Complete Hausa Novels

Farar Wuta Book 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Farar Wuta Book 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 5 of 9

BABI NA TARA
~~~~~
Let's go back to when we had not learn our names, when we introduced our souls, while our heart gasped for breaths. -Aliyu Jalal.
*
A cikin sabon gidan mutane sun fara raguwa sosai, ba kamar a ɗazu da koina yake a cike da mutane ba, Aunty Safiyya ta taho daga hanyar falo ta biyo wani ɗan dogon korido mai ɗauke da ɗakuna ta shigo ƙofar ɗakin dake gefe, a cikin ɗakin duk ƴan uwa ne na kurkusa sai kuma amaryar dake tsakiya kanta a sunkuye tana faman kukan da babu sauti sai hawaye kawai da take sharewa.
Aunty Safiyan da ta shigo tace.
"Na rasa yadda akayi aka manta da tsitsiyoyin nan wallahi, yanzu da ba sai a share gidan ba kafin mu tafi."
"Aunty ai na zata sharar dare babu kyau."
Ummi dake kokarin dora akwatuna can saman wardrobe din dakin tare dasu Momi ta fada tana juyowa.
"Wannan ai kamawa tayi..." Cewar Aunty Ma'u.
"Baki ga falon nan ba duk kasa ce wallahi, don bana ji akwai wanda ya shigo babu takalmi."
"Ni maigidan ma nake ji, haka zai shigo yaga waje duk ƙura?"
ÆŠaya daga cikin matan Baban Kurna tace.
"Da za'a iya tunda akwai kofa ta baya sai a shiga gidan a tambayo su wallahi.
Mahaifiyarsu Ummi da itace zaune a gefen Amina rike da hannayenta ta girgiza kai tace.
"A hakura kawai, gobe da safe insha Allah sai su Maryam su zo su kawo mata kawai, su taya ta sharar ma."
Ta fada tana kallon Maryam din dake tsugunne a gaban Amina ta riko É—aya hannunta.
"Ɗan kunnayen nan naki suna cikin wata ƴar ƙaramar jaka pink, ina jin a cikin wata Ghana must go aka saka."
Cewar Maryam din tana kallon idanun Aminan da duk yadda suka yi ja saboda kuka wannan kyallin na cikinsu na nan. Ta san ba zata amsa ba saboda haka ta cigaba da cewa.
"Hijaban sallarki ma suna cikin wannan karamin akwatin na undies, Amma ce tace in sa miki anan."
Sai ta gyada mata kai kawai tana ƙara share hawayenta lokacin da Aunty Safiyya ke tambayar su Ummi idan sun kwashe kayan cikin akwatunan kafin su dora su.
"Duk mun zuba su a cikin wadrobe ɗin, na kayan kwalliyar nan ne da kuma wannan Ghana must go ɗin zamu bari a ƙasa.
"Eh, ku barsu ta gyara ta kanta, sai ku zo mu tafi kuma don goma ta wuce."
Jin haka yasa Fatima ta taho daga wajen su Ummin tana ƙarasowa gaban Amina, lokacin da Maryam ke cewa.
"Idan zamu zo goben zamu zan taho da Hafsa insha Allah."
Fatiman ta sunkuyo tace.
"Amina litattafan nan naki ba'a É—ebo ba, sai dai daga baya ko Aminu ya kawo miki."
Sai a lokacin ta ɗago da idanunta ta kalle su, me yasa ne suke ta yi mata zancen kaya bayan ba abinda ke gabanta kenan ba? Mantawa suka yi cewa tafiya zasu yi su barta? Su barta a wannan wajen da bata san makamar abinda zata fuskanta ba, ko Abdallah ta aura ai dai sun san cewa wannan lokacin mai ciwo ne a wajenta, balle kuma mutumin da bata san ya yake ba balle takamaimai halinsa. Aunty Ma'u ta miƙe tsaye tana gyara mayafinta tace.
"Sai hakuri Amina, kin ji dai duk nasihar da akayi miki daga can gida, sannan su ma iyayen mijin naki kinga yadda suka karɓe ki, sunce ƴa suka karba ba suruka ba tunda dama duk ɗaya ne, kuma kowa ya san halinki Amina, duk wanda ya sanki yabonki yake yi... Mutanen nan sune basu sanki ba, kuma yanzu ne mafarin zamanku, dan Allah ki ɗorar da halinki a wajensu Amina... Don wannan gaɓar itace mafi alkhairin rayuwarki, ki sa su zasu zo suna bamu labarin kyautatawarki..."
Ba shiri Amina ta sake fashewa da wani sabon kukan da ya nemi mazauninsa a zuciyar duk wanda ke É—akin, taji zuciyarta na sake karyewa da tausayin kanta, kalaman suna tuna mata da na Gwaggo Balkisa a dazu kafin tahowarsu, É—akin Amma da suka cika aka kaita don ayi mata wannan fadan na al'ada, kuma sai da kowa ya gama nasa sannan ita Gwaggon ta kamo hannayenta duka biyu tace.
"Amina kin sani cewa daga yau sabuwar rayuwa zaki fara wadda babu iyayenki bale kuma sauran ƴanuwanki a kusa, zaki zama ɓarin wani mutum daban da zai bukaci tsananin kulawarki,
Kiyi amfani da hankalinki da kowa yake yabo ki zame masa mata kuma Uwa, ki kokarin zame masa komai a rayuwa ta duk wata hanyar da zaki iya.
Ba abu ne mai wuya ba Amina, don maza banbancin su kadan ne dana yaro ƙanƙani, kulawarki kawai yake buƙata sai ki ganshi a tafin hannunki. Kar ki dauki kulafucin barin gida ki sa a ranki fiye da ƙima, shima nasa iyayen zai bari yazo ya zauna dake, banbancin kawai shi namiji ne da zai daure ke kuma mace ce, ki saki ranki ki saba da sabuwar rayuwar da zaki fuskanta don itace rayuwarki ta yanzu dama ta gaba.
A kowanne aure akwai sirri Amina, ki riƙe sirrin gidanki ki riƙe sirrin sa, ki zauna lafiya kamar mahaifiyarki, kina ganinta dai shekaru fiye da ashirin kenan da muka kai ta daki amma daidai da rana guda bamu taba jin bakinta ba. Kiyi wa mijinki biyayya, ki girmama shi, idan kika yi haka kema kin girmama kanki.
Mace mai wayo ita ke gina gidanta Amina, sakarya kuma da hannunta take rusa shi."
Don haka a yanzu ma da Aunty Ma'u ta fara sai taji kukan da ta sha ɗazu ya sake dawo mata sabo. Fatima ta taho ta rungume ta daga tsaye tana gaya mata abinda kowa ke faɗa, cewa tayi haƙuri, kuma sai su Ummi ma suka karaso suna tayaa ta, tanajin yadda kukan bata ke jijijiga jikinsu kafin Aunty Safiyya tasa su suyi gaba.
"Wannan shine dakin da muka kawo miki kaya, watakila zaki ga sauran biyun dake gefe sun fi shi kyau, amma kiyi zamanki a cikinsa Amina, don shine mutuncinki."
Aunty Safiyya ta raÉ—a mata a kunne lokacin da kowa ke mata sallama, kuma tana ji tana gani dukkaninsu suka tafi, tayi niyyar tasowa suje ko wajen kofa ne amma mamansu Ummi ta hana, tace tayi zamanta kawai.
Ta dade a zaune tana kallon hannyenta bayan tafiyar tasu, ji take yi kamar an saka ta a wani jikin ne da ba nata ba, an ce komai nisan jifa kasa zai faÉ—o, ta yarda da auren nan kamar wasa, zuciyarta na hango mata shi a can nesa sai gashi tun ba'a je koina ba har anyi an gama, kowa ya taka rawarsa ya matsa, an bar mata filin da tace zata iya yakin a cikinsa.
Kamar wani yana kallonta da kyar ta É—ago idanunta tana karewa dakin kallo, kayan cikinsa dama ta riga ta sansu, har gadon a waya Aminu ta nuna mata don tare suka je shi da Baban wajen masu kayan katakon, labulen kuma duk a tsakar gidansu akayi ta dagawa ranar da su Aunty Safiyya suka siyo daga kasuwa, carpet din da aka shimfida a kasan gadon ma, a É—akinsu aka jingine shi.
Don haka ginin gidan da shine baƙo a wajenta take kallo, ɗakin kato ne yasha fenti da kuma tsarin fitulun da ba sai an gaya mata ba ta san masu tsada ne. Ta tuno yadda taji su Ummi nata yabon sauran bangaren gidan, ba shiri taji wani abu ya wuce ta makogwaronta, kowa ya sani cewar akwai dalilan da suka kawo ta wannan gidan, ba'a banza kamar ita zata sami irin wannan wajen ba, kowa ya sani cewa akwai wani abu daban a tare da auren nan, kawai kowa yayi shirun ne yana jiran ganin abinda zai biyo baya.
Tafi minti goma tana tunane-tunanen abinda zai iya faruwa da kuma mafita kala-kala, amma duk abinda ta kamo sai ya suɓuce idan ta tuna cewar a yau zata yi ido biyu da mutumin da aka daura mata aure dashi, mutumin da ya riga yayi mata gargadin cewa kar ta yarda ta aure shi, zuciyarta ta sake matsewa kamar zata fashe zuwa wasu dubunnan ƙananan atoms.
Da kyar ta cillar da komai a cikin kanta ta miƙe ta nufi toilet din dake manne a dakin, kuma sai da numfashinta ya tsaya sanda idonta ya kalli ciki, toilet ne da yasha adon wasu baƙaƙen marbles masu kyalli da santsi, anyi wasu hadaddun drawers a ciki da wani bakin katako da ya dace da kalar marbles din, ta ja numfashi a hankali sannan tayi addu'a ta taka kafarta ciki a hankali tana jin sanyinsa na ratsa ta.
A gaban katon mudubin ciki ta tsaya tana kallon yadda idanunta suka yi ja dama yadda fuskarta ta dan kumbura, sai kawai ta bude fanfon kasan sa tayi alwalarta, ta haÉ—a da wanke wuyanta dama rabin bayanta, kuma dadin ruwan yasa wata zuciyar tace mata taje ta É—auko sabulu a akwatin cosmetics É—in nan tayi wanka gabaÉ—aya amma ta girgiza kanta. Ba yau ba, ba yanzu ba.
A akwatin undies ɗin nan da Maryam tace ta dauko hijabinta guda daya, ta dawo kan carpet din dakin tayi sallah raka'a biyu, bayan ta idar ta dago da hannayenta da niyyar addu'a amma sai ta rasa ma me zata roƙa, saboda haka sai kawai ta dunƙule jikinta waje ɗaya ta ɗora kanta daga gefen gadon tayi shiru.
Shirun da a cikinsa taji lokacin da aka buÉ—e kofar dakin.
**
Karfe sha ɗaya daidai ta iso da Ma'aruf ƙofar gidan, ginin ya tsaya a gabansa kamar wani tsauni, babu wanda zai ce ma a cikin gidansu aka fitar dashi, don gate dinsa yayi gefe da yawa ta daya bangaren. Ya lashe lebbensa na kasa daya bushe yana gayawa zuciyarsa cewa sun zo matakin da suke jira, sakon ya isa kuma maimakon ya dawo cike da kwarin gwiwa sai ya dawo da wani raunin da kalaman da Ishaq ya gaya masa a dazu suka yi sanadiyarsa.
"Ka sani cewa wannan ba labari bane Ma'aruf, ba labari ne da zaka rubuta a yadda kake so kuma har ka kai ƙarshe da son zuciyarka ba. Na fahimci dukkan abinda ka faɗa da kuma dalilin da yasa ka dawo ka yarda da auren, amma hakan baya yana nufin cewa ka tsallakewa abinda zai iya faruwa ne.
Kar ka manta a baya ciwonka ko matakin HypoMania bai kai ba abubuwan da suka faru suka faru, yanzu kana stage na karshe Ma'aruf, kai da kanka kana tsoron wannan matakin, ba sai ka gaya min ba, a idanunka kawai nake gane cewar kaima kana tsoron faruwar wani abu kamar yadda kayi tunani a farko, tunda ni da kai mun sani cewa ba lallai ne mu iya binne komai ba a wannan karon..."
Ya sake lashe leɓɓensa yana jin yadda har a yanzu tasirin kalaman ke yawo a cikin kansa, gargadi Ishaq ɗin yake yi masa ya sani, gargadin da shima ya riga yayi wa kansa duk da cewa bai tsara komai game da auren ba bayan cewar yana son samun bayanansa daga yarinyar, zai tafi da abinda lokaci ya bashi ne kawai yana kuma ƙoƙarin kiyayewa dukkan abinda gaban zata haifar, haka ya gayawa Ishaq, ya kara gaya masa cewar shi yanzu abubuwan dake gavansa ma Allah yayi yawa dasu, sai yaga komai ya lafa masa tukunna ma zai maida hankali kan yarinyar.
Ta cikin glass ɗin motar ya hango ƙofar gate ɗin shiga wajen su Mami dake can gefe, babu kowa a wajen alamun da gaske dare yayi don ya sani cewar an sha hidimar mutane tunda yau ne rana ta karshe a bikin.
Wayarsa ya jawo ya kira Mamin, bugu daya biyu, kuwa ta dauka tunda dama jiran isowar tasa take, har a hanya ta kira shi taji idan ya taho.
"Ma'aruf..." Muryarta dake shaida dimbin gajiya ta kira shi da sunansa.
"Mami na iso amma ba zan shigo ciki ba."
Sai da ta É—anyi shiru kafin muryarta tace.
"Kai da mutane ne?"
Ya girgiza kansa.
"Ko Ishaq ma nace yayi zaman sa kawai. I'm alone."
"Tohm shikenan da safe na ganka, dama bana son kayi dare sosai baka iso bane, don tun wajen Isha'i suka ƙawo ta, anyi muku addu'o'i masu tarin yawa, hatta ƴan uwan Hajiya Maimuna da basu so abin da farko ba sun yaba sosai da ita da kuma ƴanuwanta Ma'aruf, Ina fatan Allah ya sanya dukkan alkhairinsa a zaman da zaku yi, Allah ya baka ikon sauke sabon nauyin da ya hau kanka."
Bai san lokacin da ya haÉ—iye wani abu a makogwaron sa ba kafin ya amsa a hankali, don ji yayi kamar itama tana tuna masa da abinda Ishaq ya faÉ—a ne.
"Insha Allah Mami. Nagode."
Yaji kamar ta gyada kanta kafin ta sake cewa.
"Na san da wuya idan kaci wani abun, ga abinci nan ma nasa Samira ta tanadar maka tun dazu, a miƙo maka ne?"
Ya girgiza kansa tun kafin ma ta ƙarasa, don baya tunanin a yanzu ko ruwa zai iya sha, tarin abubuwan da ƙwaƙwalwar sa da kuma zuciyarsa ke rabawa basu da adadin da har zai sami nutsuwa ta cikinsu.
Saboda haka sai kawai ya canja zancen da cewar.
"Na zata ma kowa yayi bacci Mami."
"Baccin mai gaskiya? Yanzun nan fa suka dawo daga kai sauran amaren, ai gidan nan yana nan kamar rana don baka shigo daga ciki bane, kuma naku ɓangaren ai yasha dab-dalarsa, sai da kayi haƙuri da abinda zaka gani."
Wani guntun murmushi da bai san dalilin sa baya suɓuce a gefen fuskarsa, don shi a yanzu baya son ganin yarinyar baya jin akwai abinda ya dame shi na harkar auren, sai kawai ya zaro hannunsa daga cikin gashin nasa yana bude kofar motar dashi sannan yace.
"Shikenan Allah ya bamu alkhairi, Allah ya huta gajiya, ta amsa kafin ya kashe wayar. Ya tsaya daga wajen yana kallon ginin gidan kafin ya sake komawa kan wayarsa ya danna wata number, bugu É—aya biyu matar dake É—aya layin ta dauka, kuma bayan sun gaisa ta tabbatar masa da cewar Hamida tayi bacci sannan ya katse wayar.
Inda ya kira É—in, wani Creche ne kamar asibiti inda ake bawa yara kulawa ta musamman, na wasu Æ´an Turkey ne musulmai, amma akwai hausawa a cikin ma'aikatan nasu, asibitin da aka kwantar da Hamidan ne da farko suka bashi shawarar ya kawo ta wajen, kuma sai hakan yazo daidai da cewar bai shirya kaita gida a lokacin da ake hidimar bikin nan ba.
Ranar farko da suka je, tayi rigimar cewa ba zata zauna, amma cikin ƙwarewar aikinsu da kuma tarin abubuwan wajen dake kama zuciyar yaro, sai rigimar tata bata je ko'ina ba.
A iya kwanakin nan yana zuwa kullum ya ganta wanda hakan yasa yayi sabo da ita sosai don har ta fara sakewa dashi tana amsa duk ƴan ƙananan tambayoyin da yake mata, da farko ne duk maganar da zai yi mata sai dai ta kalle shi kawai, sai bayan barinsu asibitin ne da ya kawo ta nan sannan ta fara yi masa magana, kuma ya fahimci tana da maganar sosai, kawai bata gama sabawa dashi bane har yanzu, amma ya san aƙalla suna making progress din da za'a zo gabar da zata fahimci cewa shi mahaifinta ne.
Ya sake kallon gidan, babu maigadi don haka shi ya shiga da motar, sannan ya sake rufe gate din ya dawo, ƙafafunsa suka taka kan barandar gidan sannan ya tura ƙofar falon ya shiga a hankali.
Hasken fitulun É—akin ya shiga idanunsa tare da hotunan kayan da suke ciki, daga kujeru labulaye dama carpet É—in cikin komai kalar Army green ne da kuma brown, babu wajen dining don haka kofofin korido biyu ne kawai da ya san É—aya ta kitchen ce É—aya kuma ta hanyar É—akuna, sai kawai ya juya a hankali ya rufe kofar falon.
Iskar da akeyi a waje mai zafi ce, yaji ta bayan ya fito daga Acn motarsa, amma a yanzu da ya shigo gidan yaga yadda labulayen falon ke dagawa sai yaji kamar ba irinsu ɗaya da ta wajen ba. A hankali ya zame takalmansa daga kafarsa sannan yayi gaba, ya kuwa ji ƙurar da Mamin ke fada amma bai damu ba, ya shiga hanyar koridon a lokacin da yake jin wani abu kamar bugun zuciyarsa na ƙoƙarin canjawa.
Ƙofofi uku ne a ciki, kuma bai buɗa kowacce ba don guda ɗayan dake gefe da kuma ta can karshe ta kasan kofofinsu ya kula duk fitulunsu a kashe suke, ta farko daga gefen daman sa ce kawai hasken cikinta ya saje da na cikin koridon.
Don haka kai tsaye ya ƙarasa gare ta ya ɗora hannunsa akan mariƙinta, sannan ya buɗe ta a hankali ba tare da tayi wata ƙara ba, kuma babu wani hijabi idanunsa suka sauka akan matar da kowa ke kira da tasa, ɗan karamin frame ɗin jikinta na naɗe a gefen gadon ɗakin, ta jingina kanta da gefen gadon idanunta a rufe, rabin fuskarta na shigewa cikin gadon yayin da hasken fitilar ɓangaren ɗakin ya haske ɗaya gefen fuskar tata.
Hijabin dake jikinta ne ya shaida masa cewa sallah tayi, kuma kafin ya iya sake wani tunanin ta buÉ—e idanuwanta duka biyun ta kalle shi.
Bai san me ya zata ba, bai san yadda yayi tunanin zai zo ya ganta ba, bai taɓa ma hasko ta a cikin kansa ba balle ya kintaci yanayinta, amma a lokaci guda yaji wani abu ya balle daga cikin zuciyarsa ganin ƙanƙantar ta, don duk a lissafinsa irin Ruƙayya zai gani, amma wannan ƙarama ce sosai, idanunta are so young haka ma jikinta ƙarami ne, yawun da ya sake haɗiyewa yana kallonta yasa wannan karon Adam's Apple dinsa motsawa sama da ƙasa. Kuma a lokaci guda kallon dake cikin idanunta ya canja zuwa wani abu kamar tsoro, yaga ta mike tsaye da sauri rike da hijabinta sannan ƙafafunta suka yi taku biyu baya, a yanzu ya tabbatar tsoratar tayi.
*
Lokacin da ta mike tsaye tana kallonsa, zuciyarta ta shiga tseran kilomitoci a ƙirjinta, yayin da take jin ƙafafunta na rawa kamar ma zasu iya daukanta ba, don haka ba shiri zuciyar tata ta shiga ambaton kalaman Innalillahi har zuwa ƙarshe yayin da take cigaba kallonsa.
Bata yi tunanin kawai bude ido zata yi ta ganshi tsaye a gabanta ba, bata ma yi tunanin haka yake ba, yadda take hango shi a tunaninta ya zarta hakan, dogo ne sosai ɗan siriri amma kuma mai cikar halitta, ba fari bane ko kadan haka nan ba baki bane, idanunsa na kallonta da wani yanayi da suke lumshewa, fuskarsa fayau yana tsaye yana kallonta daga bakin ƙofar, kayan jikinsa kalar ruwan toka ne mai irin sealed dinkin nan, babu ko hula akansa sai gashin kansa mai yawa da ya taru.
Zuciyarta ta cigaba da fat, fat, tana kallonsa, so take yi ta tantance idan har shi É—in ne ma ko kuwa aljani, tunda bata ko ji sallamarsa ba, sai kuma wata zuciyar tace mata ta yaya mutumin dake shirin fara nuna mata wutar da ta kawo kanta zai fara da yi mata sallama?
Taji kamar ta tafi ta shige toilet din dakin kawai ta kulle kanta, amma wani bangaren zuciyarta ya ture hakan, yana gaya mata cewa ya kamata ta jajirce ta fara ganin abinda zai yi tukunna, don ta gayawa zuciyarta zata iya yafi cikin carbi, kuma dukkan kalaman da ta faÉ—awa mahaifinta dama kowa suna nan a cikin kanta, don haka bai kamata ta fara karaya tun yanzu ba. Kuma ga mamakinta sai abinda take jira din ya faru.
"Assalamu alaikum." Muryarsa mai zurfi ce da a lokaci guda ta daɗa hargitsa tunaninta, tasa numfashinta katsewa a maƙogwaronta.
Ma'aruf ya sake lura cewa a tsorace take, don bayan yanayin fuskarta yana iya ganin yadda ta damke hijabin jikinta da duka hannayenta biyu tana cigaba da kallonsa, bata amsa sallamar ba, kamar ma bata ji yayi ba, kamar jira kawai take yi yayi wani abu ta ɓace daga dakin.
Ya fitar da numfashin daga ƙofofin hancinsa, me ya zata dama ga yarinyar da yayi wa wannan barazanar, don haka ya sani cewar yanzu a farko dole ne yayi kokarin kore wannan tsoron nata game dashi, yasa ta fahimci cewa a yanzu ba abinda ke gabansa game da ita kenan ba.
"Ki kwantar da hankalinki, na shigo ne don kawai mu gaisa ki san cewar ba ke kaÉ—ai ce a gidan ba, idan akwai wani abu da kike bukata kuma zaki iya gaya min..."
Kalaman suka daki zuciyar Amina ta yadda numfashinta ya tsaya cak! Wani abu a cikin kanta ya gaya mata cewar hatta lokaci sai da yayi shawara sau biyu kafin ya motsa. Kallonsa kawai take yi da tsananin mamakin da ta kasa auna shi a mizanin hankalinta.
Ya fahimci ba zata yi magana ba don haka ta ga ya sake riƙe hannun kofar sannan ya furta mata.
"Sai da safe."
Ya rufe ƙofar daidai lokacin da kafafunta suka kasa ɗaukarta gabaɗaya.
**
Hasken safiyar dake shigowa ta liner labulen ne ya tada ita, ta kifta idanunta tana kallon yadda wajen yayi mata kyau a ido, yadda hasken ya haɗe da kalar labulen dama liner yana ratsowa ta cikinsu, amma duk da kyan nasa sai taji kewar gida ta kamata, taji tana kewar ɗakinsu har ma da katifarta don ba zata iya tuna rana ta ƙarshe da taje wani wajen ta kwana ba tun bayan data gama makarantar Boarding fin da tayi.
Ta rufe idanunta ta buɗe tana sake kallon windon wanda tsawon yadda take ganinsa yasa ta tuna cewa a ƙasa take, akan carpet din nan, don anan bacci ya dauke ta bayan zuciyarta ta cika da sake-saken al'amarin da ta kasa ganewa.
Ba irin tunanin da bata yi ba da abinda bai zo kanta ba a jiyan nan, amma daga ƙarshe da ta tattara duk lissafinta da kuma abubuwan da aka gaya mata dama abinda ta shirya, sai taga cewar bata da wani zaɓi illa ta fara fahimtar manufarsa akanta kafin ta yanke hukuncin da zata iya kare kanta dashi.
Ta miƙe zaune a hankali tana son daidaita ganinta, a sannan ne ƙwaƙwalwarta ta tuna mata cewar bata yi sallar asuba har gari ya waye haka, ƴar wayarta dake gefe ta jawo tana tunanin yadda akayi alarm ɗinta bai tashe ta ba amma sai ta tarar ta mutu saboda ba caji, don haka ta mike da sauri ta nufi bandakin a lokacin da idanunta suka sake kallon ƙofar dakin ta tabbatar muƙullin data kulle ta dashi yana jiki har yanzu kafin ta shiga ciki.
Bayan ta idar da sallar ta daɗe tana addu'ar neman gafara da kuma ƙwarin gwiwar tunkarar duk abinda ke gabanta kafin ta mike, a cikin akwatin kayan kwalliyar nan ta samo sabulu, ta shiga tayi wanka, kuma duk da cewar komai sabo ne a wajenta bata sha wahalar gane kan fanfunan dake ciki ba tayi wankan ta fito.
Ta dawo cikin ɗakin dake ƙara tuna mata cewar rayuwarta ta canja da gaske, don har yanzu yanayin da take ciki ba zata iya fassarashi ba, aayƙin da take ji daya ne kawai na cewar ƴan gidansu zasu zo, don haka da ƙyar ta ture duk wani tunani dake ranta ta shirya cikin wata doguwar rigar da hannunta ya fara kaiwa a cikin kayan dasu Ummi suka jera mata jiya, bata ɗaura ɗankwalin ba sai kawai ta yafa shi akanta.
Ta kalli kanta a mudubin É—akin tana ganin yadda idanunta suka fara washewa da kukan da tasha a jiya kafin tasa duka hannayenta tana gyara zaman É—ankwalin akanta, siraran awarwarayen da har yanzu ke hannunta suka shiga rawa suna tuna mata da zamansu, don haka tayi saurin cire su gabaÉ—aya ta ajiye akan mudubin sannan ta juya ta kalli kofar dakin.
Kai tsaye ta ture komai a ranta ta nufi kofar ta buɗe ta, korido ne mai dan tsawo dake dauke da ƙofofin ɗakuna guda uku, ta sani cewa dole a daya daga cikin dakunan ya kwana tunda yace mata yana nan, don haka bata ko yi gigin bude kowacce ba kafafunta suka taka suka fita zuwa falo, anan ne, zuciyarta ta narke da kowanne abu na cikinsa dake shaida haɗuwarsu tun daga nesan da take, komai yana haɗewa cikin kalar ɗanuwansa cikin wani simple ado daya dace da wurin.
Ta jinjina kai a hankali kafin ƙafarta ta tafi zuwa daya korido ɗin anan, tana jin yadda fatarta ke sulalewa akan santsin wajen duk da ƙurar data lura akwai, kofar wani katon kitchen anan da komai na cikinsa ash ne da kuma fari, akwai store mai ɗan girma data buɗa ta tarar da kayanta fal a ciki, wasu ma duk a cikin buhu suke ba'a buɗe ba.
Ta dade tsaye tana kallon kayan da kuma tsarin drawers din kitchen din kafin ta hango wats kofa a can gefen fridge, taje ta bude ta, hanya ce mai dan fadi dake zagayawa kowanne bangare na gidan, inda daga can jikin katangar kuma ta hango wata kofa data tabbatar ta nan ne ake shiga cikin gidansu. Ta rufe kofar ta dawo tana sake komawa store din nan don ganin kayanta, tsji wani abu kamar magana amma bata tabbatar ba ta cigaba da duba kayan.
A lokacin ne kuma ta jiyo muryarsa, kamar irin ruwan saman dake sauka a lokaci guda tana ƙarasowa hanyar kitchen ɗin, ba shiri hannayenta suka nemi hannun kifar store ɗin amma kafin ta iya rufe ta gabadaya, ya karaso don hannun nata ya tsaya cak tare da numfashinta, idanunta suka hango mata shi ta zirin ƙofar da bai gama rufuwa ba, kuma a lokaci guda taji zuciyarta tayi kuli-kulin kubra ta faɗo daga wata sama mai nisa.
Ashe jiya bata lura da tsawonsa sosai ba, a yanzu daya canja cikin wani yadi kalar sararin samaniya da irin É—inkin rigar da bai kai gwiwa ba, bata jin a cikin abokan Aminu gabadaya data sani akwai wanda zata iya kwatanta shi tare dashi. Ta hadiye yawu tana kallon yadda idanunsa ke lumshewa da sauraren abinda ake gaya masa ta cikin wayar kafin yayi magana.
"Me kace?" Muryarsa a hankali ta fito, da wani irin amon da yasa jikinta girgizawa, numfashinta yana katsewa ba gaira ba dalili. Me yazo yi ne ma a kitchen din?
Ta ga ya girgiza kansa sannan ya zura hannayensa cikin gashin kansa yana motsa su, a lokacin ne kuma iska ta buso mata da ƙamshin turarensa, wani abu kamar ƙamshin musk ko mint, ko kuma meye hancin nata ya jiyo mata, sai kawai ta juyar da kanta gefe yayin da muryarsa ta sake fitowa.
"That issue aside Faruk, ba yanzu zamu neme shi ba, let's give him atleast two weeks to settle down, (mu bashi kamar sati biyu da zai huta) babu wuya zamu kama shi a sannan. Yanzu let's just focus akan waÉ—annan mutanen, I have somewhere to be now amma zan kira Martha ta min sending duk wani back-up da muke dashi akansu, zuwa yamma we decide where to meet sai ka kawo naka mu ga me zamu fitar."
Murza Æ´an yatsunta kawai Amina ke yi tana fatan ya juya ya fita, amma ga mamakinta sai kawai taji wata muryar mace ta taho tana faÉ—in.
"Yaya baka ganta bane?"
Kuma kafin ƙwaƙwalwar ta ta gama lissafawa, wata budurwa ta shigo cikin kitchen ɗin hannunta dauke da wani katon food flask, doguwar riga ce a jikinta shade din albasa (onion color) da wani dan karamin mayafi data yafa a sama maroon colour.
"Bata nan kitchen É—in?"
Ta sake tambaya tana ƙarasowa ciki fuskarta ɗauke da murmushi, a lokaci guda taji wani abu ya ratsa ta har tafin kafa, don babu wata kwana-kwana ta gane ƙannensa ne suka zo, kuma shigowar sa kitchen ɗin ita yake nema. Taga yadda hannayensa ke motsawa a cikin gashin nasa alamar bai san me zai ce ba lokacin da yarinyar ta tafi tana ajiye food flask ɗin can kusa da gas cooker.
Sai kawai tayi karfin halin ɗauko wani jug a gefe sannan ta buɗe ƙofar store ɗin ta fito, zuciyarta na gaya mata ai tunda a yanzu ƙirgen ya tashi daga su biyu ta tsira.
"Sannu da zuwa."
Muryarta tasa duka su biyun juyowa suna kallonta, yarinyar ta washe baki cikin fara'a sannan ta taho da sauri ta rungume ta.
"Ashe kina ciki, Barka da safiya."
Sai da zuciyarta ta buga a kirjinta saboda mamaki, mamakin da ta daure cikin nata murmushin itama tana rungume ta.
"Sunana Samira, tare muke da Surayya da Munaya suna falo, fatan kin tashi lafiya?"
Ta faÉ—a bayan ta janye daga jikinta, sai ta É—aga kai da nata murmushin mai fadi ta amsa da.
"Lafiya kalau, nagode sosai."
A lokacin ne kuma idonta ya kai kansa, ta san kallonta yake tun da ta fito don tana jin tasirin yadda idanun nasa ke shiga jikinta, gabanta ya faÉ—i sakamakon haÉ—a idanun da suka yi, kallon da yake mata mai cike da nazari ne, kamar yana saka scanner cikin idonsa yana son tantance ta.
Kuma a lokacin ne babban al'amarin safiyar ya faru, bakinsa ya motsa da wani guntun murmushi yana rufe idanunsa ya buɗe su akanta, kamar ma ƙifta mata idanun yayi, abinda kafin ta gama tantacewa ya juya ya bar kitchen ɗin.
A kusa da kafafunta taji cikinta ya faɗi gabaɗayansa har ƙasa tsabar tsurewa da kuma mamaki, ilahirin jikinta ya ɗauki rawa kafin muryar Samirah ta cigaba da magana cikin tunaninta, sai ta hango kanta ta tsugunna tana ƙoƙarin tattara jikinta waje ɗaya kafin ta iya fahimtar me take cewa.
"Abinci muka kawo muku kafin mu fara zagayen gidan sauran amaren, gamu nan da kaya fal cikin mota kowacce tayi mantuwarta... Na san kema kinyi taki ko?"
Bata gama daidaita tunaninta ba, don haka bata san sanda ta É—aga mata kai ba tace.
"Ina tashi nima naga na manta chager wayata."
"Ai sai a hankali ma zaki yi ta neman wasu abubuwan, Ya Shukra har da system É—inta gabadaya ta manta kuma project É—in masters take yi..."
Ta gyada kai tana ƙoƙarin murmushi sanda wata ta ƙaraso cikin kitchen ɗin itama, watakila itace zasu yi sa'anni ɗaya ko kuma ace ta fita da kadan, tana da glasses wanda kana gani ka san medicated ne, ita kuma bakar abaya ce a jikinta wadda ta fito da ɗan hasken fatarta don ita ba fara ce sosai kamar Samiran ba, zata iya jera su layi ɗaya da yayan nasu.
"Ashe kina nan matar Yaya..."
Ta fada da nata murmushin itama tana karasowa kuma ga mamakin Amina itama sai kawai ta rungume ta tana fadin.
"Oyoyo, we welcome you into the Family dear, jiya mutane basu bar mu mun ganki ba."
A yanzu ƙwaƙwalwar Amina kwancewa tayi gabadaya, don ita ko a gyangyadi bata taba kawowa haka abubuwa zasu kasance ba, ko jiya sai da su Aunty Ma'u suka gaya mata cewa tayi taka-tsan tsan da ƴanuwansa.
"Ƴan gayu ne na karshe Amina, kija jikin ki ki tsira da mutuncinki..."
Haka Aunty Ma'un ta raÉ—a mata a kunne.
To me yasa ne komai yake faruwa saɓanin tunaninta ne? Ko dai akwai wani abu da ba daidai yake tafiya bane?
"Sunana Munaya.."
Ta kara faÉ—a tana miko mata hannu, sai tayi karfin halin mika nata tana murmushi itama.
"Yanzu zaki ganta kamar normal mutum amma idan kika tabo wajen karatu zaki fara tunanin aljana ce."
Samirah ta faÉ—a tana kallonta.
Sai kawai ta girgiza kanta.
"Yarinyar nan ta raina ni da yawa, kar ki yarda da ita."
"Wallahi da gaske nake Aunty Amina idan kina da ƴanuwa a Buk ki tambaye su kowa zai ce miki ya san GB (Genius Brain) haka suke ce mata, irin ƙwaƙwalwar su ɗaya da Yaya."
Munaya ta girgiza kanta tana murmushi.
"Astagfirullah, Allah ka tsare ni daga sharrin yarinyar nan, zo muje ku gaisa da Surayya, tana can tana ta aikin pressing waya."
Da haka Munayan taja hannunta suka yi hanyar fita, Samurah ta biyo bayan su.
A falon wadda suka kira da Surayya na zaune kan kujera mai zaman mutum ɗaya tana ta faman danna wayar hannunta, daga ƙasa kuma wasu ƴan mata biyu ne su ma da kallo daya zaka yi musu ka san ƴan aiki ne, gabansau dauke da wasu trays din dake dauke da food flask har hudu da kuma jug na lemo shima kala biyu, alamu su suka shigo dashi daga motar da Samirah tace suke.
Kuma da shigowarsu Surayyan da zata ce sun yi sa'anni da Munaya ta dago da nata murmushin itama sannan ta ajiye wayar ta taho ta rungume ta, a yanzu Amina taji kamar ta saba ne ma da yanayin gaisuwar tasu.
"Na san ma wannan mai bakin ta gaya miki sunana koh?"
Ta tambaya tana kallon Samirah da tayi wajen ƴan aikin nan tana gaya musu akwai wata baƙar keda da badu shigo da ita ba.
"Nima tun kafin in shiga ta gabatar dani ai." Cewar Munaya tana neman waje kan daya daga cikin kujerun.
Amina ta daga kai tana murmushi.
"Ta fada min, naji dadin ganin ki kuma."
"Haba dai godiyar tamu ce ai, na san na samu wajen zuwa idan Mami ta matsa min da zancen waya, da fatan dai ba zaki damu ba idan kina ganina a compound din gidan nan."
"You dey mad? Kike fada a gaban yarinyar nan? Kema kin san kamar Mamin taji ne ai."
Cewar Munaya tana dariya, Surayya ta kalli Samiran dake tsaye tana jinsu.
"Ta gaya mata mana, itama ai tana da nata secret din a wajena."
"Ba dai zancen wannan cake pack din Ya Salma bane, wlhy sai inyi confessing in fada, tunda idan nayi cake din ai har da Mamin ake ci ace yayi dadi."
"What? Kayan Salman kika dauka? Amma bata sani ba har yanzu ko?" Cewar Munaya.
Surayya ta koma kan kujera tana sake É—aukar wayarta.
"Ki bari kawai, kuma wallahi guda daya ne a cikin kayanta, ranar da ta nema ta rasa, inaga Yaya Ishaq za'a kira yayi aikinsa a gidan nan."
Suka kyalkyale da dariya gabadayansu yayin da Amina ke tsaye har yanzu da jug din nan data dauko a hannunta tana taya su da murmushi.
A lokacin É—aya yarinyar nan ta dawo daga waje. Samirah ta karbi kedar tana miko mata tace.
"Gashi Aunty Amina, cupcakes ne na san zaki iya yin baƙi a cikin satin nan, wadannan kuma abinci ne breakfast da Dinner, naga yayan ma ya fita, flask din da na kai Kitchen kuma miya ce a ciki, murfin suka balla yanzun nan da safe shi yasa na riƙo shi kar ta zube."
Wannan karon Amina ta tabbata mamakin da take ciki ta kai ta har wuya tana shirin nutsewa.
"Kar ki wani damu idan yarinyar nan ce ina jin sai kin dinga korarta daga gidan nan akan abinci..."
Kafin Munayan ta karasa fada wayarta tayi kara. Sai ta miƙe tana cewa...
"Ya Shukra ce, kuzo mu tafi kafin ta fara mitar nan tata."
Surayya ta mike kuma ga mamakin Amina sai suka zo suka sake rungume ta daya bayan daya suna gaya mata cewa in suka dawo zasu shigo sai suje cikin tare ta gaida su Mami. Itama ta rako su har kofa tana fadin su gaishe su.
Bayan sun fita, ta tsaya daga barandar falon tana kallon compound din gudan da yasha wasu interlocks masu ƙyalli, da kuma shukokin wasu kananan bishiyu a jikin katangar da basu fara girma sosai ba.
Ji tayi zuciyarta ta washe da wani abu da baza ta iya fassara shi ba, mamaki na yawo akanta har yanzu na yadda abubuwa ke canjawa daga zaton ta, kirkinsu yasa taji sun burge ta sosai yadda basu É—auki kansu wani abu ba, taji zuciyarta na dokin ta saba dasu fiye da haka, kafin ta juyo ta dawo tana rufe kofar É—akin, idonta ya kai kan tarin flasks din nan tana tunanin yadda zata yi da abincin, ko da yake ba ita kaÉ—ai suka kawowa ba har dashi ta sani.
Zuciyarta ta buga da ta tuno cewar zai sake dawowa gidan ya same ta, ta tuno kallon da yayi mata har da murmushi da yadda taji a lokacin tana kasa tantance tsoro ne ko akasin sa... Ashe dukkan abubuwan da take hangowa da sauki sun sha banban da tunaninta...
Kwankwasa kofar da akayi ya katse tunaninta, ta tafi da sauri ta bude tana fatan su Maryam din da take jira ne, su din kuwa... Har da Hafsa dasu Mimi da Fatima da wasu daga cikin ƴaƴan Baban kurna, su takwas, sun riko wasu sauran tarkacenta da tsintsiyoyin nan... Ranta ya karasa yin fari ƙal ta hau rungume su daya bayan daya tana murna, rungume sun da bata san tayi ba sai da taji Fatima na cewa.
"A ina kika koyo wannan sabuwar gaisuwar kuma?"
Ita kaÉ—ai ta cije lebbenta tana murmushi.
**
A cikin É—akin Hajiya Kilishi, ta kalli kawarta Salamatu tana girgiza kai.
"Banbanci na dake kenan, bana faɗuwa na hakura, a sannu nake bin abu ina gutsira har in kai ga ci, kuma nasha gaya miki hakurin da kika kasa a tare da Shamsu (mijinta) kenan. Shi yasa har rayuwa ta kawo ki wannan gaɓar."
Hajiya Salamatun ta girgiza kanta itama.
"Gaɓar da nake cin duniya ta da tsinke ba, kar ki kawo wannan zancen kuma bayan mun gama na Saratu, mu tattauna abinda ya kawo ni, Ya zaki yi da al'amarin ƴar tasa?"
Hajiya kilishi ta kalle ta sosai tace.
"Na gaya miki ai, saboda ban samu nasara akanta a asibitin nan ba hakan baya nufin na hakura, ai na rantse sai naga bayanta don ko wajen uw*rta ba zan bari ta koma ba tunda har zata fara zame min ƙalubale tun daga yanzu. Babu wanda ya isa ya shiga zuciyar Ma'aruf da tasirin da yafi nawa Salamatu kema kin sani.
Saboda haka matsalolin nawa zan hade guri guda, bayan tsinannun asibitin nan da suka hana ni kwana a wajenta sun sallame ta, wani Creche wai ya kaita a hanyar Bompai saboda kin san muna cikin sha'anin bikin nan. Saboda haka a yanzu da komai ya lafa zan saka ne ya dawo da yarinyar wajen ita Aminar, ta yadda zan aiwatar da manufata hankali a kwance.
Kin san dai dalilin da yasa na shiga na fita ya auri yarinyar nan, saboda daga ita har iyayenta zan iya juya su sannan an tabbatar min tana da sanyi halin da al'ummar gidan nan kaf zasu karbe ta cikin ƙankanin lokaci, na gaya miki tana da irin fuskata Salamatu, fuskar da zata daɗe tana yin abun da ba mai iya ɗora zarginsa akanta."
Hajiya Salamatu ta kalle ta tsawon wasu sakanni tana nazarin maganganunta kafin ta girgiza kanta tace.
"Kin san nice mai gano miki da matsalar dake ba kya taba hangenta Kilishi, jiya da suka kawo yarinyar nan banga fuskarta ba, amma daga yanayin jikinta kawai na san ƙarama ce, kuma idan har halinta ne zai sa jama'ar gidan nan su sota, ba kya tunanin zuciyar yaron ma zata iya ta karkata kanta?"
Hajiya Kilishi ta gyaÉ—a kai tana murmushi.
"Daɗina dake ragon azanci Salamatu, ai dama haka nake so, in ba haka ba don me nake ta koɗa ta da ƴanuwanta a wajensa, so nake ta siye min zuciyar kowa har shi ɗin kamar yadda nima nayi, ta yadda a nutse zan sa ta dinga kai min saƙona kowacce kusurwa babu mai zarginta."
Hajiya Salamatu ta sake girgiza kanta.
"Baki gane ba Kilishi, abinda nake nufi shine idan har ta siye zuciyar Ma'aruf da darajar da zata fi taki nauyi fa? Idan har yayi nisa a duniyarta ta yadda ba zai iya jiyo ko da muryarki ba fa?"
Wannan karon dariyar da Kilishi tayi sai da ta ratsa kowanne bango a dakin ta kuma fita ta windon ɗakin da yake a rufe, tabi iska zuwa nisan da ƙarfin amonta zai iya kaiwa, hatta jikinta sai da ya girgiza saboda nauyin dariyar, kafin ta kalle ta sosai tace.
"Ita kanta yarinyar ai na shirya mata Salamatu, sau nawa zan gaya miki ne Ma'aruf nawa ne ni kadai?!"
***
Tafiyar ta fara! Insha Allah.
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
BABI NA GOMA.
Ina mai baku hakuri, an samu jinkirin wannan babin ne saboda rasuwa da aka yi min ba a gari ba don haka har tafiya sai da ta kama ni zuwa can... Ina rokon ku taya ni addu'ar Allah ya jikanta ya gafarta mata.
Sannan duk a cikin kwanakin nan mun rasa Abdallah ma, ɗan gidan Sanah S. Matazu editar Fikra, ina rokon Allah ubangiji ya bata hakurin rashinbsa yasa mataryin can ne, sannan ina yiwa duk wanda ya rasa wani nasa ma addu'a, mutuwa na taɓa mu a bangarorin da bamu san muna dasu ba, Allah yaji ƙan wadanda muka rasa mu kuma ya kyautata namu zuwan.
Ameen ya Allah.
~~~~~~~
We should talk. 
                          - Unknown
**
"Maamah don me yasa zai kira shi? Nace ya kira shi ne? Me yasa zai yi deciding abinda bai shafe shi ba kai tsaye?"
Muryar Ruƙayya ta fito da ƙarfi a lokacin da take kallon ƙaninta Ahmad dake tsaye a gaban gadon da take kwance. A cikin asibitin da aka kwantar da ita ne, tun bayan lokacin data faɗi take asibitin ba'a sallame ta ba sakamakon hawan da jininta ke tayi babu sauka, don hatta fuskarta da kafafunta dukkansu a kumbure suke suntum.
"To hell with you and him! Shi waye da baza'a kira shi a gaya masa yayi ba daidai ba? Me yasa akan Ma'aruf ƙwaƙwalwar ki ba zata taba hankali bane Rukayya? Meye a duniyar nan ki gani a jikinsa da sauran maza badu dashi? I swear to God idan kika kara daga min murya a yanzu zan sake kiranshi na zage shi a gaban idanunki."
"Maamah kina jinsa ko? Kina jin abinda yake faÉ—a?!"
Ta faɗa tana juyawa wajen mahaifiyarsu Hajiya Nafisa dake zaune daga gefe tana haɗa mata tea, idan da sabo ta saba da wannan fada a tsakaninsu, don ko Ashraf da yake sakon Rukayyan basa faɗa tare kamar yadda suke yi da Ahmad ɗin, shi mutum ne kaifi ɗaya mai tsatsatsauran ra'ayi, Rukayya kuma ba'a taka ta tayi shiru, don haka inuwarsu bata taɓa zama ɗaya.
A yanzu ma dalilin ɗaga jijiyoyin wuyan nasu, Ahmad ɗin ne ya zo ne yana shaida musu cewa shi ya sake kiran Ma'aruf akan zancen Hamida, tunda sunyi magana da Ashraf yace zai tuntube su kuma bai sake cewa dasu komai ba, don haka shi ya kira shi da ɓacin ran hakan wanda a ƙarshe wayar tasu bata ƙare da daɗi ba, don Ma'aruf ɗin har gargadi ya masa da cewar labarin zai canja idan har ya sake kiransa.
Ita kanta bata ga aibu a abinda Ahmad ɗin yayi ba, don Allah ya sani idan da Ruƙayya zata bata dama a lokaci guda ne zasu juya dukkan tanadin da suke mata akan Ma'aruf ita da kawarta zuwa sharri, zata fi jin karfin gwiwar cutar dashi akan abinda suke yi a yanzu, don haka ta cigaba da haɗa mata shayin kawai tana jinsu, tana ji kamar Ahmad na furta rabin kalaman dake cikin ranta ne da ba zata iya faɗawa Rukayyan ita da kanta ba.
Kuma sai da taji kalaman nasa na shirin yin tsauri da yawa sannan ta kalle shi tace.
"Ahmad, fita daga wajen nan."
System É—insa da ya ajiye akan Fridge din É—akin bayan shigowarsa ya É—auka cike da fushi sannan ya nuna Rukayyan da É—an yatsa tace,
"Daga yau kar ki sake kirana a matsayin danuwanki duk sanda wani abu ya haÉ—a da mutumin nan, idan ba haka ba daga ke har shi I'm gonna rip your as* off! (Zaku gane kuranku!)"
Da haka ya fice tana bugo ƙafar ɗakin asibitin, Rukkaya ta koma da baya ta rufe fuskarta da duka tafukan hannayenta biyu lokacin da Hajiya Nafisan ke miƙo mata kofin shayin.
"Kin san halinsa ai sarai, amma kika biye masa kuke ɗaga murya a cikin asibiti, na sha gaya miki da kin ga ransa ya ɓaci kawai ki rabu dashi, wannan shine girman."
Ta girgiza kanta a hankali sannan ta buÉ—e fuskar tana karbar kofin.
"Maamah ba zan iya shiru akan abinda yake fada ba, kina ji fa yace har gargadi Ma'aruf yayi masa, to waye ya san iyakar abinda ya gaya masa ma? me yasa zai sake ɓata min al'amura ya sake ɓallo wani abu kuma?"
Ta ƙarasa tana karɓar shayin, kuma garɗin abubuwan da aka cika masa da kuma ɗuminsa ya sauka har cikin ƙirjinta, ya sanya ta lumshe idanuwanta a hankali kafin ta buɗe su sosai akan kofin, da ɗaya hannun nata shiga murza bakinsa a hankali ba tare da ta kalli Mahaifiyar tata ba tace.
"Maamah kince kawai aura masa yarinyar akayi ko?"
Taji sanda Hajiya Nafisan tayi ajiyar zuciya kafin tace.
"Tabbatar min akayi cewa a cikin sati uku akayi komai, ance bai taba ganinta ba ma har aka daura auren, sannan yarinyar bata da wani daraja, mahaifinta ance irin sana'ar ƙananun aikin katakon nan yake yi, don haka na tabbatar miki akwai wata manufa ta daban dangane da auren nan da bamu sani ba, amma ba wai aure yayi irin wanda kika sani ba."
Wannan karon Ruƙayya rufe idanuwanta tayi duka, tana jin yadda wani tiririn zafi na daban da yafi karfin shayin dake hannunta yana cigaba da zurara a cikin ƙirjinta yana kona duk inda ya bi.
"Nima na sani ba auren gaske bane Mami, don wallahi na san babu ta yadda za'ayi yarinyar nan ta shigo cikin tsarinsa, a yanayin arzikinsa dana gidansu ko haukacewa yayi akwai Æ´anmatan sa suka fita daraja da yawa da zasu so shi a haka."
Shi yasa bana son inyi wasa da kowacce irin dama Mami, a yanzu ban damu da duk hanyar da zamu bi mu lalata komai ba, don ban damu da manufar kowa ba, burina kawai kada yarinyar nan ta daɗe a rayuwar Ma'aruf, don ta haka ne kawai zan iya cimma burina Maamah, idan akwai ta, na sani ba zan taɓa iya samun abinda nake so ba."
Kafin Hajiya Nafisan dake kallonta tace wani abu, ƙarar ringtone ɗin wayarta ya cika ɗakin, don haka ta dauko wayar tata dake gefen bedside drawer ta miko mata, Ruƙayya ta karba tana kallon sunan da ya fito akan screen ɗin, Jawad... Taji ranta ya ƙara dugunzuma ya ɓaci a take, bata san wane irin mutum ne shi marar zuciya haka ba? Me yasa zai cigaba da damunta alhali da kowanne yare da zai iya fahimta ta gaya masa cewa ya rabu da ita? Sai kawai ta danne buttton ɗin wayar gabaɗaya ta kashe ta sannan ta ajiye ta a gefe.
Takaicin dake cike fal da tausayin Æ´ar tata ya nuna akan fuskar Hajiya Nafisa kafin ta girgiza kanta a hankali.
"Na gaya miki ki kwantar da hankalinki ki samu sauƙi mu koma ki gida, don Hajiya Saude ta gaya min sai da haɗin kanki tukunna sannan komai zai daidaita, nayi miki alƙawarin Ma'aruf da ƙafarsa zai tako har inda kike ya neme ki."
Wani abu kamar murnushi ya fito kan lebben Ruƙayyan yayin da ta sake jingina kanta baya da jikin gadon kafin a hankali kuma ta ɗago da kofin shayin nan ta kai bakinta.
Daga can jihar Abuja, a cikin gidan rawar da Jawad yake a can sama, inda yaken wani lungu yana zaune akan luntsememiyar kujerar wajen shi kadai, a gabansa wani haddadden kwandon shisha ne da yake zuƙa yana hurawa lokaci zuwa lokaci, a ɗaya hannun nasa kuma wayarsa ce da hasken screen ɗinta ke haska fuskarsa yayin da yake danna number guda cikin contact list ɗinsa ana kuma maimaita masa abu guda daga daya bangaren wayar.
"The number you're trying to call is currently switched off, Please try again later." (Lambar da ake kira a kashe take, a sake gwadawa bayan wani lokaci.)
Hannunsa ya sake danna number yayin da aka sake maimaita masa maganar.
"Jawad?? For real? Kai kadai anan sama? Na zata wasa su Sa'id suke da suka ce kana nan ai."
Wani abokinsa da suke kira da Haro ya ƙaraso daidai wajen yana zama daga gefen kujerar, bai ce dashi komai ba don haka ya sake kallonsa yace.
"Naji rumours din, it was bad man, amma bai kamata hakan ya dame ka ba, kar ka jawowa kanka depression."
Sai a yanzu Jawad ya juyo ya kalle shi, ya san abinda yake magana, jita-jitar dake yawo cewa za'a cire mahaifinsa daga kujerar Minister, har a tunaninsa abinda zai dame shi kenan? To me zai same su idan an cire shin tunda ko a yanzu sun tara dukiyar da ya san har su mutu ba zata kare ba, ya zuki hayakin ya fesar sannan yace.
"Kar Allah yasa a fasa cire shin, al'amarin wannan tsohon ya isa ya dame ni ne Haro? abinda yake gabana daban."
Kan shishar Haro ya karɓa yana dariya sannan yace.
"Pray tell."
Sai kawai ya jefo masa wayar hannunsa shima sannan ya jingina da kujerar. Haro ya cafe wayar sannan ya kalli screen É—inta, kuma sunan da ya karanta na farko akan call log din ya sashi jan tsakin da bai shirya ba.
"Ban san ranar da asirin da yarinyar nan ta naka zai karye ba Jawad, har sau nawa zan gaya maka ka rabu da wannan tsilar abar, ub*n me zata tsinana maka da baka samu ba a duniyar nan? You're young, kana da kudi, kana da status mai kyau, kana kan lokacinka Man, sannan babu yarinyar da zaka kalla duk kasar nan ka kasa samunta. Me yasa ba zaka yi hankali ka fahimci cewa wannan yarinyar sharri ce ma a rayuwarka ba?"
Jawad ya lumshe idanunsa ya bude yana saurarensa ta cikin sautin kidan dake tashi daga can kasa kuma sai da ya kai har karshe sannan ya girgiza kansa, idanunsa na kallon fitilar dake samansu mai kala-kala a cikin duhun wajen yace.
"Ba zaka gane ba Haro, ba zaka gane abinda nake ji bane, na rantse da Allah idan Ruƙayya bata aure ni ba, ba zata sake auren kowa ba a duniyar nan!"
***
"What do you find? Me ka samo?"
Faruk ya tambaya riƙe da Tab ɗin hannunsa yana kallon Ma'aruf dake kokarin fitar da lissafin da suka kwashe fiye da awa guda suna yi akan kamfanin wasu abokan kasuwancinsu da suka gano cewar suna da nasu kamashon cikin wannan mummunar asarar da har yanzu suke bincike akanta.
Suna zaune ne daga cikin office din Ma'aruf É—in, bayan kusan jiran awa uku da Faruk din yayi yana jiran dawowar Ma'aruf da ya bar office din tun kusan sha É—aya na safe.
Kuma sai da ya dawo sannan ya buɗe email dinsa ya karanta bayanan da Martha sakatariyar tasa ta turo masa sannan suka fara haɗa komai suna tarawa da ƙaiyadewa.
"So shi wannan Mr. Ishmael Grahm É—in shine ya karbi aikin accountant É—insu a farkon shekarar nan kenan kuma sunansu É—aya da wanda ya tafi har surnane É—in."
Ma'aruf ɗin ya faɗa, idanunsa manne da tab ɗin gabansa yayin da muryar tasa ta fito kamar ta ƙwace ne daga cikin tunaninsa.
"What a ina ka ga hakan? Dama sun canja accountant ne? When?"
Faruk yayi tambayoyin yana komawa cikin kan tasa wayar.
"A cikin wanda ka min sending zaka duba, anyi naming dinsa 13th March na wannan shekarar."
Kuma sai da Faruk din ya kusan zuwa can ƙasa wajen nemowa kafin ya isa inda yake gaya masan, idanunsa suka ƙanƙance yayin da yake karanta bayanin dake wurin.
"Bala'i! B ya akayi hankalinka yaje wajen nan, I was goung through it fa tun safe amma wallahi ban gani ba."
"Shi yasa na gaya maka na kusa korarka daga aikin nan, ban san me yake ɓata maka tunaninka ba kwana biyu."
Dariya Faruk É—in yayi yana cigaba da karantawa kafin yace.
"Aikin Shahida ne wallahi, tunda ta yaye Aarif nake ji kamar watannin farkon auren mu muka koma."
A lokaci guda Ma'aruf ya tsaya da karanta abinda yake yi ya juyo ya kalle shi, sai kuma ya girgiza kansa sannan yace.
"Baka da hankali Faruk, na daÉ—e ina gaya maka."
Faruk É—in ya sake yin dariya yana daukar tambulan É—in lemon da Martha ta kawo musu kafin yace.
"Inji wanda yake amsa sunan sabon ango, you didn't even tell me ya yarinyar take."
Yaya yarinyar take. Maganar ta sake tuno masa da fuskarta a yau da safe kafin ya fito, sati guda kenan da yin auren, kuma a cikin sati gudan nan baya jin magana ta haÉ—a su wadda tafi kirgen cikin yatsu, wani lokacin dai su kan haÉ—u da asuba idan jamlock É—in kofar falo ya rufe bayan ya fita masallaci, zata zo ta buÉ—e masa idan yayi knocking sanye da dogoon hijabinta har kasa, ranar farko bata ce dashi komai ba, amma a rana ta biyu ne ta fara gaishe shi. Sannan kuma sau da yawa idan ya koma da daddare zai ganta, har ya fahimci wani lokaci ma tana fitowar ne kawai don ta gaishe shi.
Bayan hakan maganganun da suka haÉ—a su baya jin sun wuce biyar, ya san ranar juma'a da zai fita masallaci ya tambaye ta dardumar sallah ta dauko wata sabuwa kuwa fil mai laushi ta kawo masa, sai kuma ita da ta tambaye shi Panadol ya fita da kansa ya siyo mata, amma bayan hakan baya tunanin wata maganar ta kara hada su don baya son ya takura ta ko kadan, so yake hankalinta ya kwanta ta fahimci cewa da gaske ba abinda zai mata, don a o farkon nan ya lura cewa da gaske a tsorace take dashi.
Ya rasa irin tasiri kalamansa suka yi a zuciyarta, ya kasa gane ma me yasa ta yarda da auren idan har tana tsoronsa haka, wataƙila laifin tun na wannan ranar ne, da ta fito ya ganta, da tun a lokacin zai san tayi ƙanƙanta yayi mata wannan barazanar, don haka yake son da kanta ta karkade duk wani tunani da take yi game dashi da kuma damuwar kalaman nan.
A shekaranjiya da yaji tana waya da wata tana yi mata bayanin cewa har yanzu bata fara girki ba, a cikin muryar tata yaji da wani abu kamar damuwa, wani abu da ya tsaya masa a rai yasa yasa ba shiri a lokacin da ya shiga cikin gida yaji Mami na yiwa Malam Sani lissafin cefenan wata, ya bishi a baya ya ƙara masa wasu kuɗin yace duk abinda ya siya na cikin gidan ya sake siyan rabin sa ya kai mata. 
Komai na wannan auren daban yake da lokacinsa da Rukayya ya sani, babu abu ko guda daya da zai danganta shi da farkon wancan É—in, kamar komai É—in yana zuwa ne a kishiyar É—ayan, sai dai abu daya kawai zai iya dorarawa shine a yanzu yana jinsa mutum mai Æ´anci tunda babu ruwanta dashi sabanin a wancan da kwanakin farko suka sa shi yaji kamar an tsare shi a wani waje ne da lissafin abubuwan da ya kamata yayi.
"Kaji ai matsalata da kai kenan, da an taɓo wani zancen ba na aiki ba you lack interest, na tabbata da nayi ta jiranka ma anan wani aikin ka tafi yi."
Faruk ya faÉ—a yana jawo shi daga cikin tunaninsa, kuma ba tare da ya juyo ya kalle shi ba yace.
"Saboda ni ba mutum bane kenan bani da wasu personal problems, to ka leƙa motata ka gani wanki naje na karɓo sannan na karbo ɗinki, har B&L naje samo maigadi, sannan na tsaya a zoo road nayi aski."
Faruq É—in yana nazarin sumar kansa da banbancin ta kaÉ—an ne da yadda ya ganta jiya, yace.
"A haka wannan gashin naka an aske shi?"
Ya girgiza kansa har yanzu bai kalle shi ba yace.
"A'a fixing nayi."
Sai kawai Faruq ɗin yayi dariya sannan ya juya kan tasa tab din dake blinking alamun shigowar wani sabon saƙon, suka cigaba da tattauna duk abinda ke gabansu har magariba ta tadda su anan, wanda kafin magaribar suka yi sa'ar ganowa cewa tabbas wannan kamfanin sun karbi kaya na maƙudan kuɗaɗen a hannunsu kuma dukkan receipt din kudin an saka adadin kudin daidai, har ma da alert din shigar kudin cikin bankin kamfanin, amma takardar da Faruk ɗin ya gano cewa an duba balance a wancan lokacin kuma kudin bai kai ba, ita ta daure musu tunani. Don basu san yadda za'ayi alert ya shigo da wani adadin kuɗi ba alhali ba hakan aka turo ba.
Anan suka tsaya kasancewar magriba ta taho kusan kowa a Office din ya tashi tunda dama a ƙa'ida ƙarfe biyar ne lokacin tafiyar kowa.
A wajen Hamida ya daɗe bayan yayi sallar magaribar, kuma wannan karon har nuna alamun cewa zata biyo shi tayi, ransa ya cika da farin ciki kafin ta ƙarasa da cewar zata bishi ne ya kaita wajen Maminta, kuma Allah kadai ya san sau nawa ya zura hannunsa cikin gashinsa ya fito dashi kafin ya iso gida, don game da al'amarinta bashi da wata mafita ko kaɗan, abu ɗaya ya sani shine ba zai taɓa iya sake rabuwa da ita ba ko da me Ruƙayya da iyayenta zasu tunkare shi.
Ya tuno wayar da suka yi da Ahmad kanin Ruƙayyan a jiya, yaron bashi da hankali ya daɗe da sanin hakan, tunda har sunyi magana da Ashraf ya gaya masa cewa zai neme su bai ga dalilin  da zai sa shi ya sake kiransa ba, kuma  yadda yake masa magana ma ji yayi idan akwai wani mataki da yafi na haukan, zai iya saka shi a wannan layin, don haka ƙarara yayi masa gargaɗin cewa zai iya sawa a kama shi idan har ya sake kiransa da wannan batun.
Ya riga ya sani cewa duk cikinsu babu wanda zai iya ja dashi don yana da da hujjar da zai kaisu ƙasa ko a gaban waye za'a tsaya, bama wannan ba ya sani cewa babu inda Ruƙayyan zata je ta samo karfin halin da zata iya fuskantarsa a yanzu, tana yawo ne da nauyin waɗannan kalaman ɓoyayyiyar yarjejeniyar da suka yi kamar yadda koda da rana guda shima bai taɓa manta su ba.
Ya isa gida bayan ya tsaya a wani masallaci yayi sallar isha'i, ya shiga da motarsa ciki sannan ya fito ya rufe gate din yana takaicin yadda sai wani satin zai samu maigadi kamar yadda kamfanin suka shaida masa.
Kuma bayan ya É—auko wayoyinsa biyu daga cikin motar ya dade tsaye a wajen yana waya da Ishaq, a yanzu haÉ—uwarsu ta É—anyi wuya, yana ta yawon zuwa Abuja ne akan wani workshop da suka fara a kotun tasu, don haka a cikin satin ma sau daya kawai suka haÉ—u.
Magana suke tayi akan gininsu, wasu filaye da suka siya a Lamiɗo Cresent ana musu gini iri ɗaya, bayani yake yiwa Ishaq ɗin cewa zasu canja masu gini don na yanzun an basu kudin kaya mai kyau amma sun siyo wani siminti da bashi da kyau har wani waje a cikin ginin Ishaq din ya rufta. Daga karshe suka tsaya akan Idan ya dawo zasu fara neman wasu ma'aikatan kafin suyi sallama da kalaman da Ishaq din ke gaya masa a mafi yawancin ƙarshen maganarsu.
"Dan Allah ka kula B."
Ya cije leɓɓensa yana kallon wayar, har yanzu Ishaq bai yarda dashi ba ya sani, gani yake a kowanne lokaci wani abu zai iya faruwa saboda yanayin ciwon nasa, amma shi baya jin hakan, akwai abubuwan da yawa a gabansa amma baya jin sunyi yawan da a cikinsu zai iya samun abinda zai canja yanayinsa, don haka yana amsa masa ne kawai don ko yayi bayanin ba zai yarda dashi ba.
Ya kashe wayar sannan ya debo kayansa na cikin motar ya shiga ciki da ƴar karamar sallamarsa, babu kowa a falon amma ƙamshin turaren wutar daya kula kwana biyu ana yinsa a gidan ya shiga hancinsa. Yayi sallamar da babu mai amsa masa sannan ya cire takalmansa daga gefe ya taka zuwa ciki, zuwa hanyar korodon nan, fitilar dakinta a kunne take kamar kowanne lokaci irin haka idan ya dawo, ya jiyo motsinta daga ciki har da ƙara ma kamar wani abu ya fadi kafin ya zarce zuwa dakinsa.
Wanka zaiyi ya fito ya shiga cikin gida, a can wajen Mami yake cin abincinsa kullum, kafin ya fita dai ya san watakila zai ganta su gaisa, amma zuwa lokacin da zai dawo ma ta riga ta kashe fitilar dakinta ta kwanta, ta kasan kofarta yake ganin hakan idan zai wuce. Ya isa É—akin nasa lokacin da yake tuno maganganun Baffa sanda yake masa fadan rashin halartarsa wajen daurin auren nan, Baba Usman yana daga gefensa yake cewa.
"... Idan kana tunanin zaka wulakanta yarinyar nan saboda iyayenta ba masu arziki bane Muhammad, ina so ka kalli iyayenka biyu da suke cikin gidan nan, daga ita Kilishin har Maimunan da ta haife ka, ka gaya min waye ya fito daga gidan mai kuɗi, ko kuma ni kaina da nake mahaifinka, ka gaya min gidan iyayena na gado da yake Bakori yaya yake, Mahaifina har ya mutu ɗakin kwanansa na ƙasa ne bai ko kai girman ɗakin nan ba ka sani.
Saboda haka na daura aurenka da yarinyar nan ne saboda shaidar halayen kirki da aka yi mata ita da iyayenta, ba don abin duniya ba babu ruwana da abinda mutane ke faÉ—a wai kwarya tabi kwarya, zaman aure nutsuwa da kwanciyar hankali ake nema a cikinsa ba suna ba, game da aurenka na farko kaima shaida ne akan hakan, don haka ina rokonka kar ka bani kunya a karo na biyu Ma'aruf."
Ya rufe idanunsa lokacin da ya saki ruwan shower akansa, indai Baffa zai kira shi da sunansa na asali ya sani cewa babban al'amari ne.
***
Doguwar riga ce a jikin Amina ta atamfa kalar milk da sea green, ta daura dankwalin sannan ta yafa wani karamin mayafi shima kalar sea green ɗin da ya tsaya iya kafadunta, ba kwalliya tayi ba don babu ko hoda a fuskarta amma fatar ta da'a kwana biyu ta kara washewa sakamakon canjin ruwa tana haskawa tare da fararen idanunta, kuma kawai ta yafa mayafin ne don bata son fita haka, taji lokacin da  Ma'aruf ya shigo, har wucewarsa ta gani ta kasan ƙofar dakin daidai lokacin da robar vaseline ɗin dake hannunta ta subuce ta fadi.
Sati guda kenan da fara rayuwarta tare dashi amma har a yanzu duk sanda ya fita ya dawo sai taga kamar shine ganinta dashi na farko, taji zuciyarta ta kasa tsayawa waje guda duk da cewar wannan taraddain da take ji a farko ya fara tafiya, don bata san me yasa ba komai yazo ne sabanin tunsninta kuma lokaci yana saukaka mata abubuwa fiye da zatonta.
Ko kaɗan bata ga wani yunƙurin cutar da ita a tare dashi ba, hasalima harkokin gabansa yake, da sun gaisa shikenan ba zai kara bi ta kanta ba. Ita kanta ta fara sabawa da gidan a yanzu, ranar da su Fatima suka zo sun taya ta sake kimtsa komai nata, sauran kayan kwalliyar nan da jakunkuna da takalman dake cikin Ghana must go ɗin nan duk an samar musu wajen daya dace dasu, ta basu kayan kwalliyar ma da yawa da kuma wasu daga cikin undies din.
Sannan a kitchen ma sun jera komai a muhallinsa, store din ya zama babu komai sai iya abubuwan da ba lallai amfaninsu yazo a kusa ba, bata san adadin mamakin da tayi ba na yawan ganin kayan, don bayan wanda aka siya mata kusan duk wanda zai kawo wata gudunmawa kayan kitchen É—in ne, don haka har wasu abubuwa ta ware a cikin ranta cewar zata ajiyewa Maryam idan lokacin nata auren yazo.
Sauran ɗakunan nan biyu ashe ɗaya carpet ne kawai da labulaye da kuma su tintin a jere, sai ɗayan ne aka tsara shi da wani irin nau'in furnitures masu tsananin kyau da ɗaukar ido, komai kalar grey, milk da kuma ash ne, wani silk bedsheet din da aka shimfide gadon dashi yana ta daukar ido a cikin hasken fitulum ɗakin, Aunty Safiyya bata sani bane da take cewa tayi zamanta a dakinta, dama ba'a tsara wannan don ita ba, shi suka yiwa abinsu, don har wasu fitulu aka saka a tsakiyar ceiling ɗin dogwaye masu haske, ga kalar fentin shima grey ne, labulayen kuma milk gabaɗayansu.
Kasa rufe bakinta tayi a lokacin da su Ummi ke cigaba da santin ɗakin daga inda suka tsaya  a bakin kuma ƙaton akwatin dake ajiye akan gadon, shi ya hana kowannensu shiga don ba sai ta gaya musu ba sun riga sun gama sanin dakin na waye.
Ta fita ɗakin ta rufe kofar a hankali kamar mai tsoron kar a jita sannan ta nufi hanyar kitchen, daga tsakiya akan work table ɗin nan tray din dake dauke da  flask din abincin da ta gama ne, a yau zata danne zuciyartaa tayi abinda ta kasa jiya, shekaranjiya ya aiko aka kawo kayan abinci kamar ya san dana ta matsu ta fara girki da kanta, don haka kai tsaye ta gayawa Samirah cewa ta huta tunda dama ita ke kawo mata abinci kullum, abincin da ita kadai take ci don ko yana sanin an kawo ɗin ma bai taɓa tambaya ba, ta fahimci idan ya dawo yayi wanka wajen Mami yake tafiya yaci abincinsa sannan ya dawo.
Don haka ko jiya da tayi girkin, har dashi tayi amma tana É—aki tana biya abinda zata ce masa taji ya buÉ—e kofar falon ya fita, haka ta debi abincinta ta rufe a fridge, amma yau ta gama shirya cewar ba zata bari ya fita ba, ba don komai ba sai don tarin nasihohin nan da aka yi mata suna ta yawo a cikin kanta, gani take kamar laifi take idan zata yi girkin babu shi, don akwai nasa hakkokin akanta kamar yadda shi ya sauke nasa wajen kawo abincin.
Bayan haka ma, ta karanci kalolin kayautata zamantakewa fiye da adadi a wajen Ammarta, abinda ke cikin zuciyarta kenan fal kuma dashi tayi tunanin zata iya cin galabar komai dama, har yanzu bai nuna wata alama ta cutar da ita ba don haka don me yasa ita zata fara da abinda bai dace ba?
A cikin addu'o'in da Gwaggo Balkisa tayi mata tace '... Allah yasa masa tausayinki a zuciyarsa..'
To idan bata kyautata masa ba ta yaya zai ji tausayin nata, Me Æ´an uwansa ma zasu yi tunani idan hakan ta cigaba? Idanunta suka hasko mata Hajiya Kilishin da yake zuwa wajenta yaci abincin, bata san me yasa ba ita har yanzu zuciyarta bata kwanta da ita ba, ranar da su Samirah suka fara kaita wajenta, hannayenta duka biyu ta kamo tace.
"Barkanki da zuwa cikinmu Amina, zuciyata cike take da murna idan na tuna cewa ƴa ta na kawo gidan nan ba kowa ba, ki saki jikinki ki saba da kowa, don a gidan nan bama taba banbanta kanmu, kowa ɗaya ne kuma kowa yana samun tallafawar ɗan uwansa saboda ƙaunar dake cikin zuciyoyin mu, kuma kema kin shigo kenan cikin wannan lissafin namu, rayuwarki zata canja da dukkan alkhairin da dake tare damu, kuma ina fatan kema zaki bamu damar amfana da irin naki alkhairin."
Haka kurum a lokacin sai taji maganganun basu tafi har cikin zuciyarta ba, sai taji kamar sun tsaru da yawa ace kai tsaye take faɗarsu daga zuciyarta a wannan lokacin, amma ko da ta daga ido ta kalli fuskarta, sai zuciyarta ta ture wannan kokwanton a gefe, tana tuna mata cewa itace wannan Hajiya Kilishin da ta tallafi rayuwarsu ta ɓangarori da yawa.
Hajiya Kilishin da kullum Baba yake ambato da kyawawan kalamai sannan kuma kamar yadda ta gani ta itace jagorar wannan gidan, don a yinin yau kawai ta fahimci abubuwa da yawa sai da izininta ake yi, don haka saboda tana ganin itace umul'abasin faruwar wannan auren bai kamata zuciyarta tayi wannan tunanin ba.
Amma Allah ya sani da suka shiga wajen Hajiya Maimunan wadda aka gaya mata itace asalin mahaifiyar Ma'aruf, zuciyarta kusan narkewa tayi tun kafin ta kai ga zama, mace ce har mace, irin manyan matan nan masu tsananin kamala da nutsuwa, fukarta fuska ce da za'a iya amfani da ita a koina a fadin duniya ta wakilci kalmar 'Uwa a rayuwar bahaushe' sai dai babu ƙafafu, tana zaune kan Wheelchair ɗinta da Hisnul Muslim a hannunta.
Kuma abinda ya bata mamaki shine itama da fara'arta da komai itama ta karɓeta, tana ta zuba tarin addu'oin fatan alkhairi da kuma fatan zaman lafiya a tsakaninta da Ma'aruf, wani abu data lissafa cewa yayi ƙaranci a kalaman Hajiya Kilishi.
Sai kawai ta ture wannan tunanin ta dauki tray din ta taho falon, sai da ta tsaya tana ta tunani inda zata ajiye kafin ta tsugunna a hankali daga gaban Three-sitter dake gabanta, kuma tsugunnawar tata tayi daidai da fitowar Ma'aruf daga falon, ta dago da kanta lokacin da kafafunsa suka tsaya cak yana kallonta daga hanyar kofar da ya nufa.
Yayi wankan, ya canja yansa zuwa wani bakin wando da dark navy blue riga data dace da kalar daren, kallonta yake yi da mamakin dake nunawa karara a fuskarsa, sai kawai tayi saurin ƙarasa ajiye tray din sannan ta mike tsaye itama. Kanta a sunkuye hannayenta cakude da juna tace.
"Barka da dare."
A cikin shirun dakin muryarta ta fito kamar wani fukafikin dake tahowa kasa a hankali, Ma'aruf ya gyada kansa yana kallonta har yanzu da mamakin a fuskarsa kafin ya amsa da.
"Kin yini lafiya?"
Haka yake tambayarta kullum,  don haka ta gyada kanta ba tare da ta dago ko ta daina cakuɗa yatsunta cikin juna ba, kuma sai tayi shiru bata ƙara cewa komai ba. Amina ta san ya kamata tace wani abun game da abincin da yake kallo a gabanta amma bata san me zata fara cewa ba, kuma ga mamakinta sai kawai taji yace.
"Wannan abincin..."
"Naka ne..."
Ta ƙarasa da sauri tana ɗago da kanta, idanunsu suka haɗu waje guda sai tayi saurin sake maida kanta kasa ta cigaba da murza yatsunta, amma zata iya karanta mamakin daya karu cikin muryarsa sanda yace.
"Masha Allah, kamar kin sani dama yunwa nake ji."
Wani abu a cikin zuciyarta yayi tsalle da jin hakan, yayi kokarin subucewa daga zuciyarta zuwa kan fuskarta amma ta tare shi da karfi tana cigaba da motsa hannunta, ƙarar takunsa taji yana tahowa don haka tayi saurin tsugunnawa ta ɗauki plate din tana bude murfin flask ɗin farko.
Ƙamshin abincin ya shiga hancin Ma'aruf sanda ya karaso kan carpet din, idanunsa na kallonta tana zubawa yayin da ƙaramin mayafin data yafa kalar kayanta ya zame yana reto a gefen fuskarsta, wani abu yake ji na daban yana shiga zuciyarsa bayan mamaki, sai kawai ya zube wayoyin hannunsa akan kujerar sannan ya ƙarasa kan kapet ɗin gaban abincin ya zauna, ƙamshint turarenta mai sanyi ya shiga hancinsa tare da na abincin don a yadda ya zauna tray ɗin shi kaɗai ya raba tsakaninsu.
Kuma bai ce mata komai ba, yana kallonta ta zuba iya adadin da take so na komai sannan ta ture tray din gefe a hankali ya tafi cikin laushin carpet din kafin ta ajiye plate din a gabansa. Shinkafa ce fara da vegetables a ciki sai kuma miyar dake tashin ƙamshin daya baɗe falon a lokaci guda, akwai wani abu a dan bowl data zuba na cabbage da kuma Irish potato mai hade da nama duk da wanda yake cikin miyar.
Wani abu ya motsa a cikin zuciyarsa cike da yabawa kokarinta dama abincin tun kafin ya kai bakinsa, yana tuna masa da wani al'amari daya shuÉ—e a labarin aurensa na farko, ba kai tsaye ya samu irin wannan gatan ba.
"Thank you so much."
Muryarsa ta furta a hankali da wani sauti da yasa numfashin Amina katsewa a kirjinta, ba shiri ta gyada kanta sannan ta mike da sauri.
"Ina zaki je?" Shima yayi tambayar kamar kai tsaye bai shirya mata ba.
"Zanje in kawo ruwa ne."
Muryarta ta fito tana fallasa bugun da zuciyarta ke yi, kuma kafafunta basu motsa ba sai da ya É—aga mata kansa.
Ta isa kitchen din ta É—auko robar ruwa guda É—aya da ba'a fridge ba, don ta kula duk sanda zata ganshi da ruwa a hannunsa to ba mai sanyi bane, shi yasa lemon data haÉ—a ma ta kaishi can kasan fridge din baiyi sanyi sosai ba, Samirah ce ta koya mata hada lemon, kuma ta tabbatar tayi komai daidai, sai dai bata san dadinsa ko akasin sa ba tunda bata taba sha a wani waje ba.
Ta isa falon lokacin da idonta ya sauka akansa ta baya ya kai lomar da bata san ta nawa bace cikin bakinsa, zuciyarta ta kara nutsewa cikin kirjinta da tsarin nata ya tafi daidai, a hankali kafafunta suka ƙarasa kan carpet din, tana jin yadda kafar tata ke shigewa cikinsa saboda laushin sabunta. Wannan karon nesa kaɗan dashi ta zauna sannan ta fara ƙoƙarin zuba lemon a kofi.
Ma'aruf ya dago ya kalle ta, har yanzu mamakinta bai bar kan fuskarsa ba, kuma a lokaci guda yaji kalaman da Mamin ta taɓa gaya masa suna dawowa cikin kansa.
... Wannan ba irin ba irin Ruƙayya bace Ma'aruf, don nayi Imani yarinyar nan zata baka kulawar da kake buƙata.
Abinda Mamin bata sani bane, ita kanta Rukayyan tayi iya kokarinta a zamansu, don ta canja abubuwa da yawa a rayuwarta zuwa bukatarsa, matsalar kawai shine don son zuciyarta tayi komai, babu abinda tayi saboda shi ko don ta kyautata masa, don haka itama zai iya yiwuwa ta fara hakan ne don an saka ta, don bin umarnin da ya tabbatar shi tayi har auren nasu ya kasance, yaji zuciyarsa ta matse da wannan tunanin amma kuma sai ya samu sauƙi da hasashen cewa haka ba zai iya zama gaskiya ba.
Ta gama zuba lemon a wannan lokacin, ƙarar awarwaron dake hannunta ya janyo hankalinsa sanda take ajiyewa a gabansa daidai lokacin da wayarsa tayi kara daga kan kujerar nan, don haka tayi amfani da damar don miƙewa ta bashi waje amma sai muryarta ta tsaida ta.
"Ki zauna."
Fuskarsa fayau yana kallonta kafin ya juya ya dauki wayar. Ta haÉ—iye wani abu a makogwaronta a hankali sannan ta dawo da baya ta zauna É—in, nesa kaÉ—an dashi kamar É—azu.
Ya É—auki wayar yana magana ta ciki, ta fahimci da wani yake magana kuma akan harkar aikinsu ne bayan hakan bata gane komai ba, amma kuma yanayin yadda yake maganar ya saka taji zuciyarta na sakewa da amon muryar tasa. Ya gama wayar ya ajiye ta a gefensa sannan ga mamakinta taji yace.
"Faruq ne, abokina ne a wajen aiki."
Sai ta daga kanta lokacin da ya sake kai wata lomar bakinsa sannan yace.
"Abincin nan yayi daÉ—i sosai Amina. Kinyi kokari."
Wani abu ya matse a zuciyarta daga yadda muryarsa ta ambaci sunanta, kamar zata yi magana amma kuma sai ta sake gyada kanta kawai tana wasa da karshen mayafinta. Kuma Yanayinta yasa Ma'aruf yaji a lokaci guda yana son suyi hira, aƙalla yau maganar tasu ta tsallake babin gaisuwa saboda haka yana kallonta yace.
"Munaya ta gaya min kina son karatu, tace ta samu wasu novels a wajenki. kina da litattafai da yawa."
Sai da sakanni biyu suka wuce sannan Amina ta yarda da maganar da ya furta saboda É—an mamakin da ya kamata, ranar da take kokarin samawa litattafanta waje ne Munayan ta shigo ta ganta, a ciki har da wasu English novels dama na Hausa wanda take tarawa tun tana makaranta, shikenan sai suka shafe kusan rabin yinin suna hirar labarai kala-kala har ta ara mata wasu ma ta tafi dasu, don haka ta tabbata a yanzun ma ganinta yayi tana karatun É—aya daga cikin wanda ta É—auka.
"Wanne da wanne kika karanta?"
Muryarsa tana fitowa ne kamar yadda take jinta a kullum idan yana waya ko kuma da wani, amma a yanzu da ta san cewa ita yake wa magana sai take ji ta daban, tana saka ta Æ´ar rikicewar da bata shirya ba. A hankali ta daurewa hakan muryarta ta shiga jero masa sunayen littattafan da ta san sunyi suna amma da yawansu yace bai san su ba saboda yawanci akan Romance ne shi kuma yace ma yafi karanta Non-fiction, yana yi yana cin abincin cike da wani abu da zata iya kira da nishadi.
"Akwai wani 'The Life we had' na san zaki san shi.'"
Ta ɗaga kanta da sauri don ji tayi kamar hakan na kaɗe tasirin da muryarsa ke yi a zuciyarta, kuma a lokaci guda bakinta ya ɓalle da wani murmushin da bata shirya masa ba tana tuno yadda akayi ta karanta littafin a wani shagon bakin titin unguwarsu inda ake sayar da shi, zuwanta shagon nan bakwai kafin ta kai karshen littafin saboda yayi mata tsadar da ba zata iya siya ba, kuma wata ƙawarta da suka yi makaranta ɗaya da yawanci litattafan wajenta ma ita ta bata, itace ta dame ta zancensa, bayan sun bar makaranta ne a lokacin ita tana can Bauchi babu ta yadda zasu iya haɗuwa sai dai ta kira ta a waya tayi bata labarinsa. Tana tuna ranar da ta kai ƙarshen labarin da wani a cikin masu tsaron shagon ya gane ya tada ballin sai ta biya, da taimakon Aminu aka rufe case ɗin.
Bata sani ba ko shima murmushi yayi don kanta yana sunkuye amma taji muryarsa ta É—an canja lokacin da yace.
"Ke ma kamar su Munaya ce ashe, ban san me marubucin littafin yayi da ya siye zuciyarku da yawa ba, babu wani abu da yake gaskiya a labarin nan."
Amina bata san sanda ta É—ago ta kalle shi ba tana girgiza kai, tace.
"Ai dama Fiction ya gaji ƙirƙire-ƙirƙire da yawa, shi yasa ya kirkiro komai ɗin don ya fito da ma'anar labarin sosai."
Ya girgiza kansa shima.
"Saboda kawai ya karya zuciyar mutane ne, shi yasa ma ya kashe su daga karshe, daga lokacin da na fahimci itama yarinyar mutuwa zata yi, na tsayar dashi ban ƙarasa kallo ba."
Sai ta sake É—agowa ta kalle shi.
"Na zata novel ne."
Ta fada kamar tana tsoron labarin nasu zai banbanta, amma sai yayi saurin daga mata kai.
"Novel ne, amma lokacin da Munaya ta takura min da zancen labarin bani da time É—in karatu, so sai kawai na siyo film din na kalla instead."
Ta gyada kanta sau daya sannan ta sake maida shi ƙasa ba tare da tace komai, yaji wani abu na shiga zuciyarsa yadda ta fara sakewa dashi a yanzu, don haka kai tsaye ya sake tambayarta.
"Baki kalli film din ba?" ya tambaya yana nazarin abinda bata faɗa ba akan furkar ta, kuma sai ta bashi amsar da ya riga ya sani ɗin ta hanyar daga kanta.
"Insha Allah zan kawo miki ki gani."
Sai ta É—ago ta kalle shi, yayin da hannunta ya tsaya da wasa da mayafin nata.
"Allah ya yarda."
Ta furta a hankali tana kallonsa, kuma a cikin idanun nata Ma'aruf yaga daren ya tsaya cak kafin ta sake sunkuyar da kanta a hankali, yaji wani abu yaji kamar tausayinta na bi ta kan zuciyarsa.
Tana da rayuwarta ya sani, watakila har ma da mafarkai na abubuwan da take son cimma, amma yanayin yadda auren yazo ya sani cewa yabi ta kan abubuwa da yawa a rayuwar tata, wanda da shine baya taɓa jin zai jurewa hakan, amma ita gata a zaune har tana kokarin yi masa hidima, yaji wani abu ya zarce cikin maƙogwaron sa a lokaci guda, a baya yana jin zai iya bin kowacce hanya don sanin meye haɗinta da Jamal amma tun a yanzu ya fara jin cewa ba zai iya yin abinda zata yi dana sanin haɗuwa dashi a rayuwarta ba.
***
Washegari da safe Hajiya Kilishi ta buɗe kofar ɓangarenta, fuskarta ta faɗaɗa da wannan murmushin nata mai armashi a duk lokacin da ta ganshi duk kuwa da cewar a jiya tayi ta kallon agogo cikin lissafin zuwansa amma bata ganshi din ba, dalilin da yasa a yau ta tashi da sassafe kenan don ta san yana da karbar magani a yau, don haka ta buɗe kofar zuciyarta na fatan ya kasance Ma'aruf ɗin ne, kuma fatan nata ya karɓu don yana tsaye a gabanta yana murmushin da take jinsa kamar ashanar dake ƙyasta zuciyarta wajen kamawa da wuta.
"Tun jiya muke kallon hanya Ma'aruf..."
Ta fada tana kallon idanunsa da kullum suke gaya mata shi daban ne a lissafinta ba sai ta rantse ba, zuciyarta tana yin fiffike ne ta tashi sama ta zagaya a duk lokacin da ta ganshi a gabanta irin haka.
"Mami I'm sorry, jiya aiki ne yayi min yawa kuma a gida naci abinci shi yasa baki ganni ba."
Maganar ta taho kamar wani gingimeman dutsen da ya faɗo daga kolulowar sama ya dira a tsakiyar kanta, a lokaci guda murmushin fuskarta ya ɗauke, idanunta suka tsaya akansa cak a sanda ya kara wayar hannunsa a kunne ya shiga yiwa wani Benjamin magana cewa yayi wa Legal Department ɗinsu bayani su ƙarasa shiryawa kafin ya ƙaraso.
Ya katse wayar ya juyo ya kalle ta a lokaci guda da yanayin nata ya baje, fuskarta ta cakuÉ—e da murmushin da yasa shi gyaÉ—a mata kai kafin ya wuce zuwa ciki, Abinda bai sani ba shine wannan karon murmushin ba nasa bane, na halittar da take hangowa a cikin idanunta ce... Amina!
A yau an ƙaraso gaɓar da take jira, a yau tsarinta zai fara ba sai gobe ba, bata wasa da lokaci balle har tayi sake da koda ƴar mitsitsiyar dama ce... A yau Amina zata shigo cikin ukunta!
A yau duk wani mahalukin da yake da kusanci da Amina zai shigo cikin lissafinta!
**
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
BABI NA SHA DAYA.
~~~~~~~
I've never fallen from quite this high
Fallin' into your ocean eyes
Those ocean eyes.
                               -Billie Ellish
A wannan ranar Amina na kwance daga kan gadon ɗakin tana sauraren wani shiri mai taken 'Allah ɗaya gari banban' da baya taɓa wuce ta daga cikin rediyon wayarta.
Idanunta kusan a rufe suke yayin da take sauraren maganganun mutanen dake gabatar da shirin, yau hira ake akan daya daga cikin garuruwan da take son zuwa a rayuwarta, Paris... Don haka sosai take jin daɗin duk wani bayani da baƙin da aka gaiyato suke yi na yadda garin yake da kuma tsare-tsaren su.
Sai dai duk yadda hankalinta ke kan shirin zuciyarta kuma nata zarya a can falon gidan inda ta kammala komai na abincin Ma'aruf ta ajiye masa kaar jiya, a yau ta riga ta tsarawa kanta cewa ba zata fita ba don Allah ya sani bata so yaga kamar tana kokarin shige masa ne ko kaɗan, ƙundubalar da tayi wajen yi masa abincin ta wadatar tunda har yanzu bata san manufarsa akanta ba.
Ko a jiya umarnin da ya bata ne kawai yasa ta zauna ba wani abu ba, yadda muryarsa ta furta 'Ki zauna' da kuma yadda ya kalle ta da idanunsa bai bata damar zabi ba ko kadan. Duk da cewa kuwa taji dadin hirar, tsaya... Ba hirar tasu ce ta mata daÉ—i ba, zancen cewa wannan labarin yana da film ne, don Allah ya sani zata so ganin yadda dukkan tunaninta game da komai na labarin zai fito zahiri.
"... Wato ina gaya maka samun gida a garin nan shine babban abu mai wahala, gidaje ba karamin tsada ne dasu acan ba..."
Hirar rediyon ta cigaba da fitowa yayin da zuciyarta ta fara lissafin kamar yau ya daÉ—e da yawa, don ko da safe bata ganshi ba kuma yau ita kadai ta yini a gidan, su Sahla da Zahran da suka yi mata alkawarin zasu sake shigo mata yau sun manta da zuwansu makarantar Haddar da suke zuwa shi yasa bata gansu ba.
Tun da tazo gidan basu shigo mata ba sai jiyan, kuma sai a jiyan ta gane ashe su ma suna da magana kamar su Samirah, a cikin gidan idan ta gansu da littafinsu kawai gaishe ta suke yi su cigaba da harkokinsu, amma jiyan da suka shigo tasha labarai kala-kala wanda mafi yawanci ba komai ta gane ba.
Don a baiyane yake yanayin rayuwarsu da tata ba iri ɗaya bane, abubuwan da suka taso suka sansu ita har yanzu saninta bai ƙaraso nan ba, yanayin makarantar su dama ƴaƴan masu kuɗin da suke mu'amala dasu ba iri daya bane da abinda ita ta taso ta sani. Ta tuno wata magana da Aminu ya taɓa gayawa Maryam ranar da yake tsokanarta bayan ta gama kurin cewa ai ita babu inda zata je a raina ta.
"... Nan bayan layin nan idan aka ƙarasa ba sai anje da nisa ba za'ayi iya ɗebo sa'anninki biyar da in suna hira ba zaki taba iya magana ba wallahi sai dai kiyi ta binsu da kallo kina wage baki."
Itama dai kuwan ta wage jiya, don murmushi kawai tayi ta binsu dashi kamar yadda take yi a wajensu Samirah, don har gwara su Zahran ma, su idan suka fadi wani abu sai ta biya shi sau biyu akanta kafin ta fahimta musamman Surayya da ta fahimci tafi su iyayi gabaÉ—aya. Suna da daÉ—in mu'amala sosai, da gaske suke sun karbe ta a cikinsu ba tare da tunanin komai ba,
Ta tuna sanda Samirah ke mata bayanin dalilin da yasa basu je gidansu da biki ba.
"Mu fa bamu san da bikin ku da Yaya ba sai ana saura two weeks da aka haÉ—a lefe sannan Mami ke gaya mana, kuma ko ranar dinner ma munso mu kai muku cards din. Yaya Shukra ce ma ta bani ranar luncheon na saka a jakar Khadija (wata kawarta) ita kuma sai tazo da wata jakar kuma ta manta bata É—ebo ba. A ranar ni kuma I was so busy kamar me, shikenan ban samu time munje mu É—auko ba. Da na kira Yaya kuma na gaya masa cewa yayi kar mu damu kawai."
Amma duk da yadda ta fara sakewa a cikin nasu, tana kewar gida kamar ba gobe, abubuwa da yawa akwai su anan na duk wata buƙatar rayuwa, ga komai sabo koina ƙal-ƙal, gashi babu wanda ya taɓa ko haɗe mata rai har yanzu, idan ta shiga cikin gidan kowa haba-haba yake da ita, hatta su Salma amaren da akayi bikinsu tare dukksnsu sun gaisa a wayar Samirah, da Salman ma ba sau biyu suna gaisawa.
Ga Hajiya Kilishi da take nan-nan da ita kullum fuskarta dauke da fara'a tana fadin ita Æ´arta ce, Ranar da taje ta gaishe da Baffa ranar ta fahimci dalilin da yasa Baba ya bada aurenta a gabansa ba tare da wani tunani ba, dattijo ne kamili mai nutsuwar da a fuska kadai kowa zaiyi masa shaidar hali na gari, don haka babu wata matsala da ta guskanta a gurinsa shima.
Sannan shi kansa uban gaiyar har yau ko haɗe rai bai taba yi mata ba, amma duk da haka, tafi son rayuwar cikin ƴanuwanta akan wannan, tunda har yanzu zuciyarta bata gama kwantawa da komai ba, tunaninta iri ɗaya ne da Amma dama kuma Fatima, dukkaninsu sun yarda cewa akwai wani abu dake tahowa wanda bai karaso ba, don ba'a ɗora turbar auren da cewar komai ya tafi daidai ba, sun sani cewa ba sun kawo ta cikinsu ne don su nuna mata kirkinsu ba dashi da ƴan gidan nasu, dole akwai wani abu da yake a ɓoye wanda har yanzu basu kai ga saninsa ba.
Su Aminu da Baba ne kawai hankalinsu a kwance don duk sanda suka yi waya da Baban, zai yi ta zubo mata tarin addu'o'in da suke karya zuciyarta, shi har yanzu zuciyarsa guda ɗaya ce game da auren, ya riga ya aminta da Baffa da ma Hajiya Kilishi ta yadda baya taɓa iya hango komai.
Ta lumshe idanunta a hankali tana jin yadda bacci ke shirin ɗaukarta a lokacin, ta shiga ƙokarin kore shi don aƙalla tana son jin lokacin da Ma'aruf zai dawo amma baccin mai nauyi ya ƙara karfinsa, don haka wata zuciyar ta gaya mata cewa zata iya ɗan runtsawa tunda tayi sallar isha kuma bata wani samu baccin safe ba sosai, da wannan lasisin da zuciyarta ta bata taji maganganun cikin rediyon nan suka zuƙe daga kanta a hankali, taji su suna yin nisa da kunnenta kafin a lokaci guda taga Aminu a tsaye daga bayan idonta.
"Me yasa kika kasa Amina?"
Kai tsaye ya tambaye ta yayin da idanunsa ke kallonta, kuma kalaman suka isa kanta amma suka kasa bada ma'ana saboda dukkan tunaninta ya tsaya cak tana kallonsa da dimbin mamaki, Yaushe yazo? Yaushe yazo ko kuma ita yaushe ta bar cikin gidan, don daga nesa tana hango duhuwar wasu dogwayen bishiyu, hakan yasa gabanta fadi da dukkan tsoron da zuciyarta zata iya dauka.
Tayi ƙokarin ta kalli kanta amma sai ta fahimci bata iya ganin jikinta kwata-kwata, kamar idanunta ne kawai a wajen suke ganin komai amma babu gangar jikinta, ta ɗago ta sake kallon Aminun da har yanzu ke tsaye a gabanta.
A lokacin ta kula cewa idanunsa sun canja, kalolinsu ba iri ɗaya ne daga yadda ta sansu ba, sun koma baƙiƙ-ƙirin dauke da kyallin kwalla yayin da fuskarsa ke nuna dukkan wasu kalolin tashin hankalin da bata taɓa gani a fuskar Aminun ba, Aminun mai raha da fara'a, Aminun data sani mai ɓoye damuwarsa a kodayaushe.
"Me yasa kika kasa Amina?"
Muryarsa ta sake tambaya da amon da ya kara  hargitsa ta, kuma bata san lokacin da ya matso gabanta ba sai kawai taji ya riƙo hannunta na dama.
Ta kalli inda hannun nata ya kamata ya kasance, babu komai sai yadda yatsunsa suka riƙe ta, lokacin da ta ɗago da idonta sai taga ashe ya jawo ta ne har sun iso wajen duhuwar bishiyun nan, tashin hankalin ta ya ƙaru don tana jin yadda ƙafafunta da basa nan suke tafiya, da kuma yadda hannayenta ke rawa a cikin nasa.
Hankalinta ya kasu wajen nazarin bishiyun sanda suka tsaya a wani waje, ta juyo tana kallon yadda yanayinsa ke haskawa da dukkan raunin da bata taɓa hange ba, taji ta ƙara rikicewa, taji abubuwa da yawa suna tasowa cikin kanta, tambayoyi fal suna ihu da kokawar fitowa daga bakinta da ta san babu shi balle har ta iya furta su, kowanne lungu da saƙo na tunaninta ya cika da hanƙoro, kamar tana jiran wani abun da bata san meye ba.
Kuma kwatsam sai ta nemi bishiyun nan dake kewaye dasu duka ta rasa, warin ƙonewarsu ya cika hancinta amma babu su ɗin balle kuma alamun wutar, kuma babu wani ɓata lokaci kunnenta ya fara jiyo mata muryoyinsu, Maryam ta fara ji, tana ihu mai haɗe da salati, sai ta jiyo ta Hafsa da Adam ma, kowanne yana kuka mai nuna tsananin azaba, bata san ya akayi ta iya tsinto muryoyin su Fatima, Ummi har ma da ta wasu daga cikin ƴaƴan kawu Malam ba.
Kuma kafin wani abu ya sake giftawa a cikin kanta ta jiyo muryar Baba yana faman kiran sunayen su Maryam ɗin har ma da sauran mutanen da bata iya tantance muryoyinsu ba, hankalinta ya kara tashi duniyarta ta rikice, ihu da hargowar suka cika kanta kota'ina, kuma a lokacin da ta juya zata kalli Aminun sai taga babu shi, a yanzu Amma ce tsaye tana kallonta, fuskarta ɗauke da wani irin murmushi mai ciwo yayin da take kallonta da dukkan wani fata na duniya.
"Me yasa kika yarda ba zaki iya ba Amina?"
Tayi tambayar a lokaci guda da itama ta neme ta ta rasa, wajen ya koma babu komai sai tashin ihun ƴanuwanta da kuma hargowarsu yayin da warin ƙonewar nan ya cigaba da cika wajen. Ta kasa gane komai ko kuma abinda yake shirin faruwa, abinda kawai zata ita tunawa kafin ta farka shine daga cikin muryoyin dake ihu, ta jiyo wata murya da ta kasa gane wacece ko kuma inda ta santa, muryar tana ƙyalƙyala wata irin dariyar da bata taɓa jin irinta ba!
Dariyar ta shiga amsa kuwwa a kowanne ɓangsre na wajen yayin da ihun mutanen dake amsa sunan rayuwarta ke cigaba da tashi.... A lokacin ne kuma ta farka a firgice, kafafunta suka mike tsaye akan gadon bakinta na biyo kalaman Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, a cikin ɗakinta take har yanzu, akan gadon da bacci ya ɗauke ta, amma tun yaushe? Don rediyon wayarta da ta bari a kunne yanzu ƙarar shuuuu kawai take fitarwa.
Tasa hannu ta jawo ta da sauri, ta kashe rediyon tana neman lokaci, karfe ɗaya da rabi na dare, wani salatin ya sake suɓucewa a bakinta cike da mamakin yadda akayi tayi bacci mai nisan haka, sai kawai ta wullar da ita gefe ta janyo dankwalinta daya zame akan filon data kwanta tayi saurin ɗaure kanta, koina a jikinta rawa yake har yanzu yayin da mafarkin ke ƙara dawowa cikin kanta, bata fahimci komai a cikinsa ba amma Allah ya sani ta tsorata sosai da yadda abubuwa suka faru don bata iya tunawa idan ta taɓa irin wannan mafarkin a rayuwarta.
Taji maƙogwaronta ya bushe yayin da amon muryar nan dake dariya a cikin mafarkinta ke dawo mata, bata san me hakan
ke nufi ba, bata san waye zaiyi dariya alhali tashin hankali irin wannan yana faruwa ba, kuma har a yanzu tana jin cewa kamar ta san muryar amma ta kasa tabbatar da inda ta santa.
Makogwaronta ya ƙara bushewa yayin da take kokarin saita zuciyarta da har yanzu ke bugawa, ta sauko daga kan gadon, wata doguwar riga ce a jikinta ta bacci da bata kai ƙasa ba ta gaba, don haka kusan tun daga saman gwiwoyinta a waje suke, kuma ba tare da tunanin komai ba tayi hanyar fita daga ɗakin.
Kitchen zata je ta ɗauko ruwa, wataƙila zai iya wanke bugawar da zuciyarta ke yi bayan ƙishirwar, idan ta dawo tayi sallah raka'a biyu kuma, watakila tunaninta zai iya komawa daidai.
Jikinta na rawa har a lokacin da ta isa kitchen ɗin, ta buɗe ƙofar a lokaci guda da hasken fitilar da aka kunna ya shiga idonta kafin shi, yana zaune daga kan worktable ɗin tsakiya na kitchen din, fitilar dake saman wajen ita ce a kunne da labtop a gabansa yana danne-danne, a gefe kuma foodflask ɗin abincin data dafa ne.
Kuma duk da rikicewar da take ciki, ta gane cewar babu riga a jikinsa, wata bakar singlet ce kawai da ta fito da faɗin kafaɗunsa ta kowanne gefe, shima ya dago daga kan labtop din yana kallonta daidai lokacin da ta bude ƙofar.
"Me ya faru? Me ya same ki?"
Ya tambaya kai tsaye yana kallonta, kuma ba shiri wani abu ya zarce maƙogwaronta jin yadda muryarsa ta fito a cikin shirun daren tana gaya mata kamar har yanzu a cikin mafarkin take, sai ta ɗaga girgiza kanta kawai da sauri sannan ta sake haɗiye abinda ke bakinta kafin tace.
"Ba komai, ruwa zan É—auka."
Da haka ta saki hannun kofar ta nufi wajen fridge, Ma'aruf ya bita da kallo zuwa wajen fridge ɗin, yanayin fuskarta a firgice yake sosai duk da kokarin da tayi wajen ɓoye hakan, kuma ko daga yadda muryarta ta fito ya san akwai wani abun, da wuri tayi bacci ya sani don bayan ya dawo yaga alamun hakan duk da yau cikin gida kawai ya wuce wajen Mami, acan yaci abincin darensa ma bayan sun tattauna maganganun da yasa ta kira shi, zancen Hamida.
Kuma bayan ya shigo ya tarad da nata abincin jere a falo, haka kurum sai yaji wani iri, sai yaji kamar bai kyauta ba, ya sani ba zata ji dadi ba idan har ta farka ta ganshi a yadda ta ajiye tunda jiya ta bashi kuma yaci.
Bai tsara komai tare da ita ba, abinda ya sani kawai shine aurensu zai zame masa garkuwa ne har lokacin da zai gama da case ɗin dake gabansa na kamfanin nan kafin ya fara binciken da zai shafe ta. Amma tun jiya da yaci abincin nata, sai yaji wani gefe a zuciyarsa ya kara nutsuwa da ita, har yana gaya masa gwara nata ma akan na Mami, tunda aƙalla ya san ita tayi da kanta, na Mamin kuma idan Samirah bata nan masu aikinta ne kawai.
Don haka dole a yanzu da ya É—ebo aikin daya shirya zai kwana akansa, ya É—auko abincin daga falo ya taho kitchen tunda babu Dining area a gidan, kuma ba yunwar yake ji ba amma da ya zuba ya fara ci sai yaji kamar dama bai ci komai ba, yaji hankalinsa ya sake nutsuwa sannan aikin da yake yi na tafiya akai-akai yayin da dukkan maganganun da suka yi da Mamin akan Hamida ke dawowa kansa kafin ta shigo a yanzu da yanayinta a hargitse.
Sai kawai ya tura kujerar da yake kai baya ya mike tsaye.
"Wani abu ne ya same ki?"
Ya sake tambaya yana tahowa inda take shirin buɗe fridge ɗin, kayan jikinta yake kallo a yanzu, kamar na bacci ne... wata riga mai tsawo daga baya amma daga gaba kamar an guntule ta har wajen gwiwarta, don haka kafafunta na tsaye a waje, kuma bai san me yasa ba sai yaji wani abu a zuciyarsa na yabawa da yadda ɗankwalin kanta yayi kala ɗaya da rigar, Pink. Kallonsa take yi itama, idanunta farare na nuna dukkan wani alamun tsoron da ba sai ta furta ba, don haka kai tsaye cikin hasashensa ya sake tambaya.
"Mafarki kika yi?"
Amina bata san lokacin da ta ɗaga kanta ba don kayan jikinsa a yanzu sun karawa rikicewarta tasiri, bayan baƙar singlet din nan, three-quarter din wando ne kuma a jikinsa wanda da kadan ya wuce gwiwa, sannan ga muryarsa mai zurfi da taji tana tayar da wasu abubuwa akan fatar ta bayan rawar da jikinta ke yi.
Kuma bata yi aune ba sai jin hannunsa kawai tayi ya riƙo nata ɗaya, ya jawo ta zuwa wajen kujerar daya taso ya zaunar da ita a ta gefen inda yake zaune kafin shima ya zauna.
"Kinyi addu'a?"
Tambayar ta tuna mata da abu na farko da ta kamata a e tayi, amma tsabar rikicewar da tayi, zuciyarta bata kawo mata wannsn lissafin ba, sai ta girgiza ksnta a hankali don ko tayi ƙokarin yin ƙaryar ma bata san me zata ce ba, ba zata iya wani tunani mai kyau ba slhali har yanzu yana riƙe da hannunta sannan ga kafafuwanta tun daga kan gwiwarta a waje daga ƙasan rigar nan, bama za'a lissafa da kayan jikinsa ba...
"Suratul Ikhlas sau uku, Suratul Falak sau uku, Suratul Nas sau uku..."
Muryarsa mai zurfi ta sake faɗa yana kallonta, bata da wani zabi sai ta rufe idanunta, ta haɗiye yawu a maƙogwaronta kafin a hankali bakinta ya shiga karanto su, bata jin sautin muryarta yana fitowa amma tana kaiwa karshe, ya sake cewa.
"Ayatul Kursiyu..."
Ta kai ƙarshe lokacin da taji kamar almara, ƴar rikicewar tata na bin iska, kuma shirun da yayi riƙe da hannunta bai saki ba wani abu ne daya saita numfashinta daga hawa da saukar da yake faman yi, taji kamar hannayen nasa sunyi wa nata wata rumfa ne ko kuma sun zama wani bango da ba abinda ya isa ya ratsa ta cikinsu ya cutar da ita, don haka a hankali nutsuwarta ta fara dawowa jikinta.
"Mafarki ba gaskiya bane, daga shaidan yake zuwa ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru insha Allah."
Sai kawai ta gyada kanta a hankali yayin da take ture dukkan wani tunani daga cikin kanta tana yarda da kalaman nasa don ta samu zuciyarta ta dawo daidai, Mafarki ba gaskiya bane, ta shiga biyawa zuciyar tata layi bayan layi.
Abinda bata sani ba a wannan lokacin shine, wani lokacin mafarki na juyewa tamkar mudubi, ya nuna abinda zahirin ke iya haifarwa!
***
Ƙarfe bakwai na safe.
Idan akwai wani abu daya rage a rayuwar Ma'ruf ta baya, shine ƙaunarsa da football (ƙwallon kafa) shi kaɗai ne abu guda ɗaya bayan sunansa da kuma kamanninsa da zai ce basu canja daga Ma'aruf ɗin da yake a baya ba, Ma'aruf ɗin da yake kafin rasuwar Jamal, amma duk wani abu bayan hakan komai da yake yi ba rayuwarsa bace.
Son football É—in ne kawai yayi yawa a zuciyarsa da ba zai iya barinsa ba, shi yasa yawanci duk weekend da safe yana stadium É—in Sani Abacha, team ne dasu guda da suke da ranakun yin wasa da kuma ranakun training, sannan yana É—aya daga cikin members É—in dake kula da wajen ma, duk wani taimakon harkar kudi da ake yi a wajen su suke badawa, idan ya gama ya fito haka zaka ga samarin nan ma'aikatan wajen sun biyo bayansa har wajen mota don ya sallame su, don haka babu wanda bai sanshi ba a wajen.
Yau asabar can yayi niyyar zuwa don tun da ya dawo daga sallar asuba ya shirya, amma yayi-yayi da motarsa taƙi tashi, jiya lafiya lau ya ajiye ta kuma a saninsa bata da wata matsala amma sharrin karfe ance ba abinda ba zai iya ba, haka ya hakura ya rabu da ita, sai kawai ya fito da ball ɗin sa daga booth ɗin motar ya shiga training ɗin da ya saba a compound ɗin gidan.
Kusan ƙarfe bakwai da rabi lokacin da wayarsa tayi ƙara daga can saman motar inda ya ajiye ta, kuma sai da ya kai ball din sama sau biyu sannan yazo ya ɗauka, Martha ce.
"Barka da safiya sir, RTL sun bugo waya cewa yau zasu sauka a Kano, don haka meeting din zai zama karfe huÉ—u na yamma."
Ta zayyano dukkan bayanin da harshen turanci, hannunsa ya zura cikin kansa don kwata-kwata ya manta da zancen cewa zasu iya yin meeting din a yau, yayi niyyar babu inda zai fita zai zauna ya huta ne don Allah ya sani ya aikatau a cikin satin nan gashi jiya ma bai wani samu bacci mai yawa ba. A hankali ya cije leɓɓensa yayin da ta cigaba da yi masa bayanin cewar sunyi waya da Faruq da sauran board members ɗin nasu ta shaida musu komai, shi gabadaya ya manta ma da nasa takardun da ya kamata ya karanta kafin a shiga meeting din jiya a Office.
"Sannan kuma Sir ka manta papers na background Information din a Office, dole zaka buƙace su kafin a shiga meeting ɗin."
Ya sake motsa hannunsa a cikin gashin kansa.
"Na sani Martha, yanzu kuma ban san ya za'ayi ba gashi motata taƙi tashi, amma bari na kira Ishaq sai a ɗauko min tasa."
"Okay sir." Ta amsa muryarta a ƙasa.
Da haka suka gama wayar sannan ya shiga laluben nambar Ishaq É—in da har yanzu bai dawo ba, bugu É—aya biyu kuwa ya É—aga.
"A ina ka ajiye muƙullin motarka?"
"Me za'ayi?" Ishaq É—in ya amsa daga cikin wayar.
"Motata ta samu matsala ne kuma ina da meeting anjima."
"Ka kira Jamilun?" (Makanikensu.)
"Ban kira shi ba, tunani nake sai anjima tukunna saboda gabaÉ—aya na manta da meeting É—in ne."
Dariya Ishaq É—in yayi daga ciki yace.
"Wallahi tayar motar nan a sace na tafi na barta, I don't know ma ya take take yanzu."
Ya girgiza kansa kafin yace.
"Baka da amfani."
Da haka ya kashe wayarsa, ya kira Malam Sani.
"Yallaɓai Barka da safiya."
"Barka dai Malam Sani, nace dan Allah akwai mota a cikin gida ne?"
"Ai kuwa Babu ranka ya daÉ—e, don su Baffa sun tafi gona a tasa shi da Baba Usman, ta Hajiya kuma a tsaye take tun wancan watan don haka na baro za'a kaita asibiti da ta Mami, school bus din kuma ka ganni da ita a Æ´ankaba."
Sai kawai ya gyaÉ—a kansa alamun ya fahimta kafin suyi sallama ya kashe wayar, Martha ya sake kira yace ta kira direban kamfanin nasu kawai ya kawo ta kawo masa takardun.
Da haka ya mayar da ball ɗin cikin booth ɗin motar sannan yayi hanyar cikin gidan, ya shiga cikin falon ya shiga cikin a lokaci guda da ƙamshin wani air freshener mai sanyi ya shiga hancinsa, yana tabbatar masa da cewar matar gidan ta tashi kenan, ya nufi hanyar dakinsa don yayi wanka ya shirya yayin da yanayin fuskarta a jiya da daddare ke haskawa a idonsa da kuma waɗannan siraran ƙafafun nata.
***
Ƙarar kwankwasa kofar gidan ta shiga kunnen Amina a lokacin da take kammala aikinta na karshe a kitchen, ta san ba Ma'aruf bane, don a yanzu ƙwaƙwalwarta ta haddace yanayin nasa bugun kofar duk da ba kullum yake manta mukullinsa ba.
Ta kashe gas ɗin da sauri sannan ta goge hannunta kafin ta fito, har yanzu wani iri take jin jikinta, mafarkin jiyan nan dana abinda ya faru bai gama barin tunaninta ba sam, don bayan ta koma ɗaki a jiyan bata iya komawa bacci ba, sallah tayi sannan ta zauna tunane-tunane har lokacin asuba, kuma sai bayan asubar sannan bacci ya ɗauke ta, baccin da baiyi nisa ba ƙarar wani abu ta tashe ta.
Kuma ba'a dade ba wata yunwa ta dame ta, don haka a gurguje ta karasa karatun Azkar ɗinta sannan tayi wanka kafin ta fito zuwa kitchen, inda anan ta hango Ma'aruf ta cikin sliding windows ɗin dake wajen sink yana ball, ta fahimci ƙarar data tashe ta kenan. Yana sanye da wata loose-fitted riga fara kal, da bakin wando irin na sports, (track pants) da kuma takalmin ball, rigar ta fito da ƙirar jikinsa sosai, sannan yadda yake juya ball din a kafafunsa cikin kwarewa ya tabbatar mata cewar da a cikin filin ball yake tabbas zai iya yin kokarin ture kowa ya ci.
Ta daɗe tsaye tana kallonsa cike da mamaki, don bata taɓa tunanin mutum so committed kamar shi zai samu irin wannan lokacin ba, ta fahimci a kullum ƙara sanin wasu halayensa dake bata mamaki take kuma har yanzu ba'a zo kan wani abu guda da tayi hasashensa game dashi a baya  ya zama gaskiya ba.
Komai zuwa yake saɓanin tunaninta, ita har yanzu bata ga wata alama ta ciwon nan nasa da ta riga ta gama tsorota dashi ba, shi yasa zuciyarta ke ta tantama ma akan idan shi ya rubuto mata wannan saƙon, har Fatima ta gayawa cewa in dai ba warkewa yayi ba, to ba koyaushe ciwon ke tashi ba. Shi yasa tare suka yarda da tsarinta na kyautata zamansu, da tunanin idan ya san bata da niyyar cutar dashi, ba lallai yayi mata wani abun ba duk lokacin da ciwon nasa ya tashi.
Sai dai ita bata tsara da yadda zuciyarta ke jin dadi tun lokacin da ya fara cin abincin nata ba, jiya duk da rikicewar mafarkin nan da take ciki sai da zuciyarta ta faɗa ganin kwanukan abincinta a gefensa... Tunanin hakan ya tuna mata da yadda ya riƙe hannunta a lokacin, har yanzu tana jin kamar shatin yatsun sa akan fatar ta, tana jin kamar akwai wani abu dake ƙonewa a jikinta saboda tasirin yadda yatsun nasa suka zagaye duka hannun nata gabaɗaya.
Da wannan tunanin ta kammala haɗa abincin breakfast ɗin lokacin da ta tsinci bugun ƙofar nan. Kayan jikinta riga da skirt ne na wata atamfa ash da tun ganinta da ita da farko tayi mata kyau wa ido, kuma sai akayi sa'a mai dinkin ya zabi wani ɗinki mai kyau da ya dace da ita don haka suka karbeta sosai, kuma yau bata saka mayafin data saba ba sai ta yiwa ɗankwalin V kawai ta yafa shi a haka.
Ta buɗe ƙofar lokacin da hoton wata budurwa ya shiga idonta, doguwa ce, fara, kamaninta na yare ne amma kuma kyakkyawa ce, ta bazo gashin data ɗora a saman kanta mai kyau sannan matsatstsiyar rigar data saka ma mai kyau ce, don ta fito da kowanne lungu da saƙo na jikinta yayin da hannunta ke rike da wata ƙatuwar jaka irin ta aiki.
"Good Morning my name is Martha, I'm..." ( Barka da safiya, sunana Martha, nice...)
"She's my sectary." (Sakatariyata ce.)
A lokaci guda muryar Ma'aruf ta faɗa daga bayanta, kuma ba tare da jiran komai ba taji hanayensa masu dumi dun sauka a bayanta, daidai wajen da zip din rigarta ya fara, sannan ƙamshin turarensa ya cika hancinta. Bata san lokacin da ta juyo da kanta ta kalle shi ba, idanunta na nuna mamakin da dukkan wani abu mai hankali a jikinta ke yi na yadda ya tsaya kusa da ita amma shi ba ita yake kallo ba, wadda ta kira kanta da Martha din yake kallo da wani dan guntun murmushi a leɓɓensa.
Kuma bata sake shiryawa ba sanda taji ya jawo ta baya kaÉ—an yana haÉ—a ta da jikinsa, kanta ya tsaya daidai kafaÉ—unsa.
"You're welcome Martha, meet my wife Amina Sulaiman."
Sai da numfashin Amina ya katse a ƙirjinta jin yadda ya ambaci cikakken sunanta amma hakan baiyi nisa ba saboda Martha da ta miƙo mata hannu tana jiran su gaisa, sai tayi saurin mika mata nata itama tana murmushin da bata san a yaya ya fito ba.
"You came with everything right?" (Kinzo da komai ko?)
Taji muryarsa daga saman kanta tana sake tambayar Martha É—in wadda ta É—aga kai.
"Yes sir, everything is intact, I just need to explain some things to you about Document A." (Eh yallaɓai, komai ya cika bayanin wasu abubuwan kawai zan yi maka.)
Har yanzu da murmushi a fuskarta ta amsa, kuma sai kawai yasa hannunsa ya sake matso da Amina gefensa, suka bawa Marthan hanyar shiga ciki, ta wuce su kuwa tana ƙoƙarin fito da takardu da kuma labtop daga jakar hannunta.
"Kin tashi lafiya?"
Muryarsa ta tambaye ta tun kafin ta dawo da hankalinta kansa, sai tayi baya da ƙafafunta da sauri wanda hakan yasa ya saki hannun nata, kuma maimakon ta amsa sai tace.
"Barka da safiya."
Ya shafo gashinsa ta baya.
"Barkanmu dai, hope kin dawo daidai?"
Ta san me yake nufi don haka ta É—aga kanta sau biyu idanunta akan yatsunta, ya cigaba da cewa.
"Wannan sakatariyata ce sunanta Martha zamu yi meeting anjima ne and I left my things a office shine tazo ta kawo min."
Bata san me yasa yake mata bayanin mutanen dake rayuwarsa ba, Farko da Faruk ya fara, sannan wani Ishaq da har yanzu bata gabshi ba bands yawan wayar da take jin suna yi, sai kawai ta É—aga kanta a hankali alamun ta fahimta.
"Zamu É—an yi briefing a ciki, ba zaki damu ba?"
Da sauri ta sake girgiza kanta, a wane dalilin zata damu, gidanta ne? ya gyada kansa shima sannan ya juya ya shiga ciki, hannayensa duka biyu sanye a cikin aljihunsa duka biyu, don rigar shaddar dake jikinsa bata kai gwiwa ba, kayan kamar ma sababbi ne, light brown, suna ta kyalli a cikin hasken safiyar.
Wajen da ya dora hannunsa a bayanta ya sake ɗauka da irin abinda take ji a hannunta, sai kawai ta shaƙi wani numfashi mai nauyi a ƙirjinta sannan ta rufe ƙofar falon a hankali.
***
"Me? Me kika ce Amina? Ya kawo wata arniya cikin gidan da sassafen nan?"
Muryar Fatima ta faɗa cikin wayar dake kare a kunnen Amina, a hankali ta rufe idanunta sannan ta kai kofin shayin dake hannunta baki ta kurɓa.
"Ba yadda kike tunanin bane Fatee, yace min sakatariyarsa ce, kuma zancen aiki ma suke tayi wai meeting suke dashi anjima."
"Duk da haka ni dai banga wannan ya dace ba, ko ba komai gidan aurenki ne ya kamata a mutunta ki a cikinsa ko ba komai."
Saura kaɗan murmushin da take yi ya suɓuce a cikin wayar saboda yadda Fatiman ke yawan fadar 'Gidan aurenta' ita kanta da take ciki bata ganin hakan kamar gaske tunda har yanzu babu wanda ya san abinda gobe zata haifar.
"Ni sai naji muryarki ma kamar akwai wata damuwar daban bayan wannan, me ya same ki?"
Fatiman ta sake tambaya, sai tayi ajiyar zuciya kawai, Fatima ta santa ciki da bai kwatankwacin yadda Amma ta santa, don sau da yawa ma abubuwan da zata iya ɓoyewa Amma da Fatiman zata yi shawara su haƙa su binne, ko Maryam da take ƴaruwarta ba komai nata ta sani kamar yadda Fatin ta sani ba, Don haka a yanzu ma dalilin kiran da tayi mata kenan, sai gashi ta gane tun kafin ta kai ga gaya mata.
"Wani mafarki nayi da ya tashi hankalina jiya, ban taba irinsa ba Fatee, wallahi na tsorata sosai don har na farka ina jin kamar gaske ne."
"Ya salam! Allah ya kyauta, kinyi addu'a dai ko?"
Tambayar ta dawo mata da muryarsa sanda ya tambaya jiya 'Kinyi addu'a?'
"Nayi, har asuba ma ina ta nafila, amma da na sake tunowa hankalina yake kara tashi, gashi na kasa fahimtar komai a cikinsa."
"Babu abinda yake nufi insha Allah, ki cigaba da addu'a kawai kina kokarin yin taka-tsan tsan da komai insha Allah ba abinda zai faru Amina. Zanje wajen Malam mai almajirai anjima insha Allah in saka ayi miki rubutu, wataƙila wani satin zamu zo da Maryam sai in taho miki dashi."
"Ba watakila ba, ku zo dan Allah Fatee..."
"Kin san Amma ce tace sai an kwana biyu tukunna." Ta katse ta, sai ta girgiza kanta kamar tana kallonta.
"Wallahi ko kullum zaku zo na gaya miki mutanen nan basu da matsala Fatee, yanzu kwana biyu ma kusan kullum ni kadai nake yini saboda duk sun koma makaranta, babu mai shigo min."
Fatima ta girgiza kanta itama.
"A abinda muka sani yanzun kenan Amina, gwara mu jira mu ga abinda lokaci zai haifar kafin komai ya daidaita, kar a sake ɓallo wani abu daban."
Ta haÉ—iye wani abu a makogwaronta kafin ta amsa.
"Toh shikenan. Ki gaishe min dasu Mamah da Ahmad idan yazo."
Sai Fatiman tayi dariya tace.
"Na gaya masa waccar gaisuwar taki ma sai cewa yayi wai kina matar auren yanzu kike cewa a gaishe shi? Wai in gaya miki kiyi azumi guda uku."
Suka yi dariya a tare kuma da haka suka yi sallama fuskar Amina É—auke da murmushin dake cike fal da kewar gida kamar kodayaushe. Ta ajiye wayar a gefenta tana kallon lokacin daya nuna akan É—an screen É—inta kafin hasken ya É—auke.
***
"Eh, yanzu zan fito... I will be there in 10 minutes insha Allah. "
Ma'aruf ya faÉ—a cikin wayar da yake yi a lokacin da ya fito daga É—akinsa.
"Idan kana yiwa Allah Faruq kar ka tsaya a wani wajen, Let's not make them wait." (Kar mu barsu su jira.)
Abinda aka faɗa a cikin wayar yasa shi kallon lokacin a agogon hannunsa kafin ya kashe wayar, a yanzu ya shirya cikin wasu kayan daban ba na safe ba, ƙarfe uku daidai, Martha ta daɗe da tafiya kuma shima bai daɗe da tashi daga kan system ɗinsa ba.
Don bayan tafiyar Marthan anan Amina ta same shi da kayan breakfast ɗinta, ta durƙusa har ƙasa ta ajiye a gabansa, ya tuna yadda skirt din kayanta ya baje a kan carpet ɗin lokacin da ta durƙusa, a lokacin yaji yana don ganin yadda ƴan siraran ƙafafun nan nata suka lanƙwashe da durkusawar, kuma bata ce komai ba ta shiga zuba masa kawai, idonta a kasa, dogwayen gashin idon na sama ya haɗe dana kasa kamar ta rufe su ne gabaɗaya amma kuma tana cigaba da abinda take yi.
Bai san me yasa duk abinda tayi yake jin kamar wannan ne karon farko da yake fuskantar rayuwar aure ba, shekarar sa uku tare da Ruƙayya a matsayin matarsa, amma har yanzu ba'a zo wajen da yaga wani abu nata yayi kamanceceniya da irin rayuwar da yayi da Ruƙayya ba, gani yake kamar komai sabo yake faruwa.
Yaso sunyi magana a lokacin nan, amma yawan aikin dake gabansa bai barshi ba, ya raina meeting din daga farko sai a yanzu da yaga yawan abinda za'a tattauna ya san cewa da gaske mutanen suke kuma idan har suka yi nasara ba karamin alkhairi zasu samu tare dasu ba, saboda haka dole ya ture komai gefe ya maida hankalinsa kan nazarin bayanan nasu, kuma watakila itama ta lura da hakan don tunda ta shiga É—aki bayan yaci abincin tazo ta kwashe kayan bata sake fitowa ba.
Jamilu yazo tun dazu yayi tabe-tabensa a motar komai ya dawo dai, dama ya sani gyaran ba lallai ya zama mai yawa ba tunda motar bata cika bashi matsala ba tunda ya siye ta, don haka bayan ya gama saka links din ya nufi hanyar kofa rike da wayoyinsa kawai, ya riga ya kai duk abinda yake bukatar tafiya dashi motar tun É—azu, din ya kusan haddace komai, zuciyarsa dama idanunsa kawai biyo dukkan abinda ya san zaiyi magana akai suke.
Ya ɗora hannunsa akan ƙofar falon har ya buɗe lokacin da yaji muryarta.
"A dawo lafiya, Allah ya bada sa'a."
Idanunsa suka juyo da sauri zuwa inda take tsaye, daga hanyar koridon nan ne alamun daga daki ta fito, hannunta na hagu na riƙe da wani baƙin bokiti data ciko jikakkun kaya dasu, yabi hannun nata da kallo da kuma gaban rigarta daya jiƙe yana tabbatar masa wanki tayi, ɗankwalin da take yafe dashi tun safe ta ɗaura shi a yanzu, yayi baya ma kamar zai zame gashinta na fitowa ta gaba, mai laushi ne da alama don duk ya tashi sama.
Bai san lokacin da wani guntun murmushi ya suɓuce a fuskarsa ba kafin ya ɗaga mata kai.
"Ameen ya Allah, nagode sosai."
Kuma ga mamakinsa sai itama tayi nata guntun murmushin sannan muryarta ta ƙara fitowa.
"Insha Allah meeting É—in zai tafi daidai."
Tana faÉ—in haka ta shige hanyar Kitchen É—in dake gefenta bokitin na bin bayanta.
***
Dab da magariba ne lokacin, Aminu ya kammala komai na aikinsa na ranar a garejinsu, kuma har yayi sallama da kowa ya fito bakin titi lokacin da wayarsa tayi kara, yana tsaye da gefen titin ya dauko ta ya duba, Baba ne, don haka ya dauka da sauri ya kara a kunnensa yana gaishe shi.
"Lafiya kalau Aminu, kun tashi ne?"
"Eh Baba, yanzu ma na fito zan taho gida."
"To ka biyo ta nan, akwai kayan da zaka dauka sai mu tafi tare."
"Insha Allah Baba gani nan."
Da haka ya kashe wayar, ya sauke ta ɗaga kunnensa daidai lokacin da mai mashin ɗin ya taho da wani irin saurin da ba Aminun kaɗai ba hatta mutanen dake baya dashi basu ga wucewarsa ba sai dai ƙarar injin mashin ɗin da kuma sanda yabi ta kan Aminun dake tsaye a bakin titin ya take shi tun daga kan ƙafafuwan sa.
Salatin mutane har da ihun wasu ya gauraye iska a lokacin da mai mashin ɗin ya murde kan mashin ɗin ya miƙe titi ba tare da ta tsaya ba, kansa na dauke da hular kwano baka don haka babu wanda ya iya ganin fuskar sa.
Wasu daga cikin mutanen suka bishi da jifa amma babu wanda ya same shi, gudu kawai yake yi har lokacin da ya fita daga unguwar baki ɗaya, ta lunguna ya dinga gujewa danja ba tare da ya tsaya a koina ba har ya zuwa unguwar Sardauna Cresent ƙofar gate ɗin gidan da ya fito, inda tun kafin ya karasa mai gadin dake zaune a waje yana jira yayi saurin buɗe masa gate ɗin ya shige.
A gaban wata ƙatuwar bishiya dake harabar gidan ya tsayar da mashin ɗin sannan ta cire hular kwanon dake kansa, daidai lokacin da wayarsa ta shiga fitar da karar vibration daga aljihunsa. Ya ɗago ta ya danna wajen amsawar ba tare da ya damu ya duba sunan mai kiran ba.
"Awa ta biyu a waje kafin yaron ya fito." Ya faɗa yana ƙoƙarin balle maɓallin rigarsa na gaba.
Daga ɗaya ɓangaren wayar, Hajiya Kilishi tayi murmushinta mai armashi kafin tace.
"Kace min an gama kawai Awwalu."
"An gama Hajiya, kema kin san komai daidai yake tafiya."
Ta gyaɗa kanta a hankali, tabbas haka ne, komai  daidai yake tafiya, me yasa ma zata damu da tambaya? Awwalu ya taɓa kasawa umarninta ne?ko kuwa ta manta sanda yayi babban aikin da yafi wannan a wajen hatsari ne ma? Aikin da shine ginshiƙi samun ƴancin da take kirgawa dashi a kowacce nasarar da take samu.
Bakinta ya sake tafiya da wani murmushin, abinda ya faru yanzu tsaraba ce ga Amina, don ba'a banza zata buɗe mata fuskarta ba, ba'a banza zata san wace ce ainihin Kilishi ba, dole ne ta tunkare ta da kakkarfar hujjar da kokwanton ikonta ba zai taɓa samun waje a zuciyarta ba.... Aminu shine farko a yanzu, kuma idan komai ya tafi daidai zai zama na karshe, amma da an samu wani akasi ƙofar ta buɗe kenan, duk wanda ya jiɓanci Amina ya shigo cikin lissafinta.
Zata É—aure Amina ne da jijiyoyin jikinta, bata isa ta tsallakewa dukkan sharrinta ba a yanzu, ta riga ta shigo cikin jerin mutanen da take juyawa da yatsan hannunta.
"Ya batun Ma'aruf É—in Hajiya? Na gaya miki yayi nisa a binciken da yake yi, idan har ya riga mu nemo inda Mr. Okafor yake wallahi abubuwa zasu canja daga kalar da muka san su, ya kamata ki tsayar dashi har sai mun riga shi nemo mutumin nan mun tura shi lahira tukunna."
Muryar Awwalun ta katse ta daga tunaninta, kuma a lokaci guda sai murmushin dake kan fuskarta ya ɗauke, yanayin fuskarta ya koma wani iri da babu abinda zaka tsinta a ciki, ta haɗiye wani abu a cikin maƙogwaronta tana kallon tarin magungunan Ma'aruf ɗin da ta baje daga kan gadonta, a hankali ta girgiza kanta sannan tace.
"Kar ka damu Awwalu, ina sane dashi so nake ya kammala da mutanen RTL É—in nan tukunna, idan sun gama daidaitawa kuma kuÉ—aÉ—en sun shigo zamu jefi tsuntsu biyu da dutse É—aya ne, kafin ya dawo hayyacinsa munyi gaba da kuÉ—in kuma munyi gaba da shi Mr. Okafor É—in... Kamar koyaushe sai bayan ya tashi zai fara lalube cikin duhu!"
***
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.