Farar Wuta Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Farar Wuta Book 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 3 of 9
BABI NA BAKWAI
~~~~~~~
"Mark my words, idan har wani abu ya same ta, babu wanda zan saurara Ishaq, babu wanda zan saurara."
Muryar Ma'aruf, ta faɗa a cikin ɗakin asibitin da misalin ƙarfe takwas na wannan daren, yana zaune daga gefen gadon ɗakin da waya kare a kunnensa yayin da daga tsakiyar gadon, wata ƙaramar yarinya ce kwance tana bacci.
Da hannunsa É—aya ya shafo kansa sannan ya sake cewa.
"Saboda me? Shekaru biyu ta hana ni ganinta amma yau sai na tsince ta a tsakiyar wannan gidan arnan? Idan kana yiwa Allah ka gaya min cewa zan iya maka ta a kotu a hukunta ta."
Daga cikin wayar Ishaq ya sake cewa.
"Ka taimaka ka fara kwantar da hankalinka yanzu B, ba dai yarinyar tana hannunka ba? ai anci rabin matsalar abinda zai biyo ba mai yawa bane. Sannan na tabbata shi kansa Baffan yanzu idan yaji komai, ba zai sake goyon bayanta ba, mu godewa Allah ma da ba'a dauki shekarun da suka fi haka ba."
Baice komai ba ya cigaba da motsa yatsunsa a cikin gashin kansa kawai yana sauraren duk bayanin da yake yi kafin wayar tasu ta kai ƙarshe, suka yi sallama bayan Ishaq ɗin ya gaya masa cewa sai jibi zai dawo don aiki ya kaishi wani gari a can hanyar Abuja.
Ma'aruf ya sauke wayar a lokacin da idanunsa suka sake komawa kan yarinyar, Hamida ce... ƴarsa, har yanzu tunaninsa ya kasa gasgatawa, ya kasa yarda cewa ita ɗin ya gani bayan tsawon shekaru rabonsa da ita kuma a wani waje da bai taɓa zato ba.
Tsawon sati uku kenan da ya sadaukar da duk lokacinsa da komai wajen ƙoƙarin daidaita al'amarin da yake faruwa a kamfanin nasu. Wata irin asara suka yi da bata da tushe, bata da reshe kuma babu wani abu da yaja zuwanta. Dawowarsa kawai aka wayi gari da report din ɓatan maƙudan kuɗaɗen da babu ma wanda ya kula dasu sai a lokacin da aka zo fitar da wani kaso na harajin ƙarshen shekara da ake cirewa a duk ƙarshen kowanne wata.
Anyi duk wani bincike amma babu abinda aka tarar daga ƙarshe, don haka Baffa yace a rufe zancen kawai su karɓi hakan a matsayin ƙaddara,. kasuwancinsu ya cigaba da gudana, amma haka kurum sai zuciyarsa taƙi bashi cewa hakan daidai ne, wannan aiki ne da ya riga ya saka ransa akai... Ba yana yinsa don yana sonsa bane yana yinsa ne don ya zame masa dole, dolen da a cikinta ba zai taɓa bari a lissafa da wata tangarɗa ba, don haka ya bi maganar Baffan ya cigaba da gudanar da aikinsa a gefe guda kuma shi da Faruk suna cigaba da bincike akan lamarin.
A cikin binciken nasu Faruk ya samo wani mutum ne a cikin ƙananun ma'aikatan wajen da yace yana yana da wani bayani da zai iya basu, amma bayan Faruk ɗin yaje ya same shi har gida, sai ya ƙi bashi haɗin kai game da hakan duk kuwa yadda yayi dashi. Sun fahimci tsoro ne ya kama shi don haka shi yace zai je ya same shi duk kuwa da magiyar da Faruk ɗin yayi masa akan cewar kar yaje, magiyar da ya riga ya san ta mecece don dukkansu du niyun sun san cewar idan lamarin ya ɓaci babu wanda zai iya kallon Baffan a cikinsu da wani bayani.
Amma shi kansa Faruk ɗin ya san cewa tunda har ya saka ransa babu abinda zai tsaida shi don ba tun yau ya sani cewar idan har ya furta abu zai yi to tabbas zai yi ɗin, bai taɓa ganin ya sa kansa yin abu ya fasa ba.
Don haka kai tsaye bayan ya tashi daga aikin ya nufi unguwar sabongari da address É—in da Faruk din ya turo masa don ba yadda zai yi. Ya isa da kyar bayan ya haÉ—a da tambaya sannan kwatancen ya tsayar dashi a daidai kofar gidan mutumin da yake nema.
Sunansa Okafor, wani dattijo ne arne daya dade yana aikin shara a kamfanin, ya san shi tun lokacin da idan sun dawo hutu daga makaranta yake zuwa kamfanin, kuma har sai bayan ya fara aiki ne sannan aka ƙara masa matsayi zuwa aikin hada takardu saboda tsufan da ya kama shi, ya kalli takurarren gidan dake gabansa, mutane ne ke ta fitowa daga ciki kamar gidan tururuwa, a ransa ya ayyana cewa idan har Okafor yana da sa'a watakila zaman gidan ya kusa kare masa shi da iyalansa.
Wani saurayi da ba ko riga a jikinsa sai gajeren wando da kuma sarƙa ya samu ya raka shi zuwa cikin gidan, kuma duk inda suka wuce juyowa ke an kallonsu da mamaki saboda manyan kayan dake jikinsa, nasa mamkin ya fara ne daga lokacin da suka shiga ciki inda yaga ashe gidan wani irin ƙato ne mai kuma tsawo, ga tarin ƙofofi birjiki daga kowanne gefe sannn da ɗimbin mutanen da ya san zasu iya tashin unguwa guda, ƙaton tsakar gidan ya cika taf da kaya da kuma igiyoyin shanya kota'ina, ga kwata layi-layi dake tashin wari kamar bola aka buɗe, sannan hayaniya kamar zata fasa kunne.
Ba shiri ya haɗiye yawu yana sake damƙe mukullin motar dake hannunsa lokacin da idonsa ya fara arba da tiƙa-tiƙan mata sanye da ƙananan kaya suna ta harkokinsu tare da maza da kuma tulin yaran dake yawo koina, daga can gaba ya hango wasu suna faɗa, mata biyu ne sai ihu-ihu da zage-zage suke cikin yarensu, yaga masu raba su basu da yawa kowa harkarsa kawai yake a wajen.
"Abeg no vex eh, this is Mr. Okafor's room." (Kar ka damu dasu kawai, ga É—akin Mr. Okfor É—in nan.)
Saurayin nan ya katse shi lokacin da suka tsaya a kofar wani ɗaki mai ɗauke da ragwajajjen ƙofar net. Sai kawai ya gyada kansa sannan cikin nasa kwantaccen turancin yace da saurayin ya fara shiga ya sanar musu zuwansa tukunna, kuma minti guda bayan tshin hayaniyar da ya jiyo a ciki sai saurayin ya fito yace zai iya shiga. Hannunsa ya zaro dubu guda a cikin aljihunsa ya miƙa masa, ai kuwa ya washe baki yana godiya gami da sake buɗa masa ƙofor ɗakin.
Da takalmansa ya shiga amma har a jikinsa yana jin dattin da yake takawa akan baƙin carpet ɗin ɗakin, kuma rashin iska da wari ko ƙansnin wani abinci ya hau kansa a take, amma yayi kokarin dannewa ta hanyar murmushi wa tarin al'ummar ciki dake ta ɗebe kaya don sama masa waje ana faɗin.
"Welcome sir."
Shi kansa Mr. Okaforn jikinsa rawa yake yi na ganinsa balle kuma tarin ƴaƴan sa da kowannensu ya riga ya zube a ƙasa, kuma cikin gurbataccen turncinsa Mr. okaforn ya shiga faɗin.
"Ban san da kanka zaka zo ba yallabai, ai na cewa yallaɓai Faruk ne ya bari sai na dawo aiki tukunna, matata ce ba lafiya muna ta faman jinyarta."
Ya fada yana nuna wata tsohuwa dake kwance cikin tarkacen kaya, daga nesa ƙaryane ka banbance ta ma da tarin kayan dake wajen.
Ya amsa masa bayanin yayin da ya dawo da kallonsa daga kan matar zuwa tarin ƴaƴan da suka zube a gabansa, kusan su tara wanda da kammaninsu kaɗai ya san duka ƴaƴan Mr. Okaforn ne, yaji a ransa yana ƙudirta cewa ya riga ya gama samun bayanin da yake nema don romon da yake shirin kwaɗaitawa Mr.Okaforn wani abu ne da ko mahaukaci ba zai ƙi tayin ba.
Sai dai ɗan adam baya taɓa hango tazarar faruwar wasu al'amuran, don a lokacin da ya buɗe baki zai yi magana ne, a lokacin babbar ƴar Mr. Okaforn ta fito daga wani ɗaki ɗaya tal dake manne da falon, hannunta ɗauke da Hamidan da ta saba a kafadarta a lokaci guda kuma tana ƙoƙarin cusa wasu kaya cikin jakar data ratayo tace.
"Papa, make I run go drop their pikin that woman go eat me alive if she returned." ( Baba zanje na kai musu Æ´arsu, wannan matar zata iya cinye ji idan ta dawo.)
"Mary!" Mr. Okforn ya daka mata tsawar da lokaci guda ta dago da idanunta kuma lokacin gudan itama ta durƙushe kamar ƴanuwanta tana faɗin.
"Welcome sir."
Ya tuna yadda ta dinga rantsuwa jikinta na rawa tana gaya masa cewa kula da yarinyar take a wajen aikinta ce ta taho da ita saboda an kira ta cewar jikin mahaifiyar tasu ya tashi, idanunsa a rufe ya cigaba da hango ta sanda ta biyo shi har bakin motarsa tana fadin yayi mata rai ya bata yarinyar, kuma ya san cewa sanin da tayi cewa shi shugaban mahaifinta ne, shine kadai abinda yasa bata yi masa ihu ba.
A hankali ya taso, ya dawo daga gefen Hamidan dake baccinta har yanzu, tun a gidan ya fahimci cewa baccin da take yi yayi nauyi, don har yazo ya sanya ta a mota, sau ɗaya ta buɗe idanunta ta koma bata sake farkawa ba, jikinsa ya bashi cewar tabbas hakan da matsala don haka kai tsaye ya wuce da ita wani asibiti mai zaman kansa inda aka karɓeta da gaggawa kafin likitoci su tabbatar cewar maganin bacci aka bata wanda da alamu ma ta daɗe tana yinsa don jikinta babu kwari sam, a take aka bata gado aka shiga ɗura mata drip mai haɗe da ruwan magani.
Kuma sai bayan da ya sami kansa ne sannan ya iya kiran Mami ya gaya mata dukkan abinda ya faru, bai san me ya faru lokacin da suna waya ba, amma sai a wayar Samira ta kira shi daga baya ta shaida masa cewa gata nan zuwa ta cikin hayaniyar da yake jiyowa a gidan.
Ya sake gyara zamansa a hankali yana kallon fuskar yarinyar, wani irin abu yake ji yana ratsawa har can bangon zuciyarsa, yana fito da tarin kaunar daya daɗe da binne ta, yawan ƙaunar yana sashi ganin irin ƙoƙarin da yayi a cikin shekaru biyu nayin nisa da yarinyar, yana sa shi alaƙanta abinda yake ji da cewar haka sauran iyaye ke ji idan suka kalli abinda yake gudan jininsu. A hankali ya lumshe idanunsa yana tuno kalaman Rukayya wanda su suka yi sanadin raba shi da ita.
"...bata da lafiya har yanzu Ma'aruf, ƙwaƙwalwar ta bata iya gane kowa, ka matsa daga rayuwarmu na wani lokaci, watarana lokacin da kansa zai zabi dawowarka."
Kuma ya yarda da maganarta ne a wancan lokacin ba don komai ba sai don nauyin laifin da ya san nasa ne.
Don ranar da ya shaƙe Ruƙayya bayan ya karɓe yarinyar daga hannunta yayi wulli da ita, a wannan ranar ne kanta ya bugu da kujera, har buguwar ta haddasa wani ciwo a ƙwaƙwalwar ta wanda da duk da karancin shekarunta aka fahimci cewa bata iya gane mutane a lokacin, kuma sai likitoci suka bada shawarar cewar a ƙaiyade iya adadin mutanen da zata iya sani a ƙwaƙwalwar tata har sai ta fara wayo tukunna, don haka sanin cewar gidansu cike yake da mutane yasa Baffa ya bada umarnin cewa ko bayan an yaye ta baza su karɓe ta daga hannun Ruƙayyan ba sai tayi wayon da za'a tabbatar ciwon yayi sauƙi tukunna.
Kuma bayan hakan sai Ruƙayyan ta sanya shi cikin wannan lissafin shima, tace.
"Ka taimaka kayi nesa damu Ma'aruf, wannan rayuwar ba itace mafarkina ba, ko kaɗan ba haka nake hango abubuwa ba a lokacin kake gaya min, kuma Allah ya sani na yin dukkan ƙoƙarina wajen gyara maka rayuwar amma ka ƙi barina don ban kasa ba, don haka ina so mu ka barmu mu gyara tamu, Hameeda baƙuwa ce a duniyar nan bata san komai ba, dan Allah kar son zuciyarka ya hana ka bari ta gina tata rayuwar. Allah ya sani ina tsoron kasancewar ta kusa da kai, bata da lafiya har yanzu Ma'aruf, ƙwaƙwalwar ta bata iya gane kowa, ka matsa daga rayuwarmu na wani lokaci, watarana lokacin da kansa zai zaɓi dawowarka."
Kuma bayan wannan ranar bai sake ganin Hamidan ba, abinda ya sani kawai shine a cikin shekaru biyun ya tura mata isassun kuɗin da ya san sunyi yawa ma wajen kula da yarinyar, kuma a watanni shida da suka wuce sanda aka ce Ruƙayyan zata yi aure ya san cewa sun kai ta wani asibiti a makkah, ba zai iya zuwa ba a lokacin don haka Baffa ya tura Hajiya Kilishi da Shukra da kuma wata ƙanwar Hajiya Maimuna suka je can suka duba ta suka dawo.
Yaji kansa yana ɗaurewa da tsananin mamakin da ya kasa lissafawa, tsawon lokaci... tsawon shekaru an hana shi da yake mahaifinta da kuma ƴanuwansa raɓarta akan dalilin da har iyayensa suka tsaya akansa, don tun su Samirah na naci da ƙorafi akan suna zuwa gidansu Rukayyan ana hana su ganinta har sai da suka daina suka cire ta a ransu, sai gashi yau ya tsince ta a irin wannan gidan, tsakiyar sabon gari zagaye da tarin arnan da bai san adadinsu ba.
A lokacin ƙofar ɗakin ta buɗe, wata Nurse ta shigo da takardar jerin magungunan da za'a siya kafin farkawarta kamar yadda likitan ta shar'anta, da yatsa daya kawai yayi mata nuni da ta ajiye akan drawer dake gefe, kuma budewar kofarta wajen fita yazo daidai da shigowar Hajiya Kilishi da kuma Samira dake bayanta riƙe da kwandon abinci, duk da halin da yake ciki sai da yaji zuciyarsa tayi fatan yarinyar nan tana tuna Allah kamar yadda take tuna abinci.
"Innalillahi wainna ilaihir raji'un, me ya faru mai gaskiya? A ina ka samo ta?"
Muryar Mamin ta faɗa, sai da ya taso ya miƙe sosai sannan ya shiga gaishe ta, ta amsa tana ƙoƙarin riƙe hannun Hamidan da ya saki.
Kuma sautin muryarsa a hankali ya shiga yi mata duk bayanin da zai iya a wannan lokacin yayin da take kallonsa da wannan tsananin kulawa da kuma damuwar da kullum ke É—amfare a fuskarta game dashi.
"Kar damu, komai zai daidaita insha Allah Ma'aruf, daÉ—in abin komai bai ja da nisa ba, ka kwantar da hankalinka dan Allah mu bi komai a sannu kar ka damu kanka da wani tunani, Baffa ya dawo na shaida masa, shima yayi mamaki sosai amma yace a bari ta fara farfaÉ—owa tukunna kafin komai ya biyo baya, don haka mu tsaya anan, mu tsaya a iya nan dan Allah mai gaskiya."
Roƙon da take ya san har da wani bari na muryar Baffa a ciki, don dukkaninsu sun san irin abinda zai iya, don haka bai ce komai ba kawai yayi shiru yana sauraren ta, sauraren da a cikinsa ta fahimci cewa ko ta cigaba da maganar ba fahimtar ta zaiyi a lokacin ba don haka sai tayi shiru kawai ta juya tana kallon fuskar Hamidan.
A lokacin Samirah ta zubo abinci a plate ta miƙo masa, kuma ganin ƙoƙarin ta ne kawai ya gaya masa cewa ya kamata yaci abincin ba wai don ya so ba, don haka ya karɓa a lokacin da itama ta koma gefe tana kallon fuskar yarinyar.
A cikin tunaninsa yaji Samiran na waya dasu Munaya da kuma amaren da wai dawowarsu kenan daga wajen gyaran jiki suna tambayar sunan asibitin zasu zo, amma Mami ta karɓi wayar tace duk suyi zamansu don in suka ce zasu taho ɗin a yanzu ba'a san adadin wanda zasu biyo su ba kasancewar suna dab da fitowa yanzu ma wasu ƴanuwan Hajiya Maimuna ma suka sauka daga jigawa.
Ma'aruf na jinsu bai ce komai ba, wayarsa kawai yake kallo idanunsa na wasa da adadin messages É—in dake shigowa bi da bi suna nunawa akan screen É—in, amma a cikin zuciyarsa tunawa yake da zagayen halin da yake ciki bayan wannan, cewar wannan shirye-shiryen bikin da ake shirin farawa har dashi a lissafin.
Don tun daga lokacin da ya samu wannan takardar mai dauke da sunan Amina, kuma ya tabbatar cewa zancen auren bai lalace ba kamar yadda yayi fata a farko, sai kawai ya mayar da hankali kan aikinsa kuma yawan aikin ke sa shi sha'afa da zancen auren sai wasu abubuwa kamar wannan sun faru da zasu tuna masa cewar shima yana jiran faruwar auren ne don ya fara nasa sabon binciken da har cikin zuciyarsa yake jin cewa wannan hanyar zata iya kaishi ga nasarar da ya shafe shekaru yana lalubenta a cikin duk wani abu da ya danganci kayan Jamal.
Misali irin lokutan da Mamin ke kiransa ta bashi wasu bayanai na cewar an kai kaya gidansu yarinyar ko kuma ya turo da wani adadin kudi za'ayi abu a kaza, abubuwan da suke sa shi yana jin cewa da gaske auren zai yi don Baffa ma ya kafa sharaɗin cewa gidan zai dawo ɓangaren da Baba Alhaji ya taɓa zama, yaje kamar yadda Aa ya marta har sau biyu yaga gyaran da ake yi, amma daga haka bai kara tunawa ba ya cigaba da harkokinsa don damuwarsa ba sai ta komai yayi daidai bane, ta ya iya kammala abinda ke gabansa ne kafin lokacin don ya sami nutsuwar da zai yi dukkan bincikensa akan yarinyar.
Ya cije leɓɓensa a hankali yana tuno kalaman da Faruk ya faɗa masa kwanakin baya.
"Sake yin aurenka shawara ce mai kyau B, amma me yasa sai wannan yarinyar? Kace mahaifinta ba wani bane, kuma kaima ba saninta kayi ba balle ince kana sonta ne, beleive me akwai tarin ƴaƴan masu kuɗin da har layi zasu yi idan kace zaka zaɓa."
Ya faɗi hakan ne ranar da Baffa yasa aka raba katin ɗaurin auren ga kowa a Office ɗin kuma mamaki ya kama su ganin cewa har da sunansa, don haka Faruk ɗin yayi wannan ƙorafin ne bayan ya shaida masa yadda al'amarin ya kasance. Kuma kallonsa kawai yayi a lokacin da dukkan tunanin da bai zo kansa ba, cewar iyayen yarinyar ba masu arziƙi bane, ya sani cewar maza irinsa basa aure a irin waɗannan gidajen, misali aurensa da Ruƙayya shine daidai, don ko irin manyan mutanen da suka halarci ɗaurin auren nasu daga bangaren mahaifinta ma wani abu ne.
Amma baya jin ko bashi da wani abu da yake nema daga yarinyar hakan zai dame shi, don ba auren ko itace a gabansa ba, kuma kuɗin mahaifinta ba abinda zasu tsinana masa kamar yadda na mahaifin Rukayya ma basu kare shi da komai ba sai abinda yake ganin yanzu har dasu a silar sa. Tuna cewar bai ma taɓa ganinta ba har yanzu yasa ya jinjina kansa a hankali, bai sani ba idan ya kamata a kira wannan al'amarin auren gaske bane wannan.
"Ina kika baro masu yin cin-cin É—in ne da kika biyo ni?"
Yaji Mami na tambayar Samirah bayan ta ajiye wayar, sai dai bai bari ita ɗin ta bata amsa ba ya miƙe tsaye, muryarsa da zurfi yace.
"Zanje in dawo."
Sai ta girgiza kanta..
"A'a, kaje ka kwanta ka huta kawai, ni zan kwana da ita anan, ka tafi da Samira ka ajiye ta a gida sai ta ɗebo min ƴan kayan kayan da zamu buƙata zuwa, zan kira Malam Sani ya kawo min."
Ya cije leɓɓensa kaɗan yana bin maganganun nata kafin ya gyaɗa kansa sannan yayi mata sallama ya juya tare da ɗaukar hularsa da ya ajiye daga kan wata drawer a gefe.
Samiran ta biyo bayansa, kuma har ya isa waje jikin motarsa, zuciyarsa na riƙe da yadda muryar Mamin ta fito da tsantsar damuwa da kuma kulawar da ba mai iya ƙiyasta yawanta, a lokuta da yawa yasha ƙiyasta yadda zuciyarta ke iya ɗaukar damuwar tarin mutane da tarin kyautatawa ga duk wani mahuluki da zai shigo hanyarta balle kuma shi da kowa ya sani cewa matsayinsa daban ne a wajenta.
Ya san itace ja gaba akan komai na bikin nan, amma duk da wannan hadaniyar ta tsallake ta zata zauna, bai san irin son da yake yiwa Hajiya Maimuna mahaifiyarsa ba bayan tsananin girmanta da yake gani, amma Mami zai ajiye ta ne gefe ya tara dukkan ƙaunar waninta a wani gefen, don yana daga cikin abinda yasa yake son yayi tsawon rayuwa mai kyau don ya kyautata mata.
A sanda lokaci ke wucewa da wannan tunanin a zuciyarsa, a lokacin Hajiya Kilishi ke girgiza kanta daga cikin ɗakin asibitin bayan fitarsu, zuciyarta na ƙara gaya mata cewar ba haka tsarinta yake ba, ita ke da ikon ƙaiyade duk mutanen da zasu shigo rayuwar Ma'aruf, don haka bata zana cewar abubuwan da ya rasa a baya zasu waiwayo shi nan kusa ba. A tunaninta yadda yarinyar tayi masa nisa haka tayi a zuciyarsa ma, a tunaninta ko zai neme ta sai shekaru sun ja tukunna a lokacin da hakan ba zai shafi tsarinta ba, amma har me tayi a yanzu da duniyarta zata fara girgizawa?
Ta ƙara girgiza nata kan a fili tana cigaba da kallon fuskar Hamidan da kuma yadda ɗan ƙaramin ƙirjinta ke ɗagawa wajen fitar da numfashi mai nauyi, a ɗaya gefen ƙwaƙwalwar ta tana hango idanun Ma'aruf da suka tafi ɗauke da tsananin damuwa da kuma ƙaunar yarinyar dake nunawa ƙarara.
Ta kuma girgiza kanta wannan karon a hankali, ai alƙawari ne cewar ba zata taɓa iya raba zuciyar Ma'aruf tare da kowa ba, sau nawa zata zana cewar shi nata ne ita kaɗai? Ba har da tsoron wannan yasa ta haɗa aurensa da yarinyar data san ba zata taɓa tasiri akansa fiye da ita ba? Ko uwar data haife shi a yanzu ta isa ta raba soyayyar sa tare da ita ne balle kuma wannan sabuwar halittar? Ta ƙara gurgiza kanta, ba lokacinta bane yanzu, ba lokacin da zata shigo rayuwarsu bane yanzu, bata tsara mata waje ba sam.
Numfashin yarinyar har yanzu take kallo tana so ta kai karshen lissafinta... Lissafin da ta fara tun a lokacin da wayarta ta suɓuce daga hannayenta a lokacin da Ma'aruf ɗin ke mata bayanin samun yarinyar. Kuma wucewar wasu sakanni kawai, tunanin nata ya kai kan gaɓar da kwakwalwarta tayi tanadinsa tun a gida...
Gaɓar da take shirin faruwa da zaren wani makamancin tarihin da ta taɓa ja a baya, fuskar Jamal ta haska a cikin kanta a ranar da ya shiga har cikin ɗakinta ya gaya mata cewa bata isa ba, wani murmushin ya suɓuce a fuskarta cike da fatan ruhinsa ya iya ganin yadda lokaci ke bata tarin damar dake ƙaryata kalamansa, tana fatan ace kabarinsa zai buɗe don yaga sabon saƙon da zata aika masa a daren yau wanda zai ƙara ƙaryata kalamansa fiye da cikin masaki.
Ta miƙe a hankali ta nufi wajen da ta ajiye jakarta, kan teburin da Ma'aruf ya ajiye hularsa, zata yi komai ne hankalinta a kwance don ɗakin asibitin shi zame mata mafaka mai kauri daga duk wani tunanin da zai iya taɓa farinta.
Ta gama tsara hotunan komai a cikin kanta har tayi musu fenti ma, sannan hannunta ya jawo jakar da niyyar buÉ—e ta....
***
A cikin ɗakin, da misalin ƙarfe goma na safe, Ruƙƙaya ta kalli mahaifiyarta da fararen idanunta dake shaida tashin hankali da kuma fargaba ƙulli-ƙulli, ta girgiza kanta tana share hawaye.
"Wallahi Maamah Hanan ƙawata ce ta haɗa ni da ita, tace ta taɓa yin aiki da wata ƴaruwarta suna da ƙoƙari sosai, shi yasa banyi tunanin komai ba na ɗauke ta a lokacin, kuma itama ta taɓa fada min inda take amma na manta."
Kukanta ya ƙaru lokacin da ta sake cewa.
"Na shiga uku Maamah, idan na rasa Hamida ya zanyi da rayuwata? Da me Ma'aruf zai sake kallona idan har babu ita?"
Hajiya Nafisa, mahaifiyar Ruƙayya na zaune a cikin ƙaton falon gidan na ƙasa, sanye take da wata doguwar riga irinta larabawan dubai, kanta daure da ƙaramin mayafin rigar yayi da wayarta ke riƙe a hannu.
Idanunta na kallon Ruƙayyan ne da tsananin takaici bayan tashin hankalin da suka tashi dashi na ɓatan Hamida, sai jiya da daddare jirginta ya sauka daga Paris, don haka ko da ta dawo ta hawo samanta bata nemi kowa ba tunda maigidan ma baya ƙasar. Sai a safiyar yau da ta tashi ne sannan ta san Ruƙayya bata gidan saboda haka ta nemi Hamida da mai aikinta Mary amma sai su Jamila da Aisha masu share-share na gidan suka shaida mata cewar ai kwana biyu kenan Mary ta fita da Hamidan kuma bata dawo ba.
Saboda haka kai tsaye ta kira Ruƙayyan ta shaida mata cewar ba'a san inda Hamida da Mary suke ba, kuma wucewar minti talatin sai gata ta ƙaraso cikin tashin hankalin da yafi nata, kuma a zaton ta da tazo kai tsaye zata kira Maryn ko kuma ta bita zuwa address ɗin gidansu ta karɓo yarinyar amma sai gashi tana gaya mata wai lambar Maryn bata shiga kuma ita bata san inda take ba.
Allah ya sani idan har tana da wata matsala a rayuwarta to akan Ruƙayya ne, don babu abinda ta nema ta rasa a duniyar nan illa haɗin kan ƴar tata, ita kaɗai ce mace kuma babba a cikin maza huɗu amma a abubuwa da yawa ta kan gwammace mu'amalarta da mazan akan ita.
Ta sani cewa tun daga lokacin da Ruƙayya ta fara hankali a duniya ta rasa ta, don daga lokacin da ta ɗauki zuciyarta ta danƙa a hannun Ma'aruf shikenan take zaune da ƙirjinta fanko, don bata kara marmarin saka wani a zuciyarta har ta kalle shi da daraja ba kamar shi, tun yana cikakkensa na mutum har ciwon da zata iya kira na hauka yazo ya same shi, haka akayi auren tana murna su suna jiye mata baƙin ciki, kuma ko kafin ta haihu takaici iri-iri sun sha shi, sai da ya juye ƙwaƙwalwar ta tsaf ya goge wannan Ruƙayyan da take a baya, ƴar gayu mai cike da izzar da ko a cikin ƴaƴan manya ake samun masu kwaikwayon ta.
Ya canja mata yarinya zuwa bagidajiya irin matan da basu san komai ba sai zaman aure, ɗaya daga cikin abubuwan da ba zata manta ba shine lokacin aurenta har Lagos tasa aka nemo mata wasu ƙwararrun chefs(masu girki) mata bama maza ba don sanin halin Ma'aruf ɗin, amma wucewar sati guda Ruƙayyan ta bugo mata waya cewa ya sallame su yace shi girkinta yake so, kuma duk ƙin Rukayyan da girki haka ta ajiye ra'ayinta pa gefe ta shiga makarantar koyon girki tsawon watanni don kawai farin cikinsa, abubuwan da ta canja a rayuwarta don Ma'aruf baza su lissafu ba, don a abubuwa ne da ko na nesa zai hango su balle na kusa.
Don haka a lokacin da ta fahimci cewa da gaske tana shirin rasa ƴar tata, a lokacin ta miƙe tsaye tayi wani yunƙuri da bai bawa Rukayyan zaɓin komai ba illa bin umarninta, kuma sa'arta ta zarce har bayan rabuwar tasu ta cigaba da jin maganganunta zuwa yardar da tayi ta auri Alhaji Ahmad, amma zata rantse cewar zamanta baiyi nisa a gidan Alhajin ba fitinanniyar zuciyarta ta sake karkatowa zuwa shafin da take zaton sun barshi kenan har abada wato Ma'aruf, don haka auren bai je koina ba ta fito.
Ƴarta Hamida bata taɓa damunta ba don a tunaninta ita ba tasu bace, da tayi wayo ne mahaifinta zai karɓe ta koma wajensa, don haka bata ko waiwayarta a al'amuranta ta Ruƙayyan take yi. Ashe duk ub*n shirin da suke yi mata ita da ƙawarta akan alaƙarta da yaron nan Jawad a banza suke kashe ƴan kudadensu, ashe har yanzu zuciyarta bata dawo daga inda ta juya ba, Tunani take zata sake komawa wajen wannan yaron da a wajenta kudin da yake dashi ne kawai banbacinsa da wani mahaukacin.
Har ta buɗe baki zata yi magana, Ahmad, ƙanin Ruƙayyan dake bin Ashraf (wanda yayi aure) ya hawo saman daga shi sai gajeren wando da riga.
"Wai Maamah ki dawo ƙasar nan baki gaya mana ba. Sai da na shigo wajen 12 maigadi yake ce min ai kin dawo."
Ya faɗa yana ƙarasowa kusa da ita ya zauna, kuma sai a lokacin idonsa ya kai kan Rukayya dake kuka.
"Me ya faru?" Yayi tambayar ga dukkansu biyu.
Hajiya Nafisa ta nisa sannan ta bashi amsa.
"Hamida ce ba'a gani ba, ita da mai kula da ita."
"What? Ta yaya? Tun yaushe?"
"Itama bata gidan ai, sai da na dawo tukunna."
Ransa a ɓace yace.
"Me nake gaya mata a gidan nan Maamah, don me zata dauko wata ƙedara wai ita zata dinga kula da ƴarta, wai don ta iya turanci? Turancin banza su Hausawan ba su iya turancin bane?"
Hajiya Nafisa ta girgiza kanta.
"Ajiye wannan zancen Ahmad tunda komai ya faru, yanzu nemanta ne a gabanmu. Ya za'ayi?"
Kafin ya bada amsa, Ibrahim ya shigo riƙe da wayarsa a hannu yana faɗin.
"Is it true yarinyar nan ta ɓata? Umar just called me now wai ya ganki a waje ɗazu kuna tambayar Hamida."
Hajiya Nafisa ta gyaÉ—a kanta don ita yake kallo sanda ya shigo yana tambayar.
"Ƴansanda ɗin dake gadi a bakin titi muka tambaya suka ce mana tun shekaranjiya Maryn ta fita da Hamidan kuma basu dawo ba."
"Ya salam! This is bad, yanzu me ake ciki?"
Tambayar tasa Ruƙayya sake fashewa da kuka.
Ahmad yace.
"Akwai wani abokin Ashraf da ya taɓa zuwa nan yace min ya san ita mai aikin, ban ɗauko wayata daga ɗaki ba, Ibrahim kira shi."
Ya kalle shi.
"Wa zan kira?"
"Ashraf É—in zaka kira kace ya baka number B-man."
Wayar Hajiya Nafisa tayi kara a lokacin, ta kalli number dake kiran nata, mahaifinsu ne don lokacin da Rukayyan ta dawo tace bata san inda Maryn take ba shi ta kira ta gaya masa halin da ake ciki. Ta É—auki kiran ta kara a kunnenta, gaya mata yake yi cewa yasa an turo da Æ´an sanda gidan zasu zo su nemi bayanai don su kamo Maryn.
Kuma bayan ta sauke wayar kallon Rukayyan ta cigaba da yi a lokacin Amir É—an autansu ya shigo rike da kofin shayinsa ya zauna a gefenta yana bata hakuri.
Gayawa zuciyarta take yi cewa ba zata sake kuskuren rasa ƴarta ba a karo na biyu, bata son Ma'ruf amma idan har yanzu shine zaɓin Ruƙayya, shi abinda zai daidaita rayuwarta, to zata hakura kawai ta karɓi wannan ƙaddarar, zata dawo mata da Ma'aruf cikin rayuwarta ko ta wace hanya.
***
"Allah yayi miki albarka, Allah ya haskaka rayuwarki, Allah yasa ki zama haske a cikin gidan aurenki, Allah yayi riƙo da hannayenki wajen kyautata zaman ibadarki, Allah yasa ki zama sanyin idaniyar mijinki, Allah yasa masa tausayinki a zuciyarsa, Allah ya bashi ikon sauke nauyin duk wani hakkinki, Allah yasa ku zamewa junaku inuwar salama har a ranar alƙiyama, Allah ya sanya albarka a zuri'ar da zaku samu, Allah ya tashi rayukanku cikin rahamar ibadarku a lokacin da zaku koma gare shi..."
Duk wannan addu'ar tana fitowa ne yayin da ruwa ke sauka akan Amina daga bakin wata dattijuwa ƴaruwar Amma mai suna Gwaggo Balkisa da suka zo daga Nijar a lokacin da gidansu Amina ya cika da ɗimbin jama'ar dake shaida Kamu ko kuma wankan amarya da a ƙa'idar zuri'arsu Amma ake yinshi kwanaki kafin ɗaurin aure, al'amarin da yazo musu babu shiri don kwatsam suka samu baƙoncin ƴanuwan Amman tun daga Nijar mutane har motoci biyu.
"Bikin ƴarki ta fari guda kice ba sai mun zo ba Halima? Idan kince ku komai yazo muku cikin gaggawa an gaya miki mu yanzu muka fara tanadi ne? Har a aika da katinan ɗaurin aure amma ace wai iya maza ne kawai zasu taho? Yau ko Amina ba ƴarki ta sunna bace kina tunanin zamu ƙi halartar bikinta ko da kuwa tsakaninmu daku nisan bangon duniya ne?
Amina tana tuna yadda Amman ta sunkuyar da kanta tana saurare kafin tayi musu bayanin yadda al'amarin auren yazo, kuma fahimtar al'amarin ya kawo cece-kuce a tsakaninsu, waÉ—anda suke tsofaffi a ciki basu ga aibin komai ba don sun yarda cewa dama uba ke da ikon bada Æ´arsa budurwa zamani ne kawai ya canja komai, amma sauran suma sai tunaninsu ya zama irin na Amma cewar tasirin taimakon da Hajiya Kilishi ke yiwa Baba shi ya rufe idanunsa saboda auren bai kamata ba.
Sai da aka kira Aminan ta tabbatar musu cewa ita ta amsa auren da bakinta sannan kowannensu yayi shiru. Ta faɗi hakan a lokacin da take kallon idanun Amma dake ɗauke da sauran labarin da bata ƙarasa musu ba, sauran labarin da ko ƴanuwan Baban basu sanshi ba, tana jin yadda zuciyarta ke bugu akai-akai cike da fatan kar nauyin kalaman su rinjayi zuciyar Amma a wannan lokacin, amma bata yi maganar ba, bata ce komai ba.
Kuma hakan yana tuna mata da matsayinta na Ammar su, matar da tunda suka taso a rayuwarsu babu wata rana da zasu iya ɗorar da saɓanin cewa faɗa ya shiga tsakaninta da mahaifinsu, kuma ba wai ba'ayi ba, ta tabbata ana yi ma fiye da tarin wasu gidajen auren, kawai babu ƙofar da zasu gane ne. Ta tuna watarana da taji ta tana yiwa Aunty Safiyya nasiha bayan wani saɓani da ya shiga tsakaninta da mijinta.
"Sirrin mijinki sirrinki ne Safiya, idan kika buɗe kamar kin tonawa kanki asiri ne, ko wa kika budewa littafin da wannan karatun zaiyi ta kallonki koda kuwa kin cigaba da zama ko kuma kin rabu dashi, mafitar matsaloli da yawa a hannunki suke, da wuya ake kaiwa gaɓar da wani ne zai iya magance miki damuwarki..."
Zata lissafa Ammanta cikin manya-manyan jajirtattun mata a gidajensu, zata lissafa ta cikin irin mutanen da mata da yawa ya kamata su kalla suyi koyi dasu, don ita kanta babban makamin da take taƙama dashi na shirin tunakarar sabuwar rayuwar da zata yi, halayen Amman ne.
Sai dai duk yadda ta kai ga dake zuciyarta, a wannan lokacin da Gwaggo Balkisa ke mata wannan addu'ar tana zuba ruwan ɗumi daga saman kanta, kuka take sosai, kuka mai nauyi, kuka mara sauti, kuka da zata iya cewa ya zarce na amare da yawa, don nata kalolin taraddain dake cikinsa basu da adadi, ba na barin gida ne kawai ba, bana shirin fuskantar wata sabuwar rayuwa bane, wataƙila idan tace na shirin mutuwa alhali tana numfashi ne, hakan zai iya fassara rabin abinda take ji.
Tana sanye da wani farin saƙi dasu Gwaggon suka taho dashi, anyi mata ɗaurin ƙirji dashi kawai, yayin da gashinta mai laushi da yawa ke mannewa a fatar kanta da kuma wuyanta saboda ruwan dake bi ta cikinsa, tana zaune akan wani sabon turmi dasu Aunty Safiya suka siyo a cikin kayanta, yayin da sauran jama'ar bikin ke tsaitsaye zagaye da, gidan ya cika danƙam don har ƴan unguwa sun shishigo.
Taga lokacin da Tanti ta shigo cikin masu zuba ruwan ta ɗebo nata itama tana kwara mata tare da nata addu'oin dake ƙara karya zuciyarta suna saka kukanta ƙaruwa. A lokacin ne kuma fuskar Ma'aruf ta haska Idanunta, ranar da ta fara ganinsa, ranar da ta taɓa ganinsa, yana dariya a tsakanin mutanen dake taya shi murnar aurensa, babu shiri wani kukan mai ƙarfi ya sake suɓucewa a bakinta.
A haka sai da duk wani babba na danginsu da kuma dangin Baba suka zo suka yi sannan aka rufa mata wani farin saƙin, aka lulluɓeta dashi har ƙasa sannan kuma sauran ƴanuwan Amman da basu kai irinsu Gwaggo Balkisa ba suka shiga fesa mata turare ana guɗa. Al'ada ce sabuwa ga duk wanda ya halarci wajen, irin dangin Baba da kuma sauran ƴan unguwa don haka abin ya birge kuma ya ƙayatar ga duk wanda ya gani, kuma duk da cewar ba wani abinci aka raba ba, amma kowa ya tafi yana yaba abinda akayi.
"Na gaya miki su Nusaiba duk cewa suka yi baza su zo ba wai tunda ba ke kika fada musu ba, ba'a gaiyace su ba kenan."
Fatima ta faÉ—a da daddare bayan an gama komai mutanen duk sun tafi, wadanda suka rage iya na cikin gidan ne kawai.
"To ba shikenan ba, su sha zamansu. Dasu da masu karyatawa suna cewa karyane duk su ƙarata can, ranar da suka zo nemanki akace musu kina gidanki sai su san cewar da gaske ne."
Ummi ta faÉ—a tana kallon Aminar wadda a yanzu ta canja zuwa wata doguwar riga daga cikin É—inkin kayan sallarta, har yanzu bata fara amfani da kayan lefen nan ba duk kuwa da an karbo daga dinki, gani take kawai kamar basu gama tabbata nata ba har yanzu.
Dukkaninsu suna zaune ne a cikin dakinsu tare da ƙawayen su Ummin da kuma ƙawayen Amina da basu fi biyar ba, don kamar yadda Ummin ta faɗa ne da yawansu da Fatima ta gaya musu cewa suka yi ƙarya ne basu yarda ba.
Amina bata ce komai ba saurarensu kawai take yayin da take riƙe da ƙaramar ƴar Aunty Safiyya da tayi bacci a cinyarta, daga tsakar gida hayaniya ce kawai ke tashi cikin hausa da kuma zabarmanci daga ƴanuwan Amma, ƴaƴan Baban kurn dana Kawu Malam da kuma yayyensu Ummi duk suna nan, tabarmarsu daban ana ta hirar yaushe gamo, don ma ƴaƴan su Kawu Ibrahim dana Kawu Hamza basu ƙaraso daga Abuja bane, wanda su dama ba sa'anninsu bane, su hudu ne duk sunyi aure a can Abujan ɗaya ce kawai a Kaduna, don haka ko zasu zo tabbas sai ana i gobe ɗaurin auren ne tare da iyayensu, Kawu Hamza ne kawai yake da ƴa sa'ar su Aminar amma tana Ghana ta samu scholarship tana karatu.
Amina ta sani cewar ƴanuwan mahaifinta suna da arziƙin da tun lokacin da ta gama karatu zasu iya daukar nauyin cigabanta, amma basu yi ɗin ba, don duk yadda zumuncinsu yake da karfi akwai raunin taimako a tsakaninsu, kowa yafi maida hankali kan iyalansa kawai, kuma Baba mutum ne mai son dogaro da kansa a komai shi yasa shima bai cika tambayarsu abu ba idan har ba wanda hannunsu ya miƙo masa ba.
Ta lumshe idanunta tana sauraren hirar dasu Fatima ke yi a gefenta, Baba bai ƙara yi mata maganar auren ba har yau tun daga ranar da ta shaida masa amincewarta, amma a kodayaushe ta kalli fuskarsa sai taji ƙarfin gwiwarta na ƙaruwa, taji zata iya yin abinda yafi wannan ma idan har zai umarce ta. A hankali maganganun da ta gayawa Fatima ranar da tazo mata da labarin Ma'aruf suka shiga dawowa kunnenta.
"Fatima, Baba yasha wahala akanmu a rayuwarsa, yaga tashin hankalin da ba zan iya lissafa miki ba duk saboda mu. Lokacin da nake shekara hudu, Amma tayi fama da wata irin rashin lafiya bayan haihuwar Aminu, Baba shi yayi ɗawainiyar konai damu har tsawon shekara guda kafin ta warware. Lokacin da ina aji ɗaya a sakandire nayi wata rashin lafiyar ciwon ƙafafu har bana iya tafiya, wani abokinsa ya kwantanta masa wajen wani mai magani a garin Benue, ni dashi kawai muka tafi, daren farko a hanya mota ta lalace mana gashi motocin dake wucewa basa tsayawa saboda gudun ƴan fashi, a bayansa ya goya ni Fatima, muka dinga bi ta daji tare da sauran mutanen motar har washegari kafin Allah ya taimaka mu isa wani ƙauye.
Lokacin da zanyi jarabawar shiga sakandire, Baba ya sadaukar da lokacinsa da komai wajen koya min karatu ba dare ba rana, idan ya dawo daga kasuwa yana gyangyadi yana hamma zamu yi karatun nan, ranar da sakamakon jarabawar ya fito kuma naci, ranar na fara ganin hawaye a idanun Baffa, hawayen farin ciki.
Sanda Maryam bata da lafiya kuma karayar arziƙi ta same shi, kin sani Fatima, kin san yadda Baba ya koma kamar mai roƙo yana bi kusufa-kusafa don tara adadin kudin da ake buƙata. Kullum so yake mu girma, mu zama wasu mutane da al'umma zasu amfana suyi alfahari dasu, don haka ba lallai ne mu hango fa'idar wannan hukuncin nasa a yanzu ba, amma na tabbatar miki Baba ba zai yarda da zancen auren ne haka kawai ba, yace ya amsa musu ne saboda nauyin idanunsu da yaji, amma ni na sani cewar akwai wani abu daban da yasa ya amsa wanda ba lallai ne dukkanmu mu fahimce shi yanzu ba.
Kema na yarda da maganarki kamar yadda na yarda da ta Amma, sai dai bana jin zuciyata zata dauki taku sama da tasa, don ban san wane irin butulci zanyi ba idan har na kunyata mahaifina a idon duniya, gwara ko meye ya same ni da inyi sanadin hakan."
Kuma tun daga lokacin, shikenan ta kashe bakin Fatiman, bata kara cewa komai ba, bata ƙara ƙalubalantar ta da komai ba, ta fauwalawa ubangiji al'amarin kamar yadda itama tayi, har ta saki jikinta cikin su Ummi itama ta siya atamfar nan ta kai ɗinki.
"Gobe zanje in karbo ɗinkina, kuma zamu je ni da Maryam wajen masu sarƙar nan mu ƙara yi musu tuni."
Fatiman ta faÉ—a tana katse tunaninta. Sai ta gyada kai kawai sannan tace.
"Ɗazu Maryam take gaya min, wai ta samo me zuwa ta mana ƙunshi ma."
"Ƙunshi a ina? Me zuwa gidan ce zata miki? Ai kar ma ku fara wannan zancen, kuɗi zaki karɓo zoo road zamu tafi jibi-jibin nan, idan aka gyara miki gashin nan naki da hannayenki, ba wanda za'a sake yiwa bayanin cewa ke amarya ce."
Ummi ta faɗa, kuma tana ƙarashewa wata ƙawarsu ma ta ɗauka da faɗin.
"Ni wallahi naga ta kara haske ma akan ranar da muka zo daga kasuwa."
"To kina raba amare da gyare-gyaren jiki ne? Kawai ki tambaye ta sirrin tunda kema kin kusa fara naki."
Momi ta faɗa suna ƙyalƙyalewa da dariya, Amina kuwa ta haɗiye yawu, don ita bata san wani abu gyaran jiki ba, vasiline ɗin da take shafawa kullum shine dai, robar ko ƙarewa bata yi ba balle ta canja ko kuma ta waiwayi mayukan cikin lefen nan, abinda ta sani kawai shine idan har da gaske tayi fari to kuwa tabbas na tsora ne.
Don Allah ya sani idanunsa kaɗai idan ta tuno zuciyarta na bugawa da sautin dake barazanar saka ta kuka duk da ƙwarin gwiwar da take ji, tsoron daban ne don bata san me shi da kuma zuciyarsa suka tanadar mata ba... Ta rufe nata idanun a hankali tana jiyo hayaniyar su Aunty da Aminu daga waje akan motar da zata fara ɗaukan kaya, don gobe Tanti tace ya kamata a fara jere.
Tsoro take ji da gaske,
Tana ji kamar tana faÉ—owa ne daga wata sama mai nisa, kamar tana tafiya cikin idanun nasa inda ruwan cikinsu zai nutsar da ita da kuma numfashinta.
Abinda bata sani ba shine har yanzu a gaɓa take, bata shiga koina ba ma balle ta fara nutsewar!
***
Wasa farin girki!
#Aysha Shafi'ee.
#FikraWriters
#FararWuta.
Bari nayi sauri na wuce, a yafe min.ðŸ™ðŸ™ðŸ™