Complete Hausa Novels

Farar Wuta Book 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Farar Wuta Book 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 6 of 9

BABI NA SHA BIYU.
Life is what happen to us when we are busy making other plans.
-Unknown.
**
Ranar lahadi ne da misalin ƙarfe huɗu na yamma, Amina na tare da Samirah da kuma Munaya a kitchen suna aiki tare da hirarsu wanda mafi yawanci Samiran ce ke tsokanar Munaya akan zuwan da tayi, tunda tun farko Samiran ce ta fara zuwa kafin ita kuma ta shigo m daga baya.
"Wallahi sai ayi baƙi kashi-kashi su zo gidan nan su tafi baki ganta ta fito ba, amma kiga wai itace yanzu tazo taya aiki babu gaira ba dalili."
Cewar Samiran a lokacin da take daka tafarnuwa Æ´ar kadan da zata saka a miyar dake kan wuta daga bayanta.
Munaya tana yanka carrots ta É—ago ta kalle ta tace.
"Ki kara faÉ—ar abu guda É—aya ki gani idan ban jefe ki da grater nan ba."
Amina tana murmushi daga inda take blinding abarba tace.
"Ki ƙyale ta haka mana Samirah, shikenan don tazo sai da dalili? Da nan da cikin gidan ai duk ɗaya ne."
Samiran ta girgiza kanta.
"Ba zaki gane bane Aunty Amina, saura fa sati biyu ta fara exams, da su Zahra suna nan zasu gaya miki a irin wannan lokacin ba'a ganinta wallahi, idan ta shiga É—aki sai ta yini akan littafi sallah ce kawai ke tada ita, ko Hajiya sai dai tayi ta faÉ—an taci abinci, Allah karatun da take yi har na gama rayuwata a duniyar nan ba zanyi rabinsa ba..."
Bata karasa ba kuwa lokacin da Munaya ta saita daidai bakinta da wani katon karas din dake gefenta ta jefe ta dashi, amma duk haka Samiran bata yi shiru ba, ta cigaba da bayanin ta tana faÉ—in ita bata yarda da zuwan nan nata ba sam, wanda ke saka su dariya.
Amina ta tsiyaye ruwan abarbar a hankali cikin wani katon bowl tana kokari kar ya taɓa ciwon hannunta da bata daɗe da jinsa ba wajen yanka albasa, tana jinsu har yanzu Munaya na rokonta akan ta kyale ta amma Samiran taki yin shiru.
Munaya tana da saukin kai sosai, don tazarar shekarun dake tsakaninsu da Samiran da É—an yawa, amma idan suna hira irin haka ba zaka ce ba, ta juya tana kallonsu, ita kanta dai ta É—anyi mamaki zuwan Munayan tunda tun bayan ranar da suka zo gabaÉ—aya suka gaisa sau É—aya ra kara shigowa ranar da suka yi zancen littafin nan.
Samirah ce dama kusan kullym zata leko ɗan bsyami ko saƙonta, a dazu ma tazo kawo mata wata darduma ne mai kyau daga Hajiya Maimuna taga tana aikin shine ta tsaya don ta taya ta, bata daɗe ba kuma sai ga Munayan itama ta shigo, ganin suna aikin yasa itama ta tsaya taya su.
"Ki cigaba Kar ki fasa, I have my ways of torturing you kin sani wallahi."
Munayan ta faɗa yayin da suke dariya dukkaninsu, Amina ta ɗauko bowl din da ta juye ruwan abarbar ta taho don ta saka shi fridge ya ɗanyi sanyi kafin ta ƙarasa abinda zata yi tazo haɗa lemon.
Fridge ɗin yana daga gefen kofar shigowa kasancewar shine na karshe a yadda drawer kitchen ɗin take a jere, don haka ta taho wajen daidai lokacin da Ƙofar kitchen din ta buɗe Ma'aruf ya shigo ciki, yana sanye da wata loose riga fara mai dogon hannu, gashin kansa a barbaje kota'ina kamar yadda yake tun safe kasancewar bai fita ba yau, amma babu banbanci da cewar yana nan din, don tun safen yana ɗakinsa yana faman wani aikin a computer, banbancin jiya da yau shine a yanzu fuskarsa fayau take, babu gajiya irin ta jiya ko kadan, ya riga ya manta duk wannan tunanin meeting din nan, don bayan dawowarsa a jiyan ya bata labarin cewa komai ya tafi daidai tsakaninsu da mutanen da suka yi meeting ɗin.
"Kinyi addu'a mai kyau kuma Allah ya amsa."
Kalaman da ya gaya mata kenan a jiyan wanda ta kwana suna yawo acikin kanta. Shi yasa a yau ma da safe breakfast mai daɗi suka yi yana kara gaya mata irin nasarar da suka yi suka shawo kan mutanen nan ɗaya kamfanin suka kulla alakar kasuwancin a tsakaninsu, hirar dake ƙara sawa tana fahimtar abubuwansa da yawa, tana jin zuciyarta na canjawa game da tunaninta akansa, wasu abubuwa da yawa a cikin kanta na gaya mata cewa ba shine wannan Ma'aruf ɗin da ya bata wannan saƙon ba... Ba shine kuma wanda Iyayenta suka gaya mata yana da matsalar ƙwaƙwalwa ba.
Shi yasa ko da ya gaya mata cewa Ishaq ɗin da suke waya kullum ya dawo daga tafiyar da yayi zai zo a yau, zuciyarta tayi tunanin aƙalla ta tarbe shi da irin tarbar da ya kamata, ba don komai ba sai don ta san hakan ne ya dace kuma ko zata yiwa kanta ƙarya ta sani cewa tana son yadda zamansu ke tafiya duk kuwa da yadda koina a tunaninta ke gaya mata cewa akwai abinda ke shirin faruwa.
Ƙafarta ta ƙarasa wajen Fridge ɗin ne daidai lokacin da ya shigo, taga idonsa ya haska da mamaki yana kallon su Munayan da kuma aikin da suke yi.
"Me yake faruwa anan?"
Muryarsa tasa dukkaninsu juyowa a lokaci guda, kuma a taken fuskar kowannensu ta faɗaɗa da murmushi yayin sa Munaya ta kira shi cikin wani abu mai kama da waƙa.
"Yayaaaaa B...."
A ƴan kwanakin nan Amina ta fahimci kusan duk sanda suka ganshi haka ne, haka gaisuwarsu ke farawa kamar sun daɗe rabonsu dashi, hakan ya tabbatar mata cewar ba ganinsa suke yi sosai a baya ba, a yanzu ne lokaci ya kawo musu shi kusa dasu wataƙila kamar yadda suka saba a ganinsa a baya.
Kuma kafin tace wani abu, dukkansu suka ajiye mata aikinta sunyi wajensa, wani abu ya faɗa a zuciyarta ganin yadda kowannensu fuskarsa ke ɗauke da fara'a sun baibaye shi da maganganun da kallon fuskokinsu kawai yake yi, ba irin Samirah da ta shiga bashi labarin da ta gama bata a ɗazu na wani competition ɗin kamfanin Maggi da aka zaɓe ta zasu je suyi a Abuja, Munaya kuma tana ta maimatawa wai ta gaya masa labtop ɗinsa take so ko kuma ya siyo mata wata sabuwa irinta...
Me yasa ne wai take tunanin akwai wani rami a rayuwar waÉ—annan mutanen?
Tana jiyo muryoyinsu har lokacin da ta shiga store don neman wani abu ba tare da ita taxe komai ba, kuma ba'a daɗe ba taji an ƙwankwasa kofar store ɗin dake buɗe a hankali sau biyu kafin muryarsa tayi magana a bayanta.
"Akwai ruwa anan?"
Ta juyo ta kalle shi, yana tsaye daga ƙofar store ɗin, ta manta cewa ruwan dake ajiye a kitchen ya ƙare tun dazu kuma bata fito da wani ba, don haka da sauri ta juya bayanta inda katan din ruwan yake a jere ta buɗe na saman ta ɗauko ɗaya, yana tsaye yana kallonta har ta ƙaraso ta miƙo masa, kuma ga mamakinta tana ƙarasowa sai kawai ya hado robar ruwan da hannunta gaba ɗaya ya jawo ta zuwa gabansa, ƙafafunta suka taho dab dashi yayin da ya dago da hannun nata yana kallo, ba shiri numfashinta ya katse a ƙirjinta lokacin da yasa ɗan yatsansa ɗaya ya taɓa daidai wajen data yanke ɗazu.
"Me ya faru?"
Muryarsa ta fito a yana kallon ciwon.
Sai da ta haɗiye yawu tana ƙoƙarin saita tunaninta kafin tace.
"Da wuƙa na yanke."
"Me kika saka a wajen toh?"
Muryarsa ta sake tambaya a hankali ta yadda har tana jin ƙarar wukar da Munaya ke amfani da ita daga can kitchen ɗin, da kuma nuryar Samirah da ta fita waje tana waya.
Ta sake haÉ—iye wani yawun a makogwaronta.
"Ba komai na wanke ne kawai."
Sai ya kawo daya hannunsa yasa su duka biyu ya rike natan, sannan ya buÉ—a ciwon sosai don yaga zurfinsa, zafin ya tafi har cikin kanta ta runtse idanunta da sauri tana cije lebbenta, sai yayi saurin sakin wajen sannan ya rufe yatsan nata da duka hannayensa biyu kafin yace.
"I'm sorry na duba ne na ga yadda yayi and it was deep." (kuma yayi zurfi.)
Ta buɗe idanunta a hankali sannan ta ɗaga kai ba tare da tace komai ba, kuma bai saki hannunta nata ba sai ya cigaba da rike shi yana kallonta, hakan yasa ta ɗago da idonta kalle shi da ɗan ƙaramin mamaki.
"Aikin me kuke yi haka?"
Ya tambaya tun kafin tayi wani tunanin, sai ta girgiza kanta.
"Abinci ne kawai."
"Kala-kala haka?"
Muryarsa ta sake fitowa da wani abu da ya shiga bin kowacce jijiya ta jikinta yana kassara ƙarfinta, taji kamar wani yana zazzaga mata wani magani mai karfi ne da aka haƙiƙance zaiyi tasiri akanta, kuma a yadda tata muryar ta fito tana rawa, kamar dama anyi mata baki ne cewar hakan ne zai faru.
"Kace abokin ka zai zo."
"Ishaq?" Ya tambaya kai tsaye sai kuma ya sake cewa.
"Ya salam duka saboda shi kuke yin wannan aikin?"
Shi ko kadan unaninsa bai kawo masa cewa don Ishaq ɗin zai zo ya kamata ayi wani abu ba, duk da a baya ma idan zaiyi baƙi Ruƙayya kan shirya musu wani abun amma a yanzu ya riga ya manta da hakan kwata-kwata, saboda haka a lokaci guda zuciyarsa taji dadin hakan, sai kawsi ya gyada kansa yana kallonta sannan yace.
"Thank you."
Ta É—aga kanta da sauri itama tana fatan hakan ne karshen zancen nasa, don bata san me zata zama ba idan har ya cigaba da magana rike da hannunta a hakan. Kuma kamar yaji fatanta, sai ya zare hannunsa nasa a hankali, taji É—uminsu yana barin fatarta.
"Zan nemo abu in rufe miki ciwon anjima insha Allah."
Da haka ya juya ya fita rike da robar ruwan a hannunsa.
A lokaci guda Amina taji kamar numfashinta yayi wata tafiya mai nisa ne sai a yanzu take iya zuƙo shi, ssi kawai ta juya itama ta ɗauko wata robar ruwan ta balle hancinta ta shiga sha yayin da bayanta ya jingina da drawers din store ɗin.
Sai da ta kusa shanyewa sannan ta tsaya, tasa bayan hannunta tana goge wanda ya zuba a gefen bakinta. Bata san me yake shirin fara damunta ba amma koma meye, so take ta tunawa kanta cewa duk abinda ke faruwa wannan gaske ne ba labari ba da komai zai tafi daidai, abubuwa ba zasu tafi kamar a mafarki tare da mutumin da daga shi har ita basu san juna ba sai bayan aurensu kuma har yanzu bsta san manufarsa akanta ba.
Ma'aruf ba zai taɓa sauko da kansa haka akan ita ɗin da ba kowa ba, don ta sani cewa bayan matar daya aura Allah kadai ya san matan daya sani a a rayuwarsa ko ma wanda yake tare dasu a yanzu, to don me yasa hankalinsa zai tsaya akan ita din da ba kowa ba, ita ɗin da sa baiyane yake cewar ba sa'ar rayuwarsa bace.
Ta girgiza kanta tana kokarin rufe robar ruwan, wannan lokacin kamar zubar ruwa ne kawai kafin zuwan tsawa, kamar iska ce mai daɗi kafin guguwa, sannan kamar kaɗawar ruwan teku ne a hankali kafin ambaliyar sa, akwai wani abu dake jiran ta bayan wannan, kawai dai dan adam baya taba sanin lokacin da ƙaddara ko kuma wata masifar rayuwar ke zuwar masa ne.
Muryar Amma ta cikin mafarkin nan ta gifta a cikin kanta lokacin da take cewa
"Me yasa kika yarda ba zaki iya ba Amina..."
A hankali tayi ajiyar zuciya tana fatan Allah yasa koma meye ke shirin faruwa ta iya tunkararsa da ƙafafunta a tsaye, daidai lokacin da a zahiri ta jiyo muryar Samirah ta shigo tana kiranta.
"A ina kika ajiye sugar?"
Sai kawai tayi sauri ta ƙarasa goge bakinta sannan ta ajiye robar ruwan ta fita.
****
Karfe Bakwai daidai Ishaq ya iso, kuma Amina bata san me ya faru ba, don minti biyar bayan zuwansa sai ga sallamar É—aya abokin Ma'aruf da shima ta riga ta haddace shi a waya mai suna Faruk.
Su uku kaÉ—ai suka cika falon da surutu kamar su biyar, kuma duk yadda take ganin Ma'aruf na da magana sai a lokacin taji nasa mai sauki ne, don kafin taji muryarsa taji tasu da yawa musamman Faruk É—in, don shi yafi Ishaq yi mata magana sosai ma, har matarsa da Æ´aÆ´ansa yayi alkawarin kawo mata tunda yace yanzun a sama kawai Ma'aruf ya kira shi yace masa yazo.
Kuma har lokacin da suka zo ɗin su Munaya basu tafi ba, Samirah dai taso tafiya amma sai Munayan tayi ta roƙonta akan su ƙara tsayawa tukunna, wani abu da ya ƙara bawa Amina mamaki don ita kanta ta san babu wani dalili Munayan ba zata yi ta cewa su tsaya ba. Ilai kuwa a lokacin da suka je kai musu abincin nan, a lokacin ta samu amsarta, saboda idon Ishaq na kan Munaya tunda suka shiga har ta juya Kitchen don ta ɗauko wani abun, kuma zata rantse ma taga sanda suka yiwa junansu murmushi lokacin da take zuba masa lemo, Allah ya sani yau ta fara ganin Ishaq ɗin amma sai taji zuciyarta na jiyewa Munaya daɗi idan har hasashenta akansu gaskiya ne, don duk inda nutsatsen namiji yake za'a saka Adam a wannan layin, kuma itama Munaya babu ruwanta da wani hargitsi sam.
Sun ji daÉ—in tarbar da suka samu kwarai, don ba'a kalamansu kaÉ—ai ta fahimci hakan ba, har a fuskar Ma'aruf da kuma yanayin kallon da yake mata tun lokacin da taje ta sako wani dogon hijabi bayan shigowar su, wani abu da ita kanta taji ta kyauta da tayi hakan.
Bayan sallar isha'i ne sannan suka yi musu sallama suka fita, kuma sun daɗe a waje suna magana don har bayan tafiyar Faruk ɗin shi da Ishaq suna nan, har su Munaya suka tafi ta ƙarasa wanke iya kwanukan da aka ɓata kasancewar basu tara wanke-wanken ko ɗaya ba dama a ɗazu.
Kuma tana sallah lokacin da ta jiyo ƙarar fitar motar Ishaq ɗin, sai dai har ta idar ta gama addu'o'in ta da komai bata ji lokacin da Ma'aruf ya shigo ba ko kuma don haka ta ƙudirta a ranta cewa cikin gida ya shiga. Da wannan tunanin ta ninke sallayar tare da hijabin ta ajiye su a gefe, ta ɗauko wayarta don kiran su Amma, sai dai daga layin nata har na Aminu bai shiga ba, kuma bata son kiran Baba a wannan daren, don haka ta bari zuwa gobe, ta nufi wardrobe ɗinta don ta ɗauko kayan bacci, wata sabuwar doguwar riga ta dauko sannan ta dawo gaban gadon don ta canja.
Ɗankwalinta ta fara cirewa ta ajiye shi a kan gadon sannan ta shiga kokawa da zip ɗin rigarta, amma ga mamakinta saiya riƙe ɓam yaki ko motsi, gashi ciwon hannunta ba zai bari ta rike shi da kyau ba, na dama kuma yaki ƙarasawa can saman, dama tunda tazo saka kayan ta kula yana da matsala amma bata yi tunanin ta kai haka ba.
Har sai da hannunta ya ƙage ta tsaya ta tattaro dukkan ƙarfinta sannan ta cigaba da jansa, kafin a lokaci guda kamshin turaren Ma'aruf ya shiga hancinta.
***
A waje bayan Faruk ya tafi, sun dade a tsaye shi da Ishaq suna hirar tarin wasu abubuwan da suka shafe su wanda yawanci duk akan matsalolin dake baibaye da rayuwar Ma'aruf ne, sai kuma zancen Abdurrahim, ƙanin Ma'aruf ɗin dake can New York wata makaranta ta Bebaye irinsa, (Rochester Institute of Technology.) Don Baffa ya gaya musu cewa saura watanni biyu kawai ya kammala ya dawo gida.
Bayan wannan sun tattauna zancen Hamida ma inda Ishaq yayi-yayi da Ma'aruf akan ya ɗauko yarinyar daga inda ya kaita ya dawo ta ita cikinsu, amma ya ɓata bakinsa a banza don ya riga ya rantse cewar Ruƙayya ba zata taɓa sanin inda Hamida take ba sai ya kammala da al'amarinta gaba ɗaya, ko shekaranjiya da Mami taso yi masa zancen itama kai tsaye ya dakatar da ita ta hanyar gaya mata cewa lokacin da zai ɗauko ta bai yi ba, don haka itama taja bakinta tayi shiru, don dukkaninsu sun sani cewar idan har ya furta abu, Baffa ne kawai zai iya sauke shi daga kansa, amma ko da suka yi magana da Baffan shima cewa yayi...
"Wannan zancen naku ne kai da mahaifiyar yarinyar Muhammad, duk abinda kuka yanke idan har ba kuskure bane mu namu addu'a ne tunda kune kuke da iko akanta fiye damu. Kuma kowannen ku yana da ikon da zai riƙe ta, duk da dai a matsayinta na mace an fi so ta zauna a gaban mahaifiyarta, amma idan har za'a samu matsala wajen tarbiyarta ko lafiyarta kamar yadda aka fara yanzu, to zamanta a wajen naka zai fi."
Wannan zancen na Baffa shi ya bashi ƙwarin gwiwar cigaba da shirin da yake da niyya wanda yake jiran lokacin kawai. Daga ƙarshe kuma suka ƙare da zancen ginin su wanda Ishaq ɗin ya gaya masa cewar ya samo wasu sababbin masu ginin da zasu fara aikin tunda Ma'aruf ya sallami waɗancan.
Kuma baiyi mamaki ba da Ishaq ɗin baiyi masa zancen Amina ba, don ya riga ya fahimci cewa ba sai yayi ɗin bane, akwai wasu abubuwa da ba lallai sai sun furta su a tsakaninsu ba, wasu abubuwa ne da ƙarara kowannensu ke ganewa idan ɗayan yana ciki, don haka a yanzu ma Ishaq ya riga ya sani cewar ya riga ya yanke koma wane irin hukunci ne game da zamansu ba sai sun ɓata lokaci wajen biya shi ba.
Da haka suka yi sallama, sabon maigadin da ya samo ya sake budewa Ishaq gate É—in gidan, shi kuma ya koma ciki.
***
Yayi sakanni biyu tsaye daga bakin kofar yana kallon yadda take kokawa da zip É—in rigarta kafin ta ankara dashi, watakila jikinta ne kawai ya bata cewar yana daga bakin kofar, don a lokaci guda ta juyo da sauri tana kallonsa, fararen idanunta suka zare akansa yayin da a lokaci guda ta saki hannayenta duka biyun suka sauka a gefenta.
"I'm sorry banyi sallama ba ko?"
Sai ta girgiza kanta.
"Babu komai ban ji lokacin da ka shigo bane."
Ya cije lebbensa tsaye a jingine kofar kafin yace.
"I'm sorry bana so in É—auki lokaci ne kiyi bacci."
Idanunsa na kallon fuskarta da yaga kamar tana ƙoƙarin kore wani abu wani abu mai kama da mamaki kafin ta tambaya.
"Wani abu kake so?"
Lokaci ne ya tsaya cak a cikin kansa da wannan tambayar yayin da fatar bakinsa ta bude kamar zai ce wani abu yana kallonta, tsakaninta da Allah ta fadi hakan ba tare da ta san tarin ma'anonin da za'a iya fitarwa daga kalaman nata ba, ganin tana cigaba da kallonsa yasa ya sake cije leɓɓensa na ƙasa sannan ya girgiza mata kai.
"I want to treat your hand." (Hannunki zan duba.)
Ya faɗa yana kallon yadda fuskarta ke nuna tarin yanayi kala-kala, ƙafafunsa suka tako cikin ɗakin a hankali zuwa inda take tsaye, kuma kamar a wani shiri sai iska ta buso daga windon da yake fuskantar su daidai lokacin da ya tsaya a gabanta, kuma bai ɓata lokaci ba yasa hannunsa ɗaya ya ɗauko nata mai ciwon nan.
Gabaɗaya tsawonta iya kafadarsa ne, gashin kanta da babu dankwali ya taso sama yana shaida laushinsa, da zai iya a wannan lokacin zai zare ribbon din data ɗaure shi ne don ya sauko kafadunta yaga iya tsawonsa, amma sai ya daurewa wannan tunanin ta hanyar kallon yatsun hannunta da yake riƙe dasu.
Ya san cewa shi mutum ne da yake ƙarbar respect daga ɗimbin mutane, kuma a iya kokarinsa yana kokarin ganin ya kyautatawa duk wanda ya shigo hanyarsa, da kuma kaffa-kaffa musamman a yanzu don ganin bai yi wani abu da zai iya cutar dasu ba, amma Allah ya sani bai taɓa haɗuwa da wanda a lokaci guda yaji zuciyarsa na tsoron ciwonsa akanta ba irin yarinyar nan, yarinyar da a baya bai damu da yadda zaiyi kokarin samun bayanin da yake so daga gare ta ba,
Wani bandeji ne mai haɗe da audugarsa a jiki, don haka magani kawai ya ɗiga a jiki daga cikin wata ƴar kwalba sannan ya rufe ciwon nata dashi, ai kuwa ta runtse idanunta a lokaci guda tana jin zafin na tafiya har tafin ƙafarta.
"Zuwa safe zaki iya cirewa sai a saka wani, insha Allah a kwana biyu zai warke."
Ya faÉ—a yana sakin hannun nata, kuma duk da zafin da take ji haka ta shiga daga kanta da sauri alamun ta fahimta.
Ya rufe maganin sannan ya wuce ta zuwa wajen da mudubin É—akin yake, ya ajiye roll É—in plaster da kuma kwalbar maganin akai sannan ya juyo ya dawo inda take tsaye tana cigaba da danne ciwon.
Kuma bata yi wani tunani ba lokacin da ya tsaya a bayanta, dab da ita sosai, don haka da sauri ta juyo gabadaya ta kalle shi amma sai ya saka hannayensa duka biyu akan kafaÉ—unta ya juyar da ita.
"Zan taimaka miki da zip É—in ne..."
Ya faɗa muryarsa na fitowa dab da kunnenta sosai, kuma kafin tayi ƙokarin kamo tunaninta muryar tasa ta cigaba da cewa.
"Akwai abubuwa da yawa game dani a zuciyarki na sani, amma ina so a saman komai kisa a ranki cewar ba zan taba cutar dake ko in takurawa rayuwarki ba insha Allah."
Ya furta hakan yayin da hannunsa ya kai kan zip ɗin, sauran yatsunsa na ɗaya hannun suna taba fatar bayanta, sai kawai ta rufe idanun gabadaya tana ƙoƙarin saita numfashinta, kuma da ja ɗaya kawai hannunsa yayi ya sauke zip ɗin sai dai bai kai shi har ƙasa ba, daga daidai tsakiya ya barshi, taji sanda yatsunsa suka dauke daga saman fatar ta, da kuma sanda yake matsawa, sai ta buɗe idonta lokacin da ya zagayo daidai saitin ta.
"Nagode." Ba zata ba taɓa iya tantance yanayin yadda muryar tata ta fito ba, ya gyaɗa kansa.
"You are welcome, sai da safe."
Da haka ya juya ya nufi kofar É—akin yana rufo mata ita.
Sakan ɗaya, biyu, uku, suka wuce Amina tana ƙoƙarin saita numfashinta kafin a hankali ta ɗauko rigar baccin nan ta karasa abinda zata yi, wanda har ta gama komai ta kashe fitilar ɗakin kalamansa na yawo a cikin kanta.
...ba zan taba cutar dake ko in takurawa rayuwarki ba insha Allah.
Sai kawai ta rufe idanunta sannan ta dunkule jikinta akan gadon, kuma bata bawa zuciyarta wani damar tunani ba don bata san buhu nawa zata kwance na tambayoyin da bata da amsar su a zahiri dama cikin kanta ba.
Ya rabbi lakaal hamdu kam yanbaghi li jalaali wajhika wa adheemu sulÉ—aanik.
Bakinta ya furta addu'ar hankali yayin da take jin ma'anar ta na tafiya har ƙasan zuciyarta.
***
Washegari...
Ƙarfe goma na safiyar Litinin, a irin wannan lokacin Amina ta saba da wani irin shiru don ko'ina tsit yake, duk wani mai fitar safe ya daɗe da yin gaba, ƴan makaranta da masu aiki da mafi yawanci sun fi yawa a kowanne gida.
Tana daga kitchen a lokacin tana ƙoƙarin fara aikinta ta tsinkayi ƙarar ƙwanƙwasa kofar, mamaki ya ɗan kamata don ta san babu wanda zata yi tunanin zuwansa a wannan lokacin, ta gyara zaman ɗankwalinta yadda ta yafa shi sannan ta fito daga kitchen ɗin ta iso ƙofar falon kuma ba tare da tunanin komai ba ta buɗe ta,a lokaci guda siffar Hajiya Kilishi dake tsaye ta shiga idonta tun kafin sakon saninta ya ƙarasa ƙwaƙwalwar ta.
Tana sanye da wata haɗaddiyar lafaya ruwan makuba (maroon) da ta nannaɗe ta tsaf a jikinta, fuskarta kamar kullum ɗauke da wannan murmushin nata, murmushin dake haska annurin fuskarta a kodayaushe yana ƙawata kammaninta.
Babu dalili Amina taji gabanta ya faÉ—i amma tayi saurin kore hakan wajen yin nata murmushin itama.
"Sannu da zuwa Mami, barka da zuwa."
"Barkanmu dai Amarya. Yau dai na ajiye kyuiyata a gefe nazo ganin É—akin amarya."
Wani murmushin mai haɗe da kunya Amina ta sake yi kafin tayi baya don bata hanya tana kara fadin 'Barka da zuwa', kuma kai tsaye kuwa ta shigo haɗe da sallama yayin da ƙamshin daddaɗan turarenta ke rufo mata baya.
"Wa'alaikum salam."
Ta amsa sallamar tana rufe ƙofar har a lokacin da murmushi a fuskarta, murmushin da a lokaci guda ya ɗauke sakamakon juyowar da Hajiya Kilishi tayi tun kafin ta kai tsakiyar falon tace.
"Idan akwai muƙulli rufe ƙofar dashi Amina, akwai maganar da zamu yi ne."
Zuciyarta ce ta fara bugawa a kirjinta kafin ta juyo ta kalle ta, amma ganin murmushin dake kan fuskarta har yanzu, yasa itama ta dawo da wani dan guntu kan leɓɓenta sannan tace.
"Toh Mami."
Da haka ta rufe kofar tana ƙoƙarin gayawa zuciyarta cewa gabanta ba faɗuwa yake ba sannan ta juyo ta ƙaraso ciki.
A lokacin ta zauna daga tsakiyar kujera mai cin mutum uku a falon don haka ita tameni waje daga ɗaya karshen ƙaton carpet ɗin ta zauna tana fuskantar ta.
"Barka da Asuba Mami, fatan kun tashi lafiya?"
Ba kallonta take ba amma daga yanayin yadda muryarta ta fito wajen amsawa ta fahimci har yanzu murmushin take yi.
"Mun tashi lafiya, Ya bakunta kuma? Ko da yake ai naga su Samirah sun saka kin saba tuni."
Bata ce komai ba illa wasa da karshen skirt dinta da take yi tana cigaba da murmushin da zata kira na dole, don bata san me yasa zuciyarta ta kasa zama waje É—aya ba.
Hajiya Kilishi ta kalli ƙaton screen din Tvn dake tsakiyar falon dama sauran kayan kallon da aka jera akan hadadden stand ɗin Tvn da dubu tamanin da biyar ta bayar aka siyo shi sannan tace.
"Gidan shiru ke kaÉ—ai baki ko kunna Tv ba?"
Da wani murmushin a fuskarta tace.
"Ai ba'a hada Tvn ba har yanzu Mami."
Muryarta ta fito ƴar ƙarama a cikin shirun dakin, kamar tana son ta shaidawa Hajiya Kilishin ƙanƙanta da kuma rauninta.
"Baku gaya min ba ai, gashi jiya kuwa yaro mai gyaran satelite ya shigo har cikin gida, da ya karaso ya hada muku, amma a bar ki a gida haka shiru, shi ya fice ya tafi hadaniyar gabansa ba zai tuna da wani sha'anin Tv ba.
Sai ta sake girgiza kanta tana cigaba da murmushin.
"Ba komai Mami, duk sanda aka sa baza'a makara ba ai."
Ta fadin hakan lokacin da take kokarin mikewa, amma a lokaci guda Hajiya Kilishin ta tsayar da ita.
"Ina ziki je kuma?"
"Mami, kayan breakfast zan kawo miki."
Ta faÉ—a taka kallonta, sai ta girgiza kanta.
"Barsu nagode, dawo ki zauna."
Umarnin dake cikin muryar ya kaɗa hantar ta, taji wani abu yana ƙoƙarin ɓallewa daga cikin zuciyarta, amma sai tayi saurin ture hakan ta dawo ta zauna ɗin, hannunta na taɓa hannun kujerar gefenta kamar tana neman taimakon ta.
Kuma zaman nata sai ya zama kamar shine farawar wani shafi na farko a rayuwata, don watakila idan zata bada labari, zata fara ne ta kansa, daga lokacin da kafafunta suka sake komawa kan carpet É—in nan da kuma lokacin da muryar Hajiya Kilishi ta sake ratsa shirun É—akin da cewar.
"Amina kunyi waya da mutanen gida kuwa jiya?"
Sai da ta haɗiye wani dunƙulen abu da bata san sunansa ba a kirjinta sannan ta girgiza kai.
"A'a Mami, na kira su dai jiyan amma bai shiga ba."
"Ina wayarki?" Kai tsaye ta sake wata tambayar da ta fito kamar tsawa.
Kan Tv's stand É—in nan ta nuna inda bayan fitowarta da safen ta saka ta a caji.
"To matso ki kira su."
Wannan karon sai da ta kalle ta tsawon wasu sakanni fuskarta na haskawa da mamaki sannan ta matso a hankali zuwa wajen wayar, lokacin da ta cire ta daga caji taji kamar hannunta na rawa amma tayi saurin fara dannawa ta lalubo nambar Amma.
Sai da ta sake kallon Hajiya Kilishin da murmushin fuskarta ya rage tasiri kafin ta kara wayar a kunnenta, kuma cikin wata iriyar sa'a, bugu ɗaya biyu sai Amman ta dauka, sautin muryarta kadai ya doka wani abu a ƙirjinta tun kafin ta fahimci abinda take faɗa.
"Amina yi haƙuri, tun jiya bamu kira ki ba, muna asibiti ne sai da safen nan muka fara samun nutsuwa..."
"Asibiti? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!... Me ya faru Amma? Me ya faru?"
A yanzu ta tabbatar hannun nata rawa yake, don tana jin yadda yake tafiya tare da bugun zuciyarta.
Daga cikin wayar Amma tayi ƙokarin gyara muryarta kaɗan sannan tace.
"Aminu ne mai mashin ya taka shi jiya da daddare a wajen aiki, amma sun ce jikin nasa da sauƙi kar ki ɗaga hankalinki, yanzu mu ma zamu shiga mu ganshi..."
Zancen ya katse a lokaci guda da Amina ta nemi wayar a kunnenta ta rasa. Hajiya Kilishin da a yanzu ke tsaye akanta riƙe da wayar tasa hannu ta ɓare bayanta ta fito da batirin ta jefar dashi gefe, sannan ba tare da ɓata wani lokaci ba ta karya wayar gida biyu itama.
Kuma taku biyu kawai ya mayar da ita baya kan kujerar da ta taso, ta cigaba da kallonta har a yanzu da ragowar murmushin nan a fuskarta kafin muryarta ta fito cikin wani irin sauti da yake ainahin halittar ta, sautin da yake manne a kirjinta tare da zuciyarta dake ƙawata mata tarin hanyoyin da kullum suke ɓullewa ga nasararta, sautin da a duniya kaf, mutum huɗu ne kawai suke sanin da kasancewarsa, sai a yau da ta zabi Amina ta zaman cikon ta biyar ɗin, cikon da take fatan zai zama mataki na ƙarshe da take da yaƙinin zai kai ga nasararta.
"Barka da shigowa cikinmu Amina."
Kalamai biyar ɗin data furta kenan wanda ta lissafa cewa adadinsu ya dace da lambar matsayinta, murmushi kan fuskarta cika taf da tarin kalaman da take shirin ɓare mata a yanzu wanda zasu sa ta fahimci wacece Kilishi tun daga tushe da kuma dukkanin abubuwan data aikata a rayuwarta.
***
Wane shiri Ma'aruf ke yi akan ƴarsa Hameeda da kuma Ruƙayya?
Me ya yankewa zuciyarsa akan Amina da har Ishaq ya fahimta?
Ku gaya min ina rayuwar gidan nan ke tafiya?
Munaya and Ishaq, me kuke tunani?
Hajiya Kilishi...
Ina gaya muku har yanzu sunan matar nan kawai kuke ji, next chapter zata buÉ—e muku abubuwa da yawa game da ita...
Babi na gaba zai nuna muku me ake nufi da ainihin kissa da kisisina irin ta mata kamar Kilishi, wanda suka yarda cewa kowacce mace zata iya samun duniyar da take so a tafin hannunta... Ba boka ba malam!
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.