Complete Hausa Novels

Farar Wuta Book 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Farar Wuta Book 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 8 of 9

BABI NA SHA HUDU.
~~~~~~
I fall in love with your kindness, because it adds peace to my wounded but striving soul.
- Unknown.
***
Ruƙayya na tsaye daga jikin windon, hannunta rike da kofin wani shayi dake tiriri, idanunta na manne akan shukokin harabar gidan nasu dake waje, kamar nazarinsu take tana son gano wani abu a jikinsu, amma a zahiri kalaman aminiyar mahaifiyarta da ake kira da Hajiyar Sudan wadda ke magana a baya ne suka shiga kunnenta.
" ... Da mun tura wanda za'a samu ya kwance abin nan ke kin sani Nafi, yadda na ake da tabbacin na kabari baya dawowa haka aiki na yake ci..."
Sai kawai ta juyo a hankali tana kallon Hajiyar Sudan É—in kafin kai tsaye ta katse ta.
"Ban gane ba, ta yaya zamu iya kai abin har cikin gidan?"
"Yanzu duk bayanin da muke yi baki ji komai ba? Tunanin me kike yi bayan wannan?"
Cewar Mahaifiyarta Hajiya Nafisa, amma ga Hajiyar Sudan É—in wani shu'umin murmushi tayi tana kallonta sannan tace.
"Ƙyale ta Nafi, yanzu zata fahimce ni tsaf."
Ta fada ba tare da ta ɗauke idonta daga kan Rukayyan da itama ke kallonta ba, kuma da hannunta na hagu ta yi mata inkiya da alamun ta ƙaraso ta zauna a gefenta.
Rukayya ta kalli wajen, ta sake kallon fuskarta... Allah ya sani bata son matar sam, don ta daɗe tana zargin itace ta bawa mahaifiyarta shawarar data fito da ita daga gidan Ma'aruf, sai a yanzu da suka ga da gaske babu yadda zasu yi da ita akansa sannan suka hakura, ko kuma tace mahaifiyarta ta hakura don har yanzu bata gama yarda da ita Hajiyar Sudan ɗin ba sam, amma sanin cewar bata da wata hanyar da ta wuce tata yasa ta cije lebbenta kawai sannan ta ƙarasa ta zauna ba tare da kallonta ba.
Kuma kai tsaye sai ta fara bayani daga inda ta san zata fahimta.
"Yanzu mun aika masa da takardar sammaci, ba nufinmu a shiga shari'a ba kamar yadda nayi miki bayani, a iya gaban alkali za'a sulhunta komai a tsakaninku kin san duk abinda zaki faÉ—a da kuma shaidun da muka samu wanda zasu saka komai ya tagi daidai, don haka daga nan za'a baki Æ´arki ki taho gida da ita.
Kwana ɗaya kawai a tsakani, zaki haɗa kayanta wanda a ciki zamu san yadda za'a dinke ƙullin nan a cikin jakar yadda babu wanda zai tiya gani, sai ki kirashi wani waje inda zaku haɗu ki kalallame shi da zancen wannan yarjejeniyar taku, ki karbi kuskurenki da komai ki kuma bashi yarinyar da cewar kin yarda ta koma hannunsa kamar yadda kuka shar'anta, ki gaya masa cewa bayan wani lokaci ya dinga kawo miki ita kina ganinta.
Da wannan zamu barta a wajenta tsawon sati guda inda a sannan ne za'a sami wadda zata je gidan da sunan ta kawo sauran kayanta, a wannan lokacin za'a sami dabarar da zata kwance ƙullin nan, wanda da anyi hakan Ruƙayya, shikenan sai ki cigaba da kurbar shayinki kina kallon abinda zai biyo baya."
Ta ƙarashe zancen da wani faffaɗan murmushin da ya sassauta zuciyar Rukayyan a lokacin, don sosai yasa ta jin cewar kamar da gaske sunyi nasarar sun gama, tayi niyyar magana amma sai mahaifiyarta ta riga ta.
"Idan komai ya tafi daidai, sai ke kuma ki bar hakarƙarin mu ya huta haka kije can ki ƙarata."
"Ai babu abinda zai kuskure ma, na gaya miki idan kinga an samu saɓani a wannan abin Nafi, to gawar da aka binne zata fito ta dawo duniya, don haka ku kwantar da hankalinku kawai."
Wannan zancen yasa su yin dariya dukkaninsu kafin hankalin Ruƙayya ta juya ga wayarta da ta shiga ƙara daga can inda ta baro ta a jikin windon data tsaya.
Ta mike a hankali riƙe da kofinta ta koma wajen, sunan Jawad daya nuna akan screen din wayar yasa ta kurɓar shayin kafin ta ɗauki wayar ta kara ta a kunnenta.
"Barbie yau kika ce, 5pm."
Me yasa zai tuna mata? Ta sani, ta sani cewa shekaranjiya ta gaji da nacinsa da ba zai kare ba tace masa zasu hadu a yau, kuma da zata iya a yanzun ma zata kara masa lokaci ne, amma ta san ko ta kara ba zai barta ba don haka dole ne ta daurewa kanta a yau ta fuskance shi.
A hankali ta ajiye kofin hannunta akan windon, sannan tace.
"Ban manta ba J."
Taji ajiyar zuciyarsa daga ciki kafin yace.
"Then where did you decide?" (Ina kika zaba?)
Ta sake cije lebbenta na ƙasa
"Where we first met." (Wajen da muka fara haÉ—uwa.)
Kalaman suka daki zuciyar Jawad da tasirin da ita bata san shi ba, don a nata ɓangaren ta zabi fadar haka ne don zuciyarta ta tsara mata cewar a wajen da suka fara haɗuwar anan ya kamata ta kawo ƙarshen alaƙarsu gabaɗaya, ko yaƙi, ko ya so.
Kuma ƙarfe biyar da ƴan mintunan tayi mata a kofar Joint ɗin 'Harish', ta fito daga motar ta bayan ta jera ta a layin sauran dake wajen sannan ta gyara zaman dan mitsitsin mayafin data dora akan doguwar rigar jikinta ta atamfa, wadda akayi mata wani ɗinkin mai kyau daga kasa kuma tayi buɗewar umbrella, takalmin kafarta ba mai tsini bane wannan karon don ta sani rashin nutsuwar zuciyarta ba zai barta ta iya tafiya a cikin mai tsinin ba, ta shiga ciki babu mutane sosai, ƴan kaɗan ne kawai ke zaune akan kujerun wajen yayin da iskar yamma da kuma ƙamshin shuke-shuken wajen ke shiga hancinta.
Daga can karshe ta hango Jawad, zaune akan table din da a wajensa suka fara haÉ—uwa, ba zata tantance idan tebur din ne ko an canja shi ba amma dai wajen ne, yana sanye da wasu dogwayen kaya Kaftan, yasa hula dark brown wadda ta fito da hasken fatarsa tar a cikin yammar, Jawad mai kyau ne ba sai kowa ya tuna mata hakan ba. Kuma da alamu ya jima a wajen don tuni an sauke shi da shishar da yake bula hayakinta a iska.
Kafafunta suka ƙarasa wajen a hankali sanda shima ya hango ta, kuma a lokaci daya murmushi ya sauka akan lebbensa yana ƙara tuna mata da kammaninsa.
"Kina da cika alƙawari Babe, yana daya daga cikin abubuwan da suke kara haukatani akanki."
Bata yi murmushin da ta saba kamar kodayaushe ba sai kawai ta jawo kujerar dake fuskantarsa ta zauna.
"Wane flavour za'a kawo miki?" Ya tambaya yana tasowa daga kishingiÉ—en da yake.
Ta ajiye wayarta akan table din tare da earpiece É—in hannunta sannan ta kalle shi sosai.
"Ka san ba abinda ya kawo kenan ba Jawad, idan zaka kyauta ma just put yours aside muyi magana."
Ya gyada kansa yana kallonta.
"Zanyi duk abinda kika ce Barbie."
Da haka ya ajiye tasan gefe yana cigaba da kallonta, idanunsa na lumshewa akan fuskarta. Bata damu da yadda yake kallon nata ba kai tsaye ta fara magana.
"Jawad abubuwa sun cakuɗe a rayuwata yanzu, I've got alot going on table da ba sai nayi maka bayaninsu ba amma hakan ne yasa na yanke alaƙa ta da kai, don bani da wannan lokacin Jawad, abinda nasa a gabana ya karato don haka dole ne na ajiye ka a gefe.
Kuma nayi ƙoƙarin nuna maka hakan ta duk hanyar da zan iya amma ka kasa ganewa, shi yasa na yarda muyi wannan haduwar don in shaida maka komai baki da baki."
Tunda ta fara maganar bai ko kifta idanunsa ba, kallonta kawai yake da dukkan irin emotion din da zata iya tsinta a cikin idanunsa, wanda basu dame ta ba ta cigaba.
"Idan baka manta ba Jawad, tun farkon alakarmu na gaya maka cewa babu aure a tsakaninmu na san baka dauki maganar da muhimmanci ba a lokacin amma ni da gaske nake tun a sannan. Bari na fito fili na gaya maka gaskiya Jawad, a lokacin da na haÉ—u da kai ina cikin damuwar da ni kaina ban san mecece ita ba that is bayan mutuwar aurena na biyu, so na kula ka ne kawai don ka taimaka min in manta damuwa ta, and you really did help 'cox we wasted away ta hanyar ta hanyar da har sai da kasa na kusa manta cewa ina da abinda nake so bayan kai.
Yadda kayi treating ɗina Jawad da tsananin kulawa da komai shi yasa zuciyata ta yi laushi akanka har kayi tunanin duk abinda nake yi maka zai iya sawa na canja ra'ayina akanka, but honestly ban ɗauke ka komai ba more than a toy (abin wasa), baka taɓa zama wani abu mai daraja har da zan kalla da sunan aure ba Jawad.
Zuciyata ta mutum É—aya ce a duniyar nan kuma ina jin cewa ko za'a tsaida tashin duniya akaina ba zan taba iya canja hakan ba. So ka taimaka min mu karkare komai a yanzu, Let's just end everything here don ni tuni na fara gudanar da da sabuwar rayuwar da a cikinta zan cimma burina, ka taimaki kanka ka manta dani kaima Jawad.
Erase all those memories kayi pretending babu abinda ya taba faruwa tsakaninmu wanda na san a cikin kankanin lokaci zaka ji ka manta dani gabaÉ—aya. Ka kalli kanka, kana da komai the looks, status, kuÉ—i, age, time... You have it all J. (Kana da komai) zaka samu Æ´anmata guda dubu da kallo É—aya zaka yi musu and in no time they will be throwing themselves over you. Ka fahimta dan Allah Jawad cewa ni ba komai bace a rayuwarka."
Ta ƙarashe da dukkan fatan ya fahimce ta a cikin idanunta, kuma har a lokacin kallonta yake shima, sai da ta kai ƙarshe ɗin sannan ya ƙifta idanunsa a hankali, yana komawa da baya, ya jingina sosai da kujerar da yake kamar kwanciya zai yi sannan muryarsa ta fito.
"Anything more Barbie?" (Akwai wani abu kuma Barbie?)
Ta haÉ—iye yawu a makogwaronta sannan ta girgiza kanta.
"Nothing more Jawad, shikenan idan har ka fahimce ni."
Sai ya gyada kansa haÉ—e da rufe idanunsa ya buÉ—e kafin yace.
"Thank you." ( Nagode.)
Ta kalle shi tsawon wasu sakanni zuciyarta na son nazarin yanayin dake kan fuskarsa wanda bata gane ba kuma ta kasa gano komai É—in, hakan yasa kawai ta dauki wayarta data ajiye sannan ta mike tsaye.
"Nagode nima, sai wani lokacin."
Ya sake gyada mata kansa ba tare da yace komai ba, kuma da haka ta juya ta tafi, idanunsa suka bi bayanta da kallo, zuciyarsa na tsagewa da yadda jikinta ke kaɗawa da tafiyar da take yi yayin da ƙwaƙwalwar sa ke dawo masa da kalaman abokinsa Haro.
"Ka sake gwada ta for the last time Man, idan har tana nan akan bakan ta cewar ba zata saurare ka ba, nayi maka alƙawari ni zan taya ka yarinyar nan tayi biyu babu a rayuwar ta, dama na tsane ta J, kaima ka san na tsane ta!"
Ya cije bakinsa da ya bushe yayin da wani guntun murmushi ya sauka akan leɓɓen nasa lokacin da Ruƙayya tayi kwana ta fita daga wajen tana ɓacewa ganinsa. Wayarsa ya zaro a cikin aljihunsa ya shiga neman nambar Haron, bugu kaɗan kuwa ya ɗaga lokacin da ya jawo kan shisharsa, kuma sai da ya zuƙo hayaƙinta ya busa a iska sannan yace.
"Tayi biyu babu Haro, let the plan start!"
***
Jigawa,
11:05 Am.
"Gwara ki fito fili kawai ku fadi gaskiya, yanzu ke baza ki so in fara tafiya in gano me akeyi ba? Idan yaso ko ta email sai na rubuto muku abubuwan da zaku tanada?"
Aminu ya fada yana kallon Amina da ta gama gaya masa irin tashin hakalin da ta shiga jiya, tana zaune a gabansa tana ƙoƙarin zuba sukari a kofin tea ɗin data take hada masa.
Abinda ya faÉ—a yasa ta yin murmushin da bata shirya masa ba tana kallonsa, kafin tace.
"Allah ya shirye ka Aminu, ai wallahi ina jin mutuwar ce kaÉ—ai ma zata iya kashe bakin ka."
"Daga fadar gaskiya, yanzu ke tsakani da Allah baza ku so ku sami wata Æ´ar expo ba? Wannan harkar fa harka ce ta dindin idan an tafi an tafi kenan."
Tissue din dake gefenta Amina ta dauko ta jefe shi dashi a fuska.
"Aminu wannan fa ba zancen wasa bane."
Ya É—aga duka hannayensa sama.
"To shikenan, ai ke yanzu naga alama dama baki shirya mata ba, gashi nan har kin canja sai washewa kike yi wai ke amarya, dan Allah Amma bata yi haske ba?"
Ya tambaya yana kallon Amman da ta idar da sallar walha a lokacin, bata amsa ba sai jawai ta juyar da kanta gefe kawai ta cigaba da laziminta.
Kuma sai akayi sa'a kafin shima ya kara cew komai wayarsa a gefe tayi kara, ya ɗauka ya shiga sake amsa gaisuwar tarin mutanen da duk bayan ƴan mintuna ake kiransa. Amina ta sake kallon Amma data juyar da kanta tana lazimi, kafin itama ta sunkuyar da nata ƙasa a hankali ta shiga wasa da wani zobe a yatsanta, wani abu take ji yana tokarewa a cikin zuciyarta duk sanda ta kalli Amman.
Kusan awar su guda kenan da sauka, awa guda da zuciyarta ta narke lokacin da Ma'aruf ya tsugunna a gaban su Baba harma dasu Baban Kurna da suka yi sa'ar ganinsu don a safiyar ranar suma suka zo, yadda ya tsugunna a gabansu kansa a ƙasa suna amsa gaisuwarsa wani abu ne da girmansa yasa har yanzu ta rasa inda zata ajiye shi a cikin ranta, don har ciki ya shigo ya gaishe da Amma da kuma Aminun, sannan har yanzu idanunta suna hango mata damin kudin daya ajiye a gefen shimfiɗar Aminun lokacin da zai fita.
"Guess what?" (Kin san me?)
Ta tuna yadda muryarsa ta furta hakan daga bayanta lokacin da ta sake binsa wajen mota tare da wasu yara don su É—auko kayan nan ita kuma ta dauko jakarta da lokacin da suka tsabar zumuÉ—i tsaya bata ko tuna da ita ba ta buÉ—e kofar motar ta fita.
Yadda ya tsaya a kusa da ita bayan ta juyo yasa ta kallon gefe ta hango yaran suna tafiya cikin gidan kafin girgiza kanta a hankali idanunta a kasa tana kallon jakar data dauko.
"Naga yadda zaki koma idan kin ƙara girma."
Hakan yasa tayi saurin ɗagowa ta kalle shi, ya harde hannayensa duka biyi a kirji riƙe da wayoyinsa, kuma a take sai ya bata amsar tambayar da idanun nata ne suka yi masa.
"Kamar ki É—aya da Mamanki, na daÉ—e ban ga masu kama haka irinku ba."
RuÉ—ani idon nata ne ya tafi lokacin da ta sake sunkuyar da kanta kafin ta iya lalubo muryarta.
"Haka kowa yake cewa." Ta faÉ—a a hankali.
"Haka kowa yake gani that's why."
Bata ce komai ya sake cewa.
"Naji dadin ganinsu sosai Amina, yanzu naga inda kika samo wannan kirkin naki."
Bata san lokacin da wani guntun murmushi ya suɓuce a lebbenta ba duk da halin da take ciki. Ta sake ɗagowa ta kalle shi, har a lokacin kallonta yake da yanayin da bata iya fassara shi, yanayin da yake ƙara tuna mata cewa har yanzu bata san inda zata ajiye shi a zuciyarta ba.
"Nagode sosai."
Sai a lokacin tayi masa godiyar da tunda suka taho a hanya take fama da ita a bakinta tana tunanin yadda zata fade ta, kuma murmushin da yayi a wannan lokacin sai da ya kusan tsinka zuciyarta ba don kalaman Hajiya kilishi dake daure da zuciyar tata tamau ba.
A wannan lokacin Ma'aruf na kallonta ne tunanin mai yawa a zuciyarsa, Allah ya sani wani abu ya motsa a zuciyarsa game da ita tun daga ranar da ya fara ganinta.
Ya cewa zuciyarsa tausayinta ne da kuma mamakin ganin ƙankantar ta, don a lokacin da Mami tayi masa zancenta da kuma lokacin da ya tsinci sunanta a kayan Jamal, zuciyarsa bata kawo masa ko kadan cewar zai ganta karama irin haka ba. Kuma duk sanda ya sanda yake tare da ita a yanzu yana mantawa da dalilin da yasa ya yarda da aurenta ko kuma yadda na auren nasu ya kasance, yana ji ne kawai kamar zamansu wani abu ne da ya daɗe daga cikin tsarinsa, don abubuwa da yawa ya banbanta da irin zaman da yayi da Rukayya.
Tare da Ruƙayya gani yake kamar duk abinda yake yi dole ne, don ita tana da tarin expectation ɗinta akansa, ta daɗe tsara wata irin rayuwa tare dashi a cikin kanta da a wancan lokacin shi ba abinda ke gabansa kenan ba, shi yasa abubuwa da yawa kai tsaye zata gaya masa tace yayi kaza ko ya kamata yayi kaza wanda duk da ba saurarata yake yi ba, hakan baya masa daɗi, amma ko fuskar Amina ya kalla, innocent kammaninta kaɗai yana sashi jin wani cikakken iko irin wanda kowanne namiji ke ji akan iyalinsa.
Don haka yadda take kallonsa a wannan lokacin, yasa shi ture abubuwa da yawa a cikin kansa ya tako ya karaso gabanta, ya tsaya dab da ita sosai lokacin da kallon cikin idanun nata ya koma kalar mamaki da kuma ruɗani, irin ruɗanin da ya kula dashi tun ranar da ya dawo ya same ta tana kuka, zuciyarsa ta gaya masa cewa so yake ya rungume ta har sai kayanta sun koma ƙamshin turarensa gabaɗaya, amma yayi kokarin ture zuciyar dake gaya masa hakan yace.
"Kin manta baki É—auko basket É—inki ba."
Ta kuwa juya ta kalli basket din dake ajiye akan kujera kamar bata san dashi ba sannan ta dawo da fuskarta wanda hakan yasa ta ƙara matsowa dab da jikinsa amma sai tayi saurin yin taku baya kaɗan kafin tace.
"Abinci ne a ciki, ban sani ba ko zamu yi magariba a hanya, kace kana azumi."
Bayan ta faÉ—i hakan, bata san me yake tunani ba don sai da wasu sakanni suka wuce kafin yayi magana.
"Ban san ta yaya zance miki nagode ba, amma I'm really grateful, Allah ya saka miki da alkhairi dear."
Dear, dear, dear....
Sunan da ya kasa barin zuciyarta kenan har yanzu, yake rikita zuciyarta duk sanda ta tuno duk kuwa da irin zagayen tashin hankalin da take ciki ba cewar shi kansa a yanzu bai kamata ta yarda dashi ba duk kuwa da yadda komai nasa ke nuna mata akasin haka.
"Amina..."
Muryar Amma ta dawo da ita zahiri, ta É—ago da sauri ta kalle ta, har Aminu ya gama wayar yana shan tea din data hada masa.
"Ko zaki karɓo mana maganin da za'a saka masa yau a cikin gidan, kina shiga ɗaki na farko ne wajen Malam Ibrahim ɗin."
Malam Ibrahim Mijinyawa shine ɗanuwansu Fatima mai dorin, kuma gidan nasa ba'a cikin garin Jigawan yake ba, a wani ƙauye ne dake gaba kadan mai suna Kuɗai, gida ne kato da iyalansa, amma kusan rabin dakunan gidan yana saukar marasa lafiya ne wanda ciwonsu yayi tsamari ya zama sai anyi kwanaki ukun da yake bayarwa kafin a bar wajensa, don haka inda suke ɗin dakuna ne a jere kamar asibiti, sai dai bayan su ɗin wani ɗaki ne kawai daga can gefe inda aka sauki wani yaro da nasa iyayen suma da suka zo daga Kaduna.
A jiya su biyar Amma tace mata sun zo, bayan ita da Aminun da kuma Baba, sai kuma Fatiman da ta kawo su gidan da kuma wani É—anuwanta Yusuf da a jiyan su suka koma, dama an taho dashi ne don yayi mata rakiya tunda ita ba kwana zata yi ba.
Sai ta mike a hankali ta shiga neman inda ta ajiye mayafinta a dakin lokacin da Aminu yace.
"Anjima su Baban Kurnan zasu tafi Amma?"
"Eh, Babanku yace da sun dawo daga masallaci zasu kama hanya, su zasu tafi da waɗannan kayan da Amina ta kawo ma don mu sami sauƙi jibin."
Kalmar 'waÉ—annan kayan' ita ta tsaida kafafun Amina cak a inda taje, don ta san waÉ—anne kaya take nufi, kayan abincin da suka fito daga hannun Hajiya Kilishi.
"Wallahi matar nan tana ƙoƙari Amma, Allah dai ya saka mata da alkhairi."
Taji Aminun ya sake faÉ—a kuma ga mamakinta sai taji Amman tayi shiru bata ce komai ba, zuciyarta ta buga a kirjinta, ta juya da sauri a lokaci guda ta kalle ta, kanta na kasa a yanzu tana ninke wasu kayan Aminun, fata take ta fadi wani abanin tunanin sauran mutanen ko ta sami kofar da zata iya tunkararta da zancen da bata san ita ina fara ba, amma ga mamakinta sai tayi ajiyar zuciya sannan tace.
"Amin ta kyauta kam, haka Babanku ma yayi ta fada."
Sai kawai tayi saurin sunkuyawa ta damƙo mayafinta dake ƙasa sannan ta haɗiye abinda ke bakinta da karfin da zata iya kafin ta muryarta ta fito wani iri.
"Bari naje Amma."
Da haka ta tura ƙofar net ɗin ɗakin ta fita, tana jin kamar tana ɗauke da nauyin duniya ne bakiɗaya a kafaɗunta, Amma ce kadai fatanta amma ko ita bata san ta yadda zata fara gaya mata komai ɗin ba.
Abinda bata sani ba shine, idan ubangiji ya amsa addu'ar bawa, sai komai yazo masa a bazata, don wajen karfe ɗaya Aminu ya samu bacci, Baba kuma tun bayan tafiyarsu Baban kurna ya fita zuwa cikin gari. A lokacin ne Amma ta kira ta zuwa waje, kasan wata katuwar bishiya daga cikin gidan suka zauna inda aka shimfiɗa wata tsohuwar tabarma, kuma kalamanta na farko suka gutsirtsira duk wani saurin ƙarfin gwiwa da take jin cewa tana dashi na iya fuskantar wannan tashin hankalin.
"Amina a wannan zamanin mafarki baya tabbata, kin sani ba zan taɓa yarda cewa lafiya kike zaune a gidan nan ba ko?"
Lokacin da ta faɗi hakan kallonta take da ƙwallar data cika idanunta taf, amma sai ta girgiza mata kai ta cigaba da cewa.
"Ni uwa ce ina kallon abinda ya shige wannan zahirin, dukkan kalamanki da kuma abinda ke faruwa basu isa su sa in kasa hango damuwarki ba... Watakila a kwanakin baya muryarki a waya taso ta ɓoye min wani abu tunda ba ganinki nake yi ba, amma a yau kallonki kawai na yi Amina, na zaƙulo tarin abubuwan da ban sanki dasu ba fal."
Sautin muryar Amman ya fito da ɗimbin abubuwa masu yawa, masu yawan da a cikinsu babu wanda bai sake karya zuciyar Amina ba, yana tuna mata da rayuwarta ta baya data shuɗe cikin wani kankanin lokaci, lokacin da Hajiya Kilishi bata yiwa Baba wannan kiran ba balle har a fara ƙulla zaren ƙaddarar ta, lokacin da bata kirga damuwa a cikin lissafinta tana kwana tana tashi ne kawai da mafarkin abinda gobe zata haifar.
"Me suke yi miki Amina? Ki faɗa min abinda yake ƙasan wannan kyautatawar..."
Ba shiri leɓɓenta ya tale cikin kokarin yin kuka yayin da take cakuɗa yatsunta cikin juna, kuma kaf a cikin bayanin da bakinta ya fara, layi biyu ne kawai ya sa fuskar Amma haskawa da tsananin mamakin da ko na nesa zai ganshi karara, amma bayan wannan layi biyun, saurarar bayanin ƴarta tata take yi da dukkan wata nutsuwar da take da ita a duniya... Nutsuwar da take da ita ta Halimatus- Sadiyar ta, sannan nutsuwar da a cikinta ta shafe shekaru ashirin da ɗoriya a gidan aurenta ba tare da wani mahaluki a duniyar nan ya taɓa jin kanta game da mijinta ba.
Nutsuwar da a cikinta ne idan za'a taro duk mutanen da suka santa a rayuwa, ƙaryane a samu mutum guda da zai tabbatar da wani aibinta baiyananne... Nutsuwar da a cikinta wasu tarin abubuwa suka faru da idan da za'a buɗewa Hajiya Kilishi su, zata yi dana sani sau dubu na inda ta kawo kanta, zata raina duk wani tunaninta dama wayonta, zata san cewa tayi kuskure wajen amfani da ƙwaƙwalwarta wajen cimma munafunci, mugunta, yaudara har ma da zalunci.
Zata gane cewa ba an halicci ƙwaƙwalwar mace ne don ta fitar da da kaidi kamar yadda take taƙama ba, zata san cewa Allah ya halicci ƙwaƙwalwar mace ne don ta samarwa kanta duniya da kuma lahirarta a tafin hannunta kamar yadda ita tayi.
Kuma a karo na farko tun bayan tsawo lokaci wani murmushi ya suɓuce a fuskar Amman, ita ta sani ba'a banza jikinta ya bata cewar bata son kai ƴarta cikin wannan gidan ba, ashe wata halittar ce mai ɗauke da irin ƙwaƙwalwar ta a wajen, banbancin kawai shine ita waccan ƙwaƙwalwar cike take da duhu tata kuma fara ce kal!
Idan kissa da dabara Kilishi ke taƙama dashi, tazo wajen da yake daidai ita, hausawa sunce karen bana maganin zomon bana! wasan nasu ne yanzu, kowa zai yi nasa cizon da sunan ceto! Kuma Amina da Ma'aruf ɗin data zaɓa dasu za'ayi wasan! Wasan da a karshensa Sarki ɗaya zai tsaya a wani matsayi da ita ta riga ta saba dashi.
Don mutane ukun da ta ga ƙarshen makircinsu a rayuwarta, bata jin Kilishi ta ko kamo yatsan ƙafarsu, kuma kamar yadda ta nuna musu, haka zata tabbatarwa da Kilishi itama yadda cikakkiyar macen data amsa suna da matsayinta ke amfani da ƙwaƙwalwarta a bigiren da ubangiji ya halitta mata ba bigiren shaidan ba, zata nuna mata irin yadda tayi asarar nata tunanin a duniyar nan!
A hankali ta gyara zamanta sannan ta furta.
"Daga yau kar na ƙara ganin hawaye a fuskarki kamar yadda baki taɓa ganinsa a tawa ba...!"
Waɗannan kalaman su suka zama na farko da ta shiga sauke ƴarta daga raunin da ta hau kai zuwa dakakkiyar Aminarta da ta san ta baro hannunta da ƙwarin gwiwar cewa zata iya tunkarar yaƙin dake gabanta saboda mahaifinta.
Banbancin shine wannan karon zata sa ta fuskanci yaƙin ne saboda kyautatawar rayuwarta... a tafin hannunta zata ɗora mata rayuwar gidanta sannan a ɗaya tafin, zata ɗora mata Kilishi bayan sun sa ta biyo ta kan matattakalar...
'ÆŠan hakin da ka raina...!
***
Haseenah Guest Inn, Jigawa.
04:30pm
"Gidan da ka dauko Hamidan zaka koma Ma'aruf, a cikin mutanen gidan na san baza a rasa wanda zai tsaya maka a matsayin shaida ba, na gaya maka kuÉ—i kawai zaka basu har sai kayi limiting iya wadanda kake so, don wannan ita kadai ce hanyar da nake ganin zamu bi."
Muryar Ishaq ta faɗa a cikin wayar dake kare a kunnen Ma'aruf wanda ke tsaya a barandar wani ƙayataccen Guest inn dake cikin garin na Jigawa. Hannunsa ɗaya ya zura a cikin gashin kansa kasancewar ya cire hular kansa ya baro ta a cikin mota.
"Na gaya maka babu shaidar da zan gabatar Ishaq, ka barsu suyi dukkan abinda zasu yi, I have my ways akanta ita Ruƙayyan ita ta sani."
"Ka shirya faÉ—uwa kenan tunda ka san kotu ita da shaidu take dogaro ko?"
Ya cije leɓɓensa kaɗan.
"Ko hakan ne zai faru let them Ishaq, na san abinda zanyi. Kar ka tanadi komai kawai ka cigaba da harkokin ka, Allah ya kaimu ranar."
Da haka suka yi sallama a wayar da wataƙila itace ta huɗu tsakaninsu a yau kaɗai, ya kashe wayar daidai lokacin da wani ma'aikacin Guest inn ɗin ya ƙaraso inda yake.
"Yawwa yallaɓai, gashi an kammala komai."
Cewar matashin yana miƙo masa wani muƙulli.
"Nagode sosai."
Ya faɗa da murmushi yana karbar muƙullin ya zura a aljihunsa, kuma a cikin wayar tasa ya sake nemo nambar Hajiya Kilishi.
A wanna lokacin Hajiya Kilishi na ɗakin Baffa wanda dawowarsa kenan daga tafiyar da yayi zuwa Kaduna, shayinsa take ƙoƙarin hada masa yayin dashi kuma yake daga can kan kujera yana shafa man robb akan kafarsa don fitowarsa daga wanka kenan a lokacin.
Fuskarta É—auke da faffaÉ—an murmushi ta É—aga wayar tana fadin.
"Mai gaskiya na, kun taho ne?"
Ma'aruf ya girgiza kansa lokacin da yake tafiya wajen motarsa.
"A'ah Mami, yamma tayi sosai, so zamu kwana ne sai gobe, yanzu ma zanje in dauko ta daga can."
A lokaci guda irin wannan shirun dake biyo bayan walƙiya bayan haskawarta kuma kafin zuwan tsawa ya ratsa ƙwaƙwalwar Hajiya Kilishi da ta tsaya daga kokarin ɗebo madarar da take yi tana jinsa.
Biyu kenan! Sau biyu kenan a jere Ma'aruf ya yanke irin wannan hukuncin ba tare da tuntubarta ba, na farko tafiyar tasu zuwa Jigawan da kai tsaye yazo yake gaya mata tare da kowa, a yanzu kuma kwanansu a garin? Me yake shirin faruwa ne?
Ta girgiza kanta a fili lokacin da shi yake cigaba da gaya mata wani sabon labari na cewar baya son tuƙin dare ne, ba sai wani satin ba kamar yadda ta tsarawa Awwalu, a gobe ko jibin nan Ma'aruf zai sake komawa cikin ciwonsa. Ba ta yin saken da abubuwa ke cakuɗe mata, dole ne ta kwantar dashi don ta fahimci duk abubuwan data gano cewa suna ɗagewa daga cikin tsarinta.
Wani abu da bata sani ba shine, abubuwa ma basu fara É—agewa ba ko kaÉ—an!
***
Kun fahimci cewa kowa ya shirya a wannan Babin??😅😅
To su waye zasu yi nasara? su waye zasu fara su kasa? Su waye kuma zasu faÉ—i kasa wanwar??
Me kuke tunani game da Amma da kuma ƙudirinta?😀
Kar ku manta kuma, zamu yi kwanan Jigawa....😍😆😆
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.