Farar Wuta Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Farar Wuta Book 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 2 of 9
BABI NA SHIDA.
~~~~~~
Wani mai adaidaita sahu ya shigo layin har zuwa ƙofar wani gida mai baranda, kuma da tsayuwarsa Aminu ya fito daga ciki yana dariya alamun sun daɗe suna hira da saurayin dake jan adaidaita sahun wanda shima ya fito bayan ya kashe mashin ɗin, kuma a tare suka kamo wani buhun shinkafa ƙato guda suka shiga kiciniyar shiga dashi cikin gidan, inda tin daga soro ƴar hayaniyar mutanen ciki zata shaida maka cewar an samu baki fiye da mutanen gidan.
A tsakar gidan Amma ce tare da Æ´anuwanta su uku da suke uwa É—aya uba É—aya suke ta kiciniyar hada wasu kayayyaki a cikin kwalaye.
Yayarta mai suna Zahra'u da suke kira da Tanti wadda ke zaune a goron dutse ta kalli Amman da ta fito daga kitchen riƙe da ƙaton tire ɗin data yanko kankana tace.
"Ni kuwa Halima wai yarinyar nan kaya kala nawa ta É—inka a cikin lefen?"
Amma ta ajiye farantin hannunta a tsakiyarsu kafin tace.
"Ina ga kusan rabi ne, ai tun zuwan su Momi Æ´ar gidan Kawu Mallam wancan satin suka É—iba suka kai mata wajen mai É—inkinsu, har da na fitar bikin."
Tanti ta gyada kanta tana faÉ—in.
"Ko da naji, don na lura ita bata da wannan niyyar, a baki kawai Amina ta karɓi zancen auren nan amma banda a al'amuranta wallahi."
"Kinga ko jiya..." Ɗaya ƙanwar Amman mai suna Ma'u ta shigo zancen.
"... Abinda nake gaya mata kenan, nace tunda dai har ta amsa, ya kamata ta saki ranta tayi komai kamar kowacce amarya a haka ne zancen zai cigaba da rufuwa, komai ya tafi daidai."
ÆŠayar da take Æ´ar autarsu Safiya tace.
"Ai ce miki zata yi hankalinta a kwance yake, ba irin faɗan da banyi mata ba wancan satin amma  ƙiri-ƙiri ce min tayi ita ba abinda ke damunta."
"Allah ya kyauta, yaya kuka sake yi da ita Hajiya Kilishin? Yaushe za'a fara kai kayan ne? Ya kamata ma aje a ga wajen."
Aunty Zahra'u ta tambaya tana rufe ƙaton kwalin da ta gama tara ƴan ƙananun kayan kitchen a ciki.
Kuma tambayar ta dawowa da Amma tarin abubuwan da suka faru a cikin wucewar sati uku, yadda ka ranar da taje gidan Tantin a goron dutse, ta hau ta da fada bayan ta shaida mata komai, tace Uba yana da ikon zaɓawa ƴarsa mijin aure don haka ita bata ga aibu a cikin zancen ba, tunda a yadda ta san Baba ta ba zai aurawa ƴarsa mara hankali ba kamar yadda Amman ta kira lamarin.
Don haka babu yadda ta iya dole ta ja bakinta tayi shiru, kuma kamar wasa al'amarin auren ya cigaba gudana bi da bi, a yanzu saura sati guda bikin, an karɓi kuɗin aure hade da lefen da bai wani girgiza su ba kamar yadda take zato a gidan Kawu mallam, sannan har sau biyu Hajiya Kilishi ta kira ta a waya tana shaida mata yadda wasu daga cikin al'amarin bikin zasu kasance a wajensu da kuma cewar gidan da za'a kai Aminan a cikin gidan da suke ne.
Sannan a jiya ta aiko da ɗan aike ya kawo tulin wasu katinan ɗan aure da ba su ko san yadda zasu yi dasu ba, don haka a dole ta karɓi al'amarin itama suka fara shiri sosai, Baba yana ta fafutukar kayan katako da ƴan kudin hannunsa da kuma wanda yayyensa suka haɗa masa, yayin da ita da ƴanuwanta mata ke iya nasu ƙoƙarin na kayan kitchen da kuma sauran na amfanin gida, wanda su Aunty Safiyan ke ta sintirin zuwa kasuwa tun wancan satin.
Sai da al'amarin ya kai duk da irin halin da zuciyoyinsu ke ciki, shirye-shirye a yanzu sun kama kamar dama sunyi tanadin lokacin. Don haka kafin ta bawa Tantin amsa su Aminu suka yi sallama a lokacin suna shigowa da buhun shinkafar nan.
"Yawwa master, nagode sosai..."
Cewar Aminun bayan sun jingine buhun shi da wani saurayi daya kamo masa, saurayin yayi waje yana fadin babu komai yayin d shi kuma ya juyo ya kalli su Amma dake kallonsa suna jiran ba'asin abinda zai ce.
"Haba Amma ke ma fa kin san bana sata, Baba ne ya kira ni yanzu naje na karɓo a wajensa."
Ya faÉ—a cikin raha yana kallon Amman. Aunty Ma'u tace.
"Na ga ranar da zaka yi al'amarin ka kai tsaye Aminu, in ma satar kake ai kowa ya san ba zaka kawo gida ba."
"Ameen wallahi..." Cewar Aunty Safiya.
"Amma da ƙyar ne canjawar Aminu, ai hali ZANEN DUTSE ne."
Ya ƙaraso ciki da dariyarsa yana shirin buɗe babin shafin tsokanar Aunty Safiyan da yafi rainawa, amma tun kafin ya zauna Amma ta katse shi.
"Zaka koma ne?" Ta tambaya.
"Eh yace in É—ebi kati in kai masa."
Kai tsaye ya bada amsar da a lokaci guda ta shiga kunnen Amina wadda ta fito daga ɗakinsu a lokacin riƙe da tsintsiyar laushin da abin kwashe sharar data ɗebi abinci fal a ciki kasancewar Aunty Safiya da Aunty Ma'un duk sun zo da ƙananun ƴaƴansu, suna ta dabdala a ɗakin.
Riga ce Æ´ar kanti a jikinta kalar ruwan toka da wani tsohon zanin atamfa da babu mitar da Amma bata yi ba amma ta kasa rabuwa dashi saboda daÉ—in É—aurawarsa, sai ta bayar da sabuwar atamfa ma amma shi yana nan, Gashinta mai laushi yana ta fitowa ta saman É—ankwalinta dake zamewa.
Tayi wajen sharar ta zubar lokacin da su Amma suka cigaba da zancensu, Aminu kuma ya dage wai sai sun yi cinikin sabuwar motar Aunty Safiyan da mijinta ya siya mata kwanakin baya kasancewar sa mai hali.
Sai ta juya ta koma É—akin a lokacin da wata Æ´ar Aunty Ma'u mai suna Yusra ke janyo kaya daga cikin drawer ta.
"Me kike nema anan Yusrah?"
Yarinyar ta juyo ta kalle ta.
"Hijabi Aunty Amina, Sallah zanyi."
"To ya zaki yi da hijabina, duka sun fiki tsawo... Kije É—akin Amma ki É—auko na Hafsa, me yasa ma baki bi su Hafsa aiken ba?"
Ta faɗa sanin cewar Hafsan da ƴar gidan Tanti da kuma ɗaya yayar Yusran basu daɗe da fita siyan kayan miya ba. Adam ma tunda ya samu sa'ansa ɗan gidan Tanti mai suna Mubarak suka fita filin ball shikenan sai an gansu kuma.
Ta tsugunna tana ƙoƙarin kwashe kayanta bayan fitar Yusran, yayin da hayaniyar ƴan ƙananan yaran da suka ɗane katifar Hafsa suna doki ke shiga kunnenta, tunda satin nan ya kama komai ƙara gaya mata yake yi cewar sauran wasu ƙaiyadaddun kwanaki rayuwarta ta fara daga gaɓar da zata ƙare.
Musamman wannan haɗuwar ta ƴanuwan Amman a gidansu, wani abu ne daban da basu saba ba don Tanti itace babba a cikin su Amman, don haka mafi yawanci a gidanta ake yawan haɗuwa, ko da Sallah kowa can yake tafiya su haɗu har su, shi yasa ganin yadda gidan nasu ya zama wajen haɗuwa yanzu yana ƙara tabbatar mata cewa da gaske komai ke shirin faruwa, gashi Baba ma har ya fara aiko da tanadin abincin biki duk da Amma ta daɗe da kafa layin cewa ba wani taro za'ayi mai yawa ba, ko ƴanuwansu a can Niger tace duk a waya za'a shaida musu kawai, sai dai idan maza zasu zo ɗaurin aure don ya zama shaida a wajensu.
Wani abu ya wuce ta maƙogwaronta lokacin da idonta ya kai kan tulin katinan ɗaurin auren nan, sunayen mutane takwas ne a jiki banda sauran bayanai, amma idan ta kalle shi ba abinda idonta ke gani sai nata sunan dake ƙasan rubutun Ma'aruf Mansur Bakori, sunan da ko sau nawa zata maimaita shi sai ta ji bugawar zuciyarta a cikin allon ƙirjinta.
Ta rufe idanunta ta buÉ—e tana jin yadda har yanzu zuciyarta ta kasa yarda cewa tana shirin buÉ—e shafin kaddarata ne da hannayenta. Ba lallai ne ya kashe ta kamar yadda ya rubuto a takardar nan ba ta sani, ya rubuta ne kawai don ya tsoratar da ita, amma hakan ba zai hana ta É—anÉ—ani gwargwadon azabar da ya tsara mata ba, tunda ta tankwabe gargaÉ—in da yayi mata.
Ta tuno shekaranjiya lokacin da Tanti ke tambayar Amma 'yaron kuwa yazo?' sai da ta ƙware da yawunta tsabar yadda tsoron hakan ya shige ta, ita har yanzu bata hango cewar in dai wannan Ma'aruf ɗin da ta sani ne zata ganshi a kusa da ita ma balle ƙaddara ta haɗa su. Gani take yi kamar za'ayi auren ne kawai a kaita wajen Hajiya Kilishin da sunanta ne kaɗai ke yawo a gidansu game da auren. Shi yasa bata fatan kowa ma ya ambace shi, tafi son ayi dukkan abinda za'ayi a kaita ɗin kawai, acan zata tsara matakan da watakila zasu iya siyar mata lokaci kafin dukkan abinda zai faru ya faru har Amma tazo tace.
'Dama na gaya miki Amina'
Fatima ma tace.
'Me yasa kika yi tunanin zaki iya Amina?'
Maryam zata dinga da binta da kallo kawai, Aminu kuma zai iya cewa.
'Ko ba komai kin ƙoƙorta Amina.'
Baba ne kadai zai saka mata albarka ta sani, yayi mata addu'o'in da wataƙila zasu iya gyara rayuwarta a gaba, don ya san tayi komai ne don shi, don tallafar mutuncinsa.
Ta kai ƙarshen tunaninta lokacin da sallamar su Ummi da Momi ta cika tsakar gidansu, taji su suna gaisawa dasu Amma har da muryoyin wasu daban don haka ta rufe wardrobe ɗin ta juyo tana korar yaran zuwa waje. A lokacin Ummi ta ɗage labulen ɗakin ta shigo.
"To amaryar ƙulle, kina nan mu munje mun samawa kanmu mafita.."
Suka shigo suna ajiye ledojin hannayensu yayin da Momy ke cewa.
"Amina ruwa dan Allah, wallahi mun É—ebo rana."
Da murmushi ta fita zuwa kitchen ta É—auko jug É—insu na roba haÉ—e da kofinansa ta É—ebo musu ruwa sannan ta dawo.
"Wai daga ina kuke?" Muryarta a hankali ta tambaya tana ajiye musu ruwan.
Ummi ta miƙo mata ledar kusa da ita tace.
"BuÉ—a ki ga."
Ta karɓa kuwa ta shiga zaro wasu atamfofi masu kyau kalar ruwan hoda, (pink). Wani abu ya zarce ta maƙogwaronta, tun lokacin da aka kawo kayan lefen nan su Ummi suka san zancen auren, tunda suma sun san Hajiya Kilishin a matsayin ƴar uwarsu kawai dai tafi shiri da Baba ne duk a cikin si Kawu Mallam ɗin, don haka sai rawar ƙafarsu ta ƙaru kamar me sanin cewar bikin irin wanda suke so ne.
"Kowacce dubu ɗaya kenan da ɗari biyar, jikinsu mai kyau ne baza ki taɓa cewa roba bace."
"Wai na meye?"
Momi tace.
"Har tambaya kike? To anko ne muka fito dashi tunda ke baki da niyya, kin san mu Æ´an ayi sha'ani ne babu ta yadda za'ayi muyi biki lami ko amaryar bata so."
Amina bata ce komai ba, Momi ta sake cewa.
"Ina Fatima? Ga guda ɗaya nan ta Maryam mun siyo sai ta nunawa ƙawayenku ita, wanda yake da hali yayi tunda dai saura ƴan kwanaki, waɗannan kuma ƙawayen mu ne su ma gashi sun siyo tasu."
Sai a lokacin ta ɗago ta kalli ƙawayen nasu da murmushi a fuskarta tace.
"Allah ya saka da alkhairi, nagode." Ummi ta kalle ta tace.
"Su da kuÉ—insu kike musu godiya? Zo muje ni kiga wani abu."
Da haka ta ja ta suka fita daga É—akin, a tsakar gida su Amma duk sun shige can É—akinta suna cigaba da haÉ—a kayan dake ciki, sai Aminu kawai dake ta É—aga yaran nan sama suna dariya.
A ƙofar ɗakin Baffa suka tsaya Ummin tace.
"Amina duk shiru-shirunki na san ba haka halaiyarki take ba, akwai wani abu game da auren nan da kike ɓoye mana, kin sani ni da Momi ƴanuwanki ne kuma sa'aninki da zamu iya jin irin ciwonki, idan akwai matsala ki gaya mana, wallahi in zamu iya zamu taimake ki."
Amina ta haɗiye wani abu, duk kauɗin su Ummi ta sani cewa suna da zuciya mai kyau a can ƙasa, kuma ta sani cewa suna sonta fiye da yawanci daga cikin ƴan uwansu don haka zasu iya taimaka matan da komai, sai dai bata yi tunanin cewa Ummin zata iya ganin damuwarta sama da ɗokin bikin da suke yi ba. Amma duk da haka ta san babu amfani sanin nasu kamar yadda Baba ya shar'anta tun farko, musamman su biyun nan da ta san idan suka ji kamar ta saka lasifika ne a tsakar gidan Kawu mallam ta faɗawa kowa. Don haka sai kawai ta girgiza kanta.
"Wallahi ba wani abu bane Ummi, kin san ban taɓa kawowa kaina aure a yanzu ba ne kawai, kuma sai komai yazo a lokaci guda shi yasa kawai nake jin wani iri."
Kamar Ummin bata yarda ba, amma bayan ta kalle ta na wasu sakanni sai ta gyaÉ—a kanta tace.
"To ai shikenan, idan wannan ne da an kai ki sati É—aya na san zai tafi, don duk da haÉ—a ku akayi ke bata wasa bace Amina, kuma duk yadda yake jin kansa na san zaki iya dashi....Wai yaushe zamu ganshi ne ma? Ya bamu kuÉ—in walima..."
Wai me yasa kowa yake son ganin sa? Me yasa kowa yake son jawo shi da baki? Basu san a lisafin tashin hankalinta wannan shi ne a sama ba? Jin bata ce komai ba yasa ta sake cewa.
"Ko da yake da alama kema ba wani ganinsa kike ba, masu kudin nan sai a hankali, amma dai na san zaku haɗu kafin wani satin sai ki karɓo a madadinmu, idan ba haka ba kuma ni zan karɓi lambar wayarsa na tambaya da kaina."
Jin haka yasa tayi saurin girgiza kanta tace.
"Kar ki damu baza'a kai hakan ba ma."
Ina zata kai kanta idan har Ummi ta kira shi da wannan zancen? Ai ko a mummunan mafarki ta san wannan rashin sa'a ce babba a rayuwarta. Ummin ta kalle ta sosai.
"Amina auren masu kuÉ—in nan fa dama ce da kuma rabo, ki saki jikinki ki ci kuÉ—in gayen nan son ranki, don baki san irinsa ba, ba lallai ne in kin shiga ma ya buÉ—a miki ba."
A yanzu ta dawo Ummin data santa, ƙanwar ƴanmatan Kawu mallam me cike da buri, don haka sai kawai ta faɗaɗa murmushin ta tana fadin.
"Toh shikenan."
Da haka suka koma wajen su Momi, inda suka dasa hira su da ƙawayensu, hirar da taso tafiya da yawan tunanin zuciyarta, don hira suke har da dariyar da har ƙasa suke kaiwa wajen ƙyaƙyata ta, daga baya ta zubo musu abinci a ƙaton faranti suka zagaye shi su bakwai suka cinye tas, a lokacin su Tanti duk sun tafi kuma har Amma ta yaba da atamfar da suka siyo bayan an nuna mata.
Maryam ma ta dawo ita da ƙawayenta da suka tafi gidan wata mata tambayar Beads ɗin da zasu yi amfani dasu a bikin, kuma ganin atamfar murnarta ta ƙaru don tace tayi kalar beads ɗin da ta bayar ayi mata na atamfar da Baba yayi musu na fitar bikin. Kallonta kawai Amina take don ta lura ita mantawa ma take da zancen cewar ba auren da suke so za'ayi ba, don gabadaya ma ta manta da zancen saukarsu da suke ta shiri, yanzu bikin ne a gabanta don ko jiya tana jinta tana takurawa Aminu cewa ya ƙara mata kuɗi zata siyo kayan da zata yiwa ƙawayenta 'takeaway'.
"Tun safe Fatee, tun É—azu nake ta kallon hanya, baku dawo da wuri bane?"
Ta faÉ—a lokacin da Fatima ta shigo gidan da daddare, don tun safe tace mata zasu je bikin Æ´aruwarsu.
Sai dai maimakon Fatiman tayi dariya kamar yadda ta zata sai kawai tace.
"Go slow ne wallahi ya rike mu a wajen Gandu."
Da haka ta juya ta gaishe da Amma dake yankewa Hafsa farce anan tsakar gidan sannan a lokaci guda ta jawo hannun Aminan dake jikin durum tana kokarin ɗiɓan ruwa a buta suka yi soro.
"Amina dama wanda zaki aura da kika ce min É—anuwanku ne shine wani Ma'aruf Bakori wanda gidansu yake a sharada?"
Sai da gaban Amina ya faÉ—i duk da bata san me zata ce ba, ta gyada kai tana kallonta da fararen idanunta da ake gani tar a cikin rashin hasken soron.
"Eh, baki gani a jikin katin? Me ya faru?"
"Bikin da muka je a sharada ne Amina, kuma a layin gidansu, ƙanwar amaryar ce take gaya min cewa ta san duka ƴan gidan kuma da gaske bashi da hankali."
Sai ta girgiza kanta.
"Su Baba fa sun gama duk bincikensu Fatee, har ganin sa ma sunyi, sun ce ciwon ba mai yawa bane, sun ce har aiki yake yi a kamfanin babansa, ba wai bashi da hankali bane gabaÉ—aya."
Fatima ta girgiza kanta.
"Amina baki san me tace min bane..."
Da sauri ta sunkuyar da kanta sannan ta shiga girgiza shi itama tana faÉ—in.
"Mutane sun iya yaÉ—a irin wannan jita-jitar Fatee, ba yau aka fara ba, musamman a sha'anin aure..."
"Yana da wa sunansa Jamal?"
Fatiman ta katse ta, ba shiri ta ɗago ta kalle ta yayin da muryar Baba ta kwanakin baya ke haskawa a cikin kanta, lokacin da Amma ke tambayarsa idan Ma'aruf ƙani ne a wajen wanda suka je bikinsa a shekarun baya.
'A'a, shine dai wanda kuka je auren nasa, ai ya rabu da matar ne daga baya. Wa É—aya yake dashi sunansa Jamal kuma ya rasu shekaru goma da suka wuce...'
"Ya rasu shekaru goma da suka wuce ko?" Muryar Fatiman ta tambaya tana karashewa da tunaninta.
"Me ta faɗa miki?" Bata san lokacin da bakinta yayi tambayar ba yayin da zuciyarta da abinda take tunanin ƙasusuwanta ne suka shiga rawa ba tare da kwakwaran dalili ba.
"Shi ya kashe wan nasa Amina! Shi ya kashe Jamal É—in shekaru goma da suka wuce!"
****
"Kar ki ɓata min rai Saratu, don me Allah ya halicce ki a mace? Me zaki yi da ƙwaƙwalwar da ake cewa ko shaiɗan na tsoron kaidin da zaki iya fitarwa ta cikinta?"
Muryar Hajiya Kilishi ta faɗa cikin shirun ɗakin yayin da wayarta ke kare a kunne. Ƙawarta da ta kira Saratun tayi ajiyar zuciya a cikin wayar kafin tace.
"Baza ki gane bane Kilishi, ba zaki gane yadda nake gaya miki cewa matar nan ta addabe ni ba, shi yasa naje wajen malamin nan, amma gashi yanzun ma kuÉ—in da na zuba na neman tafiya a banza."
Wani murmushi ya suɓuce a fuskar Hajiya Kilishin yayin da fuskarta take fayau! Sai dai a cikin murmushin akwai wani ɓari na sirrin mafi yawan nasarorinta.
"Tsafi gaskiya ne Saratu, amma gaskiyar da bata ɗorewa, kuma na sha gaya miki babu amfanin mallakar abinda ba zai ɗore ba, har wani ƙato a gefe ya isa ya magance miki matsalar da ke kike cikinta?
Sau nawa zan biya miki karatun nan ne? Shekarata talatin a gidan nan kin sani amma babu rana ɗaya da na taba takaws wajen wani malami da sunan taimako. Da yatsa ɗaya nake juya kowa a gidan nan yadda nake so kuma kin san ko ƴanuwana da muke ciki ɗaya su ma basu san wata fuskata bayan wadda Iyalan gidan nan suka sani ba. Shi yasa nake son ki gaya min meye amfanin buɗe miki cikina da nake yi ke da Salamatu? Ba don mu taru akan bigire guda bane? To don me a yanzu zuciya zata ja ki ki kauce?"
Tambaya ce, amma Hajiya Saratun bata amsa ba, don ta san halin Kilishin sarai, ranta ne ya ɓaci amma har a cikin ɓacin nata halayyar ta kan yi rinjaye a zuciyarta. Don haka tana jinta tayi ajiyar zuciya a cikin shirun sannan tace.
"Yanzu a ina kuka tsaya?"
"Yace ita zai mayar can Egypt É—in Kilishi, ni uwar garke in zauna in kular masa da Æ´aÆ´a."
Ta furta hakan tana furzar da wani irin huci da Hajiya Kilishin zata rantse tana jin zafinsa tun daga nan.
"Bi shi a hakan, kar ki sake ki nuna ranki ya ɓaci, kiyi kwalliya ki tausasa muryarki, ki gaya masa zaɓin da yayi daidai ne, ya duba ɗawainiyar yaranki ya taimake ki.
Sannan ki faɗaɗa murmushin ki a gabanta itama, ki gaya mata ko da ke ya zaɓa ba zaki bishi ba dama. Bayan haka kiyi mata ɗawainiya a lokacin da zai gani, misali, samu yaji da irin su busashshen tattasai kice tunanin amfaninsu kika yi musu, don kwana biyu ne abincin can zai gundure su. Idan kin aikata hakan, ki kira ni sai mu ɗora."
"Kina ganin zan iya Kilishi? Ba kowa Allah ya halittawa irin zuciyarki ba fa?" Muryar Saratun ta tambaya ɗauke da rauni da kuma wani irin tuƙuƙin dake cin ranta.
Sai ta sake wani guntun murmushin tana miƙewa tsaye kafin tace.
"Zuciyar da Allah ya halitta min nazo duniyar nan daban take da wadda nake da ita yanzu Saratu, ni da kaina na sami wannan zuciyar don haka kema ki tashi ki samarwa kanki abinda zai É—ore. Ki kira ni idan kin gama abinda na gada miki."
Da haka ta katse wayar tana mai taya kawar tata jin É—acin dake faruwa a rayuwarta, da ace tana da ikon juya zuciyar Saratu yadda taga dama, tayi rantsuwa a ciki wata daya kacal zata gyara mata komai, ta samar mata fiye da Æ´ancin da take dashi a wajen mijin nata tun kafin sake aurensa.
Amma zuciya ce kowa da irin tasa duk yadda ka kai ga iyawa, wani a baki kawai zaka bashi labarin dukkan nasararka amma tasa zuciyarsa ba zata taba iya ɗauka ba. Ƙawayenta biyu kenan a duniya Saratu da Salamatu, kuma bayan abotar tasu, tana zana su ne a cikin wasu mutane da suka taka muhimmiyar rawa a rayuwarta, suka yi mata amfanin da zata rantse ko uwar data kawo ta duniya bata yi mata ba a wajenta, don haka su biyun ne kawai duk duniya kawai take iya buɗewa cikinta su ga ainihin kalolin da take ɗauke dashi bayan farar fatar ta.
Matsalar guda ɗaya ce a wajen kowannensu, zuciyar Saratu bata iya jajircewa abubuwa har tayi yaƙi da iyawarta kamar yadda ita kanta ta furta a yanzu, Salamatu kuma sun sha banban da abinda kowannensu ke wa kallon nasara, don ita yanzu ko aure bata dashi, tafi ganewa yawon kasuwanci ga manyan mutanen da zasu dinga bata kuɗin da suka fi ƙarfin kayan nata.
Ta ja tsaki a hankali tana nufar ƙofar wardrobe ɗin ta, yau ita ke da turakar Baffa, ta gama shiryawa tuntuni wayar Saratun ce ma ta tsaida ita, a cikin wardrobe din ta dauko wata baƙar ledar magani da kuma muƙullin ɓangaren sannan ta nufi ƙofar ɗakin ta buɗe, ta buɗe ta sanda hayaniya ta cika kunnenta, hayaniyar da a yanzu kullum cikinta suke saboda ƙaratowar bikin.
Mutane ne kawai ke zuwa musu Allah sanya alkhairi tun yanzu, musamman daga ɓangaren ƴanuwan su Baffan na can ƙauye, masu kwana ma babu adadinsu don wasu tun wancan satin suka taho ma da zugarsu wai sun zo taya aiki, aikin da kullum sai anyi musu bayanin babu shi.
Don daga harkar jere har harkar abincin da za'aci lokacin bikin da duk wata hidima, kuɗi suka biya a dunƙule wa mutane daban-daban da zasu ɗauki nauyin hakan.
Kamfanika biyu na interior decoration suka biya don su yi jeran gidajen amaren, kawai ƴanuwanta dana Hajiya Maimuna ne ke zuwa su sa ido akan aikin don a hada har da tunanin mata komai ya tafi daidai, don haka su ɗin da suka zo, ba abinda suke ma illa ƙara aikin, don in banda ci su da ƴaƴansu ba abinda suke yini suna yi, dadinta ɗaya kawai basu barwa ma'aikatan gidan komai ba dasu ake girkin da duk wani aikin da ya taso, shi yasa ba wanda ya kai Inna Danejo murna a gidan yanzu ganin duk inda ta juya kawai ƴanuwanta take gani.
Surayya ta fara gani a falon tana danne-danne a wayarta kafin dandazon matan da ke ta fitar da kaya daga kitchen suna yin waje.
Ta wuce Surayyan da bata ko dago ba zuwa tsakiyar falon inda suka fara ganinta.
"Hajiya sannu da fitowa."
Wajen mutum biyar dake rike da wasu manyan fanteku tun na aurenta suka fada.
"Yawwa, waÉ—annan kayan fa? Ina za'a kai su?"
"Sameera ce tace a fita dasu waje Hajiya, na aikin cincin É—in da za'a fara ne."
"Cincin kuma? Ina ita Samiran take?"
Tana tambayar kuwa ta fito ita da wata sa'arta mai suna Khadija da take ƴar ƙanwar Hajiya Kilishin, suka fito suna jan ragowar wani buhun sukari da ya kusan kai kwata.
"Cincin É—in me ake yi shirin yi a gidan nan Samirah?"
Ta tambaya tana katse dariyar da suke yi ta kasa É—aukar buhun.
"Mama yara ne ke jin yunwa kafin a sauke abinci musamman da safe, shine nace bari ayi cincin sai ya dinga rage musu hanya."
Girgiza kanta kawai tayi tana kallonta, kowa da irin ƙaddararsa a rayuwa, ita tata ta abinci ce, don duk da science take yi a makaranta, amma course ɗin da take son yi a University shima ɓangaren girki ne, (Nutrition and dietetics.)
"Allah ya baku sa'a, kafin ku fara ki kawowa Baffa abincinsa yanzu, can zan je."
Ta faɗa sanda ta juya, a cikin zuciyarta tana lissafin layin da zata saka Samiran daya danganci ra'ayinta nan da shekara guda idan ƙwarya ta fashe!
Sahla ta fito daga ɗakinta a lokacin riƙe da labtop ɗin Munaya tana sake gyara gilasan idonta.
"Mami dan Allah ki bani 1000 muyi subscription, datar da muke streaming ta ƙare kuma Aunty Munaya tace mu kai mata labtop ɗin wallahi ba zata sake siya mana ba."
"Kije É—aki, na ajiye wasu canji akan mirror ku É—auka."
Ta san ita da Zahra ne don kullum suna manne da juna, shi yasa bata san me zai faru dasu ba nan da shekara É—ayan nan.
Ta fita daga ɓangaren zuwa harabar gidan kamar wata sarauniya, don duk ɗaukacin mutane kowa tsugunnawa yake yana mata sannu da fitowa yayin take binsu da murmushin da zuciyarta ta wanke shi tsaf, ta tace shi kafin fitowarsa. Kuma ɓangaren Inna Danejo ta fara biyawa ta kai mata maganin cikin ledar nan, na ciwon ƙafa ne wanda Innan tace tana jin daɗinsa saboda haka take sawa ana kawo mata duk wata.
Kuma bayan sun yi ƴar hira da sauran tsofaffin dake wajen da kuma tarin albarkar da Innar ke sanya mata, ta fito zuwa ɓangaren Baffa, kafin ta shiga ta hango Munaya daga gefen ɓangaren tana waya, sai gyara glasses ɗinta take alamun tana sauraren wani abu, kuma fuskarta kaɗai ta kalla ta san a rikice take tunda dama ita ko doguwar magana akayi yanzu zata rikice tace bata gane ba, duk kuwa irin mahaukacin ƙoƙarin da take dashi a ɓangaren karatu, don tun suna yara Jamal ke cewa Ma'aruf da Munaya sune Geniuses (masu kokarin) ɗin gidan.
Zuciyarta ta cunkushe a lokaci guda da ambatar sunan, shekaru goma kenan da shafewarsa a doron ƙasa, amma har yanzu yaƙi barin zukata su huta, don ƙaryane a gidan nan ance an shafe sati guda na kowanne wata ba'a samu wani ya ambace shi ba, hatta ita kuwa tunaninsa na yawan wulga mata a zuciya, ta tabbata da ace Jamal na raye har yanzu to da itace a bayan ƙasa, don ta daɗe da lissafa cewa shi da ita mutane ne da baza su taba rayuwa a lokaci guda cikin duniyar nan ba.
Ta zira muƙullin hannunta ta buɗe bangaren ta shiga. Komai yana nan kamar yadda ta sanshi, don dama ɓangaren a suna yake na Baffan amma ita ke da iko da komai na cikinsa, me ta gayawa Saratu ne ɗazu? Babu abinda ƙwaƙwalwar mace baza ta iya ba idan har ta saka kanta, ta tuno shekarun da ranta ke ɓaci idan ta ɗaga labulen ɗakinta ta hango kyakkyawar surar Hajiya Maimuna na shiga ɓangaren Baffan, idan taci kwalliyar nan tata za'a shafe tsawon dare ana musu da wani cewa bata ajiye kamar Ma'aruf balle ma wanda yafi shi a duniya ba, kuma da tayi tunanin cewa bata don ganinta a wajen lokaci yayi da zata bar mata bangaren ita kaɗai, me ya faru yanzu?
Tayi wani guntun murmushi lokacin da take kunna turaren wuta a jikin burner, a lokacin kuma Samirah ta shigo riƙe da katon tray ɗin dake shaƙe da kayan abincin da ita kadai ta san me ta dafa.
Ta ajiye su daga kasa kujerar da ta san nan ne wajen zaman Baffan sannan ta juya.
"Bana jin zan fito sai gobe kuma, kar ki daÉ—e a waje."
"To Mami." Cewar Samiran tana saurin fita, sai dai tana isa bakin kofar Hajiya Kilishin ta sake kiranta.
"Da gaske nake miki magana, kar ki wuce goma a wajen mutanen nan."
Kuma duk da ta amsa ɗin sai da taga yadda ranta ya ɗan ɓaci kafin ta fita. Dole ne ma ta ƙara dagewa wajen kokarin fara ɓanbare tarin abubuwa daga jikinsu, don komai ya kusa ƙarewa, wannan rayuwar ba dahir ɗinsu bace.
Fitar ta ke da wuya kuwa taji muryoyi daga wajen suna bin layin gaishe da Baffan da ta hango hasken fitilar motarsa da direba ya sauke shi ta labulen falon. Sai ta taho wajen kofar don ta bude, so take ya fara yin tozali da ita da kuma kwalliyarta kafin wani abu ma na É—akin.
Sai dai kafin ta ƙarasa ɗin wayar hannunta tayi ƙara, ya kalli lambar dake kiran ke shigowa kafin ta dauka, Kuma abin da muryar cikin wayar ta faɗa tun kafin ta kai ga cewa komai, shi yayi sanadin da zuciyarta ta doka a cikin ƙirjinta sannan wayar ta zame daga cikin hannayenta ta faɗi kasa ta tarwatse!
***
Hasken safiyar ya shigo ta tsakanin fararen labulen ɗakin yana ratsowa har ciki zuwa kan gadon da shima komai a jikinsa fari ne, Rukayya ta motsa a cikin baccinta tana ƙara binne kanta a cikin filon amma tasirin wasu dogwayen yatsu dake shiga cikin gashinta suka hana baccin nata cigaba.
"J dan Allah mana.."
Muryarta ta fito a can kasan numfashinta.
Jawad ɗin dake tsugunne a gaban gadon sanye da singlet fara ƙal da kuma wandon gogaggiyar shaddar daya sanya bayan ya fito daga wanka ya sake motsa yatsun nasa cikin gashinta yana matso da fuskarsa kusa da ita.
"Na gaya miki ina da meeting by 10 a Abuja, ko so kike in tafi in barki anan?"
Bata bude idanunta ba tace.
"And what time is it now? (Kuma yanzu karfe nawa?)
"Eight tana dab da ƙarasawa, kamar yadda zuciyata take dab da shirin fashewa akanki."
Bata san lokacin da tayi dariya ba sannan ta bude idonta akansa.
"Sai yaushe zaka dawo?"
"Sai nayi kwanakin da kika yi Paris."
Ta juya idanunta tana jin yadda yatsun nasa ke ƙara shiga cikin gashinta.
"Ka san bani da matsala ko zaka ninka kwanakin ne."
Ya gyada kansa a hankali.
"Na sani Barbie, na san ni zan haukace..."
Sai kuma yayi shiru yana kallon kyawawan idanunta yayin da itama tayi shirun tana sauraren yadda sautin numfashinsa ke fitowa akan fuskarta.
"You never know what I went through da bakya nan Rukayya, zan iya tsayawa a gaban ko waye in faÉ—a miki ke daban ce."
Ta lumshe idanuwan nata tana murmushi, tana da tarin hujjojin da zata yarda cewar dukkan maganganun Jawad akanta gaskiya ne, yana ƙaunarta ne da gaske, sai dai maganganun basa taba ƙarasawa har cikin zuciyarta don bata so ya tsallake huruminsa, tafi so ya tsaya a iya matsayin da tsananin kulawarsa gare ta da kuma matsayinsa na ɗan gidan minister da mahaifiyarta ke kwaɗayi yasa ta bashi kawai. Amma akwai wajajen da duk yadda ta kai ga jin sa a zuciyarsa bai isa ya tsallaka ba, Ma'aruf ne kadai mai wannan ikon akanta.
Ta tuna da text ɗin da ta tura masa a jiya ta nambar da aka tabbatar mata tasa ce, wani text layi guda kawai da ta tattara dukkan fatanta a cikinsa tana fatan ya zama silar niyya da kuma ƙudirin da ta gama tsarawa a cikin kanta har ma tayi masa ado da ƙarin wasu kyawawan abubuwan da zuciyar tata ke so.
'M'aruf, Hameeda ta tambaye ka...'
Kuma sai bayan da ta tura ne sannan bangaren ƙwaƙwalwar tata mai hankali ya shiga jero mata kuskure tare da wautar ta, yana gaya mata kamar ba haka ne daidai ba, yana hasko mata tarin yarjejeniyar data yarda da ita a cikin doguwar takardar nan, lokacin da ta yarda tasa hannu akan komai yayin da zuciyarta ke cike da ɗokin rayuwa mai kyau a gaba kamar yadda mahaifiyarta tace, yana gaya mata cewa saboda ta sami saɓanin tunaninta hakan baya nufin cewa ta shirya fuskantar duk waɗannan sharaɗan?
"Jibi zan dawo, ki gaya min zan ƙara samunki dan Allah."
Muryar Jawad ta jawo ta daga tunanin yayin da yake ƙoƙarin ƙara matsowa. Sai kawai tayi murmushi sannan a lokaci guda ta shammace shi, ta ture shi ta miƙe tsaye tana dariya, yayi ƙoƙarin kamo ta amma ta kauce saboda haka shi ya faɗa kan gadon inda ta taso.
"Zo."
Ya faÉ—a daga kwancen yana kallonta, ta matse kafaÉ—arta É—aya.
"Zanje in shirya ne kar kayi missing flight dinka."
"Wani abu zan gaya miki."
Ta ƙara matse kafaɗarta.
"Ka barshi sai na fito."
Da haka ta shige banÉ—akin tana murmushi yayin da Jawad ya dafe kansa da duka hannayen sa biyu yana jin wani abu kamar taraddadi akan abinda ke shirin faruwa.
Allah ya sani da gaske yana sonta, irin son da bai san adadinsa ba kuma bai san lokacin da ya shige shi ba, abinda ya sani kawai shine a matan da yayi mu'amala dasu a rayuwarsa Rukayya daban ce, komai nata daban ne ta yadda tun daga lokacin da ya santa, sanda suka haɗu a airport zuciyarsa ke bin ta kamar raƙumi da akala. Shi yasa a yanzu da iyayensa ke damunsa da maganar aure ya ture duk wani kokwanton zuciyarsa ya tsayar da abu guda, don ya tabbata idan yayi saɓanin hakan zai zama kamar an bar baya ba zani ne.
Saboda haka a lokacin da ta fito take tsaye a gaban mudubi tana shiryawa, sai ya ture komai ya jawo ƙwarin gwiwarsa ya isa kusa da ita ya tsaya daga bayanta. Ta ƙifta masa idonta ɗaya tana murmushi ta cikin mudubin kafin ya kira sunanta.
"Ruƙayya.."
Sai ta juyo ta kalle shi amma yasa hannayensa ya komar da ita gabaÉ—aya, tana kallonsa ta cikin mudubin shima yana kallonta lokacin da da ya buÉ—e baki yace.
"Ina so zan aure ki."
Ga mamakinsa sai kawai ta kalle shi na wasu sakanni ta cikin mudubin sannan ta ƙyalƙyale da dariya.
"Me kace?"
Ya haɗiye wani abu mai zurfi a maƙogwaronsa kafin ya saka hannayensa ya sake juyo da ita yana kallon fuskarsa.
"Wallahi da gaske nake, ina so zan aure ki Rukayya, ki bani dama ko a weekend É—in nan zan turo iyayena, saboda na fahimci cewa I can't live without you. (Ba zan iya rayuwa ba sai da ke)"
A lokaci guda ta shiga girgiza kanta yayin da duk wannan rahar ke barin fuskarta, kamar tana karkade ta ne tare da girgizawar kan nata.
"Ba muyi wannan alkawarin ba Jawad, saboda haka don me yasa zaka yi tunaninsa, ofcourse kana burge ni saboda wasu abubuwa a gefe, amma bana sonka, na daÉ—e ina gaya maka hakan, zuciyata ba taka bace."
Tana kallon yadda dukkan wani ƙwarin gwiwar da ya tashi dashi a safiyar ke zagwanyewa daga cikin idanunsa, tana kallon yadda yanayin dake cikin idanun nasa ke juyewa zuwa wani abu da ba zata iya fassara shi ba.
"Saboda me?" Yayi tambayar kamar iyakarta zata sa ta canja ra'ayinta.
"I'm sorry J, amma saboda gidan tsohon mijina zan koma kuma na riga na tsayar da zuciyata akan hakan, idan har ba zaka iya rayuwa ba sai da ni, to ni wataƙila munyi tarayya akan hakan,
don nima ba zan iya rayuwa babu Ma'aruf ba Jawad."
Bata san me yake tunani ba, bata san me yake lissafawa ba, kawai kallonta yake É—auke da wannan yanayin da, da ace lokacin da ta buÉ—e ido daga bacci ne ta ganshi a hakan, zata rantse cewar ba shi bane.
Saboda haka tayi baya a hankali ta fita daga cikin hannayensa, kuma sai ƙarar wayarta tazo a daidai wannan lokacin don haka ta isa wajen jakarta dake yashe daga can gefen gadon ta ɗauko wayar, bata ko tsaya tantance lambar dake kiran ba, ta ɗauka ta kara a kunnenta.
Kuma abin da muryar cikin wayar ta faɗa tun kafin ta kai ga cewa komai, shi yayi sanadin da zuciyarta ta doka a cikin ƙirjinta sannan wayar ta zame daga cikin hannayenta ta faɗo kasa ta tarwatse!
***
Ina Ma'aruf yake?
Kuna tunanin saƙon cikin wayar nan ya dangance shi?
Meye gaskiyar labarin Fatima?
#Aysha Shafi'ee.
#FikraWriters
#FararWuta.
Please go and read RAI DA ƘADDARA by LUBNA SUFYAN... that story is touching me.ðŸ˜