Complete Hausa Novels

Farar Wuta Book 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Farar Wuta Book 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 7 of 9

BABI NA SHA UKU.
~~~~~~~
There's a part of me that likes to beleive everything will be okay, then there's another that breaks down every chance it gets.
- Unknown.
**
Dukkan wata ma'ana ta mamaki da kuma tashin hankali shine yadda fuskar Amina tayi a lokacin da take kallon Hajiya Kilishi.
"Taɓa Aminu dana sa akayi tsaraba ce ga ƙwaƙwalwar ki Amina don ki saurare dukkan abunda zan gaya miki da kyau, ki yarda da dukkan kalamaina sannan kuma zuciyarki ta tabbatar da cewar Kilishin da zaki sani a yanzu da gaske take al'amuranta."
Tayi shiru bayan ta faɗi hakan hannunta na jawo wayarta da ta ajiye a gefe, babu ƙarar kiran dake shigowa alamun a silent ta saka ta.
"Ya akayi Awwalu?"
Muryar tata da ta canja tar ta tambaya cikin wayar bayan ta kara ta a kunnenta... Har a lokacin Amina bata motsa daga yadda take zaune ba, idanunta basu canja daga yadda suke kallonta ba, sannan ƙwaƙwalwar ta bata wartsake daga mamakin dake zagaye da ita ba, Ƙirjinta dake ɗagawa cikin numfashi mai nauyi shine kaɗai abinda zai sa ka san cewa idan ka taɓa ta ba zata tafi ta faɗi ba.
Wataƙila magana guda ɗaya aka fada a cikin wsyar wadda ta gamsar da Hajiya Kilishin, don bata ƙara cewa komai ba ta kashe ta kawai ta sake mayar da ita gefenta, sannan ta sake kallom Aminan, hasken fuskarta na yayewa alokaci guda
"Duk abinda zaki ji a yanzu ya zama tsakani dake ne Amina, idan ba haka ba a ƙarshen zancena zaki gane abinda zai faru idan har kika sako mutum na ukun mu a wannan zancen koda kuwa mahaifiyarki ce.
Da farko mu bar duk wani kewaye-kewaye mu tafi ga abinda yasa kika shigo gidan nan, tunda ni dake dama duk wani mai hankali mun san akwai dalilin aurenki da Ma'aruf..."
Ta gyara zamanta kaÉ—an sannan ta cigaba...
"... Cire mahaifinki ki ajiye shi a gefe, amma ko mahaifiyarki ta san ruwa baya tsami banza, a muryarta kawai na fahimci cewa irin zurfin tunaninta kika ɗauko Amina, ku duka kun san ba kowacce mace ce zata taka irin matsayin da kika taka a banza ba, zan ƙara tabbatar miki cewa shigowar ki cikin gidan nan dama cikin rayuwar Ma'aruf wani abu ne da ba don taimakona ba, ba zaki taɓa samunsa ba ko zaki mutu sau ɗari ki dawo, saboda a rana guda zamu iya samun mata dubu da zasu yarda da auren Ma'aruf ko da kuwa ciwon da yake dashi yafi haka tasiri, don ba'a  wayewar kowacce rana mata ke samun namiji irinsa ba.
Kuma shi kansa Amina, da an bashi zaɓi na sani tsaf zai kawo macen da zata fi ki a komai don irinsu kawai ya sani kuma yake mu'amala dasu, amma sai nayi amfani da ƙarfina da kuma ikona nace ke kaɗai za'a bawa wannan matsayin wanda dole kowa ya yarda da hakan, don haka duk wata soyayya da kika ga kina samu daga mutanen gidan nan dama shi Ma'aruf ɗin da ya fara saurarar ki duka saboda ni suke miki ba don komai ba, ni na ɗora su akan turbar zuciyarsu ta so ki kuma hakan ya zame musu kar dole."
A yanzu Amina tayi ƙoƙarin sunkuyar da kanta tana kallon hannayenta dake faman rawa suna kakkarwa akan cinyarta, zuciyarta na bugawa ne kamar zata faso kirjinta ta fito yayin da kowanne kalaman Hajiya Kilishin ke shiga kunnenta da tsantsar rudani da kuma tashin hankalin da akace ba'a saka masa rana.
Kuma shirun da Hajiya kilishin tayi baiyi tsawon da zata iya fitar da komai ba lokacin da muryarta ta cigaba da cewa.
"Bari in É—auko miki komai tun daga farko Amina, ta haka ne zaki fahimci zance na.
Lokacin da ina yarinya a wajen kakata na girma, ita ta raine ni tun daga lokacin yaye har girma na, a wajenta na samu tarbiyya da kuma tarin wayo da dabaru irin na zaman duniya, har yasa tun a ƙananun shekaru ina iya kallon rayuwar mutum na bashi shawara mai kyau da zata ɓulle ga matsalolin sa, hakan yasa ƙawayena dama mutanen unguwar a lokacin suka laƙaba min sunan ƴar baiwa.
Bayan wani lokaci sai wannan kakar tawa ta rasu don haka dole na koma gidanmu inda naje na tarar da tarin ƴanuwana, don mahaifinmu matansa uku ne kuma ƙaramar cikinsu wato mahaifiyata ce kawai mai ƴaƴa tara, sauran biyun akwai mai goma sha ɗaya da kuma sha uku.
Rayuwar gidanmu ba dadi sam, saboda a wajen kakata na saba komai namu mu uku ne kawai dani da ita da kuma wani almajirinta Awwalu da take riƙewa, don haka sai rayuwar gidan yawan tazo min a wuya, gashi babu ruwan kowa dani hatta mahaifiyata kuwa da hankalinta yafi karkata kan yayyena da suka fi girma a lokacin, don haka da lokacin shigata babbar sakandire yayi sai na samu mahaifina nace ya maidani makarantar kwana don zata fi mun daɗi, al'amarin kamar ba zai yiwu ba da ƙyar da rabo dai na samu na tafi.
A can na hadu da ƙawayena biyu kuma ƴanuwan da zan iya kira da na jini wato Salamatu da Saratu, wadannan mutane biyun Amina sunyi min duk wani gata a lokacin zama na a makaranta da ya kamata ace iyayena ne suka yi min, hatta kuɗin jarabawar karatuna tsaf su suka biya min har muka kammala, don ban daɗe da shiga makarantar ba mahaifina ya rasu abubuwa suka sake harigitsewa a gidanmu.
Kowacce mace taƙi fita tare da ƴaƴanta kuma aka ƙi a raba gado kowa ya koma yana zaman kansa ne da kuma zaman gasa a tsakani don kowacce mace tana so ne ace ƴaƴanta sune suka fi samun arziƙi, musamman Innata da take ganin itace ƙarama an riga an rainata ita da ƴaƴanta don haka bata damu da duk wata hanyar da yayyena ke bi su samo kuɗi ba indai za'a samun, burin kowacce kawai ace ita da ƴaƴan ta su ke ƙyallin maiƙo a gidan.
Abinda nazo na tarar kenan bayan na kammala makaranta na dawo, wani abu da tun bana saka shi a raina har ya zamo kwanci tashi nima tunanina ya karkata ga hakan, sai dai ni tawa ƙwaƙwalwar ta raina irin hanyoyin da suke bi, na kasa yarda cewa mutum ba zai iya magance matsalolin kansa a rayuwa ba sai ya tsugunna neman taimakon wani daban, don haka na shiga amfani da ƙwaƙwalwata wajen cimma manufata.
Almajirin da kakata ta riƙe Awwalu yana aikin masinja a wani kamfani, da taimakon sa da kuma dabara ta na samu aiki a kamfanin a matsayin mai gyara da kuma harhaɗa takardu... In taƙaice miki zance Amina, wata na biyu a wajen nan na fara karbar kuɗi sama da albashi na ba tare da kowa ya sani ba, kafin a shekara kuwa, ni da Awwalu muna samun daidai da abinda ma'aikatan wajen nan ke samu, ban taɓa bawa wani jikina ba sannan ban taɓa bin wani malami ko boka ba, da wayo da dabarata nake komai ta yadda babu mai zargina kuma dukkan wani bincike ba zai taɓa biyowa ta kaina ba.
Kuɗin da nake samu a kowanne wata sai da ya zama hatta a cikin gidanmu babu wanda ake kallo sai ni, mahaifiyata da ƴanuwana duk suka dawo suka raja'a a kaina, aka shiga bani wani irin girma da ban san yana wanzuwa a duniyar nan ba, ya zama zan iya taka kowa a gidanmu in zauna lafiya, nasa aka rushe ɓangaren ɗakunan mu aka gina mana danƙarere da ya tsone idon sauran ƴanuwana kafin daga baya suma su dawo su kwantar da kansu."
Muryarta tayi shiru a daidai wannan lokacin alamun ta tuna wani abu da ya saka ta murmushi, wani murmushi da har sautin sa sai da ya fito kafin tace.
"A wannan lokacin ne kuma na nemowa kaina mijin aure Amina, munyi ƙoƙarin canja kamfanin aiki ne ni da Awwalu don na yarda da karin maganar da hausawa ke cewa zama wuri ɗaya tsautsayi, don haka muka je kamfanin Bakori a wata ranar laraba, inda kafin mu shiga na hango Alhaji Mansoor ya fito daga ciki ya shiga motarsa, tun da na ganshi a wannan lokacin na sawa zuciyata cewa shine mijin aure na, don haka bamu nemi aikin ba nace da Awwalu mu juya, kuma kafin sati ya zagayo na bi hanyar da sani na ya manne a zuciyar Alhaji Mansoor.
Na kashe kuÉ—i sosai a wannan lokacin duk da ba sai na gaya miki yadda na aiwatar da komai ba zan gaya miki cewa sati guda na shafe ina siyan shafi guda a jaridar da Alhaji Masoor ke karantawa, ana wallafa hotona cikin irin ayyukan da na san dole suka ja hankalinsa.
Har da masinjan ofis É—insa da ma direbansa na haÉ—a baki dasu suna bashi labaraina, kuma bayan ya yarda da auren nawa, sai da na toshe bakin mutane da yawa wajen fallasa wani abu mummuna akaina.
Lokacin da na shigo gidan nan kuwa Amina da naga Maimuna, a lokaci guda na raina kaina na kuma ƙara yarda cewa sa'ata ce kawai ta shigo dani cikin rayuwar Baffa, don wanda yake da mata irin Maimuna babu abinda zai kaishi auren irina.
Amma ban damu sosai ba, tunda na san na shigo daular arziƙi ne kuma na ciri tuta a cikin ƴanuwana da a lokacin suka maida ni kamar mahaifinmu saboda biyayya.
Ban daÉ—e ba lokacin da Maimuna ta sami cikin Shukra Æ´arta ta uku, don haka sai nayi amfani da hali irin nawa na ja É—anta na biyu wato Ma'aruf a jikina, na so haÉ—awa har da Jamal ma amma shi da yake yafi wayo a lokacin sai ya mannewa uwarsa.
Ni na yaye Ma'aruf da hannuna Amina, ni na raine shi tun daga wannan shekarun har zuwa girmansa, don ko bayan haihuwar Maimuna bai bar wajena ba itama kuma bata yi magana ba saboda nauyi na da take ji a sannan, don a lokaci guda na zage na karɓi gidan, ni nake yin komai musamman da bata da lafiya, bayan tayi haihu kuma ni nayi ɗawainiyar da ƴanuwanta ma basu yi ba, hakan yasa a lokaci guda na samu soyayyar kowannensu, hatta Baffa kuwa, don sanda ya aure ni ba zan tantance irin son da yake min ba, amma a cikin shekara guda sai da na tabbata ni da Maimuna munyi kunnen doki a zuciyarsa.
Soyayyar kowa na siya tsakani da Allah don bana yarda da gaibu Amina, kamar yadda baba yarda da aikin wani boka ko malam da baya zuwa ko'ina, ni ina yin shiri na shekara da shekaru ne ba na wani É—an lokaci kaÉ—an ba.
A haka rayuwa ta cigaba da tafiyar mana har ta kai na fara haihuwa nima, a wanann lokacin tsananin kirki da kyautatawata yasa na kere Maimuna a zuciyar Baffa ta yadda ita kanta bata damu ba, don tana ganin cewar na cancanci hakan."
Tayi shiru wucewar wasu sakanni tana kallon Aminan kafin ta cigaba.
"Bari na gaya miki wani daga cikin babban sirrina don ki ƙara tabbatarwa cewa da gaske nake al'amarina... Nice na gurguntar da Maimuna..."
Babu shiri Amina ta ɗago ta kalle ta, idanunta na haskawa da tsananin mamakin da yake ƙaruwa akan wanda take ciki. Sai kawai tayi murmushi mai zurfi tana kallonta itama.
"Ƙwarai Amina, ni na saka Maimuna ta rasa ƙafafunta, kin san dalili?"
Ba ta bata damar amsawa ba ta cigaba.
"Na gaya miki Maimuna tana kyau, to labulen ɗaki na kawai nake ɗagawa in hango ta ranar girkinta ta nufi ɓangaren Baffa, idan tayi kwalliyar nan bana iya daurewa kishina dake tasowa Amina, rana daya na yanke cewar ba zan iya jurar cigaba da ganin zuwanta ba don haka takanas na tafi asibiti na samu wani ma'aikaci a ɓangaren ƙashi, na bashi maƙuden kuɗaɗen da a lokaci guda ya bani wani magani mai kama da poison wanda ke lalata har ƙashin mutum.
Kuma sai da na jira har bayan watanni huɗu da rashin lafiyar zazzaɓi ya kamata sannan na haɗa baki da wani yaro daga Nijar yazo har gida yayi mata allurar maganin nan a matsayin likita, kuma babu wanda ya san ni na dauko shi don nambarsa na sanya a wayar Baffa da sunan likitan gidan Dr. Ashiru, nace idan yazo yace Dr. Ashirun ne ya turo shi.
Kuma bayan yayi mata allurar ƙafafun nata sun lalace gabaɗaya na bashi kuɗi ya koma ƙasar sa Nijar, shi kuma Dr. Ashiru yazo yace bai san yaron ba, da aka duba lambar aka ga ma ba tasa bace dole aka haƙura don ko ƴan sanda basu iya samo komai ba.
Kuma bayan haka ni na zauna nayi jinyarta Amina, tun kafin a yanke ƙafafun har muka je India aka cire su gabaɗaya, shekara guda da rabi na ɗauka ina jinyarta, na hana kowa wannan ɗawainiyar hatta ƴaƴanta da ƴanuwanta tunda na san na samu abinda nake so, na san tsawo na da nata ba zai taɓa daidai a idanun Baffa ba, kuma hakan ya ƙara min ƙima a idanun kowa a gidan nan ta yadda nake cin kare na babu babbaka, kowa yana girmama ni da bani darajar dana siya a wajensu, hatta ƴaƴan Maimuna a idon kowa kamar nawa suke don babu adadi su  Munaya zasu zo su faɗa min abinda mahaifiyar tasu ma baza su iya faɗa mata ba ko kuma su nemi shawarata akan abinda ita bata ma sani ba.
Don haka yanzu na san kin fahimci cewa saboda ni kika samu soyayyar kowa gidan nan, da kuma abinda nake nufi cewa duknwanda kika furtawa wannan zancen kamar kin bude masa kofar lahirarsa ne."
Muryarta tayi shiru a wannan lokacin,  wucewar wasu sakanni sai kuma ta taso a hankali ta dawo kujerar kusa da inda Aminan ke zaune, kuma bata damu da rashin kallonta da har yanzu bata yi ba ta cigaba.
"Mu dawo kan abinda ya kawo ni, dalilin da yasa na aura miki Ma'aruf Amina, kamar yadda na faɗa ba don ki zo kiyi rayuwar zaman aure bane kamar yadda naga kin fara kokarin yi a yanzu, na kawo ki gidan nan ne saboda ki taya ni mu ƙarasa babban burin da nake dashi a duniya.
A farkonsa ban tsara dake ba, amma daga ranar da Baffa ya yanke shawarar cewa dole Ma'aruf ya ƙara aure, daga ranar kika shigo cikin lissafina Amina, don Ma'aruf ginshiƙi ne guda a cikin burin da nake son cimmawa a yanzu, ina ɗora shi ne akan matakan da zasu kaini ga yin nasara ɗaya bayan ɗaya, don haka idan har aka samu matar da zata raɓe shi wadda ba zan iya juyawa ba Amina abubuwa zasu lalace min ba kaɗan ba, shi yasa tun kafin kowa yayi wani yunƙuri musamman mahaifiyarsa dana san a tarin ƴanmatan dake danginsu zata iya haɗa shi da wata, na duba bayana na zaɓo ki."
Sai da ta sake gyara zamanta tana fuskantar Aminan dake zaune a gabanta ta sunkuyar da kanta sannan tace.
"ÆŠago nan ki kalle ni Amina..."
Ta kuwa ɗago da kan nata amma bata kalle ta ba, gashin idanunta sun hade suna shaida jiƙewar hawaye alamun kuka take yi, wani murmushin yaso giftawa a leɓɓen Hajiya Kilishin amma ta tare shi, don da kukan Aminan da kuma shi ɗin, duka bata ga muhallinsu a yanzu ba.
"Sati guda zan baki kiyi tunani, idan har kika yarda dani, zan ƙawata rayuwarki da dukkan ƙawar da baki taba tunani ba Amina, zan miki liƙin alheri har sai hannayenki sun kasa tarewa, zan ɗaga ki ki zama tauraruwa a idon kowa musamman cikin danginki, zan kyautata rayuwarki da ta dukkan makusantanki idan har kika miƙo min hannunki na kama kamar yadda na tsara komai..."
Ta sake yin shiru tana kallon haɗewar gashin idon nata, sai kawai ta haɗiye yawun dake bakinta sannan ta ƙarasa furta abinda ke tahowa tun daga ƙasan zuciyarta, abinda take jin ko da duniya zata taru akanta ba zai canja ra'ayinta ba.
"... Idan kuma har kika zabi yin katoɓarar fallasa ni don ki tsira, na rantse miki da ubangijin da ya halicce mu rayuwarki zata dulmiya ne a baƙin ruwan da zaki yi ta yin ihun da babu wanda zai taɓa jiyo muryarki!"
***
Tun da ya shigo gidan jikinsa ya bashi akwai wani abu da ya faru, don fitilar falo ma a kashe take, iya hasken ta korido ne  kawai yake a kunne, a falon ya ajiye wayoyinsa da su kaɗai ne a hannunsa sannan kai tsaye ya nufi hanyar koridon, ɗakinsa yayi niyyar wucewa ya watsa ruwa don Allah ya sani a gajiye yake, amma a lokaci guda idanunsa suka kai kasan ƙofar dakinta da nan ma fitilar a kashe take.
Har ya wuce ya dawo ya tsaya ya kwankwasa, kusan sau uku amma shiru bata amsa ba, sai yayi tunanin sallah take don a lokacin masaltai ke kiran isha'i, don haka sai kawai ya juyo ya dawo É—akinsa.
Ya kunna fitulun ciki da suka gauraye da haske a ɗakin komai yana fitowa tar cikin kammalen da yake. Ma'aruf yana da tsaftar da duk wanda ya zauna dashi zai gane, don indai abu nasa ne to ba zaka taɓa zuwa kaga komai ba'a muhallinsa ba, sannan kuma yana da haƙurin da zai zauna da wanda bai damu da hakan ba, shi yasa ya iya zama da Ishaq dake wular da komai inda yaga dama.
Minti goma kawai ya ɗauke shi gama shiryawa cikin wasu kayan bayan yayi wanka, ya dawo falon daidai lokacin da wayarsa ke ƙara a inda ya ajiye ta, lambar mutumin da yasa ya nemo masa bayani akan Mr. Okafor ne, ya tsaya kawai yana kallon kiran ba tare da ya dauka ba har ya katse sannan ya tura masa dan guntun saƙo cewar suyi magana zuwa gobe.
A yanzu ya sani cewar  tarawa kansa abubuwa yana ɗaya daga cikin abinda ke saka shi damuwa har ciwonsa ya tashi don Allah ya sani a yanzu yana tsoron ciwonsa fiye da kowa, ya sani cewa idan abubuwa suka lalace masa a yanzu bai san me ya cimma a rayuwarsa ba. Shi yasa bai ɗauki kiran mutumin ba, don a yau kaɗai abubuwan da ya fuskanta suna da yawa.
Takardar sammacin da ya samu ɗazu a Office ta girgiza shi ba kaɗan ba, ya kasa hango inda Rukayya da iyayenta suka samu karfin gwiwar kaishi kotu akan zancen Hamida, kalaman Baffa su suka bashi damar ƙin saurararsu amma bai taba tunanin hakan daga garesu ba. Ya kira Ishaq sunyi maganar amma duk tsawon tattaunawar su ya gaya masa cewa chance din da suke dashi kaɗan ne don a matsayin Hamida na mace dole ne a wajen mahaifiyarta ya kamata ta zauna har girmanta kuma ƴan bayanan da suke dashi game da dalilin su na dawowarta wajensa basu da karfi sosai.
Sannan bayan yayi haka ya san yayi aiki a Office din amma ya tabbata idan ya koma gobe zai samu kura-kurai da yawa, don a cikin aikin ya gama yanke dukkan abinda ya riga ya tsara game da zancen kotun da kuma Hamida.
Kuma baya buƙatar yin zancen da kowa shi yasa ko cikin gida bai shiga ba tunda Baffa baya nan yayi tafiya Abuja, yaga kiran Mami amma shima bai bi bayansa ba kuma itama bata sake kiran ba har yanzu.
Ƙafafunsa suka sake komawa kitchen ɗin bayan ya kunna fitila yana nazarin komai, akan table ɗin kitchen ɗin, jerin kayan abincinsa ne kamar yadda take tsara su kullum, yaji wani abu ya zarce cikin makogwaronsa, a cikin ƴan kwanakin nan ya sani cewar yarinyar nan ta taimakawa ƙwaƙwalwar sa wajen samun hutu ta wani ɓangaren, don akwai nutsuwa sosai ace idan aiki ya zuƙe shi da rana akwai inda zai iya zuwa ya huta ba wannan hargitsatsen gidan nasu shi da Ishaq ba. Kamar ya zauna yaci abincin sai kuma kawai yaji ba zai iya hakan ba alhallin bai ganta ba.
Sai kawai ya zaro wayarsa ya kira lambar Samirah, bugu É—aya biyu kuwa ta dauko, muryarta a ciki ta fara cewa 'To Mami.' kafin tayi sallama.
"Yaya barka da dare."
"Kun yini lafiya?"
"Lafiya ƙalau."
Ta amsa sannan tayi shiru tana jiran abinda zai faÉ—a a gaba, kuma hakan kaÉ—ai ya bashi amsar da yake nema cewa Aminan bata ciki don haka kai tsaye yace.
"Sai da safe."
Ya kashe wayar ya zura ta a aljihunsa sannan ya koma cikin gidan, ɗakinta da bai shiga ba a yanzu shi ya nufa kuma bai jira komai ba ya buɗe shi, fitilar a kashe take kamar yadda ya gani sai dai babu duhu a ciki don hasken fitilar waje na shigowa ta windon ciki, kuma a lokaci guda idonsa ya hango masa ita, tana zaune daga gefen gadon ɗakin ta ɗora kanta akan gadon yayin da jikinta yake a dunƙule, kamar dai ranar daya fara ganinta, ranar da ya fara ganinta a matsayin matarsa.
Wannan shine karonsa na biyu shigowa É—akin kuma ya sake tarad da ita a irin wannan yanayin da ya san cewa tabbas akwai abinda ya faru. Hannyensa duka biyun suna cikin aljihu, sai ya fito da É—aya daga aljihunsa ya sosa kan hancinsa yana kallon idanunta da suke a rufe.
"Assalamu alaikum." Muryarsa ta ratsa É—akin cikin amonta.
Kamar wancan karon ta dago kanta da sauri ta kalle shi amma bata mike ba, kallonsa take yi cikin hasken ɗakin wucewar sakanni biyu kafin bakinta ya amsa sallamar tana ƙoƙarin dagowa daga kishingiden da take.
Sai kawai ya juya ya koma ya kunna fitilar dakin, haske ya gauraye koina, yana nuna masa kumburarrun idanunta da tabbas kuka tasha dasu.
"Me ya faru? Me ya same ki?"
Tambayar ta fito sak kamar ranar da ya ganta cikin daren nan, amma wannan karon sai yaji abinda yake son tambayar yafi hakan, zai iya jero kusan guda goma don ya samu gamsashshiyar amsa.
"Babu komai."
Ta fada tana ƙoƙarin juya kanta gefe don naɗe sallayar da take kai, yana iya ganin dogon hancinta wanda da alama ta murza shi fiye da kima.
"Kayi hakuri, ban ji lokacin da ka shigo ba, barka da dawowa..."
Muryarta ta faɗa sanda ta gama ninke sallayar ta miƙe tsaye tazo zata wuce shi, amma sai kawai ya riko hannunta na hagu ta baya ya tsayar da ƙafafunta.
Ba shiri Amina ta cije lebbenta tana kallon tiles ɗin dake ƙasan dakin, gayawa zuciyarta take yi cewa ta daurewa wani kukan dake shirin tasowa a ƙirjinta amma sakon baya tafiya sam, don lokacin da ya jawo ta baya ta dawo gabansa ƙwalla ta sake cika idanunta taf.
A yau ɗaya rayuwarta ta canja, ta shiga tashin hankalin da bata san da me zata kwatanta shi ba, a cire mamakin halayen Hajiya Kilishi daya nade zuciyarta a gefe, tsoro da taraddadin hatsarin da ta kawo kanta cikinsa ya hargitsa kowanne abu mai kyau na tunaninta, tana tuna kalamanta, tana tuna ranar da ta yanke hukuncin karɓar auren nan, da wani zai gaya mata da wani abu ko da makamancin haka ne... da tabbas labarin zai canja daga yadda yake yanzu.
Ita bata san ma me take ji ba, bata san yadda zata fassara halin da take ciki ba, kawai dai ta sa zuciyarta ta karye da kowanne abinda kalaman Hajiya Kilishin ke nufi, kuma shi kansa Ma'aruf É—in ma a yanzu bata yarda dashi ba, don bata san me Hajiya Kilishi ke nufi da 'matakan da take É—ora shi akai don tsarinta ya tafi daidai ba.'
Zuciyarta tayi rauni da yawa ta yadda fuskar Aminu ce kawai ke yawo a kanta da tunanin halin da yake ciki, shi yasa a  karo na farko tun bayan ranar da aka kawota gidan, hawaye ya kasa tsayawa a idanunta, don a wannan lokacin tana jin cewa kukan shine kawai sauƙin abinda take ji a kirjinta.
"Ki gaya min abinda ya faru da kuma dalili da yasa kike kuka."
Ma'aruf dake riƙe da hannunta ya fada da muryarsa cike da ikon dake nuna mata cewa da gaske yake yi, sai tayi ƙokarin maida kukanta ta hanyar share idanunta da ɗaya bayan hannunta sannan ta shiga gyara tsayuwarta don ji take kamar zata fadi.
"Me ya same ki Amina?"
Bai gaji ba ya sake tambaya a lokacin da take jin kamar ƙamshin turarenta na kassara kasusuwanta ne, bata da wani zaɓi da ya wuce ta lalubo wani sauti daga can ƙasa maƙoshinta idanunta har yanzu suna ƙasa tace.
"Aminu ne ya gamu da hatsari, yana asibiti tun jiya."
"Ya salam, Ya salam, wane asibiti ne?" Bai san waye Aminun ba, amma ya fahimci É—anuwanta ne.
Ta girgiza kanta wani kukan na shirin ƙwace mata.
"Ban sani ba, muna waya da Amma sai... Sai wayar ta É—auke."
Zancen ya fito daga can ƙasan maƙoshinta ba tare da ta tsara shi ba.
Sai kawai yasa ɗaya hannunsa da baya rike da ita ya zaro wayarsa daga aljihu, santsinta ya biyo hannyensa yayin da ya kunna password ɗin da yatsansa sannan ya shiga wajen dial log kafin ya miƙo mata.
"Ki kira ta sai muji wane asibiti ne?"
Sai a yanzu ta ɗago ta kalle shi kuma kafin tayi saurin sake maida idanunta ƙasa, ya gani cewa har yanzu kwalla ce taf a cikinsu, a hankali nata hannun suka karbi wayar don babban abinda take bukata a lokacin kenan, kuma ga mamakinsa bata matsa ba ta shiga danna nambar wayar Amman.
"Assalamu alaikum."
Sautin muryar mahaifiyarta da ya fito ta ciki yasa a yanzu ƙwallar idanunta ta gangaro... Karo na farko a duniya taji so take ta ganta a gabanta wannan lokacin ta rungume ta, so take ta cusa kanta a jikinta ta rera kukan da har yanzu take jin nauyi ta a ƙirjinsa, ta gaya mata cewa tayi nadamar ƙin gasgata maganganunta, don abinda ya shigo cikin rayuwar tasu yanzu wani abu ne da duk ƙarfin hangensu basu gano ko rabinsa ba, wani tashin hankali ne da ya tsallake dukkan tunaninsu.
A yau ta ƙara yarda da zancen Amma na cewar babu wani auren gaske tsakanin mai kuɗi da talaka a wannan zamanin, indai ya faru to tabbas akwai wani boyayyen abu dake ƙasa, Amma tace rayuwarki zaki sadaukar musu Amina, ashe su duka basu sani ba cewar bayan tata rayuwar suma tasu ta shigo ciki wataƙila har da sunan duk wani da ya rabe su ma.
"Amma, Amina ce."
Muryarta ta fito tana kakkarwa kamar yadda hannunta keyi acikin nasa.
"Amina... Amina." yadda muryar Amman ta kira ta a jere da wani irin sautin ajiyar zuciya yasa lebbenta talewa cikin kokarin wani kukan.
"Me ya faru É—azu wayar ta dauke? Mun gwada yafi sau hamsin kuma bata shiga ba. Har Hajiya Kilishi na kira ita kuma ba'a dauka ba?"
Sai da ta hadiye wani abu a ƙirjinta jin sunan Hajiya Kilishin  sannan ta iya cewa.
"Amma wayar mutuwa tayi kawai, kuna ina yanzu? Ya jikin Aminun?"
"Gamu nan mun dawo gida don Baba yace bai yarda yayi zaman asibitin ba, yanzu dai sunyi masa abinda zasu yi masa mun dawo gida, gobe kuma zamu tafi jigawa gidan wannan  ɗanuwansu Fatiman mai gyaran karaya, saboda duka ƙafafun nasa biyu sun karye Amina."
Sautin kukan da ya fito daga bakinta shi yasa Amman cewa.
"Ba kuka zaki yi masa ba Amina, addu'a zamu yi Insha Allahu zai samu sauƙi don ance shi mutumin ya iya aikinsa, ba za'a haɗa dana asibiti ba."
Muryar Amman dake lallashinta itama a karye take kawai, ta sani suna da kuma matsayinta na Uwa shine abinda ke rike ta daga nata kukan.
"Ku duka zaku tafi Amma?" Tayi ƙokarin tambaya ta cikin kukan muryarta a rarrabe.
"A'a, dani da Baba da kuma Fatiman da zata kaimu gidan zamu tafi, su Maryam suna nan saboda makaranta, ita kuma Hajiyan Fatiman saboda jinyar Inna (kakar Fatiman) ne ba zata samu zuwa ba."
Sai da tayi wata ajiyar zuciya mai nauyi sannan tace.
"Ina Aminun?"
"Bacci yake Amina, tun jiya sai yanzu bayan magaribar nan sannan ya samu baccin, idan ya tashi na kira ki, wannan nambar waye?"
Bata amsa ba don bata san me zata ce ba, kuma shirunta ya bawa Amma amsarta don haka sai tace.
"Addu'a zaki yi tayi masa Amina, kowanne ɗan adam baya wuce ƙaddararsa, komai zai zo da sauki insha Allah."
Kalaman kaɗai sun isa su kara tsoratar da Amina, don ta san idan har Amma zata faɗi haka to al'amarin ba ƙaramin abu bane, don komai tsananin rashin lafiyar mutum Amma bata zuzuta shi haka, balle ma akan Aminu da yake namiji, don haka bata san lokacin da bakinta ya ƙara talewa da ƙoƙarin yin kukan da har yanzu take dannewa ba.
"Zan saka Maryam ta kira ki da safen kafin mu tafi, su can gidan Kawu Malam zasu koma kafin mu dawo."
Ɗaga kai kawai take kamar Amman na kallonta yayin da sautin kukan ke shaƙewa a ƙirjinta yana fitowa a kakkatse, Allah ya sani rabonta da irin wannan kukan tun Maryam bata da lafiya, lokacin da aka nemi kuɗin maganinta aka rasa, tana kallonta a kullum tana tunanin mutuwa zata yi.
Ma'aruf yasa hannu ya karɓi wayar daga wajenta  bayan sunyi sallama, ya maida ita aljihunsa, bata kalle shi ba har yanzu tasa bayan ɗaya hannunta tana ƙoƙarin share hawayenta, da hannun da ya mayar da wayar ya sake riko ɗaya hannun nata ya tsayar da ita daga goge hawayen, sannan a lokaci guda ba tare da ta ankara ya jawo ta jikinsa, karo na farko ya rungume ta, hannunsa ɗaya ya zagayo wajen ƙugunta yayin da kanta ya samu mazauninsa a kusa da wuyanta.
"Kar ki maida shi zai cutar dake... Just let it out."
Muryarsa ta faÉ—a a cikin kunnenta da wani sauti daya shiga dagargaza dukkan wata jijiya ta dauriya a jikinta.
Kuma a karo na farko Amina ta manta komai akan Ma'aruf ta sunkuyar da kanta a jikinsa don babban abinda take buƙata kenan, kukan da sautinsa kaɗan ne ya suɓuce daga bakinta yayin da jikinta ke girgizawa a cikin hannunsa.
***
Bayan kwana biyu.
"Kin shirya?"
Ma'aruf ya tambaya yana kallon Amina data fito riƙe da wata ƴar ƙaramar jaka a hannunta da kuma wani madaidaicin basket, doguwar riga ce a jikinta ta baƙar abaya, ta yafa baƙin mayafin kawai akanta ba tare da ta saka ɗankwali ba, tana tsaye daga hanyar koridon dakunan tana cakuɗa yatsunta cikin junansu, har yanzu ta kasa yarda da abinda yazo dadaddare ya gaya mata jiya cewa ta shirya zasu je jigawa a yau.
Jiya da safe a wayar tasa suka yi waya da Amma ta shaida mata lokacin tafiyarsu wanda bayan hakan tayi ta binsa da kallo tana so taji yace wani abu amma bai faɗa ɗin ba har ya fita, ya barta a zagayen halin da take ciki, kuma Allah kaɗai ya san yawan abubuwan data saka ta kwance a cikin kanta a jiyan wanda duk iya tunanin nata yana ƙarewa ne a gaɓar da bata san yadda zata yi ba.
Haka ta yini har a jiyan tana share hawaye duk lokacin da ta tuno cewa duk irin halin ciwon da Aminu ke ciki saboda ita ne, saboda itan da bata san yadda zata budi baki ta gayawa wani ba, ko da Ma'aruf É—in ne kuwa tunda shi kansa babu alamun yana da wata masaniya irin wadda ita ta sani yanzu akan Mamin, duk da cewa bata gama sanin ainihin abinda take nufi game dashi ba ko kuma shi nasa ra'ayin akanta.
Sai da daddare bayan ya dawo ne kawai yace ta sako mayafinta zasu shiga cikin gida, wajen Mami suka fara zuwa kamar yadda suka zata, kuma gaishe ta kawai suka yi kafin ya furta abinda yasa kowannensu mamski daga ita har Hajiya Kilishin.
"Gobe zamu wuce Jigawa Mami, na san kin samu labari, brothern ta ne ya gamu da hatsari zan kaita ta dubo shi."
Har yanzu tana jin nauyin yadda idanun Hajiya kilishi suka dinga kallon fuskarta, tana jin tafiyarsu a ko'ina na fuskar tata, yadda ta dinga kallonta da wani irin yanayi da yake nuna mata cewa itama a lokacin taji zancen, da kuma yadda tata zuciyar ta dinga bugawa har sai da taji kamar ta tsugunna ƙasa ta ɗauko ta lokacin da suka miƙe tsaye, don tsabar tsoro ƙirjinta fayau ta dinga jinsa kamar yadda jikinta ya zama kamar fallen takarda har lokacin da suka tafi ɓangaren Hajiya Maimuna, idan acan ma suka sha addu'ar Allah ya kiyaye hanya kamar yadda Mamin tayi tata.
Jiya haka ta kwana tana juyi akan gado, da asuba kuma tunda tayi sallah bata koma ba, don yace mata ƙarfe takwas zasu tafi a yau ɗin zasu je su dawo kamar yadda ya tsara.
Abincin breakfast ɗin da tayi ma bai ci ba don yace mata azumi yake yi kasancewar ranar Alhamis ce. A yanzu ya shigo daga wajen maigadi ne da ya gama wanke masa motarsa, yana tsaye daga bakin ƙofar falon yayin da karar yadda maigadin ke share ruwan wankin motar daga waje ya cika falon.
"Kin shirya a haka?"
Ya ƙara tambaya yana kallonta, sai ta sunkuya ta kalli kayan jikinta sannan ta dago ta kalle shi tace.
"Eh na shirya."
Shi nasa kayan dogwaye ne kalar sararin samaniya, ya saka hula wadda ta dace dasu, da ace zuciyarta a nutse take ta sani tsaf zata tsaya yabawa yadda kayan suka karɓe shi amma a yanzu ba abinda ke gabanta kenan ba, tashin hankalin dake kwance a ƙasan zuciyarta ya isa ya binne ta da ranta. Sai kawai ya taho gabanta riƙe da mukullin motarsa a hannu, kuma bata matsa ba, don watakila a yanzu ta saba dashi a kusa da ita, kar a lissafa da shekaranjiya lokacin da ya rungume ta, wannan don ba'a cikin hayyacinta take ba kowannensu ya sani.
Hannunsa taji ya sauka akan gashinta da ya fito ta gaba kafin yace.
"Shi wannan ba'a rufe shi?"
Zuciyarta ta buga yayin da wani abu ya tsarga tun daga saman kan nata har zuwa tafin ƙafafunta amma ta haɗiye shi, sai ya matsa baya kadan sannan yaba cigaba da kallonta yace.
"Bana son wani yaga gashinki."
Bata É—ago ta kalle shi ba amma kalaman sun daki zuciyarta ta yadda duk tarin hargitsin dake ciki sai da suka girgiza. girgizawar da bata yi tunanin zuciyar tata zata yi ba a yanzu tare da abinda ya faru game da ita.
A hankali ta juya ta koma ɗaki, wani pink dankwali ta ɗauko ta daura, ai kuwa ya hau sosai da kayan ya ƙara haska fuskarta, wanda bata ko gani ba ta sake ɗaukan ƴar ƙaramar jakarta da kuma wannan basket din ta fito, sai da ta tabbata ta kashe fitulu da switches ɗin ko'ina, na fridge kawai ta bari sannan ta fito.
Yana tsaye daga bakin barandar falon yana jiranta, wani guntun murmushi da yayi mata yasa gumi fitowa a tsakanin yatsunta kafin ta bashi waje ya kulle ƙofar gidan, kuma juyowar da yayi yasa shi tsayawa dab da ita, wanda kafin tayi tunanin yin gaba idonta ya hango mata wasu manyan ledoji akan booth ɗin motarsa.
"Mami ce ta aiko a kawo miki, yanzu muka yi waya tace ki kai musu." Muryarsa ta faÉ—a dab da bayanta.
Zuciyarta ta buga a ƙirjinta, hannayenta suka fara rawa riƙe da kayan nan, ta sani bana tasirin muryarsa ne kaɗai bane har da na sunan Hajiyan Kilishin daya furta. Numfashinta ya shiga kakkatsewa a kirjinta ta yadda tayi tunanin zai iya jinta amma sai taji lokacin da yayi baya ya ɗauki waya yana cewa.
"Zuwa 10 zasu iso Faruk, idan kana ƙaunar Allah ka tabbata kana nan..."
Sai kawai tayi ƙarfin halin motsa kafafunta ta tafi wajen motar, ta isa wajen daidai lokacin da idonta ya nuna mata sauran kayan daga gefen motar, buhun shinkafa guda biyu da jarkokin mai suma guda biyu.
Ta haɗiye wani abu a maƙogwaronta kafin ta ajiye kayan hannunta, ta buɗe ledar farko inda kayan tea manya-manya gwangwanayen su Madara ya shiga idonta, a ɗaya ledar kuna wani ƙaton food flask ne shi kadai mai faɗi, taji har a lokacin hannunta na girgizawa a hankali sanda ta buɗe shi, kuma tun kafin ta gani ƙamshin wani farfesun naman kaza ya cika hancinta, shine fal ya kusan cika flask din har baki.
Ba shiri ta rufe idanunta tana jin koina a jikinta na girgizawa. Fata take da dukkan imaninta cewa Allah ya kawo mata mafita akan matar nan.
"Ya ubangiji kaine tanadin kowanne bawa idan ya fada masifa, Ya Allah na miƙo maka hannaye na ka taimake ni akan wannan al'amarin da yafi ƙarfina, ba zan iya ba ya rabbi! Bani da wata mafita da wata dabara wadda ta wuce taka ya Allah."
Wani lokacin bawa yana yin addu'a ne akan gaɓa, wani lokacin ubangiji yana amsa addu'a ne a take! Kuma komai yana da tushe yana da asali, kamar yadda tafiyarsu Jigawa ke shirin zama tushen faruwar abubuwa masu yawa.
Kuma rashin sani yana É—aya daga cikin raunin É—an Adam!
***
Waye yake cikin wannan rashin sanin ne?
A cikin dukkan wannan hargitsin, me yake jiran mu a jigawa ne?😉
Wace mafita Amina zata samu game da Hajiya Kilishi kafin zagayowar sati guda?
A yau kun fara jin tarihin Hajiya Kilishi!😰
Ku shiryawa abinda ke faruwa daga ɓangaren Ruƙayya.
Har da Jawad ma.😅
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.