanayin da take ciki ta sani cewa kamar yadda Hajiya Kilishi ta faɗa ne, idan banda kaddara ko zata mutu sau ɗari ta dawo Ma'aruf yafi karfinta, don a yanzu da kowacce wucewar rana tana ƙara gane cewa yafi ƙarfin hangen da take masa a lokacin da ta yarda da auren nan. Shi yasa ko a yanzu kawai ƙwaƙwalwarta ta kasa auna mata adadin kuɗin da ya kashe wajen kama ɗakin nan don kwana ɗaya kawai.
Ta ɗebo farfesun kifi na ƙarshe a cikin wani ɗan bowl sannan ta juyo tana hango shi daga can inda ya zauna a jikin table din yana magana, kuma kayan jikinsa na T-shirt da gajeran wandon nan suka sake tuna mata da wanda ke jikinta itama, ba shiri ta hadiye wani yawu a maƙogwaronta tana jinjinawa kaddara, don in ba ƙaddarar ba ba zata taba hango kanta a irin wannan yanayin tare da wani namiji kuma dadin daɗawa a Hotel ba.
Ƙafafunta duka karasa a hankali har gabansa, ta tsaya daga gefensa sanda ya dago daga rubuta wani abu da yayi a jikin wata ƴar jotter yana kallonta, ya taimaka ya ture mata kayansa dake kan table din kafin ta ajiye plate din a hankali kusa da dayan sannan ta juya niyyar dauko ruwa wanda tun dazu ta ganshi a fridge din dake can gefe, amma sai kawai taji ya riƙo hannunta na hagu, dogwayen yatsunsa suka ratsa cikin nata yana riko ta, a lokaci guda numfashinta ya katse a ƙirjinta yayin da yatsunta suka yi sanyi kalau!
Ya sake riƙo hannun nata sosai sannan ya jawo ta baya ta dawo gabansa, shi yana zaune ita kuma tana tsaye a gabansa da kafafunta duk a waje, ba shiri ta dunƙule tafin kafarta akan sassanyan marbles din ɗakin, sannan ta rufe idanunta a hankali tana jin yadda yake motsa yatsunsa a cikin nata.
Ta buɗe su daidai sanda ya gama wayar, idonsa yana kan kafafunta ne da har yanzu ta rasa me yake gani a jikinsu, kuma kafin ta gama tunanin hakan taji ya jawo ta zuwa kasa a hankali, ya durƙusar da ita a gabansa, dab dashi sosai wanda hakan yasa ta sunkuyar da idanunta ƙasa tana cije gefen lebbenta.
"Wata magana nake son muyi Please..."
Yadda muuryarsa a fito a hankali da kuma zurfi ya haddasa faduwa da saukar numfashinta.
"Zamu iya yi yanzu?"
Ya ƙara tambaya a lokacin da take kokarin tsayar da iska a kirjinta, da kyar ta daure ta daga kanta sau biyu babu kari. Shina ya gyada nasa kan a hankali yana cigaba da kallon fuskarta.
"Na sani a yadda komai ya fara a tsakaninmu akwai tarin irin tunanin da kike yi akaina, na san an gaya miki tarin abubuwan da ba lallai ne na iya ƙaryata miki su ba, kinji wanene ni ta bangare da yawa na sani Amina, kuma har nima na bada gudunmawa wajen saka miki wani tunanin akaina tun a wancan lokacin, wani abu da nayi shi ne ba don komai ba sai don in hana faruwar auren a tsakanin mu."
Yayi shiru ya cigaba da kallon fuskarta, kuma ganin yanayinta bai canja ba yasa shi cigaba.
"I'm a mess Amina, akwai tarin abubuwan dake gabana kuma a tsakiyarsu ne na tsinci zancen aurenmu wanda ni tun bayan lokacin dana rabu da Ruƙayya ban kara tunanin cewa zan sake aure ba, abubuwa sunyi min yawan da bana son nauyin komai ya sake ƙaruwa akaina, saboda haka wannan wasiƙar da na baki nayi ne don in tsorata ki ta hanyar da zai sa ki ƙi yarda sabida su Baffa baza su saurare ni ba a lokacin, abinda na manta a wannan lokacin shine ban isa in canja ƙaddarar da Allah ya hukunta ba tunda hakan babu abinda ya canja."
A wannan lokacin numfashin dake ƙirjin Amina ya kasa tsayawa waje guda, sai kokari take dashi kamar kifin da ya fito daga rywa yana wutsil-wutsil, hasken fitukub dakin ya karu a idanunta yayin da wata iska ta shiga busuwa daga maka-makan windunan dskin kasancewar a sama suke.
"Daga ranar da na fara ganinki Amina, nayi nadamar abinda nayi, na san cewa ban kyauta ba da har na saka wannan tsoron da na gani a cikin idanunki, wanda duk da hakan kuma bai hana ki kyautata min ba, bai hana ki nuna min kirkin ki da kuma halayenki na gari ba, kuma yanzu wannan kirkin naki nake kwaɗayin cigaba da samu Amina, ina son nutsuwar da nake samu a wajenki don itace babban abinda nake bukata wajen tafiyar da rayuwata a yanzu, shi yasa nake rokonki da ki manta duk wani hasashe da kike yi kaina Please, ki bani damar da zamu yi normal life kamar yadda kowa yake yi, wallahi nayi alkawarin ba zan taɓa cutar dake ba insha Allah."
"....Kamar yadda na faɗa miki mafitar ta riga tazo hannunki Amina, Kilishi ta bude miki kofar samun nasarar da ita kanta bata sani ba, so nake ki dauki dukkan maganganunta kiyi wa taki zuciyar ado dasu Amina, don takunta zaki bi, dukkan abinda ta fada kema shi zaki yi, banbancin da za'a samu tsakanin ke da ita shine, ke ita zaki yiwa Amina, ita zaki lulluɓe da rigar amincinki ba kowa ba, ita zaki zamewa farar wutar da ba zata taɓa sanin cewa ƙonata kike yi ba.
Kuma hanyar farko da hakan zata kasance shine idan kika sami soyayyar mijinki..."
Kalaman da Amma na ɗazu su suka biyo bayan dukkanin bayanin Ma'aruf a cikin kan Amina, ta tuna yadda take kallon Amman cike da ƙarin bayanin da bata furta ba Amman ta cigaba.
"Kilishi ta gaya miki cewa soyayyar mijinta ta fara samu a saman ta kowa, shi ya fara yarda da ita kafin ta buɗe zuciyar kowa ta fara aiwatar da manufarta, idan baki sani ba yau ki sani Amina cewar taƙamar kowacce mace a duniyar zuciyar mijinta ce, idan taci riba anan to wallahi duk girman wata matsala koda kuwa ta mahaifiyarsa ce ta tsallake ta.
Yaron nan ya riga ya zama mijinki a yanzu ko munso ko bamu so ba, don haka kije ki ƙara dagewa, ki dage wajen kyautata masa har zuciyarsa ta ƙara yarda dake akan yanzu, sannan da zarar kun koma kije wajen Kilishi ki tsugunna ki gaya mata cewar kin yarda da sharaɗinta bama sai lokacin da ta gindaya miki yayi ba, ki ƙasƙantar da kanki a gabanta ta sigar da ba zata taba iya haska cikin zuciyarki har tayi wani hasashe ba, waɗannan sune matakan farko Amina, kuma ina tabbatar miki idan kika tsallake su, dukkan sauran zasu zo ne bi da bi kuma a sauƙake..."
WaÉ—annan sune kalaman dake saka sa hannyenta rawa a É—azu, sune kalaman Amman dake rikita lissafinta suna gaya mata cewar ba zata iya dorar da wani abu akan Ma'aruf ba tunda bata gama sanin tunaninsa akanta ba... Sai gashi tun ba'aje koina ba hanyar farko tazo mata da sauki.
Allah ya amsa addu'ar ta, Ma'aruf ya cire dukkan wani kokwanton dake zuciyarta da waÉ—annan iya kalaman nasa, a yanzu ta yarda cewa shi da gaske zuciyarsa wankakkiya ce akansa, abinda take ta taraddadi daga bangaren Hajiya Kilishi yake dama.
Taji yadda mamaki ke cinye zuciyarta tun daga ƙasa, ashe komai ba mai wuya bane kamar yadda Amman tace, kowacce mace tana da irin nata ikon a hannu, kawai burga da barazana ce ke saka wasu yin ƙasa su yarda cewa an fisu su baza su iya ba, gashi tun basu ko bar garin nan ba ta fara samun yardar Ma'aruf a hannunta, idan haka ne kuwa ta yarda da maganar Amma na cewar da gaske Kilishi ta kiyaye su, don ko ita a yanzu tana jin ƙarfin gwiwar cewa zata iya.
Kuma cikin wata irin sa'a, sai ya ƙyale ta bai nemi amsarta ba har suka kammala cin abincin da komai.
Wajen ƙarfe goma sha ɗaya saura Amina ta dunkunkune a karshe gadon ɗakin har a lokacin tana ta faman sake-sake a ranar, don ko ka kaɗan ba bacci take ji ba, abubuwan da ta fuskanta a yau suna da yawan da har yanzu basu gama narkewa a cikin ranta ba. Ta juya bayanta ne tana kallon ɗaya gefen ɗakin yayin da hannunta ke wasa da ƙarshen bakin mayafin nan data yafa a akanta.
A yanzu fitulun É—akin duka a kashe suke, Ma'aruf ya kashe su kafin ya shiga toilet don ta riga shi kwanciya, sai da ya gama aikinsa tana kwance tana sake-sakenta sannan ya tashi ya kashe fitulun duka ya shiga toilet din.
A yanzu babu wani haske sai na waje da yake shigowa cikin ɗakin, kuma wucewar minti biyar kawai sai kofar toilet din ta buɗe, hasken fitilar ciki ya ratsa duhun ɗakin kuma duk da ta juya bayanta sai da hasken ya shiga idonta kafin taji ya rufe ƙofar duhun na sake dawowa.
Taji gadon ya motsa yana shaida mata hawowarsa zuwa daya gefen da sanda yaje jan sauran bargon da ta rufe ƙafafunta dashi zuwa nasa jikin.
Sakan ɗaya, biyu, suka wuce tana cigaba da wasa da mayafinta kafin taji muryarsa, can ƙasa a hankali kamar duhun daren.
"Amina..."
Ya kira sunanta kamar wannan ne karo na farko daya fara faÉ—a, yadda tunaninta ya tsaya cak haka ma daren ya tsaya, kamar shima yana jiran amsar da zata bayar ne.
Tayi kokarin haÉ—iye wata busashshiyar iska a makogwaronta sannan tayi dauriyar amsawa a hankali.
"Can I hold you.. ?" (Zan iya riƙe ki?)
Bata san me take tunanin a wannan lokacin ba, bata san ma me taje yi va ko kuma abinda yake faruwa a cikin kanta, ta san dai kawai zuciyarta ta ƙirga wucewar wasu sakanni ne data san cewa jiranta yake yi kafin duk wata dauriyarta ta rinjaye ta wajen ɗaga kanta a hankali.
Kuma bata san ya akayi yaji ta ba, don a lokaci guda yasa hannunsa daya ya janyo ta zuwa jikinsa, ya juyo ta tana fuskantar sa yayin da hannunsa ɗaya ya zagaye waist ɗinta, sannan ɗan kaɗan ya ratsa ƙafafunsa a tsakanin nata.
Ya hade ta da jikinsa har tana jin kara bugawar zuciyarsa kamar kaɗawar igiyar ruwa a bakin teku wanda sautinsa ya haɗe da amon tata zuciyar, ya zama idanunta basa ganin duhun daren sai wanda ke tsakaninsu kawai, numfashinsu ya hade waje guda yayin da ƙamshin turare da kuma sabuntar kayansu ya cika hancinta.
Kuma bai isa Ma'aruf ya gama rikita zuciyarta ba sai da ya sunkuyo da fuskarsa daidai cikin wuyanta ba shiri kuwa jikinta ya shiga girgizawa gabaÉ—aya a cikin nasa, kuma ga mamakinta sai taji yayi wani abu kamar murmushi sannan a cikin kunnenta ya furta maganar data rikito da duniyarta bakiÉ—aya ta rugurguje.
"Kar ki damu, not now, not here." (Ba yanzu ba, ba anan ba.)
Shikenan! Ma'aruf ya gama da rayuwarta!
***
Kano.
09:30Am
No. 58 Mafara Street, NNDC SharaÉ—a Quaters.
"Wai har kun dawo?"
Surayya ta faÉ—a a lokacin da ta fito dafa daki tana kallon Amina daje zaune a tsakiyar falon nasu tare da Sameerah wadda ta cika gabanta da kayan breakfast.
"Tun wajen ƙarfe takwas fa suka dawo. Yayan har ya tafi aiki ma." Sameerah ta bata amsa lokacin da take hada nata tea din.
"Auren ma'aikacin kamfani na da wuya ko?"
Surayyan ta fada tana kallon Amina lokacin da tazo ta zauna a kusa da ita tana É—aukan pillow É—in kujerar zuwa cinyarta.
Da murmushi a fuskar Amina tace.
"Gashi nan dai, ni ban saba ba har yanzu."
"Gaya min zaki yi idan da wuya tun wuri in kori Tahir."
Kafin ta amsa Sameerah tace.
"Ki kore shi ma, don Wallahi Baffa yace ba wanda zai sake yiwa aure a gidan nan sai man da shekara biyar. Su Salma sun karya tattalin arzikinsa."
Dariya kawai Amina tayi tana kallonsu lokacin da musun da suka saba a kullum ya kaure tsakaninsu, don ma wai Munaya na can ɓangarensu ne.
Sai dai duk yadda dariyar tata ta kai akan lebbenta kawai take, don daga can kasan zuciyarta taraddadi ne fal da kuma tunanin abinda ke shirin faruwa.
Don kamar yadda Samirah ta fadawa Surayya ne, tun wajen karfe takwas da ƴan mintuna na safe suka iso garin Kano, don Ma'aruf ya gaya mata cewar yana da tarin aikin dake jiransa a office, kuma ya sauke ta a gida ne ya tafi bayan ya rungume ta yayi kissing saman kanta lokacin da suka shigo ciki ya buɗe mata gidan da muƙullin dake jikin na motarsa, sannan ya juya ya barta tana kokarin hada zuciyarta waje guda ya koma wajen motar tasa da ya bari a waje.
Kuma shigarta gidan ya sake tsayar da zuciyarta waje guda, yana tuna mata da kalaman Amma.
"...da zarar kun koma kije wajen Kilishi ki tsugunna ki gaya mata cewar kin yarda da sharaɗinta bama sai lokacin da ta gindaya miki yayi ba, ki ƙasƙantar da kanki a gabanta ta sigar da ba zata taba iya haska cikin zuciyarki har tayi wani hasashe ba, waɗannan sune matakan farko Amina, kuma ina tabbatar miki idan kika tsallake su, dukkan sauran zasu zo ne bi da bi kuma a sauƙake..."
Zuciyarta ta gaya mata cewa wannan lokacin shine zaiyi daidai da zuwanta wajen Hajiya Kilishin, don a yanzu ne zata yarda cewa da gaske zuciyarta ta wanku wajen yarda da ita. Shi yasa ta tattaro dukkan dauriyarta ta taho cikin gidan inda Sameerah ta shaida mata cewa Mamin tana wanka.
"Kin gama? Mamin tace tana jiranki a ciki."
Muryar Sameerah ta dawo da ita zahiri, ta ɗago tana kallonta daga can jikin hanyar koridon dakin Mamin, ta san lokacin da Surayya ta tashi ta shiga ciki amma ita bata san lokacin da ita ta tashi ba, taji zuciyarta ta buga a cikin ƙirjinta amma kuma sai fuskar Amma ta gifta a idanunta ta kore hakan, ta gyara yafen mayafinta sannan ta mike a hankali tana zagaye table din da Sameerah ta cika da kayan breakfast din, kafafunta suka taja cikin korido din lokacin da Sameerah ke gaya mata cewa ta tafi ta shiga wanka, kanta kawai ta gyada mata kafin ta rike handle din kofar dakin.
Da dukkan addu'o'in da zata iya karantowa a zuciyarta ta tura kofar dakin, kuma kamshin turaren wutar da taji tunda ta shigo dakin shi ya fara shiga hancinta, ta hango shi kuwa yana ci daga can kan bedside drawer dakin daga cikin wata haÉ—addiyar burner irin wadda Sameerah ta taba kai mata.
Sai taji ta shaki wata busashshiyar iska a makogwaronta lokacin da ta hango Mamin, tayi wankan kamar yadda aka fada ta shirya cikin wata doguwar rigar atamfa da aka baza mata stones tana ta kyalli, kamar ƙyallin dake son nunawa duniya cewa ita kadai ce Kilishi irinta.
Ƙafafunta suka karaso ciki da sallama, sallamar da Mamin ta amsa da murmushi a fuskarta, murmushin nan nata mai nauyin da sai a yanzu Amina ke jinsa a saman kafadunta.
"Ashe Æ´an jigawan har sun dawo, yaya kuka tarar dashi Amina?"
Takaicin da ya taho ya taru a kirjinta wani abu ne da ba zata iya misalta shi ba, amma haka ta daurewa masa ta amsa.
"Jikinsa da sauki Mami."
Kuma sai da ta jira ta nemi bakin gadonta ta zauna sannan kai tsaye muryarta ta sake fitowa.
"Mami na yarda da dukkan zancenki, na yarda zanyi dukkan abinda zaki sani ba tare da wani ya san komai ba, dan Allah kar ki sa a sake taɓa kowa a cikin ƴanuwana, raunin dake jikin Aminu yayi yawa, dukkan kafafunsa biyu sun karye... Zanyi dukkan abinda kika ce da yanzu Mami don ni kaina ina son rayuwata ta inganta, na miƙo miki hannayena kamar yadda kika umarta don ba zan taɓa yin katoɓarar yin ganganci da rayuwar iyayena da ƴanuwana ba, darajarsu tafi komai a wajena."
Muryarta tayi shiru na wani lokaci sannan ta sake ratsa shirun É—akin amonta na rawa.
"Na rantse da ubangijin daya halicce ni Mami, zan yi miki biyayya kamar yadda kika umarta, baza ki taɓa dana sanin bayyana miki sirrina ba insha Allah."
A cikin ɗakin wani irin shiru ya sake giftawa, irin shirun nan mai tsantsar zurfi, zurfin da a cikinsa zukata ke saƙa abubuwa da yawa, kamar yadda zuciyar Kilishi ke saka mata dubunnan abubuwa a wannan lokacin yayin kallon Amina take da dukkan irin nazarin da ƙwaƙwalwarta ke iyawa, tana jin yadda a bayan kanta wasu kofofi ke buɗewa kuma tunaninta na nutsewa cikinsu na son gano wani abu daban saɓanin abinda bakinta ke furtawa.
Sai dai duk iya kokarinta, ta kasa gano abinda yake saman fuskar Aminan, a wannan lokacin, don tsoro da kuma rudanin da take gani karara suna fitowa tare da kalamanta, kuma takaicin yadda ubangiji ya biye sirrin kowacce zuciya ya kamata, don baza ta taɓa yarda kai tsaye cewa yarinyar nan ta karbi tayin ta kai tsaye haka ba, amma da yake ita Kilishi ce, sai tayi gyaran murya a hankali sannan ta faɗaɗa murmushin dake kan fuskarta, a kusa zata gane komai ba sai anje da nisa ba ta yiwa kanta wannan alƙawarin.
"Shi yasa na barku kuyi tafiyar nan dama Amina, don so nake kije ki ga É—anuwanki ki san cewa babu wasa a al'amarina kamar yadda na jaddada miki komai, kuma Alhamdlilah naji dadi sosai da idonki ya buÉ—e kika fahimci gaskiya tun a yanzu, tun kafin mu shigo da wasu cikin lissafin."
Muryarta ta fito ne da wani irin sanyi kamar ƙanƙarar dake narkewa a cikin ruwa, Kuma da faɗin hakan bata jira komai ba sai ta taso, ta wuce ta ta nufi wardrobe ɗin dake dakin. Wajen da ta bude na farko ya nuna mata ajiyar da tayi na wata bakar jaka, ta dauko ta sannan ta sake buɗe wani wajen inda jakunkunan ta suke a jere, kuma a cikin aljihun guda ɗaya ta ɗauko Sachet mai yawa na wani magani sannan ta rufe komai ta juyo, da takunta a hankali ta sake dawowa wajen da Aminan ke zaune akan carpet, inda daga gabanta akwai wani stool da aka bari a wajen, ta ajiye wannan jakar da kuma magungunan a gaban Amina sannan ta nemi kan stool din ta zauna kafin muryarta ta sake ratsa dakin.
"Komai mai sauƙi ne Amina, umarni na kawai zaki dinga bi shikenan sai duniyarki ta koma kamar aljanna, don zan cika miki dukkan wadannan alkawuran dana dsukar miki har ma da karin wasu da bamu lissafa ba, Kin fahimce ni ko?"
Kuma kamar yadda ta zata, sai ta É—ago ta kalle ta idanunta na shaida sauran tsoron da a lokacin dama ya kamata ace yana barin fuskar tata, ta gyaÉ—a kanta sau biyu sannan ta sake maida shi kasa, kuma abinda Hajiya Kilishi ta gani a idanun nata ya shiga barazanar goge kokwanton da take yi akanta, amna tayi wulli dashi a lokaci guda.
"Yayi kyau, yanzu ki saurareni sosai kiji abinda nake so dake."
Amina ta sake gyaɗa kanta tana ƙara gyara zamanta lokacin da Muryar Hajiya Kilishin ta cigaba da shiga kunnenta.
"Akwai abinda zanyi a kamfanin su Ma'aruf cikin satin nan, kuma zan yi shi ne ba tare da yana nan ba, don haka yanzu za ki taya ni abinda ya kamata ace ni zanyi don dama lokaci yayi da hakan zai koma hannunki.
Abinda ke cikin jakar nan magunguna ne, na san an gaya miki cewa Ma'aruf yana da wata rashin lafiya ta ƙwaƙwalwa, sunanta 'Bipolar Disorder' ya same ta ne a shekarun baya lokacin da rayuwarsa ta canja bayan rasuwar ɗanuwansa, cuta ce dake canja tunaninsa a duk lokacin da ta tashi, abubuwa suna cakuɗewa a cikin kansa har baya sanin abinda yake yi.
A London ake yi masa magani tun daga wancan lokacin kuma suna ɗora shi akan ingantattun magunguna tun daga sannan, amma da farko Ma'aruf bai karbi ciwonsa hannu biyu ba balle har ya dinga kula da kansa, baya taba shan magungunan sa akan kari wanda hakan ke ƙara bawa ciwonsa bigiren yaɗuwa, tun kafin yayi aure nake yi miki wannan zancen Amina kuma tun a sannan na karɓi magungunansa na ajiye a wajena.
Ma'aruf kamar ɗan dana haifa na dauke shi, kin sani tun a wancan labarin dana baki, don haka a baya na tsaya da ƙafata sosai wajen takura masa a duk lokacin da ya kamata yasha maganin, kafin daga bisani na fahimci cewa hanyar nasarata tana tattare da ikon da nake dashi ne akan magungunan sa. Ina son Ma'aruf Amina, amma son da nake yiwa cikar burina yafi karfin nasa, shi yasa nake rufe idona a duk lokacin da buƙatar in kwantar dashi ta taso min ina yin hakan."
Tayi shiru na tsawon wasu sakanni tana kallon yadda tasirin maganganun ke aiki a fuskar Amina kamar yadda ta zata kafin ta cigaba.
"Magungunan dake cikin jakar nan har America naje na nemo su Amina, magunguna ne dake birkita ƙwaƙwalwar mutum a lokaci guda ya fita daga hayyacinsa, kuma dama ciwon Ma'aruf abinda yake bukata kenan ya tashi, don haka duk sanda nake shirin yin wani abu da na san zai iya zame min ƙalubale, sai in kwantar dashi in gama duk abinda zan yi kafin ya dawo hayyacinsa."
Ta kai karshen maganar kamar bata karasa ba, don dukkansu shiru suka yi yayin da nauyin kalaman ke zagaye iskar dakin, ba irin ga Amina da taji hannayenta har rawa suke yi É—auke da sabuwar rikicewar da maganganun suka sata, don yau ne karo na farko da ta ji ciwon Ma'aruf daga makusantansa, ko shi bai gaya mata ba, cewa kawai yayi 'I'm a mess Amina...'
Zuciyarta ta ajiye komai a gefe ta shiga gaya mata cewa har ta gama rayuwarta a duniya ba zata taba iya haɗuwa da wata muguwar halittar irin Hajiya Kilishi ba.
"Na san idan Ma'aruf yayi aure dole ne zargi zai shiga zuciyar wasu idan har na cigaba da rike magungunan sa, don haka wannan yana daya daga cikin dalilan da suka sa na kawo ki gidan nan, daga yau magungunan nan sun koma hannunki.
Ki ɗauka ki tafi dasu, guda uku ne a ciki, ki ɓalli kowanne guda ɗaya ki bashi a gobe, don jibi zan fara aiwatar da abinda ke gabana kuma a sannan bana buƙatar ganinsa a kamfanin.
Wannan shine aikin ki na farko Amina, kuma idan komai ya tafi daidai, zaki fara ganin daidai bari nayi miki alkawarin farko tun a yanzu, idan na samu abinda nake so Amina zan sa a fitar da ɗanuwanki Aminu ƙasar waje a gyara masa kafafunsa su kamar yadda duke a da."
Shirun da ya sake ratsa ɗakin mai tsawo ne da babu abinda zaka tsinta a ciki kafin Hajiya Kilishi ta kai ƙarshen zancenta da magana ta karshe kuma mafi girman da daki zuciyar Amina babu zato, maganar da daga ita har Amma basu taba hango ta ba balle tasa ta a jerin tunanin Hajiya Kilishin, kuma duk da dauriyar da take da ita a lokacin sai da kalaman suka tasa allon kirjinta girgizawa da karfin da ta san har Mamin ta lura.
"Maganin dake gefe kuma naki ne Amina, ki dauka ki dinga shansa kullum, na san ba zan iya hana Ma'aruf kula ki ba idan har yayi niyya, amma kuma ba zan lazimci wani abu ciki ba don babu shi ko kadan a cikin lissafina!"
***
Yaya kuka ga sharaÉ—an farko na Kilishi??
Ta yaya kuke ganin Amina zata bullo musu??😅😅
Ta yaya zata sa komai ya faru ba tare da Hajiya Kilishi ta É—orar da zargin da take mata ba??
Mu dai jira hukuncin Amma ko??
And the Uban gaiyar is over there going crazy akan ƙafafun Amina ba tare da ya san me ke shirin tunkaro shi ba!😅
Wani ya gaya masa cewa su Rukayya ma na can nayi masa nasu shirin suma...
Jawad ma kuma yana nasa!
A tsakiyar komai kuma dai, zamu samawa Ma'aruf wannan nutsuwar da yake nema insha Allah.ðŸ˜ðŸ˜
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
SANARWA.
~~~~~~
Assalamu alaikum.
Fatan alkhairi ga tarin Masoyan FARAR WUTA da ma duk wani littafi da ya kasance nawa. A lokaci irin wannan nakan nemi kalamai in rasa, nagode da dukkan support É—in ku tun daga shafin farko na farar wuta zuwa in da na tsaya.
Ina kuma ganin tarin saƙonni da ƙorafin ku akan rashin samun update akan lokaci, ina jin kalmar HAKURI kamar tayi kaɗan, amman ita kaɗai nake da ita. Na fara littafin nan ne ba tare da na hango tarin uzururrukan da suka dinga taso mun ba, suka kuma zama dalilin rashin samun update ɗin da ba kwayi.
Na sani...
Na kuma fahimta tun kafin ku furta.
Kuyi HAƘURI, don saboda dalilai da yawa littafi na biyu (Farar Wuta 2) zai koma Paid Story cikin tsarin da nake fatan dukan mu zamu ji daɗin shi. Wanda na ɓatawa a farkon tafiyar nan zuwa yanzun, banda kalamai masu yawa sai neman afuwa da kuma bada hakuri.
Allah ya tabbatar mana da alkhairi ya kuma bamu aron lokacin sake haduwa dan karasa tafiyar FARAR WUTA.
Kar ku manta yanzu tafiyar ta fara...
Zan baku labarin yadda nasara ke samuwa babu boka ba Malam!
Zan baku labarin soyayyar Ma'aruf da wataƙila zata narkar da zuciyarku kamar ruwa.
Zan kuma baku labarin yadda mata ke samawa kansu mafita ta hanyar wayo da dabarar da Allah ubangiji ya halitta a ƙwaƙwalwar kowacce mace.
Ku tuntube ni ta wannan lambar. 08067794315.
Nagode muku fiye da yadda baki zai iya furtawa.
#AyshaShafi'ee
#fikrawriters
#FararWuta.