Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: TURKEN GIDA Part 1 by Janafty.txt
Chapter 96 of 103
"Gaskiya ne Sadiya mganar ki Haƙƙun."
 Hauwa ta faɗa tana mai jinjina kai. Munnira da ta yi tagumi ta na saurerena sai ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce" Kuma gaskiyan ku ne. To zan dage in sha Allahu. Kuma kamar na fara ganin wani alamu a wajen Nasir duk da bai yi mini mgana ba."
"Alamun me?
Na tambaya ina kallonta.
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce" Yanzu ba ya daÉ—ewa da mun fara mintina goma sai ya sauka kuma da ba haka ya ke yi ba"
Ni da Hauwa muka kalli juna kafin na maida kallona kan Munnira ina faɗin" You see. Akwai sanyi ajikinki kuma a yadda na fahimta ba ya wani jin daɗin ki yana dai yi ne saboda fita haƙƙi ki sai kin dage Munnira"
Tuni ta natsu tana faɗin" To zan dage gaya mini mafita. Allah Sadiya ba na ƙaunar kishiya"
Yadda ta yi mganar ne cikin tausayi ya sa muka tsintsire da dariya ni da Hauwa kamar za ta yi kuka ta ce" Don Allah ba dariya ba. Ku taimaka mini."
Sai na gyara zama ina faɗin" Za mu taimake ki amman ke ma sai kin miƙe kin taimaki kanki."
Sai ta ce ta ji duk za ta yi nan take na ɗauko wayata na kira Hajiya Surayya Halin yau. Bayan mun gaisa sai na ce zan haɗa ta da Munnira domin ta yi mata bayani ina ba ta wayar sai na ce ta shiga ciki yadda za ta samu damar yi mata bayani sosai. Sun ko jima suna waya sannan Munnira ta kawo min wayar nan Surayya ke faɗa min za ta fara shan na infection kafin haɗin kayan gyaran ya biyo.  Mun rabu akan Munniran za ta karɓi lambar wayarta su ƙarishe mgana.
Washegari ma ta ce za ta aiko ma da Munnira saƙon ko ba ta saka kuɗin ba tunda ta hannuna ne.
Duk mai bukatar mganin infection sadidan, ko mganin gyaran uwargida da amarya contact Surayya Halin yau.
+234 803 277 3332.
Kano Nigeria.
 Nuna Gwammaja har wajen ƙarfe goman dare. Domin da mazajen namu suka shigo gidan can bayan sallar isha'i gabaɗyansu suna falon Nene da ƴan'uwansu suna ta hira a tsakaninsu. Mu kuma muna ƙasa mun yi sallah mun koma muna ta zaman hira. A lokacin mganar haihuwa muke yi sun sin ina son na ƙara haihuwa ko daga yadda na ke kan hanyar yawon asibiti. Hauwa ce ke tambayata ya ake ciki ne yanzu? Kai na rausayar kafin na ce" To ana dai kan gwaje gwaje duk da kamar guda biyu suka rage amma Likitan tana ta ba ni tabbacin ba matsala ko ma akwai ba wacce za ta gagare su ba ne."
 Tare da Munniran suka haɗa bakin faɗin" In sha Allahu ma ba wata matsala."
Sai na amsa da Allah ya sa cikin wani yanayi na ce" Yallaɓai na son yara sosai. Biyu sun yi masa kaɗan ni na sani."
Hauwa ta ce" Amma ai ba ya nuna damuwa ko?
Sai na gyaɗa mata kai Munnira ce ta karɓe da cewa" Yallaɓai fa bai da damuwa. Damuwar su ne su Anty Bahijja. Ni da na ji ma wani batu amma dai ba ri na yi shuru."
 Sai na kalleta gabana ya faɗi saboda na san tabbas abin da ta ji ya shafe ni.
Da sauri Hauwa ta ce"Gwara ki yi shurun Munnira. Ni ma da na je Rano cikin azumi na ji batun a gida."
Sai kawai na kallesu kafin na yi mgana Munnira ta ce" Au kema? To me za a ɓoye mata ai mgana ce ba cewa muka yi ya tabbata ba. Kuma zaman tare kenan gwara mu faɗa mata ta san halin da ake ciki ko da ta faru ma ta san in da za ta bullo ma lamarin."
Cikin É—auriya na ce" Wai menene? Ku faÉ—a min ai ban isa na hana Allah ya yi ikon shi ba."
Hauwa ce ta kalleni kafin ta ce" A bakin Autar gidanmu na ji wai ƙannen Gimbiya ke faɗin Tafida za ta aura. Da na ce ban san da wannan mganar ba Innamu ta ce itama ta ji kuma a bakin makusantan ita Hajiyar Tafidan an ce daman tun farko Hajiya Nene da Hajiya tafidan sun so su haɗa zumunci na auran Gimbiya da Tafida Allah bai yi a wancan lokacin ba. Mutuwar mijinta ya nuna cewa rabon Tafida ce."
Ina kallon Hauwa amman na kasa mgana Munnira ta karɓe da cewa" Nima haka na ji wallahi. Kun san wacece ta min mganar?
Hauwa ce ta girgiza mata kai ni dai ko motsi ban yi ba
"Suwaiba ce fa kwanaki da ta zo gidana ta ke min zencen. Wai Anty Bahijja ta ce wannan karon Gimbiya Rabon Tafida ne. Shi ya sa ma wai ƙila aka dawo da ita wajen Nene."
Hauwa ta ce" Ni kaina na yi mamakin dawowarta. In aiki ne ai ba kullum ta ke zuwa ba kuma tunda tana da mota za ta iya zuwa a ranar kuma ta koma gida."
Munnira ta ce" Har Nasir na yi ma mgana ya ce mini shi bai sani ba gulma ce ta mu ta mata. Amma wallahi Sadiya na hango gaskiya ba rami me zai kawo mganar rami? Da man ta yi ta shige masa ni fa wallahi haushi ta ke ba ni."
Hauwa ta yi tagumi kafin ta ce" Ni kaina na fara hango hakan. Mganar fa daga bakin ƙannen Gimbiyar ta fito. Kin ga ko sun ji ana mganar ne."
 Ganin yadda na yi shuru kawai ina sauraran su ya sa Hauwa ta dafa kafaɗata tana faɗin" Kar ki damu Sadiya. Ni na san ko auranta Yallaɓai ya yi ba za ta sha gaban ki ba."
Munnira ta taɓe baki kafin ta ce" Ni wallahi da wata ta waje ne wacce ba a sani ba. Amma wannan Gimbiyar fa ban so. Sai Sadiya ta zama mujiya Allah su Anty Bahijja ware ta za su yi daman ya ya a ka cika?
Hauwa ta yi ajiyar zuciya kafin ta ce" Da wannan kuma da wanman."
Munnira cikin jin haushi ta ce" Har fa wani suna take kiran shi Daddy shi kuma ya ce mata me ne ma?
"Daughter"
Na faɗa ina kallon Munnira da ta yi tsaki kafin ta ce" Ke kuma wai duk kika ƙyale? Suna waya to?
Sai na gyaÉ—a kaina kafin na ce
" Suna yi mana."
Gabaɗayansu suka kalleni cikin mamaki sai na yi mirnishi kafin na ce" To ai ban isa na hana shi yin waya da ita ba tunda yar uwanshi ne ko da na aure shi suna tare. Hauwa Munnira daman tun da na ji Mijin Gimbiya ya rasu da irin hidiman da ta ke yi ma yarana na san gwara na shirya domin watan wata rana ko Yallaɓai bai yi tunanin auranta ba za a tusa masa tunanin. Bakomai in ma ya auro ta fatana Allah ya zaunar damu lafiya abu ɗaya na sani ba zan yi ma Yallaɓai baƙin ciki domin ya ƙara aure ba. Sannan ba zan yi faɗa da dangin shi ba amma na kudiri niyar in sun yi mini hallaci na yi musu in ba su yi mini ba wallahi ba zan yi musu ba sai dai gayyar ta watse."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.